makauniyar soyayya hausa novels 5

 *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞



*STORY & WRITTEN*



    *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*






*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*






*EDIT BY*

*MRS MANSOOR*






 

*Wannan shafin naku na baku shi ne kyauta*



*Aisha* (Auta Mama)


*Maman Walida*


*Fatima Arkilla*


*Fatima Muh’d*


*Maman Baffa*


*Aisa*


*Ina tare daku na yadda kuke bin wannan novel d’in*





*TUKWICI GAREKU*


*Xarah Auwal*


*Aisha* (Auta Mama)


*Ina muku fatan alkhairi na amsar da kuka bayar daidai a Question of the day da wanda suka yi k’ok’arin ba da tasu amsar*.

*Amsar Question of the day shine, Sunan ta Ramlat ‘yar Abu sufyan, nick name d’in ta* (Ummu Habiba) *kuma itace ta tara* (9) *a cikin matan manzon Allah (s.a.w)*.


*Allah ya bamu ikon yin amfani da ilimin mu ta hanyar da ta dace ya kuma*

*k’ara mana ilimi mai amfani*.






*TUNATARWA*: 



ka/ki zamo mai hak’uri, amma kar ka/ki yadda hak’urin ya jawo maka raini.



Ka/ki zamo mai kyauta, amma kar ka/ki yadda kyautar ta jawo maka riya.


Ka/ki zamo mai soyayya, amma kada ka/ki so wani daidai soyayyarka/ki ga Allah da Manzon sa.






29&30


Washegari da misalin k’arfe hud’u da rabi, yaya Faruk ne cikin shigar shi na wani lallausan yadi mai kalar sky blue, kayan sun matuk’ar dacewa da kalar jikinsa.


Ta d’akin shi ya shiga side d’in Momi kasancewar akwai k’ofa a d’akin shi da zai iya shiga ba tare da ya fito ba.


Samun ta yayi tana kallon tashar Manara Tv a tauraron d’an adam.


Guri ya samu ya zauna kusa da ita kana ya gaishe ta.


Amsa masa tayi tana mai maida gaba d’aya hankalin ta gareshi.


"Ina za ka ne Faruk? na ga alamar kamar fita za ka yi’ Momi ta tambaye shi.


"Momi za mu d’an fita outing ne dasu Anisa, daga nan zamu biya mu d’auki Fatima" cewar yaya Faruk.


Fara’ar ta ce ta k’aru saboda yau taji dad’in yadda Faruk zai kai su gurin shak’atawa wanda a da ko zama yayi hira dasu bai dame shi ba.


"ko kai fa Faruk, gwara ka dinga jawo k’annen ka a jiki ko sa cire tsoron da suke ma ka"


"ba na jin dad’in yadda suke tsoron ka" cewar Momi.


Murmushi yayi kana ya d’aura da cewa "Momi yaran ne naga suna tashen girma, dole sai ana nuna musu hanya, amma insha Allahu zan yi k’ok’arin jawo su jiki na, nima yanzu ba na jin dad’in yadda ba sa sakewa dani".


"Momi ina Anisa ne? nace ta shirya around this time, amma naga tana so ta ‘bata min lokaci kuma tasan bana son jira"


"Tana ciki bari in kira ta a waya" Momi ta fad’a.


Kiran ta tayi akan tayi sauri yaya Faruk na jiran ta.


Momi ce ta kalli yaya Faruk cike da kulawa ta kira sunan shi.


"Umar"


Saurin d’agowa yayi ya kalle ta saboda yasan duk abin da za ta fad’a mai mahimmanci ne tun da kira shi da Asalin sunan sa.


Da sanyin murya ya amsa da "Na’am Momi".


Sai da tayi shiru kamar ba za ta yi magana ba kana ta d’aura da cewa


 "Faruk! cikar mutum ya samu a rayuwa shine ya sami  abokiyar zama, abin da nake nufi mata, idan mutm ya samu mace ta gari to ya cika rabin addinin sa".


Kallon ta yayi ganin yadda take maganar yasan abin na damun ta.


Ci gaba tayi da cewa "Faruk duk tak’amar mutum na kud’i, mulki, kyau, ilimi, nasaba da duk wani abu da mutum ya ke tunk’aho da shi, mutane ba sa ganin sa da wannan mutuncin har sai ya samu abokiyar zama sannan duk wa’innan abubuwan da na lissafo kana dasu bare ace baka da halin yin aure ne, babu yarinyar da zaka nema tayi rejecting d’in ka in har ka fad’a mata kana son ta".


"wanccan hutun da ka dawo, ni da Dadin ka mun tuntu’be ka akan maganar aure amma sai wasu excuse kake kawo mana wanda ban gamsu da su ba, idan kana da matsala ne ka fad’a min sai a samu mafita tun da naga kai abun bai damun ka"


"idan kuma idon ka har yau bai gama za’ba maka macen da ta dace dakai ba, ni ka bani za’bi, zan nemo maka a cikin familin ku ko nawa ko a k’awaye na".



Cikin ladabi yaya Faruk ya fara Magana "Momi Plss ku k’ara hak’uri, nima nasan abin na damun ku, insha Allah nan ba dad’e wa ba zan gabatar muku da yarinyar da nake so, matsalar itace har yau ban furta ma yarinyar ina son ta ba dan ba ta dad’e da gama SSCE d’in ta ba shi yasa".


Ranta ne ya fara ‘baci da yadda Faruk yake son raina musu hankali, dan haka ta fara Magana cikin ‘bacin rai "Faruk wai wacece yarinyar nan, da in an maka magana sai kace ba ka fad’a ma ta ba, what do you mean by that, kana nufin muyi ta jiran ka har sai ran da kayi niyya sannan za ka fad’a mata mu kuma muna zuba maka ido, kana nufin ba ka da confidence d’in da zaka tunkari yarinyar ne ka fad’a mata or what?


Zuba mishi ido tayi cikin ‘bacin rai dan tana son jin wace amsa zai ba ta.


"Momi pls take patient, insha Allah everything will be alright" yaya Faruk yayi maganar in a polite way.


Za ta fara mai fad’a ta ga Anisa ta fito daga d’akin ta, dan haka fasa fad’ar abin da za ta ce tayi.


Anisa ce ta tunkaro in da suke cikin shigar wata doguwar riga mai kalar bak’a, ta yafa d’an k’aramin mayafin rigar, takalmin da tasa wani flat shoe ne kalar white yayin da ta rataya side bag a hannun ta kalar white, gaskiya shigar ta amshe ta.


Kusa da Momi ta nemi guri ta zauna yayin da ta d’aura kan ta a jikin kafad’ar Momi.


"my dear you look so cute" Momi ta fad’a.


Anisa kuwa sai murmushi take yi jin Momi tace tayi kyau.


Yaya Faruk kuwa sai watsa mata wani harara yake yin da ta sa shi ya jira ta, dan shi ba abin da ya tsana irin jira.


"za ki tashi mu tafi ko sai kin gama shagwa’bar, since i was waiting for you but you waste my time, instead of you to apologise amma kin zauna za ki fara shagwa’ba".


A ranta kuwa cewa tayi "mai hali ba ya barin halin sa, gwara in bashi hak’uri mu rabu lafiya kar in ja ma kaina wani hukuncin".


A hankali ta furta "sorry yaya Faruk".


Ko sauraren ta bai yi ba illa mik’ewa da yayi yana ce wa "Momi sai mun dawo".


Anisa kuwa waving d’in hannun ta tayi tare da cewa "Momi sai mun dawo, me zan tawo miki dashi?


"Anything that is special" abin da Momi ta ce Kenan tana dariya.


Ko da suka shiga motar, hira suke yi jefi-jefi kasancewar sa ba mai yawan san Magana ba.


Parking yayi a k’ofar gidan su Fatima ba tare da ya shiga da motar ciki ba kasancewar yanzu za su shiga su fito su tafi.


Ko da suka shiga ciki, kallon Anisa yayi akan cewa taje ta ce wa Ftima ta fito su tafi, shi kuma ya nufi d’akin Ummu in yaso sai ta shigo ta gaida Ummu.


Samu na tayi a gaban dressing mirror ina sa jan baki a lip d’ina.


"haba Fatima! ya kamata ace by now kin shirya, kin san yaya Faruk ba ya son jira".


Hararar wasa na mata kana nace "yanzu ai ina jin wasa nake yi".


Dariya tayi tace "koma dai me kike yi kiyi sauri kisa kayan mu tafi".


Mik’ewa nayi na d’akko doguwar riga kalar ta Anisa, sai dai tawa an mata ado da golden colour a jiki na sa, nayi rolling da mayafin rigar, na rataya side bag kalar golden, na d’akko bak’in low past na sa.


"Wow"! gaskiya naga wannan wankan, Fatima ba ki ga kyan da kika yi ba" Anisa  ta fad’a.

 

"Duk kyan da nayi ai ban kai yake ba" na ce da ita.


"hmm haka dai kika ce Fatima, amma ko ki yadda ni dai kin min kyau".


Anisa ce ta kalli Fatima ta ce "Fatima yaya Khalil nan kuwa?


Kallon ta nayi na kya’be baki sannan na fara dariya a lokaci d’aya.


"yana nan, yau ko kin manta hanyar d’akin shi ne in miki jagora".


"to miye abin dariya daga tambaya, ko na fad’i abin da bai dace bane" Anisa ta fad’a tana ta’be baki.


"ba komai Anisa, ke da yayan ki, ai ba zai zama laifi ba dan kin tambaye shi, gani nayi kawai kamar akwai wata a k’asa".


" ke kika sani"cewar Anisa.


Tare muka fito daga d’aki na inda Anisa ta kalle ni tace "bari in lek’a gurin yaya Khalil mu gaisa sai in shigo gun Ummu mu gaisa".


Mamaki ta bani saboda yanzun nan ta gama ce min yaya Faruk na jiran mu amma gashi za ta tafi gurin yaya Khalil.


"ke ma dai kin san sauran in kika dad’e, kya same ni a d’akin Ummu zan je in yi mata sallama" na fad’a.


San da na shiga d’akin, samun ta nayi da yaya Faruk suna hira.


sallama nayi na samu guri a can gefe na zauna na d’ago na kalle shi ganin yadda yayi wani so cool.


"yaya Faruk ina wuni" na fad’a.


Shirun da naji bai amsa ba yasa na yi tunanin ko miskilancin ne ya motsa, d’aga idanun da zan yi naga ya kafe ni da idanun shi alamar yayi nisa a kallo na.


Ummu ce ta kira Sunan sa "Faruk!


Kamar wanda ya tashi daga bacci ya d’ago ya kalli Ummu.


"Ummu Magana kike yi ne" ya tambaya.


"Dama Fatima ce take gaishe ka" ta fad’a.


K’ara kallon ta yayi ya basar kamar bashi bane yake min kallon k’urilla.


"oh! lafiya, ban ji ba ne" ya amsa a gajarce.


Ta'be baki na nayi alamar kai ka Sani.


Mik’ewa yayi kana yace "Momi bari mu tafi sai mun dawo, yamma tayi".


"Sai kun dawo Faruk" Ummu ta fad’a.


Ummu ce ta kalle ni tace "Ki tashi ku tafi ma na kar yayi ta jira, wai ina Anisa ne?


"Tana d’akin Yaya Khalil, ta je su gaisa".


Sallama nayi wa Ummu, na fita daga d’akin.



A can ‘bangaren yaya Khalil kuwa, Anisa ce tayi sallama ta same shi kwance akan gado.


Amsawa yayi kana ya mik’e ya zauna yana murmushi ganin shigar da tayi yadda ta amshe ta.


"yaya Khalil ina wuni, barci kake yi ne halan".


Wani had’ad’d’en murmushi yayi ya kalle ta "Sister sai ina haka, you look so beauty".


"Tanx Bros, zamu d’an fita outing ne da yaya Faruk".


"kai Anisa, shine ba gayyata, lallai kun zama ‘yan gatan yaya Faruk, ya baku purnishment ya Kuma d’auke ku outing, dad’in ya muku yawa" ya fad’a da alamar tsokana.


"kai yaya Khalil, tun da abin ‘yar tsokana ce bari in tafi, dama na shigo ne mu gaisa".


Dariya ya fara yi yana cewa "Sorry Anisa, ni ma in na samu time zan shirya ma na outing amma ni da ke zamu je outing d’in".


Saurin juyowa tayi tace "kaima kasan ba zan iya tafiya ni kad’ai ba sai da Fatima".


" Dama tsokanar ki nake yi, ai tare zan kai ku, muje in taka miki".


""a ka bar shi yaya Khalil, d’akin Ummu zan shiga mu gaisa, ina zuwa direct nan na tawo".


"Muje dai na gaisa da yaya Faruk d’in".


D’akin Ummu ta shiga suka gaisa a gurguje kana ta fito suka jera da yaya Khalil.


Ita kuwa Fatima tun da fito, tsaya wa tayi a gefen motar, yayin da take pressing d’in wayar ta.


Yaya Faruk da ke zaune a mazaunin driver, cool music ya kunna inda sautin ke tashi a hankali.


Ganin Anisa da yaya Khalil sun a tawo wa yasa ya k’ara tamke fuska saboda yadda ta ‘bata mishi rai.


Yaya Khalil ne ya k’arasa ya mik’a masa hannu suka yi musabaha kana ya gaishe shi.


Amsawa yayi ya juya yana watsa wa Anisa banzan kallo.


Cikin ta ne ya kad’a saboda tasan abin da kallon shi yake nufi na zata fuskanci hukunci a gurin shi.


"Anisa kin raina ni ko? a gida haka ki ka ‘bata min time sannan yanzu ma kin k’ara ‘bata min time saboda kin ga na fara sakar miki fuska ko?


Cikin rawar murya ta fara Magana "ya hak’uri, na je mun gaisa da yaya Khalil ne".


"you are stupid! Sai an miki Magana ki fara ba da hak’uri".


Ya juya da kallon shi zuwa ‘bangaren yaya Khalil yana cewa "kai ma har da laifin ka, kasan ba na son jira shine ka ja ta da hira ko?


"Ayi hak’uri babban yaya, mun amsa laifin mu".


Murmushi kawai yayi ya shiga cikin motar ya kunna.


Ni kuwa dake gefe kamar ban san dramar da ake yi ba, sai aikin danna waya kawai nake yi.


Hon d’in da yayi ne yasa muka yi saurin shiga back seat muka zauna.


Wani irin kallo ya watsa mana kana yace "Uban wa kuka mai da driver da za ku zauna a baya".


Anisa ce ke faman ta’ba ni alamar in koma gaba amma nayi biris kamar ba dani take yi ba.


Jin tsawar da ya daka mana ne yasa Anisa ta fito da sauri ta na k’ok’arin bud’e gidan gaba.



Jan motar yayi da k’arfi alamar ranshi a ‘bace yake ya bar layin.

[4/1, 13:38] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞



*STORY & WRITTEN*



     *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*




*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




*Wannan shafin naku ne, masoyan yaya Faruk da Fatima*

*Ina mik’a gaisuwa ta gare ku*.




*Question of the day*


A wace surah ce Allah (s.w.t) yayi Magana akan bashi kuma Ayah ta nawa ce?

 



31&32


Tun da muka fara tafiya, na lura da yadda yaya Faruk ya saita madubun gaban shi yake kallo na akai-akai, tun abin ba ya damu na har na fara takura da kallon da yake min.


Shirun da yayi yawa ne a motar yasa na cire tsoron da nake ji na fara jan Anisa da hira saboda bazan iya zaman kurame ba, jefi-jefi yaya Faruk yana sa bakin shi a cikin hirar.


Ko da muka isa gurin, wani ke’bantaccen guri yaya Faruk ya samar mana muka zauna yayin da ya je ya siyo mana ice cream da snacks muka fara ci.


Yadda mutane ke harkar gaban su, ba ruwan kowa da kowa yasa naji gurin ya burge ni.


Wasu suna ciye-ciye, can gefe kuwa gurin hutawa ne da mutane ne ke zaune, yayin da wasu ke wajen swimming pool suna wanka, kowa dai da abin da yake yi.


Kujerar da na zauna tana opposide d’in yaya Faruk, yawan kallon da yake mun ne yasa na fara tsarguwa da kallon saboda ni ban ga dalilin kallon ba.


Tambayar kaina nayi da cewa "ko dai shigar da nayi ne ba ta dace ba? ko kuma ban yi kyau bane? na tambayi kaina, ko ma dai menene shi ya sani saboda tun a mota na lura da yadda ya tsure ni da kallo a mota".


Yaya Faruk ne ya fara da cewa "yau dai gashi na kawo ku outing, kun fita daga cikin layin wanda kuka ce ana takura ma wa ko?


Shiru muka yi ba wanda ya amsa mishi.


Ci gaba yayi da cewa "I know you will enjoy this place shi yasa na kawo ku nan, so in mun gama refreshing za ku iya zagayawa, ba na son hayaniya da mun zagaya ni da ku".


A raina nace "ba ma buk’ata, dan in ka bimu takura mana za kayi".


Mik’ewa muka yi muka fara zagaya gurin kana muka ya da zango a kujerun da aka ajiye da table a wajen swimming pool d’in dan hutawa ko refreshing, a gurin akwai kuma rest chair da aka ajiye musamman dan hutawa kafin ka fara wanka ko in ka gama wanka.


Zama muka yi muna kallon yadda mutane ke wanka a ciki.


Yaya Faruk yana can gefe kwance akan wata kujera ta hutawa yana sipping d’in  hollandia, yana kallon duk abin da ke gudana a gurin.


Wani handsome guy ne ya zo ya zauna a d’aya daga cikin kujerun da muke zaune ya mana sallama.


Amsa masa muka yi muka d’auke kan mu.


"Sannun ku da hutawa ‘yan mata" guy d’in ya fad’a.


"yawwa sannun ka"

 Anisa ta amsa a tak’aice.


"Suna na Aliyu, plsss in ba damuwa zan iya sanin sunan ku".


Wannan karan ma ban yi Magana ba illah juyawa nayi ina kallon wani side kamar ba da mu yake yi ba.


Anisa ce ta bashi amsa da cewa "ni suna na Anisa, ita kuma sunan ta Fatimah".


"wow! Nice name, Anisa in ba damuwa ina son in yi Magana da Fatima, ina neman alfarmar ki na five min zuwa ten in ba damuwa".


Murmushi tayi tace "ba matsala bari in baku guri".


Mik’ewa tayi tace "Fatima bari in je can grass carpet d’in, kya same ni a can".


Ni kuwa in ban da hararar ta ba abin da nake yi saboda yadda ta wani zauna tana bashi amsa.


"Fatima! kamar yadda na fad’a muku ne, suna na Aliyu amma zaki iya ce min Haidar, tun da na zo gurin nan na ganki na ji na kamu da son ki, ina rok’on alfarma ki ba ni guri a zuciyar ki ko na samu shiga".


Sake d’agowa nayi na kalleshi, ba laifi guy d’in bai da wani aibu amma a loakci d’aya na lura da yanayin shi kamar yana tashen samartaka ne da kud’i.


A estimating ba zai wuce ishirin da takwas ba, a shekarun haihuwa.


Murmushi nayi kana nace "Haidar na gode da son da kake min, but am sorry ni ba yanzu zan fara soyayya ba, karatu zan yi saboda ban dad’e da kammala Secondary school d’ina ba, kuma a gida ma ba za a bar ni ba"


Lokaci d’aya fuskar shi ta nuna ya shiga cikin damuwa da abin da nace mai dan haka yace "duk da kin bani uzurin ki Fatima amma ina ganin wannan ba hujjar da zaki ce ba za kiyi accepting d’ina ba, ni zan iya jiranki ki fara high institution d’in".


A raina kuwa cewa nayi "wannan daga gani zai yi naci, gwara in lalla’ba shi mu rabu lafiya".


"kayi hak’uri Haidar, ba na son in yi deceiving d’in ka, shi yasa na fito na fad’a maka gaskiya, ina maka addu’ar Allah ya baka mai son ka da gaskiya".


Yalwata murmushin shi yayi kana yace "gaskiya Fatima naji dad’in addu’ar da kika min duk da na gane kora da hali kike min, hakan yasa na gane ba k’aramin rashi nayi ba, duk da ba anshi tayin soyayya ta ba saboda na gano akwai wata baiwa da Allah ya miki, in ba damuwa zan iya samun phone number d’in ki mu dinga gaisawa tun da ba a bani damar nuna kalar soyayya ta gare ki ba, yanzu sai naje na lallashi zuciya ta, na ba ta hak’uri tun da an dasa mata ciwo".


Ganin mafita d’aya ce a gare ni a gurin Haidar shine in bashi numba ta ko na samu ya rabu dani, dan haka na fad’a mishi numba ta.


Kallo na yayi ya rausayar da kai yace "Fatima ki bani aron wayar ki in sa miki numba ta, kar in kira ki dinga ce wa waye? Ban gane mai Magana ba".


Murmushi nayi saboda a yadda na karance shi yana da ban dariya.

Waya ta na mik’a mai ba tare da nace komai ba.


Duk wannan abun da yake faruwa yaya Faruk na kallon mu har zuwa san da na mik’a ma Haidar waya ta.


Takun tafiya naji a kusa da mu, shi yasa ni d’aga kai dan ganin waye.


Ido na ne ya had’u da na yaya Faruk wanda tsantsan ‘bacin rai ne kwance a fuskar shi.


Ni in ba ido na yake min gizo ba, har wani ja na ga fuskar shi tayi, abun ka ga farin mutum, idon nan nashi ya kad’a ya koma kalar ja, jijiyoyin kanshi ko duk sun tashi.

Wani irin rawa jiki na yakama yi da bugawa da k’irji na da yake yi saboda tsoron da ya kama ni a lokaci d’aya.


"Wayyo! Naga ta kaina" na fad’i haka a raina.


Sai faman zare ido nake yi kamar wacce tayi wa sarki k’arya.


Ciikin izza ya amshi waya ta dake hannun Haidar ya maka ta a k’asa.


Tun san da yaya Faruk ya fasa min waya naji wani k’unci ya ziyarce ni da kuma tsanar sa da naji ta ka’ra shiga min a cikin zuciya, in ban da zalunci akan me zai fasa min waya, ko yana tak’amar ba ni da k’arfin rama wa shi yasa ya aikata hakan ko kuma duk cikin k’iyayyar da yake min ce? me nayi wa yaya Faruk da yake min haka? tambayar da nake ta yi wa kaina kenan.


Haidar kuwa bin shi yayi da kallo saboda ganin k’arfin halin wannan mutumin da bai san waye ba.


"Malam akan me za ka amshi waya a hannu na sannan ka fasa ba tare da wani dalili ba, hasalima ni ba sanin ka nayi ba".


Kallon rainin wayau ya mishi sannan yace "ba sai ka san ko ni waye ba da na aikata hakan, na isa ne shi yasa na aikata hakan dan nasan ba abin da zai faru".


Haidar shima ran shi ne ya ‘baci da abin da wannan mutumin ya mai saboda rainin hankali "kai waye? me kake ji dashi da za ka aikata haka sannan kana fad’a wa mutum maganar da ka gadama".


Da ‘bacin rai, yaya Fruk ya fara magana "gentle man you have to control your tongue, if not, you will face da consequences, sanin ni waye ba zai maka amfani ba saboda haka ka kula, lastly abin da zance maka shine ka fita hanyar k’anwa ta dan ba da irin kai ta dace ba saboda kaima naga har yau baka gama mallakar hankalin kan ka ba bare ka iya kula da wata ko ka bata caring irin na lovers, bayan haka ma she is a teenager, bazan bari a ‘bata mata tarbiyya ba, wannan shine gargad’in da zan maka in ka ji kenan".


Wannan maganar da yaya Faruk yayi, shi ya ba Haidar amsar tambayar shi saboda ya gano suna da alak’a da Fatima.


In a cool sound Haidar yace "Am sorry! Ban san cewa k’anwar ka bace kuma ni tsakani da Allah na ji ina son Fatima, kuma ni ba da niyyar cutar da ita nayi ba ko in yadaure ta ba kamar yadda kake nufi, sai anjiman ku".


Bai jira jin amsar da yaya Faruk zai bashi ba ya bar gurin cikin fushi.


Juyowa yayi cikin fushi ya fara Magana.


"Fatima! ki kiyaye ni, kar ki bari in nuna miki true colours d’ina, ba za ki ji dad’i na ba, yanzu abin naki ya wuce na yin chat da hoto da mazan ‘yan class ya koma kin fara kula samari at your small age? Ana so a gina muku future d’in ku amma ke ba kya ganin haka, kina amfani da yadda rayuwa take tafiya wanda hakan matsala ce, let me warn you, duk san da na sake ganin kin kula wani, hmmm zaki fuskanci hukunci mai tsanani a guri na, ki tashi mu tafi gida".


Duk wannan maganar da yake fad’a, kaina a sunkuye yake ina faman zubar da k’walla na takaici da bak’in ciki a lokaci d’aya.


Wata tsawa da ya daka min ita tasa ni tashi ban yi niyya ba saboda har cikin kaina naji ta.


Anisa kuwa dake kwance akan grass carpet can d’an nesa damu tana pressing d’in wayar, tun san da yaya Faruk ya baro gurin da yake ya k’araso gurin mu har san da ya fasa min wayar hankalin ta ya dawo kan mu.


Abin da yake mata yawo a ranta shine "mai yasa yaya Faruk ya fasa ma Fatima waya kuma da alama ranshi ya matuk’ar ‘baci, ko ma dai menene ita a ganin ta wannan bai kai laifin da zai sa ya fasa mata waya duk da ita ma ya ta’ba fasa mata waya akan ya kama ta tana yin chat".


Zuciyar ta ce ta ba ta amsa da cewa "yaya Faruk yayi hakan ne don ba yaso mu fara kula samari a yanzu wanda har yanzu kallon yara yake mana, yana so yaga mun maida hankalin mu a kan karatu".


Jiki a sanyaye na mik’e na fara tafiya kamar mai fama da rashin lafiya saboda yadda a lokaci d’aya naji jiki na ya min duk a sanadin ‘bacin rai.


Anisa da ba ta ji dad’in abin da ya faru ba yasa ta rasa mai za tace dan yadda Fatima ta hau dokin zuciya ba lallai ta saurare ta ba.


A wani bakery ya tsaya ya siyan musu ice cream da snacks.


Ko da muka shiga cikin motar ba wanda yake da k’arfin yin Magana saboda yadda ran mu yake a ‘bace.


Jin shirun yayi yawa ne yasa ya kunna k’ira’ar sheikh Al Gamidi cikin suratul Rahaman, bin surar yake yi yana jin zuciyar shi na sa mun sauk’i.


Gaskiya ne, duk wanda ya rik’e Alk’ur’ani, zai saman masa waraka da mafita a dukkan lamuran shi.


Parking yayi a k’ofar gidan mu ba tare da ya shiga ciki ba.


Fitowa nayi ba tare da nace komai ba, ko Anisa ban yi wa sallama ba, har yanzu abin da yaya Faruk ya min ya tsaya min a rai.


Bayan fita na daga mota ya kalli Anisa wacce ta rasa abin da yake mata dad’i yace "Anisa d’au ledan nan ki kai ma Fatima, ki yi ma Ummu sallama sai ki fito mu tafi".


Jiki a sanyaye ta fito daga motan ta nufi cikin gidan.


Ko da ta shiga cikin main parlour, ba ta same ni a ciki ba, direct d’aki na ta wuce.


Samu na tayi a zaune akan gado ina wani irin kuka mai ban tausayi.


Anisa cikin sanyin jiki ta zo ta zauna kusa dani ta dafa kafad’a ta ta fara da cewa "Fatima! me yasa kike kuka alhalin kin san halin yaya Faruk, ko ni ban ji dad’in yadda ya fasa miki waya ba, though shi a ganin shi wannan ce hanyar da zai yi abiding d’in mu da kar mu kula samari".


Cikin kuka na fara cewa "Anisa na gaji da abin da yaya Faruk yake min, tun ina iya daure wa har takai zuciya ta na ingiza ni akan in yi fito na fito dashi ko na samu freedom".


"why? me yasa yake son takura min? me yasa yake interfere a cikin personal life d’ina? me yasa zai yaga min hoton da na d’auka da ‘yan class d’in mu yanzu gashi ya fasa min waya, me yasa ya takura min a cikin rayuwa ta… na k’arashe maganar.


Anisa tace "wani hoto kuma ya yaga?


"hoton mu ya yaga wanda muka d’auka da mazan class d’in mu".


Anisa kuwa ba kalar tunanin da bai zo ma ta ba a ranta, a k’arshe dai ta dasa alamar tambayoyi akan abin da yasa duk Yaya Faruk yake aikata hakan.


Kuka na ci gaba da yi ina k’ara jin haushin yaya Faruk a raina.


Anisa kuwa in ban da hak’uri ba abin da take bani, k’arshe ma rok’o na tayi akan kar in fad’a ma su Ummu da Abbu, ita za ta fad’a wa Momi abin da ya faru kuma tasan za ta d’auki mataki akai sannan za ta sa yaya Faruk ya siyan min wata sabuwar waya.


Yaya Khalil ne ya shigo cikin d’akin kana yace "Anisa kije yaya Faruk na jiran ki, ina tsarabar outing?


Zaro ido tayi ta mik’e saboda ita ta manta yaya Faruk na jiran ta, yanda yake cikin ‘bacin ran nan, zai iya huce wa akan ta.


Narai-narai tayi da ido alamar za tayi kuka.


Yaya Khalil ne ya kalle ta da mamaki yace "ya akayi ne naga kamar za kiyi kuka?


" tsoro nake ji yaya Khalil kar yaya Faruk ya ta’ba ni, in ya kama ni sai na gane kure na".


Yanda tayi maganar yasa shi darawa, hango Fatima yayi sai faman shasshek’ar kuka take yi.


Kallon Anisa yayi da alamar tambaya yace "Anisa me ya samu auta naga tana faman kuka".


"ita da yaya Faruk ne" ta bashi amsa.


Ta’be baki yayi yace "Auta ta yaya Faruk Kenan, ai fad’a a shirya".


Anisa ce ta kalle ni tace "Plsss Fatima ki daina kuka, yaci ace kin saba da halin shi, ni zan tafi, sai na sake ‘bullo wa".


Ganin ko amsa mata ban yi ba yasa ta gane har yanzu ina kan dokin zuciya, dan haka tayi murmushi ta bar d’akin.


D’akin Ummu ta shiga ta mata sallama ta fito yayin da Yaya Khalil ya raka ta bakin gate, ta nufi inda Yaya Faruk yayi parking d'in mortar shi.


*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀


*STORY & WRITTEN*



     *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




*Wannan shafin tukwici ne gare ku*

*‘yan Facebook*, *mazan ku da Matan ku*

*Ina yin ku sosai na yadda kuke son wannan novel d’in*.




*KUN YI BAJINTA*


*Meeynah*


*Salmah*


*Autan mama* (Aisha matar Abdul)


*Kune kuka bayar da amsar daidai*.


*Da sauran wad’an da suka yi k’ok’arin amsa tambayar Question of the day amsar da suka bayar akan wace Surah ce a cikin Alkur’ani aka yi Magana akan bashi kuma Ayah ta nawa ce, amsar itace Suratul Baqara a cikin Ayah ta 282, wasu sunyi k’ok’arin cewa Suratul Baqara*.


*Allah ya albarkaci ilimin mu baki d’aya*.





*K’ORAFI*


*Na samu k’orafin ku da dama, wasu suna k’orafin in k’ara yawan typing, wasu kuma suna k’orafin ban a posting da wuri*.


*Na gode da k’orafin ku kuma insha Allahu zan duba, amma yanayin rashin time yasa hakan ke faruwa da kuma wasu uzuri da za su iya tasowa*.


*Da fatan za a min uzuri*.


*Na gode*.🤝🏽🤝🏽





*TUNATARWA*


Ka/ki zamo mai adalci, amma kar ka/ki ce sai ka iya wa kowa.


Ka/ki zamo me neman na kai, amma ka da yakai ka/ki ga neman haram.


Ka/ki zamo mai son iyalin ka/ki amma kada ka/ki yarda ka/ki shagala.




 

33&34


Ko da ta shiga motar, tarar da yaya Faruk tayi ya kifa kansa akan sitiyarin mota, sun d’au kusa minti biyar a haka kamar bai san da shigowar ta ba.


Anisa kuwa in ban da addu’a ba abin da take yi saboda tasan me k’watar ta a gurin yaya Faruk sai Allah, tasan tun a gida take ‘bata mishi lokaci gashi yanzu ma yace ta shiga ta kai ma Fatima ledar shopping d’in da ya musu gashi ta da’de. 


D’ago kai yayi ya mata wani banzan kallo sannan ya d’aura da cewa


 'uban me kika zauna yi a ciki bayan kin san ina jiran ki, ga driver kin samu ko? put in your mind sai kin fuskanci hukunci".


"plsss yaya Faruk kayi hak’uri! Wlh ban je da niyar zama ba, Fatima na gani tana kuka shine na tsaya ba ta hak’uri".


Jikin shi ne yayi sanyi saboda yasan shine silar da yasa Fatima kuka kuma shima yana ji a jikin sa bai kyauta wa Fatima ba amma sai ya dake ya fara Magana cikin fad’a da cewa "amma da kika tsaya ba ta hak’urin ina fatan kin had’a da goya ta, saboda ina ganin za ta fi jin lallashin da kike mata, ni kuma da kika maida d’an iska shine kika shanya ni ko?


Ita dai ba ta k’ara ce mai komai ba illa sauraran fad’an da yake ta jero mata, fatan ta su isa gida ta fad’a wa Momi duk abin da ya faru, dan gaskiya abin ya tsaya mata a rai.


A guje ya ja motar kamar wanda zai bar garin.


 parking d’in motar shi yayi a parking space, tsoron fito wa take yi kar yace ba ta jira ya fara fito wa ba.


Tsawar da ya daka mata da cewa "uban me kika tsaya yi a ciki? ko sai na zo na fito dake ne!


saboda rikicewa ba ta tsaya d’aukar ledar ba ta fito ta kwasa da gudu kamar wanda aka biyo ko murfin motar ba ta rufe ba.


Gajeran tsaki yayi a lokacin da ya ga ta bar ledan a motar, ya d’auka ya rufe motar kana ya nufi side d’in shi ta k’ofar baya.


Tana shiga cikin falon ta dinga sauke numfashi, tarad da Momi tayi zaune a falo.


Momi ce ta kalle ta tare da cewa "ke kuma lafiya zaki shigo a guje kamar wanda aka biyo".


Cikin basar da zance ta amsa da "ba komai Momi, sannu da gida".


"yau an sha yawo kenan Anisa" cewar Momi.


Kusa da ita taje ta zauna tana bata labarin gurin da suka je.


Wayar tace tayi k’ara alamar kira ya shigo.


Ganin sunan yaya Faruk yasa ta d’auke wuta kamar ba ita ke ba da labari ba.


"ki same ni a d’aki na" abin da yaya Faruk yace kenan ya katse wayar.


Cikin sanyin jiki ta mik’e tana cewa Momi "bari in je d’akin yaya Faruk ya na kira na".


"Ok" momi ta amsa a gajarce. 


Samun shi tayi zaune akan rest chair, yana sanye da vest da three quarter.


Sallama tayi ta shiga d’akin, ta nemi guri ta zauna.


Amsa mata sallamar yayi kamar ba ya so.


Taso wa yayi ya d’au d’an k’aramin cup dake ajiye akan fridge d’in shi ya kama hannun ta ba tare da yayi mata Magana ba.


Bin shi kawai take yi ba tare da tasan in da za su je ba.


K’ofar baya ya bud’e ya nufi wajen flowers d’in dake cikin gidan.


Tambaya take ma kan ta "me za su yi anan da taga ya d’akko kofi ya kawo ta nan".


Kallon ta yayi cikin d’aurewar fuska yace "je ki d’akko waccen bucket d’in na wajen tap d’in can".


"dakko wa tayi tare da cewa "gashi yaya Faruk".


Mik’a mata kofin yayi yace "wannan kofin da na baki shi zaki yi amfani ki cika min wannan bucket d’in, wannan shine purnishment d’in ki for today na ‘bata min time da kika yi".


Saurin kallon k’aton bucket d’in tayi da kuma d’an k’aramin kofin da ke hannun ta, da ratar in da tap d’in yake da wajen bucket d’in.


Tunanin ya za tayi ta cika wannan bucket d’in take yi da d’an k’aramin kofin nan?


"za ki fara ko sai jikin ki ya fad’a miki, ba na son ‘bata lokaci".


Hawaye ne ya fara ambaliya a fuskar ta.


Kallon ta yayi yace "will u wipe your tears & start your work".


Tap d’in ta nufa ta fara tarawa kana tazo ta juye a cikin wannan bucket d’in.


Kujera ya samu ya zauna ya d’aura k’afa d’aya akan d’aya yana sauraren cool music a wayar shi.


Haka Anisa ta dinga d’iban ruwa a cup tana juyewa a wannan bucket d’in.


Momi kuwa da taji shirun yayi yawa yasa ta mik’e ta nufi side d’in yaya Faruk.


Ko da ta shiga ba ta tarad dasu a ciki ba.


Momi ce ta tambayi kan ta da cewa "ina suka tafi kuma".


Ta glass window ta hango su a gurin flowers.


Ta k’ofar d’akin yaya Faruk ta fito ba tare da ta koma side d’in ta ba.


Anisa wacce saboda jeka ka dawo d’in da take yi yasa taji k’afar ta rik’e mata gashi ko rabin bucket d’in ba ta cika ba.


Hawaye ne ke ta zuba a idon ta amma yaya Faruk bai da alamar tausaya mata, sai ma rausayar da kanshi da yake yi alamar yana jin dad’in music d’in da yasa.


Momi ce ta k’araso da sauri tana cewa


 "me zan gani Faruk! me ta maka da zaka ba ta such kind of purnishment irin wannan daga dawowar ta".


Cikin sanyi yayi magana "Sorry Mom, laifi ta min shi yasa".


Anisa kuwa in ban da filling d’in bucket d’in ba abin da take yi, taji dad’i da Allah ya kawo Momi a lokacin, ko ba komai tasan yanzu zai kyale ta.


Momi ta kalli Anisa cikin tausayawa tace "Anisa stop that work!


Anisa da kamar jira take yi tayi saurin ajiye kofin ta tawo gurin Momi.


Juyawa tayi ta kalli yaya Faruk cikin fad’a taci gaba da cewa "Faruk! am warning you amma ba ka ji, ka daina ba su irin wannan purnishment d’in saboda kasancewar su mata amma ka k’i ji, A wani dalilin za ka sa ta cika ruwa a wannan big bucket d’in da ‘dan k’aramin cup d’in, bayan kasan kan ta cika sai ta wahala, to ni ‘ya ta ba ta iya aikin wahala ba, ka kiyaye ni Faruk in ba haka ba zan sa’ba maka".


"Sorry Mom" abin da yace kenan.


A lokaci d’aya yana jin ‘bacin rai na yadda Momi za ta mishi fad’a a gaban k’anwar shi, salon ta raina shi.


Hannun Anisa kawai Momi ta kama suka nufi side d’in su.


A can ‘bangaren Fatima kuwa, yaya Khalil ne ya kalli Fatima wacce ke faman kuka yace "Wai Fatima me yaya Faruk ya miki ne haka da kike faman wannan kukan'.


Fatima cikin shasshek’ar kuka tace "plss yaya Khalil, help me ask yaya Faruk what have i done to him da yake min irin wannan hukuncin?


"tell me abin da ya miki" ya fad’a cikin hasala.


Zayyane masa duk abin da ya faru tayi a outing d’in da suka fita.


Shiru yayi yana kallon ta sannan yace "Fatima ba wai yaya Faruk bai yi laifi bane da ya fasa miki waya, ina so ki sani shi yaya Faruk matuk’ar ka kiyaye dokikin shi za ku zauna lafiya, yana son ci gaban ku na son ku ci gaba da ilimi shi yasa yake lura da takun ku, ku ke ganin kamar ya takura muku ne, tun da ya nuna ba ya son ku fara soyayya, ya kamata ace kin kiyaye dokokin".


Kallon shi nayi da mamaki nace "are my not big da ba zan kula saurayi ba? infact ni ba ni na kira shi ba, after all ni ban yi accepting d’in shi ba, yaya Khalil mai yasa da yazo bai tambaye ni ba, sai ma fasa min waya da yayi".


"Fatima! ya kamata ki d’auki yaya Faruk a matsayin wa a gare ki kamar yadda ni da yaya Aminu muke a gurin ki, duk abin da zai miki ki barshi a matsayin ke k’anwar shi ce kamar Anisa, kin fahimce ni ko?


D’aga mishi kai tayi alamar eh.


'yawwa Auta, share hawayen ki, ni zan siyan miki irin taki ta da".


Goge hawaye na nayi ina murmushi, sai naji na samu relief akan abin da ya faru.


***************************

Momi kuwa direct d’akinta ta tafi da Anisa tana ci gaba da fad’a.


Anisa wacce ta kwanta a jikin Momi sai faman ajiyar zuciya take sauke wa kamar wacce tayi gudu.


"Mtsww" Momi ta ja wani gajeren tsaki.


"Wai me kika mai ne ya baki wannan purnishment d’in?

 Momi ta tambaye ta.


"Akan yace in kai wa Fatima ledar shopping d’in da ya mana cikin gida, shine da na shiga sai na tarar da ita tana kuka, ni kuma na tsaya ba ta hakk’uri ban fito da wuri ba, da na shiga mota shine yace sai ya bani purnishment" Anisa ta fad’a cikin shagwa’ba.


"To ita Fatima me aka mata take kuka" Momi ta tambaya.


Nan Anisa ta kwashe duk abin da ya faru ta fad’a wa Momi.


Momi wanda ranta ya gama ‘baci da labarin da Anisa ta gama ba ta tace


 'Akan wani dalili zai yaga mata hotuna ya kuma fasa mata waya saboda ta kula saurayi? Ni kaina na gaji da irin wannan abin da Faruk yake yi amma zanyi maganin shi, dole ne ya fito da mata yayi aure saboda ina ganin har da rashin aure yake sa shi yin wannan abubuwan, in ba haka ba zai gamu da ‘bacin rai na".


"ina zuwa" abin da Momi tace wa Anisa kenan ta bar d’akin.



Shi kuwa Faruk tun da ya shiga d’aki ya rasa me ke masa dad’i.


"me yasa ban tsaya ta min bayani ba na fasa ma ta waya? Why? me yasa zuciya ta take ingiza ni akan d’aukan mataki akan ta? bai kamata ina taking action cikin zafin rai ba dan ba abin da zai jawo sai ‘bacin rai".


Yana cikin wannan tunanin Momi ta shigo cikin ‘bacin rai.


Kallon shi tayi ta kira sunan sa


 "Faruk"


Saita kansa yayi ya amsa "Na’am Momi".



"Faruk akan wani dalili ka yaga ma su Fatima hotunan graduation alhalin kasan na tarihi ne, hotunan ne suka d’auka bai dace ba ko ganin ra’ayin kanka ne yasa ka yaga? Sannan duk wannan bai ishe ka ba shine sai ka fasa mata waya akan ta had’u da wani a inda kuka je? ina so ka fad’a min dalilin ka na yin haka?.


zuciyar shi ce ke umartar shi da ya fad’a mata dalilin shi nayin hakan amma yana ganin da sauran time, sabida haka yace "Momi kiyi hak’uri, yarinyar ce naga tana da rawar kai".


"kid’an kai take dashi ba rawar kai ba, ka fita hanya ta Faruk, akan irin hukuncin da kake musu zan sa’ba maka, mata kowa yasan lalla’ba su ake yi, ni ba ina nufin kar ka hukunta su ba ne in suka yi laifi, ya zamana akwai lokacin hukunci da kuma wasa".

Ci gaba yayi da cewa

"yanzu abin da nake so dakai shine ka siya mata wata sabuwar wayar ka kai mata, sannan maganar mu ta d’azun akan maganar auren ka ba wai na manta bane, in Dadin ka yaga zai iya zira maka ido akan rashin auren ka to ni a zan iya ba, na baka nan da d’an wani lokaci kafin ka koma aiki in ba haka ba zan baka mamaki in za’ba maka".


Ba ta jira jin cewar shi ba ta fita daga d’akin.


Kan shi ya dafa wanda yake ji ya mishi nauyi.


Kwantawa yayi akan gado yana kallan sama wanda ke nuni da ya fad’a tunani.


"ya zama dole ya samar wa kanshi mafita a ‘bangare biyu, yanzu gashi Momi ta taso shi gaba akan zancen yarinyar da yake so bayan har yau bai furta wa yarinyar yana son ta ba, yanzu ya zai yi?


Ya zamar mishi dole ya d’auki za’bi a d’aya a cikin biyu, ko dai ya fad’a ma yarinyar ko kuma Momi ta za’ba mishi yarinyar da ta mata kamar yadda take furta wa.


Yau kwana biyu kenan rabon yaya Faruk da gidan mu, sai hakan ya min dad’i.



Da yammaci ina zaune a wani ke’battaccen guri da akayi shi dan hutawa, inda aka ajiye kujeru da ta table, yayin da aka yi wata ‘yar bukka a sama.


 Pineapple-cocunut drinks ne a gaba na ina sipping a lokaci d’aya ina pressing d’in I-pad d’in yaya Khalil da ke hannu na.


Jin shigowar mota yasa na d’aga kai na kalla dan ganin wanda zai shigo..


Ganin Motar yaya Faruk ce yasa na kau da kaina na ci gaba da abin da nake yi.


Parking d’in motar shi yayi a parking space.


Hango ni yayi a gurin shak’atawa yasa ya nufo gurin.


Guri na naga ya na tawowa rike da wata leda a hannun shi, tamke fuska nayi dan ban san kuma da mai yazo ba.


Sallama ya min ya nemi d’aya daga cikin kujerun ya zauna.


In ban da amsa sallama dole ce da ban ga abin da zai sa ni in amsa mishi sallamar ba.


Ciki-ciki na amsa sallamar kamar ba na so kana na gaishe shi wanda ko ni nasan ba lallai bane in ya ji gaisuwar da na mishi.


Ga mamaki na sai naji ya amsa da "lfy lau Fatima, ya hak’uri da ni?


A raina kuwa cewa nayi "ji wani tambayar rainin wayau da yake min, hak’uri da kai sai dole dan ba yadda mutum zai yi dakai ne, amma da sai na rama abin da kake min".


Sanin ba zan bashi amsa ba yasa yayi murmushi.


"Fatima" ya kira suna na a hankali.


D’ago wa nayi na kalle shi ba tare da na amsa ba.


Ci gaba yayi da cewa "nasan kina jin haushin abin da na miki ran da muka fita ko? kina d’auka na a mara adalci wanda yake k’ok’arin matsa miki, a guri na ba haka na d’auka ba, du kina miki haka ne ke da Anisa dan ganin yadda yanzu rayuwa ta koma, nasan nan gaba za ku gane hakan, za kuma kisan dalilin da yasa nake miki haka, anyway ga wata sabuwar waya na kawo miki, ina fatan za ki min uzuri akan wayar ki da na fasa".


Mik’o min wayar yayi na k’i amsa saboda yadda zuciya ta ke tuno min san da ya fasa min d’ayar wayar inda a gani na ko zai yi amfani da wannan damar ne ya samu hanyar k’ara cusguna min.


Wata zuciyar kuwa ingiza ni take yi akan in amsa tun da shi ya fasa min wayar.


"Fatima, ba ki da wani za’bi da yafi ki amshi wayar nan, dan ba zan koma da ita ba" abin da yaya Faruk yace kenan.


Ba ni da za’bi da ya wuce in amshi wayar dan nasan kafiyar shi.


"Na gode" na furta mai a gajarce.


"No need to thank me Teemah, komai zan iya miki ke da Anisa saboda ku k’anne na ne".


"kamar gaske" abin da nace a raina kenan.


Jin kiran sallar magrib yasa yaya Faruk ya mik’e da niyyar tafiya masallaci, ni kuma na koma cikin gida.


Ko da na shiga d’aki, kwalin wayar na bud’e naga model d’in wayar Tecno K7, ko ba a fad’a min ba nasan babbar tawa ce saboda ni a da ina rik’e Tecno W4 ne.


Dad’ i ne ya kama ni, ganin na samu promotion.


Bayan sallar magrib ne na ji shigowar yaya Faruk da yaya Aminu, da alama had’uwa suka yi gurin shigowa.


Zama na nayi a d’aki yayin da na jona sabuwar waya ta a charge.


Ban fito ba sai da nayi sallar isha’i dan nasa yanzu Abbu zai fara tambaya ta.


Zama nayi akan kujera ina jiran fitowar su, shigowar yaya Aminu da yaya Faruk ne ya katse min shirun da nayi.


Guri su ka nema suka zauna yayin da yaya Aminu ya kalle ni.


Da sauri nace "sannun ku da hutawa, ina wuni yaya Aminu" saboda nasan yanzu sai ya fara min fad’a dan shi ma kamar yaya Faruk yake, sai dai shi ya fi shi hak’uri.


"wai dama kina cikin gidan nan tun d’azun amma ban ji motsin ki ba" yaya Aminu ya tambaye ni.


"ina ciki, ina yin wani abu ne a ciki" na ba shi amsa.


"yayi kyau"abin da yace kenan, ya juya ga yaya Faruk suka ci gaba da hira.


Shi kuwa yaya Faruk tun san da yaya Aminu ya fara min Magana naga ya maida hankalin shi kaina, ko me yake so ya gano? Oho mishi.


Ummu ce da Abbu suka zauna aka ci gaba da hirar dasu, duk hirar da suke yi sauraren su nake yi kamar ba na gurin ganin yaya Khalil ba ya nan, sai naji hirar ta ginshe ni.


Ummu ce ta umarce ni da in d’akko food flask akan dinning a ci abincin a falo ba sai an koma kan dinning ba.


Serving d’in kowa nayi na nemi guri na zauna nima na fara cin abincin.


Muna cikin cin abincin ne yaya Kalil ya shigo parlour d’in yayi sallama.


Amsa masa muka yi kana yazo kusa dani ya zauna.


sannu da gida yayi wa Abbu da Ummu, ya gaisa da su yaya Aminu.


Spoon d’in shi yasa a cikin abincin na muna ci muna hira k’asa k’asa.


Bayan Abbu ya gama cin abincin ne ya kalli yaya Faruk ya kira sunan sa


 "Faruk".


Tattaro hankalin shi yayi ya mik’a shi ga Abbu dan jin mai zai ce mai.


Abbu ne yaci gaba da cewa "Lokaci yayi da ya kamata ace ka ajiye abokiyar zama, rayuwa ba za ta tafi ba sai da abokiyar zama, ya kamata ka bincika ka samo matar, kai kan ka za ka fi jin dad’in aikin ka da mu’amalar ka da mutane".


Had’a ido muka yi a lokacin da Abbu yake mai magana, ganin kallon da yake min ne yasa na kau da fuska ta.


Cikin ladabi yace "insha Allahu Abbu na kusa fito da matar da zan aura, akwai abin da ya tsayar dani ne shi yasa, amma a taya mu da addu’a".


"Ana nan ana muku Faruk, Allah ya za’ba muku na gari da kai da ‘yan uwan ka". Abbu yace dashi.


Yaya Faruk ne ya amsa "Amin Abbu" .


Nan ita ma Ummu tayi ta mishi nasiha akan ya kamata ya fito da matar aure..


A raina kuwa cewa nayi "mutum ya girma amma yak’i yin aure ko mai yake jira? Gwara ma Allah yayi ya kawo mishi matar yayi auren ko ma samu sauk’i".


Ummu ce da Abbu suka mik’e suka mana sallama, suka nufi side d’in su.


Yaya Khalil ma sallama ya mana ya tafi d’akin shi saboda yace min yau bacci yake ji da wuri.

Ya rage daga ni sai su yaya Aminu muka rage a falon.


Post a Comment

0 Comments