Masu cushe aikin albashin jihar bauchi .asarin wassu ya tuno

 Asirin masu Cushe cikin Albashin jihar Bauchi ya fara tonuwa masu Bincike sun gano wasu masu Sace Miliyoyin kudin da sunan biyan Fansho

__________________


A yau ne Jami'an tsaro suka fidda rihoto kan wasu mutane da aka cafke masu zambatar Jihar Bauchi miliyoyin kudade Dukkanin karshen wata da sunan biyan Fansho wannan mutane sun amsa Laifin su kai tsaye. 


Hukumomi sun bayyana sunayen su da kuma Hotunan su ga manema Labarai Domin ya zamo Darasi ga Yan baya 


(1) Yasir Sulaiman mai shekaru 37 mazaunin unguwar Bayan Airport ya cusa sunayen mutane biyu, hakan yasa yake karban N320,000 duk karshen wata har na tsawon watanni 23, jimillar kudin daya zambaci jihar Bauchi ya kama N7.360,000 


(2) Umar Mohammed Madara dan shekara 49, mazaunin Ibrahim Bako quarters ya cusa sunan mutum daya, wanda yake karban N120,000 duk wata har tsawon watanni 6 wanda jimillar kudin daya zambaci jihar Bauchi yakai.N720,000.

.


(3)Samaila Musa mai shekaru 38 mazaunin unguwar Federal Low-cost ya cusa sunayen mutane biyu, hakan yasa yake karban N65,000 da N85,000 duk karshen wata har tsawon watanni 18. Jimillar kudin daya zambaci jihar Bauchi sun kai kimanin N2, 700,000.


(4)Garba Bala mai shekaru 39 mazaunin unguwar Tirwun ya cusa sunan mutane biyu, yana karban N300,000 duk karshen wata har na tsawon watanni 36 wanda jimillar kudin daya zambaci jihar Bauchi yakai N10.800,000.


Wannan Babban Lamarine da kuma Babban Nasara ne ga jihar Bauchi ya kamata Alumma Subada Gudumuwa da hadin kansu ga Gwamnatin jihar Domin kawo karshen masu aringizon Alba


shi ga jihar mu.

Post a Comment

0 Comments