DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*39-40*
Cikin watannin da suka biyo baya Soyayya sike kaman yacinyeta yakeji, dama ita kunyarsa datake matuk'ar ji yake hanata maida masa da martanin irin zafafan kalaman dayake gaya mata.
Saranar biki akai nanda sati shida.
"Cin lokacin duk tabi tarame ga ciwan Inna yatashi jikin ya matsa mata, hakan yak'ara sanyayarwa da Naja'atu jiki.
"Duk dare kafin su kwanta bacci se Innar tai amfani da wanna damar taita musu nasiha gameda rayuwa. Tak'ara had'awa da bata makamai na addu'a yadda zata bi da arun dazasu taimaketa a sabuwar rayuwar dazata shiga.
"Ba abinda takeyi se kuka dazarar Innar tafara, gani take kaman wasiyya Innar take basu.
"To ganin Innar tafara warwarewa yasa hankalin Naja'atu kwantawa tad'an fara walwala har take samun damar karanta wasu daka cikin littattafan da Innar tabata:
*ZINAREN MA'AURATA*(MY ANEE😍)
*WASIYYATUL-UMMI*
*ZAMANTAKEWAR MA'AURATA*(DIDIN-ANEE)
Dawasu sauran littattafai dasuka shafi Rayuwar Aure da Tarbiyar Yara a Musulunci. Uwa tagari kenan.
"Gyaran jiki da akema Amarya kuwa Innar ce da kanta take mata tun tana jin nauyi har tasaki jiki take gyara 'yarta duk abinda yadace takemata.
Ana cikin turareta da Dukhan Usman yabugo mata waya, gata a lullu6e badaman d'aga wayan, dole samiha ta d'aga tasa mata a kunne, wata sassanyar dariya tasaki, meya gaya mata tace "nide baruwana a shagwa6ance, tama manta da Inna tana gurin, "mezan fad'ama to? Usman yace kina ina yanzu?
"Ina gida Allah yasa lafiya? Naja'atu tafadi.
"Yace to mekikeyi, kinmaci abinci kuwa?
"Naci mana mikagan?
"Nikam kinganni dangatan Mamata gyara miki ni take tayi. Tahad'an wani abu mai dad'i konazo nakamaki?
"La la! nids banceba baruwana. Hhhhhh
"Kinji ai ke kita kunya abundama kinkusa zama tawa, itadai shiru tamai yanatayi. Da abun ya ishetane tace ana kiranta.
Bawani kiranki da ake zaki kashen waya dai? Usman yafad'a yana murmushi abinsa. Kinga nama san komi ai da akeyi inma kin 6oyen. Sema na fad'o miki basu .......
"Ai bata yadda yakai k'arshen zancenba takashe wayan tanata murmusawa. Inna kuwa tabita da kallo tana me addu'ar Allah yasa Farincikinsu yad'ore a zaman dazasiyi.
Sunkuyar da kanta tayi ganin irin kallon da Innar kebinta dashi.
"Hada-hadar biki ta kankama, danma Amaryar tace it ba bidi'ar daza ai. Komi bisa tafarki za ayishi.
Ana saura kwana uku afara biki dangi na nesa suka fara zuwa mutan getso da Gusauma ba abarsu abayaba. Anty husna itada Ummi farin zuwa, suka cigaba da shirye,shiryen biki. Ita dai Amarya duk tak'ara sanyayewa abincima se Inna ta matsa mata takeci, setakoma dama Kunun Alkama da Madara. Dukdan kada tai rama dayawa. Bayan daffaffiyar Madarar shanu safe da yamma, tun bata iya shanyewa harta hak'ura shiyasa jikinta yai lumi, fatarta tak'ara santsi da taushi. Se shek'i take irin na Amaren da suka sha gyara.
"Ana i jibi d'aurin auren laraba dasassafe suka tafi k'unshi k'awatenta biyu Sady da Hafsa dan Nafisa a lokacin tayi nauyi. Juwairiyya Samiha harda Anty Husna suka tafi. Sun babbaje anata hira agidan lallen itakuwa seda taga anfara mata Jan lalle jikinta yakuma mutuwa ya tabbata takusa barin Inna da 'yan k'annanta jita hawaye masu d'umi sunabin kuncinta. Ganin haka itama Samiha tafara hawayen, Anty Husna kuwa mezatai inba dariyaba.
Tahau yimada fad'an ai Aure shine DARAJAR MACE. Kumashi Katangane babu wani mahaluk'i dazai kamiki wargi matuk'ar girman nan ya hauki, Rigar mutunci tamiki lullu6i duk inda kika samu kanki za abaki girma da MARTABARKI(Ummi-Aishha) ta D'IYA MACE(Khadija Sidi). Taita mata ita kuwa tak'ara rushewa da kuka. Sauran kuwa sukai ta tsokanarta. " ```Ke kikacw kinaso Amarya dabaki so da ba abaki shiba``` sukaitayi suna dariya.
"Meyi mata k'unshi kuwa dakatawa tai, tanata ganin ikon Allah. Wannan shagwa6a ta Amarya har ina.lalla6ata sukai tai shiru akagama mata lallen sannan suma akayiyyi musu.
"Bayan la'asar suka dawo mutane dayawa sun zazzo anata aikace-aikace, shigowarsu tasa aka kaure da hayaniya masu gud'a nayi abokanan wasanta suna tsokananta, kowa da abinda zaice aikuwa meneman kuka anjefishi da kashin awaki(inji hausawa) aikuwa tasa kuka. Seda wata k'anwar Babansu tazo tajanyeta, suka k'yeleta.
"Alhamis akaimata kamu irin na Al'ada, dayamma kuwa Walima akashirya Matan aure zallah se Ango da abokanansa. Kuzo kutayani ganin Amarya cikin shiga ta alfarma wata had'dd'iyar gown ce ajikinta gold colour da veil inta and'ora shi akan Top Knot inda akaimata jikinta rufe ruff light make-up aka mata ba k'aramin kyau taiba.
Malam Auwal Muhamnad da Malam Nazifi sunyi fad'akarwa sosai akan Aure. Da matakan daza subi subi su mallake junansu. Ba Boka ba Malam musamman ga ita Amarya da sauran mata. Walima cikim tsari ba hayaniya akai lectures sosai kan Addini. Kafin magriba akai addu'o i da neman Albarka acikin Auren. Akatashi itade Amarya Murmushi kawai take.
Sunda gida taga se had'a mata kayanta ake jikinta yak'ara mutuwa kamar anzare mata laka.
Ranar jumu'a Takama 24 ga watan 10 dubban jama'a suka shaida d'aurin Auren *USMAN BELLO GALADIMA* da Matarshi *NAJA'ATU ABDUL-MU'IZ AUWAL* bayan Sallar Jumu'a bisa rangwamen sadaki.
"Yinin biki aka zarce dayi bayan angwaye sunzo gaisuwar dangi akayiyyi hotuna. Amarya masha Allah kamar kasace ka gudu. Nikaina Didi ba k'aramin burgeni Amarya dashi kansa bikin yaiba. Lek'e nake tayi chan na hango su Haleema da Maman Ansar ansha anko. Sukuwa su Ukty yadda zasu Amshi take away suke. Nakallesu nace daga Take kuma se Away mukasa dariya dukanmu.
"Kuka take kaman ranta zai fice, anata shiryata wankanma dak'yar tayi.wankan turaruka Anty Husna da yar Babansu suka mata nakaima dabanne Aka nad'eta da yalwataccen Mayafi, gurin Babansu aka kaita yaimata iya tashi Nasihar yahad'a mata da Al-Qur'an charbi da babbar Dadduma, shima jiyake kaman yasa kukan.
Zagayawa da ita akai gurin sauran matan gidan suma sukasa Albarkacin bakinsu. Masu yada maganganu nayi kowa da abinda yadameshi.
"Itadai Inna k'arfin hali kawai take, "Allah yasa kishiga a sa'a abinda ta iya furtawa kenan. Tai musu alamada hannu aka wuce da Amarya. Deedat ya k'ank'ameta shi bazata tafi tabashahiba dayawa cikin mutan gurin saida sukai k'walla. Aka tafi da Amarya gidanta dake Sharad'a. Gidan ya k'ayatar da mutane danba k'aramin dukiya dangi suka narka mataba. Kowa yataho akabar ta daga ita sai halinta.
Semuce Allah ka d'anbaba mai k'uli-k'uli😜
Am so sry makaranta Abubuwan dayawa shiyasa baku ganin postn akai2. Inkomi ya gyaru zakunajina koda yaushe inasanku nima aduk inda kuke. Allah bar zuminci da k'aunar juna
Luv u all😘
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:48 AM] +234 703 962 5239: [25/11, 2:50PM] Didin Anee😍
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*41-45*
Abokanan Ango sukayo masa rakiya suka wuce bayan sunyi Addu'o i danemanmusu farinciki dazama lafiya mai d'orewa. Suka d'anyi ciye-ciyensu itadai akunyace tasha Ruwa shima danya matsamata ne.
Usman ya Umarci Naja'atu data sake alwala, cikin toilet in d'akin tai Alwala. Sallar isha suka fara sannan suka d'ora da nafila yai musu Addu'a mai tsaho sannan yai mata tambayoyi gameda Addini, yak'ara mata haske har Wankan Janaba yakuma mata bayani dayadda take samuwa. Kanta a sunkuye yake tamata bayani, wani tai magana wani tai shiru.
"Hannunta duka yakama, yajanyota jikinshi janye mayafin duka yayi yarungumeta tsam ajikinsa, dukda hakan bak'on abune agurinta jinta tai she is safe, zippin rigarta yasoma yana kuma cusa kanshi ajikinta cikin wani salo na soyayya dabata ta6a tunanin haka abin yakeba, nikam danaga lamarin yajuye abin yafi k'arfin ganina. Najuya nabasu guri.
Kunsandai bakyau bincike balle su wannan daya zama sirrinsu. Asuba tagari couples.
"Wayewar asabar, komi shiyayi mata, Addu'a kuwa tashata ba adadi takuma narkewa soyayya yake gwada mata wadda ba algus acikinta. Har sukai karin kumallan safe. nok'ewar da takene adan fusace yace "ai aikin gama yagama, abunda take kunyanma yagani tomiyai saura? Itadai murmushi kawai take tana k'ara sunkuyar dakai. Kujerar da take kai yadawo ganin ta mik'e yasashi janyota tafad'a kanshi. K'ok'arin zamewa take yak'ara k'ankamota.
Zauna ma kiji abinda zaki fara ma shine indai ina gida bakida gurin zama daya wuce nan, yanuna mata jikinshi. Kinsan body contact yanada tasiri wurin shak'uwa da mararin juna ga ma'aurata.
"Bugun k'ofar da akeyine yadakatar dasu, saurin mik'ewa tai daka jikinshi tayafa mayafi akan kayanta tanufi k'ofa danta bud'e, Abdullah ne da Shukra k'annan Usman mama ta aiko suka mata abincin Rana.
Guri tabasu suka shiga falon gaisar da Yayan nasu sukai, itama suka gaidata tacikasu da kayan mak'ulashe. Shukra Autar mama dasaurin sabo duk inda Najan tayi tana biye da ita. Har Usman ke tsokanarta tayi 'yar zaman d'aki, murmushi tai tace " aikam danaji dad'i daza abarta ta zauna.
Hararar wasa yabita da ita tareda fad'in "bakowa ma kink'i sakin jiki musha Luv inmu bare anka miki wannan mai surutun. Tace " aida Mama zata ban ita danaji dad'i.
"Hmm! Bakisan yadda Mama da Shukra suke bane bame rabasu se makarantar data shiga amma da ko ina suna tare, har yanzunma. Bata yadda tazauna agidan kowa se Mama. Dakwai sanda mama suka tafi Dabinai aka kaisu gidan Sisto, har yamma basu dawoba data fara kuka, kowa seda yaji haushinta Sadiq da Anas sukai zamansu harsun kwanta amma Shukra seda akada da ita gida k'arfe 10 nadare. Tana ganin Mama shiru kikeji.
Wai lallai kuwa naga ranar rabuwarsu da Mama. Allah sarki aikam dolene rabuwar ta fad'a tana rau-rau da ido.
Laah! Nibance kiman kuka ba kingama natafi. Yafice daka kitchen in yana dariya.
"Bak'i sukai tayi danginsa da nata danma ankakkamata abinci taita zuba musu faranfaran takar6i jama'ar. Tacikasu da kayan arziki.
Washe garima haka sauran danginsu dabasu tafiba sukazo ganin idan amarya.
"Anty Husna dasu Samiha se yamma suka tafi bayan sun gyaramata ko ina dasauran kayayyakin ta nagida, takuma ware wasu kayayyakin daza a rarraba harda wasu daka cikin kayan lefanta. suka turare mata gidan bayan anty Husna tasata tai wanka kwalliya sosai tasa tayi, dan yanzu bada bace dole sekina gyara ladabi da biyayya sannan zaki mallake mijinki atafin hannunki. Kud'an bamu guri tace dasu Samiha. Suka fita suna k'us-k'us batasan yaran zamani wasu sunmafi masu Auren sanin abubuwa ba.
Tacigaba dabata tip da dabarun zama da miji. Da sirrikan dazasu k'aramata Ni'ima batareda tayi amfani da abunda zasu cutarda itaba wanda batasan dame akaiba.
" *Sirrri na daya*:- kisamu kankana kiyayyanka kisa madara kinasha.
" *Sirri na biyu*:- kisamu zogale ganyansa da cocomber kiyi blending insu sekisa zuma da madara zakisha mamaki.
" *Sirri na uku*:- kwakwa dabino dankalin,hausa(kadan) farar shinkafa cukwi. Ki markada shiima kinashan ruwan. Inkinso kuma zaki iyayin na gari kina damawa da madara kinasha.
" *Sirri na Hudu*:-kihadasu gero mazankwaila dabino farar shinkafa kwakwa busasshiya busasshen muruci kida kasu siyi gari. Seki zuba man habbatussauda kihadesu guri daya. Yazama gumba.
" *Sirri na biyar*:-Man zaitun Man tafarnuwa Man Habbatussauda Miski kihadesu kina shafawa/insert.har maganin sanyi yikeyi.
"Taita gayamata abubuwa tana rubutawa wanima intayi harshi zasuna sha kaman inzata dafa shayi tazuba Minannas da kirfa aciki kunasha tare tsafta dayadda zata tsaftace gida da jikinta turaren bayan kunne daban nagashi, na matse-matsi cibiya. Shikansa mijin tadinga tsaftaceshi da kayansa yadda bazai taba zamada daud'a ba balle ajiwani unwanted odour yana tashi daga jikinsu.
Seda Anty Husna tacikata da abubuwan Alheri sannan suka tafi tanata kewarsu.
"Alwala tai tazauna kan akira sallah tanata lazimi abinta. Alamun bud'a k'ofa taji da sallama yashigo cikin husky voice insa, sansanyan k'amshin turare yaji yabigi hancinsa wanda bazai tantance ainayi wasu iri bane. Tun alokacin tafara aiki da hud'bobin Anty Husna.
Tasowa tai zuwa inda yake ganin kaya da ledoji fal a hannunsa tarusuna tamai sannu da zuwa takar6i kayan hannunsa janyota jikinsa yai yakuma jin wani k'amshi na musamman natashi. Eye ball to Eye ball suke kallan junansu yana mata wani sassanyan kallo da murmushi dashi kad'ai yasan ma'anarsu.
"Kinyi kyau yace da ita. Tallafota tai tagefansa suka k'arasa cikin falon, takai kayan inda yadace shikuma yai Alwala yatafi Masallaci.
"Cikin kwanakin Amarcinsu kawai sukeyi, seda tai sati sannan yakaita gidansu tagaida Mama da Abbansu. Dabinai kuma seta k'ara kwana biyu zaikaita taga danginsu nacan. Yanata rawar kai agaban Maman itakuma duk yasa tatakure, Maman bata k'ara ganin rashin kunyaba saida suka gama abinci tazubamai waishi da Matarsa zaici. Taitamai tsiya kuwa, itadai Naja sai murmushi kawai take ta duk'ar sa kanta. Da Maman tagaji da shak'iyancin nasa tace itama tatafi gano nata Mijin. Bak'aramin burgeta sukaiba yadda suke abunsu faran-faran kamar ba Mahaifiyarshiba. Komansu a kammale ba raini in social life. Taji sunk'ara shiga ranta. Musamman mijinnata. Habeeb injita da fad'a dukdan karta ambaci sunanshi. Yayi-yayi da ita amma taki, irin abubuwan dasuke k'aramata Martaba da Daraja agurinsa Allah yai yawa dasu, banda zazzafar Soyayyar dayake mata wadda bazata misaltuba. Agidan suka wuni se dare sannan suka tafi tinda bawani nisa garesuba duk Unguwa d'aya ce.
Kubiyo *Didin anee*😘 danjin ya rayuwar Naja'atu zata kasance bayan Aurenta???
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: Didin_Anee😍
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*46-50*
Da k'afa suka k'arasa gidan, shi yabud'e musu get in gidan tunda ba maigadi garesuba. Seda yakunna hasken gidan, Masallaci ya wuce dangabatar da Sallar Isha, ita kuma tashiga ciki, wanka tafarayi tagabatar da tata sallar, shafa tazaunayi rigar bacci tasa silk light blue, turare tafeshe jikinta dashi, kowana sak'o seda ta mulkeshi da nashi kalan turaren. Tahad'e gashin kanta da ribbon tareda d'ora hula aka. Jin shiru beshigoba yasata dawowa falon kallo takunna, Eternal Love take kalla a Ztv.
Bata dad'e da zamaba taji Karan rufe k'ofa Alamun yadawo kenan, da d'an saurinta tataroshi, kayan hannunsa ta kar6a tai kitchen, tana wawwarewa yashigo kitchen in. Yatayata aje kowane abu agurinsa ita kuma tayayyanka fruits in dayashigo dashi, tin a kitchen in yahau shan kankanar datake yankawa, dataga haka ta d'auke plate in kankanar ta ajemai na lemo dasauran kayan fruits in.
"Abun ma hakane? Yafad'a ashagwa6e kaman shine matar, ganin tayi blending in ragowar Kankanar, ido kawai yabita dashi tamarkad' kankanar tasa madara da zuma amemakon Sugar. A fridge tasa tagyara gurin suka fito atare daka kitchen in se murmusawa take ai kuwa ya hau fad'in.
"Shifa beyadda da wannan murmushin da take ba, tafad'a masa metake shiryawa.
Murmushin takumayi sannan tace "bakom muje nahad'ama ruwan wanka tinda ba abinci zamuciba. Tashige cikin d'akin tana dariya ganin yadda yabita da idanu kaman baisantaba.
"Ruwan wanka ta had'a masa wankanma seda ta lalla6ashi yashiga. Wai yayi fushi tinda tak'i gayamasa metake shiryawa. Kayan bacci tafito mai dashi tafeshesu da turare, tak'ara kintsa d'akin dukda bawani datti yaiba se bada k'amshin freshner yake.
Kallonta tacigaba dayi tanata farin ciki itama da Allah yabata miji irin Usman. Ganin yadda Sahiba da Ranveer suke zuba salon tasu soyayyan.
"Kitchen tashiga, ta d'auko kankanar datai blending tayi sanyi, bame yawaba tazauna tanasha, d'an sanyi dayai yanabin jikinta harwani lumshe ido take, k'anshin turarensa kawai taji tabud'e manyan idanunta duka akansa, k'arasowa kujerar datake yayi yazauna jikinsa na gogar nata. D'ebowa tai zata kai bakinta yai saurin kai nasa bakin, "irin dad'in dakike sha kenan ashe, yafad'a yana lumshe narkakkun idanunsa.
Sunkuyar dakai kawai tai murmushin de takuma, hannu yasa ya d'ago fuskar yahad'ata da tashi kowa nashak'ar numfashin d'an uwansa, yana mata wani sassanyan kallo dashi kad'ai yasan ma'anarsa. Cup in hannunta ya kar6a yana bata yanasha har suka shanye, seda yakalli News sukai brush yasunkuceta sukai d'akinsu. Tareda rufo k'ofa.
Safiyar alkairi.
"Kwance yake kaman bazai tashiba tinda yai bacci dagari yafara haske, bayan yagama yamutsa Naja atun Queen injishi da fad'a.
Wayan tak'ara ringin akaro na uku, jin vivration in yayi yawa yasashi bud'a ido da kyar. Ganin a sch inda sukai ne yai saurin ansa wayar, "ok godiya nake prop, Allah yak'ara girma. Yamike yashiga band'aki already yasan tahad'a masa ruwan wanka ilai kuwa tarufe mai ruwan yasamu yayi daidai wanka.
Wajen k'arfe goma yafuto, se kamshi gidan yake, yaduba ko ina batanan yai d'akinta.
Sark'a take k'okarin sanyawa, ya kar6a yasa mata har d'ankunnen yak'arasa shiryata, tana tabinsa da kallo ire-iren abubuwannan dayake mata nakulawa da soyayya su suk'e k'ara mata k'aimi wajen yin duk wani abu datasan zai farantamai yasashi nishad'i da farinciki cikin d'an zaman dasukayi tare. So da K'aunarsa kuwa sun mamaye jini da jijiyoyinta, duk wani motsi da zatai da k'aunarsa take, Addu'arta kullum suzama cikin so da k'aunar junansu da farinciki mai yawa a rayuwarsu.
"Rungumeta yai tabaya yad'ora ha6arshi a kafad'arta, suna kallon junansu ta madubin.
"Queen Tunanin mekike kina tare dani? Idan muna tare bakida sauran damuwa a rayuwanki. Am always there for you. *Ina tare dake*(Meemee bea ta) cikin kowana yanayi *Komai Rintsi*(Hama Gee). Kikasace dani kowana hali samu da rashi, cuta da lafiya yafad'a yana k'ara rungumota kaman za a k'wace masa ita.
"Hannayenta duka tasa tana shafo kansa, tahau rattabomai tsadaddun kalamai "kazama ni nazama kai mijina komai inzanyi dole saidakai. A kullum ina godiya ga Allah daya bani kai mai hak'uri da kawaici mijina takuma narkewa ajikinsa. Sund'au lokaci suna kallan junansu kowa na Sakar zuci sukasa dariya gaba d'ayansu yabata kiss a fore head inta, dak'yar yabari ta d'aura d'ankwalin suka fito dansuyi break fast.
Agurguje yaci abincin, shima saida tai kaman zata masa kuka yazauna dakanta tabashi Oat ne yaji madara da Omylet, tanad'e mai Pan cake a foil da ginger drink aroba yatafi dasu. Dan idan yai irin fitar wurinnan baya dawowa da wuri, takanyi k'ok'arin yimai dabarun dabazai sa yaji yunwa dawuriba. Tinda ba abincin ko ina yake ciba.
"A ranar ma kuwa se yamma yada gidan. Tana zaune itakad'ai se Radio data kunna, wak'an Nayi gamo ake tana tabin wak'ar dan tana santa(Miss zo6o😜) kawai ganin mutum tai jitai anyi sama da ita tai saurin rintse ido, yai juyi sosai sannan ya ajeta. Neman kujera tai tai saurin zama gudun fad'uwa, seda ta maida numfashi ta iya cemai sannu da zuwa, kusada k'afarta yazauna yana "Addu'ar dakuke min a kullum ta k'ar6u anza6eni cikin wanda akai sponsoring inmu miyi masters a sch in damuka baro, dan haka kihau shiri dake za atafi. Dirowa kansa tai tarungumeshi tanata murna itama, jin bakinsa tai cikin nata tin tana tirjewa harta soma maidamai da martani ganin yana neman zarcewa yasata janye jikinta tai gefe sunata ajiye nannauyan numfashi.
"Ruwa takamai yasha suk'a k'arasa maganar nanda wata biyu zasu tafi, kannan itama zata zaga dangi har gida zata tinda yau wata4 da zuwanta gidan bataje gidaba. Shiko yajajje gaidasu. Kafin magriba yatafi gida yagayawa Mamansu da Abbansu. Suji zancen suma. Sula kuwa samai Albarka dafatan samun Nasara arayuwarsu gaba d'aya.
*Bayan Wata biyu*
"Kafin lokacin seda tazazzaga dangi, dasukaje gida kuwa Inna kamar tacinyeta dan farin ciki ganin yadda 'yarta takuma cika da murjewa fata se shek'i take alamun hutu da kwanciyar hankali. Tawuni cir agida har mak'ota tazazzagaya.
Gidan Yayarsa Yusra ma takar6esu hannu biyu-biyu sukai ta hira kamar sun saba. Tahado mata abubuwa dangin kayan k'amshi tinda su take siyarwa.
"Daga getso suka ziyarci dangin mahaifinta, yacikasu da shatara ta arzik'i wanda basu sanshibama duk suka ganshi. Gusau suka wuce kwanansu biyu Anty husna kam tafi kowa farin cikin zuwansu. Tak'ara mata dabaru da sirrika irin na Mata masu aji.
"Seda sukai kwana biyar dadawowa daga Gusau sukai shirin tafiya Dabinai. Suka k'ara kwanaki acan yadda dasunda se shirin tafiya. Taga karamci da mutuntaka irinnasu, taita godewa Allah daya had'ata da miji da danginsa masu so da k'aunarta da mutuntata. Tsaraba iri daban2 suka had'o su dashi taita kunya ganin ita bawani abun azo agani takai musuba. Turaruka sai k'ananun turamen atamfofi takai aka rarraba. Sukai ta farinciki dasa Albarka.
"Tun ana sauran kwana5 sutafi kayansu sukai gaba a motar haya, se d'an abunda ba a rasaba, sunata shirin tafiya. Agidansu Usman ne Mama taita musu Nasiha musamman ma shi tinda ita bak'on guri zata shi bayau yafara zuwaba. Tajamai kunne yarik'e mata 'yarta Amana. Yaita dariya yana "ya kar6a to shi wazai rik'eshi? Allah mana inji Maman sukaita abunsu. Itadai Naja kanta a sunkuye. Tana k'ara san sirikar tata da irin d'abi'unta.
"Dayawa daga cikin dangi sunmusu rakiya, haka sauran likitocin da aka za6esu suma yawanci 'yan uwa sun musu rakiya. Akaita sallama da 'yan uwa da abokan arzuk'a. Se alokacin jikinta yai sanyi. Dan tasam zatai kewar gida da dangi gaba d'aya. Taita Addu'ar Allah yahad'ata da abokan zama nagari. Hawaye kawai yagani a fuskarta. Yasa handkchf yasharemata tareda kamo hannunta suka shiga jirgi, tak'ara narkewa ajikinshi tana kewar ahalinsu.
Kowa yabar gida.... Gida yabarshi inji hausa people..!!
Semuce asauka lafiya!
Team Naja'atu suna rakiya..😜
Am realy sory makaranta. Zaku naji yanzu in sha Allah akai akai. Tnx 4 ur luv and prays. Luv u all😍😘
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: {5/12, 9:35AM} Didin_Anee😍
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*51-55*
``` EDO STATE```
Saukarsu keda wuya babbar mota lexirius ta makarantar ita tazo d'aukansu, takwashesu dukansu masu mata da singles in d'alibai.
To tun amota Naja'atu ta lura da wani abokin karatun su Usman d'in ya kafeta da ido duk wani motsin dazatai a idansa yake koya ta d'ago ido sesun had'a ido dashi. Har aka saukesu a Staff Quaters, yawancin masu Aure 2 room apartment aka basu, sukuma marasa matan wasu suna Hostel wasu kuma su 4 gida d'aya aka basu.
"Gida ne matsakaici, babban falone da toilet ahad'e mai d'auke da d'akunan bacci kowanne da band'aki aciki, kitchen matsakaici se varenda.
Tinda suka sauka agidan ruwa kawai ta iya sha suka hau gyara ko ina, sauran kayansu ta aje kowanne a inda yadace. Ruwan wanka tahad'a masa yayi, itama tashiga tai.
"Ranar dai bai barta tayi girkiba. Darana abubuwan dasuka taho dashi sukaci da yammaci kuma yayo musu take away.
"Rayuwarsu a garin tai musu dad'i, rayuwa suke cike da so da kulawa ga junansu. Baya ta6ayin nesa da ita saidai in makaranta yashiga ko Teaching Hospital in da aka turasu. Dayawa mak'otan datayi ba hausawa bane, ita da Fatima matar abokin Usman d'ince sune kad'ai Hausawa itama ganin yadda Fatyn take fiffik'a da d'aga kai yasa tarage shiga sabgarta. Yawanci in yafuta gidan Maman Benue take shiga sita hirarsu takoyamata abubuwa dayawa irin na yaransu da abincikansu. Ba bak'inciki ko hassada zama suke na amana da mutunta juna. Kafin itama yanemarmata gurbi ta d'ora karatunta a Jami'ar tasu. Matsalarta guda ta wani abokin karatunsa maisuna Salis amma amfi kiransa da Baby. Yadda ko kallanta yakeyi seyai wani k'asa da idanu kamar d'an maye.
"Sallar walha ta idar tanata addu'a yau batajin fitar ma, bugun k'ofa take taji, tinaninta Usman ne to amma in shine a yanada key bud'ewa kawai zai inya k'wank'wasa sau d'aya, bata cire hijabin jilkinta tai hanyar k'ofar ko mak'otane. Salis(Baby) tagani yabita da Shu'umin kallansa, yace "Minyi waya da Usee in yanzu zai dawo yace najirashi"
Jin haka yasa tabashi hanya yawuce, kamar wani gidansa yazauna a inda suke zama tareda d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana chanja tasoshi, sa6anin da datakai saudi Qur'an tana sauraran K'ira'a, tinda taji yace Habibintane yace yajira shi, kitchen tashiga takamai dambun naman datai jiya tahad'o da lemu, ruwa da cup a tray. Ganin ta ajemai yasakar mata murmushi tareda cewa "godiya nake Sarauniya. Itadai jitai wani banbarakwai wai sarauniya. Saurin d'auke tunanin maganar tai aranta.
"Tin wajen 11:30 yazo gidan, tanata 'yan aikace-aikacenta, dukda a d'ar-d'ar take dan basan zamansa takeba. Kitchen ta shiga ta d'ora girki Tuwan Semovita tai da Miyan Kuka tabirge kaza aciki, tuwan kuwa ta mulmuleshi a leda tasa a warmers. Kafin biyu ta kammala tashiga wanka. Ta had'o da alwala seda tashirya cikin riga da skirt na atamfa tai sallah, tana cikin d'aura dankwali taji sallamarshi, kafin tafito har Usman ya shiga toilet, tai sauri ta kammala kintsawa cikin sassauk'ar kwalliyarta tad'ora babban mayafi akan kayan.
Kafin yafito tafito mai da k'ananun kayan dazai chanja. Tak'ara tattare d'akin tai kitchen.
"Babbar leda da ake cin abinci akai ta shimfid'a tajere wermers guda biyu na Tuwo dana Miya ga roban manshanu da yajin daudawa agefe, tasamusu plates masu zirfi biyu da cokula ga roban wanke hannu agefe komi dazasu buk'ata ta ajiye. Usman Yana fitowa kuwa suka hau cin abinci. Salis(Baby) yanata zuba surutu Usman sede yai murmushi ko "Ah, A'A" danba d'abi'arshi ceba magana inyana cin abinci. Naja'atu tana gefe taji yak'ara bata haushi kaman ta bubbugeshi kawai sotake yatafi amma ba alama.
A kwanakin da suka biyo baya Salis(Baby) yamaida gidan gurin zuwansa inbezo daranaba zezo da dare tinda dasafe suna asibiti ko makaranta. Ko Usman d'in nanan kobayanan haka zaizo. Yabi yashiga jikin Usman sose komai tare suke. Abun yafara damunta tarasa yazatai da lamari irinnasa. Rufe k'ofa tafarayi, koyazo tanaji bazata bud'eba, hakan kuwa ba k'aramin rigima yasa sukayiba. Ranar tasha mamakin Usman din akan wani aboki zenemi yatada musu da hankali. Yak'ara jaddada mata indai yazo ta bud'e masa ai arzik'i nema anuna anayi dakai.
'Yar rama tafara dalilin sa damuwa datai aranta. Ganin zata jawa kanta ciwo yasata cire komai daka ranta ta fauwalawa Allah lamuranta da duk wata damuwarta. Allah yabayyana gaskiya kowa yaganta.
"Fuskarta d'auke da farin ciki tagama waya da Mamansu Usman takira Innarsu, bayan sun gaisa take sanarmata da kud'in auren su Samiha za a kawo, dan babansu yace duk aure zai musu kowacce tacigaba da karatunta a d'akin mijinta, murna kaman tarufe ido taganta agaban Innar tasa albarka suka gaggaisa da 'yan k'annanta tai hanging wayan.
Gama wayanta keda wuya Maman Benua tashigo. Ganinta yasata fad'in "kinji shiru ko mama(wani lokacin haka take kiranta tunda tagirmemata) kika biyo bayana, ainace nadena zuwa tunda bakyasan shigowa. Maman benua kuwa cikin rikitacciyar hausarta tace "baniso nazo mijinka yadawo yaganni nahanaku sakewa bare masoya irinku "to mezaimiki kai Mama made yanzude mekika kamun? Sukai tahira abunsu secan tatafi nata 6angaren.
*Six Month letter*
Seda sukai rabin shekara sukaje ganin gida, Naja semunna take dantayi kewarsu bakad'anba.
Nagaya miki ba inda zaki ga gidanki shima yana buk'atarki, kawai de ko ina kyaje ki wunan musu. Turo baki tai had'e da muryar shagwa6a tana "haba nawan dan Allah ko kwana biyu kabarni nayi yaushe rabona dasu.
Nafa gama magana nagaya miki yaja bargo yakwanta. Itama kwantawa tai tajuya baya sa6anin da dasetajita manne ajikinshi suke bacci, sabo dolenta tajingina dashi tahau baccin.
"Duk inda yadace seda sukaje, cikin sati biyu damin sati uku zasiyi, duk tabi takasa gane kanta, barin hakan tai dalilin zaman dabasayi.
Randa taje gidansu kuwa Inna duk tagano komai dake tattare da 'yartata, tak'ara cika da murjewa abin gwanin birgewa taita k'ara addu'a aranta. Naja kuwa sawatai akai mata d'anbagalaje taitaci kamar an aikota. tofi azam-zam innar taimata tasha, haka taitayi tana aikamata kansutafi.
Dazasu koma kuwa taimata tofin dayawa tahad'a mata da kayan kad'i yaji K'uli-k'uli har garin rogo seda tahad'a mata. Amota kuwa warin fetur yahau kanta taita kwara amai. Agalabaice dai suka dawo seda ya d'aura mata drip tada hayyacinta.
"Wani abu data futo dashi kuma cin k'uli-k'uli, taitace wataranma hadda lemu take had'awa. Idantasa daru dolensa yanemo ko a inane, ganin haka yasashi d'aukar jininta yaje lab in cikin sch dashi bayan yayi Spinig in Blood in yai Pragnency test, anan yaga positive result. Godiya ga Allah yafarayi, no wonder abubuwan da Queen keyi kaman shigan ciki ashe shid'inne. Lallai ubangiji yanasanshi tinda yaza6eshi cikin wan'yanda zasiga k'wansu a duniya. Yak'ara godewa Allah. Jiyai soyayyar Naja'atu da abinda ke cikinta tunkanma yaga meza a haifa tak'aru. Bejira komaiba yakoma gida.
"Tana tsaye tana gugan inner wears insa, jitai an d'agata juuu anjuyata, abinka dame jiri jitai tana neman fad'uwa, saurin tarota yai a jikinsh taruntse ido tareda k'ara k'ankameshi tanasake saka kanta ajikinsa.
"Kujera ya ajiyeta, yasamo ruwa yabata tasha.seda ta da nutsuwarta yatambayeta meke damunta?
"Itadai ba abinda kedamunta se nauyin da jikinta yayi, kuma taita kwad'ayi wasu lokatan, tace tana yamutse fuska.
"Lakuce mata hanci yai yace to k'aruwa muka samu. Babynane acikinki shike saki komi kikeji.
Aibata bari yak'arasaba ta sadda kanta jikinshi cike da kunya. Add'ua yaita mata yana gaggayamata abubuwan dazata kiyaye da irin wanda zatana ci. Sekuma zuwa asibiti yakuma dubata acan.
"Naja'atu tak'ara kyau takuma murjewa abinka dame matashin ciki.
Zaune take tanacin Teba da miyar Ogun da Maman Benua taka mata. Tanaci d'an tsamin teban namata dad'i, har wani lumshe idanu take. Daka ita sai wando three quater iya gwiya yamatseta da 'yar ficilar rigarta me fad'i cikinta d'an wata hud'u yataso sosai kaman wata takwas. Jitai kawai anbud'e k'ofan, tajuya ma k'ofan baya. Tasande bame shigowa se Usman, maidakai tai tacigaba dacin abincinta.
Hannu kawai taga ansaka a kwanon. Yadda kuwa takeji dad'in abincin kowaye bazata bashi yaciba. Janye kwanan tayi tace gaskiya Habeeb bazakaciba a shagwa6ance tai maganar. Haba Sarauniya nid'in?
Jin haka yasata dubansa dan bahaka yasaba gayamata ba.
"Caraf idanunta cikin nashi, Innalillahi kawai tahau ambata cikin razani tanemi tashi amma takasa dan suman zaune tayi...
Nima zaro idanu nai👀 nai duba garesu duka!!!
Kubiyo didi. Danjin yazata kaya!
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: {12/12, 5:00PM} Didin Anee😍
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*56-60*
Zafafan hawaye taji suna bin kuncinta, ita tarasa wannan wace irin rayuwa ce sam mutum baida sakewa acikin gidan, kawai wani k'ato yashigo batare da ambashi iziniba, kome gidan aiyana nuna alamun dawowarshi bare wani daban.
Tana daka zaune take jada baya, ganin haka yasashi mik'ewa.
Batasan sanda tafara gaya masa maganganu marasa dad'i ba. Ta inda tashiga batanan take fita ba. Tanayi tana kuka. Fita kawai yayi batareda yace komaiba.
Ranar kasa gane kanta Usman yayi, daya matsa mata da magana tasa mai kuka, badan yasoba ya hak'ura da tambayarta yajanyota jikinsa yana shafar bayanta.
To cikin kwanakin sam yakasa fahimtarta, abincima dak'yar takeci duk tabi ta ruruce masa banda ramar datayi se tulin ciki datake fama dashi fuskarta tai fayau. Hawaye kawai taga yanabin kuncinsa ad'an firgice ta d'ago tana kallansa, yahau fad'in "Queen yakikeso nayi? Nayi nayi kifad'amin damuwarki kink'ki, ko gida kikeso namaidaki?
"Ah ah" tace tana girgiza kai "to mikikeso kowani abun namiki plss Queen kifad'amin. Banasan duk wani abu dazai takura rayuwarki akullum banida addu'ar data wuce murayu cikin aminci da k'aunar junanmu da tattali har tudun tsira. Yaita gayamata kalamai masu shigarai da kwantar da hankali.
Hawaye tashare yabata tausayi bakad'anba, tashiga yimasa bayani duk irin abubuwan da Salis(Baby) yake mata tun randa suka zo garin har k'arshen zuwansa gidan. Yadad'e yana jimamin abun idanunsa sukai jajir yana fidda wani gauran numfashi, ya hasala sosai, ganin yai haka tashiga bashi baki. Har zuciyarsa ta sauka. Abinka da mata da miji sai Allah (Maganar gaskiyace) suka shirya kansu kamar ba abinda yadamesu.
Washegari tun safe yatafi da ita asibitinsu. Inda yake kaita Antinatal. Sabida complain in datai na nauyin jikin datakeji dole aka mata Scanning. Murmushi kawai yake dayaga hoton 'ya'ya kwance acikin mahaifarta dakoni Didi bebarni nagano muku guda nawa bane. yaita tasbihi da godiya ga Allah. Ranar kaman yamaidata ciki. Ko suraba cikin yakeji. Seda yakaita gida danufin zeda dayamma sud'an zagaya. Tana shiga kayan jikinta tarage ta watsa ruwa tazauna daka ita sawata riga iya gwiwa me fad'i. Bacci tahauyi harseda yunwa tatasheta. Sallah tai tashiga kitchen.
Tana tsaka da jajjaga attaruhu yashigo gidan, kai tsaye yayo kitchen in jin k'amshi yacika gidan. Da sallamarsa yace "Queen mikike dafama unborn babys ina kuma?
" Babys kuma? Tafad'a tana kallansa.
Bagarar da zancen yayi yahau bud'e tukunya.
Karka k'one Habibi Taliya nake dafawa me daudawa, murmushi yayi baice komaiba yak'arasa mata jajjagen yayankamata albasa harta kammala suka gyara gurun. D'aki yanufa dan yawatsa ruwa. Itakuwa kafin yafito tabaje ak'asan carfet tahaucin abincin kaman tashige kwanon.
Futowa yai kawaiy gani yai tanata zuba loma duk ta had'a zufa, fanka yayo saitinta da ita yazauna tareda nad'e k'afafu, sa6anin itada ta ware k'afafu cokali yagani agefe dawani plate in. Bismillah yayi yahaucin abincin adaddafe yai spoon biyar yakur6i lemon dake gefe. Ita kuwa seda taji dam cikinta ya d'auka taja gefe, kallanta yake kawai cike da tausayi dan duk tafara kunbura tunkamin cikin yatsufa ma kenan inaga yatsufa. Dakansa yad'auke kwanunkan yamaida kitchen. Yazauna sukaita hira abunsu.
Wajajen bayan la'asar suka fita, sun d'anyi nisa damakarantar ganin tafara gajiya yasamammusu taxi. Kasuwa yakaita taga abubuwa iri-iri na al'adun yaroba da Igbo awani 6angaren kuma hausawa ne. Siyayya yamata sosai mother care haka kayan baby komai setaga ba guda yad'aukaba itadai binsa kawai take ta idanu inya d'au wani abun seya saka ajikin cikinta itadai sede tai murmushi takalleshi kawai. Kaya fall suka siya. Wani gurin hutawa yabiya da ita tasha kayan sanyi. Tayi enjoying futar sosai, ranar ko girkin dare bataiba da gajiya dakansa yamata wanka yasa mata rigar baccinta me fad'i dan yanzu sutafi sawa dan tafi sakewa cikinsu. Komi yahad'ashi inda yadace kaman zasi tafiya.
~~~~~~~~~~~~~
Akwana atashi lokaci yaita tafiya wasu daka cikin dangi sun zazzo mata. Harsu Samiha Ya Hafiz yakasu ranar kuwa tasha surutu kaman karsu rabu. Inna taita aiko mata da rubutu da magungunar gargajiya dan ance mata tafara kumburi. Har cikinta yai wata 8 kaman yanzu zata haihu dole wasu abubuwan dakansa yake mata.
Tafiyar gaggawace tataso mai badan yasoba zaitafi yabatta tunda dama yakusa maidata gida danta haihu acan. Yanemi alfarma gurinsu Maman benua da Mijinta kan suna kula masa da ita badad'ewa zaiba danma dole ne tafiyar dabazaiba.
Dararranar kaman bazai bartaba tabashi farin ciki bakad'anba, jiyake kaman sukad'ai ne masoyan da suka rage adoran duniya. Seda yamata wanka shima yayi suka hau hira yanamaijin kama kada yatafi batareda Queen intasaba. Seda ta lallasheshi sosai da kalamai masu kwantar da hankali dasa nutsuwa. Tausa yahau yimata yana lailaya bayanta har tahau bacci yai musu addua shima yakwanta.
Safiyar Alkairy!!!
Waiyo team Naja afuwa plsss. Makaranta abun se hak'uri. Allah de yak'aremu da lafiya. Nagode sosai didi tana sanku duk inda kuke.
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*61-65*
Safiyar juma'ar dazasi tafiyar, dawuri yatashi, shara yafarayi yagyara gidan hadda kunna turare a burner.
Ruwan tea yad'ora yahau ferara Irish, yafara suya yana 6arar plantain. Yasoyawa kansa k'wai daban dan ita tunda tasamu ciki bakasafai take cinsaba. Yana cikin wanke kayan dasuka 6aci tashigo kitchen d'in ashagwa6ance tace "kai Habibi kullum saikai ta kwashe ladan" da murmushi a fuskarshi yace "Yo ai kema kullum cikin samun lada kike, farantamin dakikema lada kike samu, ballantanama cikin dake jikinki Allah kad'ai yasan ladan da kike samu. Allah dai yarabaku lafiya. Yau ace ga 'ya'yana Jinina kuma Queen itace ta haifamin wana irin farinciki zanyi. Allah de yanuna mana lokacin darai da lafiya. "Ameen" tace takarasa gyaran kitchen d'in.
"Wanka yafarayi yataimaka mata itama tayi, suka shirya sunata soyayya abinsu. Har sukai Break-fast yakuma gyara gurin, duk saboda tausayinta dayakeji. Jiyake kamar kada yatafi ba ita.
Kaya kala uku tahad'a mai tafiyar kwana biyu zasiyi a k'aramar bus in makaranta zasu tafi awannan karan. Likitoci su biyar aka za6a zasuje workshop a jami'ar kano se driver dazai tuk'asu.
"Kamar bazasu rabuba k'arfe 9 yakaita gidan Maman Benua kada zaman kad'aici ya dameta. Haka sukai sallama tanata musu Addu'uan samun nasara da sauka lafiya, k'arfe 10 nasafe suka d'auki hanyar Kano.
Maman benua da Karamci, dukda ba Musulmai bane amma Kafiran Amanane, tun farkon zuwansu tafahimci hakan. Yanzuma cemata tai "tadena girki zatana aiko mata dashi, dandai cikinta ita kad'ai bazai gagaraba musammanma yadda tai nauyi komai dakyar takeyinsa. Ranar agidan tawuni se kusan La'asar takoma tareda Stepme 'yar Maman Benua da tatayata zama. Kallo takunna mata tashiga d'aki fes-fes dashi se k'amshi yake rigar Usmance a kan gadon ta d'auka ta rungumeta sosai ajikinta tana wasu maganganu dagaji nayabone. Sallah tai tahau had'a kayan duk daya bari kowanne a inda yadace tasakashi.
Falon tadawo suka cigaba da kallan dukda ita rabi kallo rabi tana gwada kiran wayar Usman datak'i shiga.
~~~~~~~~~~~~~
Tunda su Usman suka d'au hanya basu tsayaba se awani k'auye sukai sallar jumu'a, tafiya suka cigaba dayi. Usman yanata kiran Queen d'insa da 'yan gida amma yakasa samu. Tun suna hira jefi-jefi har kowa yai shiru, se karatu da suka kunna masubi nayi masu danna waya nayi. A Kaduna garin gwamna suka k'ara tsayawa basu wani dad'e ba suka cigaba da tafiya har suka shigo kano.
Tsautsayi daba a samasa rana/lokaci sunata sharara gudu daidai kwanar Waratu mai Tifa yafito dagudu shima yai kansu motar su Usman tai gefe se cikin ruwan dake kasan kwaltar, dukda duhun dagari yai mutane sun d'an taru sunata Salati da neman agaji abakin ruwan, motar kuwa tashige cikin ruwa sai gefanta kad'an ake gani.
"Motar wata Ma'aikata ce sukazo wucewa ganin mutane a tsaitsaye sun fara taruwa yasasu parking, dasaurinsu suk'a k'arasa bakin ruwan. Mutanen dake gurin sunyi iya bakin k'ok'arinsu suga sunfito dasu amma badama dole aka nemo fire service, suka ciro motar datacika lumtsum da ruwa. Ganin rubutun dake jikin motar suka tabbatar daga doguwar tafiya suke. A Ambulance aka d'au su Usman daba wanda yake motsi acilkinsu, motar kuma akajata da jan way. Cikin gari akai dasu General hospital ala kaisu A&E ba ai wani dogon bayaniba aka kar6esu danbasu taimakon gaggawa. Tunda sunji bayanin suwaye kuma daka inda suke.
"Mama Mahaifiyarsu Usman tunda yamata waya kafin su taso yasanar mata zaizo gida ayau Abinci iri-iri taimasa yaza6i duk wanda yakeso. Jin shiru-shiru har bayan Isha baizoba wayarsa kuma tanata kira shiru.
Naja'atu takira bayan sun gaisa take tambayarta Usman ko yakirata sun sauka? Takasa samunsa awaya. Naja'atu jitake kamar ta rusa ihu dan ita har batasan iya adadin kiran data maiba muryarta araunane tace, itama tinda yatafi wayarsa tak'i shiga, lallashinta Maman tayi sukai hangin wayar.
"Kiran wayar Samihane yasa takuma motsawa tanata tsokanarta jin Yayar tata tai shiru bakamar yadda takewa samiha ba, tasha jinin jikinta, "Lafiya Maman biyu? Samihan tace tana k'ara rik'e wayar "Alhamdulillah kawai tace suka gaisa tabawa Innar wayan jin Muryarta k'asa-k'asa Innar tad'anji ba dad'i tace "Yayar Salim ko bakida lafiya ne? Kuka tasawa Innar tagaya mata "wayan Ya Usman taketa kira bata shiga dan suntaho kanon, batasaniba kowani abun yasamesu.
Hak'uri Innar tashiga bata ko matsalar network ne tabari zuwa jimawa tasake gwadawa zata sameshi, seda taji alamum tasamu nutsuwa Innar taitamata Addu'a sukai sallama kowannensu da irin sak'ar zucin dayake.
"Ad'aya 6angaren kuma a Asibiti duk wani abu dayakamata ai musu anyi Amma mutum biyune suka farfad'o ansamo numfashinsu daka Driver sewani Dr Hashir suma ba a hayyacinsuba. Suka cigaba da duba sauran. Ganin haka yasa suka kira Vc University aka sanarmusu.
Dolensu suka kira Guadians d'in duk wanda akai tafiyar dasu. Mahaifin Usman suna tsaka dacin abinci dare wajen k'arfe Tara nadare sak'on yariskesu. Bak'aramin tashin hankali suka samu kansu acikiba dajin labarin. Abincin da basu gama ciba kenan suka tafi General Hospital sauk'in abunma agarine.
"Ward d'in da aka kaisu Usman suka nufa. Usman gashinan akwance kamar ai magana yatashi yai wani fayau dashi. Kukan da Mama tasane Alh yarik'ota bashiri sukai waje alokacin yasanarwa da 'yan gidansu Naja'atu. Adaren wasu sukazo har Inna k'annan Usman ba abin suke se kuka manyan nata Lallashinsu. Anan kuma tunanin kowa yakoma kam Naja'atu baiwar Allah idan taji yazatayi ga tsohon ciki. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" shine abinda sukaji Inna tahau fad'a.
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*66-70*
""Nannauyan numfashi Abban su Usman ya sauke, wajen 12na dare suka bar Asibitin. Baban su Naja'atu da Abbansu Usman sun tattauna sosai da Likitocin inda suka sanar musu da tashin Usman se wani ikon Allah.
Washegarin ranar tun bayan asuba Abban suka koma Asibitin ko Maman bai yarda taje alokacinba sha'anin mata saisu. Tin kafin Likitan yagamai masa bayani ganin Usma d'in a lullu6e yatabbatar da zarginsa yazama gaskiya, wasu zafafan hawaye yaji suna bin fuskarsa, "Allah sarki Usman Ubangiji yaimaka Rahmarsa yaro mai biyayya da girmama nasama dashi. Allah yasa Mutuwa tazama Rigar hutu agareka." Addu'a sosai yai masa yashare hawayen dasuka zubomai. Duk wani ciki-cike yayi dan abashi gawar Usman d'in gida. Tun a Asibitin yaja gefe yana buga waya duk wanda yakamata yasani.
Kiran V.C in Jami'ar da suka aiko su Usman d'in Worlkshop wanda akan hanyarsu suka sami Accident. Tun awayar yafara masa Ta'aziya dan tun cikin daren sak'on mutuwar wasu daga cikin D'alibansu kuma Likitoci ya riskesu. Anan Abban yanemesu su sako Matar Usman ajirgi akata Kanon sabida cikin dake jikinta, zatai kumburi intai zaman mota tunda tafiyace ba kad'an ba. Yace "bakomai za ai hakan dayardar Allah" suka aje wayan. Kafin 8 nasafe sunda gida Mutane har sun fara zuwa dole aka maida Jana'izar 11 nasafe. Musamman sabida Naja'atu itama tai masa addu'a dafatan samun dacewa da tafiyar. Mama kuwa saida Abban yad'aureta da jijiyoyin jikinta kada tai kururuwa. Duk da haka suma tai da aka shigo da gawar Usman d'in.
"Naja'atu kuwa V.C in suna gama waya da Abban Usman tingari baigama haskeba suka nufi Staff Quaters in, tareda matarsa Yarabawane amma Musulmai ne, matar tabashi shawaran su nemi taimakon Naibours insu. Baban Benua shiya bud'e k'ofan ganin V.C dakansa yasashi rusunawa suka gaisa cikin yaren Yoroba bayani sukad'an masa yataso Maman Benua si musu taimako seda tafito yadda bazasi musu kwarwa ba V.C yasanar musu Dr Usman Mak'ocinsu dawasu likitoci da aka turasu Workshop sun sami Accident, har wasu sun rasa rayukansu. V.C yace "Gidan Usman d'in zasu rakasu" Maman Benua kuwa k'ara tasa tareda d'ora hannu akai tafara "Oh my Goodnees woo!" Dak'yar matar V.C tabata baki tai shiru. "Matar za a tura injishi, ance ciki gareta suje ahad'a mata kayanta duka za aturata kanon a Jirgi.
Naja'atu tana daka kwance tunda tai sallah takasa rintsawa tunane-tunane kawai take da sak'ar zuci, wayarta kuwa har tamutu sabida neman wayan Usman batareda tasameshi ba.
Jin bugu yasata tashi dak'yar seda tatsaya taja numfashi had'e da zumbula Hijabi kan faffad'ar rigar baccinta har k'asa, tanufi k'ofar.
"Bak'armin tausayamata sukaiba ganin idanunta duk sun zuge, tunaninsu tasan abinda yafaru "Am so sory" shine abinda sukee cemata, itadai basu guri tai suka shige ganin harda Mak'otanfa. V.C yai mata bayanin abinda yakasu batai musu musuba, suka shiga tattara mata kayayyakinta. Maman Benua da Lokaci-lokaci take share hawaye a wayance karta k'ara birkita Naja'atun, suka tattaramata duk kayansu itada matar V.C. dukda haka seda Maman Benua tahad'a mata kakkauran shayi wanda dak'yar Naja'atun ta iya sha. Sukai musu sallama.
"Dawani captain Oba V.C yahad"ata dan basu samu jirgin dazaije Kano awannan safiyarba se Abuja inda acan sukesa ran samun mezuwa Kano kafindai Ranar ta bud'e. Akasai mata ticket Kayanta duk aka shi cikin jirgin. K'arfe takwas nasafe sukai Abuja.
A canma bayan 'yar hada-hadar dasukai Allah yataimaka dakwai jirgi mai zuwa Kano daga abuja ticket aka kuma siya mata kafin 11nasafen sun isa Kano. Babansu dakansa yazo d'aukarta shida yayunta biyu da Samiha. Dalabinta take k'ok'arin tsugunawa tagaidasu Baban yai saurin dakatar da ita. Idanun Samiha taga sunyi ja sosai, bade wanda yace mata komai sukasa duk akwatunanta amotar suka tafi Baban nasu yana k'ara tausaya mata. Ganin k'atotan cikin dake jikinta duk abinda keciki yazama *Maraya* yanzu kuma taje tatarar da Mummunan labari. Da dabara yashare hawayen daya zubo mai batareda wani yaganiba.
Naja'atu kuwa ganin sunyi hanyar sharad'an tunaninta ko gida zaikaita, zuciyarta tai wani bugu ganin ciccirindon mutane tun daka farkon layin, har suka zo gidan Mama. Jitai duk wani k'wari datake dashi ya salu6e motsi ma dak'yar takeyi kanta tahau tambayar meke faruwa anan? Dukda haka takuma kumburi akan nada
Kasa fitowa tai daka motar dole Samiha da Baban suka fito da ita takunma dak'yar take, tunanin Mijinta yahauyi da Usman ne seya had'ata da jikinsa, ya tallafota yanayi yana mata sannu cikeda kulawa suje duk inda zasu. Toko ina yake daba'azo d'aukarta dashiba? Cikin gidan suka nufa, nanma ganitai mutane dayawa dangin su Usman Mata da Maza yawanci duk sun zubo mata idanu. Ahankali tafurta Mamace tarasu? Jikintane yahau rawa. Baban su kuwa tak'ofar gaba suka shigar da ita falon Abbansu Usman da mutane da dama a falon wasu daga ciki sunci kuka Yusra yayar Usman tana ganinta takuma sa kuka. Jitai wasu nafad'in "Mutuwa mai yankan k'auna kinga matarsa da tsohon ciki, jitai cikinnata yawani hautsuna har tana naman durk'ushewa.
"Agaban gawar Usman d'in aka ajeta. Kwance yake amik'e anmasa sutura nannad'e da Likafani ankuma yafa zani akai. Idanuwanta takai kan mutanen falon kowa taga yananan har Innarsu cikin jimami da taraddadi y
Suke, to bataga Mijinnataba. Hannu takai tana shafar jikin zanin da aka lullu6e gawar Usman dashi
"Kiyi Hak'uri Naja'atu *Kullu nafsin za'iqatul maut/ kowane rai seya d'and'ana zafin mutuwa*.kowana lokaci takan iya riskarmu to Allah daya fimu sanshi yakar6i abunsa.
"USMAN NE NE KO BABA? Abinda ta iya fad'i kenan dayawa agurin sunji tausayinta. Dan bakasafai zakaji ta ambaci *Usman* d'inba. Gaba d'aya iyayen suka matso kusa da ita suna banbaki da nasiha "tayi hak'uri da tawalkali wataran kowa in lokacinsa yayi seya amsa kiran Ubangijinsa. Karki tumami dan
*Annabi S.A.W yace "Basa tare damu, #Masu marin fuskokinsu, #Da masu yaga Aljihunansu, #Da masu D'aga murya suna kira irin Na Jahiliyya. Ayayinda akai Mutuwa. @bukhari da muslim ne suka rawaito.*
"Kiyi masa addu'a zaitafi gidansa nagaskiya muma wataren mune haka" Inji Maman Usman tana dafo bayan Najar.
"Allah yai masa rahama yakyautata namu zuwan" abinda ta iya furtawa kenan. Dukkansu sunaji suna gani musamman Naja'atu da jinta take kamar kara cikimma tanemeshi tarasa haka aka fita da Usman d'in akai mai Sallah suk tafi kaishi zuwa kushewa.
Semuce Allah yajik'an Muslim Umma. Ameen.!!
@Team naja'atu kuzo mujewa Naja ta'aziyya gsky
#sharar hawaye!!!
© *Didi_sady*🍼🍉😜
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*71-75*
""Tunda aka fita dashi ta d'ora idanuwanta kan k'ofar, gani take kamar a mafarki. Lallai Rayuwa batada tabbas, yanzu kake Mutum yanzu zaka iya zama Gawa. Shiyasa ake so kazamto mai aikata Alkairi arayuwa kazauna da mutane lafiya yadda kobayan ranka Kyakykyawar Shaida zata rik'a binka. *Hak'ik'a duk Mutumin daya manta Allah to tabbas yana tareda Shaid'an*. Allah Yai mana muwafak'a. Ameen.
Haka tazama kamar Mutum Mutumi, tana kafe aguri d'aya kamar gunki. Motsi ma kasawa tayi bare Kukan dataga dayawan mutan gurin nayi, wani irin d'imuwa tasamu kanta aciki, bugun da zuciyarta tayi hasseda taji Motsin abunda ke cikinta, kuka takeso tayi kota samu raguwar Nauyin da K'irjinta.
Cikin kwanakin Naja'atu tazama komai sede aimata ko magana bayinta tacikaba. Abinci se anyi kamar anayi zataci shima kad'an. Tabi tarafke tayi wani bak'i se k'atotan ciki dake jikinta. Damuwace sosai tattare da ita. Agidan su Usman d'in take kwana.
D'akin Maman suke kwana itada k'anwar Maman Yaya Yusra da 'ya'yanta se autar Maman. Bacci ma sede 6arawo ya d'auketa duk tabi tad'ashe tazama wata iri da ita.
Daren ranar da Usman yai kwana uku darasuwa, Naja tana kwance dare yatsala tunanin rayuwar ta take harta gangaro kan zamantakewarsu da Usman cikin Aminci, Yarda, K'auna, Kulawa da Soyayyar junansu. Lokaci d'aya Allah yad'aukeshi daga cikinsu badan baya sanshiba, tatuno yadda yake san cikin jikinta tunkafin tahaifo shi irin burin daya d'ora akan abin dayake cikinnata. Kuka tasaka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tin tanayi a 6oye har shashshek'arta tafito fili, Yaya Yusra dabata jima da komawa bacci ba, taji alamun kukanta tashitai tareda kunna fitilar wayarta tahaska kan gadon , jijjigar dataga jikin Naja'atun nayine yatabbatar mata da ita keyin kukan, gadon tanufa itama kamar jira take tasa nata kukan har Mama tashigo d'akin ganin suna kuka zuciyarta tak'ara tsinkewa, bata hanasu kukanba musamman Naja'atu dasukeso tayi kota samu ragin damuwar datake ciki.
Batasan sanda itama hawaye yakecemata ba har wani nabin wani. Maman tai dauriya tai shiru Yaya Yusran ma, ita kuwa Naja'atu seda tai mai isarta Mama tatasheta tareda jingina ta ajikin pillow Ruwa tabata tasha sannan suka hau lallashi da nasiha tareda bata Misalai iri-iri na Rayuwa itadai jinsu kawai take.
Cikin kwana bakwai darasuwar, sunsha bak'i daga 6angare daban-daban dayawa kuma sun mata ta'aziyya. Har 'yan gidansu dukda irin zaman doya da manjan dasuke. Zuwa lokacin ta kuma rama ba kad'an ba. Zagayayyar fuskarta tayi fayau da ita. Danna Inna kullum saitayi mata tofi cikin zam-zam tanasha, Addu'oi dadama take mata banda wanda tabata takeyi. Taga kuwa fa'idar hakan dan damuwar datake ciki taragu sosai. Tafauwalawa Ubangiji duk lamuran rayuwarta shiyasan miyake nufi dayai mata haka.
Bata kuma rikicewa ba seda aka kawo kayan Usman ranar dayacika kwana takwas darasuwa, taga abubuwansa dayawa komai yananan shid'in ne babu yatafi inda ba'a dawowa. Aranarma tasha kuka wanda har zazza6i yasaukar mata.
Kwananta goma gidansu Usman d'in. Alh Abdul-Mu'iz mahaifin su Naja'atu dakansa yanemi takoma gida dukda anriga anzama d'aya nanma gidane. Ganin irin damuwar dake tattare da ita, bayan hakama komai sai anmata. Hakan yasa sukace "zasu tafi da ita gida. Mama kuwa sotai abarta agurinsu har ta haihu. Kayanta duka aka kaimata gida tasha kuka harsu 'yan gidanma haka tatafi tana ganin kamar rabuwa sukai. Itada zuwa kuma se ikon Rabba. Danma zuriyar data shiga tsakaninsu in Allah yaraya abinda zata haifa.
Har sukaje gida bata k'ara cewa k'alaba, dasukaje gidan nema bayan anfito da ita daga motar wasu daga cikin 'yan Mazan gidan dasuka tarar a harabar gidan suka k'ara yimata ta'aziyya. Da hawaye tashiga gida. D'akin Innar aka gyara mata bayan gadon dake d'akin, k'atuwar katifa baban yasaimata aka samata daka gefe daduk sauran kayanta aka shirya mata, kwanciya tai tanata maida numfashi. Tafad'a duniyar tunani har bacci yai awon gaba da ita.
Zamanta agidan tun bayan dawowarta bayabo ba fallasa. Duk abinda takeso dai-dai gwargwado tanasamu. Matan gidan sunanan da halinsu, danma bakasafai take fita ba daga zuwa Asibiti dashima tafi zuwa dadare, se d'an atisayen datake zagaya cikin gidan. Ahaka har cikinta yashiga wata tara. Haihuwa yau ko gobe. Inna duk tatanadi kayan jego da ake buk'ata gamai haihuwa tashirya. Hatta kayan mai jegon duk tashirya sejiran Allah yasauketa lafiya. Zuwa lokacin Usman yayi kwana Arba'in harda d'oriya da rasuwa.
Sosai take kewarsa, danma Inna tayi namijin k'ok'ari wajen hanata zuzzurfar tunani. Data fara zatai tabata hak'uri da nasiha harta samu tasaki jikinta. Maman Usman ma tana yawon zuwa dubata banda aiken datake mata. Haka itama Yaya Yusra tana tafe da abubuwan arzik'i duk dan ragewa Naja'atun damuwa da kewar babban rashin datayi.
Afuwa makaranta ankusa k'arka'arewa da yardar Allah.


0 Comments