Sabuwar Dokar Haraji Kan Duka Masu Amfani Da Account Na Banki

 

Sabuwar Dokar Haraji Kan Duka Masu Amfani Da Account Na Banki

A jiya alhamis ne dai gwamnatin tarayya ta fito da wata sabuwar doka wacce ta bukaci ‘yan Najeriya da su garzaya bankunan da suke amfani dasu su karbi wani sabon fom su cike.

Sabon fom din tsarine na dokar karbar haraji ta kasa ta bullo dashi ta hanyar hukumar tattara kudin shiga ta kasa wato FIRS.

Gwamnatin ta gargadi cewa duk wanda bai je ya cike wannan sabon Fom din ba to zai iya fuskantar hukuncin cin tara ko kuma ya kasa amfani da Asusun Ajiyar nasa.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da Nigeria ke kokarin kara nemo hanyoyin samun kudaden shiga sakamakon barazanar durkushewa tattalin arzikin da kasashe suka fada sakamakon annobar coronavirus.


Post a Comment

0 Comments