Hotunan yadda jirgin sama ke zagaye da minista Sadiya ta na duba ɓarnar ambaliya

 Ministar jin-ƙai Sadiya Farouq na shawagi a cikin jirgi inda take duba irin ɓarnar da ambaliyar ruwa ta haddasa sakamakon ɓallewar madatsar kainji.


Ministan kasa da Muhalli a Mozambique, Ivete Maibasse ta ce an samu ragi da kashi 70 cikin 100 na farautar giwa ba bisa ka'ida ba.

Ta ce hakan baya rasa nasaba da irin matakan tsaro da aka inganta domin kare wurin da dabobbin ke rayuwa.

"Kafin 2014, ana rasa giwaye 1,200 a shekara," a cewarta, ta kara da cewa adadin ya ragu zuwa 360 a shekara tsakanin 2015 zuwa 2019.

Ministar ta ce Niassa Reserve, yanki mai tsaro mafi girma a kasar, babu giwa guda da aka yi farautar ta a cikin shekaru biyu da suka gabata


.Hukumar bincike ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu wani sauyi da aka samu a fanin kare haƙƙin bil adama a Burundi duk da zaɓen sabon shugaban ƙasa da aka yi.

Masu binciken sun ce har yanzu dimokuradiyya ba ta samu wurin zama ba kamar yadda ya kamata, sannan ana samun wasu shafaffu da mai da ba a hukuntawa, bayan shugaba Eversite ya maye gurbin Pierre Nkurunziza.

An naɗa ɗaiɗaikun mutanen da ya kamata su fuskanci hukunci kan manyan matsayi a gwamnatin Burundi.

MDD ta ce tana da shaida kan yadda ake tsare mutane da yadda ake azabtar da su da kuma cin zarafinsu kafin da kuma bayan zaɓe a watan Mayu


Dan wasan gaban Real Madrid Gareth Bale ya shirya tafiya ingila a ranar Juma’a domin kammala yarjejeniyar komawar sa Tottenham Hotspur.

Har yanzu ana sasantawa kan yarjejeniyar da za a cimma da Bale mai shekara 31, wanda zai je Tottenham a matsayin ɗan aro daga Real Madrid.

Ƙungiyoyin biyu har yanzu na kan tattauna wa wanda ake sa ran za su kammala nan bada jimawa ba, kafin tafiyar Bale Landan.

Tun asali ɗan wasan na taka rawa ne a Tottenham bayan komawar sa ƙungiyar daga Southampton a 2007, sannan ya koma Real Madrid ne a 2013 kan miliyan £85.

Ya zura wa Real Madrid ƙwallaye fiye da 100, sannan ya lashe mata kofin zakarun Turai sau hudu.



Post a Comment

0 Comments