NANNY..!*
_(Mai Reno..)_ *Alkaluman:*✍️ *AISHA ALTO*💞 *JAMILA UMAR(Janafty)*💕 _*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LUVSM💕🔐*_ *Bismillahir Rahmanir Rahim,in The Name of Allah,The Most Beneficent,the most mercifull praise be to Allah Lord of The Words,...Assalamu Alaikum Our Follow Fans,We are Starting our New Book,We Ask Allah Subhanahu wata'ala to guide Us Throught And Make it Succussful Till The End Ameen ya Allah*👏 ``` Wannan lbrin Is a Fiction Story Kirkirarre ne Daga Fasaharmu,Juyamana lbri ko Sarrafashi ta Wata Siga,Bada Izininmu ba Toh Hukuma ce Zata Rabamu Insha Allahu``` *BABI NA D'AYA* *KADUNA* _Area:Anguwan Rimi Gra_ Misalin karfe 9:30pm Daidai na Daran Ranar Asabar,ya baro Office dinsa,Direbansa Garzali ne ke Jansa Cikin Bakar Motarsa Bugatti. Hon ya Zuba akofar Tamkamemen Get din gidan nashi Mai kama da Aljannar Duniya,Megadinsa Habu ya Rugo da Gudu yazo ya Wangalemusu get Domin yasan Yallabai ne ya Dawo Adaidai Wannan Lokacin. Lokacin da Motar Ta Sulala parking Space kafin Tagama Daidaita Zama Sai ga Wasu kyakyawan Yara Guda Biyu mace Da Namiji Wadanda Ashekaru bazasu Haura Shekara goma ba Tsawonsu Daya Kuma kamaninsu Daya,sai dai mace Tafi Jiki da Kuma Tsukakkiyar Fuska yayinda Namiji yake Siriri Ammh Fuskarsa nada Fadi,Farare Tas kamar Ka Taba Jini ya Fito akallon Farko zaka musu ka Fahimci yaran yan gayu ne na Karshe Kodaga ganin yanayin Kayan Kantin Dake Jikinsu Riga da Wando da Kuma yanayin Fatarasu na Jin Dadi ne. Da gudu suka isa jikin Motar Suka Bude Bangaren Baya Suna Fadin"Wlcm Daddy..."Atare na Kallesu na sake sai alokacin Naga Dimple dinsu ya Lotsa Agefen Kumatunsu Lokaci Daya Yaran masu kama da Juna Sosai Inaga ma yan"biyu ne,Bangama Mamaki ba Sai da Naga Wani Cute and Handsome Ya Fito Daga cikin Motar yana Sanye da American Suit masu Ruwan Toka ya Matse Wuyansa Da Tie,Fuskarsa Tana bayyana Tsantsan Farincikin Dayake Ciki Naganin Kyakyawan Yaransa dayake Alfahari dasu Rumgumesu yayi yana Shafa kansu yana Fadin"Thank u my Childreen..."Yake Fada Shima Duka Kumatunsa na Lotsawa,aShe anan yaran Suka Dibe Tsantsan kyau da Kuma Kyan Jiki,Dogone kakkarfan Namiji ne mai Tsawo da jiki da Fadin Kirji,Dan Kimanin Shekara 43 aduniya ammh kuma Bazaka iya Kiramasa Wadanan Shekarun ba Saboda Yadda ya Mori Jiki da kyan Fuska Ba Fari bane Tas,Ammh Kuma Bazamu Sanyashi alayin Bakake ba,Fatarsa Tafi Kama da yan Maroco,Saboda Murjewa da jin Dadi,doguwar Fuska gareshi mai Dauke da dogon Hancinsa da Kuma Zagayayyen Bakinsa wanda Wani Bakin Saje yama Wajen Kwanya gwanin Bam Sha"awa yana da Daradaran ido masu Dauke da Wasu Sirrika,ya mallaki Zara zara Gashin Ido Tamkar yana kari,sai Giras sa Dake Cike da gashi Kamar Wani Mace. *ALHAJI TAHIR MANSUR DA'N BATTA* Kenan babban Manaja ne Dake kula da kamfanin *IBRAHIM KWATANO AND SONS LIMITED* Kuma Babban D"a Awajen Hakimin Dambatta Wato Alhaji Mansur Danbatta,Kuma miji ga *FARIDA IBRAHIM KWATANO* Kuma Uba ga *BASSAM,BASMA,NAILA...* Cikakken Jarumin Namiji mai Hakuri Hade Da Zati Da Haiba Miskilin Namiji Wanda bai maida Rayuwar Duniya da Abunda Ke Cikinta ado ba,wanda ake Alfahari dashi bayan iyayenshi Harta da Garinsa Danbatta Suna Alfahari da samu D"a Irin Tahir daya Fito Daga Ahalinsu Zumbura baki Basma Tayi Tana Fadin"Daddy ina Mami...? hararanta Bassam yayi kafin yace"Eh ina Mami..? Kin manta dazu Munkirata da wayar *ANTY MUFEEDA* Tace mana ba yau Zata Dawo ba.."Tura baki Basma Tayi kamar Zatayi Kuka Tahir Dake Tsaye yana kallonsu Wani Takaichi yacikamai Ciki Jin Farida yau ma bazata Dawo ba,Hannun Basma yakama yana Fadin"Bassam Karbomin briefcase Dina Hannun garzali muje ciki.."da Hanzari Bassam yakarba Jakar Hannun Garzali yabi bayan Daddy Wanda ke Rike da Hannun Basma yana lallashinta don Ita Haka Allah yayi ta akwai Kulafacin Uwa ammh ba domin Haka ba yadda Farida ke Banzatar da Mijinta da ya"yanta yaci Ace Basma Tadaina damuwa da Rashinta don ba yau Ake ba. Suna Shiga Cikin Kayatattacen Falon Kukan Naila yafara Musu Maraba Inda Take goye bayan Mufeeda wacce Ke Ta Faman Zagaye Falon Da Ita tana Faman Jijjigata ammh Taki yin Shuru,Cike da Tsausayi da Takaichi Tahir ke Bin Mufeeda da kallo Wacce Tajige da Zufa Duk da Sanyin Ac dake Falon Sakamon Naila Irin yaran nan Masu Kiba kamar Kajin Agric,ayayinda Ita Kuma Mufeeda Take Doguwa Siriirya kamar Ta karye saboda Rashin Nama,yarinyar sai Rinjayarta Take kamar zasu Fadi,daga gani Tafi karfinta, gata yarinya karama Domin Ashekaru bazata Haura Shekara 16 ba,Doguwar Fuska gareta mai Hade da Hancinta Shiba gajere ba,Kuma ba Dogo ba,Mufeeda baza ka Sakata Cikin Jerin kyakyawan Mata ba sai dai Tsaka tsaki. Tana ganin Sun Shigo Tayi Azaman Dukawa Tana Fadin"Sannu da Zuwa Daddy..."Cikin Siririyar Muryanta Mai Cike da Yarinta,Amsawa yayi yana karisawa gareta bayan ya saki Hannun basma yana Fadin"Mufee,Meya samu Naila ne Take Ta Kuka Haka..? Yafada yana Mika mata Hannu Alamar Ta Kwantomai Naila din. Batayi gaddama ba Ta Kwantota tana Mikamai ita Wacce Fuskarta Ta Hade da Majina da Hawaye,Ya karbeta yana Kallon Mufeeda dake Fadin"Wlh bansani ba Daddy,Tundazu ta Fara Kuka,na zata yunwa ne,sai na Hadamata Madara na bata taki sha,sai kuka take ganin Haka sai iya ta amasheta nan ma Taki yin Shuru Sai Kuka take tana Kiran Sunan Mamanita..."Tafada itama kamar Tayi kukan. Mirmishi Tahir yayi yana Rimgume Naila wacce ke ajiyar Zuciya ta Kwanta Luf akan Kafadarshi,Kallonsu Bassam yayi kafin yace"Kunci Abinci..? Suka gyada kai alamun Eh,bai kara mgana ba ya Wuce ya Fara Haura Steps yana Dauke Da Naila kafin ya tsaya ya waigo yana Fadin"Oya kuje ku kwanta sai da safe.."Yafada yana Tamke Fuska Sum Sum Bassam da Basma kowanne ya Nufi Dakinsa yana Bata Fuska yayinda Da Mufeeda Tayi Tsaye tana kallonshi Ido ya sakarmata Fuska ba Walwala yace"Tsayuwar me kikeyi ke kuma..? Jikin Mufeeda na Rawa Tace"Ba...bakomai Dama dama..."Tafada tana Sosa kai Ware idonshi yayi kafin yace"menene..? Akwai Matsala ne..? Kanta na kasa tace"Dama zance ne Daddy baka ci Abinci ba gashi chan iya taga jera maka akan Dinning..."Mirmishi ya saki kafin yace"Karki Damu bana jin yunwa,ki koma daki ki kwanta.."Kallonsa Tayi kamar Zatayi mgana sai ta Fasa ganin yadda ya Sakamata ido,jiki asanyaye ta juya tana Fadin"Sai da Safe Daddy..."Alebensa ya Karba da Fadin"Allah tashemu lafiya.,yafada yana kallonta Tana Tafiya kamar Zata Fadi Cikin Sanyinta ta Shige dakinta,. Ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya juya yana Dauke da Naila,Ya Karisa Haura Step ya Bude Kofar Farko Mai Dauke da Kayattacen Royal bed Wanda yaji Shimfidun Alfarma gwanin ban Sha'awa Dakin bashi da Yawan Tarkace sai Wani Cafet Wanda ya mamaye Dakin gabadaya mai Taushi yana Fitar da Kyalli Gwanin Ban Sha"awa sai Makeken Wardrope mai Cinye Rabin Dakin,sai Dreesing Mirror kusa da Kofar Tiolet. Kai Tsaye ya Karisa gaban Gadon sai da ya Haura Tsakiyar gadon Kana ya Kwantar da Nihal Wacce Barci ya Kwasheta Tana Sauke Ajiyar Zuciya Jin ya Sauketa,Hannu ya saka yana Shafa Goshinta Ahankali alamar lallashi nan da nan Ta Koma barci Saukowa Yayi Daga Kan gadon yana Sauke Ajiyar Zuciya kafin ya Cire Coat din Dake Jikinsa,Ya Rataye Kan Wani Dogon Abu Alamar na Rataye kayane,Towel ya Dauka ya Bude Kofar Tiolet ya Fada da Addu"a Dauke Cikin Abakinsa Akallah ya Ashafe Tsawon Minti Talatin Kafin ya Fito Daga Tiolet,kugunsa Daure da Wani Babban Towel sai Kansa yana Rike da Karami yana Goge Ruwan Dake Diga asaman kanshi kai Tsaye Wardrope din Dake dakin ya Nufa ya sanya Hannu ya Bude Kayane Jere Bisa Hanger Iya Kallanka Mallam,gefen American Suit bakake da masu Ruwan Toka,Dabam gasunan Ajere na Kowani Kamfani sai Wanda ya Zaba zai saka kama daga DKNY,Tommy,hilfiger,Armani,louls,button,Doke,and Gabbana,Bersace,hakama bangaren Manyan kaya Tazarce Kama daga Shaddodi,gezner,yadika Masu Kyau da Tsada Suma bangarensu Dabam Haka bangaren Shirt da Jeans Suma Waje Gudane,bangaren Kayan Shan Iska Irinsu Short Niker Da Riga mai Gajeren Hannu Suma Suna Waje na Dabam sai Daga Kasa bangaren Kayan barci ne gasunan kala kala masu Taushi Da Tsari. Cikin kayan Barci nashi Pjm ya Dauko Riga da Wando Masu Ruwan Toka Ruwa Na Diga Daga jikinsa ya Zura Kayan,Ammh Rabin Hankalinsa na kan Naila dake Barci,Baro Gaban Wardrope din yayi ya isa gaban Madubi ya Dauki Wani Turare Spry ya Fesa kafin ya Mtsa Chan Gefe Inda Wata Katuwar Darduma Ke Shimfide ya Tsaya Shuru kafin ya Daidaita Natsuwarsa ya Tada Sallah, Tsawon Wasu Mintina ya idar da Sallar Shafa"i da Wuturi ya Dade yana Addu"a Kafin Ya mike Wata Yunwa na Kwakulan Cikinsa In Har Bazai Manta ba,Rabonsa da Abinci Mai lafiya da Kwari Tun Jiya Da Daddare kafin ya Dawo Gida Ishaq ya matsa masa Suka biya ta gidansa Sukaci Abinci Toh bayan Shi banda Ruwan Coffea bai kara saka Wani Abu mai Nauyi abakinsa ba,Cikinsa ya Shafa yana Tuna Kalaman Mufeeda yarinyar Tana bashi Mamaki gata Karama da Ita ammh Tafi Farida sanin Halayyarshi Ta Kuma Fita Karantar yanayinsa..,wata Zuciya tace Toh Ita Ke Zaune dakai Farida Yawon Biki da Suna da Zuwa Gidan Kawaye Bai barta ta Zauna dakai ba Balle ta Karanci Waye kai Tahir Kansa ya Shafa yana Sauke Numfashi kafin ya Nufi Karamin Fridge dinsa Dake gefen Gado yazauna kafin ya Bude ya Ciro Madarar Hollandia Hade da Kofi Silba wani Karami mai kyau ya Bude ya Tsiyaya,Ya Shanye Duka Kafin ya sake Cikawa ya Kafa kai ya Shanye yana Ajiyar Zuciya mai da Komai yayi Cikin Karamin Fridge din Kafin ya Dora Kafafunsa Duka biyu kan Gadon Yana Kuma Jingina bayansa da Gado,ganin kamar Sanyin Dakin yama Naila Yawa ne yasa ya Dauki Remote din Ac ya Rageta yana Kuma Kokarin gyarama Naila Kwanciya Aranshi yana Tunanin Farida Wata Irin Uwa ce. Haushin Hakane yasa Ya Mika Hannu ya Dauki Wayarsa Wacce Da Zai Shiga Wanka ya Ijiyeta akan Side Drower,Cikin Lokaci Kadan ya Lulubo Nombarta Wacce Yayi Sarving dinta da *WIFEY*, yayi Shuru yana Bin Wayar da kallo kafin ya cije baki ya Latsa mata Kira yana kallon Agogon Bangon Dakin 10 ta Wuce,wayar ta Shiga Haka Ta Dinga Ringing har Ta Katse Bata Daga ba,bai Hakura ba ya sake Kiranta Nan Ma har ta Karishi Ringing ta Katse bata Daga ba,Tsaki yaja ya kife wayar Gefensa Kafin ya Dauko Karamin Qur'anin Dake kan Side din Drower din gadon ya Bude Suratul Maryam Inda ya Tsaya Jiya Da Daddare Kafin ya Kwanta Domin ya Riga ya Zamemai Jiki baya iya Barci sai ya Karanta al"qur"ani Shiyaasa baya Taba Kwana da Bacin Rai. Yafara Karatun Kenan Ahankali Cikin Zazzakar Muryansa mai Cike da Amo da Sauti mai Dadin Sauraro Wayarsa ta Fara Kara Tana Neman Dauki sai da yakai Karshen Ayar Kana ya Dago da Kanshi ya Dauko Wayar ganin Sunan Wanda Ke Kirane yasa Yayi Mirmishin Dayafi Kuka Ciwo ya Daga Kiran Yana Fadin"Yanzu Farida Rayuwar da kika Daukanma Kanki mai Bullewa ce..? Dagachan Bangaren Farida Dake Gefe Cikin Wani Kayataccen Hal Ana ta Dinner Wajen ya Kaure da Hayaniya Tare da Kidan Dj,Sanye Take da Doguwar Rigar Wani Ubansu Fefe les Wanda yaci Dinki mai kyau da Tsari kalan blue Head din kanta Kuma pick Fuska Taci Uban Makeup kamar Wata Amarya Doguwar mace ce Ammh ba Sosai ba,Fara ce, sosai sai Kuma Akwai Kyau da Dirin Mata gaba da baya Masha Allah,Baki ta Bude Zatayi mgana tana Yatsina Fuska Wanda Fararen Hakoranta Suka bayyana Tare da Hakorin Makkanta Yana Daukan Ido Wanda yake Karamata kyau. Cikin Kosawa Tace"Toh Uban Korafi Ai ina ganin kiran ka Nasan Abun da Kakirani ka Fadamin kenan,Haba Tahir wai Yaushe ne Zaka Daina Kunyatani ne Gaban Kawayena..? Tafada Tana Hararan Gefen Wayar Kamar Tana kallonshi,Shuru yayi yna Kokariin Danne Bacin Ranshi kafin yace"Au kinfison Kada Ki Kunyata gaban Kaawayenki Ammh Kin Manta da Lahirarki da Abunda Kikeyi zai iya Kaiki Wuta Farida...? Baki ta Tura Kafin Tace"Na Shiga Uku Wai Don Allah Tahir me nakeyi Ne..koda yaushe mganar ka kenan Zan Shiga Wuta.."ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace"Yanzu Fisabillah Kwananki nawa bakinan Kin Saka Kafa Kin Fita kin Zubar da ya"yanki Da Mijinki da Gidanki Abun Takaichi Wai Da Sunan Bikin Kanwar Kawarki Farida Anya Kina Son Gamawa Da Duniya lafiya..? Daure Fuska Tayi Kafin Tace"Ikon Allah,duk mai ya Jawo Wannan mganar..? Inace Su Bassam Sun Girma Suna da Wayon da Zasu Kula da kansu,..."Ya katseta da Fadin"Naila fa..? Kin ijiye mai Bata Nono ne..? Yamutsa Fuska Tayi kafin Tace"Ina Mufeeda..? Miye Amfaninta dama Don Ta Kula da Ita na Amince nama goggo Mgana Anemin ita,Mganar Abinci Kuma I know iya bata Wasa Komai Kuke Bukata Zata Girka Ta Baku ,Toh kuma Wht Else Tahir..? Cikin Kulufuwa da Bakin Ciki yace"Nifa..Nace Ni Mijinki fa Farida Hakkina na Aure Wa kika Rataye ya bani,Iyan ko Kuwa Ita Mufeedan...? Yafada Cikin Son Kwantar da Fushinsa Duk da yakasance mai Hakuri. Yar Dariya ta Saki kafin tace"ai dama na sani Duk Wannan Kumfar bakin naka Saboda Ban Dawo na sakarma Jiki kayi yarda kaga dama bako..? Wai Tahir na Tambayeka..? Bata bashi Ikon Mgana ba Ta Cigaba da Fadin"Kai baka gajiya da Sex ne,Narasa Wani Irin Miji Allah ya Hadani Dashi Haba Abu kamar Bambaran Masara Kaga Mallam Nifa ba Sex machine bane balle Ka Ringa Hawata Duk sanda Kaga Dama Ina laifin Sau Daya Asati,ga Kawaye nan Su Binta su Zeenat Su Smarty Ba Wacce Mijinta ya Kirata balle ya Takura mata sai ni Dayake Allah ya Hadani da Ustaz dan Jaraba Sai na Koma na Nanike a gindinka Tahir Duk Shekara kana Min Ciki ina Haihuwa Kamar Waata Akuya ko..? Toh Wlh Baka isa ba,Hakan bazata Taba Faruwa ba Don Allah kar ka sake Kirana Zan Dawo Tunda ba dauwama Zanyi Achan ba,Muna Wajen Dinner so gobe zamu kai Amarya Kano Dagachan Zan biya na kwana Awajensu Abba may be Sai Jibi zan Dawo..." Daga Haka ta yanke Kiran Tana Hararan Wayar Kafin Ta saki Tsaki Tana Fadin"Fitinanne..."Wayar ta kashe Gabadaya Ta Wurgata Jaka kafin Takoma Wajen Kawayenta Wadanda Keta Kallonta Tundaga Nesa Suna Dariya Tahir yaji Wani Abu na Tasomai Daga Kasan Ransa mai kama da Fushi Da Bacin Rai ammh yana Dannewa Wayar yabi da Kallo kafin ya Sauketa yana Sakin Ajiyar Zuciya,yana Kokarin bama kanshi Hakuri,Ammh Dole ne gobe yayi sammako yaje Kauye wajen Goggo ya sanar da Ita an Kawo Limit din Daya Gaji da Zama da Farida Saboda Haka In bata Amince ya Saketa ba Toh Dole Ta Yarjemai ya Kara Aure,Domin Shi ba Dutse bane lafiyayyan Namiji ne mai Bukatar Kulawar Mace Wanda Keson Ya"yan sa Fiye Da Kansa,yana Bukatar Wacce Zata Kula da Duka bukatunsa dana ya"yansa Wacce Take Daraja Aure ba Sakarya Irin Farida ba,wacce In Har ya Lissafa Daidai Wlh Tafi Wata biyar Rabon Data Hada shimfida Dashi,ko bayan Haihuwan Naila bai Wuce Sau Uku Suka Hadu ba. Ijiye Qur"anin yayi yana gyara Kwanciyarsa Hannu ya saka ya Kashe Hasken Dakin Kafin ya Kunna Dumlight,blanket yaja Ya Rufe kafafunsa Zuwa Kugunsa Inda ya Hada da Naila ya Rufe Mata Rabin Jiki kafin ya maida Kanshi Bisa Filo yana Nanata Dalilin Goggo na Banza Data Dogara dashi Ta Hanashi Kara Aure,Wai da Cewa yana Aiki karkashim Mahaifinta Shi ya Rikeshi Kome ya Zama Shine Sila,Shi kuma Wannam bai Dameshi ba Tunda Son da Iyayen ke mata yasa Suka kasa Tsawarta mata ,Shikan Wannan Karon ba Gudu baja da baya Koda Kuwa hakan zai saka Alhaji Ibrahim Mahaifim Farida ya Yanke Harkan Nemanshi yaji ya yarda Arziki na Allah ammh In yafada Halaka fa..? Ba wanda Zai Zargi Farida Illah Shi da Zai Shiga Cikin Duniyar Nadama na Har Abada. Da wannan Tunanin yayi Addu"ar Barci ya Shafa Kafin ya Shafama Naila,Hannuwansa ya Tallafa akirjinsa kafin ya Runtse Ido Yana Fatan Barci ya Kwasheshi bayason Tuna Wata Aba Farida... *Comment,Share,vote..And Like..* *Shakira* *Aisha Alto* *NANNY..!* _(Mai Reno..)_ *Alkaluman:*✍️ *AISHA ALTO*💞 *JAMILA UMAR(Janafty*💕 ```Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto``` _*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_ *BISMILLAHIR RAHAMIR RAHIM* *BABI NA BIYU* Tun bayan daya dawo daga masallaci shida Bassam lokacin 7 saura na safe, kai tsaye ɗakinsa ya koma ya iske Naila ta tashi tana ta kuka, ɗaukanta yayi yana lallashinta ya shiga toilet da ita ya tuɓe mata kaya ya zage yayi mata wanka tsab domin taji daɗin jikinta amma duk da haka Naila 'yar wata goma sha ɗaya bata bar kuka ba daga gani yunwa takeji shiyasa yana gama mata wankan ya naɗota cikin towel ya sauko ƙasa zuwa ɗakin Mufeeda yana ƙwala mata kira. Iya dake kichen ta fito jin yana kiran Mufeeda agaggauce in kaji ance Iya zaka zata tsohuwa ce ko ɗaya matashiyar dattijuwa ce mai kimanin shekaru hamsin da wani abu kawai su Basma ne ke kiranta Iya tun sanda Mami ta aiko ma Farida da ita daga Kano, shine kowa ya kama. Ganin Tahir da kanshi yasa ta washe baki tana faɗin "Alhaji kai ne..? Kar dai 'yar rigimar ta tashi da kukanta yau, barka da safiya..?" Yana murmushi ya ranƙwafa yana faɗin "Ina kwana Iya..?" Ta amsa cike da jin daɗin yadda Tahir ke girmamata da darajata, take faɗin "Hala rigima Naila keyi bata ga uwarta ba..?" Yana sosa kai yace "Eh wallahi Iya inaga yunwa takeji ne, na mata wanka amma har yanzu bata bar kuka ba shine nazo zan bama Mufee ita ta bata madara ko tayi shiru.." Iya ta miƙa hannu ta karɓeta tana faɗin "Eh kuma da yunwar inaga bari na dama mata inaga Mufeeda barci ne ya kwasheta don nima yau najita shiru bata fito ba..." Miƙa mata ita yayi kafin yace "To Iya..." Daga haka ta juya ta nufi ɗakin Mufeeda inda kayan madaran Nailan suke da komai nata, shi kuma ya juya ya haura sama. Wanka ya shiga yafi minti talatin kafin ya fito domin Tahir akwai daɗewa wajen wanka, yana fitowa ko mai bai tsayawa shafawa ba don Tahir kwata kwata baya ƙaunar shafama jikinsa wani abu, wardrope ɗinsa ya buɗe ya ɗauko ɗaya daga cikin fararen gezner ɗinshi ɗinkin tazarce, wanda ya amsheshi sosai aikin jikin shaddar baƙi ne, hular kansa zanna bukar mai zanen baƙi ce, haka rufaffen takalmin ƙafarsa ma baƙi ne, sai kyakkyawan haɗaɗɗen baƙin agogon fatar dake hannunsa na kamfanin Rado, shi kanshi Tahir daya kai duban kanshi a cikin madubi sai da ya murmusa a ransa yasan cewa tabbas shi mai kyau ne kuma ko a cikin maza sai an tona uwa uba kuma Baba Hakimi zaiji daɗin ganinsa yau cikin shigar manyan kaya. Yana gyara zaman hulan kansa wayarsa riƙe a hannunsa yake saukowa daga saman step ƙamshin turarensa na Man na tashi tun kafin ya ƙariso, Basma da Bassam da Mufeeda wacce ke goye da Naila bayan ta bata madaranta ta sanya mata wata bulawus mai kyau tayi shiru ta goyata ram a bayanta, haka itama tana sanye da riga da siket na atamfa cikin wanda Daddy ya ɗinka musu ita da Basma, sai Iya dake gefe suna zaune bisa wani ƙaton ƙayataccen teburin cin abinci mai kama dana alƙarya guda, dama haka aƙidar gidan Tahir yake ba'a nuna bambamci da bare dana gida duk ɗaya ake, kowa dake gidan, in ka ɗauke Megadi da Direba ne kaɗai basu haɗuwa suci abinci tare Farida kuma bata damu ba, don bata cikama zama agidan ba balle ra'ayin Tahir ya dameta, tun Iya da Mufeeda basu saba ba har sunzo sun saba domin dukkansu sun haura shekara biyu a gidan.. Tun daga nesa yaran suka zuba mai ido suna kallonsa harda Mufeeda wacce duk sanda taga Tahir sai taji ta raina duka mazan duniya domin ya gama cika kowani mizami da zati, ga kyau ga asali ga nasaba da kyan hali har misaltawa takeyi a cikin ranta Allah ya bata miji irin Daddy wanda ya iya ɗaukan wanka da gayu, tunaninta ya katse ne sanda taji su Bassam na gaisheshi, amsawa yayi yana shafa kan Basma yana faɗin "Babyna kin tashi lafiya..?" Tana haɗiye chips ɗin data tura abakinta tace "Lafiya lau Daddy. Allah Daddy Today u look so Fine kamar ɗan saurayi ko Bassam..?." Ta faɗa tana dariya gyaɗa kai yayi yana faɗin "Eh mana Daddy.." Dariya yayi fararen haƙoranshi suka bayyana yana kallon 'ya'yan nashi cike da jin daɗi ya ɗago kenan karaf idonshi ya faɗa ana Mufeeda data shagala da kallonsa rage fara'arsa yayi yana faɗin "Mufee uwar Naila, har tayi barci ne..?" Saurin dawowa cikin hayyacinta tayi kafin ta sadda kai ƙasa tana faɗin "Eh Daddy, Ina kwana..?" Yana duba agogon hannunshi ya amsa Iya tace "Ai da zarar Mufeeda ta goyata zaka nemi kuka ka rasa sai kuma barci ai inaga ko aure Mufeeda zatayi Alhaji sai kun yi haƙuri Naila tama Mufeeda zaman ɗaki.." Ta faɗa Tana dariya, shima murmusawa yayi Basma ko dariya ta saka tana faɗin "Mufeedan Iliya mai rake..." Ta faɗa tana ma Mufeedan gwalo, itako tana ɓalla mata harara, duk yana lura dasu, bai tanka ba sai ma ya maida hankalinsa wajen kallon agogon hannunshi yana faɗin "Kunga lokaci na tafiya ku kula da kanku zan tafi Ɗanbatta.." Ya faɗa kanshi tsaye yana ƙoƙarin ɗaga fulas ɗin ruwan zafi dake wajen ya tsiyaya ruwan cittan cikin wani kofi Basma ce ta miƙe tana faɗin "Kai Daddy shine bakace mu shirya ba." Bassam yace "Eh mana Daddy don Allah zamu bika mun kwana biyu bamu bika ƙauye mun je mun gaida Goggo da Inno ba.." Ya faɗa yana ɓata fuska, Mufeeda ko tunda taji an ambaci Ɗanbatta idonta ya ciko da hawaye tana tunanin kullum sai tayi mafarki gata gaban Inna Fulera suna hira da dariya, amma sai ta tashi taga ba haka ba, rabonta da garin yau wata biyar kenan tun auren Lantana data roƙi Daddy ya saka direba ya kaita tayi kwana ɗaya ta dawo. Yana kurɓan ruwan cittan daga tsaye ya dakata yana faɗin "Islamiyanku fa..? Kuna so yau kuyi missing ne..?" Ya faɗa yana kallon fuskokin Bassam da Basma, Basma ce ta fara buga ƙafa tana faɗin "Plz Daddy na yau kadai...plz Don't say no..." Ƙura mata ido yayi yana kurɓan ruwan Lipton dake hannunsa kafin ya sauke yana faɗin "Ok..ok kuje ku shirya sai mu tafi.." Ya fada yana ajiye kofin ruwan lipton ɗin dake hannunsa. Jin abunda yace ne yasa Bassam da Basma suka daka tsallen murna suka rungumeshi suna faɗin "Tanque Daddy..." A tare suka bashi peck agefen kumatunshi kafin su sakeshi kowa ya rumtuma zuwa ɗakinsa yana murna, Iya na musu dariya, Mufeeda kuwa shiru tayi ta duƙar da kai tana ƙoƙarin share ƙwallar data biyo gefen ƙunnenta, Tahir na lura da ita sai ya murmusa yace "Kema Mufee tashi kije ki shirya ki kuma shirya Naila duka mu tafi harda Iya, tunda bazamu barta ita kaɗai a gida ba.." Mufeeda jitayi kamar an sakata agidan aljannah Firdausi haƙoranta duka awaje tace "Da gaske Daddy...?" Kai ya gyaɗa mata yana kallonta yadda jikinta yake rawa saboda murna, ga goyon Naila amma haka ta kwashi gudu ta shige ɗaki da mamaki Tahir ke kallonta ganin goyon na rinjayarta Iya kuwa miƙewa tayi tana dariya tace "Nagode Alhaji kamar kasan ko ina son komawa garin nan naku gaskiya iyayenka ko nace gidanku suna da kirki sosai..." Ɗan murmusawa yayi baiyi magana ba illah ficewa da yayi yana faɗin "In kun shirya ku sameni awaje.." Mintina talatin yayi musu yawa kowannensu ya shirya baki yaƙi rufuwa karma Mufeeda taji labari wacce ke ji kamar ta buɗe ido ta ganta gaban Inna Fulera saboda yadda ta zaƙu ta ganta, ta chanza kayan jikinta wannan karon less ne ajikinta riga da zani, sai hijabinta hakama Basma itama wata shadda ce ajikinta iri ɗaya dana Bassam itama hijabin ta saka don Tahir bai yarda da sanya mayafi ba kwata kwata bama ya yarda ya siyo musu ko Farida ta siyama Basma bata sakawa in Daddy na nan saboda tasan baya so, hakama Iya ta shirya itama tsab, kayan abinci Tahir yasaka aka ɗebo daga Store aka cika booth ɗin motar kafin Garzali ya shiga mazaunin direba Tahir ya shiga gaba Mufeeda da Basma da Iya da Bassam suka shiga gidan baya da yake motar nada yalwa, nan da nan yayi ma mator key ya saki horn lokaci ɗaya Megadi ya wangale musu get suka sulala waje yana musu fatan isa lafiya da kuma dawowa lafiya. ****** *ƊANBATTA* Ƙarfe 11pm na safe motarsu ta tsaya adaidai ƙofar gidan Hakimi wanda tunda suka shigo garin Ɗanbatta yara ke bin motarsu da gudu ana faɗi ga Tahir ɗin gidan Baba Hakimi nan yazo saboda yara da manya sunsan yadda in yazo suke warkewa domin haka zai fito ƙofar gida yayi ta rabon kuɗi baya tsayawa sai ƙudin dayazo dashi duka sun ƙare, shima tunda suka shigo garin yake ta amsan gaisuwan mutane daban daban har zuwa ƙofar gidan mahaifin nashi wanda ke zaune a ƙofar gida kan wata kujera daga ƙasa kuma wata ƙatuwar tabarma ne mutane na zazzaune talakawa masu kawo ƙorafe ƙorafansu, shiko mai girma Hakimi Mansur na zaune bisa kujeran nan yana sanye da babbar riga kansa da rawani farin dattijo ne mai farin gashi da dattako, tunda motar ta tsaya farin ciki ya cikashi na zuwan ɗan nashi mafi soyuwa a cikin ranshi, nan da nan mutanen wajen suka miƙe kafin ma Garzali ya zagaya ya ɓude mai murfin motar har ansamu waɗanda suka buɗe mai suna mai barka da zuwa kamar wani babban mutum zakuyi mamakin yadda dattawa ke girmama Tahir sakamakon mutum ne nagari hankali da hikima kuma duk abokan mahaifinsa ne ya zauna cikinsu lokacin yana zaune agarin kafin ya koma cikin garin Kano domin yin makaranta sakamakon shine ɗa ƙwara ɗaya tak namiji da Allah ya bama Baba Hakimi. Hannu ya basu suna musabaha lokaci ɗaya yana ranƙwafawa alamar girmamawa har zuwa bisa tabarman dake wajen ya duƙe yana gaida mahaifinsa hakama Bassam yayi, miƙa masa hannu Baba Hakimi yayi yana faɗin "Yaka nan samarin birni.." Ya faɗa yana dariya tashi Bassam yayi yaje kusa da Baba Hakimi ya zauna ya miƙa mai hannu sukayi musabaha yana tambayanshi ya karatu daidai ƙarisowan su Mufeeda suma durƙusawan sukayi suna gaisheshi da mutanen dake wajen amsawa yayi cike da murna yana kallon fuskokinsu kafin yace "A'a amaryata me kika zomin dashi..?" Basma na dariya tace "Kaji ka me nazo maka dashi ko kuwa mai ka tara min? Nazo karɓan nawa kajin ne da zabbin wannan shekarar.." Ta faɗa tana dariya gaba ɗaya wajen sai da aka murmusa ganin duka haƙoran Hakimi awaje yana dariya kafin yace "Au hakane, toh ki shiga ciki ki kama iya iyawarki, amma in Abu ta ganki ba ruwana.." Miƙewa tayi tana faɗin "Sai me..? Nida abun mijina.." Ta faɗa kamar da gaske, Dariya yayi yana kallon Mufeeda wacce ta sauko Naila data fara rigima hannu ya miƙa mata yana faɗin "A'a wanake gani kamar 'yar wajen Fulera...?" Tahir dake gefe ya taso ya karɓi Naila ya miƙa ma hakimi yana faɗin "Eh itace ranka ya daɗe.." Karɓan Naila yayi yana faɗin "Masha Allah...Allah yayi maka albarka Attahiru, kai kaga yara duk sun girma gama wata amaryar tawa inaga fa nan zan dawo.." Ya faɗa cike da barkwanci yana kallon fuskar Naila wacce ke zare ido tana bin kowa da kallo, dariya aka sakama Hakimi jin abunda yace, miƙewa su Mufeeda sukayi suka shiga cikin gidan suka bar Bassam da Tahir da Naila dake hannun Hakimi. Gidansu Tahir babban gida ne mai ɗauke da shashe huɗu ginin bana ƙauye bane amma ginin gidan sarauta ne, duk da yanzu Tahir ya ƙara gyara gidan sosai shashen farko na Baba Hakimi ne na biyu kuma na uwargida sauratar mata wato mahaifiyar Tahir Zainabu Abu wacce suke kira Goggo, sai shashe na uku na mai bi mata ne Salamatu wacce suke kira Innaro sai shashen ƙarshe wacce na marigayiya Binta ne aka mai dashi ɓarayin 'yan aiki da kuma wajen ajiye hatsi, gidan Hakimi cike yake da al'umma daban daban kuma babu 'ya'yansa ko ɗaya sai 'ya'yan talakawa da mutanen gari da kuma masu musu hidima acikinsu harda Inna Fulera mahaifiyar Mufeeda tana ɗaya daga cikin hadiman gidan Hakimi masu dafa musu abinci. Tun isowarsu yara suka shiga da gudu suka sanar da zuwansu toh dayake Basma ta rigasu shiga suna shiga suka isketa kwance kan ƙafar tsohuwa mai ran ƙarfe Goggo Abu kana kallonta kaga inda Tahir ya kwaso kyawawan idanuwa da dogon hanci, gashin kanta cike da furfura ta zauna bisa wani lallausar cafet daya mamaye tsakar ɗakinta mace mai kirki da sanin ya kamata suna shigowa da sallama ta ɗago tana amsawa cike da fara'a lokaci ɗaya tana yi musu maraba. Gefenta suka zauna Iya ta fara gaisheta ta amsa cikin sakin fuska kafin Mufeeda wacce ke wulga ido tana son ganin ta inda mahaifiyarta zata ɓullo, cikin fara'a Goggo Abu tace "Mufeedan Fulera an zama 'yan mata ko..?" Ta faɗa tana dafa kanta murmushi tayi tana sadda kai kafin Iya tace "Aikam duk sun girma Goggo harda wannan lukutar banzar data haye miki ƙafa.." Ta faɗa tana zungurin Basma wacce ta tura baki tana faɗin "Kai Iya don ma ta samu na hau wannan ƙafar nata data kusa expier.." Make mata kai Goggo Abu tayi tana faɗin "Tashi ja'ira so take ta ƙarisa ni ta samu damar auren min miji ita kaɗai.." Dariya suka saka banda Mufeeda datayi shiru ganin haka yasa Goggo Abu ta tattaka ta miƙe bayan ta ture kan Basma tana faɗin "Ku tashi ku shiga shashen Innaro ku gaisheta inaga bataji zuwanku ba.." Ta faɗa tana nufar hanyar ɗakinta na ƙurya, miƙewa sukayi suka fita sai shashen Innaro ita ma falonta kamar na Goggo Abun ne durƙushewa sukayi suna gaisheta ta amsa cikin sakin fuska tana yafito Basma da hannu ta ƙariso da sauri ta kwanta ajikinta cike da shagwaɓa tana faɗa mata wai Goggo Abu ta hanata zama a cinyarta Innaro na dariya tace "Aiko zata gamu da mai girma Hakimi amarya guda ai dole mu lallaɓaki.." Ta faɗa tana dariya Iya na tayata Mufeeda ce tace "Innaro ina Innata tunda nazo ban ganta ba, ko ta koma gida ne..?" Innaro tace "A'a Innarki na madafi Mufeeda.." Jin haka yasa Mufeeda ta tashi da sauri ta fice kamar zatayi tuntuɓe su Basma suka bita da kallo Innaro tace "Yi a hankali Mufeeda karki faɗi, ina ruwan Mufeeda akwai ƙulafucin uwa ni banzaci ma zata yarda ta zauna gidan Attahiru har tayi wannan daɗewar ba.." Iya tace "Toh ya zatayi amma fa ranar da aka tuna da Inna Fulera toh wuni za'ayi sharan ƙwallah.." Innaro ta saki murmushi kafin tace "Allah sarki ina ruwan Mufeeda haka itama uwar take sai dai dayake ita tana da kunya da kawaichi ko tana kewar ɗiyar tata bata taɓa nunawa.." Iya tace "Allah sarki..Haka abun yake bagashi yanzu tasamu kyakkyawar rayuwa ba ai wallahi babu abunda zamu ce ma Alhaji sai fatan gamawa da duniya lafiya.." Innaro ta gyaɗa kai tana faɗin "Ameen Ameen...Haka Attahiru yake kowa nashi ne, yafi son kyautatama mutane fiye da ya kyautatama kanshi.." Iya tace "Ba shakka munga zahiri muda muke zaune tare dashi.." Mufeeda ko tana fitowa daga shashen Innaro ta nufi babban madafin gidan Hakimi nan tayi ta gamo da 'yan aikin gidan suna gaisawa kowa na mamakin ta ƙara girma gabda shiga madafin sai ga Inna Fulera ta fito da sauri domin itama ta samu labarin zuwan su Mufeedan kamar a mafarki suka ci karo ido Mufeeda ta zaro tana faɗin "Innata..." Da ƙarfi kafin ta rumgumeta cike da murna itama cikin tsantsar farin ciki ta ƙanƙameta tana murnan ganin ɗiyarta tilo ƙwara ɗaya da Allah ya bata. Ɗagowa Mufeeda tayi tana hawayen farin ciki tace "Innata banzata zuwa ganinki ba ayau...Kina lafiya..?" Kanta Inna Fulera ta shafa kafin ta gangaro tana share mata hawayen fuskarta tace "Nima haka farin cikina, yanzu Gaje ke sanar dani zuwanku kunzo lafiya..?" Farin cikina kin ƙara girma kina jin daɗin zaman gidan Alhaji ko?" Gyaɗa kai Mufeeda tayi idanunta cike da ƙwallah tana dariya tace "Innata mu koma gida akwai labari.." Dariya Inna Fulera tayi kafin ta riƙo hannunta tana faɗin "Yanzu kuwa farin cikina, bari na barma Maman Lantana sallahu sai mu tafi.." Da sauri Mufeeda tace "Yauwa Innata Lantana fa..? Ko sun tafi birnin ita da Ladonta..?" Inna Fulera tace "Tun yaushe bayan auren da wata biyu suka tafi can Kano gidan da yake gadi da zata tafi tazo tamin sallama tayi tacewa na gaisheki.." Kawai sai Mufeeda ta hau sharar ƙwallah tana faɗin "Allah sarki Lantana Allah sa mugana.." Murmushi Inna Fulera ta mata suna riƙe da hannun juna suka nufi madafi Mufeeda maƙale da ita tana mata surutu. ******* Tahir ya daɗe awaje wajen Baba Hakimi da jama'ar wajen bai shigo ba sai da ya gama rabama mutanen wajen kuɗin da yazo dashi yara da manya, Bassam ya aika yace ya sanarma Goggo Abu ta dama mai fura shida Garzali, nan ya shiga ciki ya barsa toh bai shigo ba sai da yaq gama da wajen kana yama Hakimi sallama da zai shiga wajensu Goggo. Goggo Abu na zaune ta gama dama ma Tahir furarsa kenan ta tsiyayarma Garzali nashi cikin wani kofin silba mai kyau ta miƙama Bassam kenan yayi sallama ya shigo kafaɗarsa ɗauke da Naila wacce tayi barci hannun Hakimi, Goggo Abu ta ɗago tana amsa sallamar nashi fuskarta cike da annuri kai tsaye gabanta ya nufa yana ƙoƙarin zama ta miƙa hannu tana faɗin "Kawo ta nan dama da ita kukazo..? Ina uwarta take ne kuka zo da ita ita kaɗai..?" Ta faɗa tana karɓanta lokaci ɗaya ta miƙe ta shiga da ita ciki ta kwantar da ita shi kuma Bassam tuni ya fice zuwa waje ɗauke da fura zai kaima Garzali Allah Allah yake ya fita ko ya samu damar shiga cikin gari kafin Daddy ya farga bayanan don Bassam akwai son ƙauye musamman ma na Babansu. Sai da ta fito kana tazo ta zauna inda ta tashi tana turamai kwanon sha mai cike da fura da nono tana faɗin "Lafiya na ganku kamar daga sama inace shekaranjiya mukayi magana da kai sai sati na sama zaka shigo ba.." Ta faɗa tana kafeshi da ido, rausayar da kai yayi kafin yaja kwanon furan ya buɗe yana motsawa da ludayi kafin yace "Goggo Farida bata nan ta tafi bikin ƙanwar ƙawarta Abuja tun wajen kwana uku da suka wuce.." Ya faɗa yana sadda kansa ƙasa, shiru Goggo Abu tayi kafin tace "Naji, shine dalilin zuwanka kenan ko..?" Ta faɗa fuskarta ba annuri bai ce komai ba illah maida kanshi ƙasa da yayi yana kurɓan fura itama ganin ya mata banza sai ta ƙyalesa sanin halinsa na miskilanci, bai ƙara magana ba sai da ya gama shan furan nashi kafin ya ture kwanon yaja murfi ya rufe yana faɗin "Alhamdulillah..." Ya faɗa kafin ya gyara zama yana faɗin "Goggo ya jikin ɗan wajen Ashe..? Jiya munyi waya take sanar dani Muda ba lafiya..? Tana matsa ƙafanta data miƙar dasu take faɗin "Yaji sauƙi sosai ɗazu da safe nan yake.." Daga haka bata ƙara magana ba matsowa yayi yana tayata matsa ƙafar yana faɗin "Wai har yanzu ƙafar bata bar matsa miki ba Goggo..?" Bata kalleshi ba tace "Tayi sauƙi kasan jikin tsufa fa abun sai a hankali..." Ta faɗa kai tsaye murmushi yayi ganin yadda Goggo abun ke wani cin magani duk don karya mata maganar daya saba ne, amma duk da haka bai haƙura ba gyara zama yayi yana matsa mata ƙafa yana faɗin "Goggo akan maganar Farida ne, tsakani ga Allah na gaji da haƙuri da ita da kuma hallayarta nazo ne na ƙara roƙonki ki bani dama na sanar ma da Baba Hakimi zan ƙara aure..." Ya faɗa yana ƙoƙarin son su haɗa ido. Ƙur kuwa tamai da ido kafin tace "Har sau nawa zan ce maka kabar wannan maganar Attahiru, maganar Farida nace kayi haƙuri yarinta ke damunta banaso ka yi abunda iyayenta zasu ga kamar mun ɗaure maka gindi ka tozarta musu yarinya. Cike da wani jin haushi ya marairai ce yana faɗin "Toh amma Goggo..." Kabar maganar nan nace ko Attahiru...?" Goggo Abu ta katseshi rai ɓace, kansa ya sadda a ƙasa yayi shiru yana jin kamar ya kurma ihu, ganin yadda yayi ne sai tausayinsa ya kamata ta dafa kanshi tana faɗin "Kayi haƙuri zan yi magana da ita Faridan insha Allahu kaji..." Kai kawai ya ɗaga mata idanuwansa sun canza launi saboda ɓacin rai. Ya daɗe zaune shuru kafin ya saki ajiyar zuciya ya miƙe yana gyara hulan kansa yana faɗin "Bari na leƙa na gaida Innaro daga can zan gangara wajen Ashe naga jikin Mudan." Kai ta gyaɗa kafin tace "Adawo lafiya.." Jiki asanyaye ya fice ta bishi da kallo wani tausayinshi na ratsata amma kuma bazata bari ya sanar da Hakimi wannan maganar ba sai ta ƙara magana da Faridan tunda abu na zumunci ana tare tun ba'a haifesu ba bazata bari Tahir ya ruguza wannan zumuncin ba. Koda ya shiga wajen Innaro Iya kaɗai ya gani koda ya tambayi Basma sai Innaro tace ta tafi gidan Innarsu Ashe bai daɗe ba ya fito zuwa waje ya sanya Garzali ya buɗe booth yace ya shiga da kayan ciki, shi kuma yayi sallama da Hakimi akan zai gangara gidan Ashe dayake babu nisa da ƙafa ya taka, duk inda yabi ana gaisheshi cike da girmamawa da ban sha'awa har ya isa gidan Ashe can ya iske Basma da Bassam wanda ya gansu a ƙofar gida shida Mudan wanda sa'an Bassam ɗin ne, ita kuma Basma suna cikin gida ita da Laila ƙanwar Mudan ce 'yar wajen AShe dayake tana da tsawon ƙafa har takamo girman Basma. Nan Mudan ya ɗuka yana gaida Kawun nashi shi kuma ya riƙoshi yana hararan Bassam da wasa shiko yana dariya riƙe da hannayensu suka shigo gidan Ashe na ganin Yayan nata ta shiga ina zata saka dashi Laila ma tazo ta gaisheshi ya riƙe hannunta yana tambayanta karatu bai wani daɗe ba ya miƙe ya mata sallama zai tafi 30k ya fito dashi daga aljihu ya bata ta karɓa tana ta godiya 5k ya bama Mudan da Laila yace su siya wani abun buƙatar nasu suna ta murna har waje suka rakosu Ashe natama Yayan nata godiya su Mudan kuwa har gidan Hakimi suka rakasu inda Tahir yace suyi haraman tafiya nan fa aka nemi Mufeeda aka rasa Goggo Abu tace yanzu haka sun koma gida ita da Inna Fulera Tahir bai damu ba yace sai su biya su ɗauketa nan ya cika Goggo Abu da Innaro da kuɗi hakama Baba Hakimi wanda ya dinga sakamai albarka tare da nasihan riƙo da gaskiya Allah ya taimakesu har sukazo tafiya Naila nata barci, wajen karfe 3 na yamma motar su tabar ƙofar gidan Hakimi bayan su Laila da Mudan sun sanar da Kawun nasu wannan hutun yasa azo aɗaukesu agidanshi zasuyi hutu yace karsu damu in sun samu hutun zai turo Garzali yazo ya tafi dasu, murna ta cikasu harda su Bassam, wadanda suka kwaso zabbi da kaji gidan Hakimi wai zasu kiwata Tahir na kallonsu ko tankasu baiyi ba bazai shiga tsakanin jikokin da Kakanninsu ba. Daganan sai ɗan karamin gidan da Inna Fulera ke zaune suka tsaya Iya ne da Basma suka shiga basu daɗe ba sai ga Mufeeda ta fito ita da Inna Fulera ganin haka yasa Tahir ya fito yana amsa gaisuwan Inna Fulera wacce ke neman dukamai tana ta zubamai godiya harda ƙwallarta kuɗi ya ciro 20k ya bata ta kasa karɓa sai kuka take tana faɗin "Nagode Alhaji wallahi basai kabani ko sisi ba alherinka ga Mufeeda kaɗai ya isheni ka tufatar da ita ka ciyar da ita haka zalika ka ilimantar da ita kuma baka taɓa bambamceta da 'ya'yanka ba duk da ta kasance ita ɗin hadimarka ce mai renon 'ya'yanka wallahi bani da bakin gode maka sai dai nayi fatan Allah yasa kagama da duniya lafiya ya kuma sakamaka da gidan aljannah Firdausi.." Da Ameen yake ta karɓawa cike da jin nauyin godiyarta gareshi da ƙyar ta karɓi kuɗin suka rungume juna ita da Mufeeda suna kuka gwanin ban tausayi kafin su saki juna Mufeeda ta shiga mota suna dagama juna hannu har suka bar ƙofar gidan, sun fita cikin garin kenan Naila ta tashi wacce ke hannun Tahir ya waigo yana kallon Mufeeda yana faɗin "Toh Maman Naila bar kukan haka nan gashi tana kukan neman uwar ɗakinta.." Ya faɗa cikin barkwanci yana miƙa mata Naila cikin jin kunya ta share ƙwallarta ta miƙa hannu ta karɓeta nan da nan ta ɓalle jakar data zubo kayan madaranta da Flaks ɗin ruwan zafi da ƙaramin kofi da cokali ta dama mata madaranta ta shiga bata nan da nan takoshi sai kuma ta koma barci bisa kafaɗarta ta kwantar da Naila ita kuma ta jingina kanta jikin ƙofar motar tana sharae ƙwallah.. Ta madubin gaban motar yake kallonta ajiyar zuciya ya sauke kafin ya murmusa yana faɗin "Tasan kan renon yara.." Ya faɗa yana maida kanshi cikin jikin cussinon ɗin kujeran motan shi kuma Garzali ya saki kan mota yana bata wuta. *Don"t Forget To comment,Vote and Share*
0 Comments