MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_Masoya wannan littafin, ina ganin comment d’in ku, ba abin da zan ce muku sai godiya_
_Ina tare daku har kullum_
_Na baku wannan shafin kyauta_🤝🏽
*Rabbana atinah fid duniya, hasanatan, wafil akhirati hasanatan, wa qinna azaban nar*.
*Rabbana alaika tawakkalna, wa ilaika anabna, wa ilaikal masir*
*QUESTION OF THE DAY*
_Wane gida ne Mafi raunin gida da aka ambata a cikin Alkur'ani mai girma?_
55&56
Bayan ya raka Mus’ab gurin mota ne ya koma cikin gida ya wuce side d’in Momi.
Guri ya nema ya zauna yana ba ta labarin tafiyar da suka yi garin Adamawa da irin nasarorin da suka samu, sannan yaci gaba da ba ta labarin course d’in da aka tura su k’asar Uganda.
Murmushi kawai Momi ke yi jin ci gaban da d’an ta yake samu, tana alfahari da hakan.
Kallon shi tayi tace "Alhamdulillah Faruk, kullum ina maka addu’ar Allah ya kare min kai, ya baka nasara a aikin ka, ina rok’on Allah ya ci gaba da tallafa maka a al’amuran ka".
Cikin jin dad’in addu’ar da Momi ta mishi yace "Amin Momi".
Ci gaba tayi da cewa "Bayan nan sai maganar mu ta gaba shine maganar da muka yi kafin tafiyar ka, to yanzu ina son ka tsayar min da Magana, wace yarinya ce kake so, in kuma har yanzu ba da tsayayyar Magana da ita sai ni in za’ba maka, kasan wannan karan ba zan d’aga maka k’afa ba".
Wani irin yalwataccen murushi yayi sannan yace "Momi komai ya zo k’arshe tun da na dawo, ba kowace yarinya ce nake so ba illa Fatima".
Momi cikin rashin fahimta tace "Wace Fatiman kake magana".
"Fatiman gidan Abbu".
Shiru tayi kamar mai nazari sannan tace "Dama ka fad’a mata kana son ta ne ko sai bayan da ka dawo ne ka fad’a mata?".
"Tuntuni na fad’a mata, sai dai tace min in ba ta lokaci tayi tunani".
Cikin farin ciki Momi tace "Masha Allah, gaskiya naji dad’in wannan zancen, Allah ya za’ba mana mafi alkhairi".
"Amin ya Allah Momi" ya amsa mata.
Amma a ran Momi tana juya zancen ne a ranta cewa yarinyar dama yarinyar da yake ta fad’ar yana so ita ce Fatima, amma zancen Dr Sadik da taji Anisa ta ce mata shi yake son ta fa, ko da yake mace da samari aka san ta, amma in haka ne mai zai sa Fatima ta tsaya sauraren Dr Sadik bayan tasan Faruk ne yake son ta? ganin ba za ta samo amsar ba yasa ta bar zancen a ranta.
A ‘bangaren Nana kuwa tun bayan gama wayar ta da Mus’ab da suka yi, tayi saving d’in number yaya Faruk a wayar ta.
Taso a ce sun gaisa da yaya Faruk, miskilancin ta ba zai ba ta damar yin hakan ba, duk da dai tace a gaishe shi, gaskiya tana yabawa da halin yaya Faruk.
Da daddare ta kunna data d’in ta, cikin sa’a tana chat d’in ta ga ya hau online.
Kamar ta share shi, amma wata zuciyar na umartar ta da ta mishi Magana.
Sallama ta tura mishi.
Sai da aka d’auki wasu ‘yan mintuna sannan ya turo mata reply da amsa sallamar.
"ka gane mai magana" abin da ta sake tura mishi kenan.
"No explain your self". Ya sake turo mata.
Ba ta ji dad’in haka ba, tana ganin ya kamata ace yayi saving d’in numban ta ko dan wataran.
"I by name Nana Khadija, a sister to Mus’ab".
Wannan karan bai d’au tsawon lokaci ba ya dawo mata da reply.
"Oh Nana, ya karatu? ya su Hajiya".
" Lfy lau, ya su Momi?
"Lfy lau, ki gaida Hajiya".
"Za taji"
"Gud night Khadija"
"Ok gud night yaya Faruk".
Suna gama wannan chat d’in yayi offline.
Ni kuwa tun san da yaya Faruk da abokin shi suka tafi, na dawo cikin falo d’in na nuna mata kud’in da abokin yaya Faruk ya ba ni, da kuma tsarabar da yaya Faruk ya basu, sannan na bud’e tawa tsarabar da ya min.
Gaskiya ko ni nasan yaya Faruk ba k’aramin kasha kud’i yayi ba, duba kalar kayayyakin da ya kawo min, ko ni a lokacin jiki na yayi sanyi da irin kasha kud’in da ya min, ko Ummu sai da ta jinjina tsarabar tana cewa yayi yawa, shi da ya tafi course zai tsaya kashe min wannan kud’in.
A lokaci d’aya kuma sai addu’a take yi ma yaya Faruk akan Allah ya bashi ladan zumuncin da yake yi da kyautata musu.
Ni dai ba ni da bakin Magana sai ma tattara kayan da nayi na tafi d’aki ina tunanin game d’in da za mu buga da yaya Faruk idan yazo gobe.
Lallai akwai badak’ala tsakani na dashi, koma mai zai je ya dawo, gwara ayi ta tak’are don hausawa na cewa "shure- shure ba ya hana mutuwa, kuma duk nisan jifa k’asa zai sakko".
Da wannan na samu k’arfin gwiwar ci gaba da harkoki na, ba tare da na bar fargabar da ke raina tayi tasiri a kaina ba.
Washe gari kamar yadda yaya Faruk yace zai dawo, hakan kuwa aka yi.
Ina zaune ina assignment naji rurin waya ta, ganin yaya Faruk ne na ji gaba na ya fad’i yau nake so na samar wa kaina mafita, amma na rasa me yasa nake jin kamar ban da wannan power d’in.
D’auka na yi muka gaisa.
"Ki same ni a gurin shak’atawa"
yana gama fad’ar haka ya katse wayar.
Tashi nayi na yafa veil a jiki na kasancewar rigar da nasa doguwar riga ne.
Yau cikin k’ananun kaya yayi, blue d’in T-shirt ne da bak’in jeans.
Sallama na mishi na samu guri na zauna.
Irin wannan kallon ya min da yake sa ni tsarguwa ya min, a lokaci d’aya yana sakar min sihirtaccen kallo.
Ganin kallon ba na k’are bane yasa na katse shi da cewa "yaya Faruk sannu da zuwa".
"yawwa Teemah".
Ci gaba yayi da cewa "Fatima kamar yadda kika ce in baki lokaci ki yi tunani, to na baki isasshhen lokacin da nasan ya isa kin zartar da hukunci game dani, ina kuma so ki fad’a min yadda kike ji na a zuciyar ki".
Yau ga dama na samu da zan fad’a ma yaya Faruk sirrin zuciya ta, sai dai abin takaici, zuciya ta na gargad’i na da kar in fad’a mai, gwara in bari da kanshi ya fahimci hakan.
"Amma anya in nayi haka na kyauta kuwa?".
Gaskiya ban kyauta ba, amma ina ganin wannan shine damar da zan samu in yi amfani da ita ba tare da ran kowa ya ‘baci ba.
Shawarar da na yanke shine in mishi tattausan lafazi, in yaso daga baya sai in fito in fad’a mishi.
"Yaya Faruk duk wanda yace yana son ka ya gama maka komai, ba abin da zan baka da zan saka maka da wannan Kalmar, kai d’an uwa na ne, ba yadda za ayi in k’i ka, ba abin da zance sai dai in ce Allah ya za’ba mana mafi alkhairi"
Hak’ik’a yaji dad’in wannan lafazin nawa, sai dai yaso ace na fito na fad’a mai cewa ina son shi, amma ya na ganin ko kunya ce ta hana ni fad’ar hakan, yasan da sannu zan fad’a mishi wannan Kalmar.
"Na gode Teemah, insha Allah zan ci gaba da son ki, fatana ke ma ki so ni kamar yadda nake son ki" yaya Faruk ya fad’a min cike da jin dad’i.
"Insha Allah" na bashi amsa a tak’aice.
Da haka yaci gaba da furtar min kalamen soyayya zafafa.
Bai d’au wani tsawon lokaci ba ya min sallama ya tafi da niyyar in an kwana biyu zai dawo.
Tun daga wannan lokacin yaya Faruk yaci gaba da nuna min so, sai dai ba na bashi k’ofar da kowa zai fahimci hakan.
Bayan dawowar yaya Faruk daga gidan mu, ya samu Momi ya fad’a mata yadda suka yi dani, Momi ta ji dad’in haka, saboda a gaskiya tamu tazo d’aya da ita, tana d’auka ta kamar Anisa.
Daddy da ya dawo daga aiki Momi ke sanar dashi daddad’ar labarin game da yaya Faruk da ni.
Daddy yayi farin cikin jin wannan labarin, don haka Daddy yace zai samu Abbu suyi maganar dashi.
Da daddare yaya Faruk ne a falon Daddy, su na tattaunawa game da matsalolin da ake fuskanta a k’asar mu, da irin corruption da yayi yawa, fatan dai Allah ya daidaita komai.
Daddy ne ya canza hirar da cewa "Faruk, na ji kyakkyawan labari a gurin Momin ku, ta fad’a min Fatima ita ce yarinyar da kake so, gaskiya naji dad’in hakan, kaga ga kuma Anisa da Khalil, gaskiya wannan had’in yayi, sai dai muce Allah ya tabbatar da alkhairi, Insha Allah zan samu Ibrahim da maganar".
Lallai biri yayi kama da mutum, ya lura da kusancin da ke tsakanin Anisa da Khalil, yasan hakan za ta faru, ya ji dad’in haka saboda yasan Khalil kamilin mutum ne da ba shi da matsala, yayi murna da Anisa ta za’be shi a matsayin mijin aure.
"Daddy na gode, duk yadda kuka yi da Abbu d’in shi kenan, in na dawo sai a tsayar da Magana ko Daddy, plsss amma Daddy ba na so ya d’au time".
Dariya Dadi yayi yace "lallai Faruk kace da gaske kake son ‘yar tawa, kai da ake ta fama da kai akan maganar aure, kana kaucewa, yanzu da kan ka ke rok’on kar a ja time, to zan fad’a ma Abbun ka abin da kace, na fi so ne a had’a da na Anisa da Khalil, kaga service yake yi, na fi so sai mun samar mishi aiki, in hakan bai yiwu ba sai a fara naku".
Murmushi yaya Faruk yayi yace "Allah ya kaimu Daddy".
"Amin Faruk".
Haka suka ci gaba da hirar su, kana yaya Faruk ya ma Daddy sallama ya tafi side d’in shi.
Yau Daddy ne da Abbu a office d’in su dake Wagini motors suna tattaunawa game da bunk’asar da kamfanin yake samun ci gaba, da kuma irin nasarar da suke samu a harkar motocin su, sannan su ka gangaro yadda za su assasa kamfanin ya fi haka.
Daddy ne ya canza akalar hirar da cewa "Ashe d’anka duk wannan delay d’in da yake yi game da maganar aure, Fatima yake so".
"wace Fatiman?" Abbu ya tambaya.
"Fatima k’anwar shi".
Wani irin farin ciki ne ya kama Abbu, shi gani yake yi ma yafi kowa murnar da jin wannan labarin.
Yana son halin Faruk, yana d’aukar shi kamar d’an da ya haifa da cikin saboda yadda yake masa ladabi da biyayya.
Tabbas duk wanda ya samu suruki kamar Faruk yayi dace, don a wannan zamanin suna da wuyar samu.
Cike da farin ciki ya ce "gaskiya yaya naji dad’in wannan maganar, kuma ko b aka fad’a min ba, kai mai zartar da hukunci ne akan su, saboda haka duk yadda kayi daidai ne".
Dadi yaji dad’i yanda ya bar mishi wuk’a da nama, don haka yace mishi in yaya Faruk ya dawo daga Abuja za a tsayar da Magana.
Abbu na dawowa ya sanar da Ummu halin da ake ciki, ai tsakanin Ummu da Abbu, cikin su an rasa wanda yafi murnar da wannan zancen.
Ummu cewa take yi "Fatima ta samu miji na gari, wanda na dad’e ina mata addu’ar samun Kaman shi, Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kai mu lokacin".
Abbu kuwa amsawa yake yi da "Amin Aisha".
Kallon Ummu yayi yace "wani hanzari ba gudu ba Aisha, wannan Dr fa da yake zuwa gurin ta, har ta turo shi ya gaishe ni, shi kuma a me ta ajiye shi tun da tasan Faruk ke son ta".
Ummu ce tace "Alhaji a kira ta a a ji ta bakin ta, ya kamata ta dakatar da wannan Dr d’in saboda yanzu maganar aure ce za ta shiga tsakanin ta da Faruk, in ban da ma wautar Auta, kana da wanda kuke soyayya sai kuma ka ci gaba da soyayya da wani.
Dariya Abbu yayi yace "Kin san ‘yan matan zamani, su suna ganin tsayawa da samari fiye da d’aya shine cinyewa, yanzu dai tun da shi wannan daman ba wai ya turo iyayen shi ba ne, sai a wa Fatima Magana ta bashi hak’uri don ban a son tara samari".
Abbu ne ya umarci Ummu da ta kira ni.
Samu na tayi ina kallon wani indian film mai suna "Kabhi alvidana kehna" Gaskiya film d’in akwai tausayi ga soyayya.
Ummu ce ta katse min kallon da cewa "Auta ana nan ana kallo ne".
Cikin shagwa’ba na ce "To ya zanyi Ummu, yaya Khalil ba ya nan bare muyi hira, film d’in ne zai d’auke min kewa, ina so ran weekend in tambayi Abbu zan je gidan su Anisa, daga nan sai mu je gidan su Anty Jidda da Aisha".
"Da ko kin yi zumunci".
Ummu ce taci gaba da cewa "Ki je Abbun ku na kiran ki".
"To Ummu" na amsa mata.
Bayan Ummu na bi muka shiga falon Abbu.
Kusa da Abbu naje na zauna a k’asar carpet.
"Sannu da hutawa Abbu, Ummu tace kana kira na".
"Yawwa Autan Ummu, ni nace Ummun ki ta kira min ke, saboda ina so muyi wata magana da ke akan wani labari da muka ji mai dad’i".
Shiru nayi ina sauraron jin Abbu yace labari mai dad’i za muyi Magana, wannan wane labari ne?
Abbu ne ya katse min tunanin da cewa "Fatima na ji dad’i dad’in labarin da na samu cewa Faruk shi yake son ki, hakan yasa nake alfahari da wannan familin namu, nasan Hajiyan mu in taji labarin nan za ta fi kowa da murnar haka, saboda haka ba abin da za mu ce sai dai Allah ya tabbatar mana da alkhairi, sai Magana ta gaba, game da wannan Dr da yake zuwa wajen ki, ina so ki fad’a mishi yanzu kina da wanda za ki aura, kin ga dam aba turo manyan shi yayi ba, in ban da wautar ki Auta, kin san kina da wanda kike so kuma ki ke tsayawa da wani, ban a son tara samari, yanzu in Faruk ya dawo za a tsayar da Magana".
Wani irin takaici ne ya tokare ni da naji na kasa bud’ar baki na in yi Magana, gashi ina so in fad’a ma Abbu cewa ni Dr Sadik ne za’bi na, sai dai nasan ban da damar fad’an hakan, baa bin da yafi ‘bata min rai sai jin cewa wai in yaya Faruk ya dawo za a tsayar da Magana, akan me yasa yaya Faruk zai sanar da su Abbu bai nemi shawara ta ba.
Abin da yasa ban fad’a mishi k’uduri na ba saboda ina son shawo kan matsalar ne a hankali, ashe ban san hakan zai jawo min matsala ba.
Abbu ne ya kalli Ummu yace "Aisha ko akwai abin da zaki ce".
"Ba abin da zance Alhaji, sai dai in ce Allah ya k’ara daidaita su, ke kuma Fatima ya kamata ki kula, ba yadda za ayi ki tauna taura biyu a lokaci guda, ki ba ma shi Dr Sadik d’in hak’uri, kar yaga kin yaudare shi, ki fito ki fad’a masa da wuri, ba ma kyau nema akan nema".
Duk wannan maganar da Ummu ke yi kamar tana k’ara sa zuciya ta na zafi, da ina da hali da na tashi na bar gurin ba tare da sun sallame ni ba, amma nasan hakan ba zai yiwu ba.
Abbu ne ya kalle ni yace "Fatima hakan ya miki ko, nasan in Faruk ya dawo lokacin kun yi exam, kin ga saura semester d’aya, sai a tsayar da bikin bayan kammala karatun ku".
Shiru nayi ban ce komai ba, don lokaci wani irin zugi nake ji zuciya ta na k’ara yi.
Ummu ce tayi dariya tace "Alhaji hakan ya mata tun da kaga tayi shiru, kasan yanzu auta ta girma".
Dariya dukkan su suka yi kana Abbu yace "za ki iya tafiya Fatima, Allah ya miki albarka".
"Amin Abbu" na amsa a tak’aice.
Tun da na tashi na koma d’aki na, ko falo ban zauna naci gaba da kallon film d’in da nake yi ba, a lokacin ji nake yi komai ya fitar min a rai.
Ina shiga d’aki na fad’a kan gado ina zubar da hawaye mai d’aci.
Hawaye ne yaci gaba da zuba a ido na, ban damu da in goge ba saboda nasan ko na goge wasu ne za su ci gaba da zuba.
Me yasa sai yanzu da nake ganin na kusa samun nasara akan wannan lamarin, sai gashi wata badak’alar ta shigo, yaya Faruk ya wargaza min target d’ina, ba abin da yafi d’aga min hankali sai jin cewa in yaya ya koma aiki ya dawo za a tsayar da maganar bikin mu, kenan hakan na nufin rabuwar mu da Dr Sadik ya zo kenan.
Zuciya ta za ta iya hak’ura da Dr Sadik kuwa? "Ba za ta iya ba domin nayi nisa da son shi" zuciyata ta ba ni amsar hakan.
Ya kamata in bi komai a sannu dan ganin na samu abin da nake so ba tare da ran su Abbu ya ‘baci ba.
Fitowa in fad’a musu Dr Sadik nake so na nufin fuskantar hukunci daga kowane ‘bangare.
"Allah ka kawo min mafita cikin sauk’i, ba ni da inda za ni na nemi shawara don nasan ba mai goyon baya na, Allah kai nake rok’o ka kawo min komai cikin sauk’i".
Da wannan addu’ar na samu na tashi naje nayi sallar issha’i, ranar ko abincin dare ban tsaya na ci wani abun kirki ba.
Ko shi a yanzu ya rasa inda na sa gaba, duk hirar da zai min ban cika tsayawa ina bashi cikakkiyar amsar da ta dace ba, sai dai in bishi da eh ko a’ah, in ya tambaye ni me ke damu na sai dai in ce mai ba komai, ga abin da ke damuna a raina shine yadda na kasa fitowa in fad’a mishi ina da wanda nake so ko zai k’yale ni in huta, amma abin haushin na kasa.
Yaya Faruk bai d’auki hakan da wata manufa ba, sai ma uzuri da ya min akan cewa yanayin d’an adam yana tsintar kanshi da rashin walwala.
Wannan time d’in yaya Faruk ya d’an dad’e a Kaduna, kusan 2 weeks yayi sannan ya koma Abuja.
Duk wannan abin da ya faru bai sa naji na rage son Dr Sadik ba, sai ma wani k’ara son shi da nake ji a zuciya ta, matsala ta dashi shine yadda yake kawo min uzurin bai samun zama ko lokaci, kamar akan shi aka fara aikin likita, ni kaina yanzu na rage zuwa asibiti gurin shi in muna free ba mu da lectures, a wani lokaci sweet word d’in shi ke wanke duk wani laifi da ya min.
Ko ya bani wani gift yanzu ba na nuna wa kasancewar na ga kowa a bayan yaya Faruk yake.
Na kasa fitowa in ce mai ya dena zuwa gidan mu in na tuno da danbarwar da muka yi dashi akan haka, dubara ce tazo min nace mun kusa exams, yanzu ban da wani time, mu dinga had’uwa shi a school kawai sai bayan exams.
Wannan lokacin bai min musu ba sai ma fatan alkhairi da ya min akan jarabawar da za mu fara.
Da haka na samu Sadik ya daina zuwa gidan mu, sai dai mu had’u a school, ko yazo department d’in mu, ko ni in shiga asibiti in bai da aiki.
Komawar yaya Faruk da kusan 3 weeks ne, Maryam ta haifo namiji.
Tun da aka yi haihuwar Nana ta tare a gidan, ko School ne sai dai ta tafi ta nan ta dawo.
Yaya Faruk ma yana shigowa ya d’auki yaro ayi hira dashi sannan ya tafi.
Ko wani sa’in in ya dawo daga aiki sai ya kira Nana ta kawo mishi yaron ya d’auke shi kafin ya tafi block d’in shi.
A wannan haihuwar Nana ta fara sakewa sosai da yaya Faruk duk da kasancewar su Miskilai, amma yanzu ba laifi suna hira.
Ran suna aka rad’a ma yaron sunan Dadin su Mus’ab wato Sa’id amma suna kiran shi da Asim.
Yaya Faruk siyayya yayi ta bajinta, kayan baby ya siyo masu yawa, sannan ya had’o da na mai jegon.
Mus’ab kuwa rasa bakin godiya yayi, sai jinjina halin Faruk yake yi na kyauta kamar bai san ciwon kud’i ba in ya tashi kyauta, fatan shi Allah ya k’ara dank’on amincin su da yaya Faruk, saboda yaya Faruk aboki ne na kwarai.
Yaya Khalil yana zuwa ya d’an yi kwanaki ya koma, ina kewar shi saboda shine abokin hira na.
Soyayyar su suke gudanarwa shi da Anisa cikin kwanciyar hankali ba sa tare da kowace matsala, su sun sami goyon baya ko ta ina, ni kuwa yanzu ba ni da damar yin haka.
Abin da ya bani mamaki shine yadda yaya Khalil bai min zancen yaya Faruk, hakan na nufin bai ji zancen ba ne, nasan yaya Khalil suna gaisawa da Sadik, amma in yaji kuma yaya Faruk yana so na, bayan shi zai bi, dama tuntuni yana bugar ciki na yaji ko akwai wata alak’a tsakani na da yaya Faruk in ace mai ba komai, ina ga yanzu in yaji zancen.
Dole na ja baki na nayi shiru ban mishi maganar ba.
Anisa ma ba ta min maganar ba, nasan cewa may be ba ta ji me ke wakana ba ne, nasan sai ta fi kowa zak’ewa akan maganar, in ba ta fi kowa ba, to ina jin ita ce a sawun gaba.
"Kin manta da Hajiyan Wagini ne?’ wata zuciyar tace min.
Nayi tuya na manta da albasa, Hajiyan Wagini ita ce ja gaba a ganin wannan auran ya gudana.
Kenan ba ni da tsimi ba ni da dubara, sai yadda Allah ya zartar da hukuncin shi
a kaina.
Ko dai in fad’a ma Halima halin da nake ciki ne? ko kuma Aisha, duk wanda na fad’a ma wa a cikin su nasan za su bani shawara da kuma samar min mafita.
A ‘yan class d’in mu, akwai k’awaye da nayi basu wuce 3 ba, Akwai Fauziyya, Salma sai Halima, duk a cikin su mun fi shak’uwa da Halima, shi yasa na yanke shawarar fad’a mata halin da nake ciki tun da itama in tana cikin matsala tana neman shawara ta.
Da wannan shawarar nayi amfani bayan mun fito lectures muka samu guri muka zauna.
Halima ce ta kalle ni cikin kulawa tace "Fatima ya aka yi ne, nag a kamar ki na cikin damuwa".
Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke sannan nace "Ke dai bari Halima, ina cikin damuwa".
"Me yake damun ki" Halima ta tambaye ni.
Nan na zayyane mata duk abin da yake faruwa, har kawo yanzu da ake maganar in yaya Faruk ya dawo za ayi fixing d’in date d’in bikin mu.
"Gakiya kina cikin rikici kuwa Fatima, ni dai a ‘bangare na ina goyon bayan ki, gwara ki auri wanda kike so, da a zo kuma ayi aure abu yak’i dad’i, mutane bas a gane halin da mutum yake ciki in ya fad’a tarkon soyayya, sai a dinga ganin laifin ka akan cewa kai ka d’aura ma kan ka, bayan ita soyayyar ba ta shawara da kai a lokacin da za ta shiga, ni dai shawarar da zan baki shine ki fito ki fad’a ma shi yaya Faruk d’in abin da yake ran ki, sannan ki samu su Abbu ki musu bayani, nasan za su fahimce ki, kuma shima yaya Faruk d’in in har son gaske yake miki ai zai so ki samu farin cikin ki, shi kuma ya fawwala ma Allah lamuran sa, sai ki ga Allah ya masa za’bi nagari".
Sai a yau na samu wacce ta goyi baya na akan wannan maganar, hakan yasa na ji dad’in fad’a ma Halima da nayi, ko ba komai yanzu na samu mai bani shawara da share min hawaye na.
Cikin murna da shawarar ta nace "Na gode Halima da wannan shawarar da kika bani, insha Allahu zan yi amfani da ita".
"Ba komai Fatima, amfanin zaman taren kenan da kuma aminci".
Ci gaba nayi da cewa "Kin san me? ban san ta yadda za ayi in je in fad’a ma su Abbu wai Sadik nake so ba, nasan wannan maganar da zan fad’a mishi zai iya sa wa yayi fushi dani shi da Ummu, za kuma su iya d’aukar mummnar mataki a kaina".
"Ki bi komai a sannu ne Fatima, a hankali sai ki fad’a musu, nasan da yardar Allah za su yarda da za’bin ki".
Haka muka zauna a gurin Halima na ci gaba da ba ni shawarwari.
Sai da muka ga time d’in komawa class yayi sannan muka koma class.
Lokaci na ta tafiya, sai gashi har mun fara rubuta exam.
Kamar yadda muke jarabawar zango na d’aya a ND 2, sai ya zamana mun fi shan wuya akan sauran jarabawar.
Fatan dai Allah ya taimake mu ya kuma ba mu sa’a a jarabawar mu.
Bayan gama jarabawar mu naso muje Wagini mu d’an yi kwanaki tun da ba wani hutu mai yawa aka bamu ba, amma da na tuno da yanzu Hajiyan Wagini tasan abin da ke tsakani na da yaya Faruk, nasan idan na je matsa min za tayi akan maganar, shi yasa na hak’ura da zuwan.
Hutun zangon da aka bamu ba wani mai yawa bane, shi yasa nayi tunanin zuwa gidan su Anty Jidda in yi kwana biyu a can.
Yanzu ban cika son zuwa gidan su Anisa in kwana ba, saboda yanzu kulawar da Momi take ba ni tafi ta da, duk dama can tamu tazo d’aya, yanzu sai nake ji duk gidan ya fita kaina.
Duk zuwan da nake yi Momi ba ta kawo min zancen yaya Faruk, ko tayi hakan ne dan kar in dinga jin kunyar ta ina jin.
Ko a gidan yaya Aminu da na je yin kwana biyun, ban wani ji dad’in gidan ba saboda yadda yaya Aminu shi da Anty Jiddah suke zaunar dani sun aba ni shawarwari akan yaya Faruk, suna kuma k’ara jaddada min yadda yaya Faruk yake so na, bas u san duk wannan tunatarwar da suke min ba shi zai sa in canza k’udiri na, sai dai in ji su kawai, in da nake samun sauk’i ka ga dariya ta a gidan shine in su Humaira da Nabil muka had’u ina jan su da wasa, to nan za a ji magana ta.
A daddafe nayi kwana biyu na koma gida.
Mun koma zangon k’arshe a karatun mu, sai ya zamana duk wani hope namu yana kan wannan semester, tun da a shine muke sa ran final a karatun mu, don haka muka sake ba da himma dan ganin mun samu abun da muke so.
Ina kwance da yamma a gado na lumshe ido na kamar mai yin bacci, a zahiri kuwa tanini ne ya dabaibayi ganin har yau ban samo wa kaina mafita ba, gashi kuma banyi amfani da shawarar da Halima ta bani ba, da yanzu komai ya zo k’arshe.
K’arar sautin da ke tashi ne a waya ta na musamman da nasa a wayar yasa na gane Dr Sadik ne yake kira na.
D’auka nayi cikin shagwa’ba nace "Hello, My Prince Sadik".
"My Princess Zahra" shi ma ya fad’a.
Ci gaba yayi da cewa "gani a wajen gidan ku, ki fito ki same ni".
Duk da na ji dad’in zuwan shi sai da na ji fargaba, yanzu ban cika son yana zuwa ba tun da aka san me ke tsakani na da yaya Faruk, gashi Ummu da Abbu sun ja min kunne akan in dakatar dashi da zuwa, in fito in fad’a mishi yanzu ina da wanda zan aura.
Dr Sadik ne ya katse ni da cewa "Ki na ji na kuwa Zahra".
"Ina jin ka Dr, gani nan zuwa".
Jiki na duk ba laka na sa Hijab d’ina na fito, samun Ummu nayi a falo tana zaune.
Ganin Ummu a falo yasa na k’ara jin wata fargaba, duk da haka sai ban nuna hakan ba.
Ummu ce ta kalle ni da alamar tambaya tace "Fatima ina za ki na gan ki da Hijab a jikin ki".
Rasa abin da zance mata mayi.
"Ke fa nake tambaya Fatima" ta sake jefo min wata tambayar.
Cikin kame-kame nace "Dr ne yazo, shine zan je".
Tuni fuskar Ummu ta canza zuwa ‘bacin rai tace "Dama Fatima ba ki fad’a mishi yanzu ki na da wanda za ki aura ba, kin fi son ki dinga ‘ba ta mishi lokacin shi, to ba na son irin haka, in kin je ki fad’a mishi gaskiyar magana ki na ji na ko?".
"Zan fad’a mai Ummu" na fad’a da alamar rawar murya.
"Yawwa Auta ta, je ki tun da yana jiran ki".
Fita nayi amma duk ilahirin jiki na duk a mace yake, ganin tun a yanzu yadda Ummu ta fara min fad’a, ba abin da ke k’ara sakar min gwiwa in na ji ana maganar wai ina da wanda zan aura.
Da haka na k’arasa na bud’e k’ofa na fita, na nufi inda yayi parking a waje.
Bud’e min d’ayar k’ofar yayi alamar in shiga ta cikin motar shi.
Ba na so ya fahimci halin da nake ciki yasa na aro murmushi na yafa a fuskata.
Kallo na yayi yana sakin murmushi, a lokaci d’aya muna musanyar kallo ni dashi.
"Zahra ta, sai ki ganni unexpected ko".
"Na ji dad’i da ka min zuwan ba zatan, dan nayi missing d’in ka".
Murmushi yayi yaci gaba da cewa "Zahra ina ganin lokaci yayi da zan turo su Daddy na gurin su Abbu ko, ya kamat by now a ce akwai wata magana mai k’arfi a tsakanin mu, are my right" ya tsura min ido yana jiran amsa ta.
In akwai abin da nake jira, bai wuce a ce Sadik yace zai turo iyayen shi ba, sai gashi yau ya fad’a min amma ba ni da damar amincewa da hakan, tun da nasan abin da yake tafiya yanzu game da magana ta da yaya Faruk.
"Are you with me Zahra" Sadik ya fad’a ganin yadda na yi shiru.
Ajiyar zuciya na yi kana nace "gaskiya wannan shawara ce ka kawo, amma ina so ka d’an ba ni time, kaga ana so ne a had’a mu da yaya Khalil kuma yanzu service, idan ya dawo hutu sai in mishi magana a san yadda za ayi, sai in sanar dakai, ina hakan zai fi ko".
"Hakan ma yayi, bari in k’arasa gida in huta".
"Gaskiya kuna k’ok’ari, aikin likita ba hutu".
Dariya yayi yace "Haka za mu daure mu ci gaba da yi, Allah ne zai ba mu ladan".
"Allah ya taimaka"
"Amin".
Fito wa daga cikin motar nayi na jingina da window d’in motar.
"Ya aka yi ne Zahra".
"Ba komai Dr".
Cikin tsokana yace "Ko kar in tafi ne?".
"In da akwai hali sai in ce eh, amma ina so Sadik d’ina ya samu hutu, have a nice day".
"Thanks Zahra".
Sallama muka yi na bar jikin motar na nufi cikin gida, shi kuma Dr ya ja motar shi ya tafi.
A daidai wannan lokacin kuma yaya Faruk ne ya shigo da motar shi cikin layin.
Ganin ni ce na bar jikin motar yasa yayi tunanin waye a cikin motar na ke tare dashi, kau da wannan tunanin yayi ya k’araso gate d’in gidan mu.
Horn yayi mai gadi yazo ya bud’e mai ya shiga.
Sallama yayi ya shigo cikin falo d’in.
Saurin d’ago kaina nayi don jin muryar mai yin sallama da ban tsammaci zuwan shi a wannan lokacin.
Amsa mishi sallamar nayi ina mai sakin murmushin dole.
Zuwa yayi ya zauna a kusa dani yana murmushi yace "Teemah, I miss you a lot".
Maimakon in ba shi amsar da yake buk’ata, sai ma cewa nayi "Sannu da zuwa yaya Faruk".
"Yawwa Teemah, ina Ummu take?".
"Ta na ‘dakin ta".
"Ok".
Tashi nayi na d’akko mishi Table water da glass cup nazo na ajiye mai.
"Teemah yaushe za ki k’ara min Samosa da Spring roll".
A raina nace "Sai dai in maka dan darajar kai yaya na ne, kuma yanzu muna shiri, amma ba wai dan kana duba matsayin kai masoyi na ba ne".
"Ran da kake buk’ata sai in maka" na bashi amsa a tak’aice.
"Ok ran da nake so zan miki magana".
"Teemah wa na gani yanzu a mota kin dawo daga wurin shi" ya fad’a da zafin rai kamar ba shine ya gama min magana da sanyin murya.
Tsoro ne ya kama ni wanda in ka lura da ni sosai za ka iya gane hakan, amma sai na daure na ce "Oh wai Dr Sadik kake magana, a clinic d’in makarantar mu yake aiki, wani handout d’ina na manta dashi a office d’in shi, shine ya kawo min".
"Ya aka yi yasan gidan ku?" ya sake jefo min wata tambayar.
Nasan in ba kare kaina nayi ba, zan iya ja ma kaina, don haka na shirya k’aryar da zanyi nace "Ai a bayan layin mu yake, rannan ne ya ganni na fito daga gidan mu, shine ya tsaya muka gaisa yake tambaya na dama a nan layin nake, na ce mishi nan ne gidan mu, yau da na manta hand out d’ina shine ya kawo min".
"Ya kamata ki kula, ina da kishi, ba na so wata mu’amala ta ci gaba da had’a ku in ba ta rashin lafiya ba da ya kama dole ki je in ba ki da lafiya, ki fad’a mishi ya daina zuwa gidan nan, dan ban ga amfanin haka ba".
Wani irin haushin yaya Faruk ne ya kama ni a lokacin, ya wani tasa ni ya na ba ni command kamar wani uba na, shi a ganin shi yanzu yana da matsayi biyu a gare ni da na matsayin yaya a gare ni da kuma wanda ake tunanin shi zan aura.
Ashe kuwa za muyi fito na fito dashi dan ban ga yadda zai ce in yanke huld’a ta ba da Dr.
Ko da yake bai san me ke tsakanin mu dashi ba, shi yasa yace haka, amma duk da haka saurin nuna ‘bacin rai ba nawa bane, da sannu zai fahimci Dr Sadik shine yake mulkar birnin zuciya ta.
Don haka cikin ladabi nace "Zan kiyaye yaya Faruk".
Murmushin jin dad’i ya saki sannan yace "that is my Teemah".
Ci gaba muka yi da hira amma ni duk zaman ya ishe ni, in na tuno yadda iyayen mu ke murna da wannan had’in sai in dinga jin raina yana ‘baci.
Mik’ewa yayi yace "Bari in je gun Ummu mu gaisa".
"Sai anjima yaya Faruk, nima d’aki zan shiga in yi karatu, akwai wani assignment da zan k’arasa".
"Sai mun yi waya kenan".
"Ok" na fad’a a tak’aice na tafi d’aki na.
Shiga gurin Ummu yayi suka gaisa kana ya fito ya tafi.
Yau kusan sati biyu kenan da zuwan yaya Faruk Kaduna, kasancewar ya fad’a min ya nemi hutu saboda yana so a gama komai akan maganar bikin mu dashi.
Gani nake wannan matsalar shi, koma hutun wata nawa zai d’auka wannan matsalar.
Yanzu had’uwar yaya Faruk da Dr Sadik kusan sau uku kenan, ban da wnada ya min gargad’i akan in yanke mu’amala dashi, tun yana tambaya ta ina mishi k’arya, har ta kai ya fara nuna min ‘bacin ran shi sosai.
Yau ma hakan ta kasance, muna tare da Sadik a k’ofar gidan mu kasancewar yanzu ba ya shigowa harabar cikin gidan mu, sai ga motar yaya Faruk ta shigo layin.
Wani irin tsoro ne ya kama ni da hakan ya nuna a fuska ta, nasan yau mai raba ni da yaya Faruk sai Allah.
Cikin kulawa yace "Zahra me ya faru ne, naga yanayin ki ya canza".
"Motar yaya Faruk ce na gani, kuma ya hana ni tsayawa zance".
Wani irin kallo ya min na tuhuma sannan yace "Akan wani dalili zai hana ki".
"Nima ban san dalilin shi nayin haka ba".
"In ba rami me ya kawo zancen rami, haka kawai ba zai ha na ki tsayawa da wani ba, dole yana da dalilin shi nayi hakan, ya kamata ki gano da dalilin yin haka, in kuma kin san dalilin shi nayin haka sai ki fad’a min".
Yanayin da ya min magana yasa nima na ji raina ya ‘baci dama ga kuma tsoron yaya Faruk da ya cika min rai, don haka nace "Ban gane me kake nufi da wannan maganganun n aka ba Sadik".
"Za ki gane ne in ki ka gano dalilin".
Ganin yadda Sadik yake fad’a min duk maganar da ya ga dama yasa nima na fita cikin motar ba tare da mun yi sallama ba, shi ma Sadik a lokacin ya ja motar shi ya tafi.
A lokacin kuma yaya Faruk ya ajiye motar shi a bakin gate ba tare da ya shigo da motar ciki ba.
Sauri nake in shiga cikin parlour saboda ba na so yaya Faruk ya tarad dani, dan nasan gamon mu dashi ba dad’i.
Takun tafiyar shi da na ji yasa na k’ara saurin tafiya ta, don ba na so ya tsare ni da tuhumar shi.
"Teemah!
Ya kira suna na da wata irin murya da ta razanar da ni.
Cak na tsaya da tafiyar da nake yi.
_Ni kaina 'yar mutan Paki zan so jin yadda za ta kaya tsakanin Teemah da Faruk_
*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_Wannan Shafin naku ne_
*Naga comment d’in ku a group daban-daban, hakan yasa naji dad’in yadda na ga kowa yana fad’ar ra’ayin shi game da fans d’in novel d’in*.
*Election d’in fans da na sa akan novel d’in ina ganin yadda mutane suke za’ban fans d’in su, sai dai kamar na ga akwai partiality 😀 a wannan election d’in*
*A next page zan fad’i wanda yafi yawan mabiya*
*Na gode da yadda kuke bin wannan novel d’in sannu a hankali*🤝🏽
_GAISUWA GARE KI_
*Barrister Teemah*
*Ina mik'a gaisuwa ta gare ki da irin k’ok’arin da kika yi na ba da amsar question of the day, Allah ya k’ara ilimi mai amfani*
*Haka amsar take, mafi raunin gida da da aka ambata a cikin alkur’ani shine Gidan gizo-gizo*
*TUNATARWA*:
_Rayuwar Duniya tana k’unshe da abubuwa ak’alla tara_:
_Farin ciki_
_Bak’in ciki_
_Had'uwa_
_Rabuwa_
_Samu_
_Rashi_
_Lafiya_
_Ciwo_
_Mutuwa_
_Annabi Muhammad (s.a.w) ya hore mu da muyi hak’uri da duk wanda muka yi karo dashi, domin ba zai dauwama ba, zai wuce_
_Allah ka k’ara mana hak’uri_
57&58
Cikin takun k’asaita ya k’araso in da na tsaya, gaba na sai fad’uwa yake tun san da ya kira suna na.
Wani irin kallo yake min da yake nuna yana cikin fushi.
"Fatima miye had’in ki da wannan Dr da nake yawan ganin ki dashi?".
"A clinic d’in makarantar mu yake aiki, shine yake biyo wa muna gaisawa".
Wani banzan kallo ya k’ara watso min kana yace "Amma tun yaushe na ce miki ki rabu dashi, miye amfanin zuwa gurin ki da yake yi dan kawai yana duba lafiyar ki, in har ba yana da manufar shi ta yin haka ba, Fatima let me warn you for the last time, duk ran da na sake ganin ki dashi, two of you will face the consequences, kar ki ga dan ina son ki zai hana in kin shiga gona ta in hukunta ki, ya kamata ki gane ni mutum ne mai kishin abin da nake so, bare wacce nake sa ran zan aura, ki kiyaye".
Yana gama fad’ar haka ya juya ya fita ba tare da ya shiga cikin gidan ba.
Wata irin ajiyar zuciya mai k’arfi na saki don gaba d’aya a tsorace nake dashi, yau yaya Faruk na ga alamar idan da nayi wasa zai iya fasa min jiki ya bar ni da jinya.
Haka na ja jiki na koma d’aki na ina addu’ar Allah ya kawo k’arshen wannan lamarin.
Tun san da iyayen mu suka san da zancen yaya Faruk na rasa sukuni, gashi matsalar wadda nake tunanin za mu raba matsalar tawa dasu b azan iya fuskantar su ba.
Rok’o na Allah ya d’aura ni akan su, ina ganin ko wani challenges zan iya fuskanta in dai akan Dr ne, shi nake so, ba kuma dan yafi yaya Faruk ba, hasalima yaya Faruk yafi shi komai.
"Me yasa so ya zo min ta wannan sigar"
Gashi na samu wanda nake so amma ba ni da kwanciyar hankali saboda wani Katanga da ta shiga tsakanin mu.
Ga wani k’arin damuwar shine yadda Sadik yake tuhuma ta da wani zargin shi na daban, dan ma bai san halin da nake ciki ba game dashi na yadda ake so a raba mu, gashi yanzu yaya Faruk ya min gargad’i na k’arshe akan shi, na san kuwa zai iya d’aukar matakin da ya zo mai, ya kamata in kiyaye taku na don kar in fad’a trap d’in yaya Faruk ni da Sadik, ba k’aramin aikin shi ba ne yasa a kama Sadik a je a mishi horo ko shi ya d’au mataki da kanshi, ni kuwa b azan so abin da zai ta’ba min Dr ba.
Ni ma yau yadda na ke ji na ba zan iya kiran Dr in bashi hak’uri ba dan yaga ina son shi sai ya dinga min fad’a ko ya fad’a min maganar da ya ga dama, kuma ban da halin rama wa.
Don haka na share shi na tashi na ci gaba da harkoki na amma duk da haka tunani ne a raina kan matsalar da zan fuskanta nan gaba.
Yaya Faruk tun da ya bar gidan mu ya koma gida cikin zafin rai.
San da ya shiga main parlour d’in ya samu Anisa a parlour tana waya da yaya Khalil.
Saurin katse wayar tayi ta mishi sannu da zuwa.
"Ki same ni a side d’ina Anisa" yana gama fad’ar haka ya nufi side d’in shi.
Yanayin shi da Anisa ta gani yasa ta ji ba dad’i a ran ta, da alamar akwai abin da yake damun shi.
Tun da ya shiga d’akin ya rasa mai ke damun shi, ya rasa wani irin so yake ma Fatima haka da har yake jin wani irin kishin ta haka.
Anisa ce ta shigo d’akin had’e da sallama.
Ciki-ciki ya amsa mata.
A ranta kuwa addu’a take ta jerowa saboda yau yanayin yaya Faruk ya sa ta a tunani.
Cikin sanyin murya tace "yaya gani".
Wani huci ya furzar sannan yace "Anisa waye Dr Sadik?".
"A clinic d’in asibitin mu yake aiki".
"Akwai wata alak’a ce a tsakanin sa da Fatima?" ya jefa mata wata tambayar.
"Eh yaya Faruk akwai".
Wani irin fad’uwar gaba yaji a lokaci d’aya idon shi ya kad’a ya canza kala.
"Mecece alak’ar su d’in?". Anisa ta tambayi kan ta.
Anisa ta fara mamakin tambayoyin da yaya Faruk yake jero mata, to me yasa yake son sanin alak’ar su?
Wata irin tsawa ya daka mata da ta sa ta tsoro yace "ki bani amsar tambayar da na miki".
Cikin rawar murya Anisa tace "Akwai alak’ar soyayya a tsakanin su".
Wani irin kallo ya watsa mata kamar bai yarda da amsar da ta bashi ba.
"Ita ma tana son shi? Ya k’ara tambayar ta.
"Eh ta na son shi".
"Tun yaushe suka fara soyayya".
Wannan karan tambayoyin sun ma Anisa yawa, tana tunanin yaya Faruk bayan karatun sojan da yayi, ko ya had’a da aikin jarida ne a course d’in su, saboda wannan tambaya ta isa haka.
"Anisa don’t let me come near you, in ba haka ba jikin ki zai fad’a miki, don iskanci sai in miki tambaya ki tsaya wani tunani".
Anisa tana jin abin da yace da sauri ta ce "Ina ganin tun bayan gama siwes d’in mu ne".
Shiru yaya Faruk yayi yana mamakin yadda Fatima ta maida shi k’aramin yaro, ta sa shi yaci gaba da son ta alhalin ta san ba ta san shi, baa bin da ya fi mishi ciwo shine yadda tayi amfani da damarta ta yaudare shi, dole ne ya hukunta ta daidai da laifin da ta mishi, kenan duk wannan lokacin da ya furta ma ta son shi ta d’auke shi a banza, ba ta tsaya a nan ba sai da ta had’a da son wani bayan shi bayan tasan tuntuni yake son ta, hakan na nuna sai bayan da ya furta mata yana son ta sannan ta fara soyayya da wannan Dr da kullum take mishi k’aryar ce wa suna gaisawa ne.
"Me yasa wasu matan suke da yaudara ne?".
Wannan tambayar ita ce ta ke mishi yawo a k'wak'walwar shi.
Muryar shi ce a wannan lokacin tayi sanyi ya kalli Anisa yace "Anisa dake za a munafunce ni, a yaudare ni, ina tunanin ko kowa zai min haka, ban dake Anisa, saboda duk abin da na miki, ba ki da d’an uwan da ya wuce ni".
Anisa ba ta fahimci inda maganganun yaya Faruk suka nufa fa.
Kallon shi cikin rashin fahimta tace "yaya Faruk ni ban dani aka yaudare ka, hasalima ban fahimci mai kake nufi ba".
Cikin ‘bacin rai yace "kina nufin ba ki san ina son Fatima tsawon lokaci ba, ko kina so ki fad’a min cewa Fatima ba ta fad’a miki ina son ta ba? shine ke kuma ki ka ba ta shawarar tayi soyayya da Dr saboda ni ba ki d’auke ni a matsayin yayan ki ba".
Mutuwar tsaye Anisa tayi da jin wannan magangann da yaya Faruk yake fad’a.
"Yaya Faruk yana son Fatima? tun yaushe kenan yake son ta? me yasa Fatima ba ta fad’a mata ba" duk wannan jerin tambayoyin da take dashi tasan ba wanda ya dace ya amsa mata sai Fatima.
Tausayin yayan ta ne ya kama ta a lokaci guda ganin yadda a loakci d’aya yanayin shi ya canza.
"Yaya Faruk ina son ka yarda da maganar da zan fad’a maka, wallahi tun da muke da Fatima ba ta ta’ba fad’a min kana son ta ba, yaya Faruk ya za ayi in goyi bayan bare bayan nasan d’an uwa na yana son ta, yaya Faruk ba ni da kowa da zan kalla a matsayin d’an uwa fiye da kai, ina so ka yarda da magana ta" Anisa ta fad’a da murya ta dake nuna alamun ta na son yin kuka.
Ya d’an ji sanyi game da bayanin da Anisa ta mai, ya kuma yarda cewa ba ta san me ke tsakanin shi da Fatima ba.
Nuni ya mata da zo ta zauna a inda take.
Jikin ta ba k’wari ta tako ta zo ta zauna kusa dashi.
Hannun ta ya rik’e ya fara ba ta labarin tun sa da ya fara so na, da kuma san da ya furta min yana so na.
Bayan ya gama ba ta labarin ne ya d’aura da cewa "Anisa ina son Fatima wanda ni kaina ba zan ce miki ga lokacin da na fara son ta ba, na riga na mik’a mata yarda cewa Fatima za ta so ni duk kuwa da yadda a da take min kallon mak’iyin ta, sai gashi ta shammace ni a lokacin da ban yi zato ba".
Anisa ce ta kalle shi cikin tausayi tace "yaya Faruk insha Allahu in dai Fatima rabon ka ce, sai ka aure ta kuma za ta so ka, in kuma ba rabon ka bace, duk son da kake mata sai ka ga Allah bai nufa kun yi aure ba, ka ci gaba da addu’ar neman za’bin Allah, nima zan taya ka da addu’a".
Hak’ik’a ya ji dad’in maganganun Anisa da ta mishi.
Murmushin da bai kai ciki ba ya sakar mata kana yace "Anisa na gode da shawarar ki, ina son maganar nan ki bar ta daga ni sai ke, ina so in ga iya gudun ruwan Fatima d’in, kafin in san matakin da ya kamata in yanke akan ta".
"Ba zan fad’a ma kowa ba kamar yadda ka buk’ata, Allah kuma ya kawo mafita cikin sauk’i yaya".
"Amin Anisa, nagode, za ki iya tafiya".
Tashi tayi ta bar d’akin cike da mamakin wannan labarin da yaya Faruk ya ba ta.
Tun da Anisa ta koma d’aki take juya maganar da suka yi da yaya Faruk.
Sai a yanzu ta gano dalilin da yasa ban fito ta fad’a mata alak’ar su da Dr Sadik ba har lokaci da suka had’u dashi, da irin hujjojin da na kawo mata san da ta tambaye ni me yasa ban fad’a mata soyayyar mu da Dr ba, da kuma dalilin da yasa da farko na hana Dr zuwa gidan mu.
A yadda ta ke jin ta tana ganin in ba tunkara ta tayi da tarin tambayoyin dake ranta ba za taji sauk’in tunanin da yake addabar ta.
Abu d’aya ne zai hana ta tunkara ta, sai dan yadda yaya Faruk ya mata magana akan ta bar maganar daga shi sai ita.
Yau kusan 2 days kenan rabon mu da mu had’u da Sadik ko ya kira ni a waya, daurewa kawai nake yi amma ni nasan yadda nake ji na rashin ganin junan mu.
Da daddare sai ga kiran Dr ya shigo waya ta.
Murna kamar in tashi in taka rawa, dama gashi nayi missing d’in ganin shi da zazzak’ar muryar shi.
Hannu na har rawa yake wajen d’aukar wayar.
"Assalamu alaikum Prince".
"Wa alaikis salam".
Shiru ne ya ziyarce mu, cikin mu an rasa wanda zai ci gaba da magana.
Sadik ne ya katse shirun da cewa "Zarah kin min laifi ko ki kira ki ba ni hak’uri".
Cikin shagwa’ba na ce "Wani laifi na maka Dr".
"Au har kin manta kenan, yanzu dai ina son ki fad’a min kin gano dalilin da yasa shi wanna Faruk d’in yake hana ki tsayawa zance?"
"Sadik ina so ka fahimta, yaya Faruk a matsayin yaya na yake, dole ni in bi abin da yace min, yaya Faruk yana da power a familin mu ya zartar ma kowa hukunci ba tare da an tuhume shi ba, try to get my point".
Duk wannan bayanin da na mishi ba wai ya gamsu dasu ba ne, kawai dai zai bi ni a yadda ta ke so.
Nan suka ci gaba da hira irin ta masoya.
Washe gari ko da aka tashi School, Anisa suka biyo department d’in d’auka ta, na ga yanayin Anisa ya canza ba kamar yadda take ba, da na tambaye ta ko wani abu yake damun ta, sai tace min ba komai.
Ganin yadda ta share ta d’akko wayar ta tana danna wa yasa nima nayi shiru, saboda nasan akwai wataran da za ka ga mutum bai jin dad’in jikin shi.
Ni aka fara sauke wa sannan su ka tafi.
Da daddare muna cikin waya da Dr naji alamar tsayuwar mutum a gaba na.
Saurin d’ago kaina nayi don ganin wanda ke tsaye.
Ido na ne yayi tozali da yaya Faruk.
Ba yi tsammanin zuwan yaya faruk a wannan lokacin ba.
Tsananin tsoron da nake ciki yasa na fara zufa duk kuwa da AC d’in dake d’aki na.
Cikin murtukewar fuska ya kalle ni yace "Da wa kike waya".
Halin da nake ciki a yanzu ba zai ba ni damar tsayawa yi mishi bayanin da wanda nake waya ba.
"Ba ni wayar" ya fad’a cikin ba da umarni.
Hannu na yana rawa na nik’a mishi wayar.
Amsar wayar yayi ya shiga received call, last call wya duba ya ga an sa Prince Dr.
Wani irin murmushin takaici yayi sannan yace "Fatima na sha tambayar ki, miye tsakanin ki da Dr Sadik kina ce min likitan ki ne, for the last time zan k’ara tambayar ki, miye tsakanin ki dashi".
Shiru nayi na kasa cewa komai, miyau ma da k’yar nake iya had’iyar shi saboda tsoro.
Cikin tsawa yaya Faruk yace "ki fad’a min abin da ke tsakanin ku".
A karo na biyu ban ce komai sai ma k’ifta idanuwa na da nake yi.
Wani gigitaccen mari naji a fuska ta da yasa ni rik’e kunci na.
A lokaci d’aya na ji wani ‘bacin rai ya saukar min, tsoron da nake ji ya fita daga raina.
Ina ganin yanzu ba zan jure cin kashin yaya Faruk ba, ban ga dalilin da zai dinga mari na ba.
Hawayen takaici ne yake zubo min saboda yadda marin ya shige ni.
Ina ganin lokaci yayi da zan daina ‘boye ma yaya Faruk alak’ar mu da Dr, tun da shi ya buk’aci in fad’a mai, gwara in daina tsoro in fad’a mishi gaskiyar maganar, ni kaina na gaji da ‘boyewa.
Cikin rashin tsoro na ce "yaya Faruk, Dr Sadik shine wanda yake so na, ni ma nake matuk’ar son shi, ina ganin ba namijin da zan so sama dashi".
Wani irin huci yaya Faruk yake yi, fuskar shi duk tayi ja kasancewar shi fari.
Wani kallo yake mata na ba ki isa ba kana ya ce "Teemah kin yi kuskure da ki ka yaudare ni, ki kasa na ‘bata lokaci na akan ki, zan iya yin komai a kan ki in har mutum zai yi takara da ni a son ki, ya kamata ki gane hakan, kar ki bari in fito miki ta wata hanyar da kema za ki sha wuya, ba ki isa ki so wani ba, bayan ni ina son ki, ba ayi macen da za ta wulak’anta ni akan son ta ba".
Ci gaba yayi da cewa "you are the only air i breathe, you are ticking in my heart like a little clock, I value our relationship more than you’ll ever know, you are the girl of my dreams, Fatima ashe ake duk ba haka ki ka d’auka ba a gurin ki, kin nuna min soyayya na zuwa a yananyi daban-daban".
Ganin yaya Faruk da gaske yake akan furucin shi yasa zuciyata ta bani k’arfin gwiwar in k’alubalance shi ko zai bar ni nima na auri wanda nake so.
"Yaya Faruk, sai dai kayi hak’uri, zuciyata tayi nisa a son Dr, kamar yadda ka ce ba ka san lokacin da ka fara so na ba, nima ban san lokacin da na fara son Sadik ba, yaya Faruk tun san da ka ce min ka na so na, nayi k’ok’arin sa son ka a zuciya ta, amma ban san me yasa zuciya ta tak’i amincewa dakai ba, har lokacin da na had’u da Dr muka fara soyayya, ba laifi na bane, laifin so ne, yaya Faruk ka fahimce ni".
Wani irin rad’ad’i yake ji a zuciyar shi, yau wai shi Fatima take fad’a mai tana son wani bayan shi, ba tayi duba da tsawon lokacin da ya d’auka yana d’awainiya da son ta ba, yana ganin ya kamat ya d’auki mataki a kanta.
Saukar wani mari na k’ara ji a fuska ta da ya fi na farkon zafi.
Cikin k’unar rai yace "zan iya miki komai akan yaudara ta da kika yi, me yasa tun farko ba ki fad’a min in hak’ura ba, ki ka munafunce ni, sai da kika ga komai yazo gargara sannan za ki fad’a min, tun da abin na ki iskanci ne, zan ba ki mamaki".
kuka na fara yi ina cewa "yaya Faruk ko mai za ka min, ba zan gaji da fad’a maka Dr nake so ba".
Gani yake yi in dai ya ci gaba da tsayawa yana musayar yawu da ni, zai iya yin abin da zai jawo da na sani.
Yanke hukunci yayi akan ya bar d’akin kawai.
San da zai fita daga d'akin ne ya yi wurgi da wayar akan gado.
Yana fita ya had’u da Ummu a falo, gaishe da ita yayi ya mata sallama ya tafi.
Ganin yanayin shi yasa tayi tunanin akwai matsala, don haka ta tawo d’aki na.
Samu na tayi ina kuka, ga ido na da ya yi ja.
Ummu ce ta kira suna "Fatima"
Cikin kuka na amsa mata.
"Me yasa ki kuka?"
"Ba komai Ummu".
"Haka kawai ki ke kuka?"
Wannan karan ban amsa mata tambayar ta ba, sai ma kuka na ci gaba dayi.
Ran Ummu ne ya fara ‘baci, ganin ta tambaye ni nak’i ba ta amsa, gashi kuma sai kuka nake yi.
Cikin fad’a tace "Tun da ba za ki amsa min ba, me ya had’a ki da Faruk na ga ya fita cikin fushi".
"Fad’a muka yi".
"Wani irin fad’a kuma?".
"Sa’bani mu ka samu".
"Akan me?"
Shiru na k’ara yi.
Tun da ba za ki fad’a min ba, sai ki yi tayi, in kukan zai miki magani" tana gama fad’ar haka ta fita daga d’akn.
"Na ga ta kaina" Na furta hakan a bayyane.
Yanzu ban san wani mataki yaya Faruk zai d’auka ba, ina jin yau allurer sojojin ta motsa ne, gwara da Allah yasa ya tafi, in ba haka ba ban san me zai min ba.
Yaya Faruk yana fita ya shiga mota ya ja ta a guje.
Karatun da yasa a motar shi ne yasa yaji ‘bacin ran da yake ciki ya ragu.
Yana zuwa gida ya dinga danna ma mai gadi horn da k’arfi.
Da gudu mai gadi yazo ya bud’e mishi yana mishi sannu da zuwa.
Ko kallon shi bai yi ba saboda yadda yake jin zuciyar shi.
Direct d’akin Daddy ya wuce.
Abinci ya same shi ya na ci, kusa dashi yaje ya zauna.
"Sannu da gida" yaya Faruk ya furta.
Kallon shi Dadi yayi ya lura da akwai abin da ke damun Faruk d’in.
"Yawwa Faruk".
Ganin yadda Faruk d’in yayi shiru yasa Dadi yace mai "ya aka yi ne Faruk, na ga kamar kana tare da damuwa".
Ba zai iya fad’a ma Dadin shi halin da yake ciki ba, don haka yace "Ba komai Dadi".
Ba dan Dadi ya yarda ba yace "shi kenan tun da kace haka, kaci abinci ne?".
"Yanzu na shigo gidan, ban ci ba".
"Zo mu ci wannan da nake ci".
Ji yake baa bin da zai iya ci ahalin yanzu, sabida haka yace ma Dadi "na k’ashi Dadi, ba na jin yunwa".
"Me ka ci?" Dadi ya tambaye shi.
"Ba komai".
"Common, zo ka zauna mu ci, ya za ayi ka zauna da yunwa".
Bai san musu dashi, shi yasa ya matso yasa d’ayan spoon d’in dake ajiye ya fara ci.
Ji yake yi abinci bay a mishi taste a bakin shi saboda halin da yake ciki, bai fi spoon biyar yayi ba ya ajiye spoon d’in.
Dadi ne ya kalle shi cikin kulawa yace "kana nufin ka k’oshi kenan?"
"Eh Dadi".
Dadi bai ce mai komai ba yaci gaba da cin abinci.
Bayan ya gama cin abincin ne ya maida hankalin shi ga Faruk da ya fad’a cikin tunani.
"Faruk alamu sun nuna kana cikin damuwa, but I don’t know why you d’ont whant to tell me"
"Nothing is bordering me Dadi, ina tunanin nan da 2 days zan koma aiki, Dadi ina so ayi fixing d’in bikin mu da Fatima".
Murmushi Dadi yayi yace "gobe za mu tsayar da Date d’in bikin, sai ka fara shiri".
Murmushin yak’e yayi, duk da yaji dad’in maganar sa date d’in da za ayi, hakan bai say a samu peace of min ba.
Suna wannan maganar ne, Momi ta shigo da flask a hannun ta.
Ajiye flask d’in tayi kusa da Dadi da cup a hannun ta tace "wani sirri ake yi da ba za a jira ni in shigo ba" ta fad’a tana dariya.
Dariya Dadi yayi yace "tsakanin mu ne, in tayi wari za ki ji".
"Ina zaune nasan za a zo a fad’a min".
Duk wannan maganar da ake yi, yaya Faruk bai ce komai ba, hankalin shi na wani guri.
Momi ce ta zauna aka ci gaba da hira da ita, yaya Faruk ba wani dad’in zaman yake ji ba, tashi yayi ya musu sallama ya tafi sashin shi.
Washe gari Dadi ya samu Abbu da maganar tsayar da lokacin biki, sun yanke nan da wata hud’u, lokacin mun gama Diploma d’in mu.
San da Dadi ya dawo gida ya sanar da yaya Faruk, yaji dad’in labarin, sai dai shi yafi buk’atar in so shi, yana ganin soyayya ita tafi mahimmanci kafin a je ga zancen aure, sai dai ba yadda zai yi ne yasa ya buk’aci da a tsayar da lokacin bikin, fatan shi shine kafin lokacin, zan so shi.
Ko sallama yaya Faruk bai min ba ya koma Abuja.
Tun lokacin da yaya Faruk ya koma Abuja ya rage walwala, yanzu yafi so ya zauna shi kad’ai.
Ya rasa yanda zai yi ya shawo kan Fatima, a da yana ganin abu mai sauk’i ne da zai iya jawo hankalin ta gare shi, sai dai a yanzu ya gane cewa nayi nisan da ba zan saurare shi ba, yanzu duk wayar da muke yi dashi, da fad’a muke k’are wa, gashi yanzu ya dawo da fad’an shi, abu kad’an ke sa shi hassala, ni kuma ba na jurar maganganun da yake fad’a min, hakan yasa ya rage kira na.
Yau yana zaune a falon shi, yayi nisa a cikin tunanin da ya sa bar wa kanshi, Mus’ab ya shigo da sallama.
Tunanin da yake yi yasa bai ji sallamar da Mus’ab ke mai ba.
Tako wa yayi ya zauna kusa dashi.
Dafa kafad’ar shi da Mus’ab yayi yasa ya dawo daga duniyar tunanin d yake yi ya saki ajiyar zuciya.
Kallon shi kawai Mus’ab yake yi ganin tun san da ya dawo daga Kaduna yake cikin wannan halin.
"Faruk, wai me ke damun kane?" Mus’ab ya tambaye shi.
"Me ka gani?" Shima ya maida mishi tambaya.
"Faruk, nasan ba kowace matsala za kai ta fad’a min, ina so ka dubi amincin mu da yarda da muka yi da juna, ka fad’a min matsalar ka, duk wani wanda yake tare dakai, yasan ka canza, plsss Faruk, ni kaina ba na jin dad’in ganin ka a wannan halin da kake ciki na tunani, hakan xai iya jawo maka wani ciwo ya kuma yi affecting d’in ka".
Yasan ba wanda ya cancanta ya fad’a wa matsalar shi kamar Mus’ab, yasan zai iya taimakon shi da shawara, yana ganin fad’a mishi shine maslaha a gare shi, ko ba komai zai samu sauk’in tunanin da yake yi.
"Mus’ab ina cikin matsala".
Da sauri Mus’ab ya ce "Wace matsala Faruk".
Nan Faruk ya sanar dashi halin da suke ciki shi da Fatima, da kuma matsalar da yake fuskanta a guri na.
Tausayin Faruk ne ya kama Mus’ab a wannan lokacin, yasan Faruk bai san so ba sai a kaina, dole ne ya shiga wannan halin.
Cikin tausayawa yace "gaskiya Fatima abin da ta maka ba ta kyauta ba, ko waye a ka ma haka dole ne ya shiga cikin tunani, a yadda ka bani labari na fahimci son da Fatima take ma wannan Dr d’in, irin son nan ne da ake cewa *Makauniyar Soyayya*".
Faruk ne ya katse shi da cewa "Mecece Makauniyar Soyayya kuma?".
Mus’ab ne ya bashi amsa da cewa "Makauniyar soyayya wata irin soyayya ce da mutum ya ke ma wanda yake tsananin so, irin wannan soyayyar ita ce mutum bai duba wanda ya dace yaso ba, bai duba aibun shi ko laifin shi, duk abin da zai yi/za tayi daidai ne a gurin shi/ta, mutum zai iya ‘bata wa da kowa akan wanda yake so, kuma duk a ganin shi/ta duk cikin soyayya ce saboda duk a ganin su a cikin soyayya ne saboda sun makance a so, wannan soyyar ita ce Makauniyar soyayya, kuma ita wannan soyayyar yawanci tana jawo danasani a lokacin da mutum ya hankalta".
Faruk ya gamsu da bayanin da Mus’ab ya mai, ya kuma yarda da cewa irin wannan soyayyar nake yi.
Mus’ab ne yaci gaba da cewa "shawarar da zan baka Faruk shine, ka ci gaba da addu’a akan Allah ya za’ba maka abin da yafi alkhairi a gare ka, sannan ka ci gaba da hak’uri da duk abin da za ta maka, shi so da maganar aure ya k’unshi k’alubale dama, sai dai kowa da irin yadda yake zuwa masa, nan gaba z aka ga ribar hak’urin naka, ina ganin komai zai zo da sauk’i tun da har anyi fixing d’in bikin ku".
Ba k’aramin jin dad’in shawarwarin Mus’ab yayi ba, shi yasa yake jin dad’in kasancewa da Mus’ab a matsayin aboki.
Da haka suka ci gaba da zanta wa akan matsalar, a haka Faruk yaji ya samu k’arfin gwiwa.
Sallama Mus’ab ya mishi ya tafi.
Yana kwance a d’aki yaji k’arar wayar shi, sai da aka sake kira sannan ya d’auki wayar.
Sunan Binafa ya gani a jikin screen d’in wayar, kasancewar yayi saving d’in numbar ta tun da ta sake kiran shi.
Sallama ya mata ta amsa masa.
Sun d’an yi hira kafin Binafa ta d’aura da cewa "Umar, tun san da muka had’u Asaa pyramid, na ji na kamu da son ka, nayi k’ok’arin dannewa amma zuciyata ta gaza yin haka, hakan yasa na rasa walwala da sukuni, su Dad d’ina da Mom d’ina sun ta tambaya ta akan in fad’a musu matsala ta, ina ganin ko na fad’a musu bas u da maganin matsala ta sai kai, plss Umar ka tausaya ka bani masauki ko da yaya yake, zan yi farin ciki da haka".
Sauraren ta yake na yadda take bayyana mishi yanda take son shi, ina ma a ce Teeman shi ce ke furta mishi wad’annan kalmomin, da bai san dad’in da zai ji ba, sai dai kash, ita ta riga tayi nisa da son wanin shi.
Binafa ce ta katse shi da cewa "Bregadier kana ji na kuwa".
"Ina jin ki Binafa, na gode da son da kike min, sai dai ina mai ba ki hak’uri Binafa, ina da wacce ta dabaibaye zuciya ta, sai dai ina miki addu’ar Allah ya kawo miki miji nagari".
Kuka ta fara mishi tana k’ara fad’a mishi halin da take ciki a yanzu na son shi.
Tausayin ta ne ya kama shi ganin yadda take mishi kuka, shima da yana da halin kuka da yayi ko ya samu sauk’i a ranshi.
Me yasa so yake zuwa mutane mutane da launi daban-daban, ina ma bai fad’a cikin so ba, da bai tsinci kanshi a halin da yake ciki a yanzu ba.
K’arar sautin kukan ta da ya ci gaba da ji a kunnen shi ne yasa ya tuna da waya yake yi.
Lallashin ta yaci gaba dayi yana fad’a mata kalamai masu kwantar da hankali, da haka ya samu ya shawo kanta har ta hak’ura, kafin su yi sallama ta nemi alfarmarshi akan za taci gaba da kiran shi suna gaisawa sannan suka yi sallama da ita.
Yau kusan wata d’aya kenan da gama service d’in yaya Khalil, tun da ya dawo ya fuskanci ina cikin matsala, idan ya tambaye ni sai in ce masa ba komai, tun yana tambaya na har ya gaji ya zuba min ido, sannan yayi mamakin wai yaya Faruk ke so na amma ban fad’a mai ba, ya sha gani na muna da waya da Dr, ya rasa in da na fuskanta, bayan dawowar shi yaji time d’in da aka yi fixing, ya rok’i alfarmar a k’ara mishi lokacin, in yaso a fara nawa bikin da yaya Faruk, daga baya ayi nasu.
Komai yayi farko zai yi k’arshe, hakan ta kasance gare mu, mun rubuta final exam d’in mu mun yi graduation d’in mu, karatu da dad’i da wuya in aka gama shi, yanzu ba mu da wata sauran fargaba da ta rage mana game da harkar karatu.
Bikin mu bai fi saura wata biyu ba sai ga yaya Faruk ya zo Kaduna.
Hakan ya k’ara d’aga min hankali ganin yadda lokacin bikin mu yake matsowa, gashi har yau ban fad’a ma Dr Sadik halin da ake ciki ba.
Kiran shi nayi a waya akan cewa in ba ya komai ya same ni a gida, akwai maganar da nake son mu tattauna dashi.
San da ya k’araso ne ya kira ni a waya yana waje.
Hijab na san a fito na wuce gurin Ummu na mata k’aryar cewa zan je gidan su Anisa in dawo yanzu.
fatan a dawo lafiya ta min kana tace in gaishe da su Anisa da Momi.
Ina fitowa na shiga motar nace mai ya tuk’a motar mu bar layin.
Kallo na yayi da alamar tambaya, amma ganin yanayin da nake ciki yasa bai ce min komai ba ya ja motar mu ka bar layin.
Sai da naga mun bar layin mun shiga wani layin sannan na ce ya tsaya a nan.
Sai a lokacin naji zuciyata ta karye na fara kuka wanda nima ban san dalilin yin kukan nawa ba.
Bi na yake yi da kallo ganin yadda nake kuka bil hakk’i yace "Wai Zarah me yake faruwa ne kike wannan kukan, ki fito ki fad’a min me ke faruwa dake ne".
Cikin kuka nace "Sadik an kusa raba mu, za a sa almakashi a datse soyayyar da ke tsakanin mu, na kasa danne halin da nake ciki a yanzu, shi yasa na ga gwara in fito in fad’a maka halin da nake ciki a yanzu".
"Ban gane me kike nufi ba, wai waye zai raba mu?" ya tambaye ni.
"Sadik aure za a had’a ni da yaya Faruk, yanzu haka bikin bai fi saura wata biyu ba" Na k’arashe maganar cikin shashshek’ar kuka.
Wani irin takaici ne ya kama shi jin wai an kusa bikin ta da Faruk, ba ta fad’a mishi ba, sai da ta ga komai ya rinca’be sannan za ta fad’a mishi.
Shi yasa da tace mai Faruk d’in ya hana ta tsayawa zance yasa alamar question mark, yasan daman yana da dalilin yin haka, abin ta fi yi mishi ciwo a ranshi shine yadda a lokacin ya tambayeta ta nuna mishi ba wani abu dake tsakanin su.
Cikin fad’a yace "Yanzu Zarah da kike wannan kukan miye amfanin shi, bayan sai da kika bari komai ya gama ‘baci sannan za ki fad’a min, gashi har ana maganar biki, yanzu mai ki ke so in yi akai".
Cikin kuka nace "Dr dubarata ta k’are, plss ka samo mana mafita, wallahi in dai ba kai na aura ba zan shiga wani hali, lai zuciyata take so da muradi".
Ganin yadda take kuka yaji duk jikin shi yayi sanyi, shi kanshi yasan Fatima na son shi.
Cikin lallashi ya ce "Wipe your tears Zarah, ki ba ni hakalin ki muyi magana ta fahimta".
Ina jin haka nayi saurin share hawayen dake fito wa daga fuska ta, na maida hankali na gare shi.
"Zarah, kin yi kuskure da tun farko ba ki fad’a min me ke tsakanin ki da wannan yayan naki ba, duk yadda muke son junan mu, ba mu da wani power tun da har an yi fixing d’in bikin ku, ina ganin mafita a gare mu shine mu yi hak’uri da yadda k’addara tazo mana mu hak’ura da juna".
Wani irin kallo na mishi na alamar tambaya akan abin da yace.
Maganganun da Sadik ya fad’a sun k’ara sa ni a rud’ani ganin yadda yayi saurin mik’a wuya ga al’amarin, duk wani bijire wa da halin da nake ciki a yanzu duk akan shi ne, amma shi gashi a lokaci d’aya ya nuna ya hak’ura da ni.
"Ban fahimci inda maganganun ka suka nufa ba, kana nufin har ka hak’ura dani, bayan duk fad’i tashin da nake yi duk a kan ka ne, Dr kar ka sa in fara zargin ko ba so na kake yi ba" Na fad’a cikin fushi.
Cikin cool voice d’in shi da yake k’ara sace zuciya ta yace "try to understand me Zarah, maganar ba a son ki ma bai taso ba, ke kan ki kisan ina son ki, in har da ba na son ki, bazan tsaya ‘bata ma kaina time ba, kema kuma ba zan ‘bata miki lokacin ki ba, abin da yasa ki ka ga nace haka saboda na rasa wace hanya za mu bi mu shawo kan matsalar, yanzu gashi kin ce bai fi saura 2 month bikin ba".
Sai yanzu na ji sauki a raina ganin shima Sadik ya nuna damuwar shi akan maganar, nasan yanzu zan samu relief a raina.
Da haka muka ci gaba da tattaunawa akan matsalar, mun yi da Dr zai neme ni a waya mu samu mafita akan maganar.
Fitowar da zan yi naga motar yaya Faruk ta shigo layin, da alama daga wani gurin yake tun da har ya biyo wannan layin.
Shi kuwa yaya Faruk tun da ya ganni na fito a motar ya tabbatar da cewa tare muke da Dr.
Kusa da motar Dr yazo yayi parking.
Fitowa yayi daga cikin motar ya nufo inda nake, ni kuwa jiki na in banda rawa ba abin da yake yi, hakan da nayi ne yasa Dr ya lura da halin da nake ciki.
Shima fito wa yayi daga side d’in driver ya kulle motar.
Kallon kallo ake yi tsakanin yaya Faruk da Dr Sadik, da alama kowa da abin da yake sak’awa a zuciyar shi.
0 Comments