MIJIN KWAILA. HAUSA NOVELS

 MIJIN 'KWAILA....2*🤦🏽‍♀




*chapter 5*




*by Maman meenat*








*Inayinku over y'an gaban goshin mum meenat do or die we are 2gether for ever insha Allah.always ur part of me ..*

*my die fans...hajara ghandi,sweet mum janar...my miss Ayush...jamila Muhammad...Mr's hamza....kai kunada yawafa nasan yawanku yawuce lissafin Alawee😍*





*My Qawa ta Amana,kawar arziki kawar Albarka farin wata shakallo ta Maman meenat me taqama da ayar Allah. .kinyi naki kinyi na raggo yanda kika ziyarci gidan mum meenat saboda 'Kauna Allah yabani ikon zuwa kano nakwaso shockie na 'kannin shaheed😜FATIMA ABUBAKAR MAMAN SHAHEED (KUSKURE)writer,mum meenat love you and respect to you over wlh so much luv u..*❤.






Jin maganar gwaggo rabi ya tilasta fito da aneesa tasaki murmushin ganin gwaggon,itama gwaggo rabin murmushi tasaki tana tambayar "y'ar nan kina ciki dama?"
Anee tasake sakin karamar dariya,"ina ciki Granny kwalliya nakeyi."
Tafad'a da jujjuya idanuwa.
Baki gwaggo rabi ta mere dacewa"oh sabon salo wai miya d'uwawu 'kunshi,wata kazar ce kuma gurani?(Granny) "
Anee ta fashe da Dariya sosai tace "kai don Allah gwaggo I mean kaka fa kenan."
Tsaki gwaggo rabi taja tayi gaba tana fad'in "yau dai nalura wani sabon kad'afiri kika tsiro dashi,ninan kar nake kallon kowa."

Tayi 'bangarenta abunta bayan tazabgama gefen zahra harara.

Oganniya zahra wacce taci kukanta tabama uku lada bayan shigewar Anee daki koda wasa takaici baibarta sake tunanin komawa kitchen din karo abunci ba,itama dakinta tanufa kangado tafad"a tasaki kuka sosai kewar ummanta da baba kai harma da kawayenta su ummilolo da uwande tagama cika ranta.
Idan har a taata haukar takurata Anee zataci gaba dayi toko lallai bazata jureba,gida zata koma ita dama bawani dad'in zaman gidan takeji ba.
Yaushe rabonta dazuwa tonon fad'a satar kifi da tusa wa me awara?

Tsaki taja,shikenan su ummilolo sunmata wayo sunata zuwa yawonsu itako anmata Katanga bata fita ko ina.

Yau kam alwashi tasha gida zata kwana,sam dad'in benen ma tayafe bataso.wurin umma zata koma.
Jakarta tafito tasoma yayimar kaya tana watsawa ciki,saida ta tabbata tagama cika jakar ta'ajiye agefe guda yau kam sai gida!take fada aranta.

Daga zaman shiru kuma saita bude wardrobe kukar 'bahe ta d'ebo ta hada da sikari a kofi ta kad'a tasoma zuqa tana y'an wakokinta hawaye duk sun bushe a fuska. 
Tunin duniya ta manta dawata wai ita Anee.
Da kofin korbebe a hannu bacci yayi a won gaba da ita.


Kamar koda yaushe yauma d'in sai wajen 7:30pm yashigo gidan da brief case a hannunsa agajiye kwarae yake sosai.
Sallama yayi falon tsit! Babu kowa sai kamshin turare da karar A.C,ahankali yake takawa har ya karaso inda tafkeken hoton nata yamamaye gefen kusurwar da aka makalashin.
Hannunta na dama sa'kale cikin nashi,saina hagun tad'aga wani card da alama na shedar kammala karatune don gown din dake jikinta ta shaida hakan.
Tayi matu'kar kyau har dai ko yaushe bakinta da murmushi kumatunnan a lo'be rolling daya zame mata jiki yana akanta.

Gabanshi yaci gaba da fad'uwa,sai yake ganin kamar tana rayene.wai sai yaushe zaidena kewar zahransa ne?
Sai yaushe ne zuciyarahi zata dena bugawa a duk second na kallonshi da ita?
Shafa gefen fuskarta yayi,yanasonta yanason komai nata kai! Yasaalam!
Tabbas soyayya ba karya bace.

Jingina yayi a jikin bangon idanunshi a numshe baisan yanda zai kwatanta meyakeji a ranshi ba.
Kamshin turaren Anee me fisgar hankali ya bud'e kafofin hancinshi,kamar kada ya kalleta amma bazai iyaba.
A kasalance ya bud'e idanun yazube akan fuskarta takuwa haskeshi da murmushinta.
Ta juyar dakai,kawai.


"Wlcm back," tafada da sigar yaudara dik da har a ranta taji kishin hoton zahra datakama yana kallo,tarasa jarabar daya nacenawa a wannan bakar matar me d'agggen hanci.

Bai iya bata amsaba sai sake lafewa dayayi ajikin bangon dakin.
Ta danne takaicinta,tahanyar sa'ka yatsunta a cikin nashi.

"Damuwa..damuwa bata haifar dakomai sai nadama my sheyq,Allah daya amsa zahra yayi replacing dinta da biyu fa.bai kamata kayima Allah butulci ba,kasaki ranka ka amshi jarabawar Allah ko late zahra tasamu takwanta makwancinta a cikin salama.domin lallai tasan ruhin masoyinta yana acikin walwala."

Yanda take maganar acikin kunnenshi da salonta yasakashi sauraronta,kuma tabbas tayi nasarar tankwaro zuciyarshi cikin ruwan sanyi.
Duk da be tankamata ba amma baimata shamaki daga jagorar datayi mashi tazuwa dakin taba.


Dakanta ta temakamishi wajen rage kayan jikinshi,duk da aranta tana ayyana anya zata iya wannan aikin data fara kuwa? Tun ba'aje ko'inaba duk jikinta ciwo yake.

Ganin tana niyyar rakoahi toilet yasakashi bata umarnin fito mashi da kayan dazai saka

Bahka taso ba,amma baamatsala.
[12/20, 8:46 AM] Real Mum Meenat😍: Kaya marasa nauyi ta fitar mashi,takoma tagyara dining.

Saida yagama shirinsa tsaf suka fito atare,sunyi kyau dukansu kyawawane na kwatance.

Kusan duka gidan sun hallara a dining dinne inka dauke zahra wacce take d'aki tana buga game din Mario.
Sam batamasan tym yatafi haka ba,don tun farkawarta wanka kawai tayi da sallah tasoma game dinta.


Cike da kissa Anee tasoma serving mummy abincin abunda bata tabayiba a tsawon zamanta gidan,kai ba ishaq mummy da gwaggo rabi ba hatta hanan tana mamakin canjawar Anee a lokaci guda haka.

Isha'q ne yami'ke da sauri, bayan ajiye spoon din dayake kokarin kaiwa baki.

Duka da idanu suka bishi sai gwaggo rabi datayi kokarin watsamar tambayar"oh ni rabi! Ina kuma zakaje daga fara cin abincinka sai kace me cutar d'an kanoma?"
Batare daya juyo ba yabata amsa"banga zahra ba tunda nadawo."

Aneesa ta had'e rai sosai,tare da ajiye spoon din dayake hannunta.tana sonjin me wani zai furta a cikinsu.

Gwaggo rabi ta'be baki tayi taci gaba da cin abincinta.

Yayinda mummy tace"lallai nima yau banji duriyarta ba tun dawowata."


Takaici yadad'a 'kule Anee.


Tana bisa gado tajuyama kofa baya,ita kadai ke surutunta da game tana dariya.
Sweet cotton gown ce ajikinta talafe a lukutin jikinta sosai,kannan marason kallabi yatashi fiiiiya abayanta.

Fuskarta tayi haske,kila hakan yanada nasaba da ynda batayi kwalliyar taba yau tatsaya iyakar Vaseline kawai.


Jitayi an rufe mata idanu tabaya,kyalkyalewa tayi da dariya dacewa"nasan hanan ce,wooyi na ganota."
Jin shiru yasaka tasoma fad'in"dallah bud'eni,ainasan kece."

Numfashin mutum taji yana sauka a saitin wuyanta da sauri-da sauri.

Tuni cikinta yabada "quuuuilulii"
Yage baki tayi iyakar karfinta daniyyar zubduma ihu taji ya rufe mata baki yana dariya.
.
Bude idanuwa tayi ganin isha'q yasakata mi'kewa da fashewa da kukan takaici ta rarumo pillon dake kan gado ta jefa mashi.


Kaucewa yayi yana dariya dayimata gwalo.


Tasake hassala wannan karon d'auko filon tayi tabishi aguje tana kuka,"wlh Sena rama yaro ban yarda."

Shiko dariya yake dacewa"cab! Asheko zaki rame😜yana mata gwalo."


Binsa tayi a guje suka nufi falon kasa yana dariya tana kuka.


Anee dake zaune sai juya cokali takeyi tama gaza gane a duniyar datake ayanzu.


Kusan 5mns daga kiran zahra ba zahra ba isha'q?

Badon kada tabata rawarta da tsalle ba dataje anyi duka mai yuwuwa Sam bamazata jura ba.

Zuciyarta na ayyana mata wama yasan mesukeyi a d'akin kai namiji munafuki tafada aranta zuciyarta na suya.


Kamar daga sama suka ganshi ya runtumo a guje yana haki da dariya ga zahra da katon filo a hannu tana biye dashi.




Post a Comment

0 Comments