Maimooon best hausa novels

 Maimooon


Episode Twelve : This is Me


Note: duk maganar da akeyi da Ibrahim da turanci akeyi, amma zamu keyi da hausa saboda a samu sauki fahimta. Ayi karatu lfy


"Da gaske sisters ne su? " ya fada yana kallon sauran 'yan ajin. Duk ajin ya dauka "eh sir sisters ne, baka ga suna kama ba? " ya sake kallon mu yana girgiza kai, "ni ban ga kama ba" Hafsat ta kara kulewa ta hade rai sosai, shi kuma sai ya kalleta yayi dariya yace " ok Big Sister, kiyi hakuri na takura ma kanwarki. In babu damuwa to in dawo desk dinki mana maimakon nata? " Hafsat ta bude baki tana kallonsa da mamaki, sannan tayi sauri tace "a'a yi zamanka anan" yayi dariya sosai har habarsa ta lotsa sannan yace "dama nasan zaki ce haka, nima kuma nafi son zama anan" nidai duk ina jinsu bance komai ba. Sai da period dinsa ta fita sannan yace min "kar ki manta alkawarin mu, ni kadai nasan abinda zanyi miki in kika yi min irin ta rannan" da haka ya fita daga ajin. Yana fita Hafsat ta jawo kujerar ta kusa da tawa tace " alkawarin me mutumin nan yake magana akai? Yaushe kuka hadu har kika yi masa alkawari ba tare da nasa ni ba? " na kalleta nace " wani lokacin Hafsat ina mamakin mutane in suka ce na fiki surutu, sa idonki yayi yawa Hafsat " nan Hafsat ta kuma kuluwa tace " au haka ma zaki ce ko? Duk abinda nakeyi fa dan ke nakeyi. Mutumin nan daga ganin sa ba mutumin kirki bane, bana son kowacce irin alaka a tsakanin ku. I am trying to protect you" nace " ni kuwa Hafsat kina bani mamaki duk sanda kika ce Ibrahim ba mutumin kirki bane ba, how do you know? Kin san kullum daddy yana ce mana never judge a book by it's cover, ba dai dai bane ba kawai ki yanke hukunci akan mutum ba tare da kin fahimce shi ba" tace "OK kina so ki gayamin cewa ke kina so ki fahimce shi kenan ko? " nace mata "exactly " Amira ta taso tazo gurin mu tace "pls guys not here, zamuyi maganar in munje hostel" Hafsat ta cigaba da balbalin fada ni kuma na tashi kawai na fita daga class din. Kan veranda na zauna ina tunanin yadda zan bullowa wannan lamarin, nasan Hafsat akan gaskiyarta take fada, duk da ina da karancin shekaru amma na gane duk abubuwan da Ibrahim yake min da duk kwana kwanar sa nasan inda ya dosa. Kuma ni kaina basai wani yayi min fada ba nasan nayi kankanta da zuwa inda ya dosa. Abu na biyu kuma Ibrahim bayarabe ne, ni kuma bafulatana bana jin tarayyar mu dashi zatayi kyau. Murmushi nayi sanda na lissafo fuskar mommy inta samu labarin ina dating yaroba guy. Amma koma menene zai kasance yau zamu zauna muyi magana da Ibrahim, zan bukaci ya fada min duk abinda yake zuciyar sa ni kuma zanyi masa bayanin cewa abin ba me yiyuwa bane. Ina so mu samu maslaha a tsakanin mu. 


Da aka tashi bayan munyi sallah munci abinci Amira ta jamu dakin su tana so ta daidaita tsakanin mu da Hafsat. Na zauna a nutse na yiwa Amira bayanin abinda yasa nake son muyi magana da Ibrahim. Muna ta maganar mu Hafsat tayi banza ta rabu damu, saida Amira tace mata "baki ce komai ba Big Sister" ta fadi big sister din da tsokana, irin yadda Ibrahim ya ce mata dazu a class. Ta juyo ta kallemu tana yamutsa fuska tace "She can do as she wants, ni dai tasan cewa komai tayi kamar tayi a gaban mommy ne dan wallahi sai na gaya mata" Amira tace "Haba Hafsat pls let her go, inta dawo zata gaya mana duk abinda sukayi dashi daga nan za muyi shawarar me zatayi next" Dakyar Amira ta lallaba Hafsat ta barni na tafi da sharadin cewa duk abinda yace min zanzo in gaya mata. 

Naje nayi wanka na shirya a tsanake, dama ni ko a gida ba kwalliya nake ba ballantana a school na saka hostel wears dina, har na nada vail dina sai kuma na chire na dauko dogon hijab din Hafsat na saka. Ina fita na nufi library, tun daga nesa na hangoshi a zaune a side din library din da table a gabansa dauke da littattafai, amma kuma ba karatun yakeyi ba waya yake dannawa. Na karasa da sallama, ya dago kai ya kalleni da murmushi a fuskarsa, daga gani ya dade a zaune a gurin. Ya nuna min kujerara kusa dashi yayi min nuni da in zauna. Maimakon in zauna a kusa dashi din kamar yadda ya bukata saina dauki kujerar na zagaya daya side din na zauna ina fuskantarsa. Ban gaishe shiba nace masa "am here, what do you want ?" Ya sake yin murmushi yace min good evening ma'am" sai kuma naji kunya ban gaishe shiba nace "good evening sir" ya cire glasses din idonsa yana murza idon yace "har na fara tunanin bazaki zo ba, na dauka yau ma Hafsat ta hana ki zuwa" na kalleshi da mamaki nace "ya akayi kasan ita ta hanani zuwa rannan? " yace "da ban sani ba, sai dazu data cemin ita sister dinki ce sannan na fahimci ita ta hana ki zuwa" muka yi shiru baki daya na wani lokaci sannan ya cigaba da magana a hankali " am sorry for shiga rayuwarki da nayi kwana biyu. Nima bansan mai yake hawa kaina ba tun zuwa na makarantar nan, ina so ki fahimci cewa bani da wani mugun nufi a kanki sai alkhairi insha Allah. Tun ranar da kika amsa question dina a class naji kin burgeni, bayan na fita daga ajin ku na je staff room nayi tambaya akan ki anan na fahimci cewa you are a genius " nayi saurin katse shi nace "am not a genius " yayi dariya yace "research ya nuna cewa babu genius din da ya taba yarda cewa shi genius ne" ban bashi amsaba na sunkuyar da kaina kasa. Ya cigaba da cewa "tun daga nan na zama interested akan ki, lokacin ne nayi miki offering friendship. Kuma ina saka ran babu wani abu da zai rusha friendship din mu" ya sake yin shiru kamar ya gama magana sai kuma yace "ita zuciya tana da wahalar fassarawa, na kasa fahimtar me zuciya ta take nufi dake. Kullum sai inji ina so in ganki, inna ganki kuma sai inji bana so mu rabu, in ban ganki ba kuma sai inji na rasa farin ciki na" ya sake yin shiru yana shafa gashin kansa. "What do you want from me? " na sake tambayar sa a karo na biyu. Ya yi tagumi da hannayensa duk biyun ya sauke lumsassun idanuwansa a kaina sannan cikin muryar rada yace " ina so ki kara kahuri dani mu cigaba da friendship din mu, nasan wannan feeling din da nake ji akanki zai wuce wata rana. Ina so please kiyi tolerating dina for the time being. In kina ignoring dina zan iya aikata wani abun da ba dai dai ba". Duk bayanin da yake yi ina jinsa kuma ina analyzing duk maganganun sa. Na bude baki zanyi magana kenan sai ya daga min hannu ya dakatar dani yace "kar kice komai yanzu, ki bari sai kinje hostel kinyi tunani akai tukunna. Ina so mu cigaba da zama a friends but i have feelings for you. Nace masa to zanje inyi tunanin kamar yadda yace. 


Muka danyi shiru na wani lokaci sannan ya ce " kafin kiyi tunanin amma ina so in dan baki brief labari na saboda ki fahimceni sosai. Kamar yadda na sanar dake ni bayarabe ne full blood. A yanzu shekaruna ashirin da biyar da haihuwa. Mahaifina ya rasu tun ina five years old. Nine babbar a gurin parents dina, sai kanne na mata su biyu. Bayan rasuwar mahaifina mamana ta sake aure ta haifi maza su biyu. Step father dina babban malamine a garin Ibadan, a gurinsa na koyi karatu sosai. Ya rike mu ni da sisters dina tamkar shi ya haifemu dan idan ba gaya maka akayi ba ba zaka san ba shine baban mu ba. Daga mamana har step father dina basu yi wani karatun boko sosai ba, baban mu dai yana dan taba kasuwanci kadan sai kuma islamiyya da yake koyarwa a unguwar mu, dan haka mu ba masu arziki bane sosai sai rufin asiri dai dai gwargwado. Allah ya bani kwakwalwar karatu na arabi da boko, wannan yasa baban mu ya sakani a makarantar kudi dan insamu ilimi mai kyau kuma Alhamdulillah na samu. Duk kudin babanmu akan karatuna yake karewa, sauran siblings dina duk a makarantun government suke, a cewar baba ni zan kula dasu inna samu aiki. Bayan na gama secondary school ne na samu na fara aikin teaching a wata primary school dake unguwar mu. Shekara ta uku ina teaching ina samun salary na baba yace lallai saina koma makaranta nayi degree, Allah ya taimakeni na samu admission a university of Ibadan nayi degree na a fannin mathematics. Na samu kyakykyawan sakamako na fita da first class shine NYSC suka zabe ni aka turo ni nan".



Episode Thirteen : This is Me 2


Ya dakata yana kallona da murmushi a fuskarsa yace "now, tell me about yourself" nayi shiru ina tunanin mai zance mishi, sai na tuno da maganar daddy da yake ce mana (if someone tells you about their misfortunes, don't tell them about your blessings, it will makes them feel worse)

Dan haka sai na samu kaina da gaya masa cewa mu fulani ne daga 'yalleman jigawa state. Muna zaune a abuja, babana yana aiki da gwamnati, mu biyar ne a gidan mu etc. Ban gaya masa wanne aikin daddy yake ba ballantana ya fahimci cewa mu masu arziki ne. Wannan shine babban kuskurena na farko. Sai da nayi shiru sannan na dago kaina muka hada ido sai naga yayi dariya a hankali yace "is that all? " nace masa "yes, that's all" yayi shiru sannan yace "OK, koma dai menene baki gaya min ba zan sani ne a nan gaba, kinsan a hankali kake sanin mutum, halayensa, likes and dislikes etc. Yanzu dai tell me, from what we discussed, what do you understand about me? " nayi shiru ina kallonsa for sometime, sai kuma wani tunani ya fado min a raina kawai sai na kana dariya, yana kallona shima da dariya a fuskarsa yace "what? Menene ya baki dariya?" nace "it's nothing really, a funny though just crossed my mind" yace "OK, share with me, let's laugh together" na nutsu a hankali nace "this is going to hurt a little, duk sanda naji an ambaci sunan yaroba, the first thing that came to my mind is fat, short, people masu katon ciki, kuma masifaffu, most of them Christians. So when u asked me what i learnt about u i realised that what i learnt is not about only u, it is about people in general. Mutane da yawa yanda ake kallon su ba haka suke ba. You for example, are neither fat not short, bansani ba dai ko kana da masifa, and u definitely are not a Christian. Ban taba sanin cewa akwai handsome yarobas ba" murmushi naji yana yi mai sauti, na dago kai muka hada ido sannan na fahimci abinda na fada, indirectly na gaya masa yana da kyau, kunya naji ta rufeni kamar inyi tsuntsuwa in tashi daga gurin. Nayi sauri nace cikin in ina "i did not meant to say you are handsome, i mean you are amm..you are.. I mean" ya katse ni da cewa "i understand, and thank you so much, i really appreciate it" dariya yake yi sosai, yayinda ni kuma na rufe fuska ta da hannayena biyu, sai da ya gama dariyarsa sannan yace "and you my dear are very, very beautiful. You are the most beautiful intelligent girl I have ever seen in my life. Akan maganar yaroba kuma ina tabbatar miki cewa ba gaskiya bace, we have fat, thin, short and tall people among us kamar kowanne tribe, akan maganar addini kuma, more than 60% na yaroba are muslims kuma we are very religious. Kin ga kamar ni for example, both bangaren uwa da uba na bamu da Christian ko daya. Kuma let me tell you something, ni tunda nake ban taba shiga north ba, dan haka duk sanda aka ce fulani abinda yake zuwa mind dina shine illiterate mutanen daji masu kiwon shanu" dariya mukayi gaba ki dayan mu sannan nace masa "duk family na babu masu kiwon shanu" muka sake yin dariya sannan yace "now we all know better "


Muna haka alarm yayi beefing a wayarsa, ya duba yace "time for asr prayer" Muka mike a tare muka yi shirin alwala. Bayan munyi sallah a masallaci na riga shi dawowa inda muke zaune, na bude textbook din maths a cikin littattafan da ya dora akan table din na fara karantawa, sai gashi yazo sai ya dauko notebook dinsa ya nuna min note din da yayi forming na abinda zamuyi this week a maths. Nan muka zauna yana ta koya min har magrib sannan mukayi sallah na tafi hostel shi kuma ya tafi staff quaters. Ina shiga hostel dakin su amira na tafi muka zauna tare har lokacin islamiyya yayi, muna ta hira da ita amma ga mamaki na bata tambayeni game da Ibrahim ba, har sai da muka zo tafiya islamiyya sannan nace mata "Amira baki tambayeni yadda muka yi da Thin Tall Man ba? " sai ta ce "nasan ai zaki bani labari ne when you are good and rready" naji dadi har cikin raina. Amira is such a good friend to me, bata damu da sai na gaya mata komai ba, kuma duk sanda nake bukatar shawara she ia there for me. A islamiyya muka hadu da Hafsat amma ko kallo na bata yi ba. Ibrahim ma bai yi min magana ba sai dai duk sanda muka hada ido sai yayi min murmushi kuma nima haka kawai sai na sami kaina da mayar masa. 


Da muka tashi nima banbi takan Hafsat ba nayi tafiyata daki nayi wanka na kwanta. Ina jinta ta shigo tana shirin kwanciya su naomi suna yi mata magana tayi banza ta rabu dasu. Ni dai ina kwance amma na kasa bacci ina ta lissafin abubuwan da suka faru a ranar. Alaka ta da Ibrahim tana neman kawo matsala tsakani na da Hafsa kuma bana jin dadin hakan saboda no matter what, blood is thicker than water. Duk duniya bayan iyayena bani da sama da Hafsat. Amma Hafsat tana da matsala, idan na bata dama zata ce zata ke controlling dina ne akan komai, bawai akan Ibrahim kadai ba. Dan haka na yanke shawarar ko menene zai faru bazan bata damar controlling dina ba. A bangaren Ibrahim kuma though yayi admitting cewa he has feelings for me,  amma baiyi magana akan soyayyaba dan haka na yanke shawarar zan ci gaba da kulashi kamar yadda ya bukata amma da zarar naga yana kokarin wuce gona da iri zan taka masa burki, and so help me God. A dan fahimtar da nayi masa na fahimci cewa shi mutun ne mai ilimi, dan haka nayi alkawarin zan mori ilmin sa, zan ke koyan karatu a gurin sa, in that way duk kanin mu zamu ke gaining kuma relationship din mu ba zai zama suspicious a makarantar ba. Da wadannan shawarwarin bacci ya dauke ni. 


Post a Comment

0 Comments