makauniyar soyayya hausa novels 13

 MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀




*STORY & WRITTEN*     

    


          *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*






*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽








*FATAN ALKHAIRI*


_Ina ma duk wani fans d’ina fatan alkhairi a duk inda yake, Allah ya bar zumunci da so_.





_Amsar question of the day ita ce Nusaiba bintu Ka'ab Al Mazaniyya (RA), ita ce ta d’auki takobi ta kare Manzon Allah (S.A.W) a lokacin da mazaje suka guje daga gare shi, da kuma san da annabi ya ce mata "Tambaye ni abin da kike so?" Sai ta ce masa "Ina rok’on ka kasancewa mak’ociyar ka a Aljanna da son ka a duniya da son ka a lahira"_.






73-74


Dr ne yazo ya gwada BP d’in shi inda yaga ya hau sosai akan san da yazo gida ya duba shi, ya gano ba abin da ke damun yaya Faruk da ya wuce damuwa da tunani da ya sa ma kan shi, wanda hakan zai iya sa ya kamu da ciwon zuciya.


Bayan ya gama gwaje-gwajen ne ya kalli su Dadi ya ce "Alhaji kamar yadda na fad’a muku ne a baya, Faruk yasa damuwa da tunani da damuwa a ranshi wanda hakan yasa ya kamu da hawan jini, yanzu a gwajin da na mishi BP d’in shi yayi high akan san da na zo na duba shi a gida, idan ya ci gaba da wannan tunanin da sa damuwa a ranshi zai iya kamuwa da ciwon zuciya, ya kamata a kiyaye abin da zai sa shi damuwa da tunani, insha Allahu zan d’aura shi akan magunguna".


Jin wannan bayanin yasa jikin su Dadi ya k’ara sanyi da halin da yaya Faruk yake ciki, sun san duk wannan ciwon da yake fama dashi duk a sanadi na ne.


Dady cikin dauriya ya kalli Dr d’in ya ce "Insha Allah za mu dinga kiyayewa, mun gode Dr".


Hannu ya mik’a mishi suka yi musabaha kana ya musu sallama ya fita daga room d’in.


Momi kuwa k’arin jin haushi na ne ya k’aru a zuciyar tar, ta san ni ce silar fad’awar yaya Faruk cikin wannan halin da yake ciki.


Tasa a ranta cewa za ta taya yaya Faruk addu’a akan Allah ya kawo mishi sauk’i da mafita a cikin halin da yake ciki, Allah ya canza mishi da abin da yafi zama alkhairi gare shi, ya canza mishi da wacce tafi ni.


A yanzu yadda take ganin na za’bi Dr Sadik akan yaya Faruk, ko da a ce na amimce da auran da yaya Faruk, ita ba za ta yarda ba, ba za ta yadda d’an ta ya dinga shiga wani hali ba akan mace.


Dadi ma na cikin damuwa akan halin da yaya Faruk ke ciki, yasan duk abin da ya samu bawa dama rubutacce ne daga wajen ubangiji, dan haka zai dinga ma a yaya Faruk add’a akan Allah ya bashi wacce za ta so shi tsakani da Allah shi ma yaso ta.


Dadi ne ya kira Abbu ya sanar dashi rashin lafiyar yaya Faruk.


Cikin tashin hankali Abbu ya sanar da su Hajiya da Ummu halin da yaya Faruk ke ciki, Hajiya tun da taji rashi lafiyar yaya Faruk take kuka.


Haka Abbu ya d’auke su ya kai su Asibitin, ko da suka je asibitin, kuka Hajiyan Wagini taci gaba dayi, sai da aka ce mata likita ya ce ba ya son hayaniya sannan ta daina kuka, ba abin da take mai sai addu’ar Allah ya bashi lafiya.


Sai da yaya Faruk ya farka suka mishi ya jiki kana Abbu da Ummu suka dawo gida saboda Hajiyan Wagini ta ce ba inda za ta.


Ni kaina san da naji labarin ciwon yaya Faruk sai da jiki na yayi sanyi, nasan duk a dalili na ne yake wannan rashin lafiyar, ni kaina bazan so ta dalili na yaya Faruk ya dinga kasancewa a cikin wannan halin ba, hakan yasa nima na shiga cikin damuwa, ji nayi ina son in je in ga halin da yaya Faruk d’in yake ciki.


Washegari na ma Abbu magana akan in za su koma asibitin zan bi su, da farko Abbu cewa yayi ba zani ba, zuwan me zanyi tun da ni na ja mishi halin da yake ciki, ko so nake na je na k’ara sa mishi wani ciwon, miye amfanin zuwa na asibitin, har na cire ran zuwan asibitin tun da Abbu ya ce ba za ni ba, sai gashi da za su tafi Abbu ya sa Ummu ta kira ni.


San da muka je asibitin su Momi da Dadi ne da su Anisa da Hajiyan Wagini a cikin d’akin da aka kwantar da yaya Faruk.


Ni kaina yaya Faruk ya bani tausayi ganin yadda ya canza lokaci guda, da ga gani yana jin jiki.


Dadi na gaisar da Momi da Hajiyan Wagini na gaisar tare da tambayar su ya jikin yaya Faruk.


 Dadi ne ya amsa min da fara’a a fuskar shi.


Momi kuwa ba yabo ba fallasa ta amsa min kana ta d’auke fuskar ta.


Hajiyan Wagini kuwa watsa min harara tayi kana ta ce "Uban me kika zo yi, duk wannan halin da ya shiga ba saboda ke ba ne, amma da yake rashin kunya gaba ki ka ba ta ba baya ba har ki ka iya tako k’afar ki da sunan kin zo duba shi".


Sunkuyar da kaina na yi san da Hajiyan Wagini ta fara min fad’a, raina na min k’una na yadda a yanzu Hajiyan Wagini take kyara ta.


Dadi ne ya ce "Hajiya a mata hak’uri".


Ummu da Abbu kuwa ba su ce komai ba.


Ranar haka kowa ya fita harka ta a cikin asibitin, sai hirar su suke yi ba tare da sun sa ni a cikin hirar su ba, hakan yasa nima na kama baki na ba tare da na tsoma baki na a cikin hirar ba, Dadi ne kad’ai ne ya kula ni a asibitin.


Haka muka koma gida ina mai cike da jin haushin yadda aka min a asibiti.


Yaya Mus’ab kuwa tun bayan tawowar yaya Faruk Kaduna bai kawo komai ba game da tawowar shi Kadunan ba, ya alak’anta tafiyar tashi ne da shirye-shiryen bikin shi da ya gabato, suna yawan waya dashi jefi-jefi, a wayar da suke yi dashi ne ya fahimci yaya Faruk yana cikin damuwa, ganin bai fad’a mishi ba shi yasa bai tambaye shi ba, yasan wani lokacin yaya Faruk yana da zurfin ciki, ba kowace matsala ba ce yake fito wa ya fad’a ba, sai dai a cikin kwana biyu idan ya kira wayar shi ba ta zuwa, hakan yasa yayi tunanin akwai abin da yake faruwa saboda yaya Faruk bai cika kashe wayar shi ba, sai da babban dalili.


Yau cikin sa’a yana kira wayar ta shiga, Dadi ne ya d’auki wayar ya amsa kiran.


Bayan sun gaisa ne yaya Mus’ab ke tambayar yaya Faruk, Dadi ne ya fad’a mishi rashin lafiyar yaya Faruk da kuma kwanciyar shi a asibiti.


Yaya Mus’ab ya ma yaya Faruk fatan samun lafiya, ya sanar da Dadi in ya samu sauk’i a wajen aikin su zai zo ya duba shi, nan suka yi sallama da Dadi.


Tun bayan gama wayar su yaya Mus’ab ke jinjina rashin lafiyar yaya Faruk, yasan duk abin da ya kwantar da yaya Faruk a gadon asibiti ba k’aramin abu ba ne.


Khadija ma a ‘bangaren ta kwana biyun da ba su yi waya da yaya Faruk ba hakan yasa ta shiga damuwa, tun bayan tafiyar shi Kaduna ya kan kira ta su gaisa, ita ma tana k’ok’arin kiran shi su gaisa, sai dai a kwanan biyu da ba ta samun shi a waya yasa ta dinga tunanin rashin samun shi a waya da ba tayi, gashi tana son tambayar yaya Mus’ab ta ji dalilin da yasa ba ta samun shi a waya, sai wata zuciyar ta hana ta tambayar yaya Mus’ab d’in.



Yau Nana suna zaune ne rik’e da Asim ita da Anty Maryam suna hira yaya Mus’ab ya fito daga bedroom ya zo ya zauna.


Kallon shi Anty Maryam kana tace "Dadin Asim ya aka yi ne, na ga kamar akwai abin da yake damun ka".


Nisawa yayi kana ya ce "Na kira wayar Faruk ne kwana biyu ba ta shiga, shine yau Allah ya taimaka na samu ta shiga, sai Dadin Faruk d’in ya d’auka yake sanar dani rashin lafiyar Faruk d’in har da kwanciya a asibiti yayi, nasan duk abin da ya kwantar da Faruk a gadon asibiti ba k’aramin abu ba ne, shine ki ka ga hankali na duk ya tashi, yanzu zan ta k’ok’arin neman permission a gurin aiki sai mu je mu duba shi" ya k’arasa maganar cikin damuwa.


Anty Maryam cikin jimami ta ce "Allah sarki Faruk, gashi biki na ta gabato wa ga kuma rashin lafiya, Allah ya bashi lafiya, in ka nemi excuse a gurin aikin sai mu je can Kadunan mu duba shi".


Nana da take ta faman yi ma Asim wasa ta tsayar da wasan da take mai tun san da taji yaya Mus’ab na fad’an rashin lafiyar yaya Faruk, ji tayi komai ya d’auke mata, ji tayi tana buk’atar ganin halin da yaya Faruk yake ciki, don haka ta ce "Yaya Mus’ab ni ma zani in za ku" ta fad’a a hankali.


Kallon ta yayi kana ya ce "Ke Nana ban da abinki, kina zuwa School ina zaki, ki bari in mun je zan fad’a mishi kina gaida shi".


"Toh yaya Mus’ab" ta fad’a a tak’aice, amma yanayin ta ya nuna ba haka taso ba.


Hakan da Anty Maryam ta lura ne yasa ta ce ma yaya Mus’ab "Da ka k’yale ta mun je Kadunan da ita, tun da ta nuna tana son zuwa, kasan kuma Faruk mutumin ta ne".


Murmushi yayi ya ce "Shi kenan, in za mu tafi sai mu tafi tare".


Tashi yayi ya fita yayin da Anty Maryam suka ci gaba da tattaunawa akan rashin lafiyar yaya Faruk.


Yaya Faruk sai da yayi kwana uku a asibiti sannan aka sallame shi, tare da gindaya mishi sharud’a akan yadda zai kula da lafiyar shi.


Yaya Faruk yana k’ok’arin ganin ya kiyaye duk wani dokoki da likita ya gindaya mishi, hakan ne yasa bai cika son zama shi kad’ai ba saboda guje ma tunani, hakan yasa ya samu sauk’i akan damuwar da yake ciki.


Yaya Mus’ab san da yayi requesting d’in permission aka bashi, ya shirya da su Anty Maryam da Nana suka tawo Kaduna.


Nana kuwa wani irin dad’i ta ke ji za ta zo ta ga jikin yaya Faruk, tun san da taji labarin rashin lafiyar yaya Faruk ta rasa sukuni, sai yanzu da taga sun d’auki hanyar Kaduna, tasan yanzu hankalin ta zai kwanta.


Kasancewar gudun da yaya Mus’ab yayi yasa suka shigo Kaduna a cikin d’an k’ank’anin lokaci.


Yaya Faruk su na zaune a Main parlour suna hira da Anisa suka ji sallamar su yaya Mus’ab.


Anisa ce ta amsa sallamar ta tashi ta bud’e musu k’ofa.


Yaya Faruk ne yayi arba da su yaya Mus’ab, murmushi kawai yake yi ganin su yaya Mus’ab, bai yi mamakin ganin su ba, dan Dadi ya fad’a mishi cewa yaya Mus’ab ya kira wayar shi lokacin da aka kwantar dashi a asibiti, yasan yaya Mus’ab zai iya zuwa a ko wane lokaci.


Nana kuwa tun da tayi arba da yaya Faruk wani farin ciki ya kamata ganin ya samu sauk’i, hakan yasa ta dinga sakar mishi murmushi.


Anisa ma murmushi ta sakar musu tare da yi musu sannu da zuwa.


"K’anwa ta har dake aka zo Kaduna kenan, sannu da zuwa" Yaya Faruk ya fad’a cikin fara’a.


"Da ni aka zo yaya Faruk" Nana ta amsa mishi.


Yaya Mus’ab ne cikin wasa ya ce "Da yake ai ita kad’ai ka gani, dole ka maida mu hoto ni da Maryam".


Murmushi yaya Faruk yayi kana ya kalli Anty Maryam yace "Madam sannun ku da zuwa, kar mijin ki ya dame ni da k’orafin shi".


Dariya Anty Maryam tayi ta ce "Ai gaskiya ya fad’a, ya ga ka manta da mu ne, sai ‘yar k’anwar ka gani".


"To a min afuwa Madam, na amsa laifi na duk da nasan ba laifi nayi ba".


"An maka afuwa Faruk" Anty Maryam ta fad’a cikin wasa.


Gaba d’aya falon aka sa dariya.


Kar'ban  Asim yayi daga hannun Anty Maryam yana mishi wasa.


Anisa tashi tayi ta je ta sanar da Momi zuwan su yaya Mus’ab kana ta wuce kitchen ta samo musu drinks da snacks kafin ta d’aura musu abinci.


Gaisawa suka yi kana suka mishi ya jiki.


Amsa musu yayi da ya ji sauki.


Momi ce ta zo suka gaisa cikin walwala da sakin fuska.


Bayan sun gaisa ne da tambayar ta ya mai jiki ta amshi Asim ta tafi dashi d’akin ta.


Lokacin da Anisa ta gama girkin ne ta jera musu a dining table, zama suka yi suka ci ana d’an ta’ba hira.


Bayan sun gama cin abincin ne, Anisa ta kai su Nana d’akin ta dan su huta, shi kuwa yaya Faruk ya tafi da yaya Mus’ab side d’in shi.


Suna shiga d’akin yaya Mus’ab ya d’aure fuska kamar ba shi bane ya gama wasa da dariya a falo.


Ganin haka yasa yaya Faruk murmusawa ya ce "Ya aka yi ne Mus’ab".


In a serious talk yaya Mus’ab ya ce "To be serious Faruk, ban ji dad’in abin da ka min ba, tun bayan tafiyar ka na ke sa ran kiran ka saboda ganin yadda bikin ka ya matso amma ba ka kira kace min komai ba, ashe har ciwo kayi da yayi sanadiyar ka kwanciyar asibiti, da Dadi bai fad’a min ba bai zama lallai ka fad’a min ba, wai wani irin ciwo kayi ne har ka kwanta a asibiti, ga jikin ka nan ya nuna, dan har ‘yar rama kayi, Faruk na san duk ciwon da aka kwantar da kai ba k’aramin abu ba ne".


"Abin da yasa ka ga ban kira ka game da maganar biki, ba bu buk’atar kiran ka akan wannan maganar saboda an fasa bikin mu ne da Fatima, kwantar da ni da aka yi a asibiti kuwa BP na ne ya hau" yana gama fad’ar haka ya fara danna wayar shi kamar ba shi yayi magana ba.


Yadda yaya Faruk yayi maganar yasan ba wasa yake mai ba, yasan ma yaya Faruk zolaya ba halin shi ba ne.


Wannan maganar da yaya Faruk ya fad’a main a fasa bikin shi ba k’aramin girigiza shi yayi ba, yasan ba k’aramin abu ba ne zai sa a fasa bikin ganin irin son da yake min.


"An fasa bikin fa ka ce min Faruk, me yasa zaka hak’ura da Fatima bayan kasan halin da za ka shiga in dai ka rasa ta" yaya Khalil ya fad’a cikin damuwa.


Murmushin takaici yaya Faruk yayi ya ce "Ban damu da halin da zan shiga ba Mus’ab, hukuncin da na yanke shi yafi min sauk’i da ni da Fatima akan halin da za ta iya jefa ni nan gaba saboda ta ga ina son ta".


Tunani ne kala-kala ya addabi Mus’ab, wani irin laifi na mishi da zai sa ya fasa aure na bayan bikin ya kusa.


Kamar yaya Faruk yasan tunanin da yake yi kenan ya ce "Nasan za kayi tunanin mai yasa na yanke wannan hukuncin, Mus’ab zan iya hak’ura da kowace mace in har ta nuna akwai wanda take so ko da kuwa son ta zai illata ni, hakan yasa na yanke hukuncin hak’ura da Fatima saboda yadda ta nuna za ta iya aikata komai in dai akan wanda take so ne, kai kan ka shaida ne halin da na shiga a baya duk a kan Fatima, a dalilin ta har na kamu da hawan jini, ka ga kuwa in ban hak’ura da Fatima ba za ta iya jawowa na fad’a cikin wani mawuyacin hali".


Nan yaya Faruk ya warware mishi abun da ya faru har zuwa lokacin da ya hak’ura da ni da kuma halin da ya shiga.


Ci gaba yayi da cewa "Mus’ab nasan na so Fatima, sai dai a yanzu na hak’ura da son ta, ban ce maka har yanzu ba sauran son Fatima a raina, sai dai zan yi iyakar k’ok’ari na in ga na ajiye son ta a gefe, zan ci gaba da addu’a akan Allah ya cire min son ta nima in samu sauk’i a cikin zuciya ta, zan yi abin da hausawa ke cewa in so cuta ne, hak’uri magani ne".


Tausayin yaya Faruk ne ya dabaibaye yaya Mus’ab ta ko ina ya kama shi, ji yake yi da yana da halin da zai cire yaya Faruk daga halin da yake ciki da yayi, a maganganun da yaya Faruk yayi a yanzu ya fahimci cewar har yanzu yaya Faruk na so na, sai dai yana k’ok’arin danne son da yake min ne saboda ya samar wa kanshi mafita, shi kan shi yaya Mus’ab d’in ya ji haushin abin da na yi, ya kuma goyi bayan rabuwa dani da yaya Faruk yayi.


Wani tunani ne ya fara wanzuwa a zuciyar shi, sai dai bai so yayi saurin yarda da wannan tunanin da yake zuwa mishi.


Cikin tausayawa yaya Mus’ab ya ce "Faruk Allah ya za’ba maka abin da yafi alkhairi, Fatima tabbas ba ta kyauta ba, ina son ka d’auki hakan a matsayin jarrabawa, sannan ka sa a ranka wannan abin da ya faru cewa dama can Fatima ba rabon ka ba ce, ka ci gaba da addu’a da neman za’bin Allah a dukkan lamuran ka, insha Allahu komai zai zo maka da sauk’i, nima zan taya ka addu’a".


Murmushin jin dad’i yayi kana ya ce "Na gode Mus’ab da shawarwarin ka, na gode da kulawar ka gare ni".


"Ba komai Bregadier, zan iya yi maka komai dan taya ka samun farin cikin ka" yaya Mus’ab ya fad’a.


Hira suka ci gaba da yi, yayin da yaya Mus’ab yaci gaba da kwantar mishi da hankali.


Anisa kuwa suna can d’aki suna hira da Anty Maryam, jefi-jefi Nana nasa bakin ta a hirar, in ka gansu za kayi zaton sun dad’e da sanin juna.


Da yammaci yaya Faruk ne da Nana suke zaune a farfajiyar gidan suna hira.


Nana ce ta tsura ma yaya Faruk ido tana kallon shi, had’a ido suka yi tayi saurin sunkuyar da kai saboda kunyar da ta kama ta.


Murmushi yaya Faruk yayi kawai, wannan kunyar na daga cikin abin da yasa Nana ke k’ara burge shi.


"Yaya Faruk ba ka kai ni gurin Fatima na ganta ba" Khadija ta fad’a.


"Me yasa kike son ganin ta?" yaya Faruk ya tambaye ta.


"Ina son in ga amaryar ka ce wacce kake yawan ba ni labarin ta, shi yasa na ke son ganin ta".


"Zan kai ki gurin ta ki ganta a matsayin ta na k’anwata amma ba a matsayin matar da zan aura ba, dan na da kwanaki za ta zama mallakin wani, kin ga ai ba amarya ta ba ce".


D’ago wa tayi tana kallon shi saboda yadda maganar ta ba ta mamaki tare da girgiza ta, tasan a yadda yaya Faruk ke yawan ba ta labari akan irin son da yake min, yanzu kuma gashi yana fad’a mata ba shi zai aure ni ba, wani ne zai aure ni.


Jikin ta ne yayi sanyi da jin wannan maganar da yaya Faruk ya fad’a mata, a hankali ta ce "Yaya Faruk me yasa za ka fasa auran ta ka bar ma wani ya aure ta duk da irin son da kake mata".


Murmushin takaici yayi kana ya ce "Khadija Allah bai nufa daman mata ta ba ce, shi yasa a ka fasa auren dani, ki taya ni addu’a kin ji ‘yar k’anwa ta Allah ya za’ba min abin da yafi zama alkhairi a gare ni".


"Insha Allah yaya Faruk zan taya ka da addu’a, Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi gare ka".


"Amin Khadija, Na gode da addu’ar ki".


Murmushi kawai tayi, amma a k’asan ranta tausayin yaya Faruk ne fal cikin ranta, a yanzu ta fahimci dalilin rashin lafiyar shi yana da nasaba da fasa auren shi da aka yi da ni, duk da bai fad’a mata dalilin fasa auren ba, ta alak’anta hakan ba daga ‘bangaren yaya Faruk ba ne ko kuma babban dalilin shi da yasa shi yin haka har ya bar ma wani ya aure ni duk kuwa da son da yake min.


Haka suka ci gaba da hirar su cikin nishad’i.


Kwana d’aya su yaya Mus’ab suka yi a gidan su yaya Faruk sannan suka koma Abuja, kafin su tafi sai da suka yi exchanging d’in numbobin wayar su da Anisa, a kwana d’ayan da suka yi har sun fara saba wa kamar wanda suka dad’e da sanin juna da su Nana da Anty Maryam, shi yasa da za su tafi sai da taji kewar su, su kansu su Anty Maryam sun ji dad’in yadda Momi da Anisa suka tarbe su, da za su tafi haka Dadi da Momi suka cika su da tsaraba.


Haka suka tafi Abuja suna kewar junan su.




Yau yaya Khalil ne ya je gidan su Anisa dan ya k’ara duba jikin yaya Faruk.


Sai da ya fara shiga side d’in Momi suka gaisa tare da tambayar ta ya mai jiki sannan ya fito ya nufi side d’in yaya Faruk.


Lokacin da ya shiga d’akin yaya Faruk na kishingid’e a resting chair yana kallon news d’in da ake watso wa a Afican Independent Television.


Sallama ya mishi ya amsa mishi da fara’a a fuskar shi.


Bayan yaya Khalil ya gaishe shi ne ya tambaye shi ya jikin shi.


Amsa mishi yayi da ya ji sauk’i.


Sun d’an ta’ba hira kana yaya Faruk ya d’aura da cewa "Khalil kayi hak’uri da abin da Anisa ta maka, nasan ba ta kyauta ba, in ban da abinta ta ya za ayi ta kama yin fushi dakai akan abin da ba ruwan ka a ciki, kasan yarinya ce sai a hankali, har yanzu da sauran k’uruciya a jikin ta, in har ta maka wani abu ka zo ka fad’a min, zan d’auki mataki a kanta".


Murmushi yaya Khalil yayi kana ya ce "Ba komai yaya Faruk, ni ban yi fushi da Anisa ba, nasan duk abin da tayi tana da hujjar yin shi, nasan za ta sauka daga fushin da take yi da ni, Na gode yaya Faruk da kulawar ka gare ni".


Suna cikin maganar ne sai ga Anisa ta shigo d’akin had’e da sallama.


Amsa mata sallamar suka yi ta nemi guri ta zauna.


Tun da ta gaishe da yaya Khalil ba ta k’ara bi ta kan shi ba, sai ma yaya Faruk da taci gaba da yi ma magana.


Ganin irin kallon da yaya Faruk yake watso mata ne yasa tasha jinin jikin ta, tashi tayi ta bar d’akin.


Yaya Khalil ya d’an jima a gurin yaya Faruk sannan ya mishi sallama ya fito.


Main parlour ya dawo ya zauna inda ya tarar da Anisa da remote a hannun ta tana canza channel.


Ko da ya nemi guri ya zauna ba ta juyo ta kalle shi ba, sai ma ci gaba da canza channel d’in da ta ke yi.


Shiru ne ya ratsa falon kafin yaya Khalil ya kau da shirun da cewa "Anisa!"


Jin kiran sunan ta da yayi ne yasa ta juyo ta kalle shi ba tare da ta amsa ba.


Hakan ya ‘bata mishi rai, yana ganin wannan yana daga cikin salon raini ya kira ta kuma tana ji ta mishi shiru, dan haka cikin d’aurewar fuuska yace "Anisa nasan kin ji kiran sunan ki da nayi amma ki ka min shiru ko".


Ganin yadda fuskar shi ta canza zuwa ga ‘bacin rai yasa taji jikin ta yayi sanyi, tasan ita ma ba ta kyauta ba, tasan yaya Khalil yana da hak’uri, sai dai duk ran da aka kaishi bango bai iya ‘bacin rai ba.

"Kayi hak’uri yaya Khalil" Anisa ta fad’a cikin sanyin murya.


Ci gaba yayi da cewa "Anisa zan iya jurar komai a gurin ki amma ban da raini, na zuba miki ido ne in ga iya gudun ruwan ki, sai na ga ke ba ki san haka ba, Anisa ina yabon kyawawan halayen ki, hakan yasa na ke k’ara jin son ki a cikin raina, sai dai lokaci d’aya kina so ki fito da wasu halaye da ba naki ba ta hanyar hukunta ni da laifin da ban aikata ba, ba yadda za ayi laifin wani ya shafi wani, abin da yasa na ke miki uzuri nasan ki na yin haka ne dan nuna jin haushin ki akan abin da Fatima ta ma yaya Faruk, ban hana ki nuna jin haushin ki ba ko d’auka wani mataki akan abin da Fatima tayi, sai dai ina ganin in kin tashi d’auakar matakin bai kamata ki sa ni a ciki ba, Anisa ke kan ki shaida ce akan yadda kowa ya nuna ‘bacin ranshi akan abin da Fatima ta yi, har yanzu Fatima ba ta wani sakewa a gida saboda yadda kowa yake nuna mata ‘bacin rai akan abin da tayi, ina ganin tun da har yaya Faruk ya ce ya hak’ura da ita, ya kamata kema ki hak’ura da wannan fushin da ki ke yi, ko ba komai Fatima ‘yar uwar ki ce kuma aminiyar ki ce tun kuna yara, ba wai ina fad’a miki da ki yafe ma Fatima dan ta na matsayin k’anwa ta ba, na fad’a miki hakan ne dan in nuna miki rik’o bai da amfani kuma ba shi da kyau a musulunci, saboda hakan zan barki ki yi tunanin akan maganar da na fad’a miki, duk hukuncin da kika yanke min, za ki iya kira na ki fad’a min, ko kuma in nazo sai ki fad’a min shawarar da kika yanke" yana gama fad’ar haka ya fita daga d’akin.


Tun bayan fitar yaya Khalil daga d’akin ta rasa sukunin ta, tasan cewa yau ta kai yaya Khalil k’arshe, shi yasa ya nuna mata fushin shi, bai kamata ta dinga yanke mai hukunci akan abin da ba ruwan shi a kai, ko shi wanda take yi akan shi yace ya hak’ura, tasan in har ba taje ta ba yaya Khalil hak’uri ba, yaya Faruk zai iya yanke mata ko wani hukunci,ita kanta tana azabtuwa da irin hukuncin da ta ke ma yaya Khalil d’in, ya kamata ta je ta bashi hak’uri tun kan ya tafi, tasan in ya tashi yanke mata hukunci ita ce za ta sha wuya.

Da sauri ta fito daga d’akin ta same shi har ya shiga motar shi.


K’arasawa tayi gurin shi yayin da yake k’ok’arin kunna motar.


Ganin yana k’ok’arin barin gurin yasa ta kira sunan shi "Yaya Khalil".


"Ya aka yi ne?" ya fad’a cikin d’aurewar fuska.


"Am sorry yaya Khalil, plss forgive me" ta fad’a a hankali.


Kallon ta yayi ganin yadda ta marairaice fuska kamar mai shirin yin kuka, amma duk da haka sai ya nuna mata kuskuren ta, saboda gaba kar ta sake.


"Kin gama maganar ki dan so nake yin a wuce gida, kuma ni ba hak’uri nace ki zo ki bani ba, cewa nayi ki shawarta da zuciyar ki, duk shawarar da ta baki sai ki fad’a min".


Wannan karan kasa daurewa tayi, ba za ta juri fushin yaya Khalil ba, tasan ta ‘bata mishi, shi yasa yayi fushi da ita.


Hawaye ne ya fara zubowa a idanun ta, tasan yaya Khalil ba zai juri ganin hawayen ta yana zuba ba, zai yafe mata laifin da ta mishi.


"Yaya Khalil dan kayi hak’uri da abin da ya faru, nasan ban kyauta maka ba, amma insha Allah ba zan sake kamanta irin wannan laifin ba, kai kan ka shaida ne a irin son da nake maka, ba zan juri ganin fushin ka gare ni ba, plss yaya Khalil ka tausaya ma ‘yar kanwar ka".


Ba zai juri ganin hawayen Anisa ba, yasan ta mishi laifi, tun da har ta gane kuskuren ta kuma ta bashi hak’uri ya kamata ya hak’ura, shi kanshi ba zai so su ci gaba da fushi da juna ba.


K’asaitaccen murmushi ya sakar mata kana ya ce " Is ok my lovely sister & wife to be, komai ya riga ya wuce, amma pls ki kiyaye gaba, ba zan so mu dinga samun sa’bani da ‘yar k’anwata ba akan k’aramin abu, so wipe your tears & smile for me".


Goge hawayen ta tayi, a lokaci d’aya tana sakar mishi da wani lallausan murmushi.


Hira suka fara yi kamar ba su ba ne suka samu sa’bani, gashi har sun shirya kamar ba su.


Sai da suka sha hirar su kana ya mata sallama ya tafi.



Shirye- shiryen bikin mu ya ci gaba da gudana, yau bikin mu ya rage saura kwana biyu, ranar ne ya kasance henna design, ban wani shirya event ba kasancewar yadda bikin yazo min, bridal shower da walima kad’ai na shirya, Dr yaso ayi event masu yawa, nuna mishi na yi akan ba na son event d’in da yawa, saboda haka ne ya shirya Dinner kawai zai yi ta ‘bangaren shi.


Abbu da Ummu duk sun min abin da ya dace akan bikin, Ummu ta bani magungunan da ake baiwa amare, sannan ta kawo mai gyaran jiki ta musamman dan ta min gyara na musamman.


Yanzu ba laifi su Abbu ma suna zama mu d’an yi hira, hakan ya rage min damuwar da na ke ciki.


Yaya Khalil ma yana tambaya na ko akwai abin da na ke buk’ata.


Yaya Aminu ma yana kawo Anty Jiddah ta wuni, ita ma haka ta kawo min tsarabar magunguna na sha, har da turarurruka na tsugunnawa ta kawo min, sannan tana zaunar dani ta fad’a min dabarun zamantakewar aure, ina jin dad’in yadda Anty Jiddah take ba ni kulawar ta, hakan yasa na ke k’ara ganin girman ta da mutuncin ta.


Momi da ita ake gudanar da shirye-shiryen bikin, yanzu ta rage fushin da take yi dani, in na gaishe ta cikin fara’a take amsa min.


Anisa ma ta na zuwa a gudanar da shirye-shiryen bikin, sai dai ba ta sakin jikin ta wajen gudanar da shirye-shiryen.


Hajiyan Wagini ce har yanzu ba ta huce ba, hakan yasa nima naji dad’in zaman ta a gidan su Anisa, sai dai idan tazo ne nake kauce ma had’uwar mu, dan in dai muka had’u sai tasan yadda tayi ta fad’a min maganar da ta ‘bata min rai.


Aisha ma tun san da taji abin da ya faru na fasa aure na da yaya Faruk, ta nuna rashin jin dad’in ta.


Gidan mu ya fara cika da ‘yan uwa da abokan arziki.



Yau ne ya kasance za mu yi Bridal shower, shigar cot less nayi fari na doguwar riga, yayin da aka rubuta min *BRIDE TO BE* da farin rubutu wanda aka yi min crossing d’in shi akan rigar, nad’in da aka min na head kalar light silver aka min, takalmi ma kalar light silver na saka.


Kwalliyar da nayi ba k’aramin amsa ta tayi ba.


K’awaye na kuma shigar tommy skirt da polo suka yi.


A farfajiyar gidan mu muka yi event d’in.


Music kala-kala aka dinga playing a Bridal shower d’in.


K’awaye na sun cashe a wannan ranar.


Gaskiya Bridal shower d’in ya k’ayatar.


A ranar ne dangin Dr Sadik suka zo suka sa ni a lalle tare da ba da kud’i mai yawa na sa lalle.



Washegari ran juma’a ya kasance ranar d’aurin aure na, a ranar ne kuma zan yi walima.


Da misalin k’arfe biyu na rana aka d’aura aure na ni Fatima Ibrahim Wagini da Dr Abubuakar Sadik Muhammad a k’ofar gidan mu.


D’aurin auren da ya samu halartar manyan mutane daban- daban.


Ina jin sanarwar an d’aura aure na samu kaina da wani irin fad’uwar gaba, yayin da hawaye suka zubo min a lokacin.


Ni kaina ban san hawayen me nake yi ba, amma na alak’anta hakan da hawayen farin ciki ne nake yi ganin na auri wanda nake so da kuma k’alubalen da na fuskanta Kafin auren, nasan komai yazo k’arshe tun da Allah ya nufa na kasance matar Dr Sadik.


Tsintar kaina nayi cikin farin ciki, damuwar da nake tare da ita na tsawon lokuta duk na ji ba bu ita a lokacin.


Yau Allah ya cika min burin a da ya nufa na samu Dr a matsayin miji.


Haka na ci gaba da gudanar da taron biki na cikin walwala, kowa ya ganni a lokacin yasan ina cikin farin ciki.


Walima ma a farfajiyar gidan mu nayi, Malama Khadija Muhammad ce ta gabatar da muhadara mai taken _Zamantakewar aure a Musulunci_

Malamar tayi bayani akan yadda zaman aure ya kamata ya gudana a tsakanin miji da mata ta fuskar musulunci, malamar ta jawo hankalin mata yadda za su gudanar da rayuwar su a gidan aure.


Haka dai Walimar ta k’ayatar kana aka tashi daga Walimar.


Dr Sadik yazo da abokan shi mun d’auki hotuna, haka muka sha hotuna da su Anisa da Aisha da Halima da k’awaye na, yaya Khalil ma yazo mun yi hotuna dashi, wani mun d’auka ni dashi, wasu hotunan kuma mun d’auka har da Anisa a ciki.


Yaya Faruk ya ba da gift da kyautar kud’i ya ba ma Momi ta kawo min, a ranar na samu labarin tun bayan d’aura auran mu ya tafi Abuja, na so mu had’u dashi in mishi godiya ko da ba zai amsa min  ba.


Hak’ik’a nasan yaya Faruk daban ne da har ya iya min kyauta ba tare da ya duba abin da ya faru a tsakanin mu ba.


Hankali na bai tashi ba sai da naji an ce ga motoci can a waje na d’aukar amaryar sun zo, nan nemi farin cikin da nake ciki na rasa.


Kuka na dinga yi san da aka kai ni gurin Abbu in mishi sallama, shi kanshi Abbu a lokacin na bashi tausayi, nasiha ya min akan zamantakewar aure tare da min fatan samun zaman lafiya a d’aki na.


Nasan Abbu ya nuna min gata da so, in ban da matsalar aurena da yazo da matsala har Abbu yayi fushi dani, in ban da wannan matsalar Abbu bai cika nuna fushin shi gare ni ba.


D’akin Ummu aka kai ni, muna shiga na fad’a jikin ta na ci gaba da kukan da na ke yi, ita kanta Ummu duk fushin da take yi dani, sai ta neme shi ta rasa, ganin irin kukan da nake yi ne yasa ita ma hawaye ya fara zuba a idon ta.


"Fatima yau Allah ya nuna min ranar auren ki, ba abin da zan ce sai dai in ma Allah godiya da ya nuna min wannan ranar, Fatima aure ba abin wasa ba ne, kar ki dan kin auri wanda kike so ki yi zaton ko ba za ku samu sa’bani ba, aure zaman hak’uri ne, kowa da kike gani shi yake yi a d’akin shi, a yanzu ne da zama ya had’a ku za ki k’ara sanin halin shi yasan naki, dole ne ki kiyaye duk abin da ba yaso, yi nayi bari na bari, ki yi hak’uri da ‘yan uwanshi da iyayen shi, ki kyautata musu kamar yadda za ki kyauta mana, ki koyi hak’uri, juriya, kawaici, shi zai kai ki matakin samun zaman lafiya a d’akin ki, ki kula da tsafta, kissa, kwalliya, girki, wannan abubuwan da na lissafo miki da na ce ki kula suna da fad’i, shi yasa na baki su a dunk’ule, su ne za su k’ara miki daraja a gurin mijin ki, Auta ki yi hak’uri da duk halin da za ki tsinci kan ki a d’akin mijin ki, kin ga dai ke ki ka za’be shi a matsayin miji, saboda haka ki yi hak’uri kin ji Auta, Allah ya baku zaman lafiya".


"Ummu ki yafe min duk laifin da na miki" Na fad’a cikin shashshek’ar kuka.


"Na yafe miki Auta, tashi ki tafi kin ga ana jiran ki".


K’ara shigewa jikin ta nayi na ci gaba da kuka na yayin da Ummu taci gaba da lallashi na.


Da k’yar aka samu aka cire ni daga jikin Ummu ina kuka aka fita dani daga d’akin.


San da muka fito farfajiyar gidan ne na hango yaya Khalil zaune a saman motar shi.


Gurin yaya Khalil na wuce na kwanta a jikin shi ina ci gaba da kuka, shi kanshi daga gani dauriya kawai yake yin a tafiyar da zanyi.


D’ago ni yayi yana girgiza min kai alamar in daina kukan, a lokaci d’aya kuma yana goge min hawaye.

"Ki daina kuka kin ji Auta, ki zauna lafiya da Dr, in an kwana biyu zan zo in duba ki ko ba kya so" ya fad’a a hankali.


Cikin kuka na ce "Ina so yaya Khalil".


"Yawwa Fatima, yanzu ki tafi kin ga ana jiran ki, zan kira ki a waya".


Maimakon in tafi sai ma sake fashewa nayi da wani kukan, hakan yasa ya rik’e min hannu, gurin Anty Zainab (k’anwar Ummu) ya kai ni ta rik’e min hannu.


Juyawa yayi ya wuce side d’in shi, dan a yadda yake ji ba zai juri ganin tafiya ta ba.


Allah Sarki yaya Khalil, duk a cikin gidan mu na fi shak’uwa dashi, abokin shawara na, mu yi fad’a mu yi wasa haka muke dashi, yau gashi a dalilin aure zan yi nesa dashi, sai kuma na zo gida ko shi ya kawo min ziyara.


Kinkinau aka kai ni, nan Dr Sadik ya gina gidan shi.


Gida ne mai matuk’ar burgewa ga duk wanda ya kalla, filawowin da aka zuba ne a gidan ya k’ara k’awata gidan.


San da muka fito daga motan ne Anty Zainab ta fad’a min in zan shiga in shiga da k’afar dama.


Lokacin da na zo shiga ban manta da abin da Anty Zainab ta fad’a min ba, haka ne yasa na k’ara da addu’a a raina na neman zaman lafiya a tsakani na da Dr Sadik.


Falo biyu ne a had’e wanda za a iya shiga ta gaban gidan da kuma ta ta cikin gida, falo na biyu aka kai ni inda aka jera min kaya na..

Falon da aka kai ni ba k’aramun tsaruwa yayi ba, nan na k’ara ganin kayan alatun da Abbu ya zuba min.

Bedroom aka wuce dani, nan ma ba k’aramin tsaruwa yayi ba.


Ba abin da zan ce ma Abbu da Ummu sai godiya.


Momi da Anty Zainab ce suka ci gaba da min nasiha akan zaman aure wanda yasa jiki na yayi sanyi.


Sadik ne ya kira ni akan in shirya yanzu za a wuce Dinner, ga motoci nan ya kawo.


Anty Zainab ce ta shirya ni cikin wani white gown d’in nan ce mai jan kasa, tana da adon silver a jikin flower d’in, a jikin rigar akwai duwatsu masu shining, head d’in da Anty Zainab ta d’aura min kalar golden, jakar da na rik’e irin wacce amarya ke rik’e wa ita ma kalar golden, haka ma takalmin da na saka, bayan na shirya ne ta sa min gyalen wanda yake zuwa had’e da kayan shima yana jan k’asa.


Dr Kamal ne ya d’auke ni da Dr Sadik ya kai mu inda za a yi Dinner d’in.


Hall d’in ya cika da ‘yan uwa na da da ‘yan uwan Dr Sadik.


Bayan mun zauna a grin da aka ware mana na zaman Ango da Amarya kana aka fara gabatar da program of event.


Mc ya umarci da mu fito fili mu taka rawa, abokan Dr Sadik da k’annen shi haka suka dinga mana lik'in kud'i, a ‘bangare na ma su Anisa da su Halima haka su ma suka dinga min lik'in kud'i.


An ci an sha a gurin Dinner d’in, da haka taron ya tashi.


Dr Kamal ne ya tsaya a gurin sai da kaji ya siya sannan ya tsaya ya siya Drinks kana ya wuce damu gida.


Ina zuwa gida na wuce toilet na watsa ruwa saboda gajiyar da nayi kana na d’auro alwala.


Wata had’ad’d’iyar night gown na sa na shafa humra kana na d’aura hijab na yi shafa’i da wuturi kasancewar sai da nayi sallar isha’i kafin mu tafi Dinner d’in.


Bayan na idar ne na kwanta akan gado saboda wani irin barci da nake ji.


Barci har ya fara d’auka na naji shigowar Dr Sadik d’akin.


"Zarah ba dai har kin kwanta ba, ko abincin baki ci ba?" Dr ya fad’a a hankali.


Cikin muryar barci na ce "Na gaji ne Dr, ga wani irin barci da nake ji shi yasa na kwanta".


Wani irin kallo ya watsa min mai kashe sassan jiki ya ce " Ki sakko ki ci wani abun, kin san yunwar dare tana illah, in ban da abin ki ma Zarah ai yau ba ki da barci".


Fahimtar in da maganar shi ta nufa yasa ta ce cikin shagwa’ba "Haba Dr, Allah kuwa bacci nake ji".


Hannun shi ya mik’o min ya ce "Common, tashi ki ci wani abun, in ba haka ba sai in miki allura".


Hannuna na mik’a mishi ya rik’e muka wuce side d’in shi.


‘Bangaren Dr ma ya had’u, yanda aka shirya side d’in kamar na wata amaryar duk da ba a zuba tarkace da yawa a falon ba, hakan bai hana falon tsaruwa ba, cikin bedroom d’in ma ya k’ayatar.


Plate yasa na d’akko da cup, naman kazan yasa na zuba a plate.


Saboda baccin da nake ji yasa ban wani ci naman sosai ba ga kuma rashin sabo, hakan yasa Dr ya dinga bani da kanshi, shagwa’be min yayi akan nima sai na bashi, haka na d’auka ina bashi yana ci, bayan mun gama ci ne ya tsiyaya min drinks d’in cup yana ba ni, ragowar naman na d’auka na kai frij na saka a ciki.


Bayan mun gama cin naman ne yaje ya d’auro alwala, yana fitowa yasa ni naje na d’auro alwala.


Sallah muka yi raka’a biyu kana ya kama kaina ya dinga jero addu’o’i akan Allah ya bamu zaman lafiya.


Tashi nayi da niyar in koma side d’ina saboda baccin da nake ji kamar zan fad’i.


Dr ne ya kalle ni ya ce Ina zaki ne Zarah".


Amsa mishi nayi da cewa "Side d’ina zan koma in kwanta".


Murmushi yayi ya ce "Ai baki da gurin kwanciya da ya wuci nan d’akin a kuma jikin mijin ki".


Sunkuyar da kaina nayi ganin yadda Dr yake son sa ni jin kunya.

"Zo mu je ki kwanta kin ji Zarah ta" ya fad’i hakan yana rik’e min hannu.


Bin shi nayi na hau can k’arshen gado na kwanta.


Murmushi kawai yayi ganin in da na kwanta a k’arshen gadon, gadon ya kwanta.


Duk da baccin da nake ji kasa baccin nayi saboda Dr da ya hau gadon.


"Zarah" Dr ya kira suna na.


Shiru nayi kamar mai bacci, dan yau a tsorace nake da Dr.


"Zarah nasan idon ki biyu ba ki yi baccin ba, pls come close to me" Dr ya fad’a a hankali.


Saboda tsoron da nake ji yasa na kasa matsa wa kusa dashi, hakan yasa ya matso kusa dani ya kwantar dani a jikin shi.


Lumshe ido nayi saboda yadda jiki na da na Dr suka had’u, ga kuma rashin sabo.


A hankali ya fara magana da cewa "Alhamdulillah, All praise be to Allah, yau Zarah ke ce a matsayin mata ta, ban san yadda zan fasalta farin cikin da nake ciki ba, nasan ba wayau na ko dubarata ba ce yasa na mallake ki a matsayin mata ta, sai dai in ma Allah godiya akan ni’imar da ya min da ya bani ke a matsayin mata ta, ke fa Zarah wani farin ciki kike ciki akan wannan ranar".


A hankali na bud’e ido na da na lumshe na ce "Dr farin cikin da nake ciki baki na ba zai iya furta wa ba, Dr ina maka so wanda ni kaina ban san lokacin da ya min wannan kamun ba, sai dai in gode ma Allah da ya cika min burina na same ka amatsayin miji, alfarmar da zan nema a gurin ka shine Dr ka so ni kamar yadda nake son ka, ka rik’e ni amana, yanzu kaine gata na".


Murmushi yayi ya fara cire min hijabin da ke jiki na, yayin da ya fara shafa min kaina da yasha retouching.


"Kar ki damu Zarah, am yours, u a mine".


Haka muka ci gaba da musayar kalamai masu kwantar da hankali.


A hankali Dr ya canza hirar da salon soyayyar shi, sak’onni yake aika ma ko wani sassa na jiki na.


Dr ya nuna min tsantar so mai wuyar fasaltuwa had’e da kulawa a wannan daren.


Ranar na k’ara tabbatar da babu abin da yafi dad’i fiye da kasancewa da wan da kake so.


Haka muka raya wannan daren irin yadda masoya ke kasancewa a daren su na farko.


Haka muka tsarkake jikin mu muka koma muka kwanta.


Da asuba Dr ne ya tashi ya d’auro alwala ya tafi masallaci yayi sallah.


Sai da ya dawo daga masallacin sannan ya zo yana hura min iska a kunne.


A hankali na fara bud’e ido na, dan har yanzu bacci ne a cikin ido na.


Muna had’a ido nayi sauri na rufe ido na saboda wata irin kunyar shi da nake ji a yanzu.


Murmushi yayi ya ce "Kunya ta kike ji, Sorry princess Zarah na tashe ki, sallah za ki tashi ki yi, in kika yi sallar sai ki zo mu kwanta, nasan jiya ban barki kin kwanta da wuri ba".


A hankali na tashi saboda yadda na ji kasala da ciwon jiki ya kama ni, ga zazza’bi da yake so ya rufe ni.


Tashi nayi na shiga toilet na d’auro alwala na fito na ta da sallah.


Bayan na idar ne na yi addu’o’i na dawo na kwanta.


Dr ne ya janyo ni jikin shi, zafin da yaji jiki na yayi ne yasa ya ce "Oh God, Zarah ni na yi causing d’in wannan fever ko, sorry me yasa ba ki fad’a min ba".


Lamo nayi a jikin shi ban ce mai komai ba.


Kwantar da ni yayi ya je ya had’o ruwan allura, da k’yar na tsaya ya min saboda yadda ba na son allura.


Koma wa bacci muka yi ni da Dr, ba mu tashi ba sai wajen k’arfe takwas na dare.


Side d’ina na koma na yi wanka na saka atamfa super Holland d’inkin riga da skirt, simple make-up nayi.


Momin su Dr ce ta aiko mana da breakfast, Farida ce ta kawo breakfast d’in, mun gaisa cikin mutunci, ba yadda banyi da ita ta zauna mu yi breakfast ta ce min sauri take yi tana da lectures d’in safe, alamun ta na nuna ba ta da hayaniya.


Ragowar naman kazan da muka rage na je na yi warming d’in shi a Oven, dashi muka had’a muka yi breakfast.


Bayan mun gama breakfast ne ya bani magani na pain relief na sha.


Dr ne ya sanar dani zai je gidan su Momi ya gaishe ta.


Bayan tafiyar shi ne na tashi na wanke kayan da muka yi breakfast kana na je na gyara side d’in Dr.


Ranar haka na dinga bak’i daga ‘yan uwana da ‘yan uwan Dr, Anisa ma da Halima da Aisha sun zo, da yamma Aisha da Halima suka min sallama suka tafi.


Su Momi da Anty Zainab sun k’ara gyara gidan.


An kai ni gidan su Dr an gabatar dani a matsayin matar Dr, an nuna ni gurin ‘yan uwan Dr.


Gidan su Dr ba k’aramin had’uwa yayi ba, kai da gani kasan kud’i ya zauna a gidan.


San da za mu tafi ne Momi ta ba da kud’i masu yawa a ba ni.


Muna dawowa na shiga wanka na canza shiga ta cikin wani tsadadden less.


Gidan ya rage daga ni sai Anisa, itama rok’on ta nayi akan ta bari Dr ya dawo sai ta tafi.


Dr na dawowa Anisa ta kira Driver yazo ya d’auke ta.


Da za ta tafi ne naje na d’akko mata turare da wani material da kayan make-up a cikin akwati na, sai da na nuna ‘bacin raina sannan ta amsa.


Raka ta nayi bakin k’ofa inda na ce mata "Anisa pls ki dinga zuwa kin ji, ki gaishe min da yaya Khalil".


Ganin yadda na marairaice ne yasa ta ce min "In ina free zan dinga lek’o wa, zan Isar da sak'on ki ga Yaya Kalil".


Da haka muka yi sallama da ita na koma ciki.


Yau ma haka muka kasance cikin nuna ma junan mu zallar so da k’auna.


Sai da muka d’auki sati d’aya ba inda Dr yake zuwa kasancewar an bashi hutu a gurin d’aki, ko ya fita ba ya dad’e wa yake dawowa.


Hanan da Farida sun zo sun wuni, ganin Hanan ba ta wani sake jikin ta mun yi hira ba yasa muka dinga hira da Farida.


Yau da daddare da za mu kwanta ne Dr ya d’akko ruwa a cup da wani pills ya mik’o min.


Bin shi nayi da kallo nayi ina jiran k’arin bayani.


Cikin shagwa’ba na ce "Dr ai yanzu ba in da yake min ciwo".


Kallon da yake sa ni a cikin wani shauk’i ya min kana ya ce "Wannan ba pain relief ba ne, na family planning ne".


Da sauri na kalle shi dan gasgata maganar shi, ya za ayi sati na d’aya a d’aki na ya ce in fara shan pills na family planning.


"Ban gane ba Dr, ni me zan yi da pills d’in family planning da za ka bani na sha" Na tambaye shi.


"Ina so ki fara shan pills d’in ne saboda ina so ki huta kafin ki d’auki ciki, ba na so ki sha wahala wajen laulayin nan, kin ga kuma ina so ki koma School ki had’a HND d’in ki, kin ga yanzu ki na samun ciki za ki haihu, hakan zai sa ki raba hankalin ki gida biyu wajen rainon baby da karatun ki, ki bari in kika yi nisa a karatun ki sai ki daina shan pills d’in".


Kallon Dr kawai nake yi san da yake min wannan bayanin, ni a gani na ban ga dalilin da zan sha wani pills ba, hasalima ni tsoro nake ji yadda ake samun matsala wajen yin family planning.


"Dr ina ganin ba sai mun yi family planning ba, ka ga wani lokacin yana zuwa da matsala, kuma ni ina ganin baby ba zai hana ni karatu ba, ina ganin a bar zancen family planning d’in nan, Sai ka ga ma Allah bai kawo cikin da wuri ba ko da ba ayi family planning d’in ba".


Dr haka ya ci gaba da fahimtar dani akan in yi hak’uri in sha pills d’in amma na k’i, hakan yasa ranshi ya ‘baci ya ce in tashi in koma side d’ina.


Post a Comment

0 Comments