mahaukaci hausa novels

 


👄👄👄👄👄👄

 *Mahaukaci*

💋💋💋💋💋💋

By maman noorul hudah


Wanan labari kagagen labari ne banyi shi Dan cin zarafin kowa ba 


Ban Yarda wani ko wata ta juya min labari ba ta ko wace tsiga

Please a Fara daga farko bana son sai nayi nisa mu takura juna,duk group din da ba a comment zan daina posting 


Gabad'aya wanan littafin sadaukarwa ce ga ya'ta *Rahmat* (Nazeera)Allah ya albarkaci rayuwarki ya rayaki ya kare ki daga sharrin makiya (Amin)


🅿1⃣-2️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim..



Yau ma Kamar kullum  Suna fitowa ya taso da sauri yayi ta binsu,ummi sai matsifa takeyi tace" nazeera ke Kika Saba me toh gashidai sai binmu yake nidai wanan abin ya fara isata a ce mahaukaci yayi ta bibiyar mu,gaskiya ni na kusan daina tafiya dake wallahi"sai fad'a take kamar me magana da kanwarta bazaka tab'a tunanin yayarta bace nazeera 


Itadai wacce aka Kira da Nazeera batayi magana ba saima juyawa da tayi ta kalleshi 


Kallonshi nayi da kyau sai na gan wando shadda ne jikinshi milk colour ya Sha datti sai wani Jan t-shirt da wuyar ya yage,miyau ne ke siyaya a bakin shi infact he is the real definition of an inbecile,kallonta yake Yana murmushi bakinshi a gefe 


Nazeera ta sakarme murmushi tace"ka koma gida sauri Nike zanje makaranta na makara"


Make kafada yayi alamun ah'ah,kafin Nazeera tayi magana ummi tace"nidai na tafi sai ki tsaya kiyi ta shashanci da wanan mahaukacin dama Abba zai bi shawarata ne da ya had'aki aure Dashi tunda kin rasa mashishini,Haka za a Kare ba saurayin kwarai sai kame-kame"


Dukda maganarta ya d'an sosawa Nazeera rai be hanata murmushi ba cikin sanyi irin nata tace"please ummi ki tafi ba sai kin jirani ba"


A fusace ummi daje sanye cikin uniform din government day  tace"ai dama ko Baki ce ba tafiyata zanyi in badan abba da ya nace muyi ta tafiya tare ba ni me zai kaini tafiya da Mai bakin jini irinki salon a shafa min bakin jini"


Nazeera ta kalleta kawai sai tayi murmushi ta Mika mata d'ari biyun da Abba ya Basu tace"gashi je malam idi yayi Mana canji ki kawo min d'ari"


Fisgewa ummi tayi ta ja saki ta tafi sai gata ta dawo ta wurgawa Nazeera hamsin ta ja saki ta wuce nazeera ta bita da kallo 


Mayar da kallonta tayi kanshi tace"boy kayi hakuri in naje na dawo zamuyi hira sosai,wallahi Ina da test"


Juya mata baya yayi alamun fushi ta dawo gabanshi tace"boy please da wuri Zan dawo inshaallah dama akwai Wanda Mukayi dashi zai zo zance in na dawo Zan baka labari"tana Gama magana ta juya zata wuce sai ta gan Yana binta 


Juyawa tayi ta kalleshi  tace"boy yanzu baka jin magana nace in na dawo  zamuyi magana"


Da k'yar ya bude bakin shi dake zubar miyau abin kyama yace"yun-yun-yunwa Ni----nike ji"


Hamsin hanunta ta bashi tace"gashi je wajen malam idi ka siya biscuit in na dawo yau zan dafa maka taliya"


Dariya yayi cikin irin maganar su ta inbecile yana Susa Suman kanshi ga fuskar nan baki "yak" so iritating yace"toh sai kin dawo"


Da sauri ta Karasa bakin hanya ta shige keke napep Yana ganin shigan ta ya kalli naira hamsin Yana Susa kai kawai sai yayi murmushi ya karasa shagon malam idi Yana fidda yawun kazanta 


Tana kaiwa school ta tarar har an shige an Fara test ga lecturer ya kulle kofa,wani fad'iwar gaba ta ji domin dama ita da lecturer sai a hankali niman dalili yake yayi failing dinta,cikin karfin hali ta tura kofar ta shiga gabanta na fadiwa 


Malam Ali na Jin an bude kofa ya juyo,wani Dadi ya ji ganin itace,a zahiri ko had'e rai yayi ya duba wrist watch dinshi sanan ya mayar da kallonshi kanta kafin yayi magana tace"iam very sorry sir wallahi wani uzuri ne ya rike ni  kayi hakuri ka Bari in rubuta Koda five minute ne ya rage"


Wani kallo yayi mata yace"before the count of 3 kin bar ajin Nan"dukawa zatayi ya daka mata wani tsawa yace"na ce ki fita"


Jiki na rawa ta fita ta samu wuri ta zauna takaici ya dibeta kawai sai ta fashe da kuka ita tasan tsayawa da tayi da boy ne yasa ta makara yanzu ya zatayi?she can't afford to fail his course 


Haka tana ji tana gani aka fara fitowa d'aya bayan d'aya har aka gama Bata motsa daga inda take zaune ba 


Yana fitowa da papers din a hanunshi ba tare da ya kalleta ba yace


Maman Nur 


Coming soon sai na gan comment👄👄👄👄👄👄

*Mahaukaci*

💋💋💋💋💋💋

By maman noorul 

Hudah


🅿3️⃣-4️⃣ 


Bismillahir Rahmanir Rahim 


Bin shi da kallo Nazeera tayi Tana goge hawaye,sai ga serah ta fito a aji karasawa tayi cikin damuwa tace"nazy ya Kika makara ne yau gashi kinyi missing test Kuma ke kanki kin San ba Imani ne  dashi ba tun 6:30 fa Nike makaranta Nan dan bana son in shiga hanunshi "


Kuka Nazeera ta fashe dashi tace"serah bazaki gane ba, the thought of failing course dinshi kadai yana sa zuciyata bugawa wallahi bana son in samu carryover balle a course dinshi sanin kankine typewriter yafi ko wani course a department din Nan kawo marking saboda credit unit din and in nayi failing point dina zaiyi low,I really work hard for this course jiya banyi banci ba"


Serah tace"but meya tsayar dake har Kika makara haka,Koda yike nasan bazai wuci wanan Mahaukanci ne yasa Kika makar......"


Katseta Nazeera tayi ta mike tace"serah bafa mahaukaci bane please ki daina ce me mahaukaci Lalura ce"


Serah ta tabe baki tace"iam not in the mood da zanyi argument dake yanzu dai kije office din malam Ali ki rokeshi nasan zai  Baki test d'inki"


Kallonta nazeera tayi tana goge hawayenta tace"kin san fa halinshi mutumin banza ne kin San inda Muka Kare last time wallahi har ban so mu sake kebewa"


Serah tace"kije kiji ko zai hakura  ki roke shi kin san ko ya yafe Miki,karki Bari kiyi carrying over din course din Nan"


Nazeera tace"muje ki rakani"


Serah tace"toh but a waje zan jiraki"


Suna zuwa gaban office din malam Ali Babu inda nazeera batayi da ita ba su shiga tare ta ki"


Nazeera ta shiga gabanta na fad'awa tana shiga ta ganshi zaune yana making 


Sungunawa tayi har kasa d'an nesa dashi tace"sir ka dubi girman Allah ka bani nawa test din ni ko anan zan rubuta please"


Murmushi yayi ya dawo da glass dinshi saman hanci ya mike ya karasa inda take da sauri ta matsa baya tana rarrafawa 


Dafa kafadarta yayi yace"no baby ni ba dodo bane meyasa kike guduna?"d'agata yayi Yana kallon kwayar idonta yace"baby meyasa kike wahalal da kanki kin San fa abinda Nike so ko anan ma ai sai muyi and I assure you zakiyi passing course dina infact Babu me failing dinki a makaranta Nan daga department din nan har education,gse,duk Zan tsaya Miki only in Zaki bani kanki kin San fa na dade Ina sha'awarki tun 100level Nike bibiyar ki"


Kuka ne ya kubcewa nazeera ta fara rokonshi Amma sai ya rungumeta yana shafa Mata baya


Da sauri ta  janye jikinta zatayi magana ya jawota ya had'e bakin su sosai nazeera ke kokuwar kwatan kanta Amma ta kasa kuka take sosai 


Ganin ya fara d'aga Mata riga ta tureshi da karfin tsiya tana wani irin kuka jikinta na rawa da gudu ta bar office din 


Tana fita ko  ta kan serah Bata bi ba ta bar makaranta serah na kiranta bata kula ta ba ta shige napep 


Tunda ta shige keke kuka take kamar ranta zai fita ba a tab'a Yi Mata abinda ya tsaya Mata a rai irin yau ba 


Tun daga nisa ta hango boy Yana wasa da wasu yara suna me Waka 


Tsaki tayi domin wani haushin shi take ji Yana ganin ta ya fara gudu Kamar zai Fadi ya


Maman Nur

👄👄👄👄👄👄

*Mahaukaci*

💋💋💋💋💋💋

By maman noorul 

Hudah


Godiya Mai tarin yawa masoyana nagode da kaunar ku 


Ummina har naji kunya da kikayi magana d'azu,shiyasa nace Bari I d'an kokarta inyi typing yau,wanan page din naki ne ummina hajiya *Aisha D'an goguwa* Ina Miki fatan alkhari 


🅿5⃣-6⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Yana zuwa gabanta ya fara kokarin karb'an Jakarta kamar kullum ba tare da ta kalleshi ba tace"barshi kawai tafi kaje kayi wasan ka"


Buga Kafa ya farayi alamun dai be Yarda ba"


Tace"je kayi Wasa please"


Kama hanunta yayi yasa a hammata ya danne


Janyewa tayi,ya je da niyyar zai kamo ta daka me wani mugun tsawa da ya firgita shi 


Tace"nace bana so Dole ne daga yau karka Kara zuwa inda Nike in ba haka ba wallahi zan mugun sab'a maka haka kullum kakeyi gashi kasa na makara nayi missing test"


Kallonta yake da mamaki yana kokarin yin magana abin ya gagara 


Tsaki tayi ta shige gida 


Tana shiga umma ta kalleta da mamaki ganin yau ta dawo da wuri 


Mama na ganinta ta kwashe da dariya tace"Ashe dai shiyasa na gan duhu me bakin jini ta shigo gida hasken ya d'auke 


Lami tace"hmmm ni kullum Cikin sa Ido Nike ko zan ji anyi sallama da ita amma shiru kullum dai cikin cewa ake lokaci ne ko yaushe lokacin zai zo oho?"


Mama ta kwashe da dariya tace"kila sai mun mutu"


Maryam ta fito tace"akwai Wanda ya Kai ku bakin jini tunda har kuka Kare a gidan nan,ai karuwanci daban farin jini daban ya'yan ku da kullum iskanci ake dasu a lunguna ko kun d'au bamu San komai bane kyale ku muke"


Mama ta mike tace"ke ban san rashin kunya karki nimi ki gaya min magana"


Maryam zatayi magana umma ta daka mata tsawa dama tuni nazeera ta shige d'anki ta zauna tayi tagumi 


Umma ta kamo hanun Maryam Suka shige 



Kallonta umma tayi tace"meya same ki na ganki a sanyaye?"


Murmushi yake tayi tace"ba komai"


Umma tace"ko kin samu matsala ne a makaranta?"


Tace"ah'ah"


Umma tace"toh Allah ya kyauta,ga wanan je shagon malam idi ki amso min Maggi in na aiki Maryam tsayawa zatayi tana fad'a dasu"


Amsar kudin tayi tasa hijab ta fita,tana fitowa ta gan boy a kofar gidansu yayi tagumi suna had'a ido tayi saurin daukewa taje ta siyo Maggi tana juyowa ta gan ya takure wuri d'aya sai ya bata tausayi ta koma shago ta amshi bashin taliya ta shige gida 


Tana shiga ta hura abacha ta fara jajjagen kayan Miya 


Da misalin 12:03 ta fito da kulan abinci karami ta ganshi a inda ta barshi d'azu 


Yana ganin tana tunkaroshi ya mike da sauri ya karasa ya rungumeta gam 


Tsayawa tayi na d'an lokaci Kamar me nazari domin wani kamshi ne ya bugi hancinta Mai dadi 


Da k'yar ta janye jikinta tana kallon kwayar idonshi shima nata yake kallo 


Murmushi tayi ta Kama kasar hijabinta tana goge me miyau tace"boy  nace ka daina zubar da miyau nan bana son kazanta"ta Kare magana da share me baki


Cikin damuwa yace"me---meeeee nayi Miki d'azu"Wanda in ba kasa kunin ka ba bazaka ji me yake Fadi ba"


Zama tayi a dakali ta bude kula tace"zauna Mana?"


Zama yayi ta Mika me kula  tace"iam sorry boy please forgive me raina ne ya b'ace shiyasa"


Taliyar ya Kai baki sai yaji wani uban yaji kwata-kwata taliyar beyi me ba 


Murmushi tayi ganin Yana juyawa tace"ci mana boy"


Murmushin yake yayi ya Kai baki ji yake Kamar ya dawo dashi"rufe kulan yayi yace"sai kin fad'an min abinda  ya faru dake"yayi maganar inda imbecile keyi 


Kuka ta fashe dashi tace"boy nayi missing test dina,kuma wanan d'an iskan lecturer ya...ya"kuka ne ya ci karfin shi da yasa hankalin shi tashi 


Besan lokacin da yace"me yayi Miki ba?"


Kallonshi tayi tana kuka tana goge hawayenta tuni idanunshi suka sauya kala 


 A fusace yace"me yayi miki?"yayi magana cikin d'aga murya


Kallonshi tayi tace"boy"sai yayi saurin komawa inda yake magana yace"mmmme yayi Miki?"


Tace"he kiss me,can you imagine that bastard kiss me "labarin komai ta bashi  tace"nasan ba lalle ka fahimceni ba tunda bakayi makarnta but bana son inyi failing course din"ta Kare magana da bude  sabon kuka"


Dafa ta yayi Amma beyi magana ba,murmushi yake tayi tace"sorry Ina damun ka da matsalata,Bari in baka wani good news,hmmm saurayin dana had'u dashi jiya a hanyar islamiya yace"yau zai zo zance da karfe 8:30 iam so happy today ka gan nima zanyi aure in huta da gorin yan gidanmu boy kowa cewa yake Ina da bakin jini kuma gaskiya ne har yanzu ban samu Mai Sona bane tsakani da Allah Amma ai ba  laifina bane ko boy duk samarin da Nike had'uwa dasu yan iska ne Amma sai ayi ta cewa Ina da bakin jini,Allah yasa wanan yayi serious"kallonshi tayi ganin yayi shiru yasa ta cewa"but boy bazaka min abinda kayi last time ba ko?infact ka nuna baka Sanni ba nasan Zaka so Nima inyi aure ko?"


 girgiza mata Kai yayi ta mike tace"yauwa my boy bari inje inyi Shirin islamiya"Bata jira amsarshi ba ta shige cikin gida tana shiga mama ta kwashe da dariya  tace"ko dai mahaukaci za a aura tunda masu hankali gudunki suke"


Itadai Batayi magana ba ta shige ciki 


Umma ta kalleta fuska d'aure tace"ke miye had'in ki da wanan mahaukacin?"


Tace"lah umma bafa mahaukaci bane?"


Umma tace"koma menene ki fita harkar shi,Kuma ki fito da miji domin Abba ku ya fara takura ni kema  kanki kin San Babu wata ya' a gidan Nan da tayi shekarun ki ba ayi mata aure ba asalima da an gama jss3 yake aurar da ya'yanshi "


Nazeera tace"Kai umma in Kuna fadin shekarun nan sai a d'au ko nayi arba'in dudu fa shekaruna ashirine fa"


Umma tace"nidai ba ruwana na gaji da kare ki dama dan kiyi karatune kuma ba laifi yanzu Zaki iya karasawa a gidan miji In akwai Wanda kike so sai kiyi magana"


D'aukar jaka tayi tace"umma sai mun dawo dama tuni Maryam ta fita tana fad'awa mama magana"


_____________


Saukowa take akan stairs cikin takun kasaita kallo d'aya zaka mata kasan naira ta zauna,kyawun gidan kawai ya Isa yasa mutum natsuwa domin naira yayi kuka 


Zama tayi ta kira kande Mai aikinta ,da gudu ta zo ta duka 


Hajiya turai ta kalleta tace"zuwa anjima zanyi Baki daga kano please ki fad'awa masu girki su girka Mana tuwon shinkafa miyan egusi sanan suyi white rice kad'an da Miya"


Kande tace"toh hajiya"


Salim ne ya sauko daga part dinshi yana zuwa ya kwanta jikinta tace"Kai nidai wata rana zaka karyani wallahi"


Yace"Kai mummy nifa bani da wani nauyi"


Tace"salim kunyi waya da nazir kuwa?"


Yace 


Maman Nur

[👄👄👄👄👄👄

*Mahaukaci*

💋💋💋💋💋💋

By maman noorul 

Hudah

🅿9⃣-1⃣0️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Ta kwashe dadduma ta nade sanan ta fita,tace"abba gani"


Yace"biyo ni falo"


Binshi tayi harda su umma 


Cike falonshi yake da yara kowa na gidan na ciki 


Kallon nazeera yayi yace"ke meya had'aki da ummita"

Nazeera ta fad'a me 


Kallon Maryam yayi yace"kefa me tayi Miki Kika Yi mata wanan dukar harda ciwo"


Maryam tayi shiru ta share shi a fusace yace ba dake nike ba?"


Maryam ta turo Baki tana gunguni kasa-kasa kafin tace"toh Abba ai itace ta zage yaya nazeera tana ta fad'a Mata magana harda ce Mata me bakin jini"


Dakuwa yayi Mata yace"karya tayi?inda a ce ta Kama kanta da yanzu tana gidan miji Ina zasu ganta har su rainata kanneta biyar  duk suna gidan miji,nidai gaskiya ya'yan Rabi Basu da farin jini,sun zauna sai ci min abinci suke gashi tayi tsada suyi aure Mana in huta"


Mama ta karbe zancen da cewa"wallahi daga uwarsu ne nidai alhaji ka ja musu kunnin Kar shegiyar da ta Kara tab'a min ya'ya in ba haka ba za ayi karamin yaki a gidan Nan nidai nayi shiru ne d'azu in ba haka ba da a gadon asibiti zaka dawo ka same su"


Lami tayi wani murmushi tace"kenan dama taki aure ne dan tayi ta haddasa Mana fitina a gidan"


Ummi ta fashe da kuka tace"Abba tun safe take ta tsokana ta harda Marina tayi akan wanan mahaukacin"


Abba yace"sati biyu na baki kacal ki fidda miji in ba haka Zan had'aki da wanan mahaukacin da Kika nacewa"


Nazeera tace"Abba har yanzu Babu Wanda Nike dashi Dan Allah Abba a Kara min lokaci"


A fusace yace"toh ba anan gidan ba domin kece ta farko da Kika Fara karya min doka ni yarana a shekaru Sha biyar Nike musu aure dan haka in Karin  lokacin kike bukata toh saidai ki nimi gidan wani uban,ki fito da miji domin dasu ummi za a had'a aurenku da mardiya"


Umma dai bata ce komai ba sai ma tashi da tayi tace"alhaji Saida safe"wani haushine ya cika Maryam ganin umma bata kwatar musu yanci 


Lami tayi wani irin gud'a tace"alhaji ni da zaka bi nawa da an had'ata da wanan mahaukacin na lura tana sonshi,shima haka" 


Mikewa Abba yayi yace"Bari dai a Bata lokaci"fita yayi ya bar musu falon 


Nazeera ta mike jiki ba kwari domin dariya suke mata,ji tayi anyi sallama yaron yace" ana sallama da nazeera "


Kallon juna mama da lami sukayi lami tayi gud'a tace"yau dai an Kafa tarihi"


Maryam ta hararesu tace"je ka ce tana zuwa"suna fita mama ta kalli lami tace"sallama  da nazeera toh akwai matsala?"


Lami tace"baki ji inda gabana ya fadi bane Amma Dana tuna maganar boka sai na ji hankalina ya kwanta ai cewa yayi bakin jinin da yasa Mata bana Wasa bane duk saurayin da zaizo gunta guduwa zaiyi"


Mama tace"hakane fa,nidai na tsane Yariyar Nan tunda boka yace"tafi duk yaran gidan Nan taurari naji tsananta"


Lami tace"Niko tsanar uwarta ne ya Koma kanta ku duba fa ki wata uku banyi da auren alhaji ba ya auro uwarta in baki manta ba ba karamin wulakanta mu yayi ta Mana ba ai ban tab'a mancewa,Kuma Baki ganinta kamar aljana duk tafi ya'yan gidan Nan kyau ni gaskiya bazan ma Bari Rabi ta gan Abu me kyau ba da yarda Allah yaran duk kwantai zasu Yi muna Nan"


Mama tace"ke koni ai wallahi babban burina in gan ta auri wanan mahaukacin nidai kawai so Nike in gan Rabi ta tozarta a idon duniya tunda har a sanadinta alhaji yayi min saki biyu   muna Nan inda har Ina Raye toh nazeera da Maryam bazasu tab'a ganin dai-dai ba"


Lami tace"ke ummi je ki Sa Mana Ido akansu"


Mikewa tayi tace"toh" 


Su Maryam ko Komawa sukayi d'akin ummasu suka tarar da Yaya Ahmad zaune Yana cin abinci


Maryam tace"Yaya ka gan Abba ko?sai yayi ta zagin mu Kuma umma bazatayi magana ba 


Yayi murmushi yace"ai kece me jawo maganan da Baki tankata ba da hakan be faru ba dole hakuri zamuyi da Abba tunda babu adalci a lamarin shi ku dai ku dage kuyi karatu"


Tace"toh"


Nazeera ta zauna gaban madubi ta shafa farar hoda da man baki sai perfume da ta fesa domin dama tayi wanka"


Tace"umma yanzu Zan dawo"


Tace"ki dawo da wuri"


Tace"toh"


Yaya Ahmad yace"Allah yasa ku dai-daita kema ki huta da kanana maganganu"


Tayi murmushi tana fitowa ta gan boy zaune a inda ya Saba zama kallo d'aya tayi me ta d'auke Kai 


Wani murmushi yayi ya tabe baki  karasawa tayi gaban motar Habib ta jingina 


Sauke glass yayi yace"shigo mana"


Tace"no fito mu zauna a Nan "


Murmushi habib yayi ya bude motar ya fito ya zauna a dakalin kofar gidan,itama Zama tayi cikin Jin kunya tace ina yini"


Yace"lafiya Lau ya gida?"


Yace"lafiya Lau"


Shiru ne ya d'an biyo baya na d'an lokaci  kafin Habib yace"ba sai na b'ata lokaci ba domin ni  straight forward person ne ni  bada Wasa na zo ba aure Nike so da gaggawa"


Nazeera zatayi magana kawai ta gan mutum a kanta kamar an jeho shi kafin tayi wani abu boy ya 


Maman Nur

[9: 👄👄👄👄👄👄

*Mahaukaci*

💋💋💋💋💋💋

By maman noorul 

Hudah


🅿7⃣-8⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Yace"mummy Nima fa tun last week rabon da muyi magana"


Mummy ta d'auki wayarta tana latsawa tace"I don't know what this boy is upto a kwanakin nan daga nayi me maganar aure shikenan,Amma muje zuwa"


Salim yayi murmushi yace"kunfi kusa daya dawo yanzu Zaki manta ni"


Tace"Kuma fa ko gidansu hanan Dana tura shi be je ba"


Salim ya tashi ya zauna yace"mummy kema kin san Yaya nazir ba zai tab'a Yarda da arrange marriage ba why are you stressing yourself?" 


Tace"what do you expect me to do?ya ki yin aure dole inyi wani abu akai"Kai waya tayi kunni tace"number shi be shiga "


Salim yace"mummy please chill duk inda yake nasan kina  ranshi kila aikin ne ya rike shi kin San ai he is always busy"

 

Tace"Allah yasa dai lafiya domin nazeer baya kwana biyu be Kirani ba"


______________


Da misalin karfe 6:pm nazeera ce da Maryam suna dawowa islamiya Maryam sai surutu take tace"wallahi anty ke kike musu shiru shiyasa suke rainaki"


Nazeera cikin sanyi muryarta tace"Maryam miye amfanin tashin hankali bayan kin san Abba ba goyon bayan mu zaiyi  ba saima jawowa umma magana da zamuyi,please ki daina biye su"


Maryam ta tabe baki tace"sai dai in Basu shiga harkata ba wallahi yan rainin hankali kawai"


Suna kaiwa gida nazeera ta tube hijabi ta kwashi wanke-wanke ta Kai inda suke wankewa,ummi ce ta fito  da kwano a hanun tana zuwa tayi wurgi dashi har ya sami nazeera a Kafa 


Kallonta nazeera tayi sai ta girgiza kai ummi tace"toh miye ko kina da abinyi ne,ai tunda kin  ki aure dole kiyiwa kanne ki bauta"


Nazeera Bata kulata ba saima cigaba da tayi da aikinta,ji kake passs Maryam ta d'auke ummi da mari tace"kina hauka ne ko giya Kika Sha ko Kuma kanki hayaki yake anty nazeera kike fad'awa magana?


 Ummi ta Kai hannu zata rama Maryam ta Kama hanun ta ture ta sai gata cikin robar omo har ya fashe kuka ta fashe dashi ta taso ta tunkari Maryam gadan-gadan tuni dambe ya b'arke tsakaninsu,nazeera ta fara kokarin rabasu amma Ina Maryam tawa ummi jina-jina 


Mama ce ta fito jin kukan ummi tana fitowa ta Kama Maryam ta fara duka,nazeera ta rasa me zatayi kawai sai ta fashe da kuka 


Umma ta zo da gudu jin kukan nazeera sai ta gan mama na bugun Maryam ranta ne yayi mugun b'aci ta jawo mama ta wurgata gefe ta Fadi kasa 


Ta Nuna ta da yatsa tace"duk randa Kika Kara dukan min yara wallahi sai na baki mamaki"


Mama ta mike ta Kama hanun ummi ta shige d'akinta ranta na tafarfasa jira kawai take Abba ya dawo 


Nazeera ta kalli maryam tace"kin gan abinda Kika jawo ko in Abba ya dawo mun shiga uku"


Umma ta Kama kunnin Maryam ta jata d'anki 


Nazeera ta koma ta cigaba da aikinta 


Da misalin 7:40 nazeera na zaune saman dadduma bayan ta gama sallah ta ji muryar Abba na zazzage matsifa 


Gabanta ne ya Fadi sai ta ji yace"Ina Rahmatun take?"


Tashi tayi ta 


Maman nur

[9/: 👄👄👄👄👄👄

*Mahaukaci*

💋💋💋💋💋💋

By maman noorul 

Hudah


Masu bukatar karanta paid novel dina Kamar su


Nida mijina 200

Kauna ce 200

Mai Mata biyu 200

Nida Yaya hydar 200

So makaho ne 200

Habib Mr neat 200

Mu kawaye ne 300

Yarima annur 300

Ni'imatu 300 Mai bukata yayi min magana ta wanan number 09090112846


🅿1⃣1⃣-1⃣2️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Boy ya zauna a cinyarta ya rungumeta wani Kara ta saki domin taji zafi shiko Habib ya d'an ja baya da mamaki Yake kallonsu 


Nazeera ta tureshi cikin rudewa tace"innalillahi wa Inna ilahir rajiun"


Mikewa Habib yayi rai b'ace yace"dama Ashe baki da kamun kai?haka halinki yake tirr da budurwa da Bata da kamun Kai"


Nazeera ta mike bayan ta tura boy gaban Habib taje tace"Habib dan Allah kayi hakuri please wallahi ba haka Nike ba ka duba shi da kyau bashi da lafiya fa,karka hukunta ni akan laifin da ban aikata ba, please ka kalleshi kawai Ina tausayinshi ne Amma Babu komai tsakanina dashi please,boy ka fad'a me Mana "


Kallonshi Habib yayi  sai ya gan ya hade rai 


Nazeera zatayi magana boy ya karaso ya rungumeta gam ya fara Mata kiss,tuni jikinta ya fara karkarwa,Habib na ganin haka yayi tsaki ya shige mota ya ja ya bar wajen 


Boy na ganin ya wuce ya sake nazeera ya fara tafi Yana dariya


Wani kallon tayi me,kawai sai ta zauna ta fashe da kukan takaici tana cewa"boy ka kasheni wallahi, ka cuce ni Wai meyasa ma na yarda mukayi irin wanan shakuwar?meyasa Nike tausaya maka?a gaskiya yau kayi min abinda bazan tab'a yafe maka ba, boy you keep chasing  away my suitors this is the  fifth time wallahi bazan yafe maka ba daga yau bani ba kai  sanda na roke ka pretend as if you don't know but no you disgrace and make a fool out of me in front of him now tell yaushe zai yarda ya aure ni bayan abinda  kayi min?"


Wani kallon yake Mata da ta rasa gane kanshi hakan ya Kara b'ata Mata rai ta Kama hanunshi ta dinga janshi har inda ya Saba zama ta kalleshi tace"as from today karka Kara nuna ka sanni tunda kayi San ranka, na yau ma is worst you kiss me why me na tab'a maka a rayuwa da baka son  inyi aure kullum Cikin yi min gori ake ka San komai but instead of you  to help me shine kake tarwatsa ni,I didn't expect this from you Ina tausayin ka kullum Ina kyautata maka Amma abinda zaka saka min dashi kenan?"kuka ne ya ci karfinta harda sheshsheka


Kallonta yake Kamar tv ko a jikinshi wallahi sai ma d'aga Mata hanci da yakeyi ga hura Mata hanci


Kuka tayi me isarta kafin ta Kara dunkulewa ta had'e Kai da guiwa


Ji tayi yace"inaaa Jin yunnn....wa"


A fusace ta mike tace"toh Ina ruwana Nice mahaifiyarka in kana Jin yunwa toh kaje gidan ku Mana ka ci abinci xaka wani zo ka takurani daga yau in ka Kara nunawa ka sanni wallahi sai nayi Shari'a da Kai mugu kawai shiyasa ake ce maka mahaukaci toh in ba mahaukaci ba waye zaiyi abinda kayi toh yunwa ta kashe ka mugu me bakin Hali inda fuskar ka take baki haka zuciyarka take,mugu  kawai"


Kura Mata Ido yayi Yana kallonta domin yau ne ya gan fushinta ya Sha kure ta Amma sai ta ki kulashi,kenan tafi son Habib din kenan?"


A fusace tace"daina kallona me bakin Hali kawai"tana Gama magana ta juya ta shige gida ya bita da kallo 


Murmushi yayi sai ga wata bakar mota tintec glass ta zo ta wuce bin motar yayi da kallo kafin ya bi bayan alhaji muktari


___________

Duk abinda akayi a idon ummi daga farko har karshe komawa tayi ta bawa su mama labari suna ta dariya 


Mama tace"shima ya tafi kenan inshaallah bazai dawo ba"


Nazeera na komawa ta kwanta duk inda maryam ta so ta Bata labarin abinda ya faru tsakanin su da habib abin gagara yayi saima kwantawa da tayi ta cigaba da kukanta kasa-kasa daga Nan bacci me nauyi ya d'auketa 


Da misalin 10:30pm nazeer ne ya shigo falon a sace har zai shige part dinshi  yaji mummy tace 


Maman nur

[: 👄👄👄👄👄👄

*Mahaukaci*

💋💋💋💋💋💋

By maman noorul 

Hudah 


Ummi ce dole in baki page comment dinki na sani nishad'i nagode da kauna


🅿1⃣3️⃣-1⃣4️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Tace"daga ina?"juyawa yayi sai ya ganta jingine jikin kofa murmushi yayi Yana Susa Kai yace"mum bakiyi bacci ba"


Tace"ina kuwa tunda na auri yaro irinka ai bani da bacci"


Murmushi yayi ya karasa ya rungumeta yace"mum please Iam sorry  wallahi naje wani aiki ne"


Tace"nafa Fara gajiya da wanan aikin naka I mean  most you work?ga abbanka da business empire but kafi son kana wanan aikin na Fara gajiya fa eheee"


Yace"yi hakuri mummyna it my passion tun Ina yaro"


Tace"ya maganar gidansu hanan din'


Ya juya yace"mum it late zamuyi magana gobe"Shigewa yayi part dinshi ta bishi da kallo


Yana shiga ya Kira  Salim a waya yace"please in bakayi bacci ba ka sameni a part dina"


Salim da kallo yakeyi yace"ok"


Bayan minti biyar sai ga Salim ya shiga falon sai dai ba kowa ya tura kofar bedroom din sai ya ji karar ruwa a toilet komawa yayi falon ya zauna Yana jiranshi 


Yafi minti ashirin zaune kafin nazeer ya fito cikin jallabiya,Salim ya mike ya rungumeshi yace"munyi kewarka Yaya"


Nazeer yayi murmushi yace"Nima haka,Salim Ina son ka min bincike akan wani lecturer ne Mai suna  a college of education,school of vocational some thing malam Ali ka dai Yi bincike daga yanzu zuwa gobe"


Salim yayi murmushi yace"wani ya tab'o ka kenan ko?"


Yace"ka dai kayi abinda nace"


Salim yace",ok Mai sauki ne Ina da aboki lecturer a department din Bari in kirashi in be Yi bacci ba zai fàd'a mana"


Dialling number yayi bugu biyu ya d'auka 


Salim yace"ya dai baka kwanta ba?"


Jamil yace"no abokina Ina kallo ne kasan gwaro sai a slow"


Salim yace"please Ina son bayani ne akan wani lecturer malam Ali"wayar a speaker yake


Jamil yace"Kar dai ya tab'o na kusa daku domin mugun d'an iskane yana b'ata yaran mutane d'an iska ne"fad'a musu komai da suke son ji yayi sanan sukayi sallama 


Nazeer yace"gobe zaka rakani makaranta"


Yace"ok"


Washe gari Koda nazeera ta tashi fuskarta a kumbure,umma sai tambayar  abinda ya same ta tace"ba komai"


 Shiryawa tayi ta tafi makaranta ko da serah ta ganta kallo d'aya tayi Mata ta gane akwai matsala 


Tace"meya same ki?"


Kuka ta fashe dashi tace"serah boy ya cuceni,ya Kori Habib jiya,serah shikenan ni bazanyi aure ba kullum da samari sun zo sai su gudu ko wanne da dalilin dayasa yake guduwa na gaji gaskiya ga Abba ya matsamin "


Serah tace"miye yayi this time around?"labarin komai ta Bata 


Serah ta kyakyale da dariya tace"oh Ashe mahaukaci yasan kiss Amma bakiyi amai ba kin San wanan miyau Dole tayi wari,ba ke sarkin tausayi ba kad'an Kika gani"


Nazeera ta zauna a gaban ajinsu tayi tagumi serah tace"tashi muje cafeteria jare in ma be dawo ba toh ki d'auka dama can ba mijinki bane,nazeera karki damu komai na duniya lokacine you are still young ni ban San meyasa kike damuwa ba,in Habib na sonki zai dawo yanzu dai kiyi me text message ki ce ya zo yau ya Baki dama na karshe na tabbata zai zo ki rage damuwa Dan Allah bana son wanan desperation din sai ka ce wata wowo you are beautifull dear Zaki Sami mijin aure in lokaci yayi"


Nazeera tace"wallahi serah iam not desperate but my family are not understanding na gaji da halayensu gaskiya umma ta Bata ce komai ba but nasan deep down abin na damunta"


 Serah tace"don't worried muje cafeteria mu ci abinci yau na zo da kudi"


Nazeera ta mike tace"Wai baza ayi lecture bane Kuma?"


Serah tace"ya maidashi 4-6"


Nazeera tace"ki ce yau akwai zaman jira har 6:pm gaskiya be kyauta ba"suna tafiya suna hira wasu had'adun motoci uku ne  Suka shigo bakake wulik sai kyali sukeyi su nazeera Dake tafiya motar ya zo Kamar zai kwashesu  nazeera ta je guduwa ta Fadi a jikin notice board 


Serah ta kyakyale da dariya ta Mika Mata hannun ta taimaka Mata ta tashi tana mata sannu


Nazeera ta hade rai ta ji haushin dariyar da aka Mata 


Nazeer ya kalli driver yace"baka gani ne ko kana Shan giya ne?"


Driver yace"sorry sir"


Nazeer yace"fita ka Bata hakuri"


Fitowa yayi cikin polo me shegen kyau da tsada sai bakin jeans karasowa yayi inda suke yace"sorry Yan Mata a dinga kula please "


Driver yace"kiyi hakuri dan Allah ban lura bane"


Class rep dinsu  ne ya karaso inda suke yace"lah nazeer Abdallah da muke gani a tv ne yau a makaranta mu"


Serah ta zaro Ido tace"it's a lie karka ce min famous nazeer Abdallah the son of alhaji Abdallah Mai Riga bereau the change"


Class rep yace"ga zahiri kin ganni'


Tsaki nazeera tayi tace"Wai mun fasa zuwa cafeteria ne ban San wulakanci"


Murmushi yayi aka bishi da kallo Yan matan wurin suka ji Kamar dasu ne nazeera da yayiwa magana"


Suna zuwa cafeteria Suka zauna a happy resturant suka Fadi abinda suke so


Nazeera na cin white rice da aka kawo musu tace" na turawa habib text din be min reply ba har yanzu"


Tsaki serah tayi tace"ke Bari zancen wani Habib ga nazeer ke Baki lura da kallon da yake ta Miki bane wallahi na gan soyyayarki a kwayar idonshi"


Nazeera tace"are you ok?seriously I think something is wrong with you daga ganin mutum"


Serah zatayi magana sai ga spicy ladies sun shigo


Nazeera ta natsu jikinta na rawa domin tun a 100level take tsoron su kasancewa sun gagari kowa a makarantan ana tsoronsu 


Serah tayi kamar Bata gansu ba 


Feedy tace"ke je ki anso Mana abinci"


Nazeera ta tashi da wuri zata je,serah ta rike ta tace"ba inda zata je"


Feedy ta kalli su feena sanan tayi murmushi tace"keee kin San da Wanda kike magana kuwa ko kin manta spicy ladies ne"


Serah tace"Babu wani mantuwa is high time a taka muku birki haba kun addabe mutane"


Feena tace"yanzu tunda kin tare Mata ke Zaki je ki amso Mana abincin "


Serah tace"bazan je ba wallahi"


Feedy tace"kenan ko me akayi Mata Zaki tare Mata kenan"


Feena ta taso dama Haka kawai ta tsane nazeera tace"ok yanzu Zan mareta sai ki tare Mata"ta d'aga hanun zata kaiwa nazeera Mari serah ta Kama hanun tace"


Maman nur

👄👄👄👄👄👄

*Mahaukaci*

💋💋💋💋💋💋

By maman noorul 

Hudah


Ina masoyana masu nuna min kauna ta hanya patronizing littatfaina zuwa ga masu coplaining in bude permanent group da za ayi ta biya monthly dan wanan wahalal da sukeyi in nayi paid book,toh Ina son in sanar musu cewa na kawo wani sari,Zan bude group me suna *MAMAN NOORUL HUDAH HOME of novels* Wanda shigar shi dubu d'aya ne kacal duk wacce tayi register zata karanta paid book Dina guda hud'u kafin a sake sabon registration, kun gan anan ma kun samu discount din 200 kenan Kuma karku manta in nayi free baya cikin lissafi wanda ya biya daga next book da zanyi za a fara lissafi da fatan Hakan yayi muku 

Karku manta wanan shine contact dina ga Mai niman Karin bayani sai ku tuntubeni ta wanan number 09090112846 but yin haka ba dole bane Wanda beda karfi zai iya cigaba da biyan regular as usual domin har yanzu tsarin na nan

Nagode da kaunar ku


🅿1⃣7⃣-1⃣8⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Ta ajiye musu card na  invitation a tebu nazeera ta kalleta  


Feedy tace"wanan invitation na S U G award night da za ayi next week ne  muna son kuyi Mana inviting nazeer domin mun fad'awa president shine guest of honour,Ina fatan dai ba Wasa kukayi da hankalinmu ba"


Nazeera zatayi magana serah ta katseta da cewa"and in muka sa ya zo me zakiyi Mana in return?"


Tace"komiye"


Serah ta mike ta koma kan desk tace"zai zo but only on one condition"


Feena tace"miye condition din?"


Serah tayi murmushi tana kallon kumbanta tace"you guys will apologize to Rahmat in public kuma zaku bi command "


Feena ta kalli feedy Ruky tace"what?"


Dariya serah tayi tace"you heard me right ku je kuyi tunani"


Ruky tace"bamu Yarda ba wallahi"


Serah tace"ok sai ku koma ki ce musu guest din bazai zo ba"


Feedy tace"in be zo ba Kuma bafa me zamuyi muku???"


Nazeera tace"please kuyi hakuri wallahi k......"


Serah tace"Babu wani kunya Dan Allah ai party ne ke meyasa kin fiya jin kunya"nazeera ta rasa me zata ce ganin ta juya zancen 


Serah tace"ko miye ma kuyi"


Feedy tace"mun amince,ruky tace"feedy no karki yarda su bada wani condition ba wanan ba"


Feedy tace"let take the risk"


Serah tace'kuje in kunyi tunanin sai ku dawo"


Feedy tace"mun ma amince"


Ruky ta jata suka fita,suna barin wurin nazeera tace"serah why do you always invite troble miye na karya yanzu kin sani a problem ni nasan in be zo ba makarantan nan gagaran mu zaiyi,kin San spicy ladies dinan basu da Imani kin manta inda suka Zane rabi'u?"


Serah ta d'aga Mata hanun tace"let me think bawai kiyi ta interupting brain Dina ba,yanzu dai ya zamuyi ya zo?'


A fusace nazeera tace"ni kike tambaya ke dama da kikayi karya Baki San ya za ayi ba you better think, domin Ina son in Gama makaranta lafiya serah nidai kullum sani a magana kike d'azu haka Kika sa wanan d'an ji da Kai ya zageni"


Serah tayi tsaki tace"Kai kin fiya matsifa Bari inyi tunanin  domin  Tara muka shiga ba uku ba "


Nazeera tace"toh meyasa Baku ce musu saurayinki bane Kika laka min"


Serah zatayi magana sai ga malam Ali ya shigo harya zazzage ya d'an fad'a mikewa nazeera tayi tace"sir"


Ba tare da ya kalleta ba yace"Rahmat kiyi hakuri da abubuwan da suka faru a baya ki Kuma bashi hakuri wallahi na tuba karki bari a koreni a aiki Ina da family ga yara please"


Da mamaki nazeera ta kalleshi tace"sir meya faru ni ban San meke faruwa ba 


Beyi magana ba ya Bata question yace"ki amsa tambayoyin ki Aiko class rep dinku dashi"


Tace"nagode sir"


Serah tayi shiru ta bishi da kallo,a ranta tace"sir nazeer ya zo school dinmu yau and suddenly   malam Ali Ali is a change man,meke faruwa what the connection?my suspicious was right toh Amma waye ya fad'a me abinda ya faru tsakanin malam Ali da nazeera something is fishy,I will find out"


Kallon nazeera tayi tace"nazy akwai wanda Kika fad'awa abinda malam Ali yayi miki ne?"


Tace"ah'ah ke kadai ne sai boy"


Tace"boy kawai Kika fad'awa are you sure?"


Tace"yes kema kin sani daga ke sai shine kawai friends dina meyasa kika tambaya?"


Tace"no iam just surprised nayi mamakin canji malam Ali ne"


Nazeera  tace"Nima haka nayi mamaki kila Allah ne ya tab'i zuciyarshi ko Kuma shiriya ce ta zo me"


Serah tace"toh meyasa boy ke korar miki samari ko sknki yake?"


Nazeera tace"Kai kin fiya surutu Ina fa rubuta test ne"


Serah tace"Dan Allah amsa min wanan tambayar Zaki iya auren boy"


Ba tare da ta kalleta ba tace"me zai hana shi ba mutum bane,barin rubutun tayi ta kalleta tace"serah ke kawata ce tun muna yara bana b'oye Miki komai serah Zan iya auren boy domin shi mutum ne kamar mu,serah ban San meyasa ba Nike Jin boy har cikin Raina in bazaki manta ba tun randa na fara ganin shi kin tuna ai muna tare ranan  na Fara tausayinshi ina Jin boy har cikin zuciyata in boy na cikin damuwa bana iya bacci,saboda tausayi har mafalki nikeyi in ko aka Kira boy mahaukaci Raina tafarfasa yake,boy ya Zama b'angaren na jikina da bazan iya rayuwa Babu shi ba"


Serah tace"in kin Yi aure fa?'


Tace"ba zai hanani Yi me alkhari ba"


Serah tace"toh me zai hana ki aureshi?"


Nazeera tace"wanan ba decision dina bane ni kadai in na auri boy ai Zan tozarta ummana a idon kishiyoyinta,and serah dana ce Zan iya aurenshi bawai Ina nufin sonshi Nike ba what I mean is in  Allah ya kaddara  shine mijina dole Zan amsheshi  hanun biyu domin ko ba komai Zan samu Ladar jinya,yanzu Haka ma boy na Raina Amma so Nike in bashi horo saboda karya Kara min abinda yayi min 


Serah ta sauke ajiyar zuciya Amma lamarin nazeera na d'aure Mata Kai


Bàyan ta gama ta bawa class rep sanan Suka tafi gado nasko hall domin lecture general course edu 311 awa d'aya sukayi Suka fito suna fitowa ta Kira Habib ya zo makarantan 


Bayanin tsakaninta da boy tayi me serah tasa musu Baki 


Yace"but ki daina barin Yana Miki irin Haka tunda ba hankaline dashi ba Kar wata Rana yayi Miki fyade


Tace"wallahi be tab'a min ba sai jiya "


Serah a ranta tace"Wanda beda hankali yasan ya Kori saurayi ai sai na zakulo gaskiya wallahi"


Habib yace" wuce Zan tafi sai na zo da yamma sai mu San abinda za ayi Dan bana son in rasa ki"ya Kare magana da dariya,sun dade suna Hira har lokacin lecture dinsu yayi suka sallameshi 


Wacece nazeera❓❓


Group da basa comment zan daina muku posting

 ðŸ‘„👄👄👄👄👄

*Mahaukaci*

💋💋💋💋💋💋

By maman noorul 

Hudah


Godiya Mai tarin yawa masoyana


🅿1⃣5⃣-1⃣6⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Hanunta serah ta rike tace" kin San wa kike Shirin duka kuwa?matar manya kenan bana son ki jawowa kanki bala'i,wanan dakike budurwa ce ga Nazeeru Abdallah Mai Riga Wanda akafi sani da bereau de change wallahi kina tab'a ta Zaki Sha mamaki"


Feena ta dawo da hanunta kasa a hankali itako nazeera jikinta rawa yake ruky ta jawo feedy gefe tace"in harda gaske sukeyi is better mu Zama kawaye so that mu karayin suna mu taki uban kowa "


Feedy tace"don't tell me you believe that lie"


Ruky tace"let give them benefits of doubt zai iya Zama gaskiya kuma in Suka shiga group dinmu zai zamo babba advantage "


Feedy tace"ok but in nayi found out karya takeyi wallahi sai sun bar makaranta Nan"


Kiran feena sukayi suka bar resturant din,suna barin wurin nazeera ta ja serah tace"wanan wani irin karya ne meyasa zaki musu  karya meyasa kike niman saka mu a matsifa nifa ba ruwana why????"


Serah tace"iam sorry ban San lokacin da ya fito a bakina ba I wanted teaching them a lesson and Wanan hanya ne kadai ya zo min"


Nazeera tace"nidai ba ruwana wallahi da kin bari na anso Musu abincin da haka Bata faru ba,yanzu ga abin da Kika jawo only God knows what will happend next "


Serah tace"Babu abinda zai faru karki damu"abincin da nazeera bata ci ba kenan tayi ta Wasa dashi serah ta d'auke ta had'a da nata tace"bazan siya abinci inyi asara ba"


_________________


Malam Ali na zaune a office ya gan an bude kofa kallonsu yayi da mamaki Zama nazeer yayi yace"Ina fatan ka gane ni"


Jikina rawa malam Ali yace"eh,Allah yasa lafiya"


Yace"miye tsakanin ka da Rahmat Kabir?"


Malam Ali ya fara in Ina jikinshi na rawa yace"ba bb... koma...."


Katseshi nazeer yayi da cewa"zuwa nayi in maka warning akan in ka karawa Rahmat kallon banza balle har ka kara aikata abinda kayi a baya wallahi sai kayi nadama"


Zaiyi magana ya katseshi da cewa you are very stupid in ka sabayi da wasu Mata kana wucewa free this time around sai kasan kayi da budurwata"


Zaro Ido malam Ali yayi ya duka har kasa yace"ranka dade kayi hakuri wallahi bata tab'a fad'a min Kuna da alaka ba, dani na Isa?"


Nazeer yayi me wani kallo ji yake Kamar ya shake shi in ya tuna yayi kissing dinta ya so dealing dinshi Amma Baya son Salim ya ji anihin abinda ya faru balle yasan yayi kissing dinta Hakan yasa ya bar zancen kiss 


Malam Ali yace"ai yanzu Zan Bata marking ko Batayi exams ba tayi passing"


Nazeer ya d'aga me hanun yace"ni bance   ban son zakewa dayawa wallahi ko da Wasa in ka Kara kallon Rahma sai na kwakule idon nan d'an iska kawai yanzu ka Bata test dinta Kuma abinda tayi scoring shi zaka rubuta bana son Kari"


Malam Ali yace"ai ba sai ta rubuta  Zan Bata marking"


Nazeer yace"no a Bata test din ta rubuta "


Yace"toh"sosai ya ja me kunnin tare da tabbatar me duk randa ya ji labari yayiwa wata irin haka sai yasa an koreshi a aiki"


Malam Ali yasan Hakan karamin aikine a gunshi domin suna da connection rokonshi yayi sanan suka bar office din da Salim 


Suna fitowa ya hango su nazeera na shigowa department,nazeera na magana da class rep ko me yace Mata oho sai ta dukeshi a kafada duk Suka kyakyale da dariya,sai ga Musa course mate dinta ya karaso toh dama suna Wasa cikin d'aga murya yace"sweetheart ke Nike nima in kaiki cafeteria yau Zan kula dake"


Nazeera tayi murmushi tace"no thanks mu Bari zuwa gobe bana Jin yunwa"


Yace"oh shirt,gaskiya banji Dadi ba"


Tace"I promise gobe inshaallah zamu je"


Duk abinda suke Yana kallonsu harya karaso serah ta hango spicy ladies zaune wani murmushi tayi tace"nazeera muje kiyi assignment din


Tafiya sukeyi  suna Shiga department din shi Yana fita suna kaiwa kusa  da juna serah ta mugun ture nazeera kawai jinta tayi jikin mutum,wani wawan ajiyar zuciya serah ta sauke domin batayi missing target ba 


Rungumeta yayi d'aga Ido tayi ta kalli hanunta dake kirjinshi sai ta kalli fuskarshi had'a Ido Sukayi sai ta ji wani mugun fad'iwar gaba Amma sun ki sakin juna 


Serah tayi gyra murya ganin kallon juna sukeyi da sauri nazeera ta janye jikinta tace"so sorry  wall...."


Katseta yayi yace"dama na lura tunda na shigo makarantan nan kike Niman in kula ki as in kina tallah kanki how cheap"


Cikin b'acin rai nazeera tace"escuse me,me ka d'auki kanka ne Kai ko kunya baka ji ba daka furta Wanan maganan ka kalleni da kyau nayi maka Kama da wacce ke seeking attention?in kana tunanin duk inda kaje sai Mata sun kalleka toh bana cikin sakarkarun Mata,so take your arrongance to someone else not me"


Yace"oh really it obvious you are desperate looking for who to toast you,I know your type,Dan haka I will not fall to your cheap tricks you think I will toast you by hugging me you lied"


Nazeera ta rasa ya zatayi ta buga Kafa ta kalli serah tace"kin gan abinda Kika jawo ko?"barin wurin tayi 


Serah ta kalleshi tace"sir nazeer Idanunka sun bayyana sirrin dake zuciyarka thou ka Fadi magana abinda bashi ba I don't know why Nike ji a jikina kana son nazeera  tunda na ganka"


Yace"oh ta turo ki ne kiyi toasting Dina ko?"


Serah tayi murmushi tace"karka manta wanan ranan domin kawata xata Rama"


Zaiyi magana ya hango nazeera gaban h o d office tsaye da wasu maza su biyu serah ta lura duk hankalinshi ya karkata wajen murmushi tayi ta rungume hanun domin tasan Abdul sai yayi hugging nazeera it has always been his attitude tun a year 1"


Aiko sai gashi ya rungume nazeera tana tureshi zatayi magana text ya shigo wayarta ta karanta wani murmushi tayi ta rugo da gudu tace"serah Habib yayi replying Dina yace"zai zo makaranta anjima ya bani second chance iam so happy today"idonsu ne ya had'u da nazeer ta murgud'a me baki   


Serah ta gan kwayar idonshi ya canja fisgo hanun nazeera yayi ta saki Kara zaiyi magana sai Kuma ya fasa ya tureta serah ta tarota a fusace ya koma mota dama tuni Salim sun wuce serah tace"sir ka Sha maganin ciyon zuciya kafin ta buga'


Komawa sukayi Suka zauna sai ga feedy ta zo tace"


Maman nur

Post a Comment

0 Comments