Dutsen cikin ruwa pg7 hausa novels

 DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡

                 *Na*

      *Haleema G Khaleel*



           *98-99*


~~~Haka akai biki aka gama cikin farin ciki da Annushuwa, su Husna da Hassan shigar sababbin kaya akai tamusu. Yara masu kyau dashiga rai, kowa sansu yake duk inda suka shiga kamar kasace kagudu abin gwanin ban sha'awa.

Inna nasa k'afa suma suna sauke tasu ko ina suna biye da ita sabida Mamynsu Hauahin kowa takeji jin ance "bazata tafidasuba kosu koma gidan Kakanninsu, duk dashi a 6angarensa bashida matsala Sulaiman ya amince zai Rik'esu koba komai Rik'on Maraya Ladane kuma D'A NAKOWANE. Amma iyaye sunce sesun duba labarin. Hakan yasata 6acin rai.


  Sharar hawaye take akai-akai yaranma ko kallansu batayi.

  Washegarin ranar lahadi. Daga cikin yayunsu mata Anty Husna ma tabi wanda zasu gidan Samiha suka tafi gidan Amaren dan k'ara gyagygyarawa kafin akai Amaren.


  K'arfe uku na yamma agogon Nigeria Niger da Chad. Shirye shiryen kai Amare Juwairiyya da Samiha ake ana la'asar za akai kowacce gidan Mijinta.


  Inna dai bata tankaba ganin ita Naja'atu  se shirye, shiryen fita take da alama 'yan kai amarya zatabi. K'anwar Babansu Gwagwgwo ta Getso  tashigo ganin Naja'atu tana fesa Turare yasata cewa "Hala kai Amarya zaki kema?" Sunkuyar dakai tayi "Ah Gwaggwo dan Allah kuje dani" cike da shagwa6a tai maganar hadda langa6ar dakai.

 Dariya sukayi 'yan d'akin. Gwagwgon takuma fad'in "Ai tafiya dake babu matsala mutuk'ar dayaddar Mijinki maizai hana mutafi dake, tunda ke tariyar ba yanzuba." Ai jitai kamar tasa ihu! Matar wansu dasuke mutunci da ita tace "Maida wuk'ar yanzu da Aure akanki, inda zaki fita dole saida izinin ma'ana kin tambaya komai kinma sani ai, sedai k'arin bayani. Ki kirashi kisanarmai inya amince muje mudawo ko Gwaggwo?".


  Naja tai shiru tamkar bazatai maganaba. Ganin anata shirin tafiya kai amaren har anshiryasu ankaisu gurin Baban dasauran Matan Gidan sekuka suke. Yatsuna fiska tai kamar tahak'ura ma dazuwa, tai tunani to aikuma batada ranar zuwa k'ara taje yanzu ayama.

  Kiran layinsa tayi seda tai Ringin Hud'u  yad'aga "Ran Gimbiyata kuma Amaryata yadad'e!" Rasa maizatace tayi dabara tafad'o mata tace "Tare dakai fatan kana lafiya?"

  "Alhandulillah, muna lafiya dani har Matata dakowama."

   "Uncle mai Zane"

"Na'am Mamyn uncle mai zane"

  Shiru bawanda yakuma magana sai numfashinsu dake shiga kunnuwan junansu.

 "Dama wai zanbisu kai Amarya shine wai Gwaggwo tace sena tambayeka" tafad'a harda cuno baki kamar anmata dole.


Dariya Sulaiman yai sosai lallai Matar tasa 'yar daruce ko rigima zaice. Jin yana dariya taji inama bata kiraba, kamar takashe wayan taji sedai koma takashe abanza kiranta zaikumayi. Taji yace "Tajirashi yazo yakaita dakansa danba mai kallrmasa kayansa"

  "Haba Uncle ga Jama'anan muna zuwa zamu dawo damafa Gwaggwo zamu."

  Duk yadda tabi k'iyayi dole shid'in yazo yakaisu. Samiha ita banisa cikin Unguwarsune. Juwairiyya itakuma aka kaita Hausawa. 


Semuce Allah bada zaman lafiy da k'azantar d'aki amma bata sharaba.


  Exams in su Naja tazo shikansa Angonnata Sulaiman sarara mata yai dayin Waya. Dantasamu tai karatun final Exams inta. Dataimakon Allah suka kammala exam inau da makarantarma duka sejiran sakamako.





© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜

[2/18, 10:52 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡

                  *Na*

     ® *Haleema G Khaleel*



10 jan 2017


               *100*

                  🔚



*_But if they intend to deceive you. Then sufficient for you is ALLAH. It is he who Supported you with his help and with the believers._*


~~~Tunda tafara exams Sulaiman ke kaita yadawo da ita harta kammala.

   Watarana yad'aukota daka sch suntsaya a _Go slow_ a junction mutane se hada-hada, suke. Un expected taji anrik'o hannunta abinda Sulaiman beta6a mataba, dagashi har ita wani _Haptonasty Reaction_ sukaji sosai yakuma rik'o hannunta ganin abinnasa nakuma k'aruwa cike da shagwa6a ta turo baki "Allah kaban tsoro kuma sena rama" dariya sosai tabashi yadda bakinta ke motsi da shagwa6anta ya birgeshi yace "to ai nariga nabiya dan wannan kawai, barikiga kad'an daka ciki..." Gaba d'aya ya janyota jikinsa yafara Sumbatar bakinta cikin nutsuwa k'amashin Air freshner motar da Turarensu suka had'u suka bada wani Sanyayyan k'amshi mai Sanyaya zuk'ata. Hakan yakuma ingizashi yakuma rik'ota tako ina aikamata zazzafan sak'o yake yanakuma shafota.


  K'arar horn d'in da ake yimusu yayi yawa, dole yahak'ura. Saurin komawa mazaininta  Naja tayi d'ankwalinta dayazame tagyara had'eda mayafinta. Allah yasa Motar da Tinted, nawaje bazega nacikiba amma naciki naganin nawaje.

   Sunkuyar dakai tai tana wasa da abin mayafinta, tafiya suka cigaba dayi. Jefi-jefi yana dubanta yana sakin wani k'ayataccen murmushi dake k'aramasa kyau da kwarjini.


 Sunkusa kaiwa gidansu Naja'atu yai Parking dai-dai gurin wasu masu nama wanda anan suke siyan Nama kowane iri kakeso zakasamu agurin "Haleema Suya Spot" fita yai daga motan yace "yana zuwa."

  Binsa tai da idanu aranta tana tunanin dama haka Sulaima  yake shima d'an soyayyane, murmushi tai tana kuma tuna abinda yawakana mintina kad'an dasuka wuce.

      Bedad'eba yadawo da ledoji a hannunsa. D'aya yasa abayan motar, leda biyun kuma ya d'oramata akan cinya yad'ora dacewa "Ga Tsiran Tsira da Soyayyanan da Kilish, dukda ni nasan tawa a Safe content take."

   "Kai Uncle wannan Confidence haka"

 Dariya sukai duka yaja motar yak'arasa da ita gida sukai sallama yawuce dan cigaba da shirin taryan Amaryassa.


  Kwana biyu da gama Exam inta, Babansu yasa dole tatare asatin fad'a sosai yamata. Hassan da Husna karma susata kuka aka kaisu gidan kakanninsu. Maman aranta taso datana dawani babban d'a Namiji ya auri Naja'atun takasance cikinsu. Yanzuma addua da fatan Alkairy suka mata. Daga canma gidan Yaya Yusra aka kaisu yar Usman Mahaifinsu.


  Ranar Jumu'a k'arfe Hudu da rabi, kamar yadda akakai sauran 'yan uwanta. 'Yan uwa da abokan arzuk'a nakusa suka rakata gidan Mijinta akaro nabiyu dake d'an Agundi G.R.A. kuzo kuga wani _Mension_ da Arch Sulaiman yazana Tasweerar Gidan dakansa. Tundaga wajen gidan abin kallone, ido nabud'e harda hanci da baki ina kallon Aljannar duniya. 

   Varender ce dazata sadaka da Falo mai Girma d'auke da Kitchen, Dining Area Toilet sewani D'aki da toilet ahad'e. Daga gefe nagano Stairs dabasu dayawa duk cikin falon zubin ginin Indiawa. Inka haura Saman d'akunane manya guda uku da aka k'awatasu kowanne d'auke da Toilet aciki launi daban-daban se Varender tasama itama.

  Gidan gaba d'aya abin kallone 'yan kai amarya se san barka suke dasa albarka. Amaryan nagano cikin wata Gown zubin Qatar anrufeta sinkif se walainiya take da tashin k'amashi. Wani _Purple bedroom_ aka ajeta akan gadon da Fulalluka suka yawaita akai. Nikaina nadad'e ina santin d'aki (Lol).


 Kafin Maghriba kowa yatafi akabrta se wasu daga cikin dangin Sulaiman, kukan dataitayi hartagaji tabari har ango  yazo yasameta. Nafila suka gabatar tareda 'yan Tand'e-tand'e da lashe-lashe Nakaji da lemuka harda Tsiran Tsira da Soyayya, nima Uncle mai Zane yaban K'unshi d'aya yace nasanwa Miss xoxo da besty miss Fais ceeda, danyaga abimnamu iri d'ayane.

     Tsayawa nai abakin k'ofa gan Sulaiman yafara Rud'a Naja'atu da sak'on Soyayyarsa mai girma, fuskarsa yake kuma cusawa jikinta yana k'ok'arin rabata da kayan jikinta azafafe yake shafarta har tausayi sukaban, se numfashi suke saukewa suka Lula Kogin Soyayya mai Sanyi da Wahalar Nink'aya. Bashiri nai waje. Tsiran Tsira da soyayyan da akabam nawarware nafara ci. Kuma Makaranta ganaku. Hhhhhh.


************


BAYAN WASU LOKUTA


  ~~~Soyayya suke gwadawa Junansu mai tsafta. Dukda ZAMAN TARE zomu zaunane zomu sa6a. Yaransu masu kyau. Namiji tafara haifa maisuna Sufyan, Zuwa lokacin Hassan da Husna sunk'ara girm. Babu tayadda zakace ba 'yan gida bane, kowa sansu yake adangin Sulaima. Suntaso da soyayyar dangi da gata.


  Haihuwar Safiyya takumayi 'yar Babynta gwanin sha'awa mai gashi da ita ba inda tabaro Umman Sulaiman.

    Zama suke maitarin Aminci K'auna da Soyayya dakuma Hak'uri da Juriya akomi na Rayuwa dayasamesu medad'i ko akasin haka.


  Girki tagama takuma salla wanka wata Fitted Riga da Zani tasa na Atamfar Vilisco launin sky blue da maroon ahad'e tasha _Makeup_ sek'amshi take takuma cika sabida jegon datake 'yar Chafai da ita. Bazakace tayi yara Hud'u ba. Hutawa take ita kad'ai se Baby Safiyya(yadda su Hassan ke gayamata) sauran yaran duk taturasu gurin Umman, tagyare gidan dataimakon Sulaimam kafin sufita. K'amshin turaren data sa a electric burner ketashi cikin gidan. Safiyyan tana kan jikinta anmata gayu itama tasha hoda b'angala dariya take, dahaka tasamu talalla6ata tai bacci. Kusada ita takwantar da ita.

   Wani Novel take karantawa maisuna JANAN na (CHUCHUNA AYEESH) sallamar Maul'ainain(Ruwan idonta) taji Sulaiman nagano yakuma girma, Sumar kanashi se k'yalli take gawani Zagayayyen gemu daya ajiye wanda yakuma k'awata fuskar tashi da 'yan mata kerubibi, basusan Naja takafa ta tsare kuma taraka.


  Sama da ita yai sukaita zagaye falo  sannan yadireta. Tabaya yarungumota tsam har tanajin bugun zuciyarsa. Farar takadda yafito da ita yace tarik'e, akunne yarad'a mata "nagode Allah matata mai sa'ace gashinan and'aukeki aiki a General Hospital, so get ready nanda 1-2month zaki fara attend" wani juyi tai takuma rungumo mijinnata "Alhamdulillah Nureena, Wht a Suprise Habibi" nagode sosai mijina na har abada hak'ik'a KAINE GATANA kuma FARIN CIKINA. Allah yabiyaka da d'umbin alkairy yafarantama ka kamar yadda kakemana. Nakuma Godewa Allah yadda mukazama DUTSEN CIKIN RUWA DABAI SAN ANA RANA BA. Dagamu har Mahaifiyarmu tayi hak'uri muma tad'oramu akai. Tabbas Hak'uri Ribar Rayuwane. Ba irin nacin dabanyiba kabarni nai Aikin kak'i yanzu kaga nasamu amincewarka 100% nagode Allah dasamun miji irinka. In sha Allah zanyi aiki sabida Allah zantaimakawa Al umar musulmi kuma zankare DARAJA DA MARTABAR AURENA. Allah yak'aramana  lafiya dazama Lafiya.


 _Deep french kiss_ tashiga aikamasa sak'on kuwa yashigeshi yafara fita hayyacinsa yana ba Amsa danasa salon Sak'onnin. Cak yad'auketa sukai samansu d'aki sukai tareda rufo k'ofa. Dole najuyo nace asha soyayya lafiya.


    _Soyayya gaskiyace Allah yabarmu da masoyanmu ako ina suke_


Alhamdulillah!!!


Anan nakawo k'arshen wannan labari. Kurakuran ciki Allah kayafemana kazama jigonmu.


*$adarkrwa garekune*

Hafsat GL (Miss xoxo)

Masoyiwa kuma 'yar uwa

Aneesa A Rimi (Mamyn swty Ayman)


Haleematu Bukar Saje

     Kinfi kowa san littafinnan. Allah yabar k'auna da zuminci.


'Yan uwa marubuta inamuku fatan alkairy. Allah bar zuminci.


Duk wanda ya isa gareshi nagode sosai da tarin sak'onne da soyayyarku. Inbabu ku babumu. Allah yahad'amu da rahmarsa.

                      K'arshe.

Semun had'u asabon labari.......

Taku maik'aunarku

Haleema Sadiya g Khaleel.



Post a Comment

0 Comments