NANNY ( MAI RENO) HAUSA NOVELS

 NANNY..!*

_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕

*Wattpad:* *Janafnancy13 or Aisha Alto Alto.*


_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

*BISMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*

       *BABI NA UKU*

      *ASALIN LABARI*

  
*HAKIMI MANSUR ÆŠANBATTA* Shine asalin sunan mahaifin Tahir wanda gabanshi da bayanshi haifaffan garin ÆŠanbattan ne kuma ya fito daga tsatson Hakimin ÆŠanbatta ne daboda haka sarautar Hakimi daya samu ba haye yayi ba gadon gidansu ne.

    Tun suna samarinsu lokacin tasowarsu basuyi karatun boko ba lokacin bai yawaita ba sosai sai dai karatun allo wanda yabi gari lokacin inda ake É—aukan yara dawaya daga kowane yanki suna zuwa karatun allo cikin Kano da sauraran garuruwa basu dawowa har sai sun sauke alqur'ani wasun suma har sai sun fara sana'a, sunyi Æ™arfi kafin su waiwayi gida, toh hakan ne ta faru da Mansur wanda É—ane ga mai garin ÆŠanbatta, lokacin dayake da shekara tara a duniya aka tafi dashi cikin garin Kano aka damÆ™ashi hannun wani malamin addini mai suna Malam Haruna wanda amini ne yake ga Hakimi Hayatu.

A lokacin ba dan talaka ko É—an mai kuÉ—i ba ko yaron gidan sarauta a'a lokacin ilimi bai yawaita kamar yanzu ba shiyasa zaka samu yara daga mabambantan garuruwa ankawosu wajen Malam Haruna karatun allo duk kuma daya ke iyayen yara a lokacin basu sake kamar na yanzu da in suka kawo yaro sai sun manta dashi a'a su kowane bayan wattanni suna zuwa ganin 'ya'yan nasu kuma suna musu aike akai-akai.

Wannan shine dalilin haɗuwar amintakan Hakimi Mansur da kuma Alhaji Ibrahim Kwatano wanda shima iyayensa suna da hali suka kawoshi nan makarantar Malam Haruna domin ya sauke Qur'ani lokaci ɗaya haɗuwar jini da abota mai ƙarfi ta haɗasu kuma Allah yayisu hazikai masu kaifin ilimi wanda har iyayensu duka suka shaida amintarsu ahaka suka shafe shekara bakwai kafin suyi sauka murna ba'a magana Malam Haruna ya shirya musu walima duka iyayensu suka zo suka tayasu murna, kafin kowa iyayenshi su tafi dashi gida.

Ibrahim yayi sa'a dama already kafin yazo makarantar allon ya gama Primary Sch ɗinshi suna komawa gida iyayensa suka mai cuku-cuku ya koma makarantar SS1, ayayinda shi kuma Hakimi Mansur koda ya koma sai ya fara daga Primary 1 duk da lokacin yana da shekara goma sha biyar ne toh kafin ya gama Secondry tuni Ibrahim yana BUK inda yake karantar Business Admistration, shi kuma Mansur yana gama Secondry karatunsa ya tsaya saboda rasuwar Hakimi Hayatu wanda dama Mansur ne kaɗai ɗansa namiji sauran duk mata ne so sai aka ɗaura ƙaninshi ya cigaba da riƙon sarautar maigari.

Mansur da Ibrahim suna Æ™oÆ™arin ziyarar juna duk wanda ya samu dama Ibrahim na shekarar Æ™arshe mahaifiyar Mansur ta matsa mai sai yayi aure kafin ta mutu taga kwanshi aduniya shine dalilin daya sanya ta nema mai auren É—iyar Æ™anin mahaifinshi Zainabu Abu, wanda cikin lokaci akayi komai aka gama akayi biki lafiya sai bayan bikin ne Ibrahim ya tafi service shi kuma Mansur yana zaune agidansu É“arayin gadon mahaifinsa shida matarshi Zainabu Abu mai kunya da kawaichi shekararsu É—aya da rabi da aure ta haifi kyakkyawan É—anta mai kama da ubansa sak aka sanya masa suna Tahir to bayanshi ta yi haihuwa biyu duka basu zo da rai ba, lokacin ne kuma itama mahaifiyar mansur Allah yayi mata cikawa, wanda har iyayen Ibrahim sunzo gaisuwa shi baya Æ™asar yana  Æ™asar Ughanda yatafi haÉ—a Masters É—inshi, tun kuma bayan rasuwarta sai Abu ta shiga É“ari data samu ciki baya zama sai tayi barinshi kamar bazata rayu ba abunda ya fara damunsu har suka fara neman mata magani amma kuma sai cikin yayi kamar zai zauna sai kuma tayi É“arinshi.

   Sai da Tahir ya shekara 9 aduniya kana Ibrahim yayi aure bayan ya daÉ—e da dawowa ya haÉ—a Masters É—inshi Babanshi ya bashi kuÉ—i sosai ya É—orashi kan kasuwancinsa dayake dama shi É—in motoci yake saidawa 'yan kwatano shiyasa yake amsa wannan laÆ™abi bikin da Zainabu Abu ita da Mansur da Tahir sukaje suka kwana uku suka dawo domin Mansur da Ibrahim basu yarda zumunci ba.

Matar Ibrahim Aliya itama 'yar gidan masu dashi ne irin yaran nan da jin daɗi yayi musu yawa, shekaransu ɗaya da aure ta haifi yarta mace wacce aka sakama suna Farida, yarinyar data ga gatan duniya sosai daga ɓangaren iyayenta zuwa na kakanninta kuma tunda ga ita Allah bai ƙara basu haihuwa ba.

Tahir nada shekara sha uku aduniya lokacin har ya kammalah zana jarabawarsa na Primary, Abu ta haifi 'yarta mace mai suna Aisha suna kiranta Ashe wacce Tahir yafi ma iyayensu murna da É—okin haihuwar Ashe tafi tafi rayuwa na nisa har zuwa lokacin da Tahir ya kammalah Secodary School É—insa acikin makarantar Secondry dake garin ÆŠanbatta.

Tahir tun yana ƙaraminsa yaro ne mai son yayi karatu shima ya zama wani abu ya taimaki iyayensa da garinsa na haihuwa wannan dalilin ne yasa wani ziyara da Alhaji Ibrahim Kwatano ya kawo mai suka tattauna batun Tahir ɗin shikuma yayi mai alƙawarin zai tafi da Tahir domin ya inganta rayuwarsa labarin dayayima Tahir dadi sosai bai tafi dashi a lokacin ba sai da ya karɓi takardunsa ya tafi dashi ya nema mai gurbin karatu a jami'ar BUK kafin yazo ya tafi dashi shi kanshi Mansur yaji wani iri balle Abu da Ashe da suketa kuka amma sai Alhaji Ibrahim ya lallashesu da cewa in suka samu hutun makaranta Tahir ɗin zai dinga zuwa yana gaisheshi.

Kai tsaye ya nema masa Admission bayan ya zaɓar masa course d'in da yayi wato Business Asmitration domin yana sha'awa tare da burin Tahir ya zama yayi karatu ko don ya taimakeshi bisa harkan kasuwancinsa tun bayan da mahaifansa suka rasu duka kula da kamfanin mahaifin nashi ya dawo hannunshi gashi shi kuma ɗiya mace Allah ya bashi zuwan Tahir gidan sai Farida ta samu Yaya duk lokacin tana da shekara tara da wani abu sai ya kasance shike kula da ita koda home work d'in makaranta ne shi ke mata in bai da lakca kuwa suna tare yana koya mata karatu inda bata gane ba kafin kace me shaƙuwa mai zurfi ta shiga tsakaninsu duk kuma sanda ya samu hutu zai tafi Ɗanbatta tare da Farida yake tafiya saboda bata yarda ya barta agida duk inda ya saka ƙafa anan take saka nata al'amarin daya ke ma iyayenta daɗi domin basu da abar farin ciki irin Farida shiyasa suka sangarta komai sai an mata basu la'akari da ita macece, abun na cima Tahir tuwo a kwarya yadda Farida bamai gaya mata taji tun tana ƙaramarta yarinyace mai ƙawayen bala'i da tarkace kowa nata ne ga kuma shegen zuwa gidan ƙawaye tun tana ƙaramarta jikinta rawa yake in taji labari biki kowani event da za'aje achashe sukuma iyayenta sun bata freedom wani lokacin ma Tahir ke taka mata burki taji dayake tana tsoronshi.

Yana shekarar ƙarshe a BUK Allah yama Hakimin rasuwa aka kuma naɗa mahaifinshi wato Mansur bai samu zuwa ba sai lokacin bikin mahaifinshi inda ya ƙara aure da Salamatu Innaro, lokacin ne ya daɗe agida kafin ayi posting ɗinsu su tafi service ɗinsu suna gamawa Abba Alhaji Ibrahim ya matsa mai ya tafi birnin US ya ɗora Masters ɗinshi yana chan har mahaifinshi ya ƙara aure da Binta itama irin Salamatun ne har ta shekara Allah bai bata haihuwa ba sai Hakimi Mansur ya haƙura ya fara tunanin ƙila iya ƙwanshi da zai gani a duniya kenan.

Sai da ya shekara uku kana ya dawo lokacin Farida har ta gama Secondary Sch ɗinta ta shiga BUK aji ɗaya a yayinda Ashe kuma take SS1 wanda yaje yaji wai za'a mata aure shi ya hana yace don Allah abarta ta ƙarasa toh dalilin haka aka barta sai da ta kammalah Secondry Sch ɗinta kana aka mata aure da yaron limamin garin Badamasi suna zaune anan garin Ɗanbatta.

Dawowarshi ne yasa Abba ya buɗe mai kamfani a garin Kaduna wato *IBRAHIM KWATANO AND SONS LIMITED* Wanda ya bama Tahir ragamar kula da wajen amatsayin manaja murna sosai yayi ya dingama Abba godiya haka Hakimi Mansur da yaji sai da yazo har Kano yamai godiya kowani masoyin Tahir in yaji wannan labarin sai ya tayashi murna da farin ciki, lokaci kaɗan kamfani ya fara aiki bayan an zuba ma'aikata da masu kula da abubuwa lokacin ne kuma Tahir suka haɗu da Ishaq wanda ke matsayin Accounting Manager a kamfanin, sai tasu tazo ɗaya sakamakon amana irin ta Ishaq da kuma hankali da sanin mutumcin kanshi shiyasa lokaci ɗaya abota mai ƙarfi ta shiga tsakanin Tahir ɗin da Ishaq wanda shima ɗan asalin Kaduna ne.

   A nan Kadunan Abba ya siyama Tahir gida wanda yake zaune da motar hawa mai tsada saboda taÆ™aita zirga zirga daga Kano zuwa Kaduna da zuwa ÆŠanbatta shekara uku kamfanin yayi da buÉ—ewa amma yayi ma saura zarra dama Tahir haka yake komai ya sama hannu sai anga albarka kafin kuma wannan shekarun abba na matuÆ™ar alfahari da samun Tahir hakama iyayenshi don zuwa wannan lokaci hatta gidansu ya gyarashi tsab ya kuma sakama duka iyayen nashi mata ababen more rayuwa a duka shashensu daya gina musu, lokacin kuma shekara biyu da rasuwar Binta, Ashe ma sha tara na arziki yake mata bama itama kaf al'ummar ÆŠanbatta suna alfahari da samun É—a irin Tahir saboda shi baya da burin ya tara abun duniya illah yama jama'a hidima da kuma garin haihuwarsa.

  
Farida na shekarar ƙarshe a makaranta ta furtama iyayenta ƙudirinta game da Tahir na tana sonshi da aure jin haka ya daɗaɗa ran Abba da Umma sosai sukayi farin ciki domin sun fi kowa sanin samun ɗa nagari mai halin dattako irin na Tahir sai an tona ko kafin ma Tahir ɗin yaji labarin Abba ya isa Ɗanbatta ya labartama Hakimi suma achan ɓangaren shida Goggo Abu sunyi murna sosai don aganinsu su Alhaji sun ma Tahir hallacin daya kamata shima ya saka musu har Kaduna Abba yaje ya sameshi da maganar hakika ya girgiza dayaji muradin Farida amma ba ita da cewa sakamakon Abba yayi mai abunda bazai iya ƙin jininsa ba duk da ko ya gane tuntuni Farida ba irin macen data dace dashi bane, amma bai da yarda zanyi ganin iyayenshi sun kirashi sun jamai kunne kan karyama Abba gardama kan ƙudurin haɗa auren shi da Farida.

Cikin wata uku aka gudanar da bikinsu wanda yabar dimbin tarihi domin shagali akayi kamar ba gobe, bidi'a kala kala don ma shi Tahir ɗin ya doje Ɗanbatta ya tafi bai yarda ya zauna a kano ba sai ranar aure yazo shida Ishaq da tawagar Hakimi da daddare kuma akayi dinner wanda Tahir yasha mamaki uban mutanen dasu kazo wanda shi baisan ko ɗaya ba ashe duk jama'ar Farida ne, saboda tsabar zuwa bikinta har laƙabi ake mata da Farida biki-biki, abun bai bashi mamaki da saninta da uban ƙawaye da kuma son zuwa sha'ani ita ko bikin waye ko ba'a gayyaci Farida tana zuwa indai tasan cewa za'ayi Event aji daɗi ashana ta sake yadda ranta keso balle shiganta BUK ta ƙara samun ƙawaye na gari dana banza kuma ta ƙara yawo idonta ya buɗe amma bana iskanci ba na wayewa.

Washegari aka kawota Kaduna Anguwar Rimi Gra a babban gidan da Tahir ya gina da guminsa Farida taga gata gaba da baya domin da tsala tsalan motocinta biyu aka kawota gidan, ko wata ɗaya basuyi da aure ba Tahir ya fara gaya musu, saboda ko girki Farida bata iya ba ko kichen bata shiga sai dai shi in ya dawo daga Office ya zage ya shiga ya sama musu wani abun su ci, ko kuma in zai dawo yayi musu takeaway baima wahalar da bakinsa ganin bata iya ba balle tayi ganin haka yasa tama Umma magana ta kawo mata 'yar aiki itama basu daidaita ba watanta biyu ta ƙara gaba saboda halin Farida na faɗa komai aka mata ba'a mata daidai ba, watansu huɗu da aure akayi posting ɗinsu zuwa service a kuma lokacin ne ciki ya ɓulla ajikin Farida wacce ta dinga kuka wai zai hanata tafiya service Bauchi, abu har sai da iyaye suka shigo ciki Abba ne da kanshi ya mata cuku cuku ta dawo Kaduna amma ba haka ranta yaso ba ciki zai mata cikas wajen zuwa biki ko sha'anin kece raini amma bata da yarda zatayi don Tahir ya kasa ya tsare kan cikin jikinta taga ainihin kalanshi 

Sai da cikinta yayi wata goma cur kana ta haihu shima C.S aka mata aka ciro 'yan biyu mace da namiji murna wajen Tahir ba'a magana, saboda shagwaÉ“an Farida da sangarta sai dai Tahir ya barta aka tafi da ita Kano wajen Umma, ta kula da ita yara kuma suka ci sunan Basma da Bassam, Farida bata dawo ba sai da ta kusa wata uku kana ta dawo har su Basma sun fara wayau data dawo har da 'yan aikinta guda biyu É—aya ta kula dasu Basma É—aya kuma tayi girki da gyaran gida, zamanta a Kaduna yasa Farida tayi Æ™awaye fita biki sai wanda bata jiba Tahir kuma haÆ™uri gareshi, ko tayi wani abun bai cika mata magana ba saboda miskilancinsa, uwa uba kuma fifikon soyayyarta azuciyar iyayenta da kuma damar da iyayensa ke ganin taimakon mahaifinta gareshi karya wulaÆ™anta ta amma zamansu da Farida duka  haÆ™uri yafi yawa a ciki.

Haka dai rayuwa ta cigaba da gangarawa da daɗi ba daɗi Tahir dai na haƙuri da halin Farida rayuwarsu Basma da Bassam kuwa ta walagigi ce hannun 'yan aiki da kuma shi saboda in ya dawo daga Office yana zama ya kula dasu Farida kuma bakin yawo ke cinta daga yau tana wajen bikin ƙawarta sai gobe bikin ƙanwar ƙawarta gashi ita kuma bata da sha'awar yin aiki amma kuma bata iya zama agida ita kenan yawon biki, gashi shi mutum ne da bayason hayaniya da ɓacin rai ya kai ƙararta sau biyu wajen su Abba amma ba wani chanji shiyasa ya kawo ido ya sakamata yana ƙoƙarin shanye ɓacin ranshi akanta duk babu abunda zai ɗaurar na jin daɗin aure shi kam.

Matsala ta biyu kuma shine Farida tana daga cikin jerin matanan masu ƙarancin sha'awa kuma basu ba hakan muhimmanci ba balle ta nemi magunguna ko na musulunci ne saboda shi Tahir yana daga sahun maza mabuƙata, wani lokacin sai suyi sati biyu Farida bata kalleshi ba in ko ya nemeta sai ranshi ya ɓaci ya rasa meke damunta wani lokacin yana buƙatar saboda gudun ma kanshi ɓacin rai yake ƙoƙarin daurewa shiyasa koda yaushe cikin yin azumi yake koda bana ranar Litinin da Alhamis ba.

Bayan haihuwar su Basma tayi family plaining ba tare da Tahir ya sani ba shiyasa har su Basma suka kai shekara takwas bata ƙara haihuwa ba, tunda har sun shiga makaranta Commond sch Kaduna, har tuhumarta ya taɓa yi ta turje tace batayi komai ba taƙi gaya mai gaskiya haka da suka je Ɗanbatta Goggo Abu ke tambayanta Allah sa ba ƙwayoyin zamani Tahir ɗin ya ɗorata akai ba tace ba komai. Da yake ba'a ma Allah dubara cikin wannan tsukun ta samu cikin Naila wanda ya wahalar da ita shima C.S aka mata tana haihuwarta Farida tayi alƙawarin ta gama haihuwa itama wannan haihuwar gida ta koma, 'yan aikinta kuwa tuni ta sallamesu da zata dawo daga wankan Naila ne ta dawo da Iya.

Tahir ya rasa shi wani irin ƙaddaran rayuwa ce ta faɗa mai yana ganin Ishaq da matarsa Zahra gwanin ban sha'awa amma shi ƙarya ne ya dawo daga Office ya iske Farida agida ko tana gida bashi da wani matsayin da zai shigo tazo ta mai sannu da zuwa tayi kwalliya don ya gani yaji daɗi tana ciki tana waya da ƙawayenta ana tsara yadda bikin ƙanwar wanche zai kasance kullum cikin yi mata nasiha da nusassheta yake amma bataji saboda misalin dayake yawan mata da Zahra matar Ishaq ta yanke alaƙa da ita bata wani sakarmata fuska sai itama Zahran taja baya da ita.

  Goggo Abu ce kaÉ—ai da Æ™anwarsa Ashe suka san halin dayake ciki in ya gaya mata sai ta bashi haÆ™uri ta kuma ce zatama Faridan magana toh ko Faridan taje garin in Goggo Abu ta mata faÉ—a sai tace insha Allahu zata gyara kuma bata gyarawan kuma Goggo Abu ta hanashi sanarma Hakimi wai kada ya zama sanadiyyar raba amintantakar dake tsakanin Abba da Hakimi.

  Mufeeda Kuma Tahir da kanshi ya É—auko ta faga ÆŠanbatta bisa umarnin Goggo Abu bayan Ita Faridan da kanta ta Nemi Goggon data samo mata matashiyar yarinyar wacce zata tayata kula da Naila amatsayin NANNY...."


Post a Comment

0 Comments