MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
*Wannan shafin na ki ne*
*Fauxia MB*
*Ba za ki ji mutuwar sarki a baki na ba*, *na labarin Teema da yaya Faruk*, *kuma ni ban san wake yin makauniyar soyayya a cikin su ba*, *LOKACI NE da zai nuna hakan*
*JINJINA GA*
*Batul Adam A Jatko* (Damata)
*Hauwa A Usman* (Wani Al’amari)
*Ina taya ku murnar kammala novel d’in ku wanda yake d’auke da darasi*.
*Na ya ba muku na yadda ku ka ja zaren labarin ku dan isar da sak’wanni ga mutane*.
*Sai mun ji ku a new novels d’in ku*.
*GAISUWA GA*
*Ummu Fadlu*
*Ameenatou*
*Na amsar da ku ka bayar daidai a Question of the day na cewa A cikin matan manzon Allah (s.a.w) wanda Allah ya d’aura musu aure a sama ita ce Zainab bnt Jash*.
*Allah ya k’ara ilimi mai amfani*.
*Tunatarwa*
Har kullum idan ka na so ka ci nasara a rayuwa, ka/ki fara wanke zuciyar ki kafin jikin ka/ki, kuma ka/ki wanke harshen ka/ki kafin hannun ka/ki, sannan ka/ki kyautata zato ga mutane.
21&22
Yau kwana biyu kenan da yin graduation d’in mu. Ina kwance akan gado ina karanta wani online novel mai suna ‘behind our love’ littafin ya min dad’i kuma marubuciyar tayi matuk’ar k’ok’ari a wajen salon rubutun na ta.
Waya ta ce tayi k’ara wanda ya katse min karatun da nake yi, sunan Aisha friend da na gani a jikin screen d’ina shi yasa ni sakan murmushi
D’auka nayi tare da cewa "Hi Aisha ykk?
amsa min tayi da "normal! Kina gida ne?
amsa mata da nayi "ina gida za ki zo ne?na tambaye ta.
"yeah! Zan zo, naje school ne saboda hotunan da muka d’auka an wanke mana da kuma copy d’in video d’in, sai na zo" Aisha ta fad’a.
"Ok sai kin zo" na ce da ita.
Nan muka yi sallama da ita kana na ci gaba da karanta novel d’ina.
Around one pm, sai ga Aisha tazo, nayi murnar zuwan ta dan haka ina kai ta side d’in Ummu suka gaisa muka wuce d’aki na.
Nan muka dasa hirar makaranta kamar wanda muka dad’e ba mu had’u ba, a lokaci d’aya muna duba pictures d’in mu na graduation d’in mu wanda suka yi matuk’ar kyau.
Aisha sai da takai kusan k’arfe uku sannan ta min sallama ta tafi tare da ma ta alk’awarin insha Allah ina nan zuwa saboda tace sai tazo sau nawa ban zo sau d’aya ba.
Yaya Khalil ne yazo ya same ni a d’aki yana cewa "Sister me kike yi ne a d’aki naji ki shiru?
"yawwa Yaya Khalil zo ka ga hotunan mu na graduation da video d’in da aka yi na event a ranar graduation d’in mu".
Zama yayi ya kalli hotunan yana tambaya na wasu daga cikin ‘yan class d’in mu da ya ga mun d’auka tare,
ni kuma ina mishi bayanin su, ya fara kallan video d’in ne ya duba wrist watch d’in shi ya na cewa "Sis bari in je parlour akwai wani program da zan kalla yanzu, in ya so kya ba ni labari duk da ban samu attending d’in graduation d’in ku ba saboda test da muke fama dashi" yaya Khalil ya fad’a.
"Ok bros" na fad’a da alamar zolaya.
Ficewa daga d’akin yayi yana cewa "that is my Sister".
Gaskiya sai yanzu na ji dad’in graduation d’in mu saboda wasu abubuwan sai a kaset na ga sun burge ni.
A cikin video d’in akwai wani dancing step da muka gabatar wanda namiji da mace za a sa masu cool music su fito su taka sannan wasu sai su sake shigo wa.
A cikin wanda suka yi participating har da ni a ciki, ni da wani Kabir d’an class d’in mu a ka saka mana music d'in muka rausaya, step d’in da muka bayar ni kaina sai da ya burge ni.
murmushi nayi sabo da ji nayi kamar mu k’ara yin graduation d’in.
Jiki na ne ya bani kamar ana kallo na dan haka na juya na kalli saitin k’ofar dake d’akin.
Wani irin razana da nayi ban san lokacin da jiki na ya fara rawa ba saboda wanda na gani, da kyar nake had’iye miyau a baki na saboda yanda naji mak’ogwaro na ya bushe.
Yaya Faruk ne a tsaye da uniform d’in shi na soja, yau gani nake yi kamar yafi ko yaushe d’aure wa saboda yau har idon shi sai da naga ya kad’a saboda ‘bacin rai.
Takowa ya fara yi cikin k’asaita yana tunkaro ni, matsa wa nayi kusa da gefen gado saboda ni yau tsoron shi nake ji, ga kuma laifin da na mishi a chatting.
Hotunan da muka d’auka da ‘yan class d’in mu ya d’auka yana kalla, wasu na d’auka da mazan class d’in mu, wasu kuma ni da ‘yan matan class d’in mu.
Cikin ‘bacin rai naga ya ajiye wanda na d’auka ni kad’ai da Wanda na d'auka da Anisa sai Wanda na d'auka da k'awaye na.
Ya d’au sauran ya yaga.
Wani ‘bacin rai ne ya kama ni ganin abin yaya Faruk ya wuce misali don ko a lokacin mulkin mallaka sai haka.
cikin ‘bacin rai nace "yaya me yasa za ka yaga min bayan su kad’ai ne copies d’in da nake dashi".
Lafiyayyen marin da naji a fuska ta shi yasa ni d’ago wa na kalle shi saboda ni dai a tunani na ban ga wata kalma da na fad’a mai da bai dace ba"
Wani tsanar yaya Faruk ne ya kama ni a lokaci guda saboda ni a gani na tsantsan tsana yake nuna min.
Cikin tsiwa na ce "yaya Faruk mai na maka ka mare ni!
Wani marin na k’ara ji a fuska na wanda yafi na farkon zafi wanda yasa ni gigita.
Wani abu na ji ya tok’are min k’irji wanda daga ji kasan na bak’in ciki ne da takaici don haka hawaye ne ya fara zubo min daga idanu na.
Ganin in na ci gaba da mayar mai ni ce zan wahala saboda nasan yanzu sai ya jibge ni a banza.
Cikin ‘bacin rai ya fara Magana yana cewa "wallahi Fatimah ki kiyaye ni! ina raga maki ne saboda wasu dalilai amma naga ke baki san haka ba! na ga kina tashen rashin kunya kuma kin san na tsani raini, ban da rashin kunyar da kika min a chatting sannan nazo naga video d’in ku na graduation d’in ku, kina rawa da wani d’an iskan classmate d’in ku alamar you a marture enough sannan kina d’aukan hoton da maza, sannan had kina da confidence d'in tambaya ta, you must be stupid".
Yaci gaba da cewa " idan zan hukunta ki sai kin ce anya ni d’an uwan ki ne amma tun da kin fi so in fito miki ta haka zan aikata hakan gare ki dan naga alamar kin manta ni".
Yana gama fad’in haka ya fita daga d’akin, ko kallon yaya Khalil bai yi ba da ke zaune a kujera a falo ya fice daga gidan dan ko sallama da Ummu bai yi ba.
Bayan fitar shi ne na afka cikin tunani saboda ni a gaskiya ban ga laifi ko rashin kunyar da na mai ba da yake min wannan fad’an kamar ya ari baki, dama ni na lura yaya Faruk ba ya k’auna ta dan haka nima a yanzu na d’aura d’ammarar fito na fito dashi duk nasan bazan ci riba ba amma dole ne in nuna mai nima ban sa shi a ka ba.
Hawaye ne yaci gaba da biyo min saboda har yau jin zuciya ta nake yi tana min zafi.
Shigowar yaya Khalil ne yasa na d’ago na kalle shi da idanu na wanda suka yi ja saboda ‘bacin rai.
Zuwa yayi ya zauna a guri na bai ce min komai ba illa kallo na da yake yi.
fad’awa jikin shi nayi ina kuka saboda nasan shi zan fad’a wa damuwa ta kuma shine mai share min hawaye na.
Cikin lallashi yake cewa "is ok Fatima! Ki daina kukan and tell me mai ya faru? tsakanin ki da yaya Faruk naga ya fita cikin fushi".
Ci gaba nayi da kuka ina cewa "ni ban san mai nayi wa yaya Faruk ba ya tsane ni, abu kad’an sai ya kama min fad’a ko ya bani purnishment, kuma ba hali in fad’a saboda nasan ba mai ba ni gaskiya…"
Katse ni yayi da cewa "keep that aside and tell me what is going on".
Fad’a mishi komai nayi tun daga chatting d’in da muka yi da kuma yaga min hotuna da yayi da kuma abin da yace min.
Shiru yaya Khalil yayi kamar ba zai ce komai ba, can ya kalle ni yace "Sister duk abin da yaya Faruk yake miki may be yana da dalilin yin shi saboda haka in ya dawo ki bashi hak’uri akan abin da kika ce mai a chatting da kuka bayar shi da kika yi akan me yasa ya mare ki, beside yaya Faruk zai iya hukunta kowa a family d’in nan.
Cikin ‘bacin rai na ce "akan me zan bashi hak’uri bayan shi kullum burin shi ya takura min".
Murmushi kawai yayi ya ce "do as i say Fatimah".
Nodding d’in kaina nayi amma a zuciya ta na k’udurta cewa bazan bashi hak’uri ba saboda in sa’bawa ne ni aka yi wa laifi ba shi ba".
Da haka muka bar zancen, muka ci gaba da wata hirar kamar ba abin da ke damu na.
[3/23, 13:03] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
*Wannan shafin naku ne, ina godiya da yadda kuke bin wannan novel d’in*.
*Ina muku fatan alkhairi gare ku*.🤝🏽
*Zinatu gatari*
*Amina Samaru*
*Mmn Shaheeda*
*Rahmatu Jaafar*
*Mom Affan*
*Ikram 202*
*Asiya Paki (‘yar garin mu)*
*Meeynarh*
*Question of the day*
An tambayi manzon Allah (s.a.w) a cikin maza wa yafi so? Sunan wa annabi Muhammad (s.a.w) ya ambata?
23&24
Shi kuwa a ‘bangaren yaya Faruk, yana fita daga gidan ya fad’a cikin motar shi ya ba ta wuta.
Ko da ya isa gida bai tsaya yin parking d’in motar a ma’adanar motoci ba ya fad’a cikin gida.
Anisa ce zaune a parlour tana yanke fingers d’in ta da nail cutter a lokaci d’aya ta sa cool music tana saurara ta cikin home theater speaker d’in dake parlour.
Sallama yayi a ciki-ciki wanda in dai ba ka lura da motsin bakin shi ba, ba za kace Magana yayi ba.
Anisa wacce hankalin ta ke kan yanke fingers d’in ta, ba ta lura da shigowar shi ba sai takun tafiyar shi da taji a kusa da ita.
D’agowa tayi ta kalle shi tare da lura da yanayin da yake ciki kamar yana cikin damuwa amma ba halin tambaya dan yanzu sai ya hau ta da fad’a.
"Yaya sannu da zuwa" Anisa ta fad’a.
Wani kallo da ya ma ta sai da gaban ta ya fad’i saboda tasan ruwa ba ya tsami banza.
D’akin ya d’au shiru na ‘yan mintina kana yaya Faruk ya fara magana cikin fushi tare da cewa "Anisa bi ki ji san da nayi sallama ba ne ko ke ma za ki nuna min kin kawo k’arfin kan ki ne?
Cikin sanyi murya tace ‘sorry yaya Faruk ban ji bane".
D’akko min copies d’in hotunan da kuka yi ranar graduation d’in ku!
Cikin mamaki tace "yana gurin Fatimah saboda d’azun ta kira ni tace friend d’in mu ta kawo mana".
Ci gaba yayi da cewa "kuna ganin ku kun girma ko da har zaku d’auki hotuna da maza ko? har wani dancing step kuka yi saboda kuna tashen girma, bari in fad’a miki kiji, duk san da na gan ku da saurayi ko kuna zance, hmmm a ranar sunan ku sorry dan sai na kai ku kwata kun kamo kifin oga, ban da sauran purnishment da zan baku iri iri saboda kun ga ina k’yale ku shine kuke yin abin da kuke so".
Ya ci gaba da cewa "yanzu ma saboda tsabar iskanci kina ji nayi sallama amma bi ki amsa min ba, wato ga d’an isa ko? ya kalle ta yana jiran amsa.
Anisa ko da ta fad’a cikin tunani sabida a tunanin ta ba ta san me ya ‘bata mai rai da zai zo ya huce a kan ta kuma ya aka yi yasan sunyi hoto da ‘yan class d’in su? Ko dai ya je gidan su Fatimah ne!
To in ban da abin yaya Faruq menene laifi dan sun d’au hoto da ‘yan class d’in su? Abin da ake yin shi na rana d’aya saboda tarihi.
Tsawar da ya daka mata ita tasa ta yanke tunanin da take yi.
"Kayi hak’uri yaya Faruk ban ji sallamar ka bane shi yasa" Anisa ta fad'a.
Wani gajeran tsaki ya ja ba tare da yayi Magana ba, ya nufi side d’in shi.
Tun tafiyar yaya Faruk d’aki, Anisa ke mamakin shi saboda ita dai a iya sanin ta ba ya shaye-shaye bare tace ko a buge yake, ita ko taba bata ga yana sha ba.
To ko dai allurar sojan ce ta motsa? Wannan ne ba ta da amsar shi.
Wani sa’in in ya zauna yana d’an jan ta da hira ba k’aramin dad’i take ji ba, saboda d’an uwa rabin jiki ne, hasali ma shi kad’ai ne wanda iyayen su suka haifa.
Addu’ar ta shine Allah yasa yayi aure ko ya rage fad’an da yake yi.
Yaya Faruk kuwa yana shiga d’aki ya fara kaiwa da komowa kamar wanda yake training.
Sak’a da warwara yake yi duk akan mafita da yake nemar wa kan sa don in har bai d’au mataki ba yana ganin zai iya fad’a wa a cikin rami..
Marin da ya min ne yake mishi gizo a idanun shi kamar a time d’in ne ya mare ta.
Hannun shi yakai ma naushi kamar shine ya mishi laifi.
Zuciyar shi ce ta fara raya mishi akan cewa me yasa ya mare ta? hakan ba zai jawo ta k’ara jin haushin shi ba, tun da ita a tunanin ta yana matsa mata ne?.
A fili yake fad’in "why? me yasa na mare ta? me yasa ban yi controlling d’in temper d’ina ba? duk wannan tambayoyi ne yake yi wa kanshi wanda ba su da amsa.
Hannun shi ya d’aura a kanshi wanda yake faman yi mishi ciwo.
Zuciyar shi ce yaji tana bashi command akan cewa yaje ya ba ta hak’uri ko ya samu sauk’in rad’ad’in da take mishi.
Wata kuma zuciyar na ingiza shi akan cewa kar yaje, saboda hakan zai iya jawo wa ta raina shi wanda shi kuma ba ya fatan hakan ta kasance a gare shi saboda in akwai abin da ya tsana bai wuce raini da wulak’anci ba.
Ganin bai samu mafita ba yasa ya tashi ya shiga wanka ko ya samu relief akan abin da yake damun shi.
Bayan ya fito wanka ne ya d’akko t-shirt da jeans yasa, ya d’auki kwalin exotic a fridge kasancewar shine favourite drinks d’in shi dan haka ba ya rabo dashi a fridge, ya nufi garden d’in gidan.
Sipping d’in exotic d’in yake yi a lokaci d’aya yana danna wayar dake hannun shi.
Tunanin d’azun ne ya k’ara dawo mishi a karo na biyu akan cewa yaje ya ba Fatimah hak’uri ko da yana ganin hakan na nufin girman shi zai zube a gurin ta saboda yanayin rawar kanta da yaga tana fama dashi.
*(Hmm to nima dai na k’osa in samo amsar a gurin yaya Faruk saboda zargi ne kala- kala a raina*
*Amma dai bari in bishi sannu a hankali saboda nasan amsar na nan tafe)*
Ganin tunanin bai da wani amfani a gare shi illah wani damuwar da zai k’ara mai, shi yasa ya tashi ya nufi side d’in Momi wacce ke zaune a 2-sitter rik’e da littafi da biro a hannun ta, da alama wani abu mai mahimmanci take yi.
Yaya Faruk ne yayi sallama yazo ya zauna kusa da ita yana lumshe ido kamar wanda yake jin bacci.
Amsa masa sallamar tayi kana ta maida hankalin ta gare shi.
"Faruk! ta kira sunan shi.
Cikin husky voice d’in shi ya amsa mata da "na'am Momi, Sannu da hutawa".
Momi ce ta nazarce shi a cikin ‘yan mintuna sannan tace "Faruk! what is wrong with you".
Amsa ma ta yayi da cewa "ba komai Momi, kawai dai ina jin stress ne ya min yawa".
Murmushi Momi tayi kana tace "Faruk! yanda na lura akwai abin da yake damun ka, but it seems like you don’t want to tell me, any way bazan matsa maka ba tun da kana ganin ‘boyewar shine mafita a gare ka".
"believe me Momi, i don’t have any problem, kawai dai ba na jin dad’in jiki na ne".
Kallon shi kawai tayi saboda ba ta yarda da maganar shi ba amma bari ta bi dashi a hakan.
Kasha magani ne? ta tambaye shi.
"Eh na sha" ya ba ta amsa.
Canza hirar yayi da cewa "Momi kayan sun k’araso ne?
"Sun iso, yanzu ma lissafin da nake yi kenan saboda wasu za su kai garuruwa ne, na ga ma wannan karan an fi son less, next time sun zan sa a kawo min da yawa, dan ina ganin wannan zasu yi saurin k’arewa".
Ci gaba suka yi da zancen business kana yaya Faruk ya mik’e da niyyar tafiya yana cewa "Momi bari in je in d’an kwanta".
"Ka ci abinci ne? Momi ta tambaye shi.
"No Momi i don’t feel like eating" ya amsa mata.
"Daurewa za kayi kaci, saboda zama da yunwa ba dad’i, zan sa Anisa takai ma abincin side d’in ka" Momi ta fad’a.
"Ok Mom" ya amsa mata sannan ya juya ya fita daga d’akin.
Momi ce ta kira Anisa akan taje takai ma yaya Faruk abinci.
Kitchen ta nufa ta d’akko abicin ta nufi d’akin.
Samun shi tayi a kwance akan rest chair da alama akwai tunanin da yake yi, sabida ko sallamar da tayi bai amsa ba saoda yana cikin duniyar tunani.
Ajiye food flask d’in tayi akan center table, ta nufi fridge ta d’akko mai swan water ta ajiye.
Ganin duk wannan kai kawon da take yi a d’akin bai mata magana ba wanda ke nuni da yayi nisa a cikin tunani.
Har ta juya da niyar barin d’akin, in yaso in ya gama tunanin ya ci abincin.
Yanayin damuwar da taga yake ciki tun lokacin da ya shigo gidan yasa ta kasa samun peace of mind, dan haka ta matsa kusa dashi ta kira sunan sa a hankali amma bai amsa mata ba, ganin haka yasa ta rik’e mishi hannu.
Da sauri ya d’ago kamar wanda ya tashi daga bacci yana kallon ta.
Ganin haka ne yasa tace "yaya ga abincin nan in ji Momi wai kaci".
"Ok" ya ba ta amsa a gajarce.
Ta juya da nufin tafiya ta d’ago ta kalle shi kamar da abin da take son cewa.
Kamar ya lura da yanayin ta ne yasa ya kira sunan ta.
"Anisa zo nan".
takowa tayi ta zauna a bakin gado.
"Come close to me Anisa" abin da yace da ita kenan.
Cikin sanyinta ta zauna kusa dashi.
Hannun ta ya rik’e yana cewa "Anisa tell me what is in your mind, don’t be afraid, nasan akwai magana a bakin ki, so feel free".
Kame-kame ta fara yi sannan tace "ba komai yaya, dama naga kamar akwai abin da yake damun ka ne, shi yasa na damu".
Lallausan murmushi yayi ya ce "don’t worry my Sister, ba abin da yake damu na, but still i need your prayer because there is something that i want to archieve"
Kallon shi kawai tayi ta gane he is serious of his word, dan haka tace "yaya i wish you success on what you want to archieve".
Dad’in kalamenta yaji saboda yasan ko ba komai ya samu sauk’i a tunanin da yake yi.
Haka ya dinga jan ta da hira wanda hakan ba k’aramin dad’i yayi wa Anisa ba, dan ta manta raban da ya zauna ya nuna mata caring d’in shi.
Sallama ta mai ta tashi ta tafi tana mai fatan hakan ya dawwama a tsakanin su.
[3/23, 13:03] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💖💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
*Wannan shafin naku ne*.
*Mrs Makama* (Hijira)
*Mom Hanan* (Mijin Aurenah)
*Ummien Fauzan* (Tsananin Rabo)
*Ummu Fatima* (Dija Qaya)
*Khairaty* (Ya Sheikh)
*Napheesa Isah Shehu* (Sanadin Maraici)
*'yar mutan Paki na mik’a gaisuwar ta gare ku tare da yi muku fatan alkhairi*.
*NA YABA MUKU*
*Xarah Auwal*
*Meeynarh*
*Da sauran Wanda ban samu ambatar sunan su ba*
*Kune ku ka bada amsar question of the day daidai*.
*Allah ya k’ara ilimi mai amfani*.
*Sunan wanda manzon Allah (s.a.w) ya ambata a lokacin da aka tambaye shi a cikin maza wa yafi so? Shine ya ba da amsar da cewa *‘sayyidina Abubakar radiyal lahu anhu shi yafi so a cikin maza’*.
*Tunatarwa*
Ka da ka damu da hassadar da mutum zai yi maka/ki, saboda wata ni’ima da Allah yayi maka/ki, idan ya baka/ki, babu mai k’wacewa.
Wannan nasiha ce.
Ka/ki ji tsoron yi ma mutane mummunan zato, ko da zaton naka/ki gaskiya ne, don zato shine mafi k’aryar a cikin zance.
Wannan hadisi ne.
25&26
Bayan fitar Anisa daga d’akin, yaji ya samu relief a ranshi, ko ba komai ya ji dad’in addu’ar da ta mishi, yana yabawa da natsuwar ta.
Abincin da Anisa ta kawo mai yaci, kana ya kunna tv yayin da ya kunna tauraron d’an adam, channel d’in Aljazeera yasa inda yake sauraran labarum da ke faruwa a k’asa daban-daban.
Yanda ake faman fad’a a wasu k’asashen ne ya d'au hankalin shi, yayin da wasu k’asar suke fama da kashe-kashen da ake yi musu na kashe musu ‘yan uwa, mazajensu, matayen su ko ‘yaya ba tare da wani dalili ba.
nuno wasu mutane aka yi suna kuka na yadda suke fama da yunwa da rashin muhalli duk a dalilin rashin zaman lafiya na k’asar.
Hamdala yayi wa Allah da a k’asar mu ba a fama da irin wannan fad’ace-fad’acen, sai matsalar da ba za a rasa ba, na fama da matsalar (kidnapping) garkuwa da mutane da yanzu ya addabe k’asar tamu.
Addu’a yayi akan Allah ya kawo mafita ya kuma zaunar da k’asar mu lafiya da sauran k’asashe baki d’aya.
Kiran sallar la’asar ne yasa ya mik’e ya nufi masallaci, ko da ya dawo daga salllah bai shiga cikin gidan ba illah motar shi da ya shiga ya nufi haleems dan ya huta.
Ko da ya isa gurin, ke’bantaccen guri ya samu ya zauna, yana kallon mutane da ke harkokin su.
A wani ‘bangaren kuma, abokai zaka ga suna hutawa, wasu kuma masoya ne ke hutawa.
Ido ya tsura ma wani saurayi da budurwa, kai daga gani masoyan gaskiya ne, in kai duba da yadda suke hirar su cikin nishad’i alamar ba abin da yake damun su.
Yadda suke caring d’in junan su yasa yaji sun burge shi wanda shima yana fatan nan gaba ya samu irin haka ko ma fiye da haka.
"Sai yaushe kenan? yaushe ne zai fito ya bayyana sirrin zuciyar shi da yake faman adana shi wanda yake ganin akwai lokacin da zai samu furta abin da ke ranshi? tambayar da yayi wa kansa kenan da yake buk’atar amsar a karan kanshi.
(HMM YAYA FARUK KAR KAYI SAKE…. SAI KACE BA SOJA BA?)
Yana cikin karanta wasik’ar jaki ne wata kyakkyawar yarinya tazo ta zauna a kusa dashi, ganin ko alamar kallon ta bai yi ba bare aje ga zai tanka ta.
Ganin idan ta biye mai bai san da wata hallita a gurin ba, dan haka ta mishi sallama.
Sanin darajar sallama yasa ya amsa mata, ya d’auke kan shi yana mai ci gaba da kallan wannan saurayi da budurwar.
Lura da tayi bai san da zaman ta ba yasa tace "handsome naga kana zaune kai kad’ai ne shine naga ya dace in zo in taya ka hira".
Yanda taga bai da alamar amsawa yasa tace "in ba damuwa zan iya samun numban ka".
Wani malalacin kallo ya mata na alamar gargad’i amma hakan bai sa ta ji d’ar ba illah k’ara cewa da tayi "suna na Fatima amma ana kira na da Binafa, zan iya sanin sunan ka? ".
Jin sunan da ta ambata yasa ya d’ago ya kalleta amma bai ce mata komai ba sai ma alamar tafiya da yayi saboda yadda yarinyar ta takura mai, gashi ya fito ne dan ya huta amma da alamar yarinyar ba za ta ba shi damar yin hakan ba.
Mik’ewa ya yi da niyyar tafiya, saboda ya k’osa ya bar gurin duba da yadda yarinya ta takura mai.
Cikin sauri ta k’araso gurin shi tana pleading d’in shi cikin shagwa’ba tare da cewa "plss handsome ba ka fad’a min sunan ka ba? idan ba damuwa can i have your phone number".
Ganin yadda yarinyar ke da rawar kai, da alama irin sangartacciya ce yasa yace "I by name Bregadier Umar, but you can call me Faruk" ya juya da niyar ci gaba da tafiya.
Motar shi ya shiga ya hango ta a glass d’in motar shi tana kallon shi, ya rufe motar da niyar tafiya yaga tana nokin d’in k’ofar motar, kamar kar ya kula ta sai yaga gwara su rabu lafiya da ita.
Bu’de glass d’in motar yayi yana cewa "do you need my help?
Karkatar da kai tayi alamar shagwa’ba tana cewa "pls Umar help me with your phone number, i want us to be friend!
Tak’aitaccen murmushi yayi saboda yadda tayi Magana.
numban ya d’auka ya ba ta ya ja motar a guje.
Waving d’in hannu yaga tana mai da murmushi a fuskar ta.
Direct gidan su Fatima ya wuce saboda yadda yaji zuciyar shi na azalzalar shi akan yaje.
Parking d’in motar shi yayi ya nufi cikin gidan.
Ko da ya shiga falon ba kowa a ciki, dan haka ya nufi side d’in Yaya Khalil.
Samun shi yayi yana operating d’in laptop da wanda ke nuni da wani aikin yake yi.
Sallama yayi ya nemi kusa dashi yana cewa "Bros ana aiki ne?"
Amsa masa sallama yayi yana fad’ad’a fara’ar shi "sannu da zuwa yaya Faruk, ina wani research ne saboda akwai wani presentation da zamu yi a school" cewar yaya Khalil.
"that is good, karatu sai an yi hak’uri sannan za a ci ribar abun bare in karatu yazo k’arshe sai a hankali" yaya Faruk ya fad’a.
Yaya Khalil ne ya amsa mai da cewa "Gaskiya kam, system d’in karatu ya canza, ga lecturers d’in ba kowannan su bane masu tausaya wa student".
"Allah ya kawo mana mafita kawai" cewar yaya Faruk.
Amsa mai yayi da cewa "Amin".
Zancen makaranta suka ci gaba dayi na yadda karatu ya koma a yanzu da matsalolin da ake fuskanta.
Suna cikin hirar ne ya kalli yaya Khalil yace "ina Teemah ne? naje main parlour ban gan ta ba, ko har yanzu fushi take yi ne? Nasan ta fad’a maka yadda muka yi da ita, tun da kaine friend d’in su".
Murmushi yaya Khalil yayi ba tare da yace komai ba.
"Je ka kira min ita, kace ta same ni a garden" yaya Faruk yayi commanding d’in shi.
Fita yayi daga d’akin ya nufi garden yana mai jiran zuwan ta.
Ko da yaya Khalil ya je side d’in ta bai tarar da ita ba, dan haka ya nufi side d’in Ummu.
Samun ta yayi kwance a jikin Ummu suna hira, da fara’ar shi ya k’arasa d’akin yana cewa "Assalamu alaikum in shigo ko in koma? Dan yau naga Ummu ta ware Khalil d’in ta tana gurin Autan ta".
Ummu ce ta amsa sallamar tana cewa "kai ma kasan auta dangware shalele ce, ta gaban goshi ce, sai kayi kamu k’afa a gurin ta ka samu fada" cewar Ummu.
Ni kuwa dake faman yamutsa fuska saboda nasan yaya Khalil yau da tsokana yazo.
Kallo na yayi da alamar tsokana yace "Fatima ki tashi kije garden, yaya Faruk ne yazo yake neman ki".
D’aure fuska nayi kamar ba dani ake maganar ba saboda har yanzu wani irin haushin yaya Faruk nake ji.
Ganin ban da alamar tashi yasa ya kalle ni yana cewa "Sister ba ki ji abin da nace bane!
Turo baki nayi kana nace "gaskiya yaya Khalil am sorry amma ba za ni ba, neman me yake min da har zai ce in same shi a garden banda marin da yamin bai ishe shi ba shine zai k’ara dawo wa ya d’aura a inda ya tsaya"ido na fal da hawaye.
Duk wannan tak’addamar da muka fara yi da yaya Khalil, Ummu ba tace komai ba sai yanzu ta kalle ni tace "Fatima ki tashi kije tun kan in ‘bata miki rai, tun da ke ba kya jin magana"
Cikin ‘bacin rai na mik’e na fita saboda yadda naji raina ya k’ara ‘baci na yadda ake ji da yaya Faruk a family, shi yasa yake yin duk yadda yaso ba tare da shakka ba, haka zalika ba a ganin laifin shi.
A raina na k’udurta cewa yau duk abin da yazo dashi ina dai dai dashi saboda yadda naga ya takura min, beside kowa yana bin bayan shi, ba mai ganin laifin shi.
Garden na nufa inda na same shi zaune akan kujera yana facing d’in wanda yake shigowa.
Ko da na k’arasa ciki-ciki na masa sallama na nemi guri na zauna ba tare da k’ara cewa uffan ba.
Motsin da bakin shi yayi ne ya tabbatar min da cewa sallamar ya amsa.
Ta’be baki na nayi a raina ina cewa "miskili Kenan, kafi mahaukaci ban haushi, nima zan nuna maka gidan ka tarar".
Jin shirun yayi yawa yasa raina ya k’ara ‘baci fiye da d’azun saboda ni a gani na duk salon wani cin fuska ne da kuma hanyar da zai ‘kara sa min wani ‘bacin rai, in ma hakan yake nufi bazan bashi fuskar ganin hakan a tare da ni ba bare ya samu wata damar na min yadda yake so.
(HMM READERS NASAN KUMA ZAKU SO KUJI DALILIN DA YASA YAYA FARUK YA KIRA FATIMAH, TO NIMA HAKAN TAKE A GURI NA.
KU BI NI SANNU A HANKALI DAN JIN SAURAN LABARIN)
[3/24, 22:28] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽
*Na sadaukar da wannan shafin gareki ‘yar mutan Nijar* (Dr Maimuna Matar Abdoulaye)
*Marubuciyar* (Latifa)
*Ki yi yadda kike so da shafin*.
*Allah ya k’ara baki k’arfin gwiwa na taimakon al’umma*
*Question of the day*
Wace mata ce ta tara (9) a cikin matan manzon Allah (s.a.w)? menene asalin sunan ta da nick name d’in ta?
27&28
Cikin tattausan lafazi da jan hankali ya kira suna na "Fatimah"
"Na’am" na amsa mai a tak’aice da kuma d’aure fuska saboda yadda na k’osa na bar gurin dan ni ban ga amfanin kiran da yayi min ba.
"Fatima! Kina jin haushin marin da na miki ko? a tunanin ki kamar na tsane ki ko?
"Dago wa nayi na kalle shi dan kamar yasan abin da ke cikin zuciya ta kenan amma ban da halin furta hakan.
Kallo na yayi yaci gaba da cewa "Nasan kina ganin kamar ina takura miki ko? kuma ina interfere a personal life d’in ki wanda tuntuni na gane ba kya son hakan daga gare ni, duk a tunanin ki na samun liberty da human right da yake rud’arki".
Fatima! Ina yi miki haka ne saboda future d’in ki as i take you like my blood sister, d’aya kuke da Anisa a guri na, ba zan ba ku freedom nayin socialization a matsayin ku na mata ba, any social life da kike gani da bature ya fito da tsarin fundamental human right yana da disadvantage, saboda a ciki akwai inda aka yi stating d’in cewa ‘you have the right to participate in any social activities you like’
kin ga kenan akwai illah babba a ce an ba d’an adam damar yin duk abin da ya ga dama ba tare da an tsawatar mai ba wanda a addinin mu, Annabin mu, Muhammas (s.a.w) ya fad’akar damu da cewa " idan baka jin kunya, ka aikata abin da kake so", na d’auke ki ne kamar Anisa da zan iya hukunta wa ba tare da fargaba ba, hakan yasa nake d’aukan action a kan ku, so i will not give you the opportunity to do what you like".
A ‘bangare na kuwa wannan dogon bayanin da yake yi ne ya ishe ni, ji nake yi kamar in tashi in bar mai gurin.
Cikin cool voice ya ce "Fatima am sorry da na mare ki, nima ba da san raina na miki shi ba, ke ki ka jawo hakan saboda yadda kika min magana ne ya ‘bata min rai, da kika tambaye ni dalilin da yasa na yaga miki hoto"
'Wonder shall never end" na furta hakan a raina, ko a mafarki ban ta’ba tunanin yaya Faruk zai furta wata kalma mai suna ‘Sorry’ a bakin shi ba, bare ni da yake d’auka na teenager.
Gaskiya ne da hausawa ke cewa "in da ranka zaka sha kallo".
Dad’i naji a raina yau yaya Faruk ya k’ask’antar da kanshi a kaina yana neman yafiya ta, da nayi tunanin ko wani salon ya canza da zai musguna min ko akwai wani shiri da yake yi a kaina yasa na magantu akan dad’in da naji nay a nemi yafiya ta.
Ci gaba yayi da cewa "Fatima! Zan iya jurar komai amma ban da raini da wulak’anci, da fatan zaki kiyaye saboda as from now, ina so ki d’auke ni kamar Khalil da zaki iya fad’a wa damuwar ki da kuma neman shawara a gurin shi".
Rasa a wace duniyar nake, wai yaya Faruk ne yake min Magana in a polite way da kuma neman mu shirya.
Wani tunani ne yazo min akan cewa akwai dalilin da yasa yake neman mu shirya dan ruwa ba ya tsami banza.
"Teemah" ya kira suna na da sanyin murya.
Ban samu damar amsawa ba saboda yau mamaki ne ya cika ni, bin shi kawai nake yi da kallo dan ina so in tabbatar da cewa a buge yake ko a hankalin shi yake fad’an maganganun nan, duk da ban ga wata alama na yasha wani abu ba, yana fad’ar maganganun nan ne da gaske.
Kallon da yaga ina bin shi dashi ne yasa yayi tak’aitaccen murmushi yana cewa "are you surprise? ki cire mamakin da kike yi dan na nemi yafiyar ki".
Zuciya ta ce ke ingiza ni akan kar in yadda da dad’in bakin da zai min, saboda yana da dalilin yin hakan.
Ganin ba zan ce mai komai ba yasa yace "Teemah! ba ki ce komai ba, ko ba ki yafe min ba?
Satar kallon shi nayi na yadda yake magana yana wani lumshe ido kamar yana magana da budurwar shi.
Duba da yadda nake son in bar gurin, hakan yasa nace "na yafe maka yaya Faruk kuma ni b aka min laifi ba".
Wani murmushin jin dad’i yayi wanda hakan ya bayyana a fuskar shi.
Lura da nayi da bai da alamar bani damar tafiya yasa na k’ara d’aure fuska kamar zan yi kuka saboda yadda na gaji da zama a gurin, kuma ni har yau ba wai na huce da abin da ya min bane.
Tambaya na yayi akan wane course na yi applying kuma wani school nayi za’ba?
A tak’aice na bashi amsa da cewa "computer science nayi applying kuma kaduna Polythecnic ne first choice d’in da na sa".
K’arfin gwiwa ya dinga bani akan harkar karatu kasancewar sa mai son muyi karatu.
Alamar da ya gani a fuska ta dake nuna na gaji yasa yace "Teemah za ki iya koma wa ciki, in kin je kya gaishe min da Ummu kice ina sauri ne amma zan shigo gobe mu gaisa".
Ai kamar jira nake yi, nayi saurin mik’ewa ba tare da ce komai ba, na fara tafiya, "ka ji da shi" nace a raina duba da yadda yake ta fito da sabon salo kala-kala wanda shi yasan manufar shi.
Jiki na ne ya bani cewa kamar yaya Faruk kallo na yake yi, juyawa nayi naga kafe ni da ido kamar wanda yaga sabuwar halitta.
Harararshi nayi na d’auke kaina ina mamakin kallon me yaya Faruk yake min?
amsar da ban sani ba kenan.
shi kuwa yaya Faruk yaga san da na harare shi, sai murmushi yayi kawai kamar bai ga abin da nayi ba, yanda na kalle shi ma dariya ma na bashi.
Ko da na shiga main falo, ban nemi kowa ba, na nufi side d’ina.
Gefen gado na samu na zauna ina tunanin da gaske ne yaya Faruk yau ni ya nemi yafiya ta har yana neman mu shirya?
Abu d’aya na yadda dashi shine zamu dinga gaisawa irin ta ‘yan uwan taka ba wai dan ban hak’ura ba, sai dn in ja ma kaina mutunci, tun da shi abu k’adan yake jira ya ‘bata wa mutum.
Yaya Khalil ne ya shigo ya zauna kusa dani yana cewa "Sister ashe kin dawo? ina ta jiran ki a side d’in Ummu".
Ta’be baki nayi nace "yanzu na shigo, shi yaya Faruk d’in nan ya wani tsare ni da wani dogon bayani, sai da ya gama mari na sannan zai lalla’bo wai na yafe mai sannan wai in ina da shawara in zo wajen shi, ni nasan akwai dalilin da yasa ya nemi yafiya ta amma ba wai ra’ayin kan shi bane".
girgiza kai kawai yaya Khalil yayi, ya d’aura da cewa "Fatima! ba ki gama sanin waye yaya Faruk bane shi yasa, he is a simple and nice person ga wanda ya kiyaye dokokin shi, yana da dad’in zama, duk da sometimes miskili ne kuma yana da fad’a amma ba shi da wata matsala, tun da har ya nemi yafiyan ki ya kamata ki yafe mai saboda akwai laifin da muke wa ubangijin mu kuma in mun nemi yafiyar shi ya yafe mana, kar ki zama mai k’ullatar mutum idan ya miki laifi kin ji sister?
D’aga mai kai nayi nace "ni ban k’ullace shi ba, na yafe mai, amma ni ba zan kai mishi damuwata ko in nemi shawarar shi ba".
Dariya yayi yace "is ok Fatima, zo mu tafi side d’ina akwai research d’in da nake yi, kya taya ni hira".
Fita yayi daga d’akin yayin da nake bin shi a baya.
Yaya Faruk kuwa da ya shiga mota, tsintar kanshi yayi cikin farin cikin da bai misaltuwa, lokaci yayi da zai jawo Fatima jikin shi, ta daina mishi kallon mai son kanshi da kuma mulki.
Lokaci-lokaci zaka ga ya saki wani lallausan murmushi.
Ko da ya isa gida, d’akin Anisa ya wuce, samun ta yayi da wani novel tana karanta wa.
Kusa da ita yaje ya zauna yana cewa
"Anisa!
Amsa masa tayi da cewa "sannu da zuwa yaya".
Bai damu da ya amsa mata ba illah cigaba yayi da cewa "gobe in Allah ya kaimu around five p.m ku shirya zan kai ku outing Asaa pramise ku d’an yawata ku ga gari tun da kun ce ina takura muku kamar wasu daddawar d’aka shine naga gara in daina matsa muku" ya k’arasa maganar da wasa.
Ita kanta Anisa abin ya ba ta mamaki wai yau yaya Faruk ke cewa su shirya zai kai su outing".
Ita tun jiya zuwa yau taga ya canza mata, ya dawo so cool wanda ba ta san dalilin canzawar shi ba.
Ita dai fatan ta shine Allah yasa ya d’aure a haka saboda ita ma tana son zama da shi suna hira kamar yadda wa da k’anwar shi suke yi.
Yalwatar murmushin ta tayi dan kar ya gane ko tana mamaki ne tare da cewa "yaya mun gode sosai".
Mik’ewa yayi ba tare da yace komai ba ya bar d’akin, a ranshi kuwa yaji dad’in yadda ta nuna farin cikin ta, shi yasa ma ya d’au alk’awarin zai jawo su jikin shi saboda su sake dashi.
Cikin zak’uwa ta d’au wayar ta, tayi dialling d’in number Fatima.
Daga d’ayan ‘bangaren, Fatima ce tayi receiving tana cewa "Anisa Hi".
‘how a you doing? Anisa ta tambaye ta
"normal Anisa" na ba ta amsa.
Anisa ce ta d’aura da cewa "gobe ki shirya zamu je outing".
Da murna ta nace "da gaske Sister, waye zai kai mu? na tambaye ta.
"Da gaske nake yi, ke dai ki shirya, around five za mu biyo mu d’auke ki, kuma kinsan abin mamaki? Anisa ta tambaye ni.
Amsa mata nayi da cewa "ya za ayi in sani" na ba ta amsa.
"To yaya Faruk ne zai kai mu" Anisa ta fad’a da murnar ta.
D’if nayi kamar an d’auke wutar nefa dan har ga Allah ban so a ce shi zai kai mu ba duk kuwa da yadda nake son fitar, nasan in nace ba zani ba Anisa ba za ta ji dad’i ba amma da ba inda zani.
Shirun da Anisa taji ne yasa tace
"Fatima kina ji na kuwa"
"ok Anisa, Allah ya kaimu sai kun zo" na fad’a da kasalalliyar murya
Sallama muka yi na aje wayar yayin da nake tunanin wai miye dalilin yaya Faruk na canza wa a lokaci d’aya?
Ganin ba mai bani wannan amsar yasa na watsar da tunanin.
Ita kuwa Anisa tana ajiye wayar kiran yaya Khalil ne ya shigo.
Tsadadden murmushi tayi kana ta danna received.
"Assalamu alaikum lovely Sister" yaya Khalil ya fad’a.
Amsa masa tayi da "wa’alaikumus salam yaya Khalil".
"ya kike? Yasu Momi da daddy? ya tambaye ta.
"Su na lafiya" ta bashi amsa a gajarce.
"Anisa kwana biyu ba kya nema na, gashi yaya Faruk ya hana ku yin chat da mun dinga communicating" cewar yaya Khalil.
Cikin shagwa’ba tace "plss yaya Khalil ka sa baki, naga kai na hannun daman shine, may be ya yarda mu fara chat d’in'.
Dariya yayi sannan yaci gaba da cewa "ba ruwa na, so kike yasa ni up & down, in zo ina faman yi wa k’afa ta gashi ko in sa a nemo min mai gyaran targad’e".
Kukan wasa ta fara mai saboda tasan ita yake tsokana.
Hak’uri ya fara ba ta yana dariya kana suka ci gaba da hirar su sannan suka ya mata sallama.


0 Comments