Haramta shiga Amurka kan magudi: Kada ku raina mana wayo - Gwamnatin tarayya ,haramta-shiga-amurka-kan-magudi-kada-ku-raina-mana-wayo-gwamnatin-tarayya

 Gwamnatin tarayya ta bayyana bacin ranta kan jawabin da gwamnatin kasar Amurka da Birtaniya suka saki kan zaben gwamnan jihar Edo da za'a gudanar gobe da na Ondo da za'a gudanar ranar 10 ga Oktoba. Gwamnati ta nuna rashin amincewarta kan haramtawa wasu yan siyasa samun bizan shiga Amurka saboda zargin tafka magudi a zaben Kogi da Bayelsa da akayi a 2019. Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya a ranar Juma'a ta saki jawabin cewa gwamnatin Najeriya ba zata lamunci irin wannan abu da Amurka da Birtaniya ke kokarin yi ba. Ma'aikatar ta yi bayanin cewa akwai dokokin da Najeriya ta gindaya domin hukunta masu tafka magudi

Jawabin yace, "Zai zama tamkar rainin wayo da cin mutuncin yancin Najeriya ga wasu daga waje su yiwa yan kasarmu hukunci tare da hukuntasu ta hanyar haramta musu biza haka kawai." "Gwamnatin tarayya, musamman shugaban kasa, yana iyakan kokarinsa wajen baiwa hukumomin tsaro abubuwan da suke bukata na kudi, kayan aiki domin tabbatar da ingancin zabe." "Yayinda muke mika godiya ga gudunmuwar abokanmu musamman gamayyar kasashen Turai, muna kira ga kasar Birtaniya da Amurka su hada kai da hukumominmu ta hanyar basu hujjojin da suka samu na magudi domin hukuntasu da doka," 


Post a Comment

0 Comments