makauniyar soyayya hausa novels 6

 MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



*BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽





*Wannan shafin naki ne*


*Nasiba Isma'il Uba* (marubuciyar Sanadin Aboki)💞


*My friend ina miki fatan alkhairi*






*MUNA TARE*❤


*'yan Mufy & Maryam A Paki fans*


*Maman Walida*


*Auta mama*(Aisha)


*Tawerh*


*Hajara Tijjani*


*Ramlerh*


*Hauwa Hussaini*


*Queen Aysha*


*Maymoonah*


*Fadeelah*


*Barrister Teemah*


*Har kullum ina tare daku ‘yan group d’ina da kuma son da kuke ma wannan novel d’in*.


*Ba abin da zance daku sai godiya*


*Sauran da baku ji sunan ku ba za mu had’u a next page*.



*Tawerh ina miki fatan sauk'i, Allah ya baki lfy yasa kaffara ne*





*Question of the Day*


K’ofofin aljanna guda nawa ne? Lissafo sunayen su.




 

35&36



Maida hankali na nayi gaban allon Tv ina kallon tauraren d’an adam a tashar MBC Bollywood, jefi-jefi nake jin hirar tasu.


Yaya Aminu ne naji yana cewa yaya Faruk "kai ma Soja ya kamata ace ka fito da matar aure, tun da iyayen mu sun nuna suna son kayi aure, in kuma baka fi son azumi in yazo a fara kad’a maka ganga ba"


Murmushi kawai yayi kana yace "very soon insha Allahu zan gabatar da wanda nake so, kafin in koma aiki zan zo in same ka akwai maganar da nake so muyi" cewar yaya Faruk.


"Ok sai kazo" ya bashi amsa.


Yaya Aminu ya mik’e cikin wasa ya kalli yaya Faruk yana cewa "ni zan gudu, nasan madam nacan na jira na, kai ko k’arfe nawa zaka kai a waje ba matsala, ba mai tambayar ka".


Shima mik’ewa yayi yace "nima tafiya zan yi".

Sallama suka min suka tafi.


Kasancewar yanzu ba ma zuwa ko ina tun da muka zana SSCE exam d’in mu, Abbu ne yasa yaya Khalil ya siyo mana form ni da Anisa a Al-Mannar Academy na shiga Mutawassid tun da mun yi saukar Al-qur’ani.


Bayan mun cike form ne muka fara zuwa makarantar.

Daddy form d’in computer training yasa yaya Faruk ya amso mana a Bintalya computer institute.


Sai ya zamana yanzu ba mu da wani time, da mun dawo daga computer training, ba jimawa zamu tafi islamiyya, ba mu zamu dawo ba sai yamma.


Yanzu tsakani na da yaya Faruk ba wani takurawa, ni gani nake yi neman shiri yake yi dani saboda yadda yake d’an ja na da wasa da kuma hira.


Duk wannan abubuwan da yake yi ba wai na sake dashi bane saboda sanin hali.


Yau ranar ta kasance ranar lahadi, yaya Faruk ne cikin shirin shi ya fito ya shiga side d’in Momi, bayan sun gaisa ne yake ce mata zai lek’a gidan yaya Aminu ne, fatan a dawo lafiya ta mai da sak’on gaisuwar ta ga Anty Jiddah da Humaira da Nabil.


Kafin ya isa gidan sai da ya tsaya a wani super market, ya tsaya yayi wa su Humaira da Nabil shopping.


Da isar shi gidan ya same su a falo da yaran suna kallo, su Humaira kuwa sai murna suke yi da ganin yaya Faruk saboda yadda yake kawo musu kayan zak’i da kayan wasa.


Hannu ya mik’a wa yaya Aminu suka yi musabaha kana ya samu guri a d’aya daga cikin kujerun dake kewaye da falon ya zauna.


Anty Jiddah ce ta gaishe shi tana tsokanar shi tana cewa "su Anisa ba su baka sak’o na ba?


Ta’be baki yayi yace "wane irin sak’o ne".


Dariya tayi ta d’aura da cewa "ce musu nayi su ce maka ka bani za’bi in za’bar maka mata tun da kai naga har yau ka k’i fito da wacce ta yi maka".


Murmushi yayi yace


 "Madam kenan, ke kin san class d’ina yafi a ce za aza’bar min mata saboda ba ki ga yadda ‘yan mata ke so na ba a Kaduna da Abuja, infact nan ba dad’e wa ma zaki ga wacce nake so".


"haka muke so Soja, gwara kayi zuciya kayi auren ko ka huta da gori" Anty Jiddah ta fad’a da alamar wasa.


Yaya Aminu kuwa bai ce komai ba in banda dariya da yayi.


Kayan motsa baki taje ta kawo mai ta ajiya ta nufi d’aki ta barsu dan su zanta.


Nabil ne yaje kusa da yaya Faruk ya manne a jikin shi ya fara Maganar shi ta ‘yan koyo yace


 "Uncle Soja ina bindigar da kace ja ka ciyo min".


Kunnen shi ya kama yace "sorry Nabil na manta ne amma in zan k’ara zuwa zan siyo maka".


Tsalle Nabil ya fara yi yana cewa "yeh Uncle soja jai ciyo min bindiga".


Humaira sai faman zun’bura baki take yi ganin ance za a siyo wa Nabil bindiga amma ita ba a ce za a siyo mata ‘yar baby ba (toys)"


"zo nan Humaira" yaya Faruk ya kira ta cikin lallashi.


"Me ya faru ne baby naga kina so kiyi kuka".


Cikin shagwa’ba tace "ba kai bane kace zaka siyo wa Nabil bindiga, ni kuma ba kace zaka siyo min ‘yar baby ba (toys)".


Dariya suka yi shi da yaya Aminu kana yace "ke ma zan siyo miki, an shi wannan ki kai ma Momi ta raba muku"


Cikin murna ta amsa tana cewa


 "Uncle soja mun gode" ta tafi d’akin Anty jiddah da gudu.


 ganin haka ne yasa Nabil shima ya bi ta da gudu.


5 alive na kwali da Anty Jiddah ta kawo mai ya d’auka ya tsiyaya a glass cup ya sha, ya juya kallon shi zuwa gurin yaya Aminu yace "Aminu shawara nazo nema a gurin ka game da yarinyar da nake so".


Yaya Aminu ya yalwata murmushin shi yace "Masha Allah ina jin ka, kace mun kusa yin suruka".


Sai da ya numfasa kana yaci gaba da cewa "Aminu ba kowace yarinya bace na dad’e da fad’a wa tarkon son ta illah Fatima, bazan iya fad’a maka adadin son da nake mata ba, sai dai kawai in ce maka, I really love her".


Da mamaki yaya Aminu yace "wace Fatiman kake nufi?


Gajeren tsaki yayi kana yace "Akwai wata Fatima ce da ta wuce k’anwar ka".


Dariya Aminu ya fara yi yana kallon yaya Faruk wanda ya tamke fuska ganin dariyar da Aminu yake mai.


Wani dogon tsaki ya k’ara ja wanda yafi na farko yace "wai Aminu miye abin dariya, daga na fad’a maka sirrin zuciya ta, ka tasa ni sai dariya kake min kamar kaga wani mahaukaci".


Tsayar da dariyar yayi yana cewa


 "Sorry Bregadier, my inlaw, abin ne da ban dariya da mamaki wai kai kake son Fatima, gashi kana da son girma, baka son raini, ita kuma Fatima ga rawar kai, amma soyayyar nan za ta ba da ma’ana, naji dad’i da Sister ta samu gwarzon namiji kamar ka, congrat".


"Kai matsala na da kai Aminu, kana mai da zance mai mahimmanci wasa, nazo dan ka bani shawarar amma kana d’aukar zancen as a joke".


"Ok sorry, joke aside, yanzu fad’a min shawarar da kake so in ba ka" yaya Aminu ya fad’a.


"Kaga dai Fatima ba ta dad’e da kammala Secondary School ba, nan ba da jima wa ba admission zai fito su fara d’auka lectures, yanzu abin da yake damuna shine har yau ita Fatima ba ta san ina son ta ba, tsoron da nake ji shine kar in bari ta fara high institution ta had’u da wani su fara soyayya alhalin ni ina nan ina jiran ta, kar kuma in fad’a mata yanzu in katse mata karatu tasa soyayya a gaban ta? kai menene shawarar ka".


Yaya Aminu in ban da bin shi da kallo ba abin da yake yi.


 mamaki yake yi wai Faruk ne ya zauna yana expressing d’in feeling d’in da yake ma Fatima, "lallai ya yarda Love is everything, you don’t have any choice to control yourself when you fall in love, ya kuma yarda da son da Faruk yake ma Fatima".


"A shawara ta Faruk, ina ganin ka fad’a mata yanzu saboda tasan kana son ta da wuri, kaga ko nan gaba tasan da kai, ba za ta bari ta sa soyayyar wani a ranka ba, kasan A bari ya wuce shi ke kawo raban wani".


Yaya Aminu ci gaba yayi da cewa 'yanzu kayi amfani da DAMAR KA ka k’ara jan ta a jikin ka na yadda SHAK’UWA CE za ta k’ullu a tsakanin ku, kaga daga nan sai ka nuna mata ZAZZAFAR K’AUNAR da kake mata, I know, she will not reject you, because you are one out of thousand".


Wani murmushin dad’i yaya Faruk yayi saboda yadda yaji yaya Aminu ya bashi shawara da kuma yadda yake fasa mishi kai, hakan yasa ya k’ara samun k’arfin gwiwar tunkarar ta.


Shawarwari yaya Aminu ya dinga ba wa yaya Faruk akan yadda zai shawo kan Fatima ba tare da wata matsala ba.


Canza akalar hirar suka yi kana yaya Faruk yace ya kira mishi Anty Jiddah ya mata sallama ya tafi.


Tun daga wannan time d’in ya zamana yaya Faruk na zuwa gidan mu yana ja na da hira, ga siyayya da yake min akai – akai, yanzu har dama ya bamu wai mu dinga yin chating, ga kira na da yake yi akai-akai.


Ni ko mamakin mai ya canza yaya Faruk a lokaci d’aya nake yi, yadda ya dawo so cool da friendly damu.



Yau da daddare ina zauna a d’aki ina buga game a waya ta, naji alamar shigowar war calling a waya ta.


Sunan yaya Faruk na gani a jikin screen d’in yana yawo, d’auka nayi na amsa mishi sallamar da ya min.


'ki same ni a falo akwai maganar da za muyi" abin da yace min kenan ya katse wayar.


Tunani na fara yi wace Magana ce zamuyi dashi da ba zai bari gobe ba sai da daddaren nan.


Hijab kawai na d’aura akan night gown d’ina da zani akai na nufi falo.

Samun shi nayi a falo shi da yaya Khalil suna hira.


Guri na samu na zauna na gaishe shi.


Ganin bai ce min komai ba yasa nace


 "gani yaya Faruk"


Yaya Khalil ne ya mik’e yayi wa yaya Faruk sallama ya tafi side d’in shi.


Shiru falon ya d’auka na d’an mintina kamar ba kowa a ciki.


"TEEMAHHHH"


Saurin d’ago kaina nayi saboda yadda naji yaya Faruk ya kira suna na wanda ya banbanta da sauran lokutan da yake kiran suna na.


D’aga kai nayi na kalle shi ba tare da na amsa ba.


Shiru yayi kamar mai tunanin abin da zai ce yake yi.


"Fatima! ina so ki bani aron time d’in ki saboda maganar da nake so muyi a yanzu is ver important".


Wannan wace Magana ce kuwa da yaya Faruk yake son fad’a min mai mahimmanci haka? nasan wannan tambayar ba ni da amsar ta sai dai in jira ya fad’a min ba.


"Teemah, duk maganar da zan fad’a miki ki d’auke ta da mahimmancin saboda har cikin zuciya ta haka take, kar ki zata ko da wata manufa zan fad’a miki sai dan in fallasa abin da ya dad’e a cikin zuciya ta yana damu na".


Duk da ban san wace Magana ba ce, sai naji gaba nay a fad’i duba da yadda yake amfani da cool sound wajen maganar.


"Teemah! ba kowace Magana bace da ta wuce in ce miki INA SON KI FATIMAH, I know I am in love with you because my reality is finally better than my dreams".


Gaba na ne ya fad’i na yadda maganar tazo min a bazata da firgita da nayi a lokaci guda wanda hakan ya kasa ‘boyuwa a fuska ta.


"mai yaya Faruk yake nufi da wannan kalamen nashi, ko in ce tatsuniyar da za ayi ta a lokacin a gama, an ya yaya Faruk yana cikin hankalin shi da zai tunkare ni da wannan tsadaddiyar kalma mai wuyar furta wa? ya ma san wacce yake fad’a ma wannan kalmar" na tambayi kaina.


Kamar ya san tambayar da nake yi wa kaina yace


 "Teemah, kar ki yi mamaki ko shakkar maganar da na fad’a miki, kar kuma ki d’auka da wani nufi a raina yasa na fad’a miki haka illah ina fallasa miki abin da ya dad’e a raina, duk wasu abubuwa da kika ga ina miki wanda kike d’auka a matsayin takurawa, ina miki shine dan ina kishin ki da kuma son da nake miki".


Ci gaba yayi da cewa "Teemah! True love doesn’t have a happy ending because true love doesn’t have an end. My love 4 u has no end, farin ciki na shine samun Ki, there is only one happiness in this life, to love and be loved".


Ni dai rasa a wani hali nake ciki, rasa wani hukunci zan yanke ma wannan maganar mai kama da labari shuni ya yi, na yadda namiji bai da kunya, tun da har yaya bai jin kunyar fad’a min abin dake ranshi ba, ya kuma manta abin da yamin a baya, duk ma ba wannan ba, zuciya ta ce tak’i marhabin da sak’on da yaya Faruk yazo mata dashi.


Jin bance mai komai ba yasa yace


 "Fatima zan baki time kije ki yi tunani kafin in koma aiki saboda hutuna ya kusa k’are wa, dafatan zaki yi ma Magana ta duban basira".


Ya mik’e yana duba wrist watch d’in shi yace "Gud night Teemah, na barki lafiya".


Bai jira jin abin da zance ba ya tafi.

[4/10, 20:51] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*



    *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




*Wannan shafin naku ne*


*Hussaina Ahmad da duk wanda ke group d’in Ni da yaya Farooq*


*Ina muku fatan alkhairi*




*Sak’on gaisuwa ta gare ku*


*Sakina ilyas*


*Sarah*


*Umin kareemah*


*Lubiee*


*Fauxiya Masha Allah*


*Doctor Maryash*


 *Ash, beely*


*Aysha a*


*Aeeshart* 


*Maman nabeel*


*Hafsat m Goni*


*Da duk wanda ke cikin group d’in Mufy & Maryam A Paki fans*.


*Sauran wanda ba su ji sunan su ba, mu had’u a next page*.




Wannan karan ba samu wanda ya kawo complete answer na question of the day, sai dai akwai wanda suka yi matuk’ar k’ok’ari irin su


Meeynah


Auta mama (Aisha)


Xarah auwal


Sulaiman Abdullahi (facebook)


Amsar question of the day shine k’ofofin aljanna guda takwas ne (8)

1. Jannatul Firdausi

2. Jannatul Na’im

3. Jannatul Aliya

4. Jannatul Adnin

5. Jannatul Ma’awa

6. Jannatul Darul kuldi

7. Jannatul Ar-rayyan

8. Jannatul Darul salam

Allah ka sa da mu daga cikin wannan k’ofofin.




*Tunatarwa*


Kar ka/ki bari fushi ya dinga ziyartar zuciyar ka/ki, saboda duk lokacin dab ka/ki yi fushi, shaid’an ne a cikin jinin jikin ka/ki da ruhin ka/ki.

Wannan nasiha ce.


Idan mutum yayi maka/ki abu mara kyau, ka/ki tuna da mai kyau da yayi maka/ki, saboda ko wane mutum yana da hali maii kyau, yans da mummuna.

Wannan nasiha ce.


 



37&38


Tun da yaya Faruk ya tafi na ji ban da wani sukuni, jiki na a sanyaye na mik’e na nufi d’aki na.

Akan gado na zauna ina tariyo maganganun da yaya Faruk ya zauna ya na fad’a min, kenan maganar Anisa ta zama gaske da tace yaya Faruk na matsa mana ne saboda ni, ya akayi tayi saurin gano cewa yaya Faruk so na yake yi amma ni ban gano haka ba.


Har yanzu maganganun shi suna min yawo a zuciya ta, ban san kuma dalilin da yasa na kasa gasgata maganganun shi a raina ba duk da nasan har zuciyar shi yake fad’a min.


Abin da bazan iya tantancewa ba shine ni dai a zuciya ta ba ta yi marhabun da maganar yaya Faruk ba, hakan na nufin kenan bana son shi?


Wata zuciyar ce ta gargad’e ni da cewa "kar kiyi saurin yanke hukunci dan ba a yanzu bane zaki samo amsar ki".


Ni kaina nasan yaya Faruk ya kai namiji da duk macen da ta ganshi za tayi fatan ya so ta, ya had’a duk abin da mace ke buk’ata, sannan ya na da ilimi, kud’i, kyau, duk da muna takun sak’a dashi, hakan ba zai hana fad’ar cewa yana da kyawawan halaye, matsalar shi ita ce fad’a da miskilanci.

A ra’ayi na shine ba na ra’ayin namiji so rude, na fi buk’atar namiji friendly kamar yaya Khalil.


Zuciya ta ce ta bani shawarar kar in fad’a ma Anisa wannan maganar, dan duk yadda takai ga complaining d’in abin da yaya Faruk ke mana, ba za taso in yi rejecting d’in shi ba, fad’a ma ta na nufin kamar maganar taje kunnen family ne.

Shawara d’aya na yanke shine in yi watsi da maganar da yazo min in ci gaba da harka ta, in yaso in ya tambaye ni in ce ban gama shawara ba.


Da wannan shawarar na samu mafita, na manta da wani batun yaya Faruk.




WANENE YAYA FARUK?


Yaya Faruk d’a ne ga Engineer Yusuf wagini, mahaifin shi ma’aikaci ne a NNPC dake marabar rido a kaduna, sannan yana da kamfanin sai da motoci da suka yi had’in gwiwa da k’anin shi Ibrahim. Mahaifin Faruk wa ne ga mahifin su Fatima.


 Mahaifyar shi Hajiya Rukaiyya ‘yar asalin cikin katsina ce, mahaifiyar shi business woman ce da take saro kaya daga Dubai take kawowa gida Nigeria.

Yaya Faruk ya ci sunan kakan mu ne Umar, shi yasa ake kiran sa da Faruk.

Mahaifin yaya Faruk shahararren mai kud’i ne.


Yaya Faruk d’an kimanin shekara 32 kuma shine babba a family, ya ba ma yaya Aminu ratar shekara d’aya, sai suka taso kan su d’aya kuma abokai ne.


Tun da aka haifi yaya Faruk sai da aka d’auki wasu shekaru sannan Momi ta sake haihuwa amma sai yaron bai zo da rai ba, daga nan sai da Momi ta sake d’iban wasu shekarun sannan ta haifi Anisa, dan har su Momi sun cire rai da sake haihuwa.


Yaya Faruk tun yana k’arami yake da sha’awar aikin soja har yau da yake matsayin Bregadier.


Yaya Faruk mutum ne wanda Magana bai dame shi ba, baya shiga abin da ba ruwan shi, akwai shi da miskilanci sannan ga wanda ya fahimce ci yana da dad’in zama da kuma kyauta, Shi mutum ne mai son zumunci.


Yaya Faruk irin classic d’in mazan nan ne da ake ce musu one in town, yana da kyau wanda yake d’aukar hankalin ‘yan mata, kalar skin d’in shi normal fari ne wanda bai yi yawa can ba, gashi da dogon hanci, dogo ne amma ba can ba,  yanayin jikin shi irin giant ne, yana da farin jinin ‘yan mata da kuma mutane, sai dai shi ‘yan matan ba sa gaban sa illah Fatima da yake ganin yayi gamdakatar da soyayyar ta.




CI GABAN LABARIN


A can ‘bangaren yaya Faruk kuwa tun da ya koma gida yaji ya samu relief a zuciyar shi, ko ba komai yau ya samu ya amayar da abin dake cikin zuciyar shi na wasu shekaru.


Sai dai zuciyar shi ke kai kawo akan yanayin Fatima da ya fad’a mata maganar, bai ga wata alama na farin ciki ko bak’in ciki ba, yanzu ba zai iya yanke hukuncin cewa tayi na’am dashi ba ko akasin hakan.


Idan Fatima tayi accepting d’in shi yasan ya samu farin cikin da ya dad’e yana buri, kenan idan tak’i accepting d’in shi yana nufin zai samu akasin farin ciki kenan, rasa Fatima a gurin shi yana nufin rasa jin dad’in shi ne, shi kan shi bai san lokacin da son Fatima ya mishi dabaibayi.


Baya fatan hakan ta kasance gare shi saboda bai san halin da zai shiga ba in ya rasa ta.


Yana cikin wannan tunanin ne wayar shi ta fara haske tana d’auke wa, hakan na nufin kira ne ya shigo wayar saboda a silent yasa ta.


Sunan Ogan shi yaga yayi appearing a jikin screen d’in wayar.


Da azama ya d’auka  ya mik’a gaisuwa yana jiran jin abin da Ogan zai ce mai tun da ya kira shi a wannan lokacin.


Sanar dashi yayi akan ya ajiye duk abin da yake yi ya tawo Abuja gobe, akwai wani aiki da za ayi kuma a ciki har dashi a ciki.


Cikin ladabi ya amsa mishi da insha Allah yana nan tawo wa.


Yana gama receiving d’in call d’in ya wurga wayar can gefen gado, ya dunk’ule hannun shi ya kai ma d’ayan hannun naushi kamar hannun ne ya masa laifi.


Wani irin takaici ne ya kama shi a lokaci guda, yana ganin yanzu ne ya kamata ya jawo Fatima a jiki, su fahimci juna ta yadda za ta kamu da son shi, sai gashi rana tsaka ana neman shi a gurin aikin shi ba tare da ya samu ya fahimci juna da Fatima ba.


Babbar matsalar shi shine na yadda zai tafi ba tare da ya tsaya yaji amsar shi a gurin Fatima ba, bai san wani lokaci aikin zai d’auke shi ba da zai sa ran dawowa don yaji amsar shi a gurin ta.


Wata zuciyar ce ke ce mai "kar ka damu tun da har ka fallasa mata Sirrin zuciyar ka, ko wani lokaci zaka d’auka tasan da zancen ka".


Da wannan k’arfin gwiwar ya samu ya tashi da niyyar zuwa gurin Momi dan ya fad’a mata maganar tafiyar shi.


San da ya shiga d’akin, samun ta yayi zaune akan gado tana pressing d’in waya.


Sallama yayi ya zauna awata round chair dake d’akin ya zauna.


Amsa masa tayi tana nazarin shi ganin bas u dad’e da rabuwa ba a falo.

‘ya akayi ne Faruk’ Momi ta tambaye shi.

Amsa mata yayi da cewa "Momi daman nazo in fad’a miki ne, gobe zan koma Abuja, yanzu aka kira ni akan wani aiki da za muje wani gari muyi, kuma ina daga cikin wanda za su jagoranci tafiyar".


Kallon shi tayi saboda lura da tayi kamar bai shirya tafiya a goben ba, kamar kuma akwai abin da ke damun shi.


"Allah ya taimaka ya ba ku sa’a akan aikin ku".


Cikin jin dad’in addu’ar Momi ya amsa da "amin Momi".


Shiru ne ya ratsa d’akin kamar ba wanda zai yi Magana a cikin su.


Momi ce ta katse shirun da cewa


 "yanzu Faruk ya muke ciki game da maganar da nayi maka, kana nufin haka zaka tattara ka koma ba tare da ka tsayar min da kyakkyawan Magana ba"


"Momi insha Allah in na dawo za ki ji duk yanda ake ciki, yanzu komai zai zo da sauk’i dan na riga na fad’a ma ita yarinyar ina son ta, na so ta ba ni amsa, sai ga tafiya ta taso ba shiri, abin ma duk na gida ne ai Momi".


Cikin tuhuma Momi tace "wacece yarinyar?


Murmushi yayi kana yace "in na dawo daga tafiya zan fad’a miki wace yarinya ce".


Momi dad’i ne ya kama ta jin cewa ma yarinyar da yake so ‘yar gida ce duk da bai fad’a mata wace yarinya ba ce amma duk da haka taji dad’i.


Addu’a ta shiga jera mishi tare da mishi fatan nasara akan aikin shi.


Sallama ya mata ya koma side d’in shi yana ci gaba da tunanin masoyiyar shi.


 Washe gari ko da yaya Faruk yayi sallama da su Momi, gidan su Fatima ya wuce dan ya musu sallama.


Ko da ya shiga main falo, bai samu kowa a ciki ba, wuce wa d’akin Ummu yayi, nan ma bai same ta ba.


Jin motsin ta yayi a kitchen yasa ya nufi kitchen d’in.


Fitowa tayi daga kitchen a lokacin shi kuma ya k’araso.


Yalwataccen murmushi ta sakar mai tana cewa


 "Faruk ne! sannu da zuwa".


Shima cikin murmushi ya gaishe ta tare da tambayar Abbu ko yana nan.


Amsa mishi tayi da ya tafi gurin aiki.


"Ummu da ma nazo in muku sallama ne zan koma gurin aiki, jiya Oga na ya kira ni, akwai wani aiki da ya taso kuma har dani ake buk’ata".


"ikon Allah, tafiya ba shiri, to ubangiji Allah ya taimaka ya ba da sa’a".


Amsa mata yayi da


 "Amin Ummu".


"Ummu Khalil na nan ne" ya tambaye ta.


"Ya tafi makaranta"


 Ummu ta ba shi amsa.


Jim yayi kana yace "Fatima na nan ne?


"Ba ta nan, Khalil ya d’auke ta zai kai su inda suke yin computer training, ina jin ma ai sun biya ta gidan ku sun d’auki Anisa, daga nan zai wuce makaranta".


Har a ran shi bai ji dad’i ba da bai same ta ba, saboda yaso ya gan ta kafin ya tafi.


Ummu ce tace "ban san da tafiyar ka ba, da na maka dambun naman nan da kake so, ko yanzu ma ba za a rasa ba, bari in d’ebo maka ka tafi dashi".


"To Ummu, nagode, Allah ya saka da alkhairi".


"Miye abin godiya Faruk, kaima ai kana kyautata mana, ka ga dan mun maka ai ba laifi, Allah dai ya k’ara bud’a muku".


Amsa mata yayi da


 "Amin Ummu".


Juyawa tayi ta koma kitchen dan ta d’ebo mishi danbun nama.


Yana jin dad'in yadda Ummu ke bashi kulawa kamar d’an ta.


Dawowa tayi d’auke da wani food flask a hannun ta wanda yake d’auke da dambun nama a ciki.


Mik’a mishi tayi tace ‘in kaje ka samu guri ka juye saboda kar ya lalace.


yayin da yayi ta jero mata godiya.

Sallama yayi mata ya kama hanyar zuwa Abuja.


Bayan na dawo ne, Ummuk ke fad’a min yaya Faruk yazo yin sallama saboda ana neman shi gurin aiki.


Dad’i ne ya kama ni ganin ba mu had’u dashi ba, dan har yanzu ban samo amsar da zan ba shi ba.


*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY AND WRITTEN*


              *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽






*BAN MANTA DAKE BA*❤❤


*SHAK’UWA CE tasa ki ke raina my surukas (Sameena Aliyu) marubuciyar shak’uwa ce*


*Ina miki fatan alkhairi a duk inda kike*


*Dafatan za a ci gaba da amso mana primary & secondary data*.😝




 _KINA RAINA_💝💝


_Mufida Mu’azu_ _(Marubuciyar Auren Dole)_

_Dearest friend, kamar yadda ba za ki manta ni ba, nima bazan manta dake ba_

_Har kullum muna tare ko ba novel_.

 _Ina taya ki murnar kammala littafin ki mai suna Auren Dole_

_Allah yasa an amfana da darasin dake ciki, an yi watsi da akasin haka_

_Sai mun ji ki a sabon novel d’in ki_.




*My regard to you*🤝🏽


*Al-Mirah*


*Screen play of hausa film*.


*You are one of my fans, I appreciate it*.

*I dedicated this page to you*

 



*Sak’on fatan alkhairi gare ku*

💞💞


*Softie Deeja*


*Hajara Tijjani*


*Shatu Naseer*


*Ruky wada ce*


*Barrister Amal*


*Maryam Muhd*


*Classic lady*


 *Zaihash*


*Fatima*


*Zeisha*


*Ummu Naeem*


*Ummu sulaiman*


*Ummie*


*Humairah*


*Hussainty*


*Da duk wanda ke cikin group d’in Mufy & Maryam A Paki fans*





*Question of the Day*


Yaushe ne k’uraishawa suka jaddada sabunta gina ka’aba? Sannan akan me suka samu sa’bani?

 





39&40


Mun ci gaba da zuwa islamiyyar mu da computer training d’in mu cikin jin dad’i saboda ba mu da wani lokaci na zama a gida.


Haka lokaci yaci gaba da tafiya inda kamar yau ne muka zana jarabawar SSCE, sai gashi Addmission a nan Kad Poly, sai dai ba course d’in computer science da na za’ba suka ba ni ba, sai suka canza suka bani Statistics, yayin da ita kuma Anisa suka ba ta course d’in da ta za’ba SLT (science & Laboratory technology).


Mun yi waya da k’awar mu Aisha, take ce min sun ba ta computer science.


Nan da nan muka je muka biya muka amshi acceptance letter, muka ci gaba da procedure na registration.


Bayan gama registration d’in mu ne muka fara attending d’in lectures.


Na yarda da aka ce rayuwar high institution rayuwa ce da za koyi darussa da dama, zaka had’u da na kirki da na banza, kowa da kalar rayuwar da yake gudanarwa ba tare da duka ko zagi ba, hakan yasa na kama kaina don guje wa irin bad groups d’in school.


Ganin duk wani lecturer in ya shigo class d’in mu yake tsoratar damu akan mu dage kasantuwar yadda course d’in mu yake da wuya, shi yasa na ba da k’aimi wajen karatu dan ban son samun matsala a karatuna.




 _ABUJA_ 


Tun tawowar yaya Faruk bai zauna ba kasantuwar shirye shiryen tafiyar da za suyi zuwa garin Adamawa.


Zaune yake akan three sitter, yana sanya da singlet d’in sojoji da short nicker na sojoji a jikin shi.

Kayan sun matuk’ar yi masa kyau.


Wayar shi ce ke ringing, wayar ce ta katse, wani kiran ya sake shigowa a karo na biyu.


Ganin bak’uwar numba ce yasa ya ajiye wayar kasantuwar bai gane number ba, a ka’idar shi bai cika d’aukar number da bai sani ba.


Jin wani kiran ya sake shigowa yasa ya ja tsaki ya d’auka saboda yadda mai kiran ya nace wa kiran "Assalamu alaikum" ya fad’a da cool voice d’in shi.


"wa alaikas salam Bregadier Umar Faruk".


Jin muryar mace ce yasa yayi shiru yana tunanin wacece saboda bai gane muryar ba.


"plss da wa nake magana" ya tambaya.


Cikin muryar shagwa’ba ta ce "nayi fushi Bregadier, tun da ba kayi saving number d’i na ba".


Mtsww ya ja wa wani gajeran tsaki


"hey! In za ki fad’a min wacece ke am waiting, in kuma ba ki shirya ba zan kashe waya ta" yayi maganar cikin fad’a.


Ganin yadda yayi mata maganar yasa taji ba dad’i a ranta, don haka tace ‘Sorry Bregadier, if what i have said hurt you, Fatima Binafa ce da muka had’u a haleems".


Shiru yayi kamar bai gane mai maganar ba kana yace "oh na gane, ya kike?".


"Lfy lau" ta amsa a gajarce.


Yadda yake mata Magana yasa jikin ta yayi sanyi don haka tace "da ma na kira ne mu gaisa"


"to na gode, bye" abin da yace kenan ya katse wayar.


Ya na ajiye wayar ya k’ara jan wani tsakin ganin yadda yarinyar take son matsa mishi, tun a haleems d’in ya gane take- taken ta.


Shi yanzu tunanin Fatima yake yi saboda yadda ya d’aukantu da ta bashi amsar shi, amma ba hali tun da yanzu tafiya za suyi garin Adamawa kwantar da tarzomar da ake yi a garin, bai san ranar da za su dawo ba.


Mus’ab ne yayi sallama ya shigo, ya nemi guri ya zauna.


Amsa masa sallamar yayi yana murmushi.


Mus’ab ne ya fara Magana da cewa "dole kayi murmushi, kasan abin da kayi baka kyauta ba, tuntuni nasa madam ta dafa abincin da kai, kace mana ga ka nan zuwa shine baka zo ba, yanzu sai ka tashi mu tafi".


"Sorry Mus’ab, da na dawo sai naji ina buk’atar hutawa, shi yasa na zauna na huta".


"Bregadier ba ka da hujjar k’ara kan ka a guri na, ka tashi mu tafi kawai".


Mik’ewa yayi ya shiga d’aki ya canza shigar shi zuwa wani lallausan yadi sky blue ya fito.


A K’afa suka k’arasa Block d’in su Mus’ab kasantuwar ba wani nisa a tsakanin su.


Ko da suka shiga cikin falo d’in, samun su suka yi a zaune a falo.


Bayan sun gaisa ne, matar Mus’ab mai suna Maryam ta ke mishi k’orafin ya guje su ba ya lek’o su. 


Murmushi yayi yace "ayi hak’uri Madam, kin san yanayin aikin mu ne sai a hankali".


"an maka uzuri bregadier" Maryam ta fad’a tana dariya.


Dining area su ka zarce inda aka jajjera abinci kala kala da drinks.


Mus’ab ne da yaya Faruk suke cin abinci akan dinining table d’in, yayin da Maryam ke zaune a falo tana a falo rik’e da remote a hannun ta.


"Nana! Nana" ta kira sunan ta.


Wata ‘yar madaidaiciyar budurwar yarinya ce ta fito daga wani d’aki, kalar skin d’in ta irin chocolate colour d’in nan ne, sanye take da wata brown d’in atamfa a jikin ta, an mata six pieces gown, ta yane kanta da wani d’an karamin gyale a kanta, yarinyar ba za ta wuce shekara 20 zuwa 21 ba.


Cikin natsuwa ta k’araso cikin falo d’in, yayin da ta amsa kiran da Maryam take mata.


 cikin siririyar muryar ta amsa "gani Anty Maryam"


Kallon ta tayi tana cewa "na ji ki shiru ne ba ki fito ba, ki je kitchen na d’aura farfesun kayan ciki ki duba in yayi, sai ki zuba ma su yayan ki".


Cikin siririyar muryar ta amsa "ina wani assignment ne kan mu koma school, lecturer bai da kirki, bari in je in duba".


Gurin wucewa kitchen d’in ne ta lura da Mus’ab da yaya Faruk da suke zaune a dining area.


Cikin ladabi ta gaishe da yaya Faruk kana ta wuce kitchen.


Bayan shigar ta kitchen d’in ne ta sami wani food flask ta zubo farfesun a ciki, yayin da ta d’akko wasu glass plate biyu a hannun ta da serving spoon.


In da suke zaune ta nufa cikin sanyin ta, serving d’in su tayi ta ajiye masu a gaban su.


D’ago wa yaya Faruk yayi ya kalle ta yakau da fuska sannan ya juyar da kallon shi ga Mus’ab daka faman shan farfesun da Nana ta zuba musu.


Mus’ab wannan kamar autar Hajiya ko? ya tambaya.


Ta’be baki yayi kamar ba zai ce komai ba, can yace "yanzu Faruk kana nufin ba ka gane Nana ba?"


Murmushi yayi yace "Am sorry Mus’ab, ba wai na manta ta bane, naga ta k’ara girma ne, kuma kasan na kwana biyu ban gan ta ba".


"Ba wani nan, Nana in kin koma gida, ki fad’a ma Hajiya Faruk ya manta da autar ta".


Murmushi tayi ba tace komai ba, ta koma falo in da Maryam ke zaune ta nemi guri ta zauna.


Mus’ab ne ke fa’da ma yaya Faruk, Nana ta samu break ne a school, shine tazo taya Maryam zama kasancewar tana d’auke da juna biyu.


"gaskiya ta kyauta, Allah ya sauki Madam lafiya".


Mus’ab ya amsa da "amin".


Bayan kammala cin abincin sune, suka dawo falo a ka fara hira.


Jefi-Jefi yake sa bakin shi a cikin hirar kasancewar Magana bai dame shi ba.


lura yayi da yadda ta maida hankali akan allon Tv kamar ba ta cikin d’akin.


"Khadijah" yaya Faruk ya kira sunan ta.


Amsa masa tayi cikin sweet voice d’in ta.


"Me yasa ana hira ba ki ce komai ba"


Murmushi Nana kawai tayi tace "ba komai"


Maryam ce cikin wasa tace "ai halin ku d’aya, itama Magana ba ta dame ta ba".


Ji yayi yarinyar ta burge shi kasantuwar sanyin ta da rashin maganar ta.


"Ki ce ba tayo halin Mijin ki kamar parrot ba" cewar Yaya Faruk.


Dariya Maryam  tayi tace "nafi son haka, muyi ta hirar mu, amma kai Faruk zan so in ga matar da za ka aura, dan in ka auri mai Magana dole ka koya"


Mik’ewa yayi yana duba wrist watch d’in shi yace "za ki gan ta ne Madam, duk wacce ta aure ni, dole ta rage Magana, ni zan tafi".


Mus’ab ne yace "yanzu har za ka tafi ana hira mai dad’i, kai da kake gauro ba wanda za ka tarar a ciki".


Murmushi yayi yace "akwai abin da zan je in k’arasa ne"


Kallon Nana yayi yace "Khadija in koma gida kya gai da Hajiya ki ce sai nazo gaishe ta"


"za taji" ta fad’a a gajarce.


 Juya kallon shi ga Maryam yayi yace "Madam sai anjima"


"To sai anjima Faruk" ta amsa mishi.


Tare su ka fito suna zantawa, Mus’ab ne ya kalli Faruk cikin zolaya yace "An bani sak’o in ba ka?"


Kallon tuhuma ya mishi yace "wa ye ya baka sak’o? ya tambaye shi ganin yadda yayi maganar da tsokana.


"Hafsa ce ta bani sak’o in ba ka"?


"Wace Hafsa" ya tambaye shi.


"Kai fa shegan sama ne, amma in ba haka ba Hafsa ce ba ka gane ba, yarinyar sir Bregadier General Ahmad ce, tace in ce maka wai mai ta maka ne ba ka kula ta a chat, idan ta kira ka ba ka d’auka, sannan in kuka had’u sai kayi kamar ba ka gan ta ba".


"Baka ga yadda take maganar ba, ta bani tausayi".


Ta’be baki yayi yace "ai sai tayi ta ba ka tausayi, tun farko ai sai da na ba ta hak’uri ta kama masu son ta, ko ta nemi wani, me zanyi da yarinyar da ba ta da kamun kai, ba ma haka ba ni ba ta min ba" ya fad’a yana yatsina fuska kamar itace a gaban shi.


Cikin wasa Mus’ab yace "Kai mutumi na, tuntuni fa Hafsa take son ka, sai yanzu za kace ba ka son ta, bayan kasan tuntuni kai take jira, ka amsa query a gurin Bregadier General".


Cikin hasala yace "in amsa query akan me? Tuntuni ai na fad’a mata tayi hak’uri ta kama dahir, as to me duk macen da ta bud’i baki tace tana so na, ina mata kallon wacce ba ta san darajar kanta ba, zan dinga mata kallon za ta iya fad’a ma ko wani namiji tana son shi, in tak’aice maka zancen, bana son in yi deceiving d’in yarinyar".


Kallon shi kawai Mus’ab yake yi, sanin Faruk na fad’ar abin da ke ranshi ne kuma mai tsayawa akan Magana d’aya, don haka yace "na fahimce ka Faruk, amma shawarar da zan baka shine ka same ta ka ba ta hak’uri ta yadda za ta fahimta, kuma duk mutumin da yace yana son ka ai ya gama maka komai".


"Zanyi k’ok’arin fahimtar da ita" ya fad’a cikin ko in kula da zancen.


Mus’ab ne ya canza zancen da cewa "ya shirye shiryen tafiya Adamawa"


Wani takaici ne ya kama shi ganin a sosa mishi inda ke mishi k’aik’ayi.


"Kai dai bari Mus’ab, ai wannan tafiyar ji nake yi kamar in ce a min hak’uri ba za ni ba?"


Da mamaki Mus’ab ya tambaye shi

"saboda me?"


"Mus’ab saboda ba ta bani amsar tana so na ko ba ta so na, yanzu duk wani abu da nake gudanarwa ina yi ne da rashin sanin madafar a wani matsayi nake, ina son ta, yanzu abin da yafi damuna shine ban san yaushe za mu dawo ba?"


Mus’ab in ban da bin shi da kallo ba abin da yake yi, ya yarda so mai canza mutum, wai Faruk ne ya zauna yana doguwar Magana akan mace, lallai kam shi shaida ne akan mata ba su dame shi ba, amma yanzu gashi yana fad’an irin son da yake ma ‘yar uwar shi Fatima, ya yarda SO BABBAR CUTA ne".


"Faruk ka ci gaba da addu’a akan Allah ya za’ba maka abin da yafi alkhairi, ba na so ya zamana son da kake yi ma Fatima ya koma *MAKAUNIYAR SOYAYYA*"


"Ina yin addu’ar Mus’ab, kaima ina so ka taya ni".


"Kar ka damu Faruk, Allah ya za’ba mana mafi alkhairi".


"Amin" ya amsa yana duba agogo.


Mus’ab bari in tafi, lokaci ya ja, sai mun had’u a Officer.


Nan suka yi sallama, yayin da Mus’ab ya koma gida, shi kuma Faruk ya tafi Block d’in shi.




 *_KADUNA_* 


Yau ta kasance ranar Litinin, muna cikin class, mai mana Descriptve statistics 1 ne ya fita, bayan ya kwashe tsawon awa biyu yana mana lectures, sak’o ne ya iso gare mu cewa mai mana practical statistics ba zai samu shigo wa ba.


 Ganin muna da tsawon awa biyu free yasa k’awa ta Halima tace in zo muje mu bud’e folder a cikin asibitin poly mai suna "Shehu Muhammad Kangiwa Medical center" (SMKMC) dake cikin makarantar mu za ta ga likita.


Ko da muka isa asibitin, record room muka je aka bud’e mana folder aka bamu "Tertiary Institution social health insurance programme" (Ti-ship) card da suka bamu da zamu dinga ganin likita wanda ke nuna mu ‘yan makaranta ne, ba za anshi kud’in mu a wajen amsar magani ba (pharmacy) da wajen d’iban jini (lab), za a dinga cirewa a cikin school fees d'in mu.


Tambayar mu suka yi ko za mu ga likita ne a yanzu?

Halima ce ta amsa musu da "eh"


Ganin ta riga ta amsa musu yasa nayi tunanin in naje gurin likitan mai zan ce yana damuna tun da ni lafiya ta k’alau.


Zuciya ta ce ta bani shawarar in naje in ce menstural pain nake fama dashi, in yaso in aka bani maganin sai in ajiye tun da ina fama da ciwon maran in period d’ina ya zo.


D’aya daga cikin ma’aikatan ne ya katse min tunanin da nake yi da kiran suna na da yayi


"Fatima Ibrahim"


Amsawa nayi nace "gani"


"Ki je room 2 ki jira"


"Ok" na amsa a gajarce.


Halima M Kabir suka tura ta room 3.


Guri naje na samu a ‘bangaren room 2 d’in.


Wanda ya fito shi zai kira sunan wanda zai shiga, haka aka yi har layi yazo kaina a ka kira ni.


Knocking nayi a lokaci d’aya nayi sallama na shiga.

Amsa min sallamar yayi ba tare da ya d’ago ya kalle ni ba.


Rubutu na ga yayi a wata takarda mai kalar kwai, a jiki naga an sa Ti-ship


Me yake damun ki? ya tambaye ni.


"menstrual pain nake fama dashi" na bashi amsa.


Ci gaba da tambaya ta yayi yadda menstrual pain d’in yake min.


Rubutu ya fara yi akan wannan takarda.


A lokaci d’aya na nazarci office d’in wanda ban da k’anshi baa bin da yake yi, wani hoton Doctor d’in na gani a cikin wani d’an k’aramin frame an jingine shi akan table d’in. 


"DR ABUBAKAR SADIQ MUHAMMAD" na ga an rubuta a jikin photo d’in.


A nazarin da nayi matashi ne wanda ba zai wuce shekara 30 ba, fari ne amma bai kai farin yaya Faruk ba, matsakaici ne a jiki da kyau. A yadda nayi estimating ba zai kai tsawon yaya Faruk ba, sanye yake da lab coat na likitoci da medicated glass a fuskar shi.


"hey! Student ko ba kya jina ne? 


"Sorry Dr, ban ji bane".


Miye registration number d’in ki? Ya tambaye ni.


"KPT/CST/18/5880" na bashi amsa


Wani Department kike?

"Department of Maths & statistics"


D’ago kai yayi ya kalle ni kana yace "good course, ki ci gaba da k’ok’ari".


Dad’i ne ya kama ni jin an yabi course din mu.


"I will try my best"


Wata ‘yar madaidaiciyar takarda ya mik’o min yace "gashi ki je pharmacy ki amshi magani, Allah ya k’ara sauki".


Amsa masa nayi "amin Dr, na gode".


Fad’a min yayi wacce zan kira next sannan na fita daga office d’in.


Pharmacy na wuce na amshi magani, a can na had’u da Halima ita ma ta amshi na ta muka koma class.


Post a Comment

0 Comments