makauniyar soyayya hausa novels 14

 MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*  

       


             *BY*

 



*MARYAM AHMAD PAKI*






*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝






*QUESTION OF THE DAY*


_Wace surah ce take karantar da wajibcin tsare hakk’ok’in mutane, tsakaninsu, a ciniki da wasu mu’amalolin zamantakewa_.






75-76


Ina fita daga side d’in Dr na wuce side d’ina na zauna a kan gado.


Tunani na ci gaba dayi akan pills d’in da Dr yake so in sha daga yin auren mu da sati d’aya, duk da hujjojin da ya bani bai gamsar dani ba da zai sa in fara shan maganin tsarin iyali ba tare da na jira na ga tsarin da Allah ya tsara min ba.


Nasan Dr k’wararre ne a ‘bangaren aikin shi, ba zai bani pills d’in da zai zamar min illah ba amma ni a nawa ganin  kamar yayi wuri in fara shan pills d’in family planning.


Abin da yafi min yawo a raina shine akan wannan matsalar muka samu matsala da Dr, ban yi tunanin wannan matsalar zai sa Dr yayi fushi dani har yace in koma side d’ina.


Ni ina da nawa dalilin na k’in ba Dr had’in kai wajen bijire ma shan pills d’in da yake so in sha in nayi duba da ko wata ban yi ba da yin aure amma yake so in sha pills, na sha samun labarin yadda wasu suke samun matsala a yayin da suka yi family planning, wasu ma dalilin daina haihuwar su kenan a yayin da suke so Allah ya basu yaran da sauran matsalolin da suke biyo baya a dalilin yin family planning d'in.


Hujjar da Dr ya bani na cewa yana so in yi karatu na ba tare da matsala ba da kuma tausaya min laulayin ciki da zan yi idan na samu ciki shine hujjar shi akan in sha pills bai ishe ni hujjar da zan yi dogaro da ita wajen amince ma buk'atun shi.


Haka na ci gaba sak’a da warwara akan samo mana mafita tsakani na Dr, dan ba na so wannan matsalar ta zama hanyar rusa mana farin cikin mu da muka fara gina wa a rayuwar auren mu.


Zuciya ta ce ta dinga ba ni shawarar akan in amince da buk’atar da Dr yazo min dan nasan ba zai cutar dani ba.


Da wannan na yanke shawarar akan gobe in Allah ya kaimu zan shaida ma Dr na amince da buk’atar shi.


Haka na kwana cikin kad’aci saboda yadda na saba kwanciya a jikin Dr, ya min sabo da jikin shi.


Washegari haka na tashi na had’a mana breakfast na jera a dinning table.


D’akin Dr na wuce inda na same shi har yayi shirin shi na tafiya aiki kasancewa ranar zai koma aiki yana sa socks.


Kallon-kallo muka yi ni dashi kana Dr ya kau da fuskar shi ya ci gaba da sa socks d’in shi.


Murmushi na yi na k’arasa kusa dashi na zauna.


"Good morning Dr" na fad’a.


"Morning Zarah".


"Dr fushi kake yi dani?" na fad’a cikin shagwa’ba.


Tsadadden murmushin shi ya min kana ya shafa fuska ta ya ce "Me kika gani Zarah, ni ba fushi nake yi dake ba".


Kwantawa nayi a kafad’ar shi yayin da na fara magana a hankali na ce "Dr kayi hak’uri akan abin da ya faru jiya da daddare, ba wai na k’i amincewa da buk’atar ka bane saboda nasan ba za ka ban abin da zai cutar dani ba, sai dai ina ganin kamar in na fara shan pills a yanzu yayi wuri sannan ina ganin wasu da suke samun matsala a dalilin yin family planning d’in su shi yasa ka ga na k’i amincewa, amma yanzu na amince da buk’atar ka dan nasan ba za ka mana abin da zai zamar mana matsala ba".


Rungume ni yayi ya bani peck a goshi na saboda murnar amincewar da nayi.


Hannu na ya rik’e yana murmushi ya ce "Zarah kin san ina son ki, ba zan yi abin da zai zamar mana matsala ba, pills d’in nan da za ki sha bai da matsala, kamar yadda na fad’a miki dalili na shine ya zama na mun yi planning yadda za mu tsara marriage life d’in mu, amma in har a cikin zuciyar ki ba ki amince ba shi kenan sai a bar shan pills d’in" ya k’arasa maganar yana kallo na.


Murmushi na yi na ce "Na riga na amince Dr".


"Thanks my lovely Zarah" ya fad’a cikin jin dad’i.


Hannun shi na rik’e muka wuce dinning muka yi kalaci kana ya wuce gurin aikin shi.


Tun daga wannan lokacin Dr ke bani pills na family planning ina sha.


Zaman mu ya ci gaba da gudana cikin kulawa da so da k’auna, cikin d’an lokaci na canza nayi fresh, ga wani kyau da na k’ara.




Yaya Faruk tun komawar shi Abuja yaci gaba da gudanar da aikin shi, yana k’ok’arin ganin ya cire duk wata damuwa da ka iya jawo mishi wata matsalar.


Yanzu ba shi da wata sauran damuwa, aikin shi da ya k’ara sa wa a gaba, a yanzu ya k’ara nisanta kan shi da ‘yan mata dan gudun fad’a wa halin da ya shiga wanda har yanzu bai gama jin rad’ad’in abin a ran shi ba.



Nana na iyakar k’ok’arin ta ganin ta cire ma yaya Faruk damuwar da yake ciki, duk da a yanzu ba wani alamu da ke nuna yana cikin wani hali na tunani ko damuwa, sai dai tausayin halin da ya shiga a dalilin abin da na mishi yasa tun san da suka je Kaduna ya fad’a mata fasawar auren shi da ni taji ta kasa samun natsuwa, ta sa a ranta za ta faranta ma yaya Faruk dan ya manta da abin da na mishi, a yadda ta d’auki yaya Faruk jin shi take yi kamar yaya Mus’ab, shi yasa take fad’i tashi akan ta ga yaya Faruk bai da wata damuwa, damuwar da Nana ke nuna wa akan shi yana sa yana k’ara ganin girmanta a idon shi.




Nana ce ke zaune a falo ita da Hajiyar su suna hira, wayar ta ce tayi k’ara alamar kira ya shigo, tana jin k’arar wayar amma ta k’i d’agawa.


Ganin ta k’i d’aukar wayar ne yasa Hajiya ta kalle ta tace "Nana ba kiran ki ake yi ba ne ki ka k’i d’aukar kiran".


Cikin shagwa’ba ta ce "Hajiya Mukhtar ne fa yake kira".


Kallon ta Hajiya tayi kana ta ce "Dan Mukhtar ne sai ki k’i d’aukar wayar, Nana me yasa kike haka ne, duk wanda yazo gurin ki sai kin ce bai miki ba, kullum fa k’ara girma kike yi, kuma ni ban ga aibun Mukhtar ba da ba kya son shi, yaro mai natsuwa da tarbiyya amma ke kin ce bai miki ba, ina laifin Wanda ya ce yana son ka".


Marairaicewa tayi ta ce "Hajiya na fa bashi hak’uri tun san da ya fad’a min yana so na amma ya k’i ya hak’ura, ba na so in ci gaba da tsayawa dashi daga baya ya ga kamar na yaudare shi alhalin tun farko na bashi hak’uri ya hak’ura dani, ni kaina nasan Mukhtar bai da wata matsala ta a zo a gani, kawai dai ba na jin son shi ne, sauran kuma da suke zuwa guri na yawanci behaviours d’in su ne ba su min ba".


Hajiya ce ta ce "Amma dai kin san yadda Dadin ku ya d’auki Mukhtar kamar d’an shi, kin san yadda amincin su yake da mahaifin shi Alhaji Ashiru, ni dai ba ruwa na in Dadin ku yaji abin da kike mai, ke ma kin san sai ran ki ya ‘baci".


Suna cikin wannan maganar ne yaya Mus’ab ya shigo falon da sallamar shi.


Gaisawa suka yi kana ya kalli Hajiya wacce taci gaba da yi ma Nana fad’a akan rashin kula samarin da take yi ya ce "Hajiya yau dai an ji kan ku ke da autar ki, tun da na ga sai fad’a ake mata".


"Ba dole ka ji ni da Nana ba, na zuba mata ido amma ita ba tasan haka ba, yau in wannan yazo gurin ta tace bai mata ba yana da matsala kaza, gobe ma in wani yazo haka za tace, ga yaron nan Mukhtar da yake son ta shima ta ce bai mata ba, a cikin su ta kasa tsayar da wanda ya mata, ni na fara gajiya da irin halin Nana cewar Hajiya.


Murmushi yaya Mus’ab yayi kana ya ce "Gaskiya Nana ba ki kyauta ba, duk ma su zuwa gurin ki a ce ba Wanda ya miki, ya kamata ki tsayar da wanda ya kwanta miki a ranki, ko Mukhtar da mahaifin shi yake da wani matsayi a garin nan ba na ganin yana wani abu da za a ce bai kamata ba, yana da natsuwa".


Cikin sanyin ta tace "Ni fa yaya Mus’ab ba wai na ce Mukhtar yana da wata matsala ba ne, just kawai ba na jin son shi a raina ne".


Murmushi yaya Mus’ab yayi ya ce "Hajiya ki k’yale ta tun da ta ce duk ba su mata ba, lokaci in yayi sai ki ka ga ta kawo miki surukin ki har gida ko Nana?" ya k’arasa maganar da wasa yana kallon ta.


Murmushi tayi ta rufe fuskar ta alamar jin kunya.


Hajiya ce ta kar’bi zancen da cewa "Ai shi kenan tun da kana goyon mata baya, Allah ya za’ba mana abin da yafi alkhari".


Dukkan su suka amsa da Amin.


Nan suka ci gaba da hira kana ya musu sallama ya tafi.




Yau Yaya Faruk yana zaune a falon shi yana kallon wasan k’wallon k’afa da ake watsowa a tashar New world sport, idon shi ne ke kan talabajin d’in, amma hankalin shi na wani gurin.


Sallamar da yaya Mus’ab yayi yaji shiru ne yasa ya shigo falon.


Ko da ya shigo falon, yaya Faruk hankalin shi ba ya gurin bare yaji shigowar yaya Mus’ab.


Dafa kafad’ar shin da yayi ne ya dawo dashi daga duninyar tunanin da ya tafi.


Ganin yaya Mus’ab ne yasa ya saki murmushi tare da cewa "yaushe ka shigo ne?".


Shima murmushin ya maida mai ya zauna a kujerar mai kallon ta yaya Faruk ya ce "Ai ba za kasan shigowata ba tun da kana duniyar tunani".


Hararar shi yaya Faruk yayi cikin wasa kana ya ce "Ni na fad’a maka tunani nake yi, kawai dai hankali na yana kan ball d’in da ake buga wa a Tv ne".


Dariya yaya Mus’ab yayi ya ce "Amma wannan ball d’in ta iya d’aukar hankali tun da har tasa nayi sallama ba kaji shigowa ta ba sai da na dafa ka sannan ka dawo daga duniyar wasan k’wallon da ake bugawa a Tv d’in".


Wannan karan yaya Faruk bai ce komai ba sai ma murmushi da ya ci gaba da yi.


"Faruk ni nasan tunani ka ke yi amma ba ka so ka fad’a min, duk wanda ya zo ya tarar da kai a halin da kake yasan kayi nisa ne a cikin tunani, plss Faruk ka rage tunanin da kake yi saboda samun inganci a lafiyar ka, nasan tunanin da ka ke yi ba zai rasa nasaba da Fatima ba" yaya Mus’ab ya fad’a cikin kulawa.


Watsa mishi wani kallo yaya Faruk yayi ya d’aura da cewa "Kai fa Mus’ab sa idon ka yawa ne dashi, ni na ce maka tunanin Fatima nake yi, ba dama in yi shiru sai ya zama tunanin Fatima na ke yi".


"In ma ba ka fad’a ba, yanayin ka ya nuna haka, ya kamata Faruk ka cire Fatima a ranka tun da tayi aure, nasan Fatima sai ta maka wuyar fita a zuciyar ka saboda son da kake mata, nasan abu ne mai ciwo gurin cire wanda kake so a cikin ran ka, sai ka ci gaba da dauriya da jajurcewa sannan za ka manta ta, tun san da abin nan ya faru Faruk ba ka dawo asalin Faruk d’in ka ba, ko gurin aiki duk ka canza, kai kan ka kasan da haka, dan Allah Faruk kayi k’ok’ari ka manta da komai, sai ka ga komai ya zama daidai" cewar yaya Mus’ab.


Gauron numfashi yaya Faruk ya ja kana ya ce "Mus’ab na san Fatima tayi min nisa tun da a yanzu tana d’akin mijin ta tare da masoyin ta wanda suke son junan su, nasan ci gaba da tunanin ta a raina laifi ne babba tun da matar wani ce, kamar yadda na ce ne na hak’ura da Fatima to hakan yake a guri na, sai dai ba zan ‘boye maka ba Mus’ab, ban san me yasa zuciya ta wani lokacin take bijiro min da tunanin ta ba, ni kaina ina iya k’ok’arin ganin na manta da ita a zuciya ta dan ban ga amfanin tunanin ta da yake haifar min ba sai ‘bacin rai da kuma zunubi da nake d’aukar ma kaina".


Ci gaba yayi da cewa "Plss Mus’ab ka taya ni da addu’a, ni kaina ba na so in dinga kasancewa a halin tunanin Fatima bayan nasan ta min nisa" ya k’arasa maganar cikin damuwa.


Tausayin yaya Faruk ne ya kama yaya Mus’ab, yasan son da yaya Faruk yake min ba abu ne mai sauk’i da zai yi saurin cire ni a ranshi, yasan abu ne mai ciwo rabuwa da masoyi, ji yake yi kamar shine hakan ya faru dashi, dan ya d’auki yaya Faruk kamar d’an uwan shi ba wai aboki kad’ai ba.


Yaya Mus’ab ne ya ce "Insha Allah Faruk zan ci gaba da taya ka addu’a akan Allah ya kawo maka sauk’in halin da kake ciki, sai dai hanya d’aya ce za ta kai ka ga manta Fatima cikin sauki tare da samun natsuwa".


"Wace hanya ce wannan Mus’ab" yaya Faruk ya tambaya.


"Ba ko wace hanya ba ce da ya wuce ka samu abokiyar rayuwa kayi aure, in dai ka bi wannan hanyar za ka samu maslaha a halin da kake ciki, dan aure yana kore damuwa yasa mutum cikin natsuwa" yayaMus’ab ya bashi amsa.


"Mus’ab ba na ganin zan yi aure nan kusa, saboda a yanzu na k’ara d’aukar darasi akan ‘yan mata, ba ko wace mace ba ce za ta yi maka so tsakani da Allah, hakan yasa na ke kauce musu, sai gashi Allah ya jarabce ni da son ‘yar uwa ta Fatima, amma ba ta saka min da komai sai ‘bacin rai, kana ganin yanzu in na k’ara fad’a wa son wata yarinyar na san ita kuma wani salon za ta zo min dashi, zan dai ci gaba da addu’a akan Allah ya kawo min mafita sannan in lokacin aure yazo sai in yi" cewar yaya Faruk.


Yaya Mus’ab ne ya ce "Faruk ya kamata ka gane kullum lokaci wuce wa yake yi, bai kamata ka ce ba yanzu za ka yi aure ba saboda abin da Fatima tayi maka, ba kowace mace ba ce mai irin halin Fatima, ita tayi hakan ne dan ganin ta samu cikar burin ta, shi yasa ta biyo ta wannan  hanyar dan bijire ma auren ka, ka duba ‘yan mata na wa ne ke son ka amma kai ba su dame ka ba, ya kamata ka fuskanci rayuwar ka ta gaba shine ka samu kayi aure kamar yadda na fad’a maka, kai kan kasan su Dadi ba za su ji dad’i su ga ka k’i fitowa da matar aure ba".


Shiru yayi kamar ba zai yi magana ba kana ya ce "Nasan duk abin da ka fad’a min gaskiya ne, sai dai a yanzu ban jin zan iya tsayawa in nemi wata yarinyar, sai dai in bari su Dadi ko Momi su za’ba min wacce suke so ko da ba na son ta zan iya hak’urin zama da duk wacce suka za’ba min dan in faranta musu".


Kallon shi yaya Mus’ab ya yi saboda yadda yaya Faruk yake wannan maganar yasan har cikin zuciyar shi yake fad’ar wannan maganar, a yanzu yana ganin zai isar mishi da sak’on da zuciyar shi ke yawan bashi yana kore wannan tunanin daga ranshi, saboda yana ganin wannan hanyar ce kad’ai za ta fitar da yaya Faruk daga halin da yake ciki.


"Idan ka bani dama ni zan za’bar maka wacce za ta dace da rayuwar ka" yaya Mus’ab ya fad’a yana ci gaba da kallon yaya Faruk dan ganin yadda zai kar’bi zancen.


Wannan karan sai da yaya Mus’ab ya yi dariya dan yasan yaya Mus’ab akwai shi da son wasa, dan haka cikin wasa ya ce "Na baka wannan damar Bregadier Mus’ab Dadin Asim".


Shima Mus’ab d’in dariya yayi kana ya ce "A ture maganar wasa Bregadier Faruk, maganar da na ke fad’a maka da gaske nake yi, na za’bar maka matar da za ta dace da kai, sai dai ban san kai ko za ka yi marhabin da ita ba a zuciyar ka".


Ganin yadda Mus’ab d’in ya yi maganar yasan ba wasa yake mai ba, dan haka ya daure ya ce "Wace yarinya ce ka za’bar min".


"Nana Khadija ita na za’bar maka, ita nake ganin za ta dace dakai, ta kuma taimaka wajen mantar da kai damuwar da kake ciki kasancewar yadda kuka shak’u da ita…".


Duk da yaji abin da yaya Mus’ab d’in ya fad’a, amma sai zuciyar shi ke k’aryata mishi maganar da ya ji yaya Mus’ab d’in na fad’a, don haka ya katse shi da cewa "Wai wace Nana Khadijan?".


Murmushi yaya Mus’ab yayi saboda yasan dama dole yaya Faruk ya shiga rud’u a yayin da ya fad’a mishi sirrin zuciyar shi.


"Cool down Faruk, nasan ka gane  Nana Khadijan da nake nufi, amma tun da ka na buk’atar k’arin bayani, Nana k’anwa ta nake nufi, ita na za’bar maka".


Kallon shi kawai yaya Faruk yake yi ba tare da ya bud’e baki ya k’ara cewa komai ba saboda yadda maganar ta zo mishi a bazata da bai yi tsammanin ta ba, bai san a yadda zai d’auki maganar da yaya Mus’ab yazo mishi da ita ba.


Shiru ne ya ratsa falon na wani lokaci kana yaya Faruk ya d’ago kanshi ya kalli yaya Mus’ab ya ce "Mus’ab nasan kana son ganin farin ciki na, ka damu da damuwa ta, son da muke ma junan mu daga Allah ne, amma ina ganin bai kamata dan kana son ganin farin ciki na ka yanke hukunci ba tare da kaji ra’ayin Nana ba, za ta iya yiwu tana da wanda su ke soyayya, kai kuma ka yanke hukunci dan ganin ka samar min da mafita, ba zan so in shiga hakk’in Khadija ba, ba zan so ta d’auke ni a mara adalci ba alhalin tana ganin girma na, ta na ba ni matsayin wa a gurin ta, ni ma k’anwa take a guri na, zan so ganin ci gaban ganin farin cikin ta".


"Faruk kan in yanke wannan hukuncin sai da nayi nazari a kai, Nana tana da samari masu son ta, sai dai har yanzu ta kasa tsayar da hankalin ta wajen za’ben guda d’aya daga cikin su, hakan yasa Hajiya ta ke mata fad’a akan ta tsayar da miji tayi aure, nasan Nana ba za ta k’i bin umarni na ba in har na fad’a mata na za’bar mata miji, tasan ba zan zan mata za’ben tumun dare ba, shi ya sa ka ga na zartar da wannan huknci, nasan Nana ba za ta bijire ma umarni na ba, sai dai ko kaine Nanan ba ta kwanta maka a cikin ran ka ba, ko ba ta daga cikin tsarin matan da kake so".


Wannan hujjojin da Mus’ab ya bashi ya k’ara d’aure shi da jijiyoyin jikin shi, yasan yaya Mus’ab na mishi haka ne dan ya samar mishi da farin ciki, sai dai har yanzu bai san a yadda zai d’auki maganar ba, shi dai yasan Nana na ya d’auke ta kamar k’anwar shi, sannan kyawawan halayen ta na daga cikin abin da yasa ya ke k’ara ganin k’imarta a idon shi, a yanzu ba zai yi saurin yanke hukunci game da ita ba, dan shi bai ta’ba kawo Nana a ranshi a matsayi na daban da ya wuce matsayin k’anwa da ya ba ta, duk da yaya Mus’ab ya fad’a mai cewa ba ta tsayar da gwanin ta ba, yana tsoron kar ya zamana a ranta ita ba ta ra’ayin shi, hakan zai zama da cutar wa kenan.


Jin shirun da yaya Faruk yayi ne yasa Mus’ab ya katse shirun da cewa "Faruk kar ka duba kusanci mu ka cutar da kan ka, in har Nana ba ta maka ba ka fad’a min, ni zan fahimce ka".


Mik’ewa yayi yaci gaba da cewa "Zan baka time kayi tunani akan wannan maganar, duk hukuncin da ka yanke akai ina marhabin dashi".


Har ya zuwa wannan lokacin yaya Faruk ya kasa bud’ar baki yayi magana saboda a yanzu bai san wani hukunci zai yanke ba.


Hannu yaya Mus’ab ya bashi suka yi musabaha kana ya mishi sallama ya tafi.





A can ‘bangare na kuwa soyayyar mu muke ci gaba da sha ni da Dr, yanzu ba ni da wata sauran matsala ko damuwa a raina, shi yasa da ka ganni kasan ina cikin kwanciyar hankali da natsuwa.


Yau Dr ne ya kira ni akan in shirya in ya dawo daga aiki za mu je mu gaishe da su Ummu da Momin shi.


Murna ta bi ta cika ni saboda yau ce ranar da zan fara fita tun bayan aure na, ba irin rok’on da ban mishi ba akan ya kai ni gurin su Ummu amma sai ya ce in ba yanzu ba.


Ko da ya dawo sai da ya ja min rai ganin yadda na k’osa mu tafi, sai da yaga zan mishi kuka sannan ya ce in zo mu tafi.


Sai da ya tsaya a wani babban super market ya siya ma su Momin shi da Ummu turarruka masu tsada sannan muka tafi.


Gidan mu muka fara zuwa, yana parking na fito da gudu na nufi side d’in yaya Khalil saboda na ga motar shi a parking space, ganin ba ya side d’in shi yasa na fito na nufi main Parlour.


Sallama nayi na fad’a jikin Ummu na rungume ta ina murna, ita kan ta dariyar farin cikin gani na take yi.


Ina sakin ta na wuce kusa da yaya Khalil na zauna ina murmushi.


Shima murmushin yake maida min saboda murnar gani na da yayi.


"Yau Auta ce a gidan namu" yaya Khalil ya fad’a cikin wasa.


"Ni ce yaya Khalil, nayi missing d’in ku a lot, especially you Yaya Khalil" na fad’a cikin shagwa’ba.


Murmushi yayi kana ya ce "Nima nayi missing d’in ki Fatima, gidan ya min fad’i da ba kya nan".


Ummu ce ta kar’bi zancen da cewa "Au haka ma za ki ce Auta, kin fi missing d’in yayan ki akan mu ko, ai shi kenan".


Dariya muka yi gaba d’aya na ce "Kema kin san Ummu dole ne in yi missing d’in ku ke da Abbu".


"Ina wuni yaya Khalil na gaishe shi.


"Lafiya lau Fatima" Yaya Khalil ya amsa min.


"Ina wuni Ummu"


"lafiya lau Fatima, ya mai gidan naki?" Ummu ta fad’a.


Sai a lokacin na tuna da na bar Dr d’in a waje tun san da muka shigo gidan.


"lafiya lau, tare muke ma dashi".


Ummu ce ta ce "yanzu tare ku ke shine ki ka barshi a waje dan shashanci, tashi ki je ki shigo dashi".


Tashi nayi na fita inda na same shi jingine a jikin mota.


Da murmushi na k’arasa gurin shi na ce "Sorry Dr, murnar zuwa gida ne yasa na tafi ciki na barka".


Shima murmushin yayi kana ya ce "Don’t mind Zarah, nasan murnar ganin su Ummu ne yasa ki ka manta da Dr d’in ki a waje, na miki uzuri".


Turarrukan da ya siya ma su Ummu ya bani kana muka jera dashi har main parlour d’in.


Sun gaisa da Ummu da yaya Khalil kana ya musu sallama akan zai je ya dawo sai ya kai ni gurin Momin shi.


Mun sha hira da Ummu da yaya Khalil kamar kar mu rabu, sai dai har Dr yazo d’auka na Abbu bai dawo gida ba, na so mu had’u dashi yadda na kwana biyu ba mu had’u ba.


Da za mu tafi ne na ba Ummu turaren, fuskarta ta nuna jin dad’in kyautar da muka yi musu.


Haka na musu sallama muka tafi muna kewar juna.


Gidan su muka wuce in da muka same su a falo suna hira.


Bayan mun gaisa ne Farida ta cika gaban mu da kayan motsa baki.


Ba laifi Momi ta tarbe ni, yawanci hirar dai ita da d’an ta suke yin ta ina sauraron su.


Farida ce take ja na da hira jefi-jefi, ji nayi duk na takura kasancewa ta wannan shine zuwana na biyu da nayi, ga kuma rashin sabo da ban yi dasu ba.


Muna zaunen ne a falo sai ga Hanan sun shigo da wata matashiyar yarinya.


Shigar da suka yi ne ta d’aure min kai, in mutum ba yasan yaran hausawa ba ne bai zama lallai ya yarda ba, saboda wani irin English wears da suka sa da d’an wani k’aramin gyale da suka yafa a kansu.


Abin da ya ban mamaki shine ganin ba wanda ya musu fad’a akan shigar da suka yi.


Su biyun gurin in da Dr yake suka je suka zauna yayin da suka sa shi a tsakiyar su.


Ni dai bin su da kallo kawai nake yi saboda mamakin su da ya kama ni.


"Ina wuni yaya Sadik" Meema ta gaishe shi.


Da murmushi ya amsa mata da cewa "Lafiya lau Meema, ya kike, ya su Mom".


Cikin siririyar murya ta amsa masa "Su na nan lafiya lau yaya Sadik".


Hanan ce ta kar’bi zancen da cewa "Ina wuni yaya Sadik".


"lafiya lau Hanan, ya karatu?" ya tambaye ta.


"Normal yaya Sadik" Hanan ta amsa mishi.


 "yaushe ka zo ne yaya Sadik" Meema ta tambaye shi.


"Ba mu dad’e da zuwa ba ni da Zarah, ku gaisa da ita" Dr ya fad’a.


Sai a lokacin hankalin su yakai guri na da nake zaune a d’aya daga cikin kujerun da suka k’awata falon.


Kallo na yayi ya sakar min murmushi kana ya ce "Zarah ga Hanan da Meema".


Murmushi na musu kana na ce "Sannun ku, Ina wunin ku".


Hanan ce ta amsa min ba yabo ba fallasa da cewa "lafiya lau, ya kike".


Ban ba ta amsa bad an gani nayi kamar tambayar rainin wayau ta min.


Meema kuwa tun san da Dr ya ce mu gaisa ta tsura min ido tana kallo na, kallon da take min ne na rasa yadda zan fassara shi dan nasan irin kallon da take min yana d’auke da ma’anoni daban-daban.


Yatsina fuska ta yi kana ta ce "Hi Zarah".


Yadda ta amsa min gaisuwar ya min ciwo amma sai na share abin a raina kamar abin bai yi min ciwo ba.


Momi ce ta ce "Har kun dawo kenan Meema, na ga ba ku dad’e ba".


"Ice cream kawai muka je muka sha muka dawo gida" Meema ta fad’a.


"Ok dama na ga kun yi saurin dawowa ne" cewar Momi.


Wacce aka kira Meema na dinga tunanin ita wacece a gidan su Dr, a iya sani na Hanan da Farida sai  Su ne k’annen shi mata, ita Meeman ce ban san ya suke da ita ba.


Ba laifi Meema kyakkyawa ce, dan ba za ka kira ta mummuna ba, skin d’in ta so fresh, daga gani mayuka masu tsada take shafawa, sai dai a yanayin ta in ka kalle ta kasan rayuwar boko take yi ita da Hanan, shigar su kad’ai ta isa ta nuna maka haka, ganin yadda take shige ma Dr sai abin ya ‘bata min rai, na ga shi Dr hakan bai dame shi ba, sai dai kallon da Meema ta min ne yasa na dinga tunanin dalilin ta na yi min wannan kallon, ni dai a iya sani na yau ne muka fara had’uwa da ita, sai dai fuskarta ta nuna min ba tayi marhabin da ni ba.


Hirar su suka ci gaba da yi suna dariyar su da Dr yayin da Momi kan sa bakin su a hirar.


Jin ban sa baki na a hirar yasa Farida da Dr kan sako ni cikin hirar tasu, ganin hirar ba ta shafe ni ba yasa nayi shiru da baki na, sai dai in sun saka ni a hirar in yi murmushi.


Mun d’an jima a gidan su Dr, da za mu tafi ne na ba Momi perfumes d’in da muka zo mata dashi kana muka yi musu sallama muka tafi.


Haka muka koma gida raina bai min dad’i dan gaskiya yadda na ga Meema na shige ma Dr bai min dad’i ba.



Yaya Faruk tun san da suka yi wannan maganar da yaya Mus’ab ya ke tunanin hukuncin da ya kamata ya yanke akan maganar amma ya kasa, gashi suna had’uwa da yaya Mus’ab a gurin aiki amma bai canza mishi fuska ba ko ya mishi magana akan hukuncin da ya yanke, yasan yaya Mus’ab ba zai mishi magana ba dan kar ya ga ya takura mishi, yasan ya zuba mishi ido ne ya ji hukuncin da zai yanke akan maganar, a yadda ya lura yaya Mus’ab bai fad’a ma Khadija maganar ba tun da ba ta sauya mishi ba, kuma har yanzu suna waya suna gaisawa.

"Me yasa ba za ka amince da maganar da Mus’ab ya zo maka da ita ba ko dan shim aka faranta mishi?" zuciyar shi ta fad’a mishi haka.


Shi kanshi yasan Mus’ab mai son shi ne tsakani da Allah tun da har yayi tunanin bashi k’anwar shi duk kuwa da masoyan da take dashi, yasan ba abin da ya kamata ya saka ma Mus’ab dashi shine ya amince da Khadija ko da kuwa bai jin son ta a ranshi.


Har yanzu yana jin Nana a ranshi kamar k’anwar shi, tana bashi matsayi kamar na yayan ta, sannan tana nuna damuwar ta idan wani abu ya same shi, tana taya shi farin ciki idan abin alkhairi ya same shi, tun san da suka yi maganar nan da yaya Mus’ab har zuwa yanzu bai ji wani feeling na son ta daga zuciyar shi, sai dai zai iya ma Mus’ab komai dan yafi k’arfin komai a gurin shi.


Yasan Nana yarinya ce da kowane namiji zai so ta saboda kyawawan halayen ta, sannan tana da kyau d’in da duk namijin da ya ganta zai iya kamuwa da son ta, ya sa ma ranshi zai auri Nana in har ta amince dashi, sannan ko su Momi in suka ji ya samu wacce zai aura za su ji dad'i a ransu, sannan za su yi murna idan su ka ji k'anwar Yaya Mus'ab zai aura za su yi farin ciki da hakan.


Wannan tunanin da yayi ne ya yanke cewa zai tunkari yaya Mus’ab ya fad’a mishi ya amince da Nana.


Da wannan shawarar ya samu k’arfin d’aukar wayar shi ya kira yaya Mus’ab akan in ya samu lokaci yana neman shi za su yi wata magana ne kana ya katse layin shi.


Ba a wani jima ba sai ga yaya Mus’ab ya zo block d’in yaya Faruk.

Bayan sun d’an ta’ba hira ne yaya Faruk ya fara da cewa "Mus’ab na kira ka ne akan maganar da ka zo min da ita kwanaki, nasan za kayi tunanin ko ban amshi zancen ka da mahimmanci ba ne shi yasa ban tuntu’be ka akan maganar ba, Mus’ab ko da a ce wata ka za’bar min in har ka yaba da tarbiyar ta da kamalar ta zan amshi maganar ka hannu bibbiyu bare Nana Khadija da take k’anwar ka, ko da ba ka fad’a min halin Nana ba ni shaida ne a zaman da nayi da ita akan kyawawan halayen ta da natsuwar ta, Mus’ab na amince da Nana, sai dai zan rok’i alfarma a gurin ka Mus’ab shine ka fad’a ma Khadija wannan maganar, in har ba ta amince ba kar ka matsa mata akan dole sai ta amince, ka fad’a min shawarar da ta yanke akan maganar, zan yi farin ciki idan ta amince, sannan ba zan ji haushin ta ba idan ba ta amince da ni ba".


Murmushi yaya Mus’ab yayi kana ya ce "Kar ka damu Faruk, zan fad’a maka duk yadda muka yi da Nanan".


Nan suka ci gaba da hirar su akan abin da ya shafi aikin su kana ya mishi sallama ya tafi.


[7/29, 22:06] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀





*STORY & WRITTEN*

       


              *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*






*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽



www.maryamahmadpaki.blogspot.com



Facebook: Kainuwa Writers Association






*Gaisuwar ku ta daban ce a guri na ‘yan Kainuwa Writers*



*Mrs Mansoor*  _(Marubuciyar Munafukin Miji)_.


*Fauxia MB*  _(Marubuciyar Conel Akram)_


*Mrs Adam*  _(Marubuciyar Mamaya)_


*Ummy Ontop*  _(Marubuciyar Kishiya tace Silah)_.


*Shatu*  _(Marubuciyar Mai Rabo ka D’auka)_


*Hauwa A Usman*  _(Marubuciyar Kaddara Tah)_


*Batul Adam Jatko* _(Marubuciyar Amfanin Soyayya)_


*Mrs Makama*  _(Marubuciyar Ranar Baiko Na)_


*Maman Aysha* _(Halin Mutum Jarinsa)_



*Wanda ba su ji sunan su ba, su min hak'uri mu had'u a next page*.


*Ana tare ko da yaushe*.







_Amsar question of the day ita ce Suratul Mud’affifun, ita ce take karantar da wajibcin tsare hakk’ok’in mutane, tsakaninsu, a ciniki da wasu mu’amalolin zamantakewa_





*TUNATARWA*:



_Wad'annan halayen guda uku lallai suna daga cikin halayen bayin Alah na k’warai, kuma wanda yayi rik’o dasu tabbas zai zama abin yabo a wajen Allah da bayin sa_.



_Yin afuwa ga mutane_.


_Biyan Bashi da ka samu iko_


_Karanta qul huwal lahu ahad_

_Allah kasa mu dace_







77-78



Yaya Mus’ab da ya samu sauk’in aiki ne ya je gidan su dan jin ra’ayin Nana akan maganar da suka yi da Yaya Faruk.



Lokacin da ya je bai sami Nana a gida ba tana school.



Zama yayi suka ci gaba da hira, ba a wani d’au lokaci ba sai ga Nana ta dawo daga makarantar.



Bayan sun gaisa ne ya ce ta same shi a side d’in shi in ta huta.



Tana gama abin da za tayi ta nufi side d’in yaya Mus’ab d’in.



Samun shi tayi yana kallon tashar Al- Jazeera ta nemi guri ta zauna.



Yaya Mus’ab ne ya kalle ta ya ce "Nana nasan za ki yi ta tunanin dalilin kiran da nake miki da har na ce ki same ni a side d’ina ko?".



Ci gaba yayi da cewa "Kiran mai matuk’ar mahimmanci ne da har ya sa na kira ki nan d’in dan nasan za ki fi sake wa ki fad’a min ra’ayin ki akan maganar da za mu yi, Nana maganar da za muyi akan Faruk ne, nasan kin san abin da ya faru da shi na fasawar bikin shi da aka yi, Nana Faruk yana cikin damuwa wanda yake buk’atar mai lallashin shi a kusa, Faruk yana da zurfin ciki, hakan yasa yake k’ok’arin ‘boye damuwar da yake ciki, Faruk aboki na ne da ya taimaka min a gurin aiki da sauran harkar rayuwa, shi yasa nayi tunanin wace hanya ce zan fitar da Faruk daga halin da yake ciki, dan haka ne na yi tunanin ba wacce za ta cire shi daga wannan halin da ya wuce ke saboda yadda kuka shak’u".



D’ago kai tayi ta kalle shi kana ta ce "yaya Mus’ab ta wace hanya zan iya cire ma yaya Faruk damuwar da yake ciki, ina ganin in ma akwai hanyar bai wuce in ci gaba taya shi da addu’ar Allah yaye mishi damuwar da yake ciki, ya kuma za’ba mishi abin da yafi alkhairi a gare shi".



Murmushi yaya Mus’ab yayi kana ya ce "Nana akwai hanyar da za ki bi wajen mantar da Faruk daga halin da yake ciki, hanyar kuwa ita ce ki aure shi".



Da sauri Nana ta d’ago kai ta kalli yaya Mus’ab dan gasgata kunnuwan ta abin da suka ji mata da yadda maganar ta zo mata a bazata.



Tasan tana jin yaya Faruk a ranta, tana jin wani irin feelings game dashi wanda ita kanta da farko ta danganta shi da had’uwar jini ne, sai daga baya da ta ci gaba da jin feeling d’in fiye da baya ta tabbatar ma kanta cewa wannan feeling d’in ya wuce had’uwar jini, sai dai ita kanta ta rasa a yadda za ta fassara shi.



Tana damuwa a duk lokacin da ta ganshi yana cikin damuwa, haka tana cikin farin ciki idan ta ga yana cikin farin ciki, sai dai a yanzu ba za ta iya cewa farin ciki take yi ko jin haushi akan maganar da yaya Mus’ab ya zo mata da ita.



Taso a ce da kanshi yaya Faruk yayi wannan tunanin akan ya aure ta ba wai shi yaya Mus’ab yayi tunanin haka ba, ita kan ta shaida ne a irin son da yaya Faruk yake min, tasan son da yake min zai wuya ya ma wata macen irin shi, yanzu in ta amince da auren shi ba tasan ko shi yaya Faruk zai yi farin ciki da hakan ba, za taso ta mallaki yaya Faruk a matsayin miji saboda yana da irin qualities da take so a gurin namiji, hasalima yaya Faruk irin mazan nan ne da duk wata mace idan tayi gamdakatar dashi a matsayin mijin ta za tayi murna, da ta tuna da dalilin shigar shi wannan damuwar bai wuce akan son ‘yar uwarshi yasa shi a wannan halin ba sai ta ji jikin ta yayi sanyi.



Yaya Mus’ab ne ya katse mata tunanin da take yi ya ce "Nana ki fad’a min ra’ayin ki akan wannan maganar, in har ba kya son Faruk ba zan takura miki ba, shi kanshi Faruk d’in ba zai ji haushin k’in za’ban shi da kika yi ba, haka ba zai so in matsa miki akan ki amince dashi ba, sai dai in kika amince dashi kinyi taimako, dan za ki ba da taki gudunmawar wajen sa shi mantawa da damuwar da yake ciki, a dalilin wannan taimakon da kika yi sai ki ga Allah ya taimake ki a inda ba ki yi zato ba, kin ga kuma ga Hajiya ta fara miki fad’a akan rashin tsayawa da samari da kike yi, in kika amince da Faruk kin ga kin huta da fad’an Hajiya".



Wannan tattausan kalamen da yaya Mus’ab ya fad’a mata yasa ta ji ta yi na’am da maganar da ya zo mata.



"yaya Mus’ab ko da a ce ban san yaya Faruk ba ka bani shawarar in aure shi zan amince in aure shi, nasan duk wanda za ka za’ba min ya dace da ni ne, yana da halaye nagari, amma yaya Mus’ab shi yaya Faruk d’in ya amince zai aure ni ne, ba zan so muyi aure ba ya da ra’ayi na a ranshi, idan na fahimci hakan zan iya shiga wani halin".



"Kar ki damu Nana, kafin in zo miki da wannan maganar sai da muka yi ta da yaya Faruk ya tabbatar min ya amince, nasan in da Faruk ba ya ra’ayin ki ba zai amince da maganar ba, abin da nake son ji a gurin ki shine in ji kin amince ko akasin haka".



Cikin kunya ta rufe fuskar ta tace "Na amince yaya Mus’ab".



Murmushin farin ciki yayi da jin amincewar da Nana tayi ya ce "Nana nagode da ba ki bani kunya ba, duk da nasan daman ba za ki bani kunyar ba, insha Allahu sai kin yhi farin ciki da kasancewar ki da Faruk, abin da zan ce miki shine ki yi hak’uri da yanayin Faruk a yanzu, a hankali sai ki ga komai ya zama normal".



Haka yaya Mus’ab ya ci gaba da nuna mata fa’idar amincewa da yaya Faruk kana suka zarce da hira.



Lokacin da suka had’u da yaya Faruk ne yake sanar dashi yanda suka yi da Nana.



Jin ta amince da maganar yasa a ranshi ce wa zai aure ta ko da ba ya jin son ta a ranshi, yasan amincewar shi zai sa mutane da dama farin ciki, hasalima zai iya zama da Nana dan tana da wasu halaye da yake buk’ata a gurin matar da zai aura.



Ya ma yaya Mus’ab godiya da irin wannan karamcin da ya mai.




Tun san da yaya Mus’ab ya fad’a mai Nana ta amince yake tunanin yadda zai fara zuwa gurin Nana zance, hasalima shi har yanzu kallon k’anwa yake mata, sai dai yasan zuwan shi gurin ta shine da zai tabbatar da ya amince da ita, hakan ne zai sa shi yaya Mus’ab yasan ya amshi zancen hannu bibbiyu.





A ‘bangare na kuwa zaman mu ya ci gaba da gudana cikin zaman lafiya da kulawa, tsakanin ni da Dr kowa k’ok’ari yake yi wajen faranta ma d’an uwan shi.



Matsala ta da Dr bai wuce yawan hana ni zuwan gidan mu ko abin da ya dangancin family d’in mu, na sha tambayar shi dalilin shi nayin haka, sai ya ce min ba ya son ina yawan fita ne, hakan yasa na rage tambayar shi in ba abu ya kama ba.





Yau ta kasance ranar weekend, ina zaune a falo ina kallon wani indian series film da ake watso wa a tashar GH one mai suna revenge.



Knocking d’in da na ji ana yi ne ya katse min kallon da nake yi, tashi nayi in je in bud’e.



Ina bud’e wa na ga su Farida ne da Meema, hanya na basu suka shigo kana na kulle k’ofar na dawo na zauna.



Farida ce da Hanan su ka gaishe ni yayin da Meema ta d’aura k’afar ta d’aya akan d’aya tana yatsina fuska.



Tashi nayi na d’akko musu drinks da snacks na ajiye musu.



Meema ko kallan kayan da na kawo musu ba tayi ba sai ma wayar ta da ta d’akko tana dannawa.



Yau cikin shigar transparent material suka yi, sai dai kowa kalar material d’in na sa daban.



Hanan da Meema ne suke hirar su yayin da ni da Farida muke hira akan film d’in da ake yi a tashar GH one.



Hanan ce ta kalle ni ta ce "Anty Zarah yaya Sadik na nan ne, in yana nan ki yi mana magana dashi".



Amsa mata nayi da cewa "Eh yana nan, barci yake yi bari in taso muku shi".



Tashi nayi na nufi d’akin da yake kwance na zauna kusa dashi.



Hura mishi kunne na dinga yi har ya bud’e idon shi, kallo na yayi ya sakar min murmushi ya ce "my Zarah ya aka yi ne".



Murmushin na mayar mishi kana na ce "Su Farida ne suka zo".



"Ok ki ce musu gani nan zuwa, bari in d’an watsa ruwa" ya fad’a yana shafa fuska ta.



"Sai ka fito" Na fad’a a tak’aice.



Komawa nayi na sanar dasu yana zuwa kana na nufi kitchen dan in musu girki. 


Kuskus da kidney source na musu, bayan na gama ne na musu Banana milk shake.



D’akko food flask d’in nayi da plates na kawo musu inda suke, na koma d’akko drinks d’in da na had’a musu da kofuna na ajiye musu.



Ganin Farida ce kad’ai take cin abincin yasa na ce "Hanan ku ci abincin".



"Na k’oshi ne" Hanan ta bani amsa a tak’aice.



Farida ce ta kalli Meema wacce hankalin ta ke kan wata ta ce "Anty Meema in zuba miki abincin ne".



Ta’be baki tayi kana ta ce "No ki barshi, ba na jin cin abincin ne".



Raina ne na ji ya soma ‘baci yadda Meema ke min in muka had’u, a yadda na fara karantar Hanan ita ma na ga tana ji da kanta, ina ganin hakan ne yasa ma suka fi shiri da Meeman.



Faridan ce ta kalle su ta ce "Anty Meema da Anty Hanan da kun zo kun ci ko kad’an ne, kun ga saboda zuwan mu ne ta tashi ta dafa"



Meema cikin fad’a ta ce ma Farida "Mun ce ta mana girki ne da zaki ce saboda mu tayi girkin, ba ma jin ci ne ko dole ne sai mun ci, ba na son irin haka Farida".



Hanan ce ta kar’bi zancen da cewa "Ke ma Meema ki k’yale ta, kin san Farida da neman suna".



"Allah ya baku hak’uri" abin da Farida ta ce musu kenan.



Duk wannan maganganun da suke yi du kina jin su amma sai nayi kamar ban ji su ba, ban yi zaton daga abin mutunci zai koma na tsiya ba, daman Meema tun a gidan su Dr na ga take-taken ta, za ko tasha mamaki na in dai haka za ta ci gaba da yin, dan ba zan juri rainin hankali ba, ita ma Hanan naga tafiyar su d’aya da Meeman, dole in yi taka tsantsan dasu.



Falon ne ya d’auki shiru kamar ba kowa a ciki.



Dr ne ya fito cikin shigar k’ananun kaya ya zo ya zauna kusa dani.



Gaisawa suka yi kana suka ci gaba da hira.



Hanan ce ta ce "Yaya Sadik Habeela za ka kaimu".



Hararar ta yayi ya ce "Ku miye amfanin motar ku da ba zaku ba, sai ni zan kai ku".



Marairaicewa Hanan tayi ta ce "yaya Sadik mun kwana biyu fa ba mu fita da kai ba, ka ga kai kana gurin aiki, mu kuma muna school, plsss yaya ka kaimu".



Ni ce na ce "pls Dr ka kaisu".



Murmushi yayi ya ce "Zan kaisu amma sai na ci abinci".



Tashi nayi na nufi kitchen dan in zubo ma Dr abinci.



Ko da na dawo sai na tarar da Meema kusa dashi suna hira.



Wani irin takaici ne ya kama ni ganin Meema da Dr kusa da juna.



Jiki a sanyaye na k’araso nayi serving d’in shin a koma kusa da Farida na zauna.



Kallo na yayi ya ce "Zarah ki zo mu ci, ko ni kad’ai yau kike son in ci abincin".



Murmushin yak’e na yi na ce "Na riga na ci nawa" Na bashi amsa a tak’aice.



Bai ce komai ba yaci gaba da cin abincin shi.



Meema ce cikin shagwa’ba ta kalli Dr ta ce "yaya Sadik zan ci abincin".



Hararar ta yayi ya ce "Ba ga abincin can kusa da Farida ba an zubo muku, ki je ki zuba ki ci" Dr ya fad’a.



Farida ce ta kar’bi maganar da cewa "Anty Meema ba yanzu ki gama cewa ba kya jin cin abincin, yanzu kuma kin ce za ki ci".



Harara Meema ta watsa ma Farida kana ta ce "Ina ruwanki, da ban a jin cin abincin ne, yanzu nake jin ci, ko za ki hana ne".



Farida shiru tayi ba ta ce mata komai ba.



Dr ne ya kalli Meema ya ce '"Meema kin cika rigima, tun d’azun an kawo muku abincin kin k’i ci, sai yanzu da kika ga an zubo min za ki ce za ki ci".



"yanzu ne fa na fara jin yunwar yaya Sadik" cewar Meema.



"Ki je ki zuba wancan ki ci" Dr ya ba ta amsa a tak’aice.



K’ara shagwa’be mai tayi ta ce 'Ni da kai zan ci yaya Faruk".



Shiru ya mata bai ce mata komai ba, hakan yasa ta d’auki spoon ta fara ci a plate d’in da na zuba ma Dr.



Ni dai ina zaune ina kallon ikon Allah, in raina yayi dubu to ya gama ‘baci, ji nake yi kamar in je in watsar da abincin ko na samu sauk’in ‘bacin ran da nake ji, abin da ya k’ara ‘bata min rai shine yadda Dr bai nuna damuwar shi ba akan abincin da Meema take ci dashi.



Tambayar da nake ma kaina shine Meema tana da nufin ta yin haka, dan har yanzu ban san Meema wacece ita a gurin su Dr ba.



Ganin in na ci gaba da zama ina ganin wannan takaicin raina ne zai ci gaba da ‘baci, hakanzai iya sa in kasa controlling d’in kaina, dan haka ne na tashi na nufi d’aki na kwanta.



Dr ne ya shigo ya sanar dani za su fita.


Tashi nayi muka fito tare dan muyi sallama dasu.



Sallama na musu na raka su har bakin k’ofa.



Ina kallo san da za su shiga mota, Meema ce ta shiga gaba.



Dawowa nayi na zauna ina mamakin Meema, Dr kawai zan jira yazo ya min bayanin wacece ita a familin su, dan ina ganin bazan zuba ido tana min abin da ta ga dama ba.



Sai can yamma Dr ya dawo tare da siyayyar da ya min na ice-cream da snacks d’in da ya siyo min.



Ji nayi ba na marmarin abin da ya siyo min, saboda har yanzu ban daina jin haushin Meema ba a raina.



Da daddare ina kwance a jikin Dr muna hira na kalle shi na ce "Dr dama akwai tambayar da nake so in maka".



Kanne min ido yayi ya ce "You can go ahead Zarah".



"Wai Meema ita ma ‘yar uwarku ce, na ga baka ta’ba bani labarin ta ba".



Murmushi yayi ya ce "yarinyar abokin Dadi d’in mu ce, ta saba da ‘yan gidan mu sosai, in ba ma sani kayi ba zaka iya cewa ‘yar gidan mu ce dan yawanci tana gidan mu, mu ma mun saba da gidan su".



Shiru nayi ina mamakin ashe ba abin da suka had’a ma take min wa'innan abubuwan, "to miye dalilin ta nayi min haka".

Wannan dalilin ne ban sani ba.



Kamar in ma Dr magana akan abin da Meema ke min sai na ga rashin dacewar hakan.



Haka ya ci gaba da fad’a min amincin Dadin su da Dadin Meema ina sauraron shi kana muka tashi muka je muka kwanta.



Yaya Faruk ya yanke cewa yau da yamma zai je gidan su Nana, dan haka ya fad’a ma yaya Mus’ab akan ya fad’a ma Nana yana nan zuwa.



Tun da yaya Mus’ab ya kira Nana ya fad’a mata yaya Faruk na nan zuwa ta rasa sukuni.



Tunani take yi akan da wane ido za ta kalli yaya Faruk a matsayin saurayin ta bayan ita kallon matsayin kallon kamar yayan ta haka take mishi, hasalima ita kunyar had’uwa take yi dashi tun san da yaya Mus’ab ya fad’a mata maganar, shi yasa ta dinga kauce ma had’uwar su.



Da yamma yaya Faruk ne ya shirya cikin lallausan yadi kalar brown.



Motar shi ya shiga ya ja, sai da ya tsaya a super market ya mata siyayya kana ya wuce gidan su Nana.



Yana zuwa mai gadi ya bud’e mai ya shiga yayi parking a harabar gidan.



Kiran ta yayi a waya ya sanar da ita zuwan shi.



Fito wa tayi ta same shi a inda yayi parking d’in motar shi.



Bayan sun gaisa ne ta bud’e musu side d’in yaya Mus’ab suka shiga.



Sai da ta cika gaban shi da kayan motsa baki kana ta nemi guri ta zauna.



Sun k’ara gaisawa ne kana yaya Faruk ya fara jan ta da hira.



Kasa sakin jikin ta tayi ta bashi amsa saboda yadda a yanzu take jin kunyar shi.



Shiru ne ya ratsa falon, sai k’arar AC da ke tashi a falon, kowa da kalar tunanin da yake yi.



Shi yaya Faruk yana tunanin hanyar da zai bi wajen tambayarta ta amince za ta aure shi alhalin bai fad’a mata yana son ta ba, ita kuma Nana tunanin d take yi shine yadda za ta kalli yaya Faruk a matsayin saurayin ta.



Yaya Faruk ne ya kau da shirun da cewa "Khadija nasan kin san dalilin zuwa na, Mus’ab ya fad’a min ki amince akan maganar da yazo miki da ita, amma duk da haka ina so in ji daga bakin ki cewa kin amince za ki aure ni, ba na so a shiga hakk’in ki, kar ki ji kunya ta, ki d’auka kamar da Mus’ab kike magana, zan fahimce ki?" ya tsura mata ido yana jiran jin amsar ta.



Wata irin kunyar yaya Faruk take ji, duk wannan zaman a takure take.



Sunkuyar da kanta tayi ta kasa d’agowa ta kalle shi ta bashi amsa.



Shi kanshi yaya Faruk ya fahimci hakan, amma duk da haka ya ce "Khadija ina jiran amsar ki, ko ba ki amince ba".



A hankali ta ce "Na amince yaya Faruk, Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi gare mu baki d’aya".



Yaji dad’in addu’ar da ta musu, hakan yasa murmushi ya su’buce a  fuskar shi ya ce "Good Khadija, na gode da kika amshe ni a matsayin wanda za ki aura, Khadija ina yabawa da kyawawan  d’abi’un ki, natsuwar ki da hankalin ki, wannan halayen na daga cikin abin da namiji yake buk’ata a gurin duk macen da zai aura, ina so ki kalle mu a matsayin auren soyayya za mu yi, kar ki sa ma ran ki wasu tunani akan cewa a da ina da wacce nake so, daman Allah bai nufa Fatima mata ta ba ce shi yasa har ta auri wani, kin ga ni dake duk ba mu kawo ma kan mu hakan ba a baya, sai gashi Allah ya sauya lamarin wanda in Allah ya nufa za mu zama miji da mata, ina fatan kin fahimci bayani na".



"Na fahimta yaya Faruk" Nana ta fad’a.



Sun d’an ta’ba hira, yawanci duk hirar tasu yana tambayar ta ne akan School kana ya mata sallama ya tafi.



Bayan Nana ta koma gida ne ta bud’e abin da yaya Faruk ya kawo mata, kayan make-up ne da tsadaddun turare, tayi farin ciki da kyautar da ya kawo mata, tasan wannan kyautar da ya mata na daga cikin alamun nuna kulawar shi gare ta.



Tun daga wannan lokacin yaya Faruk yakan yi k’ok’arin kiran ta ko su had’u a chat, in ya samu lokaci yakan je gurin ta.



Mu’amalar shi da Nana sai ta zamo abin burgewa dan suna ganin mutuncin junan su.



San da yaya Mus’ab ya sanar da Hajiyar su da Dadin su halin da ake ciki sun yi farin ciki da jin wannan labarin, dan sun yaba da halayen yaya Faruk da kyawawan halayen shi, sun san Nana tayi dacen samun gwarzon namiji irin yaya Faruk.




Zaman mu da Dr sai son barka, ba na tare da wata matsala sai wacce ba za a rasa ba tsakanin miji da mata.



Anisa ta kan lek’o ni in tana free kasancewar ta samu D.E a Kasu, sun bata Microbiology.



Abbu da Ummu sun zo da yaya Khalil, ranar haka na wuni cikin farin cikin ganin su da na yi.

Dadin su Dr da Momin shi sun zo gidan mu.



A cikin haka ne Dr ya sai min form na HND, nayi murna san da ya sanar min in kawo credential d’ina zai min applying d’in HND ne.



Ba a wani d’au lokaci ba Admission ya fito na samu gurbin ci gaba da HND d’ina a nan Kaduna Polythecnic.



Karatu na yana tafiya yadda nake so cikin nasara.



Matsalar Meema sai abin da yayi gaba, sai dai ina k’ok’arin danne fushi na idan na ga tana nema na da fitina, a gefe kuma na ga Hanan tafiyar su d’aya da Meema, har yanzu kuma ban fad’a ma Dr abin da yake faruwa ba.




Yau ranar ta kasance ranar weekend, ban dad’e da dawowa daga School ba kasancewar wani lecturer da ya ce mu zo ran sati.



Dawowa ta kenan na kwanta a 3-sitter ina hutawa.



Sallamar su Hanan na ji sun shigo kasacewar a bud’e na bar k’ofar.



Jin sallamar su ne yasa na tashi na zauna ina murmushi.



Farida ce da Hanan suka gaishe ni, Meema kuwa ko kallo ban ishe ta ba.



Tashi nayi na kawo musu drinks.



Meema ce ta ce "Hanan zo mu shiga kitchen in samu soft food in dafa, yau throughout ban ci komai ba".



Hanan ce ta ce "Mu je toh".



Nasan Meema abin da zan tanka mata take nema ba ta samu ba, shi yasa take nema na da fitina.



Basu d’auki lokaci ba suka fito falon.



Soyayyar taliya suka dafa da suka sa mata kayan lambu.



Sun fara cin abincin ne suka kalli Farida suka ce tazo su ci ta ce ba ta ci.



Haka suka gama cin abincin nan ba tare da sun d’auke ko da spoon ba, ni kuma nayi alk’awarin bazan d’auke komai ba, dan na ga abin nasu kullum gaba yake yi.



Dr ne ya shigo falon kasancewar da zan tafi school shi yayi dropping d’ina yace min zai lek’a cikin asibiti akwai patient d’in da zai duba.



Tun da ya shigo falon yaga yadda aka ‘bata shi ya d’aure fuska, ko da su Hanan suka gaishe shi a tak’aice ya amsa musu.



Sannu da zuwa na mishi na kau da fuska ta kamar ban san abin da yake ma fushi ba, nima bai san raina a ‘bace yake ba.



Lokacin da zai shiga side d’in shi ne ya min magana akan in same shi a ciki.



Tashi nayi na bishi dan in ji mai zai ce min.



Bayan tafiya ta ne Farida ta kalli su Hanan ta ce "Ya kamata Anty Hanan ku gyara falon nan, kun san yaya Sadik ba ya son k’azanta".



Harara Meema ta watsa mata ta ce "Ba za a d’auke ba Farida, na ga kamar tsoron Zarah nan kike yi".



Farida ce ta mata wani irin kallo kana ta ce "plss Anty Meema ba da ke nayi magana ba da za ki fara min fad’a, da Anty Hanan nake, da kike cewa ina tsoron Anty Zarah ai ba laifi ba ne, dan matar brother d’ina ce".



Jin yadda Farida ita ma ta bud’e mata wuta ne yasa tayi shiru ba tare da ta k’ara cewa komai ba, in ban da faman hararar Farida ba abin da take yi.



Ita kuwa Hanan danna wayar ta take yi ba tare da ta sa musu baki a maganar ba.



Ina shiga d’akin na same shi yana rage kayan jikin shi.



Kallon shi nayi na ce "Dr me zan dafa maka, ban dad’e da dawo wa daga school ba, ban d’aura komai ba".



Maimakon ya bani amsa sai ce min yayi "Zarah akan me za ki bar falon da datti, kin san ba na son k’azanta, shine za ki bar falon a haka kuma kin san zan yi magana".



"Ai ba ni na ‘bata ba, su Hanan da Meema ne suka ci abincin suka ‘bata gurin" nima na fad’a cikin d’aurewar fuska.



"Da suka ‘bata ba sai ki gyara ba ko ki musu magana su gyara" cewar Dr.



"Ina jin kafin su tafi za su gyara ne shi yasa ban yi musu magana ba" na fad’a.



Bai k’ara ce min komai ba ya fita daga falon yayin da na nemi guri na zauna akan gadon.



Yana zuwa ya daka musu tsawa yace "Shine kuka ci abinci ku ka bar gurin haka, kun san ban son k’azanta, da ku ka bar falon haka wa kuke nufin ya gyara muku, tun kan ranku ya ‘baci ku tashi ku gyara falon nan sannan ku wanke kayan da kuka ‘bata".



Ba shiri su Meema suka mik’e suka fara gyara falon kana suka wanke kayan da suka ‘bata.



Suna gamawa suka shiga mota suka tafi ba tare da sun min sallama ba.





A ‘bangaren yaya Faruk sun fahimci juna da Nana, hakan yasa yaya Faruk ya kira su Dadi ya sanar dasu halin da ake ciki.



 Dadi da Momi sun ji dad’in wannan labarin, hakan ne yasa Dadi yace ma yaya Faruk ya sanar da Dadin su Nana d’in suna na zuwan Abujan da a tsayar da maganar bikin.



Anisa ma da Momi take fad’a mata maganar ta ji dad’i da Allah ya musanya ma yaya Faruk da Nana, dan a kwana d’aya da tayi da ita ta fahimci rashin hayaniyar Nanan da natsuwar ta.



Shima Abbu san da Dadi ya sanar da shi maganar yaya Faruk da Nana ya yi farin ciki da jin wannan maganar, hakan yasa suka tsayar da ranar da za su je Abujan.



Ran weekend su Abbu da Dadi da Kawun wagini suka tafi Abuja.



An musu tarba mai kyau da karamci, bayan sun gaisa ne su Abbu suka gabatar da abin da ya kawo su.



Sun ba da kud’in gaisuwar iyaye kana suka tsayar da nan da sati biyu za su dawo a sa rana, haka suka rabu ana wasa da dariya.



Sati biyu na cika su Abbu suka koma Abuja, an tsayar da biki nan da wata uku.



Bayan dawowar su Abuja ne aka yanke shawarar had’a bikin su da su Anisa tun da yanzu yaya Khalil ya fara aiki a wani private Hospital inda suka bashi d'aya daga cikin pharmacist store.



Ko wani ‘bangare shirye-shirye ake yi ba kama hannun yaro.



Yaya Faruk bai samu zuwa Kaduna ba saboda yadda aiki ya tsare shi a Abuja, ya ce in ya samu sauk’in aiki zai zo, dan haka ta waya suke tattauna wa akan maganar bikin.



Momi duk ta fi kowa murnar wannan auran da yaya Faruk zai yi, tana ganin hanyar fitar yaya Faruk ne yazo, ga kuma bikin auta Anisa da yazo a tare da yaya Faruk, dan haka shiri take yi ba na wasa ba.



Sun yi da da Momi akan zai turo kud’i a had’a mishi kayan akwati tun da bashi da time, san da Momi ta sanar dashi akwatin da ya had’a min yana nan, ya sanar da ita a ajiye su, in yazo zai san yanda za ayi da kayan, a had’a wasu tun da wannan sun kwana biyu.





Lokaci na ta tafiya yayin da biki ke ta matsowa.



Yaya Faruk ya tambayi Nana in akwai event d’in da ta tsara ta fad’a mishi, ta nunan mishi da walima da kamu kawai za tayi, yayin da ‘bangaren shi abokan shi suka had’a mishi crossing of the sword.





Yau biki ya rage sati biyu, dan haka ne yaya Faruk ya nemi excuse a gurin aiki ya tawo Kaduna.



Momi tayi murnar ganin shi ganin yanzu bai da wata sauran damuwa, duk tasan har yanzu abin da ya faru ba mai sauk’in wuyar fice wa ba ne a rai.



Lokacin da Momi take tambayar shi abubuwan da suka tsara ya sanar da ita, haka Momi ta dinga jero mishi event d’in da ta tsara.




Sai dai yayi murmushi kawai, yasan Momi ta na so yayi aure, ga kuma abin da ya faru tsakani na dashi, dole yanzu ta nuna murnar ta.



Ta nuna mishi akwatunan da ta had’a da wanda ita ma ta siya, shi kanshi yaya Faruk kayan sun burge shi ya kuma yaba.



Yaya Faruk ya je gidan mu, su Abbu da Ummu sun yi murnar ganin shi, sun mishi fatan alkhairi a auran da zai yi tare da sa mishi albarka.



Har kullum yana d’aukar su Abbu kamar iyayen shi, ba sa banbanta shi dasu yaya Aminu.



Yaya Faruk yaje gidan yaya Aminu inda Anty Jiddah ta dinga tsokanar shi, sun tattauna da yaya Aminu akan yadda bikin zai kasance.



Yaya Khalil ma ya had’a akwatuna na burgewa masu kyau da tsada.



Yaya Khalil na yawan kira na yana fad’an min abubuwan da suka dangancin bikin.




Nima na je gida san da muka yi waya da yaya Khalil yake fad’a min an sa biki, haka na kira Anisa ina ta tsokanar ta.



Ba yadda ban yi da Dr akan ya barni in je gidan mu tun da bikin ya matso amma ya k’i yace sai bikin ya kusa.



Haka na k’yale shi ba dan raina ya so ba, ina jiran a shiga satin bikin.


An kai kayan akwati gidan su Nana, da su Ummu aka kai akwatin da su Anty Jiddah da k’anwar Momi Anty Fauziyya sai k’awar Momi.



An basu tukwici na kai kayan da suka yi.



San da su Ummu suka dawo ne ta kira ni a waya ta fad’a min fad’a akan rashin zuwan da ban yi ba, na ba ta hak’uri akan ranar mu na test a makaranta ne duk da ba gaskiya na fad’a mata ba, nasan idan ta ji Dr ne ya hana ni baza ta ji dad’i ba, ta fad’a min lokacin da za a kai kayan yaya Khalil, mun yi da ita akan insha Allahu zan zo ranar.




Lokacin da Dr ya dawo nake fad’a mishi bai ce min komai ba, sai na d’auka ya amince min ne.



Ana gobe za a kai kayan da daddare muna kwance da Dr nake k’ara fad’a mishi gobe zan je gida ba zan je school ba saboda ina son akai kaya dani.



Wannan karan ma bai ce min komai ba, hakan ya ‘bata min rai saboda ban san ma’anar shirun shi ba.



Da safe yana shirin tafiya aiki na ce "Dr jiya na tambaye ka zan je gidan mu ba ka ce min komai ba".



"Ba za ki ba ne Zarah" ya fad’a min a tak’aice.



Wani irin ‘bacin rai na ji ya ziyarce ni, lokaci d’aya na ji wasu hawaye sun tarun min a idanu na, na rasa manufar dalilin Dr na yi min haka, in sha’anin family d’in su ne da na mishi maganar shi zai kai ni ba tare da ya min musu ba, amma in dai abin da ya dangance ni ne sai ya dinga kakkaucewa, ina ganin wannan karan dole ne in k’waci ‘yanci na, ba zai yiwu ya dinga hana ni yin zumunci da ‘yan uwa na ba.



"Akan me zai sa ba zan je ba Dr" na fad’a cikin ‘bacin rai.



"Saboda ina da ikon hana ki zuwa ko ina, shine dalilin" ya bani amsa.



Hawaye ne suka zubo min na share na ce "Dr in ka min haka ba ka min adalci ba, san da za akai akwatin yaya Faruk haka ka hani ni zuwa, yanzu ga na yaya Khalil za akai akwatin shi ka ce ba zani ba, ka kuma san yadda muke, da wani ido kake so in kalli su Ummu da mutane idan ban je ba, Dr ina so ka fad’a min dalilin ka da ba ka yawan bari na in je sha’anin family d’in mu alhalin ka na bari na ina zuwa na family d’in ka".



"Ba sai na fad’a miki dalili ba" ya fad’a min a tak’aice.



Yana gama fad’ar haka ya fita daga falo.



Zama nayi a falon ganin yadda Dr ya min halin ko in kula da damuwa ta, bai damu da abin da hakan zai jawo min idan ban je ba.



Wasu hawaye ne suka dinga zubo min na takaicin Dr.



Zuciya ta ce take bani shawarar akan in shirya in je tun da na tambaye shi ya k’i bari na.



Haka na tashi na shirya na kulle k’ofar na shiga motar da Dr ya siya min, ba ko wane lokaci nake hawa ba saboda hannu na bai gama k’wari ba.



Ina zuwa gidan mu na ga ‘yan uwa, nan wani farin ciki ya ziyarce ni.



Ban wani jima da zuwa ba aka tafi gidan su Anisa dan kai akwatunan.



A raina ina fargabar zuwa saboda so d’aya muka zo da Dr muka gaishe su, ranar Dadi na nan, ban san yadda Momi wani kallo za ta min idan ta ga har dani aka kawo akwatin.



Ga mamaki na san da muka je gidan haka Momi tayi ta nan-nan dani, haka ta dinga ja na a jiki, haka yasa na ji dad’i a raina, na san Momi ni mutuniyar ta ce, tun san da abin da ya faru tsakani na da yaya Faruk take fushi dani, yanzu na tabbatar da ta daina fushi dani.



Haka na shiga d’akin Anisa ina tsokanar ta, zama nayi muka sha hira irin wacce muka kwana biyu ba mu yi irin ta ba.



Sai da muka d’an jima kana muka tafi.



Haka Momi ta ba su Anty tukwici na

 kayan akwatin da muka kawo.



Muna koma wa gida na wuce side d’in yaya Khalil, nan na zauna muna ta tsara yadda bikin zai kasance kana muka zarce da hira.



San da zan tafi gida ne muka had’u da yaya Aminu ya zo d’aukan Anty Jiddah, tsayawa nayi muka gaisa.



Sallama na musu kana na shiga mota ta na ja.



Sai da na fara tafiya ne fargaba ta kama ni dan yanzu nasan Dr ya dad’e da dawowa daga aiki, gashi ba yaso in kai yamma idan na fita, yanzu kuma gashi yamma tayi sosai.



Da wannan tunanin na isa gida, ina shiga harabar gidan na ga motar shi a parkin space.



Ganin k’ofar falon a bud’e yasa na shiga da sallama ta.



Samun shi nayi a zaune yana kallon tashar Master Channel.



Ciki-ciki ya amsa min sallamar da na yi mai.



"Sannu da gida Dr".



Bai amsa min ba sai ma tambaya da ya watso min "Daga ina kike?".



Duk da nasan yasan in da naje bai hana ni amsa mishi da cewa "Daga gidan mu nake".



"Good" ya fad’a a tak’aice.



Ci gaba yayi da cewa "Amma ba na ce miki kar ki je ba".



Duk da masan ban da gaskiya tun da na fita ba da izinin shi ba, hakan bazai hana ni in k’watar ma kaina ‘yanci ba.



"Ka ce kar in je, amma na ga zuwa na yana da mahimmanci, shi yasa na je, amma kayi hak’uri fitar da nayi ba tare da izinin ka ba".



Bai ce min komai ba ya tashi ya tafi side d’in shi.



Ganin bai min magana ba yasa jiki na yayi sanyi na nufi d’aki na.



Da daddare na shirya cikin shigar kayan bacci na nufi d’akin Dr.



Samun shi nayi yana danna laptop.



Duk da yaji shigowata amma hakan bai sa ya d’ago kanshi ya kalle ni ba.



Kusa dashi na je na zauna na ce "Dr sannu da aiki".



"Yawwa" ya amsa min a tak’aice.



"Me kika zo yi?" ya tambaye ni.



Tambayar ta ban mamaki da takaici tare da wani irin haushi da tasa na tsaya ina kallon shi, amma sai na danne fushi na ce "wannan wace irin tambaya ce Dr, za ka ce me na zo yi, kwanciya na zo yi".



Cikin d’aurewar fuska ya ce "Ki tafi side d’in ki kije ki kwanta, a yanzu ba ni da buk’atar ki, in ina buk’atar ki zan nemi ki, tun da ni ban isa in baki umarni ki bi ba".



Tsayawa nayi ina al’ajabin Dr tare da mamakin shi, duk da kunne na ya jiyo min abin da Dr ya fad’a min amma na kasa gasgata kunne na.



Ina ganin akan fitar da nayi har ya kai ya zama wani laifi da har Dr zai hukunta ni irin hakan, bayan na bashi hak’uri akan laifin da na mishi duk da nasan akan gaskiya ta na aikata hakan.



"Wai ni yau Dr yake cewa in tashi in bar mishi d’aki bai da buk’ata ta".



Tashi nayi na fita daga d’akin.



Tun kan in k’arasa side d’ina na fashe da wani irin kuka mai cin rai.



Kwanciya nayi akan gado ina ci gaba da kuka, a lokaci d’aya ina mamakin Dr.



Sai yanzu ne Kalmar na da aka fad’a min na cewa aure zaman hak’uri ne ya fad’o min, da ni a gani na in har kuna son junan ku ba wata matsala da ka iya zuwa ta muku dabaibayi a zaman ku, sai gashi tun ba a je ko ina ba na fara ganin dalilin da yasa ake cewa in yi hak’uri.



Da k’yar na samu bacci ya d’auke ni saboda yadda nayi sabo da jikin Dr, ga kuma takaicin abin da ya min a lokaci d’aya.


Post a Comment

0 Comments