Ku kara hakuri, nan da farkon shekarar 2021 tsadar rayuwa zata yi sauki>>Gwamnatin Tarayya

 Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa nan da farkon shekarar 2021 idan Allah ya kaimu matsain tattalin arzikin da ake fama dashi a Najeriya zai ragu.

 

Hakanan suma wasu masana sun bayyana cewa hakan zata iya kasancewa lura da yanda al’amura suka fara canjawa. Najeriya ta fada matsayin tattalin arziki dalilin zuwa cutar Coronavirus/COVID-19.


Ministar kudi da tsara kasafin kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka ta bakin me bata shawara kan yada labarai, Yunusa Tanko Abdullahi, kamar yanda Hutudole ya samo muku daga Vanguard.

 

Ta yi wannan maganane yayin da take ganawa daasu gudanarwar hukumar tattara kudin haraji ta kasa, FIRS inda ta yaba musu sosai ta kuma ce cutar Coronavirus/COVID-19 bata yi illar da aka yi tsammanin zata yi ba musamman a Najeriya kuma hakan ya kasancene saboda matakan rigakafi da gwamnati ta dauka.


Tace akwai tsammanin matsin tattalin arziki da ake ciki zai yi sauki nan da farkon shekarar 2021 inda tace tana kira ga hukumar ta FIRS data kara kaimi wajan tattaro kudin haraji saboda dasu ne gwamnati ke biyan basukan da ake binta.




Post a Comment

0 Comments