Kana jiran taka ni tawa ta Iso>>Ali Jita ya gayawa Nazir Sarkin Waka kan motar Naira Miliyan 65 da aka masa Alkawari

 A jiya ne dai muka kawo muku cewa taurarin mawakin Hausa kuma jarumin fina-finan Hausa, Nazir Ahmad Sarkin ya samu kyautar motar alfarma ta G-Wagon 2019.


 


Hakana mun kawo muku cewa shafin Cars na kasar Amurka yace motar na kaiwa akalla Naira Miliyan 65.

Saidai a yayin da wasi ke bayyana mamakin an yiwa Nazir sarkin waka kyautar Motar, shi kuwa abokin aikin Nazir, Watau Ali Jita, Me makogoron zinare, Kamar yanda Baba Ari ya masa kirari, ya bayyana cewa shi tasa G-Wagon din ta karaso.


 


Jita ya saka hoton Motar a shafinsa na Instagram inda ya bayyanawa Nazir cewa a yayin da yake jiran tasa, shi kuma gashi tashi ta karaso.



Post a Comment

0 Comments