MAIMOON. BEST HAUSA NOVELS

 Maimoon


Episode Twenty: The New Job


Bayan mun koma gida da sati daya daddy ya zo. Ranar duk mun hadu a main falo muna kallo, ina kwance a cinyar mommy tana yi min tsifa, Hafsat kuma suna playing chess ita da Ya Habeeb wanda yanzu ya gama SSCE dinsa yana jiran result, da Faruk. Ya Walid ne kadai baya nan tunda su basu samu hutu ba. News aka fara daddy ya karo volume muma duk sai hankalin mu ya karkata akan TV din. Titi aka nuno chike da hold off ana ta hayaniya can gaba kuma wasu motoci ne guda biyu suka yi crossing suka rufe titin ruf babu hanyar wucewa. A kusa da motocin kuma wasu samari ne sun takarkare suna ta jubgar junansu kamar Allah ne ya aiko su. Camera tayi zooming fuskokinsu ga mamakina sai naga daya daga cikin su dariya yake yi shi kamar game ne abin a gurinsa, dayan kuma sai huci yake yi da alama dariyar dayan ce take kara kular dashi kuma daga dukkan alama me dariyar yafi shi karfi. Daddy ne yayi gyaran murya yace "Habeeb wannan ba Sultan ba ne?" Ya Habeeb ya dan kalli TV yace "Hmm shine fa daddy, yana nan sai abinda ya kara gaba" mommy tace "ai dan baka zama sosai ne, mu yanzu ai mun saba da labarai akan Sultan, kusan kullum zancen kenan. Ni na rasa wanne irin yaro ne wannan. Daga yau a kama shi da drunk driving, gobe fada akan titi ya kama yaran mutane yayi ta jubga, jibi kuma sai kaji ance yaje yayi terrorizing unguwa. Kuma wai an rasa mai daukan mataki akan sa, wannan wacce irin rayuwa ce" daddy yace "ba laifin sa bane, laifin maimartaba ne. Ni bansan yaushe ya chanza hali ba, mutum ne shi mai zafi sanda muna makaranta" da sauri muka hada baki ni da Hafsat "daddy dama sarki abokin kane" yayi dariya yace "ba abokina bane, kawai dai munyi makaranta tare, department din mu daya dashi a Oxford, first degree da second, amma ba abokina bane, tunda ni talaka ne a lokacin su kuma 'ya'yan masu kudi ne. Muna haduwa dai in za'ayi taron Nigerian students. Ni lokacin tsoro yake bani, wato kato ne gashi baki ga zafin zuciya" duk mu ka kwashe da dariya. Ya Habeeb yace "ah bara mu je mu siyo alkyabba, ai ni daga yau na zama dan sarauta tunda babana sunyi makaranta daya da sarki" nan ma dariyar muka same yi, bayan anyi shiru daddy ya shigaba da cewa "bayan mun gama masters ne, munyi applying for PhD sai na daina ganin sa, na tambaya akace sun dan samu problem ne da babansa akan yarinyar da yake so, shine uban ya chire shi yace a daina karatun. Nasan yarinyar dan ina yawan ganin su tare, balarabiya ce, I can remember in na gansu har dariya nake yi, shi bakikkirin ita fara tas, kyakykyawa ce sosai" muka yi dariya ganin yadda mommy ta turo baki kamar yarinya. Na juya na sake kallon screen din TV naga police sun zo scene din an raba fadan, wanda aka kira da Sultan ya kama police guda daya da kokawa sai da suka taru akan sa sannan suka saka masa ankwa, He was still grinning. Anan camera ta tsayar da hotonsa, reporter ta fara lissafo irin crimes dinsa amma da an kama shi za'a sake shi saboda dan sarki ne. Na kura masa ido ina kallonsa. Kyakykyawa ne first class, kana ganin sa kaga half caste, fatar sa golden brown mai kwalli da daukar ido. Idanun sa dara dara farare tas, hankinsa kamar an auna da fuskarsa, lips dinsa tamkar ya shafa jan baki. Bashi da tsaho sosai amma fa a murde yake dan sai da police uku suka hadu sannan suka iya rike shi. Na dauke kaina ina aiyana yadda rayuwar sa take. What is his story? Kawai na samu kaina da tambayar daddy "daddy to an yi auran?" Yace "auran wa?" "Auran balarabiyar, naga wannan kamar halfcast ne" daddy yayi shiru yana kallon hoton sultan a TV sannan yace "gaskiya I can't say ko anyi auran ko ba'ayi ba" mommy tace " anya kuwa anyi? Dan na taba shiga fadar amma matar sarkin da na gani bahaushiya ce, and she is far from being beautiful, kuma na lura Sultan din dan ta ne dan lokacin tana ta fada wai an tafi dauko shi daga airport da wrong car, specifically ya fada yace ga motar da yake so a dauko shi amma aka ki. Gaskiya ina ganin kamar itace ta bata sultan" daddy ya girgiza kai yace "Allah ya kyauta".


Washe gari da sassafe na tashi, na shiga kitchen naga cook din mu tana ta kokarin hada breakfast. Pancakes na yi irin yadda naga mommy tana yiwa dadday, na hada masa coffee shima irin yadda yake so. Na hada da cup da komai akan tray na hau saman daddy. A balcony dinsa nagan shi kamar yadda nayi tsammani. Yana zaune yana karatun news paper. Na durkusa na gaishe shi sannan na koma falonsa na dauko stool na dawo na dora masa tray din da na kawo akai. Na zauna a kasa a gefen sa. Sai da ya fara shan coffee dinsa sannan yace "ya akayi ne maimunatu?" Na sunkuyar da kaina na kasa magana. Ya ajiye cup din hannunsa ya bani dukkan attention dinsa yace "You know I can do anything for you, in dai bai sabawa addini ba, just say it and it will be done" a hankali na fara magana "daddy ba akai na bane" "OK, akan waye?" "Dama wani copper ne a makarantarmu" sai kuma nayi shiru "ina jinki" "dama wani copper ne a makarantar mu, to sun gama service dinsu wannan watan, to daddy mun saba dashi sosai kuma yana taimaka mana sosai, gashi soon zamu fara SSCE" na sake yin shiru kirjina yana bugawa, saboda is simple amma baya tolerating nonsense, bai ce komai ba amma ni yake kallo, naci gaba "daddy so nake yi ko zaka saka baki a bashi aiki a school din mu" yayi shiru yana cigaba da shan coffee dinsa, na daga kaina naga idonsa yana kaina, da alama studying dina yake yi. Can ya nisa yace "maimunatu shi copper din shi yace miki yana son aiki a school din ku?" Nayi sauri nace "eh daddy shi yace yana so" "kuma yace ki nema masa?" Na girgiza kaina, " yace dai yayi wa pc din mu magana in da akwai vacancy yana so" "then that's all, in suna da vacancy, in he is as good as you said he is, za su bashi ba sai nayi magana ba" nayi shiru kuma naki tashi daga durkushen da nake, daddy yace "menene qualifications dinsa?" Nayi sauri na zaro CV din Ibrahim dana boye a jikin rigata, daddy ya karba da mamaki a fuskarsa yace " How did you get his CV?" Nan fa ido na ya raina fa ta, idonsa har yanzu a kaina yake kuma ni kaina nasan nayi alamar rashin gaskiya. Ya sake tambaya "Maimunatu how did you get his CV?" Nace " He just mentioned it in class cewa yana neman aiki a school din mu, to rannan na ari book dinsa sai naga CV din a ciki shine nayi tunanin in kawo maka ko zaka taimaka masa" na fada bakina yana rawa, a nutse daddy yace min "you are lying" wani daci naji a cikin bakina, nan danan zuciyata ta fara bugawa a cikin makogwaro na. "What tribe is he?" A sanyaye nace "he is a Muslim dad" yace "OK, naji musulmine, what tribe is he" can kasan makoshina nace "yaroba" kalmar yaroban kamar wani garwashi naji ta a bakina. Daddy ya ninke takardar dana bashi ya ajiye sannan yace "Hafsat ta tashi?" Nace "a'a" yace " tashi ki tafi, in Hafsat ta tashk ki turo min ita" jiki a sanyaye na tashi na koma saman mu. Ina shiga toilet na shiga na rufe kaina, nan da nan hawayen da nake rikewa suka fara zuba. I was a fool to think I can fool daddy. Shikenan tawa ta kare, yanzu da Hafsat taje zai tambayeta ita kuma zata gaya masa gaskiya, shikenan mommy tana zuwa zai gaya mata ita kuma zata sakani a turmi da daka. Hafsat ce tayi knocking kofar tana jira na, na wanke fuskata na fito ina sussunne fuska. Tana kallona tace "kuka kuma da sassafen nan?" Nayi banza na rabu da ita. Sai da ta fito tana saka kaya na gaya mata kiran daddy, ta zura hijab dinta zata fita na sha gabanta nan da nan wani kukan ya taho min tace "lafiyar ki kuwa Moon?" Cikin kuka nace "Hafsat please, akan maganar Ibrahim daddy zai tambaye ki, dan Allah kar kice komai" tana kallona da mamaki tace "saboda me?" Tambayar ta ta bani mamaki nima, ban gane saboda me ba? Ita ai tasan saboda menene. Tacigaba da cewa "bakya ganin cewa it will be easier for you both in aka gayawa daddy in za'ayi yace eh in kuma baza'ayi ba yace a'a? The longer kuka jira the more painful it will be in aka hana ku aure, ni bazan ce da daddy komai ba, it is not my call, amma shawara ce nake baki" daga haka ta juya tayi tafiyar ta. Sam Hafsat bata gaya min yadda suka yi da daddy ba kuma shima bai ce min komai ba. Washegari muna breakfast daddy yace min "Moon na duba takardun copper din ku, naga yana da first class a maths kuma yana da experience a teaching, zan kira PC dinku in suna da vacancy zanyi endorsing dinsa" daga haka bai kuma cewa komai ba, Hafsat ta mintsine ni a bom bom nayi kara muka saka dariya muna godewa daddy. Mommy ta tsaya tana kallon mu tace "maganar me kuke yi ne?" Hafsat ce tayi mata bayani, mommy tace "ok, wanda kuke extra lessons dashi?" Nace mata "eh" tace "OK, Allah ya sanya alkhairi, adaiyi hankali, the youth of nowadays are not to be trusted" daddy ya kalleta yace "extra lessons kuma?" Nan mommy ta bashi labarin yadda suka yi da pc din mu. Daddy ya kallemu da serious face yace "I want the extra lessons to stop, in zai maku lesson yayi fixing kuyi a class da sauran dalibai, bana son any special treatment a tsakanin ku, da banyi niyyar ne ma masa aikin ba sai da Hafsat tace min shi ya roke ku a class akan duk wacce tasan baban ta zai iya samar masa aiki ta kai masa takardunsa" nayi sauri na kalli Hafsat ita kuma ta daga kafada. Har cikin raina banji dadin abinda Hafsat ta gayawa daddy ba, Ibrahim is a very proud person amma ta ce wai shi ya roke mu mu samar masa aiki. Daddy ya cigaba da cewa "zan taimaka masa ne saboda bana son in discouraging dinku akan taimako, amma no strings will be attached, shi yasa zance da pc din kar ta gaya masa baban ku ne, saboda bana son wani special something. Allah yayi muku albarka baki daya" muka ce amin. 


Kamar yadda al'adar makarantar mu take, duk second day na first term ake yin speech and prize giving. Wannan session din ma haka. Muna shiga hall na tuna cewa shekara guda kenan da haduwa ta da Ibrahim. Muka gaida su mommy muka zauna. Yana shigowa idona ya sauka akan sa, ya saka complete yaroba attire har wannan hular tasu. Ina binsa da kallo har ya zauna a side din baki. Muna ta karbar gift duk gift din da za'a bani sai na kalleshi shi kuma sai yayi min 👍 har aka tashi. Ban je gurinsa ba na wuce gurin su mommy muka basu gifts din mu suka tafi gida. Ina komawa hall din naga students sun zagaye shi ana ta tambayarsa me ya dawo dashi. Na tsaya daga gefe kawai ina kallonsa. Yana gani na ta taso ya kara so inda nake bakinsa har kunne. Sai kuma muka rasa abin cewa "you didn't call me" yace yana dan bata fuska, na rufe tawa fuskar nace "sorry". Muka sake yin shiru nace "ashe baka manta yau speech and prize giving ba" yace "I wouldn't miss it for the world, ko da kuwa da rarrafe zan taho" nayi dariya nace "thank You". Can ya sake cewa "I also wanted to tell you, principal din ku tace next week inzo interview, wai wani ambassador ne ya nema min aikin, bansan ko waye ba" na kirkiro mamakin karya nace "congratulations, amma naji dadi sosai" shima yace min "thank You " sannan yace "by the way, Happy Anniversary to Us" na saka hijab dina na rufe fuskata na tafi na bar shi a gurin. 


Episode Twenty one: Amira


Ibrahim ya kawo mana kaya babu lefi, kayan tea, biscuits, cosmetics da drinks. It must have cost him dukkan albashinsa. Yazo yayi interview din, kuma bayan wata daya aka aika masa da offer dinsa har ibadan. A week after that, ya tattaro ta dawo abuja. An bashi gida a staff quarters. Nan take ya fara siyayyar kayan gida, kusan komai ya saya sai ya gayamin ni kuma sai in gaya masa menene next abinda ya kamata ya saya. I wanted to help him with money amma nasan ba zai karba ba, kuma bama nason yasan financial status din family na. Farko sai aka bashi ss2 shi kuma ya dage lallai baya so shi ss3 yake so, a cewar sa ya saba damu tunda mu ya dauka sanda yana service. Sai da kyar suka bashi SS3 din, ranar bakinsa har kunne yana murna yazo yake gaya mana, sannan kuma an bashi sports master. Yanzu kam da yawa daga 'yan ajin mu sun san alaka ta da Ibrahim tunda sam yanzu baya boye abinda yake ranshi, ni ce dai nake dan ja da baya.A haka har muka yi hutun first term. A cikin hutun abubuwa da yawa sun faru, na farko Allah yayi wa baban Amira rasuwa. 


Asalin su Amira 'yan kano ne, baban ta babban mutum ne sosai, yana da manyan 'ya'ya a kano sai aiki ya mayar dashi Abuja, ita kuma uwargidansa tace sam ba zata koma Abuja da zama ba tunda ta tara iyali a kano. Nan 'yan'uwansa suka hada musu auren zumunci da maman Amira ya taho da ita Abuja. Amira ce kadai 'ya a tsakanin su tunda shekarunsa sunja sosai. Sam 'yan uwan Amira babu wanda ya damu da ita balle mahaifiyarta, dan haka sai mutuwar tayi musu zafi sosai. Maman Amira bata san komai na dukiyar baba ba sai gidan da suke ciki a abuja, duk harkokinsa da manyan 'ya'yansa yake yi. Matarsa ta kano ta dage lallai sai a sayar da gidan na Abuja a hada kudin da sauran dukiyar sa ta kano sannan a raba gadon. Ita kuma maman Amira bata son sayar da gidan saboda bata son tashi daga abuja tunda nan ta saba dashi, daga ita har Amira. Mommy ce tayi tsayin daka akan maganar tunda ita lawyer ce har sai da taga an bar musu gidan a matsayin gadonsu, bayan gidan kuwa babu abinda suka tsira dashi, hatta motar da maman take hawa sai da aka karbe. Maman Amira sec sch kadai tayi, dan haka babu zancen neman aiki, ga Amira ita ko sec din bata gama ba. Mommy ce ta biya wa Amira school fees na second and third term sannan ta biya mata kudin SSCE din da zamu yi nan bada jimawa ba. 


Muna komawa pc tayi taron Muslim students ta sanar mana cewa akwai musabaka da federal government take shiryawa, ance a bada daliba guda daya da zatayi representing din school din mu, dan haka mu zaba a tsakanin mu wa muke ganin zata iya. Nan take muka zabi Amira, kuma tace ta yarda zatayi, muna ta murna sai pc tace zata hada ta da malami guda daya wanda za su ke yin tilawa tare kafin likacin musabakar. Muka tashi daga taron muna ta yiwa amira murna. 


Da daddare after islamiyya sai Ibrahim yace da Amira ta tsaya yana son ganinta, inajin haka nasan shi akace yayi coaching dinta. Amira ta ja hannuna muka tsaya tare. Sai da aka gama tafiya sannan yazo yace mata "congratulations Amira, naji abin alkhairi, Allah ya bada sa'a" muka ce amin. Nan suka fara tsara yadda zasuke karatun ni kuma ina jinsu ina dan bada tawa shawarar. A karshe suka yanke shawarar zasu keyi daga magrib zuwa isha. Haka kuwa akayi, kullum in munyi sallar magrib sai Amira ta zauna a masallaci tare da Ibrahim har sai munzo sallah isha tukunna mu tafi ialamiyya tare. 


A bangare na kuma lokaci daya girma razo min, ni kaina bansan yaushe ba sai gani nayi kayana duk sunyi min kadan. Kirjina kullum kara chika yake haka hips dina, har saida nakai ga komawa aron kayan Hafsat ina sakawa ita kuma tace sam ba zata yiwu ba sai dai in aika gida akawo min wasu kayan. Ina aika wa kuwa sai ga kaya akwati guda duk size din Hafsat kuma dana saka sai naga duk sunyi min dai dai. Wata ranar sport muka saka sport wears kamar yadda muka saba muka fita. Ni dama basketball nake yi tun jss1 haka Ibrahim ma, duk ranar sport tare muke yi dashi kuma ya iya sosai saboda yana da tsaho. Ina zuwa na tarar dashi already a field da wadansu staff su biyu tare da students wadanda mostly 'yan kallo ne. Ban yi wata wata ba na shiga muka fara bugawa, amma sai na lura Ibrahim hankalinsa sam baya kam ball din, duk ya zama distracted, ya kasa scoring ko kwallo daya, gashi anaso ayi mana game, nan na tafi gurinsa da niyyar in tambayeshi mai yake damunsa sai na lura gaba daya ransa a bace yake. Ina zuwa kusa dashi sai kawai naga ya chire jacket din daya daura a kugunsa ya kama kokawar saka min, na kwace daga hannunsa cikin fada nace "what is wrong with you?" ya dora min jacket din akan kirjina yace "just go and play table tennis or snooker, ai ba sai lallai kinyi basketball din ba" raina naji ya fara baci, nace "saboda me? Kullum ba basketball din nake playing ba? Dan me yau zaka ce wai inje inyi snooker bayan kai ne ma kake bata mana game din" wani kallo da yayi wa kirjina yasa naji kafafuwana duk sun sage, kallon kawai yayi min na gane ma'anar me yake nufi, wata kunya ce naji kamar zan narke a gurin. Bai ce min komai ba ya juya ya bar field din. Daga baya na naji wasu sababbin coppers suna cewa "wannan Ibrahim din dan bakin ciki ne wallahi" wani hawayen takaici naji yana taho min, nayi sauri na mayar dashi. Da sauri sauri na zura jacket din Ibrahim na bar gurin. Ina jin wata tana kwalla min kira na rabu da ita. Can kasan wata bishiya na hango hafsat tana zaune akan kujera da novel a hannunta tana karantawa, ta dora kafa daya kan daya. Itama sport wears din ne a jikin ta amma tayi rolling farin vail har saman kirjinta. Na tsaya a gabanta nace "why didn't you tell me?" Ta kalleni da rashin fahimta tace "tell you what?" Na zauna kusa da ita nace "ba za kiyi min fada kice kayan jikina are showing ba, kika barni na fito mutane suna kallona?" Dariya tayi ni kuma na kara kuluwa, sannan tace "kusan shekaru biyu da suka wuce na taba fada miki magana akan Ibrahim sai kika ce min you are old enough to make decisions for yourself, to dan me yanzu kuma zan yi miki magana, tunda you are not blind. Yanzu ai kin dauki darasi ko?" Na kara bata rai bance mata komai ba. Kamar daga sama naji yana cewa "barka da hutawa big sister" duk muka kalleshi Hafsat tana dariya tace "ni fa bana son big sister dinnan, sai inji duk tsufa ya kamani" suka yi dariyar su su kadai. Ya zauna kusa dani naja kujera ta na matsa yace min "am sorry, bai kamata inyi miki magana a cikin mutane ba, amma bazan iya hakura mutane suna kallonki ba" Hafsat tayi gyaran murya tace "Hello, ina nan fa" ya kalleta yace "in ba zaki tashi ba to ki toshe kunnuwanki" ni dai bance musu komai ba dan duk haushi suke bani. Tun daga ranar na koma saka dogon hijab irin na Hafsat, 'yan sport din mu kuwa tun suna nemana har suka hakura. 


Muna gab da fara SSCE Amira tace min sun daina karatu da Ibrahim. Na tambayeta dalili tace babu komai kawai tana ganin ta iya duk abinda ya kamata ta iya. Washe gari muna class aka kira ta a staff room, shiru shiru bata dawl ba sai na tashi na bi bayanta. A hanya muka hadu da ita. Abinda na gani a fuskarta ya bani tsoro, na tambayeta "Amira lafiya, ko a gida ne wani abu ya faru?" Wani kallo ta yi min wanda naji tamkar ta doka min guduma aka, cikin sarkewar murya tace "me kika biyo ni kiyi min kuma, nace na fasa karatun dashi ba shikenan ba? To yanzu na fasa musabakar ma gaba daya, kije kiyi na bar miki, besides you are the golden one ai, you are so perfect that you must have everything that you want. You can have him, you can have the musabaka and everything else" ta bangaje ni da kafadar ta ta wuce. Ni sam ban gabe ina maganganun Amira suka dosa ba dan ni a iya sanina banyi mata komai ba. Tana tafiya sai naga Ibrahim ya fito daga office din PC muka hada ido ya girgiza min kai alamar kar inyi magana ya tafi. 


Tunda muka shiga class Amira ta kifa kanta a desk take kuka, kowa ya tambayeta sai tace babu komai. Hafsat tace a rabu da ita, dama tun mutuwar babanta she has not being herself maybe mutuwar ta tuna. Ana tashi Ibrahim yazo ya kira ni ya tambayeni ko zan iya yin musabakar? Da mamaki nace masa "Amira fa" yace "tace ta fasa" na tambayeshi dalili yace bai sani ba. Muna zuwa hostel nayi wa Hafsat bayanin duk abinda ya faru. Tayi shiru sannan tace "Are u sure babu wani abun a tsakanin su?" Naji maganar ta kamar kibiya a zuciyata amma sai na maze nace "wani abu kamar me fa?" Ta kalleni da nutsuwa tace "Amira ba haka take ba, in har ta gaya miki wadannan maganganu to da akwai dalili, kuma they have been spending a lot of time together lately, maybe something happened".


Maganar Hafsat ta shige ni kuma nayi niyyar zan samu Ibrahim inji daga bakinsa. Dama yanzu mun daina lectures sai dai revisions ko kuma muyi ta tutorial. Dan haka muna zuwa class na tafi staff room na cewa Ibrahim ina son ganin sa. Mu ka fito tare muna tafiya, direct na tambayeshi nace "Me ya hada ka da Amira?" Ya tsaya yana kallona yace " bangane ba, wani abun tace nace mata" nan na fada masa duk maganganun da Amira ta gaya min, yayi shiru bai ce komai ba. Direct na sake tambayar sa "is Amira in love with you?" Yace da sauri "what?  Me yasa zaki fadi haka" na sake cewa "are you in love with Amira?" Da karfi yace "hell no!!" Nayi shiru saboda naga yana son yayi min ihu a cikin mutane. Sai da muka jima a tsaye muna kallon kallo sannan ya fara magana "OK, na jima da sanin cewa amira tana so na, tana dannewa saboda she is your friend, ni ma kuma ban taba nuna mata na sani ba, but I know the signs. Yanzu da muka fara karatu da ita sai ya fara zama worst har bata concentrating akan karatun sai dai tayi ta tambata things about me and other stuffs, to sai nayi suggesting cewa mu gayyato ki kizo muke yin karatun tare, shine taji haushi tace ta fasa karatun, na gaya wa pc kuma shine tace ta fasa musabakar gabadaya, sai dai ke kiyi tunda nace dake nake so muyi karatu" tun daya fara maganar nake sauraron shi ina jin wani daci yana taso min a baki na, ji nayi kamar in rufe shi da duka, amma dana kalleshi sai naga iyakacin gaskiyarsa yake fada min. Na juya da sauri zan bar gurin ya kamo hannuna, wani mugun kallo na jefa masa nan da nan ya sake ni nayi gaba. Ina jinsa yace "maimunatu 🙏please "


Post a Comment

0 Comments