Ma'aikatar ilimin tarayya ta ce gwamnatocin jihohi ne zasu yanke lokacin da zasu bude makarantun dake karkashinsu - Chukwuemeka Nwajiuba, karamin ministan Ilimi ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai - Ministan ya kindaya ka'idojin bude makarantu kuma an baiwa dukkan jihohin Najeriya Gwamnatin tarayya ta ce ta baiwa jihohi daman bude makarantu kuma su ke da zabin lokacin da zasu bude. Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya bayyana hakan ranar Alhamis, 17 ga Satumba, yayin amsa tambayoyi a hira da manema labaran kwamitin fadar shugaban kasa na yaki
Ministan ya ce tuni gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi daman bude makarantunsu. Amma Nwajuiba ya ce wajibi ne gwamnatocin jihohi su bi sharrudan kare dalibai da cutar COVID-19 da gwamnatin tarayya ta gindaya. Ya ce gwamnatin tarayya ta yi na ta aikin na samar da takardan sharrudan saboda haka hakki bude makarantu ya rataya kan jihohi. Tuni Jihohi da dama sun sanar da ranakun bude makarantunsu. Daga cikin jihohin da suka sanar da ranar budewa akwai jihar Legas, Oyo, Delta, Bayelsa, Ogun, Ekiti, da sauransu.
0 Comments