Gwamnatin Najeriya ta nemi afuwar ƴan kasar kan wani sabon fom din banki da ta fitar kuma ta bukaci su shiga bankunansu su cike..
Gwamnatin ta ce akwai kura-kurai a kan bayanin da tsarin cike fom din don haka ta goge sakon da ta wallafa na neman bukatar cike wannan fom din.
A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriyar ta wallafa sanarwar a shafinta na Tuwita inda ta buƙaci ƴan ƙasar da su shiga bankunansu su cike wani sabon fom.
Sannan masu amfani da banki fiye da ɗaya dole sai sun shiga bankunan sun cike sabon fom ɗin. Tsarin kuma ya shafi duk wani mai asusu a banki da suka haɗa da kamfanoni.
Cike sabon fom ɗin na banki wani sabon tsari ne da gwamnati ta ɓullo da shi da ya shafi haraji.
Sai dai a sanarwar da ta sake wallafa ranar Juma'a a Tuwitar gwamnatin ta ce: "Muna bayar da haƙuri kan saƙonnin tuwita da ba daidai ba (an goge su a yanzu) da aka sanya a jiya, kan cike wani fom na banki da bayanan mutane. Saƙon wanda yake shafin @firsNigeria ba kowa ya shafa ba. Hukumar karɓar haraji ta FIRS za ta fitar da bayanan da suke dai dai nan ba da jimawa ba.
Fusatar da ƴan ƙasa tun farkon sanarwar
Gwamnatin Najeriya ga alama ta fusata ƴan ƙasar a shafukan sada zumunta kan wata sanarwa da ta fitar a Tuwita, inda ta tilasta cike wani fom a bankuna.
Da fari gwamnatin ta ce tana buƙatar bayanan ƴan Najeriya a sabon fom ɗin daga cibiyoyin hada-hadar kuɗi domin aiwatar da ƙa'idojin da suka yi daidai da dokar haraji ta 2019.
Gwamnatin Najeriya a cikin sanarwar, ta yi gargaɗi cewa za ta ɗauki mataki ga duk wanda bai je ya cike sabon fom ɗin ba. Matakin kuma ya shafi cin tara ko kuma toshe asusun ajiyar mutum ko kamfani.
Wannan sanarwar da gwamnatin Najeriya ta fitar ba ta yi wa ƴan ƙasar daɗi ba inda suka dinga tsokaci na martani ga sabon matakin.
Wasu ƴan ƙasar na ganin akwai tsoffin tsare-tsare na tantance asusun ajiyar mutum da ya kamata gwamnati a ce ta yi amfani da su, musamman lambar BVN da lambar haraji ta Tin da kuma katin shaidar zama dan ƙasa waɗanda suke ganin duk suna iya sawwaƙe wa gwamnati ba sai ta ɓullo da wata sabuwar hanya ba.
0 Comments