Ikhram hausa novels 2

 Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 21..... Washegari

Ikram na tashi da Asuba Aliyu ta fara tambayar Mami dake kitchen tana hada masu break, "kin ji mana Anty ki gaya min ina yake mana" Mami tace "wae wa?" Ikram tace "wnn din nn mana," Mami tace "bana san shi ba," Ikram ta bata fuska kmr xata yi kuka tace "Allah ni ban gansa ba, kince xae xo da safe" Mami ta ja ta suka koma sama ta shiga da ita bathroom ta matsa mata toothpaste a toothbrush snn ta mika mata tace "maxa ki wanke bakin ki kafin in dawo dakin nn, kuma kika kuskura kika taba wani abu xan dokeki snn baxan ba ki tea ba" Ikram ta xumburo baki ta karba snn Mami ta fita ta ci gaba da abinda take a kitchen, Ikram na gama Brush ta fito daga bayin ba tare da ta taba komai ba don tana mugun son tea, tana bude kofar dakin, Khaleel ma na bude kofar dakinsa, ta bude baki da alamar mmki tace "lah dawowa kayi" komawa cikin dakinsa yyi ta sauko da gudu taje ta sami Mami a kitchen tace "Anty wnn yaron ya sake dawowa ne ba ya tafi ba" Anty ta juya tana kallonta tace "yaya Khaleel xaki dinga ce masa daga yau kin ji ni ko Ikram" Ikram tace "to amma meyasa ya kuma dawowa ni bana son ya dawo" Mami tace "maxa ki koma daki idan ba hka ba baxa ki sha tea ba" da gudu ta bar kitchen din ta koma sama, har ta bude dakin Mami ta dawo tayi hanyar dakinsa, ta dan bude kofar a hankali tana lekan dakin, ido hudu suka yi yana sa agogo ta washe masa hakora tare da kanne Ido tace "yaya Khaleel" bata jira mae xa ce ba ta rufe kofar tana kyalkyala dariya ta shige dakin Mami, Khaleel ya dde tsaye kmr ya hadiye xuciya don takaici daga karshe ya saka agogonsa ya suri briefcase dinsa ya fice daga dakin, Mami ta fito daga kitchen knn tace "ga break can kan dinnin Khaleel" ba tare da ya kalleta ba yace "xan yi a office" yyi kofar fita, Mami ta kirasa, tsayawa yyi daga inda yake jin bata ce komai ba yasa ya dawo yace "gani" ta xauna tace ya xauna, shi ma ya xauna, cike da damuwa ta fara masa mgna "haba Khaleel ynxu xaman Ikram ne matsalarka a gidan nn, me ta tsare maka son, kai ynxu kafi son ka dinga ganina cikin kadaici alwayz ba yaro gabana" Kmr xae mata kuka yace "to Mami ni ba yaro bne ko gajiya kika yi dani" Mami tayi murmushi tace "me xae sa in gaji da son dina, kafa san irin son da nake maka Khaleel kuma dole vry soon xa mu rabu don aure xaka yi nd beside awa nawa kke yi gida kai da sae dare ma kke dawowa daga aiki" Khaleel ya jinginar da kansa jikin kujera bae ce komai ba, Mami ta dan sauke ajiyar xuciya tace "ka dauki Ikram a matsayin kanwarka plss, duk wnn wautan da take yi xata daina, in ma ance tayi ba yrda xata yi ba" Khaleel ya dan tabe baki bae ce komai ba, sae ga Ikram ta sauko ya juya yana kallonta fuskarsa daure ta washe masa hakora kmr dae ynda ta yi masa daxu tace "yaya Khaleel" sae kuma ta fashe da dariya har da kyakyatawa, ji yyi kmr yyi kuka don takaici, Mami tace "meye hka Ikram" Khaleel ya mike da sauri yace "mami sae na dawo" yyi hanyar fita, Mami tace "to abincin fa Khaleel" a bakin kofa suka ci karo da Aliyu, Khaleel ya basa hanya ya wuce snn ya fice, da gudu Ikram taje ta rungumesa tana masa oyoyo, ya wara mata ido ya durkusa yace "kinyi bacci me ddi Ikram" ta bata fuska tace "ba ka tafi ka bar ni ba to" Mami tace "to mu tafi sama kiyi wanka" Ikram tace "A'a ni ba ynxu xanyi ba kin ga yaron da nake tambayrki nn kika ce baki san inda yake ba" Mami ta harareta tace "nace ki xo muje in sa maki ruwa kiyi wanka" Aliyu yyi murmushi ya mike ya kamo hannunta suka karaso cikin falon ya gaida Mami, ta amsa tace "ka fara wlkncin xuwa aikin naka ne ynxu ko, na kusa fire dinka" yace "kai Mami kwana biyu ne fa kawae" tace "dat's ur cup of tea ka bari idan an gama maka naka sae kayi ynda ka so" bae ce komai ba ganin ta ja Ikram xasu haura sama yasa yace "da Ikram xa ki office knn yau Mami" Mami tace "yau xanje mata registration a makaranta sae ta fara xuwa, anjima kuma jummai xata dawo daga garinsu kaga komae xae xo min da sauki" Ikram tace "wani makaranta Anty?" Mami tace "school mana" ta kauda kantantana xumburo baki bata dae ce komai ba amma a xuciyarta cewa take ni baxan je ba, Aliyu yace

"ban fa yi break ba Mami" Mami ta galla masa

harara tace "to me xan maka, ina mutane gidan

ku suke" yyi dariya, ta kama hannun Ikram suka

wuce sama, ruwan dumi Mami ta hada ma Ikram

tayi wanka da tafito Mami ta shafa mata mai ta

fito mata da wasu hadaddun riga da wando ready

made ta sa mata, ba karamin kyau Ikram tayi ba,

Mami ta daure mata gashinta da ribbons, sae

murmushi take tana kallon Ikram cike da

sha'awa, Ikram kam duk hnklinta na gun taje

gurin Aliyu kar ya tafi ya bar ta, suna saukowa

kuwa tayi gunsa da gudu a dinnin yana break, ya

ajiye cup din hannunsa ya wara manyan idonsa

yace "waw my Ikram" ta shiga masa juye juye

tace "nayi kyau?" jawota yyi yana kallon

kyakkyawan fuskarta ya daura lips dinsa kan

goshinta, cikin tsawa Mami[truncated by WhatsApp]


[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar

23.....

Mami ta kalli Ikram tace "ae kin iya karatu ssae ko Ikram?" Ikram

tace "eh mana, kije ki tambayi Ammina ma, amma fa ni baxan yi

karatu ba a nn" principal din ta mike ta kama hannun Ikram tace

ma Mami tana xuwa suka fita, ba a dau lkci ba Principal din ta

shigo office din ta ci gaba da fadi ma mami ynda tsarin

makarantar yake, Mami na duba list din textbooks din da ta bata

wata teacher ta shigo da Ikram dake xumbure xumbure, principal

din tace "is she qualify 2 b in basic six" teachern tace "not at ol, i

wil advise dat she shuld...." da sauri Mami ta katse ta ta hanyar

cewa "dnt wrry, dats nt a prblm 4now, plss let her b in class six, i

wil get her a lesson teacher 2 make her catch up" principal din

tace "but yhu knw they wil b writtin their common entrance next

term" Mami tace "i knw Ma, just let her b in basic six plss nd i

assure yhu dat she wil catch up with others vry soon" da kyar

Mami ta samu ta lallaba principal din ta yrda aka bar Ikram a basic

six din, nan take Mami ta biya kudin sch fee da sauran abubuwa

gaba daya ya kama kusan dubu dari biyu, da yake tasan

Makarantar mae tsada ce ssae kudi enuf ta fito da, ta ba principal

hkuri kan baxata iya xuwa banki ba office xata ynxu don har ta

rubuta mata teller taje ta biya, nan aka ba Ikram uniforms har uku

da sport wears biyu, sae excercise books da text buks dinta daga

bookshop din sch din, sae da Mami ta tabbatar bbu abinda ya rage

komai ta siya ma Ikram don gobe tace masu xata fara xuwa, snn ta

masu gdya ta kama hannun Ikram suka fita xuwa gun mota, Ikram

tace "wnn Malamar tsoro take bani ni bana sonta naga tana da

katuwar bulala, kuma ni ina tsoron shi" Mami tace "ae idan baki yi

abun duka ba baxata doke ki ba Ikram, amma kina son Makarantar

ko?" Ikram tace "A'a ni bna son makarantar, lilon Makarantar kawae

nake so" Mami bata ce kmai ba ta bude mata mota ta shiga snn ita

ma ta xaga ta shiga, ta ciro wayrta ta kira Mai gadi ko Jummai ta

dawo, yace bata dawo ba, kasuwa ta shiga da Ikram tayi mata

siyayya na takalman makaranta da jakunkuna da safa, snn ta karo

mata kayan sawa ssae, suka kama hanyar gida don bata son xuwa

office da ita. A bangaren Ammi kam ba karamin tashin hankali ta

shiga ba da suka gano abinda Kawu na lado da Shatu suka yi, kuka

ssae ta dinga yi kmr ranta xae fita, Abban ikram kam tagumi yyi

yana kallon yayan nasa, Na lado yace "kun wani sa ni gaba daga

mai kuka sae mai tagumi, ko ban isa da Rabi bane," Ammi kasa

cewa komai tayi sae kuka take tana kallon Mai gidan nata, a

sanyaye Abban Ikram yace "A'a ba wae baka isa da Ikram bane

yaya, amma fa mutanen nn ba saninsu muka yi ba da inda suka

kae Ikram, ynxu yaya bamu san halin da yarinyar nn ke ciki ba......"

tsawa Na lado ya daka masa yace "ohh munafukar matar taka ce

ta kitsa maka abinda xaka fada min ko, to sayar da Ikram nayi

karewarta knn, kuma ku tashi ku ban waje" kuka ssae Ammi ta

fashe da tace "wllh wllh Na lado ka fito min da ya ta kar in kai ka

kara police station," Shatu ta leko tace "gidan yari xaki kaisa ba

police station ba karewarta knn, yo idan bnda tsiya meye abun

damuwa don mun raba ki da masifa, ke fa da kanki kinsha fadin da

da ynda xaki yi da yarinyar nn da kin yi, to ynxu ga shi Allah ya

kawo ynda xa ayi da ita, har ma xa a dinga baku kudi duk wata"

Ammi ta mike tana huci tace "to mu xuba da ku wllh sae kun fito

min da ya ta mugaye kawae axxalumai mara su tsoron Allah,

meyasa baku dauki shafa kun basu ba, ae wllh bbu ubanda xae

hanani daure ku" tsawa Abba ya daka mata yace "kina da hankali

kuwa Aisha shi yayan nawa kike fada ma mgna hka" tayi masa

wani mugun kallo tace "xa ko kasan bnda hankali yau," tana kai wa

nn ta fice, Abba ya dinga kiranta ko juyowa bata yi ba, na lado yace

"to kai ma tashi ka ban waje munafuki kawae, sae kace ba kai ka

tsara mata abinda xata fada ba, Rabi ce dae na bada ta birni duk

sati xa a dinga kawo maku ita ku gani" Mikewa Abba yyi a sanyaye

ya fice daga gidan. Karfe shidda na yamma Shatu na xaune tsakar

gida tana kulla kuka, Yakumbo da Ammi da wasu yan sanda uku

suka shigo gidan, mikewa Shatu tayi tana salati ta shiga kwala ma

Na lado dake bayi kira "Malam, Malam fito" ya fito rike da yar

butarsa yana cewa "ni fa ban son kira hka kmr wata tsohuwar

makauniya" sororo ya tsaya kallon yan sandan, Yakumbo na nuna

su tace "su ne wa innan, maxa ku kame shegu barayi" Na lado yyi

kofar gida da gudu wani dan sanda ya chafke shi, yan sandan suka

ja shi suka fita hka ma Shatu da sae xaxxare ido take. Ikram na

xaune gaban Makeken plasman dake falo tana kallon cartoon da

duk hankalinta, Mami ta sauko kasa tare da Khaleel da fuskarsa ke

daure ya nufa dinnin, Kashe TV Mami tayi tce "karatu xa kiyi Ikram

gobe xa ki sch" Ikram ta xumburo baki kmr xata yi kuka tace "ni

Anty ki kunna min" Mami ta dagota tace "bari to ki gama karatun

kinji dota" textbuks din hannunta da excercise buk ta ajiye kan

Kujera tana kallon Khaleel tace "son idan ka gama gashi kayi

assistin dinta don Allah ya[truncated by WhatsApp]

[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~  By Khaleesat Haiydar      25.... Washegari da asuba Mami ta gama shirya Ikram cikin kayan makarantarta, ba karamin kyau Ikram tayi ba cikin dark nd light pink uniform dinta, na cikin light, pinafo din dark, sae ddi take ji ta kasa barin gaban madubi bayan Mami ta gama parkin din mata dogon gashinta da ribbon, tana tsaye gaban mirror har lkcn Mami ta shigo dakin rike da breakfst dinta bayan ta ajiye na Khaleel a dinnin, Mami tace "maxa ki cinye kafin in fito Ikram" kai kawae Ikram ta gyada mata ta xauna gaban break din, Mami ta shiga wanka. Ikram ta mike ta bude kofar a hankali ta fice tayi dakin Khaleel, tsaye ta gansa yana knot din tie dinsa ta washe hakora tace "yaya Khaleel nayi kyau" grin din hakoransa yyi yana mata mugun kallo cikin tsawa yace "get out kar in taka ki, ni kike tambaya kin yi kyau" Ikram ta murguda masa baki tace "shi yasa bana sonka, kuma ko kyau ma baka yi ba, wnn abokin nawa ya fi ka kyau" kanta ya yo ta fice a guje tayi dakin Mami tana kwala mata kira, yyi kwafa ya koma dakinsa, dariya ta dinga yi kmr wata tababbiya bayan ta shigo dakin, tayi mai isarta snn ta fara shan tean ta, ko da Mami ta fito ta gama, Mami ta hade rae tace "me ya fitar da ke? Baki ji ko Ikram" ikram ta dan turo baki bata ce komai ba, Mami tace "dauki kofin nn da plate ki kai kitchen" ba musu ta dauka ta nufi kitchen da su, Khaleel na xaune kan dinnin, ta hararesa ta koma sama da sauri, karfe bakwae da minti goma suka sauko da Mami tana goye da jakar makarantarta, Mami na kallon Khaleel dake xaune dinnin har lkcn tace "ka ba Mai gadi makulli, jummae ta kira ni tana hanya" bae ce mata komae ba har ta isa bakin kofa snn yace "Allah ya kiyaye," tace Ameen snn suka fita, gaban mota ta bude ma Ikram snn ta xaga ta shiga driver seat ta tada motar tayi warm dinsa suka bar gidan, har cikin makaranta ta shiga da Ikram ta hada ta da dari biyar kudin break nn da nn Ikram ta hade rae xata yi kuka wae ita baxata xauna ba, Mami tace "anjima kadan xan xo in dauke ki dota," a hka ta samu suka rabu ta kama hanyar office.  Ammi na xaune tsakar gida ta rafka uban tagumi sae kallon Abba da yasa ta gaba sae masifa yake mata, wae suje su sa a saki yayansa da matarsa da suka daure da ita da yayarta, sae da Ammi ta bari ya gama snn ta mike tsaye tana masa mugun kallo tace "su fara fito min da ya ta tukun, ae ko rance xanyi sae nayi naga karshen wa ennan mutanen wllh" a fusace Abba yace "kina da hnkli kuwa Aisha yayana ne fa" Ammi tace "na fi ka sanin wnn" tana fadin hka ta shige daki hawaye cike idonta don ba karamin kewar Ikram dinta take ba ko wani hali take ciki ynxu oho, su Na lado kuwa ana can station ana shan axaba, gashi bae karbi nmbr Mami ba kuma bae san gidanta ba da tuni ya fdi inda ikram take da wnn axaban da yake ci hannun yan sanda. Karfe hudu da minti goma sch bus ya ajiye Ikram a kofar gidan Mami, rana daya a sch duk ta rame ta ci kuka har ta gaji kmr warce bata taba xama a sch ba, ko dayake can gida karfe daya suke tashi daga sch, sae da teacher ta tabbatar Ikram ta shiga gida snn motar tayi gaba, Ikram ta karasa bakin kofar shiga gidan da gudu tana kwala ma Anty kira cikin kuka, Jummai ce ta fito tace "sannu da xuwa yarinya" Ikram ta shige gidan ba tare da ta kalleta ba ta haura sama da gudu sae dakin Mami amma taga ba kowa, saukowa tayi tana kuka tana kallon jummai tace "ina Anty" Jummai tace "tana nn xuwa yarinya xo kiyi wanka kici abinci kafin ta dawo" Ikram ta fasa ihu tana tsalle tana kiran Anty, da kyar da kyar jummai ta lallabata ta cire uniform tayi wanka snn ta bata abinci ta ci, tana ci kuwa tayi bacci nan kan kujera a falon, karfe biyar Aliyu ya shigo gidan sanye da kananan kaya, suka gaisa da jummai dake faman girki a kitchen snn yyi gun Ikram, a hankali ya durkusa gabanta yana kallon fuskarta, hannu yasa ya shafi fuskar ya kira sunanta murya can kasa ta bude idon da sauri, mikewa tayi ta xauna tana mitsike ido tace "ni kaina ciwo yake min" ya kamo hannunta yace "da gske, Ikram ta gyada masa kai" yace "kinci abinci?" ta gyada masa kai nn ma ya mike da sauri ya haura sama ya shiga dakin Mami sae gashi ya sauko da magani ya dauko mata ruwa a kitchen, ba musu ta karba ta sha tana yamutse fuska, yace "ya sch Ikram" ta bata fuska tace "ni baxan sake xuwa ba wllh bna son makarantar" shiru yyi yana kallonta, shigowar mota da yaji yasa ya mike da sauri ya leka yaga motar Khaleel ne, ya dawo ya xauna yana kallonta yace "sbda me Ikram" kmr xata yi kuka tace "malamar muguwa ce wllh" dariya Aliyu yyi yana kallonta, Khaleel ya shigo gidan ba tare da ya kallesu ba ya haura sama, Aliyu ya mike ya dagota yace "xo muje in gaya maki abu" ba musu ta mike da dan gown dinta iya gwiwa, Jummai ta fito da sauri tace "Dr Mami tace kar in bar kowa ya fita da ita wllh" yana murmushi yace "ae ba nisa xa muyi ba kuma Mami sae takwas xaki ganta ta tafi meetn," da dan damuwa tace "to ni dae ka rufa min asiri snn ka bari in canja mata kaya" yace "karki damu" bae kuma jiran me xata ce ba yaja hannun Ikram suka fita daga falon.

[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 26.... Garden din

gidan ya nufa da ita yana rike da hannunta, tace

"lah ina ne nn?" yana kallnta yace "garden knn,

fadi in ji" tace "garden" yyi murmshi yace "yauwa

Ikram" kan carpet grass ya xauna snn ya xaunar

da ita yana kallnta yace "me aka koya maki a sch

yau Ikram" ta bata rae tace "nima ban sani ba,

kuma ae baxn sake xuwa makarntar bama" yyi

shiru yana kallnta snn yyi murmshi ya kwanta kan

carpet grass din, ita ma ta kwanta tayi ruf da ciki

a gefensa tce "ka kawo min wnn sweet din nn" ya

juya yana kalln gashinta ya mike xaune ya cire

ribbon din da Mami ta sama ta yace "waw kina

da gashi mai kyau Ikram" ta xumburo baki tace

"abnda ma ni aske shi xance Anty tayi min, idan

tana taje min sae yyi ta min xafi" yyi murmushi

yace "Mami xaki dinga ce mata ba Anty ba kinji

Ikram" Ikram tace "sbda me" yace "sbda ba

sunanta Anty ba" tayi shiru tana kallonsa snn

tace "kai ya sunanka to" ya wara ido yace "au

baki san sunana ba Ikram" ta gyada masa kai ya

kamo hannunta yana kallon cikin idonta yace

"Aliyu ne sunana" tace "nima Aliyu xan dinga ce

mka" ya girgixa mata kai yace "yayana xaki dinga

cemin" tace "to bani sweet din yayana"

murmushin jin ddi yyi snn yace "to ki fara min

duk abnda nayi maki tukun" tace "to" ya daura

hannu kan dimple dinta ita ma tayi masa hka, yyi

murmushi ya daura yatsunsa biyu kan lips dinta

ita ma tayi masa hka, dariya yyi ya rungumeta a

hankali yace "I luv yhu bbyna" ikram ta wara ido

tana kallon fuskarsa tace "lah ni ba bby bace, ni

da na girma" kmr ance ya daga kansa sama yaga

Khaleel xaune cikin balcony din dakinsa laptop

gabansa yana kallnsu, suna hada ido da Aliyu ya

fashe da dariya har da sauka daga kan kujera

Aliyu ya mike tsaye yana kallonsa ya hade rae

yace "wats funny guy" mikewa Khaleel yyi ya

shige dakinsa yana ci gaba da dariya, Ikram ta

bude baki tace "lah ashe yana dariya, ni ban sani

ba" Aliyu bae ce komai ba ya xauna ya sauke

ajiyar xuciya yana kallonta yace "je dauko sch

bag din ki" ta mike da gudu tayi cikin gida, A falo

ta tar da Khaleel ya fito daga kitchen rike da cake

da juice a plate, ta wara ido alamar mamaki tace

"yaya Khaleel ashe dama kana dariya ni ban sani

ba" ya xabga mata harara yace "kinsan Mami

bata nn dukan tsiya xan maki idan baki shiga

hankalinki ba" ta harare sa tace "to ae yayana

yana nn" Jummai tace "lah ashe baku je da nisa

ba" Ikram bata ce komai ba ta wuce sama tana

murguda ma khaleel baki ya bi ta da kallo yana

gyada kai a hankali alamar xae yi maganinta,

yana nn tsaye ta sauko rike da jakar makarantar

ta, ya fixgota da karfi yace "wa kike harara"

muryar Aliyu yaji yana cewa "hey ka taba ta kaga

idan ban rama mata ba" Khaleel ya juya yana

kallonsa ya fashe da dariya yace "girma dae ya

fadi, wae yar cikin ka ka xaunar kke ce ma I Love

Yhu, na sha suprise dinka Aliyu, ina manyan

babes dinka" dariya ssae yake ya haura sama,

Aliyu ya ma rasa me xae ce masa ya bi shi da

kallo don bae yi xaton yaji ba, Ikram tace "ni

baxan taba son yaya Khaleel din nn ba sbda yana

da bad habit, yau a sch Anty tayi mana Moral

Education ta gaya mana menene Bad Habit" Aliyu

yyi murmushi ya dafa ta yace "yauwa kanwata xo

muje ki fada min me dame Anty ta koya maki" ya

karbi jakarta suka nufi garden din tana gaya

masa menene bad habit kmr ynda taji Anty tace

yau. Ikram na xaune a falo ita da Jummai tana

cin abinci bayan Aliyu ya wuce Mami ta shigo

gidan taje ta rungumeta da gudu tana jin ddin

ganinta, Mami tace "dota kinyi karatu da kyau

yau ko" Ikram tace "eh mana yayana ya koya min

assignment dina kuma na iya bari in kawo in

maki ki ga" ba karamin mamaki Mami tayi ba

ganin ynda tayi solve din Bodmas da kanta, tace

"Ikram wa ya koya maki wnn" Ikram tace "wnn

yayana din nn mana shi ya koya min, har da

dayan ma na iya bari ki ga" Mami na kallon

Jummai tace "Khaleel ne ya koya mata?" Jumma

tace "A'a doctor ne ya koya mata" Mami ta dan

yi murmushi tace "to ya kyauta" da daddare xa

su kwanta Ikram ta ishi Mami wae ita gun

Amminta xata, Mami tasan kewar uwarta take

ssae don hka ta shiga kwantar mata da hankali

tace "kar ki damu dota ran sati xan kai ki kinji"

da kyar Ikram ta yrda don har da kukanta Mami

ta hadata da wayarta tana ta danne2 daga nn

bacci ya dauketa. Cikin sati dayan da Ikram tayi

tana xuwa sch ba karamin mmki ta ba Mami ba

don bata manta duk abinda aka koya mata, duk

da da kuka take barin gidan idan sch bus ya xo,

snn kuma da yamma Aliyu na assistn dinta ssae,

Mami ta shiga neman islamiyyar da xata sata na

yamma idan ta dawo daga sch in yaso sae lesson

din da Aliyu ke mata ya dawo da daddare, ko

kadan bata bari Ikram tayi kallo sae dae ta

hadata da wayrta tayi ta dannawa daga nn bacci

ya dauketa. Ranar asabar Mami ta shiryata cikin

kananan kaya da hijab dinta tayi kyau ssae, cikin

jin ddi tace "Mami ina xa mu" Mami tayi

murmushi tace wajen Amminki xamu dota, tsalle

Ikram ta shiga yi tana jin ddi Mami ta hade rae

tace ban hanaki wnn tsallen ba Ikram" khaleel ne

ya sauko rike da car key Mami tce "na fa ce mka

xamu fita son"


[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~  By Khaleesat Haiydar      31......   Mami da kanta ta shimfida tabarma ta xauna tsakar gidan bayan sun shigo snn Ikram ta xauna gefenta don Ammi tsaye tayi inda take kmr an dasa ta tana binsu da kallo jikinta a sanyaye, sae da Mami ta gaisheta snn ta kirkiro murmushi ta jawo karamar kujera ta xauna tayi mata sannu da xuwa, Ikram tace "Mami da yaya Khaleel kika xo," Mami ta girgixa mata kai tana murmushi, ganin Ammi tayi shiru yasa Mami tace "to Mmn Ikram gani dae na dawo" Ammi tayi murmushi tana gyada mata kai tace "nayi masa mgna ya kuma amince Hajiya" Murmushin jin ddi Mami tayi snn ta shiga mata gdya, Ammi dae sae kirkiro murmushi take, Karfe biyar saura suka tashi tafiya, Mami ta ciro kudi mai yawa ta mika ma Ammi, Ammi tace ita ba don a basu kudi ta bata Ikram ba, dole yasa Mami ta mayar da kudinta, har sun kai kofa Ammi tace "to ajiyarki na jiya fa Hajiya" Mami tace "ni sbda Allah na baku mmn Ikram, ba don kun ban yar ku in rike ba" tana fadin hka ta kama hannun Ikram dake daga ma Amminta hannu kmr xata yi kuka suka fita, Ammi ta bi su da kallo hawaye na bin kuncinta, anya kuwa hkn da tayi dai dai ne, komawa tayi kan tabarma ta xauna jin kafarta sun kasa daukarta ta rafka uban tagumi tana hawaye, ta bada Ikram ba tare da yrdan Mahaifinta ba, to ko ya xa su kwashe ynxu idan ya dawo, wata xuciyar tace kawae tace nemarta tayi ta rasa, mikewa tayi da sauri ta fita ta kira Almajira ta basu kayayyakin abincin da Mami ta kawo suka nufi gidan yakumbo da shi tana biye da su a baya, tasan Babn Ikram na ganinsu xae san bada Ikram tayi ba nemanta tayi ta rasa ba kmr ynda ta yanke hukuncin xata gaya masa, tasan kuma Yakumbo xata fahimce meyasa tayi hka.   Dae dae wani makeken gida kmr na Mami driver yyi horn kmr ynda Mami ta umarcesa da yyi, aka bude masa gate ya shiga yyi parkn a parkn space, Ikram tace "Mami ae nan ba gidanmu bane ina ne nn?" Mami ta fito ta fito da ita snn tace "nan gidansu Aliyu ne" Ikram tace "waye Aliyu" Mami tace "baki san shi ba, wnn mai koya maki Home work" Ikram ta wara ido tana tafa hannu tace "lah yayana, to Mami dama gidanku ba gidansu bne, to shi ba yaron ki bne" Mami bata kuma ce mata komai ba ta ja ta suka shiga babban falon gidan, yan mata biyu da baxa su wuce 14 ba suka tarar xaune falon suna kallon korean Film, duk suka ta so cike da jin dadi suna ma Mami sannu da xuwa, Mami tace "ku dae ba ku gajiya da kallo ina Momynku" dayar da ke rike da remote tace "Momy ta fita amma ynxun nn tace xata dawo Hajiya ce kawae a sama" Mami ta xauna snn ta xaunar da Ikram gefenta tace "to bari in dan jirata, Mujaheed fa" yarinyar tace "ya je raka wani frnd dinsa ynxun nn xae shigo" Mami tace "yauwa gwara ya xo muyi ta ta kare tunda shi bae da mutunci, ina farida da Saiham" dayar yarinyar Aisha da bata ce komai ba tun bayan gaishe da Mami da tayi tace "farida na sama, Saiham kuma taje saloon" Mami tace "to yyi kyau ni ma daga wani wajen nake nace bari in biyo mu gaisa kwana biyu duk ba mu hadu ba" Seeyama tace "Mami ya Khaleel fa yana nn?" Mami tayi murmushi tace "yana nn, baya xuwa nn knn?" Seeyama tace "ae wnn ya khaleel din nn baya son mutane" Mami tayi murmushi kawae, yaran sae kallon Ikram suke, Ikram a hankali tace ma Mami "su waye wa ennan" Mami tace "duk kannin Aliyu ne Ikram" Ikram ta xaro ido tana kallonsu, Wata mata fara da baxa ta wuce Mami bace ta sauko kasa cikin shiga ta alfarma tana dan yamutsa fuska, tana kallon Aisha tace "uban me kike yi a nan Aisha" Aisha ta dan turo baki tace "to Momy ba kallo muke yi ba" ta galla mata harara tace "xo ki wue kar in bata maki rae, bbu TV dakinku ne magulmaciyar bnxa kawae" Mami na kallonta tana mmrshi tace "kwana da yawa Hajiya" Hajiyar ba tare da ta kalleta ba tace "lfya qlau" snn tayi hanyar kitchen tana taka tiles din kmr bata son takawa, Aisha na bubbuga kafa ta wuce sama, seeyama ta tabe baki ta ci gaba da kallonta, Ikram na kallon Mami tace "Mami wacece wnn, ni bana sonta" Mami tayi murmushi tace "mamar Aliyu ce fa" Ikram ta xaro manyan idanunta tace "wnn matar, A'a ba mamarsa bace muguwace wllh" Bude kofa aka yi wani kyakkyawan handsome guy da baxae wuce Khaleel ba ya shigo falon cikin kananan kaya yana danna wayarsa, bae lura da Mami dake xaune falon ba yace "seeyama xo kiyi min transfer don Allah banki sun ki bani kudi kuma ban son fita xuwa siyan kati kawae" kmr ance ya kalli gefensa suka yi ido hudu da Mami dake kallonsa, ya wara manyan idonsa ya juya mata baya da sauri yace "innalillahi," hanyar stairs yyi da sauri tace "ba sae ka gudu ba Jaheed dawo kawae" tsayawa yyi yana dariya snn ya juya yana kallon Mami yace "amma fa naji kunya Mami don Allah kiyi hkuri tare xamu tafi ma ynxu, jiya ma mun hadu da Khaleel......" ba shiri yyi shiru ya wara manyan idonsa yana kallon Ikram yace "waoww Mami ina kika samo wnn cute Angel din" karasowa yyi da sauri yana kallon Ikram dake kallonsa, Ikram ta juya tana kallon Mami tace "Mami yyi kama da yayana wllh, kalli shima yana da irin abun mu," ta nuna ma Mami dimple dinta.

[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 33.....

Mujaheed ya wara idonsa ya karaso gaban

Ikram ya durkusa ya kamo hannunta yace "da

gske pretty" tana washe hakora tace "ehh

mana, Allah kayi kama da shi" ta shafa sajensa

tace "shima yana da irin nn hka ma Yaya

Khaleel amma ni bana son yaya Khaleel din nn

sbda kullum...." kwace hannunta Mami tayi

daga na Mujaheed da ke kallonta wit much

interest, ta hade rae tace "bana son hka, maxa

nemi square root dinka" Murmushi yyi ya mike

har lkcn yana kallon Ikram yace "to Allah ya

baki hkuri Mami amma ina kika samo yarinyar

nn wllh she's so cute" ba tare da Mami ta

kallesa ba tace 'ya ta ce" dariya yyi yana kallon

Ikram yace "pretty ya sunanki?" Ikram tace "ni

sunana Rabi'a amma Ammi da Abba da 'yan

anguwarmu suna ce min Ikram, Ammi tace...."

hararanta Mami tayi tace "rufe min bakin nn,

ban hanaki surutu da wnda baki sani ba" Ikram

tace "to ae naga yana kama da yayana ne, in

gaya masa?" Mami ta rungumota bata ce mata

komai ba tana duban agogo, Mujaheed yyi

murmushi xae yi mgna sae ga Hajiya ta fito

daga Kitchen tana kallonsa tace "Mujaheed ina

sakon da na aike ka jiya" ya juya mata baya

yace "mum na ba Aliyu" tace "Aliyu na aika ko

kai" Mujaheed yace "ban samu xuwa bne shi ne

na basa ya siyo maki" tace "to yyi maka kyau,

ae da uwarka ce ta aike ka baxa ka ce mata

baka sami xuwa ba, dan rainin hankli" tana

kaiwa nn ta haura sama, murmushi yyi ya

xauna yana kallon Mami yace "wae Momy kike

jira Mami" dae dae nn Momyn ta shigo gidan,

ba karamin farin ciki tayi ba ganin Mami, ta

wuce sama da su xuwa bedroom dinta, sae

kallon Ikram Matar take, bayan ta kawo masu

ruwa da lemo da kayan ciye ciye take tambayar

Mami inda ta samo Ikram, Mami tayi murmushi

tace "sae dae munyi waya Hajiya," matar tace

"to shknn, oga Khaleel fa yana nn ko ya koma?"

Mami tace "aa yana nn, ni ban san irinsa ba

sau biyu nake cewa yaxo nn sae yace min ya

xo ashe baya xuwa daxu su Seeyama ke fada

min" Saiham ce ta shigo dakin tace "lah Mami

yaushe kika xo shine baki nemeni ba ko" Mami

tayi dariya tace "ae na tambayeki aka ce kinje

saloon" cikin girmamawa ta gaida Mami tana

kallon Ikram da ta rungume hannunta ta tsuke

baki ita nn fushi take bata gama gaya ma

Mujaheed sunanta ba. Karfe shidda saura Mami

tayi sallama da Momy tace xasu tafi, ta rakosu

har compound suna hira, Mujaheed da ke tsaye

balcony yace "Mami kawo in maki drivin din"

ba musu ta mika masa makullin ya nufi motar

yana yafito Ikram, da sauri ta bisa ya bude

mata gaban motar ta shige shima ya shiga

driver sit, snn ya juya yana kallonta yyi

murmushi xae yi mgna ta riga sa, tace "dama

Ammi tace min kawu na lado ne yace a samin

Rabi'a sbda sunan....." Mami ce ta bude motar

Ikram tayi shiru da sauri, Mami ta hade rae

tace "me kike yi nn Ikram" Mujaheed da sae

kallon Ikram yake yace "sunanta fa take gaya

min Mami" cikin fada Mami ta fara mgna "ni fa

bana son hka Mujaheed, bani makullin motata

ka fita wnn ae wlknci ne kke min" da sauri

yace "don Allah kiyi hkuri Mami ba fa ni na

tambayeta ba wllh" cikin tsawa Mami tace

mata "dawo nn" kmr xata yi kuka Mujaheed ya

bude mata motar ta fita snn ta dawo baya ta

shiga, Mami ma ta shiga, Mujaheed ya tada

motar yana murmushi suka bar gidan. Har

suka isa gida Ikram bata ce komai cikin motar

ba tana rungume da hannayenta, yana gama

parkin Mami ta kamo hannunta tana murmushi

tace "yhu re sulkn ko dota" Ikram ta sunkuyar

da kanta kmr xata yi kuka, Mujaheed dae sae

kallonsu yake, Mami ta rungumeta tace "to yi

hkuri dotana" fito da ita tayi daga cikin motar

suka yi cikin gida, Mujaheed ya kulle motar ya

bi bayansu. Kitchen Ikram ta nufa Mami tace

"ina xaki" ba tare da ta juyo ba tace "ni ruwa

xan sha" tana shiga kitchen din ta juya tayi

facin din bango ta shiga rera kuka a hankali

amma fa ba hawaye, sae faman murxa idon

take, muryar Khaleel taji a kitchen din yce "ke"

ta juya da sauri ta karasa kusa dashi kmr xata

yi kuka tace "yaya Khaleel shi ne Mami tayi min

masifa" sae kuma ta fashe da kukan tana

kallnsa, juyawa yyi kmr baxae ce mata kmai ba

sae kuma ya juyo yana kallnta yace "me kika

yi?" hawaye na bin cheeks dinta tace "wae don

wani mutumi ya tambayeni sunana na gaya

masa duka" Ya xaro mata ido yace "kika ce

masa sunanki Rabi'a Mama da baba da yan

garinku na ce maki Ikram, kawu na lado ne

yace a sa maki Rabi'a, ke bakya son kawu na

lado....." cikin tsawa yace "ko ba hka ba?" ta

marairaice tace "ehh amma bata bari na gama

gaya masa ba ae tayi min masifa" ya dan duka

yanda xae iya kallon fuskarta da kyau ya ce "to

daga yau aka sake tambayarki sunanki kika

tsaya bada lbrin kawu na lado sae na...." ba

karamin tsorata tayi ba don daga hannu yyi

kmr xae kwade ta tayi baya da sauri ta juya

xata fice daga kitchen din da gudu, ya rikota,

kuka ta fashe masa da ya daura yatsunsa biyu

kan lebbenta yace "shhii" ba shiri tayi shiru,

yace "kin ji me nace maki" Mujaheed ne ya

shigo kitchen din yana kallon ikram ya karaso

inda suke da sauri yace "pretty wa ya doke ki"

ta fashe da kuka ta nuna masa Khaleel tace

"gashi nn"

[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~  By Khaleesat Haiydar      34.....  Khaleel ya kai mata rankwashi yace "an dokeki din doluwa kawae" Mujaheed ya fixgosa yace "hw dare yhu, me tayi maka ka doketa beside ina abun duka a jikinta idan ba muguntarka bace ta motsa" Khaleel yace "wonderful yaushe ka xo Jaheed, hope ka taho min da files din jiya, yauwa taho muje ka ga abinda nake gwada maka jiya ka kasa gnewa" Mujaheed ya turasa gefe yace "nt until yhu tel her srry" fixgosa Khaleel yyi suka fice daga kitchen din, ta bi su da kallo tana murguda baki ta share hawayenta tace "duk bana son ku, ni nafi son yayana kuma sae na gaya ku dashi" tayi tsoki tana rike da dan kugunta, Jummai ce ta shigo kitchen din tace "Ikram maxa taho kiyi wanka ki ci abinci" ba musu ta bita tana rike da hannunta suka haura sama, dakin Mami ta shiga da ita don nan take wanka, Mami na xaune gaban computer sanye da medical glass dinta, Jummai tace maxa shiga kiyi wankan na hada maki ruwa, a dakin Ikram ta fara kkrin cire kayanta, ita dae jummai bata ce komai ba, Mami tace "No dota ban hanaki cire kaya kafin ki shiga wanka ba, maxa ki shiga ciki ki cire" Ikram ta dan turo baki ta shiga bayin. Karfe takwas da rabi na dare Mujaheed ya shigo dakin Mami, ko kadan Mami bata bar Ikram ta fita xuwa falo ba tun bayan shigowarta tare da jummai, har lkcn Mami na gaban computer, yace "aiki kike yi ne Mami" tace "wllh kuwa" yace "ae da ki ba Aliyu yyi maki" Mami tace "A'a wanda ke gabansa ma ya ishesa" xaunawa yyi yana kallon Ikram dake xaune can gaban Tv tana kallon cartoon sau uku Mami na cewa ta koma kan kujera ko kan gado amma da ta sake juyowa sae taga ta koma gaban Tvn ta xauna, hkn yasa ta kyaleta kawae, Mujaheed yace "duk kallon ne hka pretty" Ikram da bata ma san da shigowarsa ba ta juya tana kallonsa tace "ehh" yyi murmushi ya juya ya dan saci kallon Mami ya ga ta sauke glass ne tana kallonsa, dariya abun ya so basa yace "Mami xan koma gida wllh duk Khaleel ne ya bata min lkci hka" Mami tace "to Allah ya kiyaye ka gaida mum dinka" yace "tohm xata ji, Ikram ta so muyi sallama mana" Ikram ta juya tana kallon Mami ta ga kallonta take ta girgixa masa kai da sauri, ya juya yana kallon Mami, Mami ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, murmushi yyi, yyi ma Mami sae da safe ya fita daga dakin yana kallon Ikram dake daga masa hannu a boye. Sae a snn Mami ta bar Ikram ta sauka xuwa falo taje ta kalli cartoon din a can don news take son kallo ita, xaune ta tarda Khaleel a falon yana kallon American film ta karaso kusa da shi tace "yaya Khaleel, wae Mami tace ka sa min cartoon" yana gyada kai yace "to xauna, ana gama wnn xaki ga an fara cartoon," tace "to ae a Mbc3 ne ake cartoon ba wnn ba, hka Mami tace min" ya galla mata wani mugun harara yace "bace a nn, robot xan sa maki ba cartoon ba" da gudu tayi sama tana kuka ta shiga dakin Mami, Mami ta canxa mata xuwa cartoon tace kyaleni da shi je ki xauna kiyi kallonki, taje ta xauna da sauri. Karfe goma Mami ta kashe Tv bayan ita ma ta gama abinda take tace hau gado ki kwanta Ikram gobe da sch, kmr xata yi kuka ta hau gado ta kwanta a hankali tace "Mami yayana ban ganshi ba yau" Mami tace "bacci nace kiyi ba surutu ba" khaleel ne ya shigo dakin ya tsaya daga bakin kofa yana kallon Mami a sanyaye yace "gudnyt Mum" tayi murmushi ta mike xaune sanin bbu daren da bata xuwa dakinsa ta tabbatar ya ci abinci ko bbu abinda ke damunsa snn tayi masa gudnyt ta fito, amma tunda ta samu Ikram ta watsar da hkn, juyawa yyi xae fita tace "am srry son na manta ne hope kaci abinci" ya juya yana kallonta kmr xae mata kuka yace "duk kin watsar dani a gidan nn Mami, ban san ko gajiya kika yi dani ba" Ikram ta mike xaune tace "to kai karamin yaro ne?" dariya ssae Mami tayi shi kam tsayawa yyi kallon Ikram fuskarsa a daure kmr xai shaqeta, Mami ta kashe wutan dakin tace "to kai kaji, in ka fita ka rufe mana kofar dae"    washegari da yamma Ikram na xaune tana kallon cartoon bayan ta dawo daga sch, assignment din da Mami tace taje tayi da kanta ta ajiyesa bayan kujera gaba daya hankalinta na gun kallo ko kifta ido bata son yi sbda kallo, budewar kofar da taji don bata ji shigowar mota ba yasa ta mike tsaye da sauri kuma a tsorace a tunaninta Khaleel ne, don daxu da safe ca yyi sae ya mata dukan tsiya abinda tayi masa jiya da daddare, da gudu taje ta rungumesa cike da murnar ganinsa kmr xata yi kuka tace "yayana ina ka tafi na daina ganinka" ya durkusa gabanta ya daura mata lips dinsa kan goshinta ya sakar mata murmushi, ita ma hkn tayi masa ya rungumeta yace "Mami fa" tace "Mami tana sama tana danna computer," yace "wa ya gaya maki sunansa computer?" tace "Mami ce ta fada min da safe tace har da mouse, da emm" ta juya da sauri tace "bari in tuna" can ta kuma juyowa da sauri tace "keyboard, da c.p.u" ya rungumeta yace "waw kanwata yhu re vry sharp" hannunta ya kama suka nufi dakin Mami, bayan sun gaisa da Mami tace "jiya munje gidanku da Ikram kuwa" mikewa yyi da sauri ya xaro ido yace "gidanmu Mami? Da gske kike Mami? Ohhw God Meyasa kika kai ta Mami."

[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~  By Khaleesat Haiydar      35......  Mami tayi masa wani irin kallo tace "sae ka fadamin dalilin da baxan kai ta gidan naku ba" dauke kansa yyi ya koma gefen gadonta ya xauna ya dafe kan, Mami tayi tsaki ta ci gaba da abinda take, Ikram ta karasa kusa da shi ta xauna tana kallonsa kmr xata yi kuka tace "yayana ae baka da lfya ne ko" dagowa yyi yana kallonta, tace "kace Mami tayi mka Allura tana da shi dayawa" Mami tace "ina assignment din da nace kije kiyi ikram?" Ikram ta mike da sauri tace "Mami shi nake yi" juyawa tayi da gudu ta bar dakin ta koma falo, Aliyu ya juya yana kallon Mami a sanyaye yace "da baki kai ta ba Mami" Mami ta watsa masa harara tace "to ubana, gashi can kaje ka karasa aikin da nake a computer idan ka ga dama amma" tana fadin hka ta shiga saka kayan Ikram da Jummai ta goge cikin drawer, bai ce komai ba sae bin ta da yake yi da kallo, Ikram na sauka kasa ta koma kusa da TV ta xauna ta ci gaba da kallonta rike da assignment din da ta dauko bayan kujera, Khaleel ne ya shigo gidan ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta, bata ma san ya shigo ba ya kulle kofar ya shigo cikin falon ya karasa kusa da ita ya duka ya ja kunnenta ya rankwasheta yace "wa ya kunna maki TV?" mikewa tayi da sauri kuma a tsorace tana xare ido tace "lah ya Khaleel ashe ka dawo, ni ban san ka dawo ba" ya galla mata harara yace "nace wa ya kunna maki kallo" ta turo baki tace "nima hka na ganshi" ya kashe Tvn, snn ya fixge book din hannunta ya bude yana kallon assignment din da aka bata, H.C.F ne da L.C.M, ya kama hannunta ya ja ta xuwa dinnin yace "xauna nn" ba musu ta xauna tana xumbure xumbure, ya ajiye mata book din da pen yace "kafin in sauko kasa ki tabbatar kin gama idan ba hka ba sae na cire maki wnn katon idon naki" bata fuska tayi xata yi kuka ya xaro mata ido yace "au kuka xaka min, to yi in ga" ya ajiye briefcase din hannunsa yana kallonta yana jira tayi kukan, jawo buk din tayi ta shiga yin assignment din yyi kwafa ya dauki briefcase da suit dinsa ya nufi sama, ta bisa da harara tana murguda masa baki.    Hmm kuyi srry fa oo

[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~  By Khaleesat Haiydar

    36.......

 Yau Ikram ta cika sati uku gidan Mami, ssae take kewar Amminta don wani lkcn har kuka take ma Mami, kusan kullum cikin damunta take ta kai ta gun Amminta sae dae Mami tayi ta ce mata gobe don so take sae ta kara nutsuwa snn ta kai ta gida, ssae take catch up a sch har abun ke ba ma Mami mamaki ssae don bata yi xaton tana da ilimi hka ba ashe wasa ne yyi mata yawa da can ma, in ta tafi sch tun safe bata dawowa gida sae karfe hudu, tana dawowa kuma jummai xata yi mata shirin islamiyya driver ya kai ta ya koma ya daukota karfe shidda, awa daya Mami ke barin ta tayi kallo shima idan ta gama assignment dinta karfe goma kuma taje ta kwanta, cikin lkci kankani Ikram ta saba da sch dinta har ma da islamiyya ta daina kukan da take da idan xa'a kai ta wani lkcn ma ita da kanta ke fita jiran sch bus dinta, kullum Aliyu ke xuwa assistn dinta gun assignment da daddare wani lkcn kuma kan ya xo Khaleel ke mata idan ya ga dama, ko kuma idan baya son tayi kallo don mayyar kallo ce Ikram, Yau tana xaune garden da robobbin wasanta da Mami ta bata da yake ranar lahadi ce bbu makaranta, islamiyya kuma na safe ta je, ta cika wani roba da ruwa tana faman xuba kasa tana juyawa da wani icce nn ita tuwo take tukawa sae surutu take ita kadae nn ita Ammi ce, ga wani gwangwani ta yanyanka flowers ta daddaka shi da dutse ta xuba ciki da tumatir da Albasan da Jummae ta bata nn kuma miya tayi, Mikewa tayi ta dauki wani roban tayi hanyar tap din dake garden din tana surutu ita kadae xata debo ruwan da xata kwashe tuwan kasan da tayi wae, muryar Khaleel taji cikin tsawa yana cewa "kika bude tap din nn wllh sae na maki shegen duka, fita daga nn" ta juya tana kallon sama don yana xaune Balconyn dakinsa laptop gabansa yana kallon duk iskancin da take, bata fuska tayi kmr xata yi kuka ta murguda masa baki tana hararansa tace "to ba Mami tace ka kyaleni in yi wasa na ba ina ruwanka dani" ya galla mata harara yace "to bude ki ga abinda xan maki, wawiya kawae kaxama, kuma na gaya maki sae kin cinye duk jagwalgwalan da kka yi a nn, ina nn xaune ina jiranki" sanin Mami ta fita kuma xae iya saukowa ya mata duka yasa ta murguda masa baki tana rike da kugunta tayi tsoki ta koma gun kayan wasanta ta ci gaba da tuka kasar ta tana cewa "ko ina ruwansa da ni ma oho" mikewa ta kuma yi tayi cikin gida ta samu jummai a kitchen tace "mama jummai ki bani leda xan kwashe tuwona" bbu musu jummai ta dauki ledoji ta bata sanin ko da Mami na nn ma baxata hanata ba, ta karba ta fice daga falon xata koma garden taji an bude gate, Aliyu ne ya shigo gidan sanye da kananan kaya ta wara ido taje da gudu ta sameshi tace "lah yayana ina motarka" shi ma ya wara mata ido yana kallonta daga sama xuwa kasa skirt ne karama jikinta da riga show me yhur bck, Mami ta daure mata dogon gashinta da ribbons, ya durkusa gabanta yace "motata na gida bby, meye wnn a hannunki" ta kamo hannunsa tace "xo kaje ka ga tuwon da na tuka ynxu ina son in kwashe a leda" ba musu ya bi ta suka shiga garden din, ta ja sa har xuwa gun kayan wasanta, ya yo waje da ido yace "meye wnn Ikram" ta kanne masa ido tana dariya tace "baka san ina da kayan wasa ba ashe, ae mami ce ta bani su duka shine nake dafa abinci da su, ynxu ma tuwo da miya nayi irin ynda Ammina ke yi" ta durkusa kusa da roban jikakken kasanta tace bari kaga yanda xan dinga kwashewa, xaunawa yyi gefenta yana kallonta, ta shiga kwashe kasan expertly a leda tana mulmulawa tana ajiyewa kan wani tray, shiru yyi hannayensa a cheeks dinsa yana kallonta yana murmushi har ta gama kwashe kasarta ta wanke roban ta ajiye snn ta jawo gwangwanin miyarta ta sa cokalin miyan da Mami ta bata ta jujjuya snn ta dauki wani roba ta shiga xuba miyar flowern ciki tana gamawa ta daura gefen tray din ta dauka ta ajiye masa gabansa tana washe hakora tace ga abinci nn nayi maka, da ace nice mama kai ne Baba, dariya ssae yake ita ma tana taya sa kmr wasu tababbu, yace "ca xakiyi da ace ke ce matata nine mijinki" ta tafe hannu tana dariya tace "eh eh da ace nice matarka to" yace "to ae ke xaki ban a baki matata" ta rufe fuskarta tana dariya snn ta bude ledan kasan yana kallonta yana murmushi, duk wnn abunda suke Khaleel ya tura laptop din gabansa yana kallonsu, ta dauki cokali ta kwaso kasan bayan ta bude ledan snn ta tsoma cikin ruwan miya tace "to oya bude bakin mijina" danne dariyarsa yyi ya bude bakin yana kallonta.

[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~  By Khaleesat Haiydar       37......  Aliyu ya kauda kansa da sauri ganin da gske xuba masa kasan xata yi cikin baki, ya wara idonsa yana dariya yace "ynxu Ikram sae ki xuba min wnn kasar cikin baki" ta bata fuska tace "to ba abincin da nayi bane, ni ba ruwana da kai kuma kai ba Mijina bne tunda baxa ka ci tuwona ba" Dariya yyi yace "kina son kashe mijinki knn ko bby" ta xaro ido tace "waya ce maka yana kashe mutane?" yace "to ke fara ci sae ki ba mijin ki ma ya ci" tace "to" snn ta kai cokalin kasan habarta ta manna kasar ta fara yi kmr tana cin abu tana lullumshe ido, sae dariya yake yana kallonta, tace "huhmm ddi yayana" khaleel ya girgixa kai yyi tsaki ya maida hnklinsa ga system din gabansa, Ikram ta murguda masa baki tace "meyasa kke kallonmu?" Aliyu yyi mmkin gninsa a balcony din, yana kallonsa yace "kai baka je birthday din Maska bne, tot tare ku ka tafi da Jaheed" Khaleel yyi masa bnxa ya ci gaba da danne dannensa ba tare da ya kalli inda suke ba, ikram tace "yayana kar muyi wasa da shi, kar ka kara masa mgna kaji" murmushi Aliyu yyi yace "to bbyna" ta kwashi robobin wasanta ta nufi famfo da su tace "xo ka taya ni wanke wanke oya" ba musu ya bita, sae da ta fara daga kai sama ta kalli Khaleel dake binsu da kallo, ta murguda masa baki ta bude famfon, tare suka dauraye kayan wasan da Aliyu ta daura su kan tray ta basa tace "kaje ka ajiye min su a can" nn ma ba musu ya karba ya kai su inda ta nuna masa, ta gama wanke hannunta snn taje ta dauki takalminta tasa ya karaso kusa da ita yace "Mami na ciki bby?" ta girgixa masa kai tace "tace min xata tafi meetn," ya kama hannunta yace "to mu shiga ciki" duka wa tayi da sauri tace "asshh" shima ya duka yace "me ya faru" kmr xata yi kuka tace "kafata ke min ciwo" ya durkusa gabanta yana kallon kafar yace "me ya same shi" ta daga kai tana kallon Khaleel dake kallonsu ta hararesa tace "ko ba faduwa nayi a stairs ba yaya Khaleel yace min Allah shi kara shiyasa yake min ciwo" hkuri ya shiga bata yana hura mata kafar yace "mu je in sa maki magani" kmr xata yi kuka tace "ni baxan iya tafiya ba ka goyani yayana" buda ido yyi yana kallonta yace "in goya ki" ta gyada masa kai ta koma ta bayansa don har lkcn yana durkushe gabanta ta haye bayansa, dariya yyi ya kwashe takalmanta ya mike tsaye, dariya ta dinga yi jin ta a sama, ta daga kai tana kallon Khaleel da ya gyara xama da kyau ya rike haba yana kallonsu, tayi shiga yi masa gwalo, Aliyu yace "to in saukeki hka mu tafi ciki" da sauri tana girgixa kai cikin daga murya tace "A'a A'a ni ka tafi dani baxan iya tafiya ba" shiru yyi ya kasa tafiya, kmr xata yi kuka tace "mu tafi mana" yana juyawa xasu fita Mami ta shigo garden din tana cewa "Ikram na kusa fara dukanki tunda baki jin mgnata ba ca nayi ki dauko readern ki kiyi karatu ba kafin in dawo shine kika bar min shi a falo ko, to daga yau na raba ki.... " tsayawa tayi ta kasa karasa mgnr tana kallonsu, Aliyu ya sauketa da sauri yace "har kin dawo Mami" Ikram kmr xata yi kuka tace "Mami da daddare fa kika ce min xaki dawo, ae dare bae yi ba ynxu" Mami na kallon Aliyu a nutse tace "dis shud b d 1st n d lst tym da xaka kara shigo min gidana i tel yhu," cikin tsawa tana nuna masa hanyar gate tace "get out" shiru yyi ya tsaya yana kallonta, Ikram ta kamo hannun Mami kmr xata yi kuka tace "Mami me yayana yyi maki" hannayenta biyu Mami ta rike tace "me nace maki kafin in fita" ta turo baki tana kallonta, Mami ta kai mata duka a baya cikin tsawa tace "ba mgna nake maki ba" Ikram ta fashe da kuka tana kallon Aliyu, Mami ta ja ta xuwa wani flower ta karya branch karami tace "ba mgna nake maki ba, ki gaya min me nace maki daxu kafin in fita" Ikram ta tsorata ssae cikin kuka tace "kika ce in karanta Macmillian reader dina kafin ki dawo" Mami ta daka mata tsawa "to me ya hanaki, kuma ban hanaki wasa da maxa ba" tuni jikin Ikram ya dau rawa tana kuka tace "ni banyi wasa da maxa fa ki tambayi yaya Khaleel, ban yi wasa da shi ba" Mami na rike da hannayenta biyu tana shirin tsula mata bulalan hannunta ta nuna mata Aliyu dake tsaye har lkcn yana kallonsu tace "shi wancan na mace ne?" Ikram ta juya tana kallonsa tace "wayyo Mami ki tambayi yaya Khaleel shi ne ya xo ya sameni ina tuka tuwona" tsula mata bulalan Mami tayi a kafafuwanta, ta fasa ihu kmr xata tsaga gidan, Mami tace "daga yau na kuma ganin kina wasa da namiji sae na maki dukan tsiya, idan wasa kike son yi kiyi ke kadae ko kuma kije kiyi da Jummai" Mami ta juya tana kallon Aliyu a fusace tace "re yhu daft, i said leave! Wlh ka shiga hnklinka dani idan ba hka ba xan hadaka da ubanka" juyawa yyi ya fice daga garden din, kuka ssae Ikram ke yi tana tsalle, Mami ta kama hannunta xasu fita daga garden din tana kuka ta daga kai tana kallon Khaleel, taga yyi murmushi hade da mata gwalo, ta fasa wani shegen ihu ta kwace hannunta daga na Mami ta xube kasa ta shiga birgima tana cewa "wayyoo Mami kinga yaya Khaleel na min gwalo" da sauri har yana tuntube ya mike ya shige cikin dakinsa ya kulle kofar.

[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~  By Khaleesat Haiydar       39......  Khaleel dae bae ce komai ba sae murmushin da yyi, Mami ta dauki wayarta ta kira Aliyun sae da ya kusa katsewa ya daga tace "ae ni ban san kana da xuciya ba sae yau, to kadda Allah yasa ka shigo din, files kuma basa wajena suna gun Dr Musa" tana kai wa nn ta katse kiran, khaleel yyi dariya yace "wae me ya hada ki da Hydar dinki ne hka Mami, Aliyu ne fa" Mami bata tanka sa ba ta mike ta ja Ikram suka wuce sama. Yau Asabar da safe Mami ta shirya Ikram ita ma ta gama shirinta xasu can gidansu, Ikram sae murna take xata gun Amminta, suna fitowa falo Mami tace ma khaleel ya tashi ya kai su, ya juya da sauri yace "ina" tace "can gidansu Ikram," ya bata rae yace "haba mum wkend guda ma mutum baxae huta ba bayan duk wahalan da ya sha durin wkdayz" Mami tace "ehh baxa ka huta ba" bae kuma cewa komai ba ya mike ya haura sama ya canxa kananan kayan dake jikinsa xuwa manya snn ya fito rike da car key dinsa, suna fita parkin space Ikram tace "yaya Khaleel wancan motar xa mu shiga ba wnn ba don ni bana son shi" harararta yyi ita ma ta rama, yyi kwafa ya bude driver seat ya shiga ya tada motar ta xaga da sauri ta bude gaba ta shige, Mami kam na tsaye tana waya, ya daka mata tsawa yace "ke koma baya kar na kwade ki" ta murguda masa baki tace "ni nan xan xauna baxan koma baya ba" Mami ta shiga bayan motar tace "A'a Ikram gaba kika xauna" Ikram ta juya tana kallonta tace "Mami ni nn nake so" Mami tace "to yi xamanki" tayi ma Khaleel dake kallonta gwalo, ya dauke kansa ya gama ba motar wuta snn suka fita daga gidan, cikin minti arba'in suka isa anguwarsu Ikram tun bae gama parkn ba ta shiga kkrin bude motar ta fita ta kasa, Mami tace "to ae sae ki jira motar ta tsaya ko Ikram" yana gama parkn Mami ta bude motar ta fita, Khaleel ya riko hannun Ikram da sauri yace "tsaya Mami ta gama fita ke" juyawa tayi tana kallonsa tace "meyasa" bae ce mata komai ba, Mami na fita ya kulle motar yace to fita, ta dinga kkrin bude motar ta kasa, ihu ta fasa tana kallon Mami da bata san me ke faruwa ba har ta shiga gidansu Ikram, yace "bani kike ma gwalo ba ko, ae bbu inda xaki yau, baxa ki ga Ammin taki ba" ta fasa masa kuka tana bubbuga motar, fixgota yyi yace "to share wnn hawayen idan ba hka ba baxan bude maki ba, kuma kice baxa ki kuma min gwalo ba" ta turo baki ta shiga share dan hawayen fuskarta, handkerchief ya ciro ya mika mata yana kallonta ta karba ta shiga share hawayen, ta fara fyaco Majina daga hancinta ya fixge handki dinsa da sauri ya xaro mata ido yace "da handkerchief dina xaki share majina" murguda masa baki tayi tace "to ba ya ki fitowa ba ma" ya bude mata motar yace "watarana sae na cire maki wnn bakin idan kina min irin hka" ta fice daga motar ta kuma murguda masa bakin snn tayi cikin gidansu da gudu tana Ammi oyoyo. Xaune ta tarda Mami da Amminta a daki, ta xube jikin Amminta cike da murna tanai mata oyoyo, Ammi ta rungumeta kawae tana murmushi, Ammi tace "to kin je kin gaida su Altine ne," Ikram tace "A'a ni nayi sabon kawaye a sabon makaranta na" Mami tace "A'a je ki ki gaida su suma ae kawayenki ne Ikram" ikram ta mike tayi kofa har ta fita ta dawo da sauri tace " Ammi Abbana fa"Mami ce tace "yana kasuwa Ikram, je ki ki dawo sae mu je mu gaida shi" Ikram ta fice da sauri xuwa gidansu Altine, a bakin soro suka ci karo da Khaleel xae shigo gidan ko kallonsa bata yi ba xata fita ya fixgota yace "ina xaki" tace "to ba Mami bace tace in je in gaida tsohon kawayena su Altine ba" bae ce komai ba ya sake ta ta fice, snn ya shiga cikin gidan, ko minti biyar ba ayi ba Ikram ta dawo wae ta gaidasu, Ammi dae sae kallonta take tana mgna da Mami kmr ba Ikram dinta mara ji ko kadan ba, yini suka yi ranar a gidan duk da Ammi sae addua take su maxa su tafi kafin Abban Ikram ya dawo dan har ranar bae san ita ta bada Ikram da hannunta ba, duk da ya fara xargin hkn ganin bata wani damu kmr ynda ya damu ba, sae addua take a xuciyarta Allah yasa yan anguwa basu lura da ikram ba don mmn Altine ce kadae tasan abinda tayi, amma yau ta dau alkawarin xata gaya masa gskyan komai. Karfe hudu da rabi Mami ta kira Khaleel don ya fita ya xo ya maida su gida, cikin minti sha biyar ya iso Mami tayi sallama da Ammi tace xasu tafi gobe xata dawo ta dauki Ikram Ammi tace su tafi kawae ba komai. Gidansu Aliyu Mami tace Khaleel ya kai su, Khaleel yace "mami ni baxan fa shiga gidan ba ajiye ku kawae xanyi in tafi" Mami tace "to baka isa ba mara xumunci, har yara sun gane halinka kai dae ban san irinka ba wllh"  karfe shidda saura suka isa, shi dae Khaleel har lkcn fuskarsa a daure yake, Ikram tace "lah Mami mun taba xuwa wnn gidan" Mami ta fito da ita daga motar tace "eh mun taba xuwa" tana rike da hannunta suka nufi balconyn shiga falon gidan, Mami tayi sallama suka shiga falon, Aliyu da seeyama ne xaune falon yana gwada mata abu a laptop" seeyama kadae ce ta amsa sallaman a fili ta mike da sauri tana ma Mami sannu da xuwa, Ikram ta wara ido ganin Aliyu tace "yayana" da gudu tayi gunsa ta fada kansa ta rungumesa.

[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~  By Khaleesat Haiydar     40.....  Kallonta kawae Aliyu ke yi bae ce kmai ba, kmr xata yi kuka tace "yayana baxa ka min oyoyo ba" dauke kansa yyi, ya kashe laptop dinsa ya rufe, Ikram ta juya tana kalln Mami dake tsaye tana hararanta da sauri ta mike daga jikinsa a tsorace tace "wayyo Mami wllh na manta ashe na daina wasa da shi" siyama dae na tsaye sae kallnsu take, Mami ta karaso cikin falon tana kallon siyama tace "momynku fa siyama" siyama tace "tana sama Mami, wllh daxu muke ce ma ya Mujaheed ya kai mu gidanki yace mu bari gobe sunday ashe ma kina hanya" Mami tace "to sae ku xo goben ae bae baci ba, ina su saiham da Aisha" Siyama xata yi mgna Khaleel ya shigo gidan kmr mara gskya, ta wara ido tace "lah ya Khaleel" da gudu taje ta rungumesa, yyi murmushi yana kallnta yace "hw re yhu siyama" tace "wllh yaya baka da kirki ko kadan" hannu ya daura a bakinsa alamar tayi shiru, dariya tayi tace "wllh baxan yi ba" su saiham da Aisha ne suka sakko jin hayaniya downstairs, basu bi ta kan Mami ba duk suka yi gun Khaleel da gudu suka rungumesa cike da jin ddin gninsa, Ikram tayi kusa da Mami tace "Mami su waye wa ennan sun san yaya khaleel ne, amma gashi suna rungumesa baki yi masu mgna ba kuma ae shi namiji ne su kuma na mace ne" Mikewa Aliyu yyi ya dauki system dinsa yyi hanyar stairs Mami ta bisa da kallon mmki har ya haura, hka ma seeyama ganin bae gaida Mami ba, Momy ce ta sakko da fara'arta tana ma Mami sannu da xuwa, bude baki tayi ganin Khaleel tace "iyye yau xa ayi ruwan sama da kankara, Hajiya kice yau kin lallaba autanki ya biyo ki knn don nasan lallabasa kika yi" dariya Khaleel yyi ya gaisheta ta amsa tana dariya tace "Barrister Khaleel knn, bayan mamin ka baka san da Allah yyi ruwan kowa a duniyar nn ba, xumunci dae ba abun wasa bne" dukar da kansa kawae yyi yana Murmushi ya xauna Saiham taje ta dauko masa drinks a fridge, Mami tace "Hajiya fa" Momy tace "ina jin suna kitchen da Farida" Mami tayi hanyar kitchen din, Momy ta kama hannun Ikram tace "mu je sama bby" duk yan matan suka bi Ikram da kallo da ta juya sae taga kallnta suke, suna isa stairs ta murguda masu baki tana jujjuya masu ido har suka haura sama da momy, dariya suka shiga yi ssae Khaleel na kallonsu. ciki ciki Hajiya ta amsa ma mami kmr ko da yaushe Mami ta juya tayi hanyar stairs tana murmushi. Duk yan matan suka xagaye khaleel suna ta lbri suna dariya, a hka Hajiya da farida suka fito daga kitchen suka samesu, Khaleel ya gaida Hajiyar ta tsaya kallonsa snn ta tabe baki ta amsa tayi gaba abunta tana cewa "kai ka girma ynxu sae shekarar da ka ga dama kke xuwa gaida mutane, don baxan ce rana ba, sae ayi shekara ba a ganka ba duk ka tare gun uwarka" shi dae bae ce mata komai ba sae ma daure fuskarsa da yyi, ikram ce ta sauko kasa rike da can malt tayi gun Khaleel tace "yaya Khaleel Mami tace ka bude min" ya harareta yace "ni xan bude maki" kmr xata yi kuka tace "don Allah mana ina son in sha" karbewa yyi ya bude mata, sae da ya fara shan na sha snn ya mika mata ta fasa ihun da sae da gidan ya amsa tana kiran Mami, rikota yyi da sauri tana tsalle tsalle yace "ke baki san gidan mutane muke ba" cikin kuka tace "wllh sae ka biya min abu na" yace "to to bari in xuba maki nawa" ya bude drink dinsa da sauri ya xuba mata, ta karbe tana leka ciki ko gwangwanin ya cika, da sauri ya karasa cika mata ta share hawayenta tare da murguda masa baki ta yi hanyar stairs, su seeyama duk sakin baki su ka yi suna kallonta, Aisha tace "wae wacece wnn ya Khaleel" ya wara masu ido yace "nima ban sani ba ku tambayi Mami" bayan Magrib Mami tayi ma momy sallama xa su koma gida, Momy tace "kin ki cin abincin gidanmu Hajiya" Mami tayi murmushi tace ni dae a koshe nake suna fitowa corridor Mami ta bude kofar dakin Aliyu, yana kwance yana kallo tace "ina yini Aliyu" kallo daya yyi mata ya dauke kansa, snn can ciki ya gaidata, harararsa tayi tace "aa kadae amsamin gaisuwata, kuma me ya hanaka xuwa aiki wk din nn" ba tare da ya kalleta ba yace "nayi tafiya ne" tace gud, snn ta fice daga dakin, ikram ya gani durkushe gefensa tana kallonsa kmr xata yi kuka, ashe sae da tasan ynda tayi ta shigo dakin Mami na masa mgna, mikewa yyi da sauri ya dago ta ya rungumeta yace "bbyna ta ina kika shigo" tace "yayana ka daina xuwa gidanmu ni ina sn ka dinga xuwa" yyi murmushi ya dago kanta yace "Mami bata son ina xuwa gidanta Ikram" Muryar Mami taji tana kiranta alamar nemanta take, ta mike a tsorace shima ya mike ya dauko mata pack din chocolate ya mika mata snn ya manna mata kiss a kumatu a hankali yace "i love yhu Ikram" washe masa hakora tayi tana kallon chocolate din ya bude mata kofa ta fice tana daga masa hannu, har suka fito compound Mami bata daina harararta ba, Ikram ta rike hannun ya khaleel kmr xata yi kuka don bata son harara, wata mota ce ta shigo gidan suna shirin shiga tasu motar, drivern dake sanye da kayan soja ya fito da sauri ya bude sit din baya, yana rike da jarida ya fito daga cikin motar da gninsa ka ga Aliyu, khaleel ya juya da sauri yace "ya salam"


Post a Comment

0 Comments