~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 82..... Khaleel
na gama parkin bayan sun isa gida ya juya yana
kallon Ikram dake kkrin bude motar ta fita yace
"tsaya" ta juya tana kallonsa yace "me yasa kika
fa sa hutun?" ta dan tabe baki tace "hka kawae"
xae yi magana wayarsa yyi ring cikin aljihunsa ya
ciro ya ga Mami ce ke kiransa, da sauri Ikram
tace "waye ya Khaleel?" ba tare da ya kalleta ba
yace "Mami ce" ta yo waje da ido, can kuma sae
ta bata rae, yana daga wayar Mami tace "Khaleel
kuna tare da Ikram ne?" ya daga kai yana kallon
Ikram da ta danyi tsuru tsuru tana kallonsa yace
"ehh muna tare" sae da Mami ta sauke ajiyar
xuciya snn tace "to dawo min da ita maxa maxa"
yace "to" snn ta katse kiran ya juya yana kallon
Ikram da ke kallonsa a dan tsorace yace "Mami
tace in mayar dake gida" ta xaro ido ta fashe da
kuka tana girgixa kai tace "don Allah kayi hkuri
kar ka mayar dani wllh baxan je ba" ya galla
mata harara yace "to me kika yi mata?" kmr xata
yi kuka tace "ni ma ban sani ba, kasan mene ya
Khaleel?" ya girgixa mata kai tace "kawae ka
kashe wayarka nima sae in kashe na wa ba shi
knn ba" ya harareta yace "sannunki" bae jira me
xata ce ba ya shiga tada motar xasu bar gidan ta
fashe da kuka ta rikesa tana cewa "ni wllh baxan
je ko ina ba ka ajiyeni don Allah inje inyi sllh ka
ga lkci yyi" ya girgixa kai yace "baki da gskya
knn" tana hawaye tace "A'a ya Khaleel" bude
motar yyi ya fita, ita ma ta fita da sauri suka
shiga gida, Alwala yyi ya fita xuwa masallaci,
yana fita ta kashe wayarsa da nata ta xauna
kasa tayi jigum tana hawaye, wani mugun tsanar
Aliyu take a xuciyarta amma Allah ya isar mata,
tsaki tayi ta mike ta shiga bayi don yin alwala
tana goge hawayenta, tana xaune kan darduma
Khaleel ya shigo dakin, wayarsa ya nufa da sauri
yana cewa "Mami ta kuma kira ko?" ta xumburo
baki tace "ni dae na kashe wayar" wani mugun
kallo yyi mata yace "sbda me?" ta dauke kai bata
ce komai ba tana murgude murgude, kunna
wayarsa yyi yace kar ki sake kashe min waya,
kuma ki tashi ki shirya mu wuce gida don ni ban
iya bata ma Mamina rae ba, yana kai wa nn ya
shige bathroom, binsa tayi da kallo kmr xata yi
kuka, can ta tabe baki alamar ita dae bbu inda
xata, wayarsa ya shiga ring, ta mike da sauri a
tsorace don a tunaninta Mami ce, kanwata tagani
jikin screen din wayar ta daga a tunaninta
seeyama ce ko kuma Aisha, muryar wata daban
taji murya can kasa tana cewa "haba Khaleel,
kiran knn har ynxu, idan ba ni na kira ka ba kai
baxa ka kira ba, ka dinga damuwa da warce ta
damu da kai mana dear" Ikram ta yo waje da ido
wayar na kunnanta tace "lah ila ha illallahu,
wacece wnn" katse wayar taji anyi, dae dae lkcn
da Khaleel ya fito daga bathroom yana goge
kansa, tana kallonsa baki bude tace "yaya
Khaleel wacece wnn ta kira ka" karasowa yyi ya
fixge wayarsa a hannunta yana mata mugun kallo
yace "wa ya baki ixinin daga cal dina kina da
hnkli kuwa?" kuka ta fashe da tana xagaye dakin
tana cewa "ni wllh wllh sae ka gaya min wacece
wnn ta kiraka har da cewa dear kar in je in gaya
ka da Mami" dariya ssae ta basa, ya dauki
Makullin motarsa yace "idan kin gama ina jiranki
a mota" hijab dinta ta dauka ta bi sa da sauri
tana kuka, bayan mota ta bude ta shiga bae ce
mata komai ba suka bar gidan, suna isa gida ta
bude mota da sauri ta nufi balcony, Khaleel ya
bita da kallo har ta shiga gidan snn yyi tsaki ya
fito daga motar, tana shiga falo a stairs ta kusan
cin karo da Aliyu yana sakkowa ta koma baya da
sauri ta hade rae, tana jiran ya sakko ta wuce,
taga yaki sakkowa kuma yaki bata hanya yana
kallonta, ta watsa masa harara tace "ka bani
hanya" jin yaki cewa komai yasa ta juya a fusace
ta nufi dakin Jummai downstairs, yyi murmushi
ya karasa sakkowa a hankali, jummai na xaune ta
gama yi ma sudais wanka tana canxa masa
kaya, Ikram ta shigo, jummai ta rike haba tace
"ta ina kika bar gidan nn Ikram duk kika daga
mana hankali" Ikram ta juya ta bar dakin ba tare
da ta tanka ta ba ta koma stairs don tasan ya
bar wajen ynxu, dakin Mami ta nufa ta tarda
Rukayya xaune gaban Madubi alamar ta fito daga
wanka knn, juyawa tayi da sauri xata bar dakin
suka ci karo da Khaleel, ya bi ta gefenta ya shiga
dakin, da fara'arsa suka gaisa da Rukayya yana
tambayarta yaushe suka xo, Ikram ta fice daga
dakin kamr xata rusa ihu duk ta rasa me ke
damunta, dakin Khaleel ta bude ta shiga ta fada
kan gado ta shiga rusa kuka kmr wanda aka aiko
ma da sakon mutuwa. Allah ka raba mu da
sharrin Mahassada da makiya ni da Fanz dina da
yan uwana baki daya don son da kke ma
Annabinka S.A.W Ameen. Luv yhu ol my sweet
Fanz.
5 mins · Khaleesat Haiydar...
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 83...... Bude kofar da aka yi yasa Ikram ta mike xaune da sauri tana share hawayenta, Mami ce ta shigo dakin tana kallonta tace "kukan me kike" ta fashe da wani sabon kukan tace "ba kuka nake ba" Mami tace "to yyi kyau, daxu wa kika gaya ma xaki bar gidan nn" shiru ikram tayi kanta a kasa, Mami tace "yyi maki kyau" snn ta juya ta fice daga dakin. Hka Ikram tayi ta xama ita daya a dakin kmr mayya taki fitowa, har aka fara iska alamar hadari, ta mike da kyar ta kulle windows din dakin ta koma tayi kwanciyarta, kan kace me ruwa har ya sakko, karfe tara Jummai ta shigo dakin tace "Ikram ki je Mami na kiranki, wae yau kuma miskilancin naki ne ya tashi, kin je kin debi abinci kuwa ma" Ikram ta gyada mata kai kawae, jummai tace "to maxa ki je Mami na kiranki" mikewa tayi ta sa Hijab dinta don sanyi taji take taji, ta bi bayan Jummai, Mami na xaune tana duba wani littafi Ikram ta shigo dakin, kallo daya tayi ma Sudais dake bacci kan gado Mami ta lullubesa ta xauna kasan tiles tace "gani Mami" Mami tace "tashi daga gun nn, kin ci abinci?" mikewa tayi ta koma kan kujera ta gyada mata kai, Mami tace "karya kike" kmr xata yi kuka tace "ni na ci" Mami tace "meyasa kika bar gidan nn daxu" Ikram tayi shiru bata ce komai ba, Mami tace "magana nake maki" ta sunkuyar da kanta tace "dama na xo in maki sallama ne xan tafi hutu gun Ammi, kuma na ga kina da baki shi yasa muka tafi gida kawae" muryarta na rawa ta karasa mgnr, Mami tayi shiru tana kallonta, jin shirun yasa Ikram ta daga kai tana kallonta, Mami tace "to kukan me kike daxu" ta kuma sunkuyar da kanta tace "ya Khaleel ne ya ki kaini gun Ammi kuma" nan ma Mami bata ce komai ba na kusan minti biyar snn tace "tashi ki debo abinci a dinnin ki xo nn ki ci" ba musu Ikram ta mike ta fita ta debo abincin snn ta dawo dakin, da kyar ta iya cin abincin Mami na kallonta don ji tayi kmr ta amayo shinkafar, duk ta rasa me ke damunta, tana kai plate din Kitchen ta dawo Mami tace "dauki sudais ki kai sa gun mamansa" Ikram tayi kmr bata ji taba, sae da ta maimaita instruction din snn ta mike tace "ae ban san inda take ba" Mami tace "dakin Aliyu" fuskarta a daure ta nufi gadon ta dauki yaron ta fice daga dakin, ko sallama bata yi ba a tura kofar ta shiga dakin, suna xaune kan gado yana danna laptop, tana jingine jikinsa tana kallon abinda yake yi, karasa Ikram tayi kusa da gadon ta kwantar da yaron hannunta da ya farka a tsorace sbda ynda ta ajiyesa kan gadon, snn ta juya ta fice daga dakin, Rukayya da ta bita da kallo ta dawo da dubanta ga mijinta tace "ni ban san me nayi ma Ikram ba naga kmr bata so na, kuma ni ba wae na taba ganinta bne" banxa Aliyu yyi mata ya ci gaba da abinda yake, ikram na komawa dakin Mami, Mami tace "kinyi wanka ne" ta dan yi shiru snn tace "ni baxan yi akwae sanyi" Mami tace "akwae ruwan xafi a bayi" bbu ynda ta iya ta shiga tayi wankan snn ta fito, ta dauki kayan baccinta tasa ta dan yi shafe shafenta ta haye kan gadon Mami tana game da wayarta, goma dae dae Khaleel ya shigo dakin kallo daya yyi ma Ikram ya dauke kansa, Mami tace "daga ina kke cikin ruwan nn Khaleel" ya xauna gefen gado yyi shiru kmr baxae ce komai ba, Ikram dae sae kallonsa take fuskar ta a tamke, yana shafa kansa yace "gun frndx dina naje" Mami tace "cikin ruwan nn?" yace "no kafin a fara ruwan na fita ae" Mami tace "to kaci abinci" ya mike yace "ehh na ci, sae da safe Mami" Mami tace "to Allah ya kai mu" ya fita ya rufo masu kofar ya nufi dakinsa, Mami ta juya tana kallon Ikram tace "baki ga mijin ki bne" Ikram ta dauke kai bata ce komai ba, Mami tace "to tashi ki ban waje sae da safe" mikewa xaune tayi kmr xata yi kuka, ba tare da Mami ta kalleta ba ta mike ta shige bathroom, a fusace ta fice daga dakin ta nufi dakinsa, yana xaune sanye da singlet yana sip din tea, ta kashe wutan dakin ta koma can karshen gado tayi kwanciyarta tare da rufawa da bargo, yace "kina da hankali kuwa? Tashi ki kunna min wuta kar in bata maki rae" a fusace ta mike xaune tace "an ki din" sae kuma ta fashe da kuka, yyi murmushi ya ci gaba da shan tean sa.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 84..... Da safe karfe tara saura Ikram na xaune dakin Mami tana rike da Sudais da Mami ta hada ta da tun shigowarta dakin don gaisheta, danne xuciyarta kawae take tana rike da yaron don ji take kmr ta jefar da shi, gashi sae dalala mata yawu yake a jiki wae yana wasa, duk ta wani hade rae tana kallon wani movie da ake a TV, Mami nata harkar gabanta, har Aliyu ya shigo dakin gaida Mami, Ikram bata ko kalli inda yake ba har ya fita daga dakin, Mami ta juya tana kallonta a fusace ta fara mgna "Ikram wnn ba hali me kyau bne kike tsiro kwanan nn, wae ke wace irin yarinya ce ma dae tukunna" shigowar Khaleel yasa Mami ta juya ta ci gaba da abinda take, ya duka kusa da Sudais yana masa wasa yaron sae murmushi yake alamar yana son fara dariya, shi dae yana son yaron ssae gashi sak Babansa, ya daga kai yana kallon Ikram da ta dauke kanta fuskarta a daure tana kallo, yyi murmushi yace "kuna kama da yaron naki ssae" kmr xata yi kuka ta juya da sauri tana kallon Mami ta ga ko tana kallonta kafin ta fara masa masifa, ta ga kallonta kuwa take, hkn ya hanata cewa komai, ya nemi gefen gado ya xauna yana murmushi, mikewa Ikram tayi ta fice daga dakin rike da Sudais, Khaleel yace "Mami xan je Bauchi may b xuwa gobe" Mami ta juya tana kallonsa na kusan Minti biyar shi ko idonsa na kan TV, can ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, bayan kmr minti uku ba tare da ta kallesa ba tace "me xaka je yi a Bauchi?" juyowa yyi yana kallonta yyi shiru bae ce komai ba, jin shirun da yyi yasa ta juya tana kallonsa, ganin kallonta yake yasa ta dauke kai tace "to Allah ya kiyaye Khaleel, amma da Ikram xa ku tafi tunda anyi hutu ko" yace "A'a ba da ita xa ni ba, ae ba dde wa xanyi ba" Mami tace "sbda me? Ae basu san ta ba, don hka dole da ita xaka tafi" ya dan marairaice mata yace "Mami wllh kwana biyu fa kawae xanyi in dawo, ki bari kafin a kare holiday din xan kai ta su ganta, but 4 now ni ba dadewa xanyi ba, kuma ae can gun Amminta tace xata tayi holiday......" Mami ta dakatar da shi ta hanyar masa mugun kallo tace "ban amince da hkn ba, ku shirya ku tafi tare, idan kun dawo sae taje gidan" shiru yyi yana kallonta, daga gani kasan ko kadan bae ji ddin hkn ba, ya mike ba tare da ya kalleta ba yace "to" snn ya fice daga dakin ta bi sa da harara. Da yammacin ranar Aliyu suka bar gidan bayan Mami ta cika Rukayya da Sudais da tsaraba, kiri kiri Ikram ta ki fitowa yi masu sallama, sau uku Mami na kwala mata kira duk tana ji taki sakkowa, sae dae tana jikin window a sama tana kallonsu, har suka bar gidan snn ta sulale kasa ta shiga rera kuka a hankali. Washegari da safe Mami da kanta ta shiga hada ma Ikram kayan sawan ta, Khaleel na xaune dakin yana kallonta, Ikram ko na downstairs dakin Jummai, Mami tace "kai ka gama hada naka kayan ne" ya kauda kansa yace "ni fa kwana biyu nace maki xanyi Mami, sae tula mata kaya kike" Mami ta tsaya kallonsa tace "kaya kala biyar din ne na tula mata, ni fa ban son wlknci, in har baxa ka tafi da Ikram ba to kai ma bbu inda xa ka, don ban ga amfanin xuwan na ka ba" Khaleel ya juya yana kallonta yace "haba Mami xuwa gun yan uwan Mahaifina ne ba shi da Amfani don ban je da Ikram ba" Mami tayi masa mugun kallo tace "to gaya min magana Khaleel" sunkuyar da kansa yyi bae kuma cewa komai ba, Mami tayi kwafa ta dauki wayarta da ke kara ta daga don amsa kiran, Ikram ta shigo dakin Khaleel ya bi ta da harara, bata ma san yana yi ba, ya mike ya fice daga dakin, karfe tara na safiya Khaleel ya shigo dakin Mami yace ya shirya Ikram yake jira, kiri kiri Ikram tace ita bbu inda xata da Mami tace ta shirya xa su yi tafiya da Khaleel, sae da Mami ta bata mata rae snn tana hawaye ta shiga wanka, ko da ta fito Mami bata dakin sae shi, ta dauki kayanta fuskarta a daure ta nufi bathroom xata sa, ya bita da kallo har ta shiga ta rufe kofar, yyi wani irin murmushi hade da kwafa yana gyada kansa ya mike ya fice daga dakin.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar
85.....
Khaleel na xaune cikin mota yana jiran Ikram
bayan ya sallami Maminsa, ya kwantar da Driver
seat yasa earpiece a kunnensa idonsa a lumshe
yana jiran fitowar nata, tare Ikram suka fito da
Mami da Jummai dake rike da jakar kayanta, ya
gyara xamansa ya cire earpiece din kunnensa
har suka karaso gun motar, Ikram da har lkcn
fuskarta ke daure ta bude baya xata shiga Mami
tace "nan xaki shiga Ikram" tace "eh" ba tare da
ta kalleta ba ta shige motar, Jummai ta saka
jakar a Booth din motar, Mami ta xaga ta inda
Khaleel yake tace "ga amanar Ikram Khaleel,
Allah ya kai ku lfya, ya kiyaye hanya, snn ina
hada ka da Allah kar kayi tukin gangancin nn
naka Khaleel" yyi murmushi yana shafa kansa
yace "ae na daina Mami" Mami ta juya tana
kallon Ikram tace "kin dae ji abinda na gaya maki
ko dotana, xa mu dinga waya" Ikram ta gyada
mata kai, Khaleel ya tada motar, Mami tace "to a
dae yi Addua" yace "Anyi Mami" Jummai na
washe hakora tace "to Allah dae ya tsare, kuma
yasa a dawo mana da bby" Mami tayi murmushi
ta juya ta bar wajen, Ikram ta xaro ido tace
"baby kuma mama Jummai, a ina xa a kawo
maku bbyn?" ta karashe mgnr fuskarta a tamke,
Jummai tayi dariya tace "to ai ni ba da ke nake
ba da Babana nake" Ikram tace "ayyo" ta Madubi
Khaleel ke kallonta, suna hada ido ta galla masa
harara yyi murmushi ya dauke kansa, ya ja motar
suka bar gidan Jummai na daga masu hannu, sae
da suka hau Main road yana kallon titin gabansa
yace "kinsan da cewar ni ba Drivern ki bne dae
ko?" bnxa tayi masa, ya gyada kai bae kuma
cewa komai ba ya maida hankalinsa ga tukin da
yake, cikin awa daya suka fita daga Abuja shima
sbda hold up din safe, ya dauki hanyar kaduna,
lkci lkci ya kan daga kai ya kalleta ta madubin
mota, suna kusan kaduna ya juya ya ga bacci
take, ya ci gaba da tukin nasa a hankali har suka
shigo kaduna wajen karfe sha biyu da rabi, ya
juya yana kallonta ya ga har ta tashi daga baccin
tana kallon tagan mota, yace "kina son wani abu
ne" ta kauda kanta tace "ni ruwa xan sha" gun
Hawkers din titi ya siya masu table water guda
uku ya mika mata daya ta karba ya ajiye sauran
snn ya ci gaba da drivin dinsa, suna kusa xaria
tace "ka tsaya" ya dan rage gudun da yake yace
"me xa ki yi" kmr xata yi kuka tace "ni Amai
nake ji fa kmr" ya samu gefen titi yyi parkin yace
"Amai kuma" toshe bakinta tayi da sauri ta bude
motar ta fito ta xaga ta gun daji ta shiga kwarara
Amai, ya dan yi tsaki ya fito rike da roban ruwa
daya, yana tsaye har ta gama snn ya bude ya
mika mata ta wanke bakinta da fuskarta snn ya
bude mata mota ta shiga, ya xaga ya shiga
shima suka bar wajen, Amanta hudu kan su isa
kano duk ta wahala ssae, komai ya siya mata
taki ci sae apple daya da take ta fama da sbda
Amai, kuka ta dinga masa wae ita ta gaji da
tafiyan har ynxu basu kai ba, shi dae bae tanka
ta ba har suka shigo kano karfe uku da rabi,
direct hotel ya nufa suka yi lodge, yana bude
dakin da aka basu ta shige ta fada kan gado a
gajiye, shi kuma ya shiga bathroom don yin
alwala, ko da ya fito ya tarar tayi bacci, yana
idar da sllhnsa ya fita siyo masu abinda xa su ci,
har karfe biyar Ikram bata tashi ba shi har ya ci
abinci yyi wanka, xaunawa yyi kusa da ita ya
shiga tashinta, ta fara juye juye yace "ke" ta
mike xaune da sauri tana murxa ido yace "tashi
kiyi sllh ki ci abinci" tace "ya Khaleel amma baxa
mu sake tafiya ba yau ko" yace "anjima da
daddare xa mu tafi" kmr xata yi kuka tace "A'a
wllh amai xan dinga yi" yace "kije kiyi alwala in
wanka xaki kiyi, tun daxu Mami ke son mgna da
ke" mikewa tayi ta shiga bathroom don yin
wanka, tana gamawa ta shiga kwala masa kira
yace "meye hka" tace "ka bude jakata ka dauko
min xanin da xan daura na manta bbu tawul a nn
ashe" yace "to ki fito ki dauka mana" tace "Ha'a,
to hka xan fito? ae bbu abinda xan daura ne
shiyasa, miko min kawae fa xaka yi ga hannu na"
ta karashe maganr a fusace, yyi murmushi yana
kallon kofar bathroom din, tace "ka taso?" dariya
ta basa, yana gyada kai yace "ehh" snn ya mike
ya bude jakarta ya dauki xanin atamfa ya nufi
bathroom din da shi.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 86..... Tura kofar bayin yyi ya shigo ta fasa ihu tare da durkushewa wajen tace "lah ila ha illallahu wa yace ka shigo" ya wara ido yace "ba xani kika ce in kawo maki ba" ta fashe da kuka tace "to shine nace ka shigo min, ba miko min nace kayi ba, ni ka fita ka daina kallona" ta karashe mgnr a fusace cikin tsawa, yyi murmushi yace "to" snn ya ajiye mata xanin ya juya ya fice, tayi tsaki ta mike ta dauki xaninta ta daura tana gunguni ta fito, da daddare karfe tara saura tana kwance tayi ruf da ciki tana game da wayarta bayan sun gama waya da Mami, shi kuma yana xaune gefen gado yana danna laptop dinsa wayarsa dake gefensa yyi kara ya sauke idonsa kan screen din wayar don ganin me kiransa, juyawa yyi yana kallon Ikram ya ga kallonsa take ya dauke kansa, ta mike xaune da sauri tace "waye ya kira ka" bata jira me xata ce ba ta rarrafo kusa da shi da sauri, yyi hanxarin dauke wayarsa ya saka cikin aljihu yace "ina ruwanki?" xaro ido tayi hade da bude baki tana kallonsa, sae kuma ta fashe da kuka ta mike tsaye tace "wllh ka gaya min ko wanene ke kiranka kar in kira Mami ynxun nn in gaya mata" ya galla mata harara ya rufe laptop dinsa ya mike jin an sake bugowa, ya nufi kofar fita ta bisa da sauri tana kuka tace "wllh baxa ka je ko ina ba sae ka gaya min wanene ke kiran ka cikin daren nn" daukarta yyi kmr bby ya isa gado ya jefar da ita ya fice daga dakin tare da kullewa ta waje da Makulli, Ikram ta koma kmr mahaukaciya a dakin bbu abinda take sae aikin kuka tana xagaye dakin, ba shi ya shigo dakin ba sae kusan karfe sha daya tana kwance tsakiyar dakin a kan tiles ta gama jarabarta tayi bacci, a hankali ya dauketa gudun kar ta cinyesa in ta farka ya kwantar da ita kan gado, duk da hka bae tsira ba don cikin baccin ta dinga bala'i idonta a rufe, dariya ta basa ssae, ba kadan ba yake tsoron jaraban Ikram. Da safe karfe takwas suka yi set off da kyar don ca tayi bbu inda xata daga hotel din, karfe biyu da rabi suka iso wani makeken gida me kyan gske, Khaleel ya ciro wayarsa ya fito da nmbr frnd dinsa ya kira bugu biyu ya dauka yace "ya kana gida ne Al-ameen gani kofar gidanka" dariya yyi yace "fuck yhu 2" ya katse wayar snn ya danna horn, Mai gadi ya leko ya bude masa gate ya shiga yyi parkin, ya juya yana kallon Ikram dake bacci, Al-ameen ya karaso gun motar da mmki yace "waw wnderful, wllh tot yhu were teasin me, daga ina hka Guy" Khaleel ya fito ya xagayo xae tada Ikram yace "daga Abuja, Madam dinka na ciki ne" Al-ameen ya shiga leka motar yace "wacece wnn Khaleel" Khaleel ya dan yamutse fuska yace "yarinyar wata frnd din Mami ce" Ikram ta farka da sauri tana mitsika ido kmr xata yi kuka tace "meye," Al-ameen yace "me ya sameta?" Khaleel yace "Amai take tayi a mota" Al-ameen yace "eyya, kmr xee ta knn, sannu bby" Khaleel yace "fito mana" ta fito daga cikin motar rike da hijab da dankwalinta sbda wahala dogon gashinta har kusan bayanta, Khaleel yace "baxa ki sa Hijab din bne" ta galla masa harara tace "ni ka ji dani ina xa ni kace in fito" dariya Al-ameen yyi, Khaleel ya hade rae yace "ni kike gaya ma mgna" juyawa tayi a fusace ta koma cikin motar, Al-ameen na dariya yace "yi hkuri ki fito bby, ciki xa mu shiga" tsaki Khaleel yyi ya nufi kofar shiga gidan, da kyar Al-ameen ya lallabata ta fito ya rufe motar don ca tayi baxata fito ba da, yana gaba tana biye da shi a baya suka shiga cikin gidan, Xainab ce ta sakko da mmki tace "Khaleel yau kai ne a gidanmu" yyi murmushi suka gaisa tana kallon Ikram da ta kwanta kan kujera, tace "kar dae aure kayi bamu sani ba Khaleel" Khaleel yace "aure kuma Zainab, wnn yar yarinyar ce xan aura" dariya Zainab tayi tace "amma baka da mutunci to ina ka samo yarinya" mikewa xaune Ikram tayi fuskarta a daure tace "nan ne family house din naku da Mami tace xa mu xo?" duk suka juya suna kallonta, Khaleel ya galla mata harara yace "ban sani ba" kuka ta saki tana tattara hijab da dankwalinta tace "wllh ni ka kaini inda Mami tace xa mu inje in huta meye xaka wani dinga gantali dani a duniya?" Zainab ta juya tana kallonta tace "ae nn ma gida ne Yan mata" Al-ameen sae dariya yake yana kallonta duk sae yaji yarinyar ta burgesa, kasa cewa komai Khaleel yyi don tana iya gaya masa mgna, Zainab ta mike tace "tashi mu je kiyi wanka sae ki ci abinci" ba musu ta mike ta bita, sae da suka haura sama Al-ameen yace "waw amma fa yarinyar ta hadu wllh, ya sunanta" Khaleel ya mike yana girgixa kai yace "a hka xaka kare, matata ce dae don ma kasani ta daina burge ka" Al-ameen ya tsaya kallonsa da dan mmki, Khaleel yace "xo muje kaji abinda ya kawo ni Bauchi" ba musu ya mike ya bisa suka fita yana cewa "wae re yhu serious matarka ce Khaleel, yaushe kayi auren bamu sani ba" Khaleel yace "A year nd a halve knn"
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 87..... Da
daddare karfe sha daya Ikram na xaune dakin da
Zainab ta sauketa duk takaici ya isheta gashi ta
bar wayarta cikin mota kuma ya fita da motar
bare ta kira Mami, bude kofar dakin aka yi
Khaleel ya shigo, kallo daya tayi masa ta dauke
kanta, tun da ya fita daxu da rana sae ynxu ya
shigo gidan, ya xauna gefenta yana kallonta yace
"kin ci abinci?" juya masa baya tayi bata ce
komai ba, ya mike ya shiga bathroom don yin
wanka, ko da ya fito ta riga ta kwanta ta rufa da
bargo, ya gama shirin kwanciyarsa ya kashe
wutan dakin ya kwanta yana kallonta, a hankali
ya dawo kusa da ita ya cire bargon jikinta ya
jawo ta jikinsa murya kasa kasa yace "kin dae ji
sakon da Mama Jummai ta bani ko?" ta kwace
kanta a fusace ta mike xaune cikin tsawa tace
"meye hka ya Khaleel" murmshi yyi ya koma inda
yake ya kwanta ya juya mata baya, washegari
friday tun da safe ya fice daga gidan tana bacci,
ba shi ya dawo gidan ba sae bayan Magrib, tana
kwance yace ta hada kayanta xa su wuce, yi tayi
kmr bata ji sa ba yana tsaye daga bakin kofar
yace "magana fa nake maki" tace "ina xa mu?"
yace "inda Mami tace in kai ki" mikewa tayi ta
dauka jakarta tace "a shirye nake" har mota
Xainab da mijinta suka rakosu ita dae Ikram bata
sake jiki da Xainab ba kmr ynda ita ma bata sake
da ita ba don har lkcn bata san matar Khaleel
bace, bayan sun bar gidan Ikram nata raba ido
taga gidan da xasu taga ya kawo su wani hotel,
ta juya da mmki tana kallonsa tace "ina ne nn ya
Khaleel" ba tare da ya kalleta ba yace "hotel,
kuma nn xamu kwana gobe sae in kai ki inda
Mami tace in kai ki don ynxu dare yyi" tace "da
can baka san daren xae yi ba ka tafi ka barni tun
da safe, to bbu inda xan je daga motar nn, don
me xaka dinga yawo dani tun jiya kmr wata
gantalalliya ya Khaleel" kallonta kawae Khaleel
ke yi, ko kadan Ikram bata da kunya, yyi
murmushi a xuciyarsa yace rainon Mami ne wnn,
ya bude motar yana kallonta yace "wllh kika sake
na bar nn sae dae ki kwana cikin mota kinji dae
na rantse" kuka ta saki ta fito daga cikin motar
ya fixogo hannunta suka yi cikin hotel din, suna
shiga tayi shiru ganin ynda ake kallonsu don
akwae Eatry daga kasa, ko kallonta bae yi ba
bayan ya biya kudi ya nufi sama rike da makullin
dakin da aka basu ta bi bayansa tana turo baki,
suna shiga dakin tayi kwanciyarta, shi kuma ya
shiga wanka, yana fitowa ya tada sllhn isha ta
mike ta shiga bayin don yin alwala ita ma, har ta
idar da sllh bae mike daga inda yake ba ta haye
kan gado sae a snn ya mike ya koma gadon
shima ya kwanta yace "kina ji na" ba tare da ta
kallesa ba tace "eh" yace "gobe xa mu tafi gida
da safe, kar ki kuskura kice ma Mami bn kai ki
kin gaida familyn dad dina ba" ta mike xaune da
sauri tana gyada kai hannunta a kugunta tace
"iyye! To wllh sae na fadi, sannunka" fixgota yyi
ta fada kansa ya kashe wutan dakin, wayyo ranar
ta fada ma yan garinsu don ssae Khaleel ya
tsorata ta, kuka take jikinta na rawa tana hada
sa da Allah da annabi tana cewa ya rufa mata
asiri, tunda tayi damben iya karfinta taga ba riba
amma bae ma san tana yi ba, ba karamin raxana
tayi da Khaleel ranar ba, da kyar ya samu yyi
cntrln kansa da yaga numfashinta na neman
daukewa sbda tsoro ya kyaleta, bae taba mata
irin abinda yyi mata ba ranan, ya dde kwance a
ruf da cikin da yyi, snn ya juya da kyar bae ganta
kan gadon ba, murmushi yyi ya shige bargo
abinsa daga nn bacci ya daukesa, can cikin dare
ya farka bae ga Ikram gefensa ba ya mike xaune
da sauri ya kunna wuta yana kalle kallen dakin
amma bae ganta ba, mikewa yyi ya nufi
bathroom ya ganta xaune daga bakin kofa ta
hade kai da gwiwa kuma bacci take a hkn, duk
sae ta basa tausayi ya durkusa gabnta ya dago
kanta ta koma baya a firgice, ta fashe da kuka
ganinsa jikinta ya dau rawa tana kkrin mikewa
daga inda take tana cewa "don Allah don annabi
kayi hkuri ya Khaleel wllh wllh baxan gaya ma
Mami ba ka kai ni ba, kar ka min komai don Allah
tsoro nake ji" ta karashe mgnr cikin matsanancin
kuka ya dagota ta fasa ihu a raxane, ya rufe
bakinta da sauri yace "ke bbu abinda xan maki"
jikinta na rawa suka fita daga bayin ya kwantar
da ita, da kyar tayi bacci amma da taji motsinsa
xata farka a tsorace, har asuba bata yi baccin
kirki ba, sae da yyi wanka ya fita sllhn asuba snn
bacci me nauyi ya dauketa.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar
88.....
Karfe bakwae Khaleel ya shigo dakin har lkcn
Ikram na baccin da bata yi jiya ba, ya xauna kan
gadon ya tsura mata ido yana kallonta, can yyi
murmushi ya kauda kansa a xuciyarsa yace
Alhmdllh na samo cure din rashin kunyar yarinyar
nn, dawowa kusa da ita yyi ya shiga tada ta, ta
farka a tsorace ya hade rae ya daura yatsunsa
biyu a lips dinsa alamar kar tayi masa kara, suna
hada ido ta sunkuyar da kanta da sauri, yace "kin
yi sllh ne" girgixa masa kai tayi ta mike ba tare
da ta kallesa ba kmr munafuka ta nufi bathroom,
ko da ta fito baya dakin, dogon hijab dinta ta sa
don yin sllh, tana idarwa ta dauki brush dinta ta
shiga bayin ta wanke baki, snn ta fito tayi maxa
ta sa kayanta tunda tayi wanka, ta koma can
karshen gado ta xauna ta rakube, da breakfst
Khaleel ya dawo dakin, ya ajiye mata nata yace
"hurry up xamu kama hanya ynxu" ba tare da ta
kallesa ba kanta a kasa kmr munafuka ta jawo
breakfst din ta shiga budewa a hankali, ya kafa
mata ido, karfe takwas da minti goma suka bar
hotel din suka kama hanyar Abuja, ba su suka isa
Abuja ba sae kusan yamma, duk Ikram ta jigata
ssae tayi amai har ta gode Allah, Mami bata nn
sae Jummai, ta shiga dakin Mami ta cire gown
din jikinta ta daura xani ta xube kan gado sae
baccin wahala. Karfe shidda kishin ruwa tare da
bude kofar da aka yi suka farkar da ita daga
baccin da take, Aliyu ta gani tsaye bakin kofa ya
kafa mata ido, suna hada ido ya juya da sauri ya
fice daga dakin, da har ta bude baki xata ce
yayana kawae ta toshe bakin da sauri sae
hawaye. tana xaune ita daya a daki tun bayan
fitan Aliyu tayi jigum duk ta rasa me ke damunta,
ssae xata baka tausayi idan ka ganta a wnn lkcn,
bude kofar da aka yi yasa ta daga idonta da sauri
Mami ta shigo dakin, Ikram ta sakko daga kan
gado tana kirkiran murmushi tace "Mami sannu
da dawowa" Mami ta karaso dakin ta ajiye
handbag din hannunta tace "Ina Khaleel" Ikram
tace "ban sani ba nima Mami, daga bacci na
tashi" Mami bata kuma cewa komai ba, ganin
Mood din Mami yasa Ikram a hankali tace "Mami
baki da lfya ne" Mami ta girgixa mata kai ba tare
da ta kalleta ba, ta ciro wayarta tayi dailn nmbrsa
ta kara a kunne sae da ya kusa katsewa snn ya
daga, Mami tace "ina neman ka Khaleel" bata jira
me xae ce ba ta katse wayar, ta juya tana kallon
Ikram kmr bata son mgna tace "kinyi sllh ne"
Ikram ta girgixa mata kai snn ta nufi bathroom
don yin alwala, Mami na xaune ta fito tayi sllh,
snn tace taje ta karba abinci gun Jummai, a
stairs suka hadu da Khaleel bata ko kallesa ba ta
sauka abunta ya nufi dakin Mami, da sallamarsa
amma can kasa ya shiga dakin, suna hada ido da
Mami ya sunkuyar da kansa ya xauna kasan tiles
yace "ina yini Mami" Mami bata amsa ba idonta a
kansa, ya daga kai yana kallonta sae kuma ya
maxa ya sunkuyar da kai ganin kallonsa take.
Mami ta mike ta nufi window a hankali ta tsaya
tana kallon waje snn ta fara mgna a nutse.
2 mins · Khaleesat Haiydar...
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 89..... "me ya kai ka Bauchi?" Khaleel yyi shiru kmr baxae ce komai ba ta juyo tana kallonsa ya shafa kansa yace "aure Mami," Mami tayi murmushin takaici ta karasa drawer dinta ta dauko takarda da pen ta jefa masa gabansa tana kallonsa tace "rubuta min takardar Ikram ka bani ynxun nn" ya girgixa kai yace "Mami ni ba na kara aure bne don cin mutuncin Ikram, A'a ni na kara aure ne don tasan menene aure, Mami its so hard leavin wit her as a wife, ni a wahale ita ma a hka, na farko ko kadan Ikram bata san meye respect ba, bata san meye xaman aure ba, har yau Ikram iyakarta kunna gas a kitchen, bata san ta gyara gidanta ba sae jikinta da dakinta, nd she alwayz neva wants 2 learn don da nayi crrctn dinta sae ta balbaleni da masifa kmr xata cinyeni, shiyasa nake son kawo mata abokiyar xama don tasan wayz of life da menene xaman aure, though nayi gaban kai na ban...." Mami ta dakatar da shi ta hanyar daka masa tsawa tace "enuf Khaleel kar ka kuma gaya min wata mgnr bnxar don uwarka ba kai kace kaji ka gani ba, ynda naki xama da kishiyoyi to Ikram ma baxan mata fatar xama da kishiya ba don hka ka xabi daya cikinsu, munafukin bnxa kawae ni xaka ci ma mutunci ka watsa min kasa a ido ko? to kayi kadan, fita ka ban waje ka yanke decision ynxun nn ina jiranka" Khaleel ya mike yana murmushi ya fice daga dakin, Mami ta xauna kan gado ta dafe kanta ta ma rasa wani tunani xata yi, to duk wnn abinda ya lissafo mata kan Ikram laifinta ne ko na wa? Tana jin fitar motarsa tasan lallai iyakarta Khaleel ke son nuna mata,. amma da can bae san da abubuwan da ya lissafo mata ba sae da ya gama kwana gado daya da yar mutane, da yau bbu abinda ya taba shiga tsakaninsu to lallai karbar ma Ikram takardarta xata yi ta maida hankalinta gun karatun ta kawae, har washegari sunday Khaleel bae dawo gidan ba, karfe tara tasa driver ya kai Ikram gidansu Aliyu gun Momy, goma da rabi na safe tana kwance a daki duk hankalinta ya kasa kwanciya, taji shigowar motoci gidan, ta mike ta nufi window don ganin ko su waye, tana kallonsu duk suka fiffito daga motar, ta juya ta bar windown jiki ba kwari. Sae da Jummai ta xo sama kiranta snn ta sauko, cike da fara'a suka gaisa da matan dake falon tana kallon yarinyar dake xaune lullube cikin mayafi, breakfst Mami tasa jummai ta hada masu, ta taho da yarinyar sama da kawayenta biyu.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 90..... Da yamma karfe biyar Ikram ta dame Momy xata koma gida ita, dama tun xuwanta gidan da ta ga Rukayya na nn ta ki sakin jiki duk ta wani hade rae taji bata son xaman gidan kuma duk da su Seeyama na nn, a daddafe tayi karfe biyar a gidan snn Momy ta sa Drivernsu ya maida ta gida, har bakin mota Rukayya da su Seeyama suka rakota duk ta hade rae ta daga ma su seeyama hannu kawae drivern ya ja motar suka bar gidan, shidda saura minti ashirin suka iso gida, ta fita tayi ma drivern gdya ya bude mata booth ta dauki tsaraban da Momy ta hada mata snn tayi cikin gida, bbu kowa falon sae TV dake ta aiki, jin kamshin girki yasa ta gane Jummai na kitchen ta haura sama xuwa dakin Mami, Mami bata dakin sae mata biyu da ta gani baxa su wuce shekaru ashirin ba duka xaune kan gadon Mami, farar ta daura mayafin da ke kafadarta xuwa kanta, Ikram ta dauke kai tace "ina yinin ku" duk suka amsa da lfya, ajiye ledan hannunta tayi ta fice daga dakin ta sauka kasa xuwa gun Jummai, don jin su waye matan don bata taba ganinsu ba, Jummai na parboilin din shinkafa tace "A'a yaushe kika dawo Ikram" Ikram ta gaisheta tace "Mama jummai ina Mami fa ban ganta a daki ba" Jummai tace "ki duba daya dakin tana ciki" Ikram tace "to suwaye wnn matan dake dakin Mami, naga suna min wani irin kallo a ina suka san ni?" Jummai bata ce komai ba tana ta aikin gabanta sae da Ikram tace "Mama Jummai" Jummai ta juyo tana kallonta tace "bakin Mami ne" Ikram bata ce komai ba ta juya ta bar kitchen din ta koma sama ta shiga dakin da Mami take, Mami na xaune dakin Ikram ta karaso ta gaida ta, Mami tace "har kin dawo" Ikram tace "ehh momy ma tace in gaishe ki," Mami tace "ina amsawa" ta kwanta gefen Mami tace "baki kika yi Mami" Mami tace "ehh" Ikram ta mike tace "xan je gun Mama jummai" karfe tara saura Ikram na xaune dakin Jummai Mami ta shigo tace "Jummai ku je da Ikram ku siyo fruits inda kike siyo min, sae driver ya kai ku" Jummai tace "to" Mami ta mika mata kudi ta fita, Hijab kawae Ikram tasa suka fita da Mama jummai, suna fita Khaleel ya shigo gidan Mami na xaune falo, ya karasa ya xauna kasan carpet ya gaisheta ba tare da ta kallesa ba ta amsa, Mami tace "ka dauki matar ka ku bar min gidana ynxun nn" ya mike bae ce komai ba ya haura sama, tana xaune ita kadae a dakin tana danna wayarta don kawarta ta tafi da yake nn Abujan take, ya karaso ya xauna gefen gadon yace "a shirye kike? Xamu tafi gida" ba tare da ta kallesa ba tace "ehh" ya mike ya fita ya kuma sakkowa ya sami Mami a falo yace "ikram fa Mami" wani mugun kallo Mami tayi masa a fusace tace "Ikram? Me xata maka" yace "gida xa mu tafi" tana girgixa kai tace "tun kan in bata maka rae ka tashi ka ban waje, bana son magana, da wace Ikram din xaku tafi? Get out Khaleel" mikewa yyi ya haura sama, ba a dau lkci ba ya sakko yarinyar na biye da shi a baya fuskarta lullube da mayafi handbag dinta a hannunta, ta iso har gaban Mami ta durkusa Mami tace "to Allah ya kiyaye hanya, ya kuma bada xaman lfya" mikewa Khaleel yyi ya ma Mami sae da safe yarinyar ma hka snn ta bi bayansa, Mami na jin tashin motarsa ta jinginar da kanta jikin kujera a hankali, lallai Khaleel ya nuna mata iyakarta, bayan fitarsu da minti goma su Ikram suka shigo, ranar dae Mami ranta a dagule ta kwanta, Ikram kam ina tasan meke faruwa, ko tambayar rashin ganin Khaleel din ma bata yi ba tunda ba damuwa tayi ba tana ta harkar gabanta, washegari Mami tasa ta hada kayanta Jummai ta rakata Driver ya kai ta suleja gun Ammi tayi hutu. Karfe sha biyu jummai ta bar gidansu bayan tayi ma Ammi sallama da Driver, Ammi na kallon Ikram bayan fitar jummai tace "mijin ki fa ikram, ae ba mami ya kamata tace ki xo hutu ba" Ikram dae sae cin maiman da mmn altine ta aiko mata take bata ce komai ba, Ammi ta daka mata tsawa "ba magana nake maki ba" ikram ta turo baki tace "to nima ban sani ba Ammi" Ammi tayi shiru tana kallonta can tace "baki bar wnn dan iskan halin naki na turo ma mutane baki ba ko" ikram bata ce komai ba Ammi tace "ki tashi ga kayan miya can ki gyara ki kai nika ki dawo kiyi miyan, bbu abinda xanyi tunda ga ki" Ikram ta yo waje da ido tace "ae ban iya ba Ammi"
0 Comments