MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
*Wannan shafin na sadaukar dashi ne ga masu son wannan novel d’in, masu min Magana ta pc, masu kira na daga wasu gari, ‘yan faceebook, ‘yan whatsapp, da duk group d’in da ake posting d’in wannan novel d’in da wanda na sani da wanda ban sani ba, na nesa da na kusa*
*Ba abin da zance muku sai dai fatan alkhairi, Allah ya bar zumunci*
*QUESTION OF THE DAY*
_A halayen larabawa kafin musulunci, mai suka kasance suna bauta ma wa? saboda me yasa suke kasha ‘ya’yayensu?_
47&48
Bayan gama jarabawar mu na zangon farko, aka bamu short break na hutun zangon.
Muna zaune a gurin shak’atawa ni da Ummu muna hira, motar gidan su Anisa ce ta shigo.
Bayan ta fito daga motar ne ta nufo in da muke tayi tana murmushi.
Gaisawa suka yi da Ummu kana na gaishe ta, muka nufi main parlour.
Kitchen na shiga na d’ebo drinks da snacks a d’an k’aramin tray da glass cup.
Ajiyewa na yi gaban ta, na nemi guri na zauna.
Da fara’ar ta tace "Fatima kwana biyu ba ki lek’o mu ba, tun da kun samu hutun first semester, in zan tafi sai mu tafi tare".
"Bari in je ciki Momi, in za ki tafi sai mu tafi, Ummu kya fad’a ma Abbu in ya dawo".
Mik’ewa nayi na nufi d’aki na don in basu guri.
Da na shiga d’aki, kaya set 5 na d’iba na sa a jaka.
Momi sun dad’e a falo suna hira kana ta kira ni muka tafi.
Tun da naje gidan su Anisa muke hira, mu yi ta labarin ‘yan course d’in mu da rayuwar school life.
Haka yaya Khalil ke zuwa mu zauna a parlour ko a garden muyi ta hira.
Gaskiya ina jin dad’in yin hutu a gidan su Anisa.
Kwana biyar nayi a gidan na koma gida.
Mun koma school in da muka shiga zango na biyu, karatu ya k’ara zafi fiye da zangon farko, komawar mu da 2 Weeks result ya fito, GP d’ina yayi kyau, dad’in da naji shine ban da wani matsala na carry over ba, da muka had’u da Anisa ma ta fad’a min GP d’in ta yayi kyau.
Mun yi nisa a zangon aka fara maganar siwes (Industrial training), tunani na fara yi inda zanyi siwes d’in.
Zuciya ta ce ta ba ni shawarar in sa Asibitin school d’in mu dan lecturers d’in mu sun fad’a mana ana samun experience a can.
Yau ta kasance ranar lahadi, yaya Khalil ne ya shirya cikin tsadadden yadi kalar ruwan k’asa, yadin ya matuk’ar yi masa kyau.
Ta slice window na hango shi ya fito daga side d’in shi ya nufi parking space zai shiga mota.
Da sauri na fito na k’arasa gurin shi ina cewa "yaya Khalil ina zaka ne? na ga wannan kwalliyar kamar gurin Anty na za ka, duk da ban san ko wacece ba".
Ta’be baki yayi yace "Kin ga Auta ki bari in na dawo sai muyi maganar, in ba haka ba sai ki hana ni fita da maganar ki".
Dariya nayi nace "kai yaya Khalil daga fad’ar gaskiya".
Shi ma dariya yayi yace "To yanzu dai shi kenan sister, tun da kina so in samo miki Anty, zan bincika in gani, yanzu dai bari in tafi, sai na dawo".
"Sai ka dawo yaya Khalil".
Shiga motar yayi ya kunna ya bar gidan yana d’aga min hannu, d’aga mishi hannu nayi na koma cikin gida.
Yana isa gidan, ya danna hon.
Mai gadi ne yazo ya bud’e masa ya shiga da motar.
Samun Anisa yayi a balcony d’in gidan, in da aka k’awata gurin da kujeru da tebur a can gefen gidan.
Gurin ya k’arasa yana sakar mata tsadaddan murmushi, ya nemi guri ya zauna.
Gaishe shi tayi ya amsa mata, tambayar ta yayi ko Momi na ciki?.
Amsa masa tayi "Tana ciki".
"Bari in shiga mu gaisa, yanzu zan dawo, yau akwai sabon labari da zan baki" ya fa’da da alamar wasa.
"Sai ka fito".
Tashi yayi ya nufi cikin falo d’in.
Ko da ya shiga parlour d’in ba kowa sai k’arar tv dake aiki shi kad’ai a parlour d’in.
Hango ta yayi tana sakkowa daga upstairs d’in dake parlour d’in.
"Khalil yaushe ka shigo, maimakon ka hawo sama ina can".
"shigowa na kenan".
Momi, Ina wuni". Yaya Kalil ya gaishe ta.
"lafiya lau, ya su Hajiya da Fatima". Momi ta amsa masa.
"Suna nan lafiya".
"Haule!" Momi ta fara kiran mai aikin ta.
Cikin ladabi ta amsa ta tsuguna tana cewa "Gani Hajiya".
"Drinks da ruwa da abinci za ki kawo ma Khalil".
"Toh Hajiya" Haule ta amsa ma ta.
Khalil ne yayi saurin kar’ban zancen da cewa "Momi ta bar shi kawai, zan koma gurin Anisa ne, tana can balcony".
"Ba ayi haka ba, ke Haule je ki d’akko ki kai mishi can".
"Toh Hajiya" Haule ta amsa cikin ladabi ta bar parlour d’in, ta nufi kitchen d’in.
"Kace ba za ka zauna muyi hira ba, za ka tafi gurin mutuniyar ka" Momi ta fad'a
"Ai zan dawo ciki Momi".
"Sai dai na gan ka kawai, nasan sallama ce za ta shigo dakai, in ka had’u da Anisa ai sai Allah in kuka fara zancen ku".
Dariya yayi ya bar falon, Momi kuwa neman guri tayi ta zauna.
San da ya koma, samun ta yayi tayi playing ‘din wak’ar Rihana da tayi mai suna *if its love* bin wak’ar take yi a hankali kamar ita ta rera wak’ar.
Murmushi yayi ganin yadda take bin baitin wak’ar, ita ma murmushi tayi tace "yaya ya aka yi ne? naga kana murmushi".
Na ga ai kina son wannan wak’ar ne".
"yaya Khalil ai ta iya wak’a ne"
Haule ce ta k’araso ta ajiye tray d’in a kan table d’in, ta bar gurin.
Kwalin chivita ya d’auka yayi shaking, sannan ya tsiyaya a glass cup d’in.
Sai da ya fara sha kana ya ajiye yana kallon ta.
"Anisa! ya kira sunan ta.
Amsa masa tayi tana jiran ji mai zai ce ma ta.
"Anisa zan bayyana miki abin da ke zuciya ta ne, ina so ki ba ni shawara".
Ita dai bin shi take da kallo, saboda tasan in yaya Khalil zai yi Magana mai mahimmanci, manta wa yake da wani abu wai shi wasa, dan haka ta bashi dukkan hankalin ta.
Ci gaba yayi da cewa "Anisa akwai yarinyar da na dad’e ina son ta, mun shak’u da ita, da farko ban d’auka cewa son ta nake yi ba, na d’auka *shak’uwa ce* sai daga baya na gane son ta nake yi, shine nake neman shawarar ki akan yadda zan tunkari yarinyar in fad’a mata".
Wani abu ne taji ya tsaya ma ta a zuciyar ta, wanda ta rasa ko na menene, ba ta so yaya Khalil ya fahimci tana cikin wani hali.
Cikin dauriya ta fara da cewa "Ina ganin yaya Khalil gwara ka fad’a ma yarinyar, barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa, kuma tun da kace kun shak’u da ya yarinyar ina ganin ba za ta k’i amsar tayin soyayyar ka ba, yaya Khalil ba wai zan yaba ka bane, amma ina ganin duk yarinyar da ka fito ka ambata mata kana son ta, za ta amince dakai, ka je ka fad’a mata".
Wani irin murmushi dad’i yayi, saboda amsar da yake son gano wa, ya gano cikin sauki duba da re-action d’in Anisa d’in.
"Anisa! Ya kira ta a karo na biyu.
Wannan karan ba ta samu damar amsawa ba, ganin yadda ya zuba mata ido.
Bai damu da amsawar ta ba yaci gaba da cewa "Anisa ba kowa bace yarinyar da nake nufi illah Anisa".
Saurin kallon shi tayi tana jiran k’arin bayani.
Lura da hakan da yayi yasa yace "Anisa ke nake nufi, ke nake so…., ina fatan za ki amshi tayin soyayya ta da na miki da hannu bibbiyu".
Saurin rufe fuskar ta tayi da tafukan hannun ta.
Cikin tsokana yace "Bari in tashi in tafi, tin da ba a amince da ni ba".
Da sauri ta bud’e fuskar ta tace ‘kai yaya Khalil ni ban ce haka ba".
"Kin amince kenan?".
Sunkuyar da kan ta tayi tana murmushi kasancewar tana jin kunya ta fito tace mai ta amince.
Duk da ya fahimci ta amince dashi, amma yana so ta fad’a da bakin ta saboda zai fi yin marhabun da hakan.
Yaya Khalil bai bar gurin ba sai da ya samu amsar shi daga bakin Anisa na cewa ta amince da soyayyar shi.
Nan ya dinga fad’a mata yadda yake son ta a zuciyar shi, hira suka ci gaba da yi kamar wanda suka dad’e a soyayya.
Da zai tafi ne ya kalle ta yace "Kin san da zan tawo nan, sai Fatima ta tsare ni wai ina zani haka, kamar wanda zai je gurin budurwa, shine n ace mata tun da Anty take so zan samo mata, kinga yanzu in na koma sai in fad’a mata Antin da na mata".
Cikin marairaicewa ta fara cewa "Plsss yaya Khalil kar ka fad’a mata, kasan Fatima tsokana ta za ta dinga yi".
Dariya yayi yace "Shi kenan tun da ba kya son k’awar ki ta sani, ni nasan Fatima da kan ta za ta gano".
"Ni ma ai zan fad’a mata, amma ba yanzu ba".
"kunyar ta kike ji kenan, ko su Ummu da Momi ki ke jin kunya su ji".
Shiru ta mishi ba tare da ta amsa mishi ba tare da ta ce mai komai ba.
Girgiza kai kawai yayi ya sakar mata murmushi ya wuce cikin falo d’in.
Cikin parlour d’in yaya Khalil ya koma yayi ma Momi sallama ya fito ya tafi.
Fitowar da yayi suka had’u za ta shiga falo d’in, kallon junan su suka yi wanda ke nuni da sak’on da suka isar ma juna sannan ya mata sallama ya tafi.
A school, Orientation na musamman aka mana akan Siwes da gurin da ya dace muyi siwes d’in mu.
An bamu form mun yi filling, inda muka cike sunan mu, account number d’in mu, Bvn number d’in mu, sai sunan inda za muyi siwes d’in da address, daga k’arshe suka amshi form d’in.
K’awancen mu na nan da Aisha amma ba mu cika had’uwa ba, kasantuwar department d’in mu ba d’aya ba, sannan akwai nisa tsakanin mu da department d’in su.
Mun fara jarabawar mu na zangon na biyu wannan karan ma cikin nasara, inda aka raba mana takardar siwes inda za mu kai ayi accepting d’in mu, period of attachment d’in 4 month ne za muyi.
Halima ce ta tambaye ni inda zanyi siwes d’ina, na fad’a mata a cikin asibitin school zan yi, jin hak ita ma tace bari tasa nan.
Naji dad’i hakan da Halima tace nan za tayi, saboda zan so ace akwai wandda na sani a gurin da zanyi a ‘yan class d’in mu.
Mun kai namu a asibitin school d’in mu, sun yi accepting d’in mu a d’aya daga cikin siwes student d’in su.
Anisa ma jin cewa a cikin school zanyi siwes d’ina yasa ita ma takai takadar ta laboratory dake cikin asibitin.
Bayan jarabawar mu da sati d’aya mu ka fara siwes d’in mu ni da Anisa da Halima a Shehu Muhammad kangiwa Medical Center dake cikin Polythecnic.
Sanye nake da lapcoat, yayin da nasa farin baby hijab, hakan sai ya k’ara min kyau da shigar.
Folder na d’auka zan kai office d’in Dr Abubakar Sadik da Dr Fatima.
Sai da na fara zuwa office d’in Dr Fatima na kira sunan patients d’in da ke waje kana na shiga ciki muka gaisa da ita na ajiye mata folder.
Gaskiya ina matuk’ar ganin girman Dr Fati kasancewar ta dattijuwa, mai son mutane, asibitin mutane na yabon halin ta ita da Dr Abubakar Sadik.
Office d’in Dr Sadik na wuce na kira sunan wanda suke waje, na yi knocking d’in k’ofar.
"Yes come in" abin da yace kenan.
Sallama nayi na shiga ciki na ajiye mai folder, amsa min sallamar yayi.
Gaisawa muka yi cikin wasa kasancewar shi ma na lura yana da wasa, amma shima na lura miskilin kanshi ne wani time d’in.
Kallo na yayi yace "Fatima Zarah ko"
Sai naji sunan ya min dad’i, ko hakan na da nasaba da dan ba a kira na da sunan ne?
"yaushe kika fara Siwes a nan" ya tambaye ni.
yau 1 week kenan da na fara, lokacin naji ance kai duty d’in safe kake dashi, ni kuma da duty na rana na fara".
"Allah ya taimaka" yace min.
Amsa masa nayi "Amin Dr"
Kallon folder dake gaban shi yayi yace "Zarah, za ki rage folder d’in nan, ba zan samu ganin duka patient d’in ba, akwai inda zani".
"Dr taimakawa za kayi tun da na riga na kawo".
Cikin wasa yace "Sai dai in za ki zo ki taya ni".
"Sai in taya ka Dr, in dai za ka nuna min yadda zanyi, amma kai zan nuna in patient suka zo kama ni na rubuta musu wrong medicine".
Murmushi yayi yace "Kin dai min dad’in baki, zan duba su, amma plss kar a sake kawo folder daga wannan zan fita ne".
"Insha Allah, za a kiyaye Dr".
Sallama na mishi na bar office d’in.
Yau kusan wata na uku a cikin asibitin, mun sa ba da mutane da dama, daga ciki har da patients da suke kawo katin su record room.
Mun yi wani irin sabo da Dr na ban mamaki, mutane na mamakin yadda muka saba dashi kasancewar ba kowa ce mace yake kulawa ba.
Yanzu haka muke chat dashi, wani time d’in ya kira ni mu gaisa kasancewar muna da number juna.
Kusancin mu da Dr yasa na fara jin shi a raina, amma ban sa hakan a raina illah d’auka da nayi shak’uwar da muka y ice ta janyo haka
Muna cikin yi siwes ne, result d’in mu ya fito.
Naje na duba, wannan karan GP na ya k’aru fiye da firsr semester.
A haka har mu ka cinye 4 month a asibitin na gama siwes d’ina muka yi sallama du da ba wai an rabu ba kenan, tun da zan ci gaba da shigowa in mu gaisa ko zan ga likita.
Mun sami hutun 1 Week na siwes d’in mu kafin mu yi resuming mu shiga ND 2.
Wannan karan Anisa ce tazo gidan mu da niyar yin kwana biyu.
Tun da tazo na fahimci kamar akwai soyayya a tsakanin su da yaya Khalil, ganin yadda yanzu take jin kunyar Ummu, idan tana waya kalamen da suke maida wa junan su, da kiran ta da yake yi garden suna hirar su.
Sai da na matsa ma ta ne ta fad’a min cewa suna soyayya, amma ba yanzu take so a ji a family ba.
Hakan yasa na dinga tsokanar ta ina cewa "Anty na ta kaina, ni zan fara fad’a ma su Abbu da Daddy a bani goron albishir".
Haka tayi ta rok’o na akan kar in fad’a musu kunya take ji.
Da yaya Khalil ya shigo ina tsokanar shi nace "yanzu shine kamin Anty amma ban sani ba, kuka ‘boye min, nima zan rama".
Dariya yayi yace
"Sorry Fatima, laifin Anisa ne, da nace zan fad’a miki, cewa tayi ba yanzu ba wai da kan ta za ta fad’a miki".
Hararar wasa na mata nace "Kin kyauta Anisa, yanzu ai gashi na sani, tun da ba kya so in Sani".
D’aura fuska tayi kamar da gaske tacce "ke ni fa yanzu Antin ki ce, saboda haka sai ki yi biyayya".
Duk’a wa nayi nace "Sorry Anti".
Gaba d’aya muka yi dariya saboda yadda nayi maganar.
Haka yaya Khalil ya zauna muka ci gaba da chapter kana ya mik’e ya fita.
Kwana 2 da Anisa tayi naji sun burge ni saboda yadda suke gudanar da soyayyar su cikin so da k’auna.
Tana gama kwana 2 ta koma gida.
Har yau muna zuwa islamiyya ran weekend, yanzu haka muna jarabawar shiga JSS3.
Mun koma school muka fara registration na shiga ND 2, yanzu karatu yafi zafi fiye da ND 1, yanzu ba ni da wani lokacin kaina sai na karatu.
Yau Wednesday, mun fito ni da Halima daga MSSN da muke yi duk ran Wednesday, mun fara tafiya ne zamu je masallaci saboda lokacin sallah yayi.
Waya ta ce tayi ruri alamar kira ya shigo
Sunan wanda na gani ne a jikin screen d’in yasa na saki wani sansanyar murmushi sannan na d’auka.
"Assalamu alaikum likita bokan turai".
sautin dariyar shi naji yace "Zarah manya, ya kike, ya karatu?"
"lfy lau Dr".
"ya aiki, ya patents".
"Aiki Alhamdulillah, patients kuma kullum cikin su muke".
Ci gaba yayi da cewa "yanzu kina ina ne?"
"Ina hanyar zuwa masallaci ne".
"Ok yau k’arfe nawa za ku tashi daga School?".
"Mun yi closing yau, lecturer da zai shigo mana bayan sallah ya bamu group work ne tun last week, saboda ba zai samu shigowa bay ace wanda ba su yi ba, su yi amfani da period d’in shi, gobe zai amsa, already mu mun riga munyi tun last week, yanzu in nayi sallah, zan biya SUG Hall ne, daga nan sai in wuce gida".
"In ba zan takura miki ba, bayan sallah mu had’u a fanta fun tun da ba ki da lectures, akwai maganar da nake so mu yi".
"Ok sai mun had’u".
"Bye, take care" abin da yace kenan ya katse wayar.
Bayan gama wayar mu ne na kalli Halima nace "kin san da wa muka yi waya?"
Girgiza kaai tayi alamar ba ta sani ba.
"Dr Sadik ne ya kira ni, wai yana so mu had’u a fanta fun".
"ke dai taku tazo d’aya da shi, in kun had’u ki ce ina gaishe shi’.
‘zan fad’a mai insha Allah".
Masallaci muka shiga muka yi sallah, bayan mun fito ne muka wuce cikin SUG Hall muka ci abinci, nan muka yi sallama da Halima ta wuce gida.
Direct fanta fun na je na nemi guri na zauna ina jiran k’arasowar shi.
[4/24, 21:59] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
_Wannan shafin naku ne ‘yan Kainuwa Writers fans na facebook da kuma fans 10 na whatsapp_
_Ina godiya da son da kuke ma wannan novel d’in, Allah ya bar zumunci_
_INA MUKU JINJINA TA MUSAMMAN_
*Meeynah (Princess of question of the day)*
*Ramlah*
*Fadeelah*
*Kune ku ka ba da amsar tambayar daidai, Allah ya saka muku da alkhairi, ya biya muku buk’atun ku da sauran musulmai baki d’aya*
*Amsar tambayan shine a halayen larabawa kafin musulunci shine sun kasance suna bauta ma gumaka, sannan suna kashe ‘ya’yayen su saboda tsoron/gudun talauci*
_TSOKACI_
_A kwanakin baya, akwai wani tambaya da nasa a question of the day, in da na ce menene sunan bishiyar dake cikin aljannah? a next post d’ina sai nasa (jannatul Kuldi), to ina nufin bishiyar sunan ta shajaratul kuldi)_ _ganin yadda wasu suka min Magana ta pc akan cewa bishiyoyin dake cikin aljanna suna da yawa, wasu kuma suna challenging d’ina akan ba shajaratul kuldi bace_
_To ni dai har yau binciken da nayi da kuma fad’ar malamai ban samu akasin amsa ta ba_
_Amma ina rok’on duk wanda yake da cikakken amsar tambaya ta tare da hujja zai iya min Magana ta pc domin fahimtar dani, har yau ni d’aliba ce, kuma duk tambayar da nake rubutawa sai nayi bincike akai kafin nayi tambayar_
*TUNATARWA*
_Allah yana jarabtar bawansa a lokacin da yaso, a kuma San da ya so_
_Allah ka bamu ikon cin dukkan jarabawar da za kayi mana_
49&50
Kusan zaman minti biyar nayi ina jiran shi, sai ga motar Dr Sadik yayi parking d’in motar shi a gefen Fanta fun.
Sanye yake cikin tsadadden yadi kalar white, kayan sun matuk’ar yi masa kyau, kasancewar Dr Sadik akwai d’aukan wanka, k’arasowa yayi da murmushi a fuskar shi.
Kujerar dake opposite dani ya zauna yana ci gaba da sakar min sansanyar murmushin shi.
Gaisawa muka yi cikin wasa da dariya kana ya bani hak’uri akan delay d’in da yayi.
D’aya daga cikin ma’aikatan ya kira akan ya kawo mana drinks.
Juyowa yayi ya tambaye ni yace "wani kala za a kawo miki Zarah?".
Girgiza kai nayi nace "table water kad’ai ma ya isa".
Kallo na yayi bai ce min komai ba yace wa ma’aikacin ya kawo table water guda biyu, ya had’o da fanta guda 2.
Sipping yake yi kamar ba ya son shan fanta d’in.
Wucewar kusan 2 minute, gurin ya d’au shiru ba tare da yace min komai ba.
Shirun da naji yayi ne yasa na fara pressing d’in waya ta.
"Zarah" naji ya kira ni cikin cool voice d’in shi.
"Dr" nima na fad’a.
Cikin tsadaddiyar muryar shi ya ci gaba da cewa "Zarah, na dad’e ina neman wacce ta dace da rayuwa ta, amma ban samu ba sai a yanzu, ni da kike gani Zarah, da ban yarda da wani soyayya ba bare in tsaya ‘bata lokaci na akai, yanzu ne nasan mahimmancin soyayya saboda na fad’a a cikin ta, ina kuma tunanin wacce nake so d’in za ta yarda ta amshi soyayya ta".
Tsayawa yayi kamar ba zai ci gaba da Magana ba, can ya ci gaba da cewa "kar in ja ki da nisa, Zarah ke nake so…., I crown you the queen of my heart, so many reasons are there to love you, your cute smile, your sweet laugh, your innocence and your kind heart makes me love you…
Wani irin fad’uwar gaba na ji a lokacin da ya sani saurin d’agowa na kalle shi.
Wannan shine karo na biyu da aka zaunar dani aka fad’a min Kalmar soyayya.
Tunano kalaman yaya Faruk nayi a lokacin da yake ce min _INA SON KI FATIMAH, I know I am in love with you because my reality is finally better than my dreams_
Gashi yanzu Dr ya zo min da wani sabon karatun wanda ban gama gane na farkon ba.
Na so na fara warware matsalar yaya Faruk, hakan bai yiwu ba sai ga Dr ya k’ara zuwa min da wani al’amari mai wuyar fassaruwa.
Idan nace ba na jin Dr a raina nayi k’arya, sai a yanzu da ya furta min yasa na tabbatar da cewa I am in love with Dr Sadik, sai dai yanzu ba ni da k’arfin amincewa kasancewar yaya Faruk bai san a wani babi yake ba.
Dr ne ya katse min wasik’ar jakin da nake karantawa.
"Zarah, I am a free person, duk yadda nake son mutum, in ya nuna bai amince ba, bazan matsa mishi ba, nasan so gamon jini ne, u are free to tell me if i am not your choice, zan fahimce ki"..
Ajiyar zuciya na saki kana nace "Dr ka d’an bani time, zan fad’a maka ra’ayina game da kai".
Ba tare da wata damuwa ba yace "Kar ki damu Zarah, na ba ki nan da gobe, ki yi shawara, zan kira ki in ji amsar ki, ko ki turo min text".
Mik’e wa yayi yace
"Zarah ni zan tafi, ki zo in sauke ki a gida".
Shiru nayi ina tunanin kar yaya Khalil ko direban gidan su Anisa su zo d’auka ta ba su ganni ba.
Wata dubara ce ta fad’o min na mik’e na bi shi cikin motar.
Kasancewar yasan layin, gidan kawai na nuna mishi ya ajiye ni a bakin gate.
Sallama muka yi ya ja motar shi ya tafi ya bar layin.
Ina shiga parlour d’in ban ji motsin kowa ba, hakan yasa na wuce d’aki na watsa ruwa na canza shiga zuwa English wears, kitchen na wuce na d’ebi abinci a plate na nufi d’akin Ummu.
Samun ta nayi tana gyara kayan ta a wardrope, sallama nayi na nemi guri na zauna.
Ummu ce ta amsa tana cewa "Fatima an dawo?".
"Na dawo Ummu, sannu da gida, san da na shigo ban sami kowa a parlour ba, shi yasa na wuce ciki na watsa ruwa" na ba ta amsa.
"Ai kuna shawo rana, dole sai da watsa ruwa".
Dariya nayi nace "Ummu karatu sai ka daure"..
"Allah dai ya baku sa’a a karatun ku".
Cikin jin dad’i nace "Amin Ummu".
"Ummu aiki kike yi ne?" na tambaye ta.
Amsa min tayi "mai wankin da guga ne ya kawo kayan, shine nake jera wa".
"Ummu ki bari in na gama cin abinci sai in jera miki".
"Ki barshi kawai Fatima, ke da kika dawo yanzu, ai na kusa gama wa".
A haka muka ci gaba da hira da Ummu ina cin abinci.
Bayan na gam cin abinci ne na d’auki plate d’in na tafi gurin sink na wanke.
D’aki na wuce na kwanta akan gado, kalamen Dr ne suka fad’o min a rai
*"Zarah ke nake so*., *I crown you the queen of my heart*
Wani dad’i ne ya kama ni a lokacin, ji nake yi kamar yanzu yake fad’a min wannan tsadaddun kalmomin.
D’aga kai sama nayi ina tunanin mafita.
A wannan lokacin ina cikin tsaka mai wuya, ina buk’atar mai ba ni shawara, gashi ina da masu ba ni shawara, yaya Khalil da Anisa, amma ba ni da halin tunkarar su da wannan zancen, saboda duk inda suka ji cewa yaya Faruk na so na amma nayi rejecting d’in shi na za’bi Dr, ba mai ba ni shawarar in za’bi Dr, da alamu kuma zuciya ta baza ta k’i tayin Dr ba, dan alamu sun nuna son shi ya yi dabaibayi a zuciya ta, wannan shine hausawa suke cewa "Ga biki, amma babu zanin d’aurawa".
Yaya Faruk da Dr Sadik na d’aura akan ma’auni, ko wanne na duba qualities d’in shi, sakamakon sai ya nuna min cewa yaya Faruk ya fi Dr qualities, hasalima ya fi shi kyau, son mutane, gashi kuma d’an uwana na jini, sa’banin Dr da mutane ke shakkar shi kasancewar sa miskili kuma bai damu da mutane ba
"Me yasa zuciya ta tak’i amsar gayyatar sa da ya min na so? Menene aibun shi?
Nayi k’ok’arin dasa son yaya Faruk a cikin raina amma hakan bai samu ba,
Menene mafita?" na tambayi kaina.
Zuciya ta ce tace min "mai zai hana ki amince da yaya Faruk saboda shi yafi cancanta ki so, in hakan ta kasance iyayen mu za su yi farin ciki da haka, ga k’arin zumunci da zai k’ullu a tsakanin su, hasalima shi yaya Faruk ne ya fara fad’a mi ki yana son ki, idan kika mai haka ba ki mishi adalci ba, kin sa yana ta jiran amsar ki, amma sai ki ka za’bi wani a kansa".
Wata zuciyar kuma ce min take yi "Ba wani rashin adalci da kika masa, ko da yace yana son ki, ai baki ce kin amince ba, kuma shi so ba ruwan shi da ‘yan uwantaka, so yana zuwa ne a zuciyar mutum ba tare da yayi shawara dashi ba, ki bashi hak’uri kawai".
Shawara ta biyu na d’auka saboda ina ganin ita ce mafita a gare ni.
Zuciya tace ta bani shawarar in tura ma yaya Faruk text na ban hak’uri akan cewa yayi hak’uri dani, Allah shi ma ya bashi mai son sa.
Wani tunani ne yazo min akan cewa in bari in ya dawo daga tafiyar da yayi yazo Kaduna sai in fad’a mishi, nasan zai fahimce ni, duk da nasan akwai ciwo, ba ni da yanda zanyi ne.
Da yamma ina d’aki ina wani assignment naji yaya Khalil na kira na.
Fitowa nayi na same su a falo, dashi da yaya Aminu suna hira.
Gaishe da yaya Aminu nayi, kana nayi ma yaya Khalil sannu da gida.
Yaya Khalil ne cikin tsokana yace "Fatima yau ina kika shiga ne a school, ni da Anisa muna ta neman ki a department d’in ku, gashi wayar ki is not reachable".
"Yaya Khalil yau da kaina na dawo, ganin mun gama lectures da wuri".
Yaya Aminu ne ya fara fad’a yana cewa "Tun da kun yi closing, ba sai ki nemi numban Khalil d’in ba ko Anisa, ki fad’a musu kin tafi, amma sai ki yi tafiyar ki su yi ta shan wahala, idan kika sake, za ki had’u dani".
Cikin shagwa’ba nace "To ba kaina ne yake min ciwo ba".
A raina nace 'yanzu na rabu da fad’an yaya Faruk, saura kai".
Cikin tausayawa yaya Khalil yace "Ayya sorry sister, Allah ya k’ara sauki".
"Amin na amsa".
Yaya Aminu ne ya tashi ya nufi side d’in Ummu.
Zama nayi muka ci gaba da hira kamar ba ni bace nace kaina na ciwo.
Washe gari da daddare, kamar yadda Dr ya bani time, sai gashi ya kira waya ta.
Ko kan in d’auka, wani special smile kawai nake yi.
"Assalamu alaikum Dr" na fad’a.
"wa’alaikis salam Zarah a cikin taurari".
"dafatan kin wuni lafiya".
"lafiya lau Dr, ya aiki?".
"aiki alhamdulillahi, ya karatu".
"karatu normal".
Shiru muka yi na d’an mintuna kafin yaci gaba da Magana.
"Zarah da fatan kin gama tunanin ki, yanzu amsar ki nake jira".
Cikin jin kunya nace "Nima na amince, Dr nima ina son ka".
"Wow! Zarah, I don’t know how to show my happiness to you, na ji dad’i, Allah ya barmu tare".
"Amin Dr".
Haka ya dinga ci gaba da fad’a min irin son da yake min, ban cika bashi amsa ba, kasancewar rashin sabo da hirar soyayya.
Haka muka yi sallama muna masu shauk’in junan mu.
Yau kusan watan yaya Faruk 5 rabon shi da Kaduna, yanzu ba mu cika had’uwa ba kasancewar ba network a inda suke.
Sai dai wani lokacin Ummu tace ya kira yace a gaishe ni.
A can ‘bangaran yaya Faruk kuwa, tun zuwan su garin Adamawa, basu da wani lokaci kansu, aikin da ya kawo su suke yi na kwantar da tozarmar da ke tsakanin Fulani da Iyamurai da aka samu sa’bani a tsakanin su, wanda hakan ya jawo asara da dama, ciki har da asarar rayuka.
Bai da wani lokacin yin waya ko chat saboda rashin samun lokaci, wani lokacin in da suke zuwa akwai matsalar network a gurin, hakan yasa ba kullum yake kiran gida ba ko ya kira ni.
Duk yadda suke tunanin rikicin mai sauki ne tsakanin Fulani da Iyamurai, abin ya wuce haka.
Sun yi kusan wata uku a can Adamawa, sannan sak’o yazo musu cewa akwai wani course da za a tura su k’asar Uganda wanda za su iya d’aukan 3/4 month a can.
Ko da suka dawo Abuja, bai samu damar zuwa Kaduna ya musu sallama ba saboda dawowar su kawai ake jira su tafi.
Ko da ya kira Daddy ya fad’a mishi, fatan alkhairi ya mishi, amma yaso ganin shi ganin watannin da ya d’iba bai zo ba.
San da ya sanar da Momi, fad’a ta fara yi akan wannan wani irin aiki ne? mutum ace rabon shi da gida kusan wata uku, sannan kuma yana dawowa an k’ara tura shi wata k’asar.
Daddy ne ya dinga lallashin ta yana nuna mata aikin soja ya k’unshi haka, ta mishi addu’a da fatan nasara kawai.
Haka kuwa Momi ta dinga mishi addu’a, ji take yi kamar taje ta ga d’an ta.
Yanzu kusan wata 7 rabon shi da Kaduna, a wannan satin ne suke sa ran dawowa Abuja.
Duk wannan watannin da yaya Faruk yayi a garin Adamawa da Uganda, bai manta dani ba, kullum ina cikin ransa, yana ganin yafi kowa k’osawar su dawo Abuja ya samu a basu hutu su je gida.
Soyayyar mu da Dr ta zama wata irin soyayya da muke gudanar wa mai tafiyar da nishad’i, ba ko wani lokaci yake kira na ba, hakan bai damu na, saboda ina mishi uzurin yanayin aikin shi.
Ba laifi Dr yana bani caring d’in da nake buk’ata a gurin lover d’ina, duk da wani lokacin ina ganin gazawar shi a ‘bangaren hakan, amma ina sa wa a raina cewa in muka yi aure, komai zai daidaita.
Yau bayan mun tashi daga School ne, Ina cikin motar Dr Sadik muna hira, naji waya ta na ruri.
Ganin Anisa ce yasa na d’aga da alamar tsokana nace "Matar yaya Khalil ya aka yi ne".
Dariya tayi tace "Fatima Allah dai ya shirye ki, kina ina ne? gamu a department ni da Driver muna jiran ki".
"Ok ki k’araso gaban department d’in mu, za ki ga wata mota ash colour a gurin, ina cikin motar".
"Ke da waye a cikin motar" tayi saurin tambaya ta.
"Idan kika zo kya gani" abin da nace da ita kenan na katse wayar.
Ba a d’au wasu mintuna ba, sai gata ta k’araso motar.
Ganin ta da nayi yasa na bud’e motar ina murmushi.
"Anisa ga Dr Sadik ku gaisa" na fad’a.
Kallo na tayi kamar za tayi Magana, sai kuma ta juya kallon ta zuwa ga Dr tace
"Ina wuni Dr".
"lfy lau Anisa, ya karatu".
"lfy lau, ya aiki".
"aiki alhamdulillah".
Ita kuwa Anisa mamaki ne ya kama ta, saboda ita a sanin ta, Dr Sadik a asibitin school yake aiki, menene alak’ar shi da Fatima da zai biyo ta Department? duk da tasan sun yi Siwes a asibitin, kuma tasan sun saba da Fatima da Dr, yanzu to zuwan me yake yi gurin ta?
Kamar nasan tunanin da take yi kenan nace "Anisa, wannan shine Dr Sadik, nasan kin gane shi, saboda yana aiki ne a cikin asibitin school, kuma shine my lover".
Na juya kallo na ga Dr nace "Dr Sadik, wannan ita ce Anisa, k’awa ta kuma ‘yar uwa ta".
Dr Sadik ne yace "Ina jin labarin ki Anisa gurin Zarah, ki ci gaba da kular min da ita, saboda ita special queen ce a guri na".
Murmushi Anisa tayi tace "kar ka damu Dr".
Sallama ta mana akan cewa tana jira na a mota.
Dr Sadik ne ya min kallon da ke sani k’ara fad’awa tarkon son shi kana yace "Zarah, bari in tafi, tun da ga Anisa can na jiran ki".
Fitowa nayi daga motar ina waving d’in hannu na.
Anisa tun da ta koma mota take tunanin yaushe na had’u da Dr, me yasa ban fad’a mata ba?
Wannan tunanin ta ci gaba dayi har na k’araso cikin motar.
Mun fara tafiya ne Anisa ta kira suna na.
"Fatimah!
"Anty na ya aka yi ne" na fad’a da alamar tsokana.
"Fatima wai yaushe ku ka fara soyayya da Dr Sadik ne? me ye dalilin ki na k’in fad’a min, bayan kin san ba ma ‘boye wa junan mu sirrin mu, ko da ki ka ga ban fad’a miki soyayya ta da yaya Khalil saboda ba na so yanzu Abbu da Daddy su fara tunkara ta da zancen, kin ga yanzu yaya Khalil sevice yake yi, na fi so sai ya gama service d’in, kin ga lokacin mun kusa gama Diplomar mu, amma ke wace hujja kike da ita? Gaskiya bazan ‘boye miki ba, ban ji dad’in abin da kika yi ba". Anisa ta fad’a da alamar damuwa.
"Sorry Sis, ke ma kin san bazan k’i fad’a miki ba, kawai dai na ga ba mu dad’e dashi bane, shi yasa ban fad’a miki ba, kuma ina ganin nan gaba za ki iya cewa in hak’ura dashi".
Da mamaki Anisa ta kalle ni tace "akan me zan ce ki rabu dashi Fatima, bayan na ga alamun kina son shi, kuma miye aibun shi da zan ce ki rabu dashi? kawai dai kin fad’i ra’ayin ki ne".
A raina cewa nayi "da kinsan yaya Faruk ke so na kafin Dr, da ba ki ce haka ba, kuma ni nasan duk ran da kika san haka, ba za ki bani goyon baya ba akan Dr Sadik".
Saboda mu rabu lafiya da ita yasa nace "yanzu dai ki yi hak’uri Anisa, na amsa laifi na".
Murmushi tayi tace "kar ki damu Fatima, ke ai k’anwa tace tun da kina matsayin k’anwar miji, dole in hak’ura".
Hannu na ba ta muka tafa, muka ci gaba da hira, ina k’ara ba ta labarin Dr Sadik.
Bi na kawai take yi da kallo, tana jinjina irin son da nake yi ma Dr Sadik a d’an wannan lokacin da muka had’u dashi.
Yanzu soyayyar mu muke sha da Dr Sadik ba tare da wata matsala ba, yawanci lokuta yana d’auka na mu jeostrich bakery ya min siyayya.
Akwai lokacin da muka je Ostrich bakery d’in, na za’bar ma Anisa favourite snacks d’in ta da ice cream.
Da na mik’a mata ledar take cewa "Fatima, maimakon ki bari in za mu koma gida sai mu shiga gurin, kin ga yanzu ice cream d’in ruwa zai yi".
"Oh Sorry, ni da Dr Sadik ne muka je gurin ya siya mana".
Anisa kuwa mamaki na take yin a yadda na fara canza halaye na daga had’uwa ta da Dr.
"Fatimah, shawara zan baki, amma kar ki d’auka da wata manufa".
"Ina jin ki Anisa".
"Ki rage bin Dr Sadik yana fita dake, ba wai nace yana da matsala bane, hakan zai sa ya gane u a special, gwara ya siyo ya kawo miki, wani time d’in ki nuna mishi ba ki da buk’atar hakan".
Wani irin kallo na bi ta dashi, saboda ni ban gane me take nufi da hakan ba?
"yanzu ke nan nayi laifi dan mun je Ostrich bakery da Dr Sadik".
"No Fatima, ba wai na ce kin yi laifi ba ne, ina fahimtar dake halin maza ne, ki iya takun ki, kuma ai nasan Ostrich bakery da poly ba nisa, tun da tsallaka titi ne, ina nuna miki yanayin high institution ne, kin ga sometimes yana zuwa department d’in ku, yanzu in wani wanda yasan ki, ya gan ki a gurin bakery d’in ya fad’a ma wani, za a iya canza muku manufa, yanzu duniyar nan mutum ake kiwo ba dabba ba, da fatan kin fahimce ni".
Jiki na ne yayi sanyi da maganar da Anisa ta fad’a min, nima nasan gaskiya ta fad’a min.
Don haka nace "Anisa na fahimce ki, zan kuma kiyaye".
Yawwa k’anwata ta fad’a da alamar tsokana.
Hararar wasa na mata muka canza hirar.
Yanzu abin da yafi damu na shine yadda Dr Sadik ya matsa min akan yana so ya nemi izini gurin su Abbu, saboda yana so a san dashi a family d’in.
Hak’uri na bashi akan yayi hak’uri ba yanzu zan bashi damar ya fara zuwa gidan mu zance ba, ba kuma yanzu zan gabatar dashi gurin su Abbu ba.
Wannan kara da alama ba zai hak’ura ba, ganin yadda ya taso min cikin fad’a yace "Zarah, look, gwara ki fito ki fad’a min hujjar ki da ba kya so in fara zuwa gidan ku, na gaji da yadda kike kawo min excuse d’in ki in na miki magana, tell me what do you mean?".
Cikin salon lallashi na fara bashi hakuri "Dr ka fahimce ni, nima na fi so ka zo gida akan department d’in da kake zuwa, insha Allah zan fad’a ma Ummu zancen ka, sai ta fad’a ma Abbu, in yaso sai ka fara zuwa, sorry Dr na" na fad’a kamar zan yi kuka.
K’asaitaccen murmushi yayi yace "Na fahimce ki Zarah, sorry in na "ba ta miki rai".
Girgiza kai nayi na ce "ya wuce Dr".
A raina kuwa ban ji dad’in yadda ya min fad’a ba, ban san me yasa na kasa nuna mishi hakan a fuska ta ba, nasan ba komai yasa haka ba illa son da nake mai.
Ci gaba yayi da ja na da hira, ina bashi amsa amma ba kamar yadda muke hira a lokuta da dama ba.
Watak’ila fahimtar hakan da yayi ne yasa ya min sallama ya tafi.
[4/29, 22:32] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
_Alhamdulillahi ala kulli hal_.
*QUESTION OF THE DAY*
_Qoramun(kogi) Aljannah guda nawa ne? lissafo sunayen su_
51&52
Tun da na koma gida na rasa sukuni akan sa’banin da muka samu da Dr Sadik.
Ni kaina nafi so yazo gida su Abbu da Ummu su san dashi, sai dai ba ni da wannan damar, tsora na shine idan wataran su ka had’u da yaya Aminu, zai iya fallasa sirrin da nake ‘boye wa tsakani na da yaya Faruk, hakan na nufin rashin amintar su da Dr Sadik kenan.
Jiki na yana bani cewa yaya Aminu yasan abin da ke tsakanin mu da yaya Faruk, idan nayi duba da amincin su, ba sa ‘boye wa junan su sirrin su.
Hakan na nufin dole in iya taku na dan ba na son kowa yasan tsakanin mu da yaya Faruk har sai ya dawo na bashi hak’uri, sannan in samu damar gabatar da Dr Sadik a matsayin wanda nake so.
Ya kamata na nemo ma kaina mafita saboda kar Dr Sadik ya d’auka da wata manufa a guri na da na hana shi zuwa gidan mu.
Kira ne ya shigo waya ta, mumban k’asar waje na gani, nasan ba kowa zai kira ni da wannan number ba sai yaya Faruk.
Nayi mamakin ganin kiran shi a wannan time d’in kasancewar mun kwana biyu bai kira ni ba kuma ba mu had’u a chat ba.
Jiki na a sanyaye na yi picking d’in call d’in.
Sallama na mishi ya amsa.
"Teemah na" abin da ya fad’a kenan.
Ban amsa kiran da ya min ba illah cewa da nayi "yaya Faruk ina wuni, ya aiki".
"lfy lau, ya su Ummu".
"Suna nan lafiya".
"Ya studies?" ya tambaye ni.
"karatu alhamdulillah".
"Nasan yanzu kun shiga ND 2 ko? ya tambaye ni.
" Eh yaya har mun yi nisa".
"To Allah ya taimaka".
"Amin yaya Faruk".
Teemah kin ji ni shiru ba na kiran ki, gashi ba ma had’uwa a chat, ba na samun zama ne, da ina sa ran a week d’in nan za mu dawo, amma ina ganin sai mun kai next month za mu dawo, nima na k’osa in dawo in ga kyakkyawar fuskar ‘yar k’anwa ta, in ga ko tayi missing d’ina".
Murmushin jin dad’i nayi don a gaskiya, nasan yaya Faruk ya damu dani, alamomi da yawa sun nuna min hakan.
"Allah ya dawo daku lafiya".
"Amin Teemah nah, na gode da addu’ar ki, bari in barki haka, sai kin sake ji na".
Sallama ya min ya katse wayar.
A zuciya ta kuwa fargabar dawowar yaya Faruk nake yi, nasan cikin biyu za ayi d’aya, ko dai ya hak’ura dani idan na fad’a mishi ina da wanda nake so, ko kuma ya bijire ma buk’ata ta saboda ni kaina nasan yaya Faruk ba k’aramin so yake min ba.
Yau ma kamar kullum, ni da Dr Sadik ne a cikin mota muna hira irin ta masoya, Tsayuwar Anisa muka gani a gaban mu tana murmushi.
Gaisawa suka yi da Dr kana ta juya kallon ta gare ni tace "Tun da naga motar Dr, nasan kuna tare, shi yasa ban wahalar da kaina gurin kiran ki ba, na k’araso".
"Kun gama lectures ne" na tambaye ta.
"Eh mun gama, ni yanzu zan tafi gida, yau b azan tsaya jiran driver ba, tun da yaya Khalil ba ya gari".
"Ok in kin je gida kya gaida su Momi da Dadi, ki ce ma Driver ba sai yazo ba, zan dawo da kaina".
"Za su ji, zan fad’a mishi".
Duk wannan zancen da suke yi, Dr bai sa musu baki ba, sai a yanzu yace "Anisa in ba damuwa, ina son yin Magana dake".
Gaba d’aya maida kallon mu gare shi muka yi don sauraren mai ze ce.
Murmushi tayi tace "Ba damuwa Dr ina jin ka".
"A gida ba a barin ku kuna kula samari ne?" tambayar da ya Dr ya fara yi ma Anisa kenan.
"Me ka gani Dr? ita ma ta jefa mishi wata tambayar ba tare da ta amsa mishi ba.
"Naso ki amsa min tambayata ta farko, amma sai ki kamin halin ‘yan nijah ki ka sake jefa min tambaya akan wadda na miki, abin da yasa na tambaye ki shine yadda Zarah tak’i bani damar gabatar da kaina a gurin parents d’in ta, beside ni ba na son abin da zai zubar min da girma na, kin ga yawancin students sun san ni, so yanzu sai ki ga an fara wa mutum wata fassara ta daban, amma ita naga hakan kamar bai dame ta ba, ina so ki mata Magana, may be za ta fi d’aukar zancen ki da mahimmanci".
Anisa kuwa tambayar da ta fara yi ma kan ta shine "Menene dalilin da yasa ba na son gabatar da Dr a gida? Duk kuwa lurar da tayi ina son shi".
"kayi hak’uri Dr, zan mata Magana inshaAllah".
Duk wannan maganar da suke yi ban ce komai ba, kamar ba na gurin.
Anisa ce ta mana sallama ta tafi.
Gaskiya yau Dr ya ‘bata min rai, ban so ya tunkari Anisa da wannan maganar ba, saboda ba na so Anisa tayi zargin ko ta kawo wani abu a ranta akan k’in gabatar da Dr da ban yi ba a gida.
Bayan tafiyar Anisa ne na kalli Dr cikin damuwa na ce "Dr!
D’agowa yayi ya kalle ni ba tare da ya amsa kiran da na mishi ba.
Ban damu da amsawar shi ba naci gaba da cewa "Sadik, ban ji dad’i ba da ka fad’a ma Anisa halin da muke ciki, ba wai dan ban yi trusting d’in ta ba, na fi so in kammala wani shiri ne Kafin in tunkare su da zancen ka".
Wayar shi yake pressing kamar ba dashi nake Magana ba, ga dukkan alamu, bai damu da yadda na nuna ‘bacin raina ba.
"shiri? Wane irin shiri ne haka da zai hana ki gabatar dani a gidan ku".
Ka k’ara hak’uri Sadik, komai ya kusa zuwa k’arshe".
Wannan karan cikin ‘bacin rai ya fara Magana "look Zarah, ina ganin haka za mu ci gaba da tafiya, to bai da wani amfani, na baki yau ki yi tunani akan wannan maganar, in ba haka ba ni zan samar mana mafita".
Wani irin sanyi jiki na yayi, yadda Dr yake fad’a min maganar da ranshi yake so, abin takaici shine na kasa nuna masa ‘bacin raina, duk kuwa da yadda maganar ta min zafi a raina.
Sai kace ba Fatima ba da ba na bari a fad’a min mai zafi ba tare da na rama ba?
Sai yanzu na yarda da Hausawa ke cewa *SO HANA GANIN LAIFI*.
"Zan tafi" Dr Sadik ya fad’a.
Jiki na kamar ba nawa ba, na fito daga motar.
"Sai an jima" na fad’a a sanyaye.
"Take care" ya fad’a a gajarce, kana ya figi motar a guje ya bar department d’in mu.
Ko da muka class, jiki na duk a sanyaye yake, wanda yasa har Halima ta tambaye ni dalilin canzawa ta.
Sanin ba ni da wani gamsashshiyar amsar da zan ba ta yasa, nace mata ba na jin dad’in jiki na ne.
Cikin kulawa ta min fatan samun sauk’i.
Ko da na koma gida, damuwa ce ta addabe ni ganin yau mun rabu da Dr Sadik cikin ‘bacin rai, babban abin da yafi d’aga min hankali shine yadda na ga Dr Sadik ya d’au zafi a yau.
Haka nayi ta tunanin halin da Dr yake ciki a yanzu, ganin ba irin sallamar da muka saba yi dashi muka yi ba.
A haka Ummu tazo ta same ni tana tambaya ta me yake damuna.
Nasan Ummu na da saurin fahimtar halin da nake ciki yasa na yi murmushin da bai kai ciki ba, na ce mata ba na jin dad’in jiki na ne.
Kallo na Ummu tayi kamar mai son gano wani abu, ganin haka ne yasa na tsargu na mik’e nace "Ummu bari in je in kwanta".
"Allah ya k’ara sauk’i" Ummu ta fad’a tana bi na da kallo.
Ni da na tafi d’aki da niyyar in samu hutu da tunanin dake addabar zuciya ta, sai gashi ina kwantawa barcin gaske ya d’auke ni.
Ba ni na farka ba sai da naji Anisa ta d’aka min duka a jiki.
A firgice na tashi ina waige-waige kamar wadda take neman wani abu.
Anisa ce ta koma gefe tana ta kwasar dariya ganin yadda nayi.
"Ba ki da abin yi ne yasa ki ke kwasar wannan dariyar". abin da nace mata kenan.
Ban k’ara bi ta kanta ba, na wuce bathroom da niyyar yin alwala, ganin yadda lokacin sallah ya wuce ina bacci.
Ko da na fito, samun ta nayi tana waya da yaya Khalil.
Sallaya na shimfid’a na ta da sallah, har na idar da sallah ba ta gama wayar da take yi ba.
Mik’ewa nayi da niyyar barin d’akin, saboda ban san lokacin da za ta gama wayar ba.
Har na kusa kaiwa bakin k’ofa naji ta kira suna na.
Juyowa nayi na kalle ta, katse wayar tayi ta ce "Fatima ki dawo ki zauna, akwai maganar da za muyi".
Ban musa mata ba na dawo na zauna a gefen gado.
"Ina jin ki" na ce da ita.
Anisa ce ta ce "Fatima, ki yi hak’uri da abin da zance miki, wata k’ila maganar ba za ta miki dad’i ba".
Anisa taci gaba da cewa "Fatima kin canza".
Da sauri na katse ta "Kamar ya na canza?".
"Fatima ki bari in gama maganar da zanyi sannan ki yi challenging d’ina, a da nasan ke ba kya ‘boye min komai naki, amma yanzu na lura ba kya son in san halin da kike ciki, ni bance ki dinga fad’a min komai naki ba, saboda ko wani mutum yana son sirri a rayuwar shi, yanzu na fara sa wa a raina cewa akwai abin da kike ‘boye min, na farko kin ga ba ki fad’a min alak’ar ki da Dr Sadik ba sai da Allah yayi naje department d’in ku, sannan ki ka fad’a min, da na miki Magana sai ki ka kawo min excuse d’in ki, na bar zancen, na biyu shine ban san hujjar ki ban a k’in ba Dr damar yazo gida su Abbu su san dashi, bayan nasan cewa in akwai dalilin ki nayin haka za ki fad’a min, shima ba ki fad’a min ba sai da Dr ya tare ni da zancen".
Tsayawa tayi da min magana tana tunanin ko zan ce wani abu, amma ban yi Magana ba.
"Fatima hakan ya tabbatar min kenan da abin da kike ‘boyewa wanda ba kya so in sani, in ba haka ba nasan ba za ki tsiri ‘boye-‘boye ba".
Ban so Anisa ta d’au zancen a haka ba, duk abin da zan fad’a ma ta zai zama k’arya, tun da b azan fito in fad’a ma ta alak’a ta da yaya Faruk ba ne yasa na dakatar da Sadik zuwa gidan mu, ba kuma na so ta ci gaba da sa zargi a ranta.
"Anisa ni fa ba ni da wani dalili da yasa ban ba Sadik damar zuwa gidan mu ba, kawai dai ina ganin kamar ba mu wani dad’e ba, shi yasa".
"Wannan ba hujjah bace, in dai kin san ba wani dalili to ki barshi ya fara zuwa zancen a gida, instead of ya dinga zuwa department d’in ku, wasu su fara muku wata fassara ta daban". Anisa ta fad’a.
Gaskiya ne da Hausawa ke cewa "Mai shawara aikin sa ba ya ‘baci" yanzu gashi d’an maganar nan da muka yi da Anisa yasa na samu relief akan tunanin da suka min dabaibayi, abin da yasa bazan nemi shawarar ta ba akan yaya Faruk da Dr Sadik, na san yayan ta za ta ba ni shawarar in za’ba, gwara dai in bar abin a raina har lokacin da komai zai zo k’arshe.
"Insha Allahu zan fad’a mishi ya fara zuwa gidan"
"hakan dai yafi".
Narai-narai da ido nayi kamar zan yi kuka nace ‘Anisa ba zan ‘boye miki ba, ina son Dr Sadik, hakan yasa ba na so in ga na ‘ba ta mishi ranshi wanda zai jawo yayi fushi da ni, yanzu haka ban san me yake min dad’i ba saboda mun samu misunderstanding dashi akan wannan maganar, Anisa ki ba ni shawara".
"Wannan wani irin so ne, Fatima take yi na Dr?" Anisa ta tambayi kanta.
"Fatima, gaskiya ya kamata ki gane ke mace ce mai class, ba wai ina zuga ki ba ne, ina so kin san mace aka sani da jan aji, kar ki bari namiji ya gano irin son da kike mishi, hakan zai sa ya raina ki, ko ya samu damar juya ki, ba wai ina nufin kar ki nuna mishi irin son da kike mai ba, a harkar soyayya yana da kyau idan d’aya ya ‘ba ta ma d’aya rai yasan cewa shine da laifi, amma ba wai ya zamana mutum d’aya shi zai dinga amsar laifin da ba shi ya aikata ba, sorry to say Fatima, son da kike ma Dr ya fara wuce limit, saboda na ga hakan a tare da ke, ya kamata ki dawo hanya, ki kuma yi karatun ta natsu, ba komai nake guje miki ba, sai dan kar ki fad’a *MAKAUNIYAR SOYAYYA*, shawarar da zan ba ki shine ki tura mai text ko kira shi a waya akan cewa kin amince ya fara zuwa gida zancen, ina ganin zai daina fushin da yake yi dake ko Zarah" ta k’arashe zancen da alamar tsokana.
Murmushi nayi saboda nasan tana tsokana ne da sunan da Sadik yake kira na.
"Na gode da shawarar ki Anisa, ba abin da zance miki sai godiya, kuma zan yi k’ok’arin gyarawa".
"Kar ki damu Fatima, matsalar ki, matsala ta ce".
Hira muka ci gaba da yi da Anisa, sai wajen yamma sannan Anisa ta tashi ta tafi gida.
Shawarar ta na d’auka na tura ma Sadik text akan cewa na amince ya fara zuwa gidan mu.
Ran da ya fara zuwa gidan mu na gabatar dashi gurin Abbu, sun gaisa da Abbu cikin mutunta juna.
Tun daga sannan jefi-jefi Dr Sadik yake zuwa gidan mu, mafi lokacin zuwan shi ran weekend.
Haka muke ta gudanar da soyayyar mu da Dr Sadik.
Yau bayan na dawo daga makaranta, Ummu ke sanar dani Hajiyan wagini (mahaifiyar su Abbu) tazo tana gidan su Anisa, murna da tsalle haka na dinga yi, saboda mun kwana biyu ba mu je wagini ba, ita kuma ta na dad’e wa, bata zo ba.
Ko abincin ban tsaya ci ba, ina watsa ruwa na canza kaya na fito, na tafi shashin Ummu.
"Sai ina?" Ummu ta tambaye ni.
Dariya nayi nace "sai wajen waccen tsohuwar za ni, ba zan iya jiran ta tazo nan gidan ba, gwara in je in ganta".
"In kin je kya gaishe su, in Abbun ku ya dawo za mu je mu mata sannu da zuwa".
"To Ummu sai na dawo".
"Sai kin dawo Auta".
Saboda yadda na k’osa in kai gidan, ban tafi a k’asa ba, na tari keke napep na hau.
Ina shiga gidan na same su a falo suna zaune.
Sallama nayi da guda na fad’a jikin Hajiya na k’ank’ame ta.
Anisa ce ta amsa sallamar ta na dariya.
Sai a lokacin na lura da Momi dake zaune a d’aya daga cikin kujerun dake girke a falon, na gaishe ta.
Amsa min tayi ta na murmushi.
Ture ni daga jikin ta tayi tana dariya tace "Ja’ira za ki k’arasa ni ne, dama yanzu mu ka gama yi da Anisa".
"Kai Hajiya mun yi missing d’in ki ne fa, shine za ki gwasale mu".
"Ke raba ni da yaren nasaran nan naku, za ki wan ice kun yi misin ko musin d’ina ne oho miki".
Dariya muka kwashe da ita ni da Anisa.
"Ja’irai ni kuke ma dariya, bari iyayen ku su zo zan fad’a musu shak’iyancin da ku ke min".
Anisa ce cikin dariya tace "Sorry Kakus, ba za mu sake ba".
Yamutsa fuska tayi tace "Abin naku gaba yake yi, har da sauro ku ke had’a ni dashi".
Sake fashe wa da dariya muka yi, ni kuwa har da rik’e ciki.
Haka muka dinga wasa da dariya da Hajiyan wagini, sai da yamma na mik’e da niyyar tafiya.
Momi ce tasa Driver ya maida ni gida.
Da daddare su Abbu da Ummu da za su gaida Hajiyan wagini na sake bin su, saboda muna shiri da ita sosai.
San da muka je gidan su Anisa, haka aka had’u a falon Dadi ana ta hira, da wasa da dariya.
Sai wajen k’arfe tara na dare muka baro gidan.
Hajiyan wagini sai da tayi kwana uku a gidan su Anisa sannan ta tawo gidan mu, tun da tazo na tare a d’akin ta, wani lokacin Anisa na zuwa a sha hira da ita.
Yau ta kasance ranar jumma’ a, ba mu da wani lectures da yawa, hakan yasa na dawo gida da wuri.
Ina dawo wa, na wuce d’akin Hajiyan wagini zaune akan carpet tana cin farfesun kaji.
Zama nayi kusa da ita ina cewa "Kai Hajiyan wagini, an samu dad’i ko Magana ba a iya yi, tun da ba za a min tayi ba bari in wa kaina".
Duk wannan maganar da nake yi Hajiyan wagini ba ta ce min komai ba, sai ma ci gaba da tayi da cin naman ta.
Hannu na saka a cikin plate d’in na d’auki yanka d’aya daga ciki na sa a baki na.
"gaskiya Hajiya dole ba za ki yi magana ba, wannan delicious haka".
Harara ta tayi tace "wannan bature bai kyauta ba, a ce mutum yana d’an bahaushe gaba da baya, in zai yi Magana sai ya had’a da harshen nasara".
"Kai Hajiyan wagini, yanzu zamani ya canza, mun riga da mun sa ba da wasu kalmomin da turanci, idan za muyi Magana sai mun had’a dashi".
"wannan bature dai ya nace mutane".
Dariya nayi nace "Hajiya kenan".
Kallo na tayi tace "Ke Fatima kina da number Soja ki nemo min shi mu gaisa".
A gaskiya bazan iya kiran yaya Faruk ba a gaban Hajiyan wagini, nasan za ta iya fahimtar wani abu, saboda nasan zai yi wuya in kira shi ba tare da ya fad’a min wata kalma da ta k’unshi so ba, ko in kira ta ya fad’a ma ta abin da ke tsakanin mu, nasan kuwa Hajiya sai tafi kowa murnar da wannan zancen, dan haka nace "Ba ni da ita, nima idan ya kira Abbu ko Ummu ne muke gaisawa".
Hajiyan wagini ce ta ci gaba da cewa "Allah sarki Mai gida na nakai na, Allah ya dawo dakai lafiya ka fito da mata mu sha biki".
Ganin Hajiya ta d’akko zancen yaya Faruk yasa na mik’e, don nasan ba ta gajiya da zancen shi.
Tafiya na fara yi ina cewa "Ni dai bari in je in huta, yanzu in kika fara min maganar shi, ba gajiya za ki yi ba".
"To ‘yar nema, da ma nasan ai ba zama za ki yi ba, tun da kin ji an ambaci wanda ba kwa shiri, dole ki tafi".
"Ni dai kin ga tafiya ta Hajiya" na fice daga d’akin.
Ran lahadi muna zaune ni da Dr a gurin shak’atar dake gidan mu, motar yaya Aminu ce na ga ta shigo gidan.
Gaba na ne yayi wani irin buga wa, nasan idan har yaya Aminu yasan me ke tsakanin mu da yaya Faruk, ba k’aramin ‘bata min zai yi ba, ko ya fad’a ma su Abbu abin da ke tsakanin mu da yaya Faruk, nasan kuwa zan fuskanci hukunci gurin Abbu.
Parking yayi a gurin parking space, Shi da Anty jidda ne da su Humaira da Nabil suka fito daga motar.
Su Humaira ne da Nabil suka rugo da gudu gurin da muke, yayin da Anty Jiddah da yaya Aminu suka shige cikin gida.
Bud’e musu hannu nayi suka fad’a jiki na suna dariya.
Murmushi Dr Sadik yayi yace "wannan yaran waye Zarah"
"yaran brother d’ina ne, yaya Aminu" na bashi amsa.
"ku zo mu gaisa, ko sai Antin ku kawai ku ka sani".
Humaira ce ta tawo gurin shi, shi kuwa Nabil k’ara mannewa yayi a jiki na, alamar ba za shi ba.
San da Dr Sadik za tafi, kud’i ya bani a siya ma su Humaira su chocolate.
Ko da na amshi kud’in, tunanin w azan ba tsakanin yaya Aminu da Anty Jidda nake yi, nasan dukkan su in suka sa tsakanina da Dr Sadik, ba za su yi wani murna da kyautar da ya yi musu ba, zuciya ta tafi kwanciya akan in ba Anti Jidda, nasan ita ba ta da wata matsala.
Godiya na mishi, kana muka yi sallama ya shiga motar shi ya tafi, ni kuma na rik’e hannun su Nabil muka nufi cikin gida.
Ina shiga cikin parlour d’in, na ga ba kowa, nasan ba za su wuce suna d’akin Hajiyan wagini ba, hakan yasa na nufi d’akin.
Sallama na musu na nemi kusa da Anti Jiddah na zauna, na gaishe ta.
Cikin Magana k’asa-k’asa tace "Fatima wanene wanda na gan ku a tare, ko da yake mu bar maganar, zan zo d’akin ki mu yi maganar, yanzu ki tashi ki je, yayan ki na neman ki, yace ki same shi a garden".
Jiki na ne ya min nauyi, nasan kiran da yaya Aminu ya min na nufin zai min magana ne akan Dr Sadik, ko kuma akan yaya Faruk.
Tashi nayi na nufi garden d’in don in ji mai yaya Aminu zai ce min.
*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
_Allahumma innaka afuwun karimun tuhibbun afuwa fa afu anna, wagafirlana, warahamna, anta maulana fansurna alal qaumiz zalimin_
🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽
*Wanda suka yi k’ok’arin ba da amsar question of the day su ne*
*Meeynah (Princess of question of the day)*
*Ramlah*
*Allah ya saka muku da alkhairi da irin k’ok’arin da kuke yi*
*Amsar tambayar ita ce: A cikin Aljannah akwai Qoramu (kogi) guda bakwai*
Kogin ruwa
Kogin Madara
Kogin ruwan zuma
Kogin ruwan giya (sharabun Tahoorun)
Kogin Kafoor
Kogin Zanjabeel
Kogin Tasneem
*TUNATARWA*
_MAGANGANUN MANZO (S.A.W)_
_Yace_:
_mafi girman Haske (ilimi)_
_Mafi girman duhu (jahilci)_
_Mafi girman kyauta (afuwa)_
_Mafi munin zance (K'arya)_
_Mafi kyawun zance (gaskiya)_
_Mafi kusantuwar al’amari (tashin alqiyama)_
_Ya ku muminai, mu yi amfani da lafiyar mu da lokacin mu da dukiyar mu kafin mutuwa tazo mana_
53&54
San da na isa garden d’in, samun shi nayi a garden da jaridar Daily trust a hannun shi yana karantawa.
Sallama na mishi kana na gaishe shi.
Ciki-ciki ya amsa sallamar da na mishi da gaisuwar.
Ci gaba yayi da karatun shi kamar bai san da tsayuwa ta a gurin ba.
Ajiye jaridar yayi ya kalleni ya ce min "Fatima zauna ina da Magana da ke".
Jiki na a sanyaye na nemi d’aya daga cikin kujerun na zauna.
"Wane ne wannan da na gan ku a tare ya zo gurin ki?". Tambayar da ya fara jefo min kenan.
"Sunan shi Dr Sadik" na bashi amsa.
"Ba sunan shi na tambaya ba, me yazo yi gurin ki" ya k’ara jefo min wata tambayar.
"A asibitin school d’in mu yake aiki, muna mutunci ne dashi tun lokacin da nayi Siwes a asibitin".
Wani irin kallo ya min sannan yace "Duk mutuncin bai isa a makarantar ku ba, sai ya zo gidan ku?".
Wannan karan ban bashi amsa ba saboda ban san me zan ce mai ba.
Ganin haka yasa yaci gaba da cewa "Fatima na ga kan ki na rawa, zan yi mummunan sa’ba miki, in ma wani abun yak e kawo shi gidan nan ki fad’a mishi ki na da wanda yake son ki kuma shi za ki aura".
Da sauri na d’ago na kalle shi jin har ya yanken hukuncin wai yaya Faruk zan aura.
Ci gaba yayi da cewa "ko an fad’a miki ban san me ke tsakanin ki da Faruk ba ne? abin da yasa ki ka ga ban ma su Abbu Magana ba, saboda Faruk d’in yace min ya kusa dawowa, amma da tuntuni sun san da maganar, Na ga take-taken ki yana nufin ba ki amince da Faruk ba, wannan ne kuma ba ki isa ba, in kin k’aryata kuma ki gwada ki gani".
Tashi yayi ya bar gurin ba tare da ya jira jin amsa ta ba.
Wasu hawaye ne suka zubo min masu matuk’ar zafi, wanda ni kaina ban san dalilin zubar hawayen ba.
Tun a yanzu kenan na fara fuskantar k’alubale game da soyayya ta da Dr Sadik a dalilin yaya Faruk, ina ga in su Ummu da Abbu in su ka ji gaskiyar maganar cewa
Faruk ne ke so na? nasan ko me zan yi Abbu ba zai barni da Dr Sadik ba.
Haka na jawo k’afa ta na shiga cikin gida.
D’aki na wuce, na zauna akan kujerar dressing mirrow ina ci gaba da tunanin hanyar da zan bi in warware komai cikin sauk’i ba tare na ‘bata ma kowa rai ba.
Addu’a ta d’aya ita ce Allah yasa yaya Faruk ya dawo in fad’a mishi abin da ke raina, nasan shi zai fi fahimta ta akn kowa, duk da nasan ba k’aramin matsala zan janyo a familin ba ganin yadda ake zaman mutunci da kuma zumunci, wannan ina gani shine mafita a gare ni.
Shigowar Anti Jiddah ne yasa na k’ak’alo murmushin yak’e saboda ba na so ta gano halin da nake ciki.
Gefen gado ta samu ta zauna tana bi na da kallo.
"ya aka yi ne Fatima?" ta tambaye ni.
"Ba komai Anti" na ba ta amsa.
Ban son ta k’ara jefo min wata tambayar yasa na ce "Ina su Humaira ne?"
"Suna gurin Hajiyan Wagini".
Ku’din da Dr Sadik ya ba ni in basu na d’auka na mik’a mata.
Bin kud’in tayi da kallo alamar tana buk’atar k’arin bayani.
Dariya nayi nace "ki amsa mana Anti Jidda, sai in miki bayani".
Murmushi tayi ta amshi kud’in tayi godiya.
"Dr Sadik ne ya bani yace in ba Su Humaira da Nabil a sai musu chocolate".
"Waye Dr Sadik? ta tambaye ni.
"wanda ki ka ganni dashi d’azun" na bata amsa a gajarce.
"Ko shine surukin mu?" ta fad’a da alamar tsokana.
Wannan karan ban ba ta amsa ba, sai mumushi da nayi.
Hakan yasa ta fahimta shirun da nayi me yake nufi.
"Allah ya za’ba mafi alkhairi".
"Amin Anty Jiddah".
"Amma sai naji Dadin su Humaira kamar ya ce min Faruk ke son ki?" ta k’arashe maganar da min kallon tuhuma.
Sanin Anty Jiddah ta riga tasan maganar, gwara in fito in fad’a mata abin da yake raina, wata k’ila ta samo min mafita.
Don haka nace mata "Eh shi yace yana so na, amma ni ai har yanzu ban ce mai ina son shi ba, kuma ni maganar gaskiya Dr Sadik nake so".
Kallon mamaki Anty Jiddah ta bi ni dashi, kamar ba za tace min komai ba, can ta d’aura da cewa "Fatima, nasan so daga Allah ne, shi yake sa ka wa mutum ba tare da yayi shawara dashi ba, amma wani lokacin mutum na iya sa son mutum a ranshi, ba wai nag a laifin kid an kin so Dr Sadik ba ne, sai dai ina duba miki wanda yafi dacewa da rayuwar ki, duk da ban san halin Dr Sadik ba, amma nasan ba wanda zai so ki da gaskiya ya kuma rik’e ki da amana irin Faruk, samun a Faruk a gurin ki ba k’aramin riba bace a gurin ki saboda yana duk wani qualities da mace za taso a gurin namiji, ba ki kyauta ma Faruk ba da tun farko ba ki fito kin fad’a mishi ya hak’ura ba, sai yanzu da ki ga kin samu wanda kike so, ni dai shawarar da zan baki shine ki rik’e Faruk a matsayin masoyin ki da kuma farin cikin su Ummu da za ki duba in har suka san da zancen nan.
Ta ci gaba da cewa "mu dai muna bayan Faruk, ba za mu bari aka da Faruk a fagen soyayyar ba kamar yadda bai fad’i ba a fagen yak’i ba" ta k’arashe zancen tana dariya.
Da alama ni zan sha k’asa, yanzu ma gashi Anty Jiddah tana bayan yaya Faruk, ga d’azun yaya Aminu y agama min fad’a akan shi, ina ga su Anisa da yaya Khalil, bare aje ga su Abbu da Ummu, nasan in da zan samu sassauci shine ta ‘bangaren Dadi, nasan ko Momi bayan d’an ta za ta bi.
Cikin raunin murya na ci gaba da cewa "Anty Jiddah, tun kafin in had’u da Dr Sadik nake ta k’ok’arin in ga nasa son yaya Faruk a raina, amma hakan ya faskara, har yanzu ina ganin yaya Faruk a matsayin yaya ne a guri na, ba wai matsayin masoyi ba, ni ba zan iya nuna mishi ina son shi ba, alhalin ba haka yake a raina ba, hakan ya zama yaudara kuma daga baya zai ji haushi na akan haka, shi yasa na yanke shawarar in ya dawo in fito in fad’a mishi abin da yake raina game dashi".
Da sauri Anti Jiddah ta katse ni da cewa "wace yaudara? ai Fatima kin riga kin yaudari Faruk, me yasa tun a lokacin da ya fad’a miki yana son ki ba ki fito kin fad’a mishi gaskiyar yayi hak’uri dake ba, sai yanzu da yayi nisa da son ki sannan za ki zo mishi da wannan maganar taki mara ma’ana, in har kika mishi haka ba ki mishi adalci ba".
Tana gama fad’ar haka ta taso ta tawo guri na, dafa kafad’a ta tayi tace "Fatima, *KUSKURE D’AYA TAK*zai iya jawo miki danasani mara iyaka, ki yi nazari kafin ki yanke hukunci, ba ri in k’arasa gurin Ummu".
Tana gama fad’ar haka ta bar d’akin.
"Allah gani gare ka, ka kawo min komai da sauki" abin da na rok’a gurin Allah.
Ban sake fito wa falo ba sai da Anty Jiddah za su tafi na fito in musu rakiya gurin motar su, yanda na lura yaya Aminu sai harara ta yake yi.
Hajiyan Wagini sai da tayi kwana uku a gidan mu sannan ta koma gidan su Anisa wanda za ta tafi a washegarin ranar, ganin ranar da za ta tafi ya kasance ranar Friday yasa muka ce za mu bi ta, in yaso sai Driver yazo ya d’auke mu.
Ran jumma’a ina dawowa daga school na had’a kaya na a d’an kit, na tafi gidan su Anisa, nayi ma Ummu sallama, dama mun riga munyi sallama da Abbu da safe.
Ban wani dad’e a gidan ba, muka nufi hanyar Wagini.
Tun da muka je Wagini, muka dinga zagaye ‘yan uwa, in mun dawo mu zauna da Hajiyan Wagini, d’an kwanakin da muka yi a garin kamar kar mu dawo.
Kwanan mu biyu a garin, Dadi ya turo Driver yazo ya d’auke mu.
Haka muka yi sallama da Hajiyan wagini muka dawo Kaduna garin gwamna.
Yaya Khalil yana zuwa Kaduna lokaci-lokaci kasancewar a Jigawa yake yin service d’in shi.
Yanzu soyayayyar yaya Khalil da Anisa ta mamaye dangi, kowa yasan da zancen, yanzu ni ake jira in wa Dr Aminu Magana ya turo da iyayen shi.
Hausawa suka ce duk nisan gagri zai waye, hakan yake, domin a yau ne yaya Faruk ya dawo daga k’asar Uganda zuwa Birinin tarayya Abuja.
Murnar shi ta koma ciki jin cewa sai sun k’ara sati d’aya a Abuja kafin a ba su damar zuwa gida.
Waya yayi ma Dadi cewa sun dawo, amma ba zai samu zuwa ba sai next week, fatan alkhairi Dadi ya mishi kana suka yi sallama.
Yau ya shirya da niyar zuwa gidan su Mus’ab saboda ya dad’e bai je ya gaida Hajiyan su ba.
Block d’in su Mus’ab ya tafi.
San da yaje ya na ta knocking amma ba a bud’e mishi ba.
Wayar shi ya d’auka yayi dialling number d’in Mus’ab d’in.
Ringing biyu tayi kafin a d’auka.
"Assalamu alaikum, Allah ya ja da ran Bregadier na Teemah" abin da Mus’ab ya fara fad’a kenan.
"wa’alaikumus salam, kana ina ne?" yaya Faruk ya tambaye shi.
"Ina gida, ya aka yi ne?".
K’aramin tsaki yayi kana yace "shine ina tsaye tuntuni ina knocking, kai da Maryam an rasa mai zuwa ya bud’e min".
"Ka mana uzuri, ba ma falo ne, kuma kasan dai ma’aurata in aka zo aka ji shiru ana musu uzuri, gani nan zuwa in bud’e maka".
Murmushi kawai yayi saboda yasan halin Mus’ab idan ya biye mai, sai ya yanko wani zancen na daban.
Katse wayar yayi ya zauna a kujerar da ke balcony.
Mus’ab ne cikin tsadadden yadi kalar ruwan toka, bud’e k’ofar yayi yana murmushi.
"Tuba muke yi Bregadier Umar Faruk’ Mus’ab ya fad’a yana dariya.
"Mus’ab ban san ran da za ka girma ba".
"Ran da maryam ta haifo babyn ta ranar zan girma".
Girgiza kai yaya Faruk yayi yace "Zuwa nayi ka raka ni wata unguwa".
"In fita ina? kana ganin tsawon lokacin da muka d’iba ba ma nan, Maryam tayi missing d’ina, nima haka, sai dai ko zuwa anjima sai in zo mu tafi".
"yanzu zaka raka ni ko in tafi?" yaya Faruk ya tambaye shi.
"zan raka ka amma sai anjima, dan saboda kaine ma yasa na fito, ina jin yau ko sallah a d’aki zan yi".
"Allah dai ya shirye ka Mus’ab, ka ga tafiya ta".
Tafiya ya fara yi, Mus’ab ne ya bishi yana dariya yace "kai matsala ta da kai ba kasan wasa ba, zan raka ka, amma ka shigo ku gaisa da Maryam sai mu tafi".
Kallon agogon shi yayi dake d’aure a hannun shi yace "ka bari in mun dawo, zan shigo mu gaisa".
"Tun da ba z aka shiga ba, bari in shiga in fad’a mata".
Shiga yayi ya fito suka shiga motar yaya Faruk suka tafi.
A wani shopping mall ya tsaya yayi parking.
Mus’ab ne ya bishi da kallo yace "yanzu dama shopping zaka kasa na bar Maryam ita kad’ai, kasan in ba dole ba, bazan fita ba".
Yaya Faruk bai ce mai komai ba, sai ma rufe motar sa yayi ya shiga cikin Mall d’in.
Tsadaddun turare ya siya ma Hajiyan su Mus’ab da Dadin su Mus’ab d’in, tuna wa da Nana da yayi yasa itama ya za’bar mata kalar na mata mai set, sai tsadaddun sabulai da su chocolate ya k’ara d’aukan mata.
Ma’aikatan ne suka biyo shi da kayan ya bud’e musu bayan motar suka zuba a ciki.
Mus’ab kuwa tambayar kan shi yake yi ina zasu da wannan kayan?
Sanin halin Faruk na miskilanci, idan ya tambaye shi ba lallai ya amsa mishi ba, hakan yasa ya ja bakin shi yayi shiru.
Unguwar su dake Maitama ya ga yaya Faruk ya shiga.
A gate d’in gidan yayi hon mai gadi yazo ya bud’e mishi.
Sai da yayi parking d’in motar shi a ma’adanar motoci sannan ya sakar ma Mus’ab murmushi yace " Mus’ab, dama gun Hajiyar ku za ka raka ni na gaishe su da kake ta min surutu a mota, sai ka fito mu shiga".
"A gaishe ka Faruk, shine b aka fad’a min ba, ka tsaya ja min aji".
"yanzu ba gashi na fad’a maka ba".
Jerawa suka yi suna tafiya suna hira, har suka shiga shashin Hajiyan su Mus’ab.
Mai aiki ce ke ta shawagin ta a falo tana ayyukan ta.
Sallama suka yi suka nemi guri suka zauna.
Amsa musu tayi tana gaishe su.
"Baraka ina Hajiya take?" Mus’ab ya tambaye ta.
"Tana sama, bari in je in kira ta".
Katse ta yayi da cewa "No ki barshi kawai, bari in je da kaina".
Kusan minti biyar sai gashi sun sakko da wata dattijuwar mata, sanye take da super exclusive wanda ak’alla kud’in ta zai kai dubu ishirin da wani abu zuwa talatin.
Da fara’arta ta k’araso falo ta zauna a d’aya daga cikin luntsuma- luntsuman kujerun dake falon.
"kace muna da babban bak’o, Faruk kaine a gidan?".
Hajiyan Mus’ab ta fad’a da murmushi a fuskar ta.
Cikin ladabi ya gaishe ta yana cewa "Ni ne Hajiya, mun same ku lafiya".
" lau Faruk, yaushe rabon ka da gidan nan, da har nayi fushi" fad’a da alamar wasa.
"A yi hak’uri Hajiya, ayyukan ne sai a hankali".
Dariya tayi tace "haka kuke kai da Mus’ab, da an ta’ba ku sai kuce aiki ne ya ‘boye ku, Allah dai ya taimaka".
"Amin Hajiya".
Hajiyan su Mus’ab ce ta fara kiran Nana! Nana!
Cikin natsuwarta ta sakko daga upstairs tana cewa "gani Hajiya".
Turus tayi ta ja ta tsaya ganin yaya Faruk a gidan su, ganin ya dad’e basu had’u ba, gashi kuma material d’in da tasa linen ne kalar peach mai transparent ne.
Cikin jin kunya ta k’araso ta gaishe da Mus’ab sannan ta juya ta gaishe da yaya Faruk.
Hajiya ce tace "Nana je ki kawo masu abinci, snacks da drinks"
"To Hajiya" ta amsa mata.
Sai da ta koma sama ta yafo farin veil mai kauri sannan ta nufi kitchen.
Mus’ab ne yace "Hajiya, Dady na nan ko? na ga motar shi, bari mu je mu gaisa dashi".
"yana side d’in shi, abincin fa, ko sai kun dawo za ku ci?"
"In ta kawo, ki ce ta kai mana side d’ina".
Shopping d’in da yayi ya ajiye ma Hajiya a gaban ta yace "Hajiya gashi ba yawa ke da Dady, d’ayan ledar kuma na Khadijah ne".
"Faruk har da hidima, Allah ya saka da alkhairi, mun gode".
"Hajiya abin da ba yawa".
"Mai yawan kenan, Allah ya muku albarka ya k’ara tsare ku daga mahassada da abokan gaban ku".
"Amin Hajiya" suka amsa a tare.
Side d’in Dadi suka nufa, samun shi suka yi yana karanta jaridar vanguard a hannun shi.
Ganin su yasa ya ajiye jaridar akan center table, ya cire medicated glass d’in dake fuskar shi.
Gaishe shi suka yi, ya amsa musu da fara’ar shi.
Kirari ya fara musu na sojoji
"Soja mazan fama, Soja marmari daga nesa, Soja birgimar hankaka, Soja ga ruwa ga yak’i".
Ci gaba yayi da tambayar su yanayin aiki da kuma course d’in da aka tura su a k’asar Uganda.
Labarin tafiyar suka dinga bashi da kuma nasarar da aka samu.
Hira suka ci gaba da yi kamar wasu abokai.
Sun d’an jima a ‘bangaren Dady sannan suka bar side d’in shi.
D’akin Mus’ab na da suka shiga, a gyare yake kamar da mutum a ciki.
Suna shiga yaya Faruk ya kishingid’a a 3- sitter yana lumshe ido.
Dariya Mus’ab ya fara mai.
Kallon ba ka da abin yi yaya Faruk yake mai.
Ganin har yau yana ci gaba da dariyar k’asa-k’asa yasa yace "wai miye abin dariya, kai wani sa’in kamar wanda kayi gamo".
"da kasan dariyar da nake yi da ba kace haka ba, ni nan tausaya maka nake yi na kad’aicin da ke damun ka, wannan lumshe idanun da kake yi na alamar gajiya ne, kaga da kana da aure, da an yi massage d’in ka shi kenan, amma kai na ga hakan ba ya damun ka" ya k’arashe maganar yana dariya.
Shima yaya Faruk sai da ya dara a wannan lokacin yace "kai dai Mus’ab ban san lokacin da zaka daina wannan iskancin naka ba"
"Ba wani zancen isakanci, maganar gaskiya ce".
Sallamar Nana ce ta katse musu hirar da suke yi.
Abincin da ta shigo dashi ne, da kuma wanda Baraka ta rik’o mata sauran drinks da snacks d’in suka ajiye akan center table d’in.
Baraka ce ta fita daga d’akin yayin da Nana ta nemi guri ta zauna.
Mus’ab ne ya nufi gurin tv ya kunna.
Tambayar su tayi yanzu za su ci abincin?
Mus’ab ne ya amsa mata da "Eh".
Plate ta d’auka ta zuba ma yaya Faruk had’ad’d’iyar fried rice wanda taji hanta a ciki, a saman abincin kuma ta d’aura pepper chicken da coslow akai.
A jiye mishi tayi, sannan ta d’akko swan da hollandia a gaban shi.
"sannu da aiki Khadija, mun sa ki aiki ko?" yaya Faruk ya fad’a yana kallon ta.
Murmushi kawai tayi tace "Ba wani aiki yaya Faruk".
Mus’ab tayi serving sannan ta mik’e ta kalli yaya Faruk tace "Na ga kaya na gode yaya Faruk, Allah ya saka da alkhairi".
Murmushi yayi yace "ya na gan ki a gida, ba ku da school ne?" yaya faruk ya tambaye ta.
"muna dashi, yau test muka yi, tun around 11 na dawo".
"Allah ya taimaka".
"Amin".
Yaya Mus’ab ne ya kar’bi zancen da cewa "kun kusa exams kenan, ina so in kun yi exams kije ki taya Maryam zama, kin ga ta kusa haihuwa".
"Allah ya kaimu yaya Mus’ab"
"Amin Nanan Hajiya" ya fad’a da alamar zolaya.
Fita tayi daga falon, tana kara yaba wa da halin yaya Faruk, haka kawai take jin jinin su ya had’u.
*SU WAYE MUS’AB DA NANA KHADIJAH?*
Mus’ab d’a ne ga Alhaji Sa’id, daga shi sai Nana Khadija, su hud’u iyayen su suka haifa, Mahaifin su da mahaifiyar su Hajiya Safiya haifaffen ‘yan jigawa ne, zama ne ya kawo su garin Abuja, Mahaifin su fitaccen d’an siyasa ne, ya rik’e muk’ami da dama a harkar siyasa, yanzu yafi maida hankali a harkar business.
Mus’ab shine d’a na biyu a gidan su, Soja ne da yake da matsayin Bregadier, yana da yaya mace Hajara da tayi aure, daga shi sai k’anin shi Usman, yanzu yana India yana karantar Medicine, daga shi sai Nana Khadija wanda a yanzu take karatu a University of Abuja, tana karantar English, yanzu haka tana level 2 a matakin karatu.
Mus’ab da yaya Faruk sun had’u ne tun a makarantar sojoji, har ya zuwa yanzu da suke aiki a Abuja, sun kasance abokanan juna da ba sa ‘boye wa junan su matsalar su.
A halayya sun banbanta domin yaya Faruk miskili ne, shi kuwa Mus’ab mutum ne mai wasa da dariya.
Nana Khadijah kusan halin su d’aya da yaya Faruk, don itama Magana ba ta dame ta ba.
***************************
Sai can yamma suka baro gidan su Mus’ab.
Yau yaya Faruk shirya cikin shirin shi na zuwa Kaduna.
Sai da ya biya ta gurin su Mus’ab suka ya d’auke shi kasancewar tare za su tawo Kaduna.
Da rana suka sauka a Kaduna.
Tun zuwan su gidan, kowa murna yake yi ganin yadda ya d’auki lokaci rabon shi da Kaduna.
Abinci na musamman Momi ta shiga kitchen ita da Anisa suka shirya musu.
Sai da suka shiga side d’in yaya Faruk suka watsa ruwa sannan suka canza shigar su zuwa k’ananun kaya suka fito falo.
Momi ce ta zo ta zauna suka sake sabuwar gaisuwa, tana mai tambayar Mus’ab ya su Hajiyan su da Maryam.
Amsa mata yayi da suna lafiya lau.
Anisa ce ta jera musu abincin akan dining table, ta dawo falo ta fad’a musu ga abincin su nan akan dining.
Yaya Faruk ne ya tashi yace ma Mus’ab yazo su je su ci abinci.
Anisa ya kira tayi serving d’in su yayin da Mus’ab ke jan ta da hira.
Bayan sun gama cin abinci ne suka dawo falo suka ci gaba da hira.
Anisa ce ta zo ta zauna tana tambayar Mus’ab Anty Maryam, duk da ba sanin ta tayi ba, amma jin yaya Faruk na yawan fad’an ta yasa ta rik’e sunan ta, ta kuma san Matar Mus’ab ce duk da ya dad’e bai zo ba.
Hira ce ta ‘barke tsakanin Mus’ab da Anisa, yaya Faruk kuwa bai cika sa musu baki ba.
Wani kallo ya jefa ma Anisa, tuni ta sha jinin jikin ta saboda ta gane ya gaji da zaman ta a gurin shi yasa ya mata wannan kallon.
Sallma tayi ma Mus’ab ta tafi d’akin ta.
Bayan tafiyar tane ya kalli Mus’ab yace "kai wai ba ka gajiya da Magana ne, ka zauna kana ba ma k’aramar yarinya labari, salon ta raina ka".
"Yanzu miye laifi dan na zauna mun yi hira, idan mutum bai yi hira da k’annen shi ba, da wa zai yi hira?"
"Matsalar kace, ai sai ka zauna kayi ta hira da yara, in suka raina ka kai ka jiyo".
"kace kai baka hira da Teemar ka saboda ka da ta raina ka, ko da yake a ‘bangaren soyayya ba yara, sai a ‘bangaren hira ne akwai yara ko".
Shiru ya mishi ya maida hankalin shi ga allon talabijin.
Mus’ab ne ya dinga trying d’in numban Maryam, amma wannan baturiyar sai ce mai take yi is not reachable at the moment, haka ya gwada na Nana shima duk amsar d’aya take bashi.
K’aramin tsaki yaja ya kalli yaya Faruk da hankalin shi ke kan labarum da ake yi a tashar Aljazeera.
"Faruk ba ni wayar ka in kira Maryam, ban san ko network bane ya hana kiran zuwa, bari in yi using da airtel numba d’inka in kira da ita, may be kiran yaje".
Dialling d’in numban yayi duk da haka bai je ba, dan haka ya yanke hukuncin kiran Nana.
"Assalamu alaikum" Nana ta fad’a bayan ta d’auka.
"Wa alaikumus Salam Nana, Mus’ab ne, na kira Maryam ban same ta ba, kuma ni yanzu ina Kaduna, idan kin fito lectures ki je can ki kwana, sai ki tafi school daga nan, nima gobe zan dawo".
"Zan je insha Allah, amma yaya Mus’ab wannan numban waye?" ta tambaya.
"Numban Faruk ne"
"ka ce ina gaishe shi".
Sallama suka yi ya katse wayar.
Mik’a mishi wayar yayi yana cewa "Nana tace tana gaishe ka".
Murmushi yayi yace "Ina amsawa".
Faruk wai yaushe zamu gidan Teemah ne, na ga sai ja min rai kake yi, gwara ka tashi mu tafi in ga sarauniyar da ta sace zuciyar soja, yanzu na san kammanin ta ya canza, tun da dad’e ban ganta ba".
Sanin in dai bai tashi sun tafi gurin Fatima ba a yanzu, Mus’ab ba k'yale shi zai yi ba.
D’aki ya shiga ya d’akko tsarabar da ya musu tun a k’asar Uganda, ware na Fatima yayi da na su Ummu da gidan su yaya Aminu.
Kallon Mus’ab yayi yace "Tashi mu tafi".
" sojan Teemah".
Sai da suka fara biya wa gidan yaya Aminu, bai same shi ba yana gurin aiki, Anty Jiddah ya ba tsarabar da ya musu, suka ta’ba hira sannan suka yi sallama ya tafi gidan mu.
Shi da Mus’ab suka shigo cikin parlour suka zauna, yaya Faruk ne ya tashi ya nufi d’akin Ummu.
Samun ta yayi da Kur’ani a hannun ta tana muraja’a, guri ya samu ya zauna a k’asan carpet ya gaishe ta.
Hira suka d’an ta’ba sannan ya sanar da ita da abokin shi Mus’ab suke.
Tashi tayi suka koma falon.
Gaisawa suka yi ta tambaye shi ya su Hajiyan su da Maryam?
Amsa mata yayi suna lafiya kuma suna gaishe su.
Da kanta ta tashi ta shiga kitchen ta samo musu abin motsa baki.
Ta d’an jima a gurin su sannan ta tashi ta nufi d’akina don ta sanar dani zuwan yaya Faruk.
San da tashigo, samu na tayi ina waya da Dr Sadik.
Ganin ta ne yasa na katse wayar ina jiran jin me za tace min.
Murmushi tayi tace "yayan ki ne ya dawo, gashi can a falo".
Da murna ta nace yaushe yaya Khalil ya dawo, shine ba zai zo ya ganni ba?".
"Faruk nake nufi ba Khalil ba".
Wani irin fad’uwar gaba naji wanda ban san dalili, nasan hakan ba zai rasa nasaba da fusakantar shi da zan yi.
Murmushin da bai kai ciki ba nayi nace "Ashe ya dawo, san da muka yi waya dashi yake ce min a satin nan zai shigo".
"ki tashi kuje ku gaisa, shi da Abokin shi yazo" tana gama fad’ar haka ta bar d’akin.
Tashi nayi na yafa gyale a saman kaina jiki na duk a mace.
Sallama na musu na nemi guri na zauna.
Tun da na zauna yaya Faruk ya tsura min ido kamar wanda ya fara gani na a yanzu.
Gaishe da bak’on da na gani a falon sannan na juya na gaishe da yaya Faruk.
"Da girman kujerar ki Sarauniya a gurin Bregadier Faruk, dafatan mun same ku lafiya" Mus’ab ya fad’a.
Murmushi nayi nace "lafiya lau, ya aiki".
"aiki alhamdulillah".
Satar kallon yaya Faruk nayi ganin yadda yake wani lumshe ido, na lura lumshe ido ya zama d’abi’ar shi.
"yaya Faruk sannu da zuwa, dafatan kun dawo lfy".
"lfy lau Teemah".
"Ina fatan kin yi missing d’ina kamar yadda nayi missing d'in ki".
Saurin sunkuyar da kai na nayi ganin yadda ya fad’i maganar ba tare da yaji kunyar bak’on da suka zo tare ba.
"Tun da ba za ki amsa bas hi kenan".
"Fatima, wannan Abokina ne, sunan shi Mus’ab, muna tare ne a Abuja a barrack d’in mu, yana da mata sunan ta Maryam".
"Sannu da zuwa yaya Mus’ab, ya Anty Maryam d’in".
"Tana nan lafiya, tace in nazo in gaishe da gimbiyar Faruk".
A hankali na furta "Ina amsawa".
Mus’ab ne yaci gaba da cewa " gaskiya na yaba da natsuwar ki a yadda na ganki, ina fatan za ki rik’e mana sojan mu da kyau saboda yana matuk’ar son ki, kullum cikin maganar ki yake yi, duk wanda ki ka ga Faruk na so to ba k’aramin abu ba ne, dafatan za mu samu guri a gun ki".
Shiru nayi na sunkuyar da kaina, a gaskiya ban san me zan ce ma yaya Mus’ab ba.
"Amaryar tamu mai kunya ce".
Yaya Faruk sai a yanzu Magana da cewa "Mus’ab kar ka cika ta da surutun ka, nasan in ka fara Magana ba ka gajiya".
"au shigan mata za kayi, wa yaga sabon shiga".
A yadda na lura yaya Mus’ab mai wasa da dariya ne.
Haka yaya Mus’ab yaci gaba da ja na da hira kamar mun dad’e da sanin juna.
Sun d’an jima a gidan mu sannan yace in sanar da Ummu za su tafi, in ya samu time gobe zai shigo.
Ummu ce ta fito rik’e da wata leda a hannun ta tace "har za ku tafi Mus’ab, gashi ba a kai ma Maryam ba yawa".
"Na gode Ummu, Allah ya saka da alkhairi".
"Ummu mun gode". yaya Faruk ya fad’a.
Kallo na yaya Faruk yayi yace "Fatima ki biyo ni gurin mota, zan baki sak’o".
Bin su nayi har gurin inda yayi parking d’in motar shi.
Ledoji ya fito dasu wanda alama ke nuna ba ta k’asar nan bace yace "ki duba, akwai na su Ummu, d’ayan ledan mai custume da sauran kayan su ne naki".
Wani tausayin yaya Faruk ne ya kama ni a lokacin ganin tun da muka shirya yake cikin faranta min rai, amma ni gashi ina son saka mishi da sa’banin haka.
"Na gode yaya Faruk".
Yaya Mus’ab ne ya ciro kud’i a wallet d’in shi yace "Fatima gashi ba yawa, kya sa credit".
Kallon yawan kud’in nayi da ake cewa in sa credit, k’in amsa nayi nace nagode.
"Nawa ne ba za a amsa ba ko Fatima, sai na masoyi za a amsa".
D’aga min kai yaya Faruk yayi alamar in amsa.
Amsa nayi na mishi godiya.
sallama na musu na koma gida ina yaba kirkin yaya Mus’ab.
A hanya suna tafiya suna labarina, yayin da Mus’ab ke ci gaba da tsokanan yaya Faruk.
Kwanan Mus’ab d’aya yayi sallama da su Momi, Momi ta had’a tsaraba tace a kai ma su Hajiya da Maryam, haka ya ma Anisa kyautar kud’i wai tasa credit.
Godiya tayi ta mishi tana cewa a gaida Anty Maryam.
Nan yaya Faruk ya raka shi gurin motar shi suka yi sallama.
0 Comments