MIJIN KWAILA. HAUSA NOVELS

 MIJIN 'KWAILA....2🤦🏽‍♀*




*chapter one*






*written by Maman meenat*





*Editing A'isha Abdullahi T. Fulani*





*HAPPY SALLAH....🤝🏽*





....... *KOTU* tayankema zahra d'aurin shekaru tamanin agidan yari....itace Kalmar dataci gaba da amsa kuwwa acikin kunnuwan isha'q wsnda yafarka firgigit kamar wanda aka tsikara da allura,ahankali yasoma bin dakin dayake ciki da kallo.Tabbas dakinsune ba kotu ba,musamman dayakai dubanshi akan fuskar gimbiya anee daketa kwasar baccinta hankalinta kwance abinta.
Ahankali kuma dukkan abunda yafaru acikin mafarki yasoma dawo masa aka tamkar dai magijine aka kunna masa dake nuna mashi hoton komai din yanda yafaru"yasalam"Kalmar 
Daya furta lokaci guda yasoma sharar zufar data tsatsafo akan goshinsa,
'Wai meke shirin faruwane dashi dakuma Amanarshi *zahra* wai zahra in prison, kaii! It will never happened"Abunda yake maimaita wa kenan saika dauka shida wanine yake maganar.
Durowa yayi daga bisa gadon dayake kwance bayan yasake tulama anee katon blanket dasuka rufa dashi,takuwa juya gami da sake ruqunqume bargon abinta.
Yajuya yanufi wardrobe bayan zura fara kal ta jallabiyya daya biyo baya,ficewa yayi adakin baiko dubi hanyar toilet ba baretane yasaka ran wanka,a tym din zahra kawai yake burin yayi tozali da kyakyawar fuskar ta me debemashi damuwa.

Dakinta yanufa wayam bata ciki sai dai ga tulin kayan wardrobe dinta nan data fidda gaba daya tawatso atsakar dakin.Saikuma gefe guda tarin yayan magarya ne datasha tajuye yayan a plate da alama shanya abinta tayi.

Yagirgirzakai zahra badai rigima ba,abunda ya raya acikin zuciyarshi.yanufi part din mummy sai dai bai karasaba yahango zahran kofar kitchen da y'ar roba a hannunta,ranshi yabashi da'akwai abunda takeson aikatawa....Saikuma mafarkinshi yadawo fess akan idanunshi yanufeta dasaurin gaske tana hangoshi tasoma dashe bakimta duka,karasawa yayi kusa da ita yarage tsawonshi tahanyar durkuwasa yakasance tsayinsu yazamo dayane yakama hannayenta dake rike da robar yana juyawa"menene wannan" shine tambayar daya watsa mata.

Tsurama ruwan ciki idanuwa tayi,saikuma tarage murya sosai tace"inka yarda amana idanna fada maka bazaka fadama kowa ba?"

Tayi maganar tana kafeshi da idanunta masu shagaltar dashi.

Numshe nashi idanuwan yayi ahankali yace"nayarda"

Zahra datayi kasa'ke saikuma tace"Amanatun...Amana..wa'azabatun azaba,yaro gwaggo rabi zan zubamawa ahanya daga tataho tana masifa saita fad'i mukuwa musha dariya,"tafada tana dariyar tun kafin abun yafaru.

Gaban isha'q yasoma bugawa da sauri-sauri yarike robar hade da yan yatsunta yatsura idanuwanshi cikinnata har saida ta kauda nata idanun tanacewa"nidai kadena kallona haka idanunka sai ingansu kamar na mage🐱😜
"Mage kuwa?" Isha'q ya tambaya yana murmushi kasa-kasa,zahra data murguda baki tace"eh mana,jinake kamar inta kallonka fa..."

Yasaki dariya akan saikuma yace"bani wannan robar kada kisake attempting yima wani mugunta hakan babu kyau, halin yn wutane kekuwa nasan yar aljannah ce koba haka bane?"

Zahra tasoma murmushi sosai tana gyada kai,bakuma tayi kokarin hanashi robar hannun nataba.

Isha'q amsa yayi yaje yazubar harya dawo tana inda take atsaye,kama hannayenta yayi "oya muje kiyi wanka..Ina jamee(me aikinsu) tazo tagyara dakinki.

Zahra wadda tamakale kafa tace" nidai yaya saikayiman goyon kura"

"Goyon kura kuma zahra"
Isha'q ya tambaya donshi baimasan wani goyon kura ba,tace"eh kokuma kayiman makawuya ba"

"Yasalam! Nikam duka wadannan ban sansu baamafa,"

Bude idanuwa tayi saikuma Amana asaki kukan shagwabar data tsiro dashi kwanannan na babu gaira babu dalili.

Tuni isha'q ya sunkuceta sama yasoma shillawa yana juyawa da'ita dukansu dariya suke kyalkyalawa yayinda zahra tamakale wuyanshi 
Tamau tana sheka dariya abinta..

"Yau nashiga ukuna ni rabi'atu mezan gani da namata..."

Gwaggo rabi tafada lokacin datake karasowa wajen rike da casbaha a hannunta.

Bama Susan da zuwanta ba baretane abunda dake fad'i.
Hakan yasake 'kona mata rai,tadage iyakar karfinta ya caulama isha'q carbin abayanshi abunda yazo mashi a bazata yasaki zahra dasauri.

Tasulmiyo batakai kasaba yasaka duka hannayenshi ya tareta,suka fad'i atare yayinda zahra tafada akan ruwan cikinshi...

Idanunta suka nitse cikin nashi,suna hada idanuwa tamashi gwalo,shikuwa ya lakace hancinta duk suka sheke da dariya...

Abinda yadada tunzura gwaggo rabi tace"au dariya nabaku tabbatattu,shikenan isiyaku kazama sallamamme akan wannan 'kwailar yarinyar dababu ibanda ta'iya sai jaraba..gotai gotai dakai kadauki yar cikinka kana wannan hauka da ita..."


Sauran maganar tata tatsaya cik! Hango anee dake labe jikin kofar dazata sadaka da kitchen din tana hawaye...



Loading.... *Anty Alawee*😍
*MIJIN 'KWAILA.....2🤦🏽‍♀*








*written by Maman meenat*






*Editing Aysha Abdullahi T. Fulani*






*chapter 2*




Dasauri gwaggo rabi takarasa kusa da anee saida takare mata kallo kamar bazata tankataba saikuma tamere baki tace"kekuwa lafiya kika tasa jama'a kina zubar da ruwan hawaye saikace wadda akama albishir din mutuwar kishiyar gyatumarta.."

Anee takauda kai ranta amatukar jagule,saikuma tajuya fuuuu tanufi part dinta.
Gwaggo rabi tabita da idanuwa kamar yanda zahra da isha'q suka bita danasu idanun.

Yayinda gwaggo rabi ta tabe baki dacewa"kyaji dashi med'an Karan kishin tsiya,"
Tajuya taci taga da surutanta"yoni inma banda kee dakika rako mata duniya har wannan *kwailar* ce zatasaki zubar da hawaye yanda Allah yagama tsara halittarki tako Ina "takuma Jan tsaki" bokonki sam be amfana maki komiba."

Tajuya tana kwafa gami da lekawa kitchen din da inna delu keta hikirkirin had'a tuwo a warmer kallo daya tamata tajuya abinta.

Ahankali isha'q yasauke ajiyar zuciya,yasabi zahra akan kafadarshi harzuwa dakinta da already angama gyarashi kai tsaye toilet ya direta yace"oya kiyi wanka maza banason dattinan"

Zahra data sake shagwabewa tace"tonidai kazo ka cud'ani ai hannuna baya kaiwa bayana"

Isha'q ya fidda idanu yanacewa"idan bananan wayene yake cud'akin?"

"Hanan mana",
Zahra wadda ke kokarin shigewa bayin tabashi amsa.

Ido isha'q yaware,kai ,ahra tana kwamacala yanda yakamata.

Dakanshi yashiga bandakin harta tu'be kayan jikinta tasoma tara hannayenta jikin shower tana wasa dashi,tana ganin isha'q tasaki murmushi hade da dukawa tana dauko soson wankan.

Wani masifaffen shock ya ziyarci isha'q tundaga kan babban yatsan kafarshi har yazuwa tsakiyar kanshi yaruntse idanu dasauri komai zai iya faruwa kallonnan dayakema yarinyar nan ahaka.

Sam zahra bata fahimci komai ba saima tambayar data watsomashi" wai me akai naga kana runtse idanu?"

Bai iya bata amsa ba sai dai hannu daya mika ya'amshi soson already tasaka sabulu hakan yasa yasoma gurzawa abayanta cikin wani yanayi daya kasa tantance koma namenene..

Akalla ba akasar ba yadau kusan 5mins yana juya soson akan lallausan gadon bayan zahra wadda tagaji da zuqunawa tamike tana cewa"kainifa bahaka ummana da hanan suke cud'ani ba,waikai saikayita gogawa bakasa ruwa kuma baka denawa."

Sai alokacin isha'q yafarga da abunda yakeyi,dsauri ya sakemata ruwan agadon baya yafice toilet din cikin mawuyacin hali.

Kai tsaye part din anee yanufa har lokacin tana cika tana batsewa,suna hada idanu tasake shan mur tana aikamashi sakon harara yayinda yasakar mata murmushi gami da sharce mata ruwan hannunshi akan fuskar ta.

Takauda kai ranta a dagule,matsowa yayi inda take zaune abakin gado hade da dora hannayenshi akan kafadarta.

Tasoma kiciniyar ture hannun nashi takasa,yayinda yasoma zagaye dukkan jikinta da hannayennashi.
Kasa jurewa tayi tamike tsaye tana harararshi saikuma tasoma "mezanmaka isha'q? Aibanan yakamata kazoba wajen waccen kwailar yakamata kakoma tunda harzaka iya bata dukkanin tym dinka abinda kagaza bani.kagoyata akan gadon bayanka kana dariya da ita abunda baka taba kwatantawa agareni ba.saikaje kagama lagujeta sannan kadawomun nan kana zaton zan kawarma da kishin ruwanka ko?"

Saikuma tasoma kuka tanacewa"don Allah isha'q meyasa baka sona,meyasa ka tsaneni why...isha'q why...u hate me"

Baibari taqarasa ba yahade bakinshi danata yasoma bata darasi mai zafin dayasakata manta awacce duniya take,dayake er hannu ce sannan kwarai isha'q yakaranci lagonta adan zaman dayayi da ita .

Saida ya tabbatar tagama shiga hannu sannan yarabu da ita yadauketa cak ya aza bisa cinyarahi ahankali yasoma magana"kidena cewa banasonki anee kisani ke babbace bazai yiwu duk abunda nayima zahra yazama lallai saina aikata agarekiba kamar yanda itama bata samu 100%na abunda nake baki,itafa goyon kadai kikesha kekuwa megoyonma sha kikeyi ba?...."

Yakare maganar yana daga mata gira.

Ta kyalkyale da dariya kamar ba itace maiyin kukaba,fadawa tayi jikinshi suka haura babban filin jirgin Aminu kano...bansani ba killa jidda suka nufa😜.



Zahra kam tana gama wankanta fitowa tayi abinta daga ita sai pant data saka tun a toilet, batako dubi inda kayan shafa sukeba takutsa karkashin gadonta tajawo wata yar bakar leda tulin gorubane da magarya aciki saikuma taura.

Qirgawa tayi taware wasu agefe,takulle ledar tamayar kasan gado tadauki goruba guda tadage dai-dai karfinta tana gwaguya tana wasa wakokinta wanda rabi duk shirmene take jabga abinta.

Wardrobe tabude saikuma taruntse ido tace"yasin duk Wanda na cafko shizan saka..."

Tadora hannunta cikin wardrobe din tasoma lalube,asa'a kuwa talalabo bakar jallabiyya tabude idanu taganta rigar bakace doguwa har kasa sai-dai hade take da hularta Wanda akama ado da kunnen zomo..

Bata damuba tazura rigar  tazauna gaban dressing mirror tana taunar goruba tanama madubi gwalo da malgwada baki tana fiddo harshe da idanuwa.

Ahaka tagama cin gorubar tajefar tsakiyar Chinese carpet dake malale adakin tasoma fesa kwalliyarta wanda tasoma da foundation tace"hmm ainaga bidiyon make over na wayar Anty hafsa....yama take cewa...tadauko foundation tafara wannan shine foundation tadai fara acting like professional make over din.

Sai daifa tun awajen saka foundation takauce hanya don saida tagama zazzage akwatinta tas babu brush na shafa foundation hakan yasaka daukar zanin data cire tajabgashi akai tasoma danbarama fuskar abunka da liquid yakuwa daddanqare mata.

Bata damuba tasoma jagira"ummmm cinko ma zanyi"

Tafada lokacin datasoma durza eye pen akan girarta ganin kamar baya fitowa yasata cillar dashi dafadin"shege kadama kayibaga kwalli ba"😏
Tafada da murguda baki bayan tasoma jagiran da kwallin matsayar jagirar agefen kunne bashine yafi 'kayata zahra ba a'a yanda tad'ora jagirar asaman ainahin natural gira da Allah yabata.saiya kasance giranta daban jagiran daban.

Takuwa bishi ta zagaye da foundation maimakon concealer dabata gani acikin kayan shafar nataba.

Wannan yabama girar tata damar cakulewa tazama tamkar ta gwaggon biri,duk da haka zahra saida ta danqara powder akan goshinta kasan habarta cheeks nata amatsayin highlight kai ranar zahra sam bata hango na biyunta wajen kyauba.

Musamman yanda tajabga janbaki meruwan ganye akan lebennata takuma tattakura tazagaye abinta da bakin kwalli,


Tasoma sakin murmushi tana tsuke baki kamar yanda taga masu nuna make up din sunayi bata raba d'aya biyu wajen gwanancewarta akan kwalliya kota amare tayi..
*Nace ba mr's hamza...mizz Ayushh...hajara ghandi ko zakuzone zahra tamaku ranar sallah*😝🤪

Daga wannan tsakar gida tanufa,gidan tsit bakowa kasancewar rana tatake sosai wannan yabata damar nufar get wajen maigadi..saidai bata hangoshiba taja tsaki afili tace"wajen gwabama zanje inhaye bishiya insha shagalina"

Kai tsaye garden tanufa,wata ringijejiyar bishiyar gwaba tahanga yayanta sun nuna kwarae hakan yasakata hadiye yawu ta takarkare tamakale bishiyar tasoma tsinka tana gatsawa intaji zaqi ta cinye,intaji bauri tajeho kasa....

Tana sama gwaggo rabi  takaraso wajen daya kasance wajen hutawarta saboda rana,acewarta batason rabar esay tana bugunta ga ni'ima daga Allah.

Karkashin bishiyar gwabar ta shimfida dardumarta da casbaha a hannunta tadan kishigid'a tana lazumi.

Zahra hankalinta yana akan gwaba sam bataga zuwan gwaggo rabiba wannan yabata damar cilli dawata rusheshiyar gwaba Mara dadi afili tace"katuwar banza saigirma ba dad'i"

Gwaggo rabi datadan saurara jin siririyar murya bisa bishiya yasata sake natsuwa😆sai dai fa batayi auneba taji jifaaa tuiiii! Gefen kafarta tajanye dasauri tana fadin"kai jarababbun tsuntsaye basason barina insha Inuwa"

Takai dubanta akan gwabar da niyyar dauka sai kuma tajefar dasauri ganin shacin hankoran mutum fici-fici...jikinta yabata ba lafiyaba,

Ahankali cikin fatgaba tad'aga kanta mezata gani....

Zahrace tawatso idanunnan nata amatukar tsorace don harga Allah batasan dazuwan gwaggo rabiba face sambatu datajiyo daga kasa...

Wata razananniyar kara gwaggon tasaki dayasaka zahra durowa wa....





Loading......



*Anty Alaweeen dai😍*

Post a Comment

0 Comments