Maimooon. Best hausa novels

 Episode Twenty Six: A Step Further Away


Basu dawo ba sai daf da Magrib. Suka dawo da kaya niki niki. Hafsat ta zauna tana bani labari kamar zata ari baki "gaskiya Moon kin yi missing, kowa yazo kuma kowa sai ya tambaye ki" nayi murmushi kawai, a raina ina cewa Hafsat ba za ki gane ba. A lokacin ne mommy take cemin an bawa Amira scholarship award dina, na tambayi Hafsat nace "ya Amira tayi kuwa da aka bata?" Hafsat ta tabe baki tace "kema kinsan ya tayi ai, she first said it is a mistake, sai da pc ta kira su ita da maman ta tayi musu bayani cewa it is a gift from you, baki ga maman ba har da hawaye tana yi wa mommy godiya. Ni fa banji dadi ba Moon, you are too soft wallahi, wai duk abinda yarinyar nan tayi miki amma shine zaki wani bar mata scholarship award dinki" mommy ta dan bata rai tace "me Amiran tayi wa Moon?" Hafsat tayi sauri tace "it is nothing mommy, wani small girl issue ne kuma munyi solving tun a school" daga gani kasan mommy ba ta yarda da bayanin Hafsat ba, kawai dai tayi shiru ne. Nan suka dauko min gifts dina suka nuna min. Duk a ciki guda biyu sunfi birgeni, na farko medal din da school ta bani, na glass ne me kauri, a ciki anyi rubutu da golden colour kamar haka:

     Award of Excellency 

           To

Maimoon Muhammad Dikko


For being the most talented student this school has ever had. 


Na biyu kuma students ne suka bani, shi kuma da wood suka hada shi, a tsakiya sun yi zanen moon, a kasa kuma suka rubuta:

Thank you Moon for brightening our lives. We will forever miss u. 

Kawai sai naji hawaye a ido na. Hafsat ta dauko wayarta ta nuna min video da 'yan set din mu suka yi suka ce a nuna min. Duk sunyi kwalliya kuma they are all laughing and talking at the same time. "Moon ashe baki da lafiya? We miss you today, kinga gifts dinki?...... " ina dariya kuma ina hawaye at the same time, can wata a videon tace "Moon shine kika rike mana uncle kika hana shi zuwa ko? Hafsat tace yana can yana jinyar ki, ki gaishe ki kice we miss him also" na kalli Hafsat ita kuma ta daga kafada. Wato karya tayi musu tace muna tare da Ibrahim shi yasa basu ganshi ba. Class monitor din mu Hamidda ta hada min take away na duk abinda aka ci a gurin party da handwritten note na get well soon. 


A ranar da daddare sai ga Amira da mamanta sunzo yimin godiya har gida, mommy ta kaisu gurin daddy shi ma suka yi masa godiya. Daga nan muka tafi dakinmu muna hira, anan muka ba ta labarin tafiyar mu England, yanda tayi da fuskarta kamar zatayi kuka. Nace mata "Amira ni ina ganin ki cike Oxford kawai sai mu tafi tare, kinga sai ki zauna a gidan mu muke zuwa makaranta tare" ta girgiza kanta idonta fal kwalla tace "I can't. Mama bata da kowa a garin nan sai ni. Bazan iya barin Nigeria in barta ita kadai ba. University of Abuja zan saka saboda in zauna a gida. I wish you guys best of luck in England, in kun je please ku kira ni saboda in samu number dinku ta can" nace mata "insha Allah, you will be among the first ones da zan kira" Haka muka yi ta hira har sai da suka zo tafiya. Casually ta tambayeni "ya labarin uncle din mu kuwa? Naga shima baije partyn mu ba" na kalleta sai ta sunkuyar da kai. Hafsat ce ta gaya mata yayi directly "yayi resigning daga aikin sa ya koma Ibadan" ina kallon fuskarta ta chanza kala lokaci daya "but you are in contact right?" Hafsat tayi sauri tace "What is it to you, in suna fa contact?" Na dakatar da Hafsat da naga ta fara daukan zafi, nan na bawa Amira labarin duk abinda ya faru, na kara da cewa "I believe He will come back like he promised" Hafsat ta ja tsaki tace "wahala da rai" tun daga nan Amira bata kara cewa komai ba har suka tafi"


Washegari muka tafi "yalleman, satin mu guda acan kamar yadda daddy yace. Amina cousin din mu da muke kusan sa'anni sati daya na bata, ta dage lallai sai ta bimu England da kyar daddy ya lallabata yace ta bari in ta gama sec sch za'a mayar da ita can. Mun shaku da Amina sosai dan bayan Hafsat, ita ce kamar second sister dina, bayan kasancewar mu sa'anni, muna kama da ita, dan idan naje 'yalleman cemin ake yi Hassanar Amina. 


Muna dawowa Abuja muka fara shirin tafiya England. Muka yi sallama ta duk makota, muka hada hada personal kayayyakin mu, duk da dai daddy yace kar mu dauki kayan sawa tunda zamu ke zuwa Nigeria, in mun je can ma sayi wadansu. Duk da cewa na zama busy a kwanakin nan amma komai nakeyi sai inji irin feeling dinnan da mutun yake ji idan ya manta baiyi wani abu mai muhimmanci ba. Ibrahim is always there tugging at my mind. Ranar da zamu tafi muka su Faruk da daada suka raka mu airport, faruk har da kukansa muna ta tsokanarsa. Muka shiga jirgi, mommy tana kusa da daddy, ya Walid da Hafsat, ni da Ya Habeeb. Jirgin mu yana tashi na kalli window, ina kallon Nigeria a hankali gajimare yana rufe ta tana bacewa. "Goodbye Ibrahim". Na fada a hankali knowing now I am a step further away from him. Na saka earpiece, na lumshe ido na na jingina kaina a jikin headrest din seat dina yayin da jirgin mu ya cigaba da lulukawa sararin samaniya. This journey is like a transition in my life



Episode Twenty Eight : University of Oxford


Karfe dayan dare jirgin mu ya sauka a birnin London. Tuni motoci masu dauke da tutar Nigeria masu fenti kalar kayan sojojin Nigeria suna jiran mu. Muna sauka suka dauke mu sai embassy. A cikin embassy din anan gidan da zamu zauna yake. Gate daya ne zaka shiga, sai ka wuce offices din su daddy sannan sai gidan, sai kuma gidajen sauran manyan staff na embassy din. Gidan katon gaske ne, dan kusan girman su daya da gidan mu na Abuja with exception of part din su inna da na daada. Amma wannan gidan yafi wancan haduwa, it makes me wonder dama Nigeria muna da irin wannan arzikin? Ko dan kawai muyi show up ne a duniya a dauka babu talauci a Nigeria? Wato rayuwa a Nigeria kamar kashin dankali ce, manya su suke danne kanana. Komai a gidan computerized ne, ko wacce kofa sai tayi detecting finger print sannan zata bude, dan haka dole a daren akayi uploading finger prints din mu. Part din mu ni da Hafsat kowa da dakinsa, falo daya, kitchen daya amma mommy tace sam sai dai mu rufe daki daya mu zauna tare, kitchen din ma tace a rufe, mu ringa zuwa main dining room muna cin abinci tare dasu. Mommy da daddy part din su daya, ya Walid da ya Habeeb ma haka. Sai kuma main palo wanda yayi connecting duk parts din. 


Washegari da yamma muka fita shopping muka siyo kayan amfanin mu kaf, tun daga kan sutura, toiletries, cosmetics da sauran tarkace. Daddy tun yana biyan cash har ya dawo using credit card, daga baya yace "kai yaran nan so kuke kuga gudun ruwa na ko? To ya isa haka" mommy tana yi masa dariya tace "kai fa kace kar su taho da komai zaka saya musu anan, duk wanda ya sayi rariya kuwa ai yasan zata zubar da ruwa" ni da Hafsat dogayen riguna mommy ta sa muka dauka saboda zuwa makaranta, tace bata son shigar english wear, kar muga muna England muce muma mun zama turawa, mun dauki english wears din dai amma saboda sakawa a gida. Mun sayo sababbin sim cards muka saka a wayoyin mu muka cire na Nigeria muka ajiye. Nan muka fara kiran 'yan'uwa da abokan arziki muna basu numbers din mu. Kamar yadda nayi alkawari, Amira tana daga cikin na farkon dana kira. 


A week after zuwan mu England aka fara maganar school din mu, ni dama daddy yasan me nake so, neurology, Hafsat aka tambayeta tace itama medicine din take so bangaren gynecology. Har daddy yace mu tafi sai nace "daddy, ina so kuma in dau some courses on psychology" yayi shiru kafin yace "anya Moon abin ba zai yi miki yawa ba? Medicine is not easy on it's own sannan kice zaki kara da wani abun kuma?" Nayi shiru bance komai ba, yace "OK, I will see what I can do, normally ba'a barin students su dau courses out of their field, amma tunda psychology is some how related to medicine zan nema miki" nayi godiya muka tashi muka tafi. Muna zuwa falon mu Hafsat ta fara tambayata "ke kuwa me yasa kike son yin psychology?" Nace "I want to know exactly what people are thinking, I want to be able to tell if someone is lying or not" tayi shiru sannan tace "is this about Ibrahim?" Nace "partly, yes"


Tunda muka koma England,duk sati sai na kira baba Habu maigadin mu na Abuja na tambayeshi ko Ibrahim yazo? Kuma duk sati amsar daya ce "bai zo ba tukun" rannan ina kiran sa kafin inyi magana yace "mai sunan daada" gaba na ya fadi nace "na'am baba" yace "indai har da gaske yana sonki zaizo, ni kuma in yazo zan bashi sakonki kuma zan kira ki in gaya miki yazo har in baki shi ma ku gaisa, idan kin ga bai zo ba, to ba son gaskiya yake miki ba ko kuma Allah bai kaddara alakar da take tsakanin ku mai dorewa ce ba, ki kwantar da hankalin ki, ki manta da batun sa, kiyi karatun ki" jikina naji duk yayi sanyi, kirjina yayi nauyi, nasan gaskiya baba Habu ya gaya min amma anya kuwa zan iya? Murya a sanyaye nace "nagode baba" daga nan ya kashe wayar. 


Mun kama karatu sosai. Ita kanta makarantar abar kallo ce, dan zan iya cewa gari guda ce, with its ancient buildings, kowanne faculty kamar unguwa guda ne, dan saida daddy ya bamu maps yace muke tafiya dashi saboda kar mu bata. School of medicine duka muke ni da Hafsat, kuma first year komai tare za'ayi mana tunda kamar introductory courses ne, daga third semester kuma zuwa sixth kowa zai dauki individual courses din field dinsa, shekara ta hudu da ta biyar kuma zamuyi clinicals, kamar practical kenan inda zamu tafi asibitoci muna koyon aiki a gurin kwararrun likitoci, shekara ta shida kuma project. Tsarin makarantar tsari ne me kyau, lecturers dinsu sunsan me sukeyi, ga kayan aiki nan kamar banza, a raina nace dole a kira ta da second best university in the world. 


Tunda muka fara lectures kawai sai naji nayi loosing interest a karatun, sam bana gane me akeyi. Ina shiga lecture hall zan tafi seat din baya in zauna in yi ta sake sake a raina ina tuno rayuwar sec sch din mu, sai inji gaba daya hankali na ya koma Nigeria. Sometimes sai inke ganin kamar a class din mu muke, Ibrahim zai iya shigowa anytime. Wani lokacin kuma sai inji kamar kamshin turarensa sai inyi ta waige waige. Duk sanda wani yazo yana son yayi min magana sai inji kamar Ibrahim yana kallona da lumsassun idanuwansa. It is like he is watching me. Sau da yawa in mun shiga lectures sai in kwanta inyi ta bacci har sai an gama sannan Hafsat ta tashe ni. Hafsat tayi fadan, tayi nasihar amma ina, sai da tace zata gayawa mommy bacci nake a class sannan na daina baccin amma still attention dina baya gurina. It is a million miles away. Only time da nake zama inji lecture sai a psychology courses dina. In homework aka bayar sai dai Hafsat tayi mana, kullum tayi ta min gori tana yimin bala'i amma bazan yi ba. It is as if spirit dina na karatu is gone. 


A haka muka gama first semester, lokacin exams ma da kyar Hafsat ta tirsasa ni na danyi karatu tana koyamin wasu abubuwan. Hutun da aka bamu babu yawa dan haka daddy yace ba zamu je Nigeria ba, ranar har zazzabi nayi, mommy ta ga ciwona yana kokarin tashi ta kwashe mu muka tafi yawo banda daddy sai security daya hada mu dasu. Mune gari gari, duk garin da muka je sai mu samu hotel mu kwana, mune zuwa kallon London bridge, mune har Scotland da Wales. Na saki raina sosai nayi enjoying time dina. 


Hutun mu yana karewa muka dawo gida. Muka cigaba da zuwa makaranta. Har yanzu bani da kawa ko aboki, in fact da yawa daga 'yan ajin mu basu sanni ba, wadanda duka sanni ma suna referring to me as Hafsat's sister, dan basu san suna na ba. It is like am afraid to get attached. Duk abinda akeyi daddy bai sani ba, tunda basu kafe result ba sunce sai at the end of the session. Mommy kuma tunda a gida ina nuna bani da wani problem itama bata taba tunanin ina da problem a karatuna ba. Ni dai kullum lissafin sanda zamu yi hutun session nake yi, dan wannan karon nayi alkawarin bincike zanyi sosai sai na nemo Ibrahim na gaya masa daddy yace bai damu ko wanne kabila ne shi ba, bai kuma damu da cewa he is not wealthy ba, gani nake yi hakan ne kawai zai saka ni in maida hankali na akan karatu na. 


Second semester tana karewa aka fitar da result na both semesters din. Tunda Hafsat ta gayamin gaba na yake faduwa, nasan ban aikata abin kirki ba. Allah Allah nake mu tafi Nigeria kafin daddy yaga result dina in yaso in mun dawo ayi wacce za'ayi. Adduah ta bata karbu ba dan washegarin da aka kafe result muna main palo muna kallo sai mommy ta kira Hafsat tace muzo daddy yana kiran mu. Muna shiga palon su na san daddy yaga result dina. Bantaba ganin bacin rai a fuskarsa irin na ranar ba. Muna zama su yaya Walid suka shigo da fara'arsu, ganin yanayin fuskar daddy suma suka shiga taitayinsu. Muna zama ya jeho min takardar hannunsa yace "pick it up" hannu na rawa na dauka, yace "bude ki karanta a fili inji" nan na bude na fara karanta sakamakona. Tun daga first semester har second bani da B ballantana A. Mostly C ne har da D. Nan daddy ya fara fada, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, tun ina daurewa har na fara kuka. Yayi min wankin babban bargo mommy ta dora a inda ya tsaya. Su bakin cikin su shine sunsan ina da kokarin kawai karatun ne suke ganin banyi niyyar yi ba. Nan daddy yace dole ayi punishing dina akan abinda na aikata. Yace "punishment dinki shine, no holiday for you. Zaki zauna ke kadai a England ba zamu tafi dake Nigeria ba. Use the time to think about what you have done to your life. Sannan kiyi karatu so that you can catch up a inda aka barki a baya" daga haka ya mike ya shige cikin bedroom dinsa ya turo kofa

 


Episode Twenty Nine: The Message


Kowa a palon yayi shiru, hatta ni da nake kuka nayi shiru ina assessing me daddy yace. It then dawn on me suddenly cewa yana nufin bazan je Nigeria ba. Ai kuwa da gudu na mike na nufi kofar dakinsa ina kuka ina "daddy dan girman Allah kayi hakuri, daddy na tuba please" amma ko motsin sa banji ba, nan na durkushe a gurin ina faman gumurzun kuka. Hafsat ce tazo ta kamani ta mayar dani falo. Na zauna a kasa na kifa kaina a cinyoyina ina cigaba da kuka. Hafsat tace "mommy please do something" mommy wacce itama daga dukkan alamu hukuncin na daddy ya bata mamaki, tayj ajjiyar zuciya tace "yayi fushi sosai, and she deserves to be punished" ya Walid yayi sauri yace "amma mommy kunsan fa yarinyar nan ba lafiya ce ta ishe taba, ta yaya za'ace mu tafi mu barta ita kadai thousands of miles away? Ni dai mommy idan daddy yaki yarda a tafi da ita zan zauna anan nima, kice masa ina harkar wani project and I need to stay in town" mommy ta harare shi tace "kana tunanin he will buy that, duk harkar karatunku babu abinda bai sani ba, yasan cewa babu wani project da kake yi" ya Habeeb yace "at least mommy try something, ba za a bar maganar nan kawai ace shikenan ba" ni daj duk ina jinsu bance komai ba, kuma ban daina kuka ba. Mommy ta mike tace "ina zuwa" sai da naji mommy ta shiga dakin daddy sannan na dago kaina ina goge hawayena. Tun muna yara nasan sau da yawa mu na cewa mommy tana da magic, duk sanda ka tambayi daddy wani abu yace no, to in ka samu mommy tace yes, daga ta shiga dakin daddy ta fito shikenan sai kaji shima yace yes din. A lokacin yarinta sai muke cewa magic ne take yi masa. Mun jima a zaune ba wanda yake yin magana, ni dai in banda sunayen Allah babu abinda nake kira "please God intervene, bana jin zuciya ta zata iya daukan wannan hukuncin" it has already been a year rabo na da Nigeria, da Ibrahim, i just want to know if he is ok. Bude kofar mommy ne ya dawo dani daga tunani na. Fuskarta kawai na kalla nasan cewa wannan magic din baiyi nasara ba. Tana zama na rarrafa gurinta na dora kaina a chinyar ta na cigaba da rusa kuka na. Bata rarrashe ni ba ta fara magana. "Moon, you will be left behind. Zaki zauna kiyi karatu for two months, zai shiga makaranta ya karbo miki textbooks na courses din da kuka yi last session wadanda zaki karanta. Kowanne textbook zaki rubuta formal report akansa in mun dawo zaki wa daddyn ki submitting shi kuma zai kai department din ku with hope zaku kara miki grades dinki. Za'a bar securities, you are not to leave this building har sai mun dawo, za'a bar miki david, chief bodyguard din daddy, duk abinda kike so a cikin gari ki gaya masa zai siyo miki. Cooks da sauran servants duk zasu zauna suna kula da ke da gida. Za'a dauko miki nurse din da zata ke zuwa tana kwana dake, kuma zata ke gwada bp dinki three times aday. A clinic din embassy take" ta juya wajan ya Walid tace "bai yarda da zaman ka ba anan. Saboda bai yarda ya barku daga kai sai moon ba. Nima kuma ban yarda ba" tana gama fadin haka ta mike ta shige daki. Knowing mommy, nasan kuka zata je tayi. 


Haka abin ya kasance, textbooks kwali biyu daddy ya lode min wai duk ni zan karanta. Ina kallon su suna ta shirye shiryen tafiya banda ni. Da assuba jirgin su zai tashi dan haka tun cikin dare su ka tashi suna ta wanka da shiryawa. Inajin Hafsat ta na shiryawa nayi banza da ita nayi kamar bacci nake yi. Ta zo ta tsaya a gaban gadon da nake tace, "Moon I am going" na kalle ta kawai bance mata komai ba. Ta sha bakaken kaya da wani bakin glass a fuskar ta. Nasan ta saka glass din ne sano da kar inga kukan ta, she is too proud to let me see her tears. Tunda aka haife ni muke tare da Hafsat, bana jin mun taba sati daya ba tare ba. Yanzu gashi zamuyi two months ba tare ba. Tace "zan yi iyakacin kokarina inga na samo miki news" na gane maganar da take yi, a hankali nace "thank you" daga haka ta juya ta fita tare da rufe ko fa. Ina nan dai a kwance naji anyi knocking kofar sannan aka bude a hankali. Kamshin turaren daddy naji nayi sauri na rufe idona. Ya jima a tsaye yana kallona sannan naji ya hawo gadon yayi kissing dina a goshi sai kuma naji ya sauka ya rufe kofa. Hawaye naji yana zuba daga idona masu zafi. Next ya Habeeb ne yazo da dariyar sa yana ta tsokana ta wai daddy so yake na zama prof kafin su dawo. Sai da ya fahimci cewa am not in the mood for wasa sannan ya rabu dani sai ga mommy nan ta shigo itama, complete ta gama shiryawa dan harda handbag dinta a hannunta. Ina ganin ta naje na rungume ta ina cewa "mommy dan Allah kice daddy ya bar ki su su tafi" ta girgiza kanta tace "kema kinsan hakan ba zai yiwu ba, kiyi abinda yace miki shine mafi alkhairi a gareki, kinsan dan yana sonki yayi hakan ba wai dan yana kinki ba, in mun barki ba karatu ai bamuyi miki gata ba. Kuma yace in dai har ba kici 70% a report din da zaki rubuta ba to next holiday ma ba zaki je ba. Take care of yourself, do as u are instructed and you will be fine" daga nan tayi min kiss a cheek dina ta fita. Na durkushe a gurin zuciyata tana yimin zafi, ina jin tashin motar su amma na kasa lekawa har suka tafi. 


Tunda suka tafi ko palo ban leka ba har bayan magrib. Ina kwance a kan gado sai dai in tashi inyi sallah in kuma komawa in kwanta. Bayan magrib ne naji ana knocking kofar bedroom din, da sauri na tashi ina tunanin ko daddy ya chanza shawara an bar wani a cikinsu. Ina bude kofar naga wata mata da kayan nurses a jikin ta tana murmushi tace "good evening, my name is... " kafin ta karasa nace cikin tsawa "go away" tare da banko kofar na rufe. Sai wajan karfe goma na bude dakin na fito shima azababbiyar yunwa ce ta dameni, ina fitowa naga abinci a jere akan center table din palon, na wuce na bude fridge na dauko fresh milk na koma daki. Washegari da sassafe yunwa ta addabeni na fito palon na sake ganin breakfast a ajjiye, naje na zauna na fara hada tea, ina cikin sha naji an bude kofar extra dakin da yake kusa da nawa, wannan nurse din ta jiya ce ta fito, kallo daya na yi mata na dauke kai, tazo inda nake tace min "good morning, my name is Victoria, your father asked me to take care of you" nace " OK " ba tare da na kalle ta ba. Har ta juya zata tafi sai kuma naji babu dadi a raina tunda ni ban iya wulakanta mutane ba, kuma ba laifin ta bane aka tafi aka barni ba, na kira ta nace "zo muci abinci" tace ok, tazo mukayi breakfast tare, sannan ta gwada bp na tayi recording, daga nan ta fice ta tafi office dinta. 12 ta dawo da sake gwada bp na ta fita, ina nan dai zaune ni kadai kuma naki bude kwalin books din ballantana in fara karatu, har six din yamma, sai ga Victoria ta shigo tace "I have gift for you" sai ta dauko wadansu CDs na movies har guda biyar ta miko min, tace "since you don't have interest in reading book, i thought maybe you will like watching movies" na karba nayi mata godiya sosai. Nan da nan na fara kallon movies din. Duk kannin su akan likitanci ne, suna koyar da harkar medicine amma a cikin labari, ranar kwana nayi banyi bacci ba ina kallo, sosai naji interest dina yana dawowa akan karatu. Washegari nace ta kawo min wadansu films din, da rana kuwa da zata zo sai gasu ta karo min wasu, sam bata takura min akan inyi karatu ba amma tana ta gayamin amfanin karatun da, dadinsa. As a doctor zaka zama kana saving life din mutane, babu wani feeling din da yafi, dadi akan ace someone is alive because of you. Da yamma ta dawo tace inzo mu fita yawo, muka fita muka zagaya cikin embassy din, duk wanda muka hadu dashi sai sun gaisa sai ta gaya masa ko ni wacece. Ina kallon David yana bin mu duk inda mukayi. 


Five days muna tare da Victoria, da yake bani da wahalar sabo nan da nan muka saba. Har yanzu dai ban fara karatu ba amma sosai ina jin son karatun a raina, kuma bp dina is great. Ranar kwana na biyar din ina daki ina kallon daya daga cikin movies din da victoria take kallo sai na ji kamar motsi a main palo, gaba na ya fadi tunda nasan sai 12 Victoria take zuwa. Na tashi a hankali na dan bude kofar palon mu na leka, kawai sai ganin daada nayi a tsaye tana ta kalle kalle, can kuma sai ta takarkare ta rangada sallama "salamu alaikum" ai bansan sanda na fita da gudu na rungume ta ba, kafin in gama recovering daga shock din ganin daada a palo sai ga Faruk da Amina sun shigo suna jan akwatinan su. Nan na saki daada na je na rungume su a tare, har da kwallar murna a ido na. 


Sai da muka gama murnar ganin juna sannan daada take gaya min cewa ai bayan su mommy sunje Nigeria ta tuburewa daddy lallai idan bai bar su daada sun taho wajena ba to ita zata dawo. Inna kuwa tana jin labarin abinda ya faru tace lallai ya kira David ya gaya masa ya sako ni a next plight in taho gida, shine yace mata ai ya zai turo su daada su zauna a gurina. Ita kuma Amina tana jin labarin tafiya England tace lallai sai ta biyo su tunda dama daddy yayi mata alkawari, Shine suka taho tare. Naji dadin zuwansu sosai, nan da nan na qara warwarewa, daada ta dage tana ta yimin nigerian dishes da nake missing. Faruk kuwa kullum sai ya fita yawo shi da David, wata rana Amina ta bisu wata rana kuma tayi zamanta. Zuwan su daada bai hana Victoria zuwa ba, ta daina kwana dai amma kullum sai tazo sau biyu ta gwada jinina kuma munyi hira wanda mostly akan harkar karatu ne da kuma harkar medicine. A lokaci daya sai naji hankali na ya karkata a gurin karatu, na zauna na ributa timetable wacce zata bani damar yin karatu for 5hours kullum. Part dinsu daddy nake zuwa inyi karatuna yadda babu wanda zai dameni. Nayi browsing yadda ake rubuta study report, nan take na fara rubutawa. 


Sai da su daddy suka yi wata biyu chip a Nigeria sannan suka dawo, ni kuma a lokacin na karantu sosai dan banajin ko Hafsat zata gaya min sanin abubuwan da aka yi mana. Na hada report dina tsaf na kai bedroom din daddy tare da apology letter ina bashi hakurin abin da nayi, da kuma alkawarin bazan sake yi ba. 


Ranar da zasu dawo gabadaya muka tafi airport muka taro su, murna a gurina kamar ranar sallah, saboda ba karamin missing din su nayi ba. Ban tambayi Hafsat ko ta samu labarin Ibrahim ba ita ma kuma bata cemin komai ba. Satin su daya da dawowa muka koma school, yanzu an raba mu da Hafsat kowa ya koma bangarensa, amma a yanzu kam Alhamdulillah ina gane karatu na sosai, in an shiga lecture ina zama a gaba kuma ina bada attention dina sosai, kuma sai naji karatun babu wahala tunda duk basic abubuwa na iya su.


A ranar wata Thursday, na riga Hafsat dawowa ina zaune a main palo ni da mommy da Amina sai ga wani security yazo yayi knocking kofa, naje na bude masa sai na ganshi tare da wani mutun. Muka gaisa dasu sai mutumin yace "I have a mail from Nigeria for miss Hafsat" nace masa "bata nan amma zan karba mata" nan ya bani wasu takardu nayi signing sannan ya miko min sakon. Brown envelope ce babba, na shafa ta sai naji kamar takardu ne a ciki. Na koma palo nace da mommy sako aka kawo wa Hafsat amma ban fada mata daga Nigeria bane, hankalinta yana kan kallo dan haka bata kalleni ba, na wuce na shiga part din mu, na ajiye sakon akan bedside table na zauna akan gado, haka kawai sai naji zuciya ta tana ayyana min in bude in ga menene a ciki, can nayi tsaki a raina nace in Hafsat ce aka kawo min sako babu abinda zai hana ta budewa taga menene, dan haka zuciya ta daya na dauko na bare seal din na zazzage contents din akan gado. Wata irin bugawa kirjina yayi saida na dukushe a gurin. 


I think this is the longest episode so far. Ko me sakon Hafsat ya qunsa? Me ma i don't know 😝


Post a Comment

0 Comments