makauniyar soyayya hausa novels

 MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*


  *BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




*Ina mika gaisuwa ta ga*

*Miss Marriam novels group*


*Maejeeddarh Othman* (Home of Hausa novels group)


*Ummi*(Kainuwa Writers fans)


*Mhiz Tawerh* (nima ina yin ki sosai)


*Fannata ta Annabi* (zinder)


*Hussaina Paki*(‘yar garin mu)


*Da sauran wanda ban samu damar anbata ba sabida yawan Ku*


*Na gode da son da kuke ma novel d’in nan*🤝🏽


*Allah ina rok’on ka 🙏🏽🙏🏽🙏🏽 kabar mu da masoyan mu a du inda suke*, *ka nisanta mu da masu mana hassada da bak’in ciki da k’iyayya*




*Wannan karan ban samu wanda suka ba da amsar question of the day na tambayar da nayi na cewa* 

*ya sunan bishiyar dake cikin aljanna*?

*Amsar ita ce* *Jannatul kuldi*


*Ina jin dad’in yadda kuke gwada hazak’ar ku*.


*Allah ka k’ara mana ilimi mai amfani*.





*Tunatarwa*


Hak’uri ya kasu kasha uku 🤟🏼


* Hak’uri gurin yi ma Allah biyayya 


 * Hak’uri saboda kiyaye dokokin Allah da sa'ba mishi


* Hak’uri gurin jarrabawa


Dukkan hak’uri yana tare da nasara, ya Allah ka bamu ikon hak’uri.






17&18


Ko da muka je gidan yaya Aminu, hira muka zauna muka yi da Anty jiddah kasancewar ta ita ma ‘yar hirar gashi tana da jan mutane kamar ba dangin mijin ta ba.


Muna cikin hira da ita ne take ce mana "ina ko Faruk, kwana biyu bai lek’o mu ba, bari in munyi waya dashi zan ce mai kar ya bari azumi yazo bai yi aure ba, in ba haka ba, zamu ba dashi sadaka"


Dariya muka yi gaba d’aya kana Anisa tace "ya koma Abuja, yana can yana fama da fad’an shi"


Ni ce na k’ar’bi zancen da cewa "ai da su Momi za su taimaka su mishi aure saboda ina jin har da rashin auren ne yake sa shi wannan fad’an da yake yi, amma kuma ina tausayawa matar da za ta auri yaya Faruk saboda ba k’aramin hak’uri za ta yi da fad’an shi da miskilancin  sa ba"


Murmushi Anty Jiddah tayi kana tace "ni da zai bi shawarata da na za’bar mai kalar type d’in shi saboda ita yarinyar za ta iya dashi"


Zaro ido nayi ina cewa "pls Anty kar ki fara, ki tausayawa ‘yar mutane, ki jik’anta in ba so kike ki sa yarinya ya aure ta, ta fara k’ashin wuya a rasa dalili ba alhalin yaya Faruk ne yake gasa mata gyad’a a hannu"


Anisa ce ta kar’bi zancen da cewa "Anti in dai zai ji shawarar taki, pls ki masa magana saboda yayi auren nan nima in samu sakewa a gida saboda komai a takure nake yi kamar a gidan yari" ta k’arashe zancen kamar za ta yi kuka.


Dariya muka fara yi saboda yadda take maganar, abin har ran ta haka yake.


Haka muka ci gaba da hirar mu kamar wasu k’awaye.


Sai da muka ci abinci sannan muka yi sallar la’asar, ba yadda ba tayi ba akan mu jira yaya Aminu ya dawo ya kaimu amma muka k’i, saboda in har muka jira shi ba lallai ya kaimu gidan k’awar mu ba amma yanzu tun da driver muke, ba mu da wata matsala.


Sallama muka yi mata kana muka nufi gidan Aisha k'awar mu.


Tun da muka je gidan muka dasa hira irin ta k’awaye, muna cikin hirar ne nake sanar dasu yanda muka yi da yaya Faruk ran da zai koma Abuja.


Dariya suka yi gaba d’aya, ganin dariyar tasu kamar da manufa suke yasa na d’aure fuska kamar ba dani ake hirar ba.

Anisa ce ta k’ara kallo na ta fashe da dariya tana cewa "wato Sister a yanzu na samo satar amsa a dramar da kuka yi da yaya Faruk da kuma dalilin da yasa ya hana mu chat da kuma takura mana da yake yi"


Kamar ya? Na tambaye ta.

 

Wani kallo ta min tana k’unshe dariyar da take bakin ta saboda yadda ta ga na d’aure fuska.


Fatima! Zargi na ya fara hararo min cewa yaya Faruk son ki yake yi! Anisa ta fad’a.


Dam! na ji k’irji na ya buga saboda yadda maganar ta zo min a bazata.


Dariyar rainin hankali nayi sannan na k’ara d’aure fuska.

 

"Anisa Kenan! ke a ganin ki mun dace da yaya Faruk? let me tell you something, na san yaya Faruk na da duk wani qualities da mace take buk’ata a gurin namiji, but to me, ba na daga cikin su saboda ke shaida ce na yadda tamu ba ta zo d’aya dashi ba, kuma ana yin aure ne idan jinin ku had’u da mutum ko ra’ayin ku amma ni duk a ciki, ba bu ko d’aya, So plss kar k’i k’ara bi na da irin wannan bak’ar fatan though shi yaya Faruk d’in ma bai ce yana so na ba kuma a yanayin girman kan shi, nasan bazai kula ni ba saboda har yau kallon yarinya yake min" 


Yanayin fuskar Anisa ce ta canza zuwa ‘bacin rai saboda maganar da na fad’a akan yaya Faruk bai mata dad'i ba kuma in da kara ai bai ci in fad’a mi shi haka ba don haka tace "Fatima ya kamata in zaki fad’i Magana ki tauna, kuma in da ka’ra bai kamata ki fad’i wannan maganar a gaba na ba saboda kar ki manta yaya na ne kuma zan ji zafin duk wanda ya zage shi a gaba na kuma duk wannan abun shi yaya Faruk bai sani ba, ni ce na ce ina zargin haka"


Jiki na ne yayi sanyi saboda ban zata maganar za ta ‘bata mata rai ba don haka nace "Sorry Sister, ban san maganar zata miki zafi ba, but am sorry to say, ba na iya ‘boye abin da ke cikin raina ne"


Duk wannan conversation d’in da muke yi, Aisha ba ta sa mana baki ba sai yanzu ne ta k’ar’bi zancen da cewa


 "Sisters ku bar wannan chapter d’in is not useful tun da shi yaya Faruk d’in bai fito ya fad’a ba, so plss dukkan ku kuyi hak’uri"


Dariya muka yi gaba d’ayan mu amma a raina na k’udurta k’ara nisanta duk wani alak’a da za ta had’a ni da yaya Faruk, duk da a yanzu ma ba abin da ke had’a ni dashi sai takurawa da fad’a.


Haka muka ci gaba da hirar mu kana muka canza akalar hirar tamu zuwa ga yadda jarabawar mu ta Waec da Neco take ta matso wa.


Misalin biyar da rabi muka mik’e dan tafiya gida saboda Dadi na hanyar shi ta koma wa gida.


Rako mu Aisha tayi har inda Driver d’in mu yake, sai da taga fitar mu daga gidan su sannan ta daina d’aga mana hannu.


Ko da muka isa gida, toilet na fad’a na watsa ruwa saboda yadda ba na shiri da zafi yayin da Anisa ta fad’a gado tana lumshe ido

San da na fito daga wankan, samun ta nayi tayi nisa a bacci.

Duka na kai mata a jikinta ina hararar ta, a firgice ta mik’e tana murza idanu alamar magagin bacci.

"Ke wai wace irin lazy ce, daga d’an fitar nan da muka yi shine kika wani baje kina bacci a zafin nan, kin wani saki baki sai kace wanda muka tafi a k’afa" nace da ita.


Amsa min tayi da cewa "in ban yi bacci ba me zan yi, kina ganin tun d’azun muka fita, ai dole ka gaji"


Simple English wears na sa, na juya ina kallon ta nace "yi ta barci ni kinga ma na bar maki d’akin" na fad’a ina fita daga d’akin.


Ko da na fito parlour ba kowa, zama nayi a d’aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun dake k’awata parloun.

Wani film naga ana haskawa a tashar Mbc Bollywood mai suna *Ramaiya vastavaiya*

Hankali na ne ya tafi kan film d’in saboda ina son indian film especially love film din su.


Yanda jarumin film d’in RIYA ya baro garin su ya tawo garin buduwarshi SONA duk da ba wani kud’i gare su ba, hasali ma ba a cikin gari suke zaune ba, ya taso a cikin daula, amma hakan bai dame shi ba illa ma hak’uri da ya dinga ba yayan Sona d’in akan ya barshi ya zauna tare dasu. 

Sharad’in da yayan Sons d'in ya gindaya ma jarumin ne ya ban mamaki,

Saboda yayan yace zai ware mai fegi d’aya na gona ya nome hatsi kuma zai dinga wanke shanu amma duk ya yarda.


Hmmm lallai na yarda india sun iya wahala akan so in ba haka ba yaushe zan yarda da wannan sharad’in.


Sai naji jarumin ya burge ni saboda ina so in ga masoya nason junan su tsakani da Allah.


Anisa ce tazo ta zauna kusa dani tana cewa "Fatimah! d’an ban labarin film d’in tun da ba a fara da ni ba’

Yamutsa fuska nayi ina cewa "pls Anisa don’t interrupt me, naga ke baki san yadda nake ji da lovers bane shi yasa zaki ce in baki labari alhalin ba gama film d’in nan aka yi ba".


Ta’be baki tayi tana cewa "ke idan kina kallo sai ki maida film kamar gaske, wai da kike zancen lover’s kina soyayya ne da zaki san mahimmancin so? Anisa ta tambaye ni.

Hararar ta nayi kana nace "in ma ina soyayyar ai kin fi kowa sani"

Murmushi Anisa tayi kana ta ce "irin kune Fatimah in kuna so baku iya son abu kad’an ba"

"Kan ki ake ji" na ba ta amsa a tak’aice.


Ba wanda ya sake Magana a tsakanin mu, muka maida hankalin mu kan allon talabijin d’in muka ci gaba da kallo.

Sai da film d’in ya k’are kana na juyo na kalli Anisa na ce "Sister dan Allah soyayyar Riya da Sona bai burge ki ba"

Kallon mamaki take min sannan tace "sun burge ni, sai aka yi yaya? Ta k’arashe zancen cikin zolaya.


Tsadadden murmushi kawai nayi ba tare da nace mata komai ba.

Haka muka ci gaba da hirar film d’in, kiran sallar magrib ne yasa muka mik’e muka nufi d’aki don ba da farali.

[3/23, 13:02] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



     *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽





*QUESTION OF THE DAY*


*Menene sunan bishiyar da take a cikin Aljannah*?






15&16


*Ci gaban labarin*


Dawowar Ummu d’akin shi ya tabbatar min da yaya Faruk ya tafi, harara ta tayi tana cewa "ke wai Fatima wani irin kunnen k’ashi gare ki? Ki na ji yayan kin a min sallama zai koma bakin aiki amma ko ki fito ki masa sallama".


Cikin shagwa’ba na fara cewa ‘ai Ummu gwara da ya tafi! mutum ya bi ya matsa min kamar a kan sa nake zaune, ni dama yayi ta zama a can Abujan da naji dad’i.


Murmushi kawai Ummu tayi kana tace "Allah ya shirye ki auta"


Dariya kawai nayi na mik’e ina cewa ‘amin Ummu, bari inje in k’arasa kallon film d’in da na ke yi wannan masifaffen yaya Faruk yazo ya katse min kallo na.

Film d’in na mayar na ci gaba da kallo na saboda yadda film d’in ya tsaya min a rai.


Scene d’in karshe ne ya fi ba ni tausayi akan na baya, tun mutuwar Jenny, johnny ba ‘kara samun natsuwa ba.


Kamar yadda suka yi wa juna alk’awari na cewa in sun mutu zasu had’u a wata duniyar, a cewar su a nan zasu ci gaba da rayuwar su.


Johnny ne yake tafiya akan keke yana tunanin mutuwar Jenny, unfortunately kawai mota tazo ta bige shi wanda a take anan shima ya fad’i ya mutu.


Lallai wannan soyayyar Johnny da Jenny ta kai a sa ma film d’in endless love.


Ganin film d’in ya k’are yasa na mik’e na nufi d’aki ina raya wa a raina an ya yanzu za a iya samun wanda zasu so junan su kamar yadda Johnny da Jenny suka yi wa junan su.





*ABUJA*

(Birnin tarayya)



Misalin k’arfe biyar na yamma, Yaya Faruk ne zaune yana sanye da farar vest a jikin sa da short nicker, a hannun shi rik’e yake da kwalin exotic.


Idon shin a kan allon k’aton Tv d’in da ke girke a d’akin amma da alama hankalin shi ba akan kallon yake ba.


Mafita yake nemar wa kan san a ganin in ba haka ba wankin hula zai kai shi dare, kuma hausawa na cewa A bari ya huce shi ke kawo rabon wani.


A rayuwar shi baya son yin abu da gaggawa domin yana iya jawo da nasani.


Yana cikin wannan tunanin ne yaji sallamar abokin shi Mus’ab, amsa masa sallamar yayi kana yazo ya zauna kusa dashi yana cewa "Allah yaja da ran Brigadier, ya aka yi ne, na ganka so cool?.


Shiru yayi kamar bazai amsa mai ba, sai da yaja wata ajiyar zuciya kana y ace "Mus’ab ina tare da wata ‘yar matsala, zuwa na KD, Mom and Dad sun nuna min damuwar su akan rashin aure na, na samu na lalla’ba su akan su k’ara min time saboda ko ita yarinyar ban sanar mata da cewa ina son ta ba kuma kai kan ka kasan komai akai"


Mus’ab ne ya kalle shi cikin kulawa yace "Farouk! For how long will you take you to tell that girl that you are in love with her, let me tell you Faruk, opportunity comes at once, so you have to face her that you really love her, ya kamata kayi amfani da damar ka kafin ta kufce maka saboda shi so ba a mishi haka, hausawa na cewa da zafi zafi ake bugan k’arfe, lokaci yayi da zaka fad’a mata saboda kar ta kamu da son wani ya zamana kana Son maso wani k’oshin wahala"


Faruk cikin damuwa yace "the bad news that i don’t expect from her shine in na fad’a mata ina son ta tayi rejecting d’ina, Mus’ab ban san wani hali zan shiga ba saboda ta dad’e a cikin zuciya ta wanda zai min wuya in iya cire ta at once"


Dariya Mus’ab yayi yana cewa "haba Bregadier! Kamar ba soja ba wanda ake turawa yak’i gari daban daban kuma kayi winning, kamar ba kai bane mata ke kawo kansu kana yarfa su, sai gashi akan yarinya d’aya duk ka bi ka damu kan ka"


Murmushi kawai yayi saboda ganin yadda Mus’ab ya maida zancen wasa.


Mus’ab ne ya mik’e ya mik’a mishi hannu don yin musabaha yana cewa "bari in k’arasa block d’in mu dan nasan tana nan tana jira na, sai k’orafi take min ka kwana biyu ba ka lek’o mu ba, ba ta san soyayya ce take d’awainiya dakai"


Shima mik’e wa yayi dan ya taka mai yana cewa "ba laifin ka bane, laifin soyayya ce take son maida ni rago"

Dariya suka yi gaba d’aya kana suka nufi bakin k’ofa dan ya taka mai.



 

*KADUNA*


Tun tafiyar yaya Faruk na samu sakewa yayin da na ci gaba da yin chat d’ina ba tare da fargaba ba duk da in Ummu ta gani tana min Magana ko tayi min barazanar za ta had’a ni da yaya Faruk in ya dawo.


Yau ba mu da School kasancewar an bamu hutun ‘happy maulud’ na kwana biyu.


Ganin haka ne yasa yau tun da safe na tambayi Abbu akan zan je gidan su Anisa in kwana, cewa yayi in sa diver ya kai ni.



Misalin k’arfe sha d’aya na safe n agama shiri na saboda a yau nake so in munje mu rok’i Momi ta bar mu muje gidan k’awar mu Aisha na yadda take mana k’orafin ba ma zuwa sai dai ita tazo..



Ummu na tarar a falo tana kallon Manara Tv, na zo na zauna kusa da ita ina cewa "Ummu zan tafi sai na dawo’

In kinje kya gaishe da su Anisan da Hajiya Hajaran"


Mik’ewa nayi ina cewa "zasu ji"


Na nufi parking space inda driver yake jira na

Knocking nayi ina jiran a zo a bud’e min, Anisa ce ta bud’e k’ofar tana gani na ta daka tsalle tana murna, nima na rungume ta muka nufi cikin falo.


Momi ce ta sakko daga upstairs tana cewa "A dole ku cika min kunne ashe babbar k’awa ce a gidan"


Dariya nayi ina cewa "Momi barka da hutawa"


Cikin yalwatar fara’ar ta take amsa min da cewa "yawwa Fatima, ya mutanen gidan"


"Lafiya lau sun ma ce a gaishe ku" na amsa mata

Muna amsa wa’ Momi tace

Hira muka fara yi da Momi kana muka nufi d’aki muka d’aura daga inda muka tsaya.


Gaskiya ina jin dad’in zuwa gidan su yaya Faruk saboda yadda Momi ta ke so na, in naje rasa inda zata ajiye ni ta ke yi don murna kuma a gidan mun fi sakewa muyi abun da muke so saboda Momi ta ce a daina takura mana, da zarar munyi aure za mu daina abin da muke yi.


Bayan sallar azahar ne muka je muka samu Momi akan zamu je gidan yaya Aminu daga nan zamu biya gidan k’awar mu.


Fatan a dawo lafiya ta mana sannan ta gargad’e mu akan kar muyi yamma saboda kar Dadi yazo yayi fad’a.

[3/23, 13:02] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



     *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




*Wannan shafin naku ne kyauta na yadda kuke son wannan novel d’in*


*Tawakkaltu A Abdul*

(Mhiz Tawerh)

❤❤❤❤❤❤


(Kince kin fi kowa son wannnan novel d’in)


*Nafisa Khaleed* (bintu Khaleed)

💕💕💕💕💕💕


*Da sauran Wanda suke son wannan novel din*.


*Ina gaishe ku*🤝🏽





*Question of the day*

Wace mata ce a cikin matan manzon Allah (s.a.w) Allah ya d’aura auran ta a sama?






19&20


Da daddare bayan mun ci abinci dasu Dadi da Momi muka nufi d’akin mu, gado na hau ina cewa "Anisa akwai data a wayan ki?


Kallo na tayi da alamar tambaya kana tace "me zaki yi da data yanzu kuma ni ban gan ki da littafi ba bare in ce ko browsing d’in assignment za ki yi"


Wani gajeren tsaki na ja sannan nace "in zaki bani ki bani don kin ga waya na ba data shi yasa sai kin min tambayar rainin wayau?


"Sorry Sis pls me za ki yi dashi saboda ina son in karanta wani novel ne da aka turo a wani group kuma na ji ance novel d’in yayi dad’i tun kan yaya ya hana mu chat" Anisa ta fad’a.


"Wani abu zan duba a internet yanzu zan baki" na ba ta amsa..


Mik’o min wayar tayi kana ta tashi ta kunna d’an madaidaicin plasma tv dake jingine a bangon d’aki, ta d’akko remote ta zauna a rest chair dake d’akin tana canza channel.


Kai tsaye whatsapp d’in ta na shiga na maida wayar silent saboda kar taji pinking d’in message.


Wata bak’uwar number ce na ga an yi min sallama.


Kai tsaye na amsa sallamar tare da tambayar "da wa nake magana"


Sai da aka d’au kusan 3 min kafin aka min reply da cewa "uban wa ya baki izinin yin chat"


A raina na ce wannan d’an rainin hankali ne da zai min wannan tambayar, sai na maida masa amsar "ba uban kowa ya bani izini ba illah ikon kaina"


Sai aka k’ara turo min da cewa "kin san da wanda kike Magana kuwa"


"ya za ayi in sani tun da ba duba nake yi bare in sani" na k’’ara da sa hoton keyboard moji na alamar murgud’a baki kana na tura text d’in.


Sai da aka k’ara d’aukan kusan 4 min kafin a turo min message da cewa


 "hmmm Anisa sorry for yourself tun kan in dawo ki fara kuka da hawayen ki, tun da ban isa in ba ki command ki bi ba, yanzu kina ganin kin girma, idan na dawo zaki san da wanda kike chat, you will regret what you have done tun da ba kya jin magana stupid kawai" abin da aka rubuta a message d’in Kenan.


Zaro ido nayi saboda sai a yanzu na gane da yaya Faruk nake chat saboda a chat d'in wata number yake using ba wacce muke da ita ba, duk da na tsorata amma hakan bazai hana in nuna mai har yanzu ban gane da wanda nake chat ba, amma a zuciya ta kuwa fargaba da tsoro ne suka cika ta saboda nasan abin da zai biyo baya idan ya dawo.


Don haka sai na maida mishi amsa da cewa "pls wai da wa nake Magana ne? ka zo sai fad’a min Magana ka keyi son ranka, if you will not introduce yourself, I wanna block you" hannuna na rawa na tura saboda ina so in ga k’arshen dramar da muke yi ni da yaya Faruk.


Message ya turo inda yake cewa "nasan kin gane ni, ki ke fad’a min magar da kika gadama, zaki iya blocking d’ina a yanzu amma ki tabbatar da in na dawo sai na canza miki kamanni, in baki yi wasa ba, abin da zan miki sai kin manta a wace duniyar ki ke dan sai na canza miki kamanni"


Duk da na tsorata da message d’in da ya turo kuma har yau bai san ba Anisa ba ce amma haka na k’ara tura mai reply da cewa


 "Kan ka ake ji"


Bai k’ara turo reply ba, dan haka naci gaba da chat d’in da nake yi da ‘yan class d’in mu da kuma ‘yan group d’in mu saboda group d’aya muke da Anisa.


Vibrating d’in da wayar take yi ne yasa nayi saurin kallon screen d’in wayar.


Sunan Yaya Faruk na gani a jikin screen d’in, da sauri na mik’a wa Anisa wayar ba tare da na ce mata komai ba.


Ko kan ta d’auka, wayar ta k’atse, wani kiran ne ya sake shigowa a karo na biyu.


Da sauri Anisa tayi receiving d’in kiran cikin ladabi saboda ganin sunan yaya Faruk a jikin screen d’in


"Anisa kin zama ‘yar iska ko? ni kike fad’a wa maganar da kika gadama a chat! tun kan in dawo ki fara tausaya ma kan ki saboda ina jin sai na karairaya ki ko Momi ta kusan haifar wata ba ke ba dan ina jin sai an  kira miki mai d’auri, dan abin da zan miki sai kin sha mamaki na, na ga alamar kin fara manta ni ne….. .


Ai tun kan ya gama fad’ar maganar da yake yi Anisa ta fara kuka ta yi kneel down tana cewa cikin maganar kuka


 "wallahi yaya ba dani kayi chat ba, ka tausaya min, Fatimah ce ta ari waya ta tace zata yi browsing, ban san chat za ta shiga ba, ta sake fashewa da kuka a karo na biyu k……

"Wannan matsalar ki ce" abin da yace kenan ya katse wayar.

Anisa ta sake fashewa da kuka tana cewa "wayyo Momi kizo ki cece ni! Fatima kin ja min!

Duk da ta bani tausayi saboda ni kaina shaida ce akan muguntar yaya Faruk amma yanda take kuka ne ya ke bani haushi Dan yadda take kukan kamar yaya Faruk na gurin.


Cikin jin haushi nace "Wai Sister miye abin kuka kamar wadda tayi wani babban laifi, kuma da kike wannan kukan ina ki ga yaya Faruk d’in, shi yasa wani sa’in kike ‘bata min rai saboda tsoron ki yayi yawa".


Duk da kuka take yi amma bai hana ta d’agowa ta harare ni kana tace "tun da kin ja min ai dole kice haka".


Dariya nayi kana na ce yanzu ya kike so ayi" na tambaye ta.


"Ki kira shi ki ce da ke yayi chat ba dani ba, in kika yimin haka kin taimake ni" Anisa ta ba ni amsa.


Zaro ido nayi sannan na ce "ki yi hak’uri kawai hukuncin ya hau kan ki tun da bai san dani yayi chat ba, kuma in dai yasan ni ce ina jin gunduwa gunduwa zai yi dani" na fad’a da alamar tsoro a fuska ta.


Ganin yadda Anisa ta tayar da hankalin ta yasa na d’kko waya ta, na kalle ta cikin jin haushi na ce "dan Allah ki mana shiru, zan tura mishi text a waya ta in fad’a mishi ni ce nayi chat da wayar ki".


Murmushine ya su’buce a fuskar ta kamar ba ita ke kuka ba, nima tsoro ne fal cikin raina saboda nasan duk san da ya diro garin nan, zan fuskanci hukunci mai tsanani a gurin shi.


Haka kowa ya kwanta da tunanin mugancin yaya Faruk.


Sai da nayi kwana biyu a gidan su Anisa kasancewar hutun yazo a tare da weekend sai ya zama kwana hud’u Kenan za mu huta sannan na tattara na koma gida ina mai jin dad’in hutun da nayi a gidan su Anisa saboda yadda nake sake wa a can ba tare da an sa min ido ba.




Yau da yin jamb d’in mu kusan wata biyu kenan wanda yai daidai da zuwan jarabawar mu ta Waec.


Dan haka ba ni da wani hutu illah karatu da na sa a gaba saboda yadda nake so in fito da grade mai kyau.


Mun fara waec exam d’in ne da Practical d’in biology a watan may/june kana jarabawar ta ci gaba da gudana cikin nasara.


Ran k’arshen exam d’in mu ka k’are da rubuta Islamic studies wanda daga nan muke sa ran samun nasara a sakamakon mu sai kuma Neco da za mu rubuta..


Ba mu samu wani hutu ba kasancewar waec da Neco ba nisa muka fara rubuta jarabawar Neco a watan June/July.

Haka muka gama rubuta jarabawar cikin nasara da taimakon Allah.



Bayan gama jarabawar mune muka fara tunanin yadda graduation d’in mu zai gudana saboda gaskiya mun shirya ma ranar.



 Yau kusan watan yaya Faruk uku da tafiya a Abuja wanda yayi daidai da ranar graduation d’in mu.

Gaskiya naji dad’in wannan ranar saboda an yi hotuna na tarihi da ciye ciye, gashi an rausaya a ranar.


Haka muka yi ta yin exchanging d’in numbers kamar kar a rabu, wasu har kuka suka yi saboda ganin an rabu Kenan kuma ba lallai a sake had’uwa ba, ni kaina sai da nayi hawaye, na kuma yarda da hausawa ke cewa sabo ake wa kuka.


Haka nayi sallama da ‘yan class d’in mu muna masu missing d’in junan mu.



A Washe gari ma akwai wani party da ‘yan class d’in mu suka had’a mana a wani hall amma ba za mu halarta ba saboda mun san a gida baza a ban mu ba.


Post a Comment

0 Comments