DUTSEN CIKIN RUWA. HAUSA NOVELS

 DUTSEN CIKIN RUWA* ♡

              *Na*
*Haleema G Khaleel*

              0⃣5⃣

Da d'ari-hudu da hamsin, tahad'a suka tafi Asibitin, Murtala dake cikin gari,
          Dukda haka bak'aramar tafiya tashaba, duk dan tarage kudim motan.
         Aka duba Samihan aka bata magani. Sunsha wiya kafin sudawo.

Da dawowarta tatarar da abin mamaki. "K'aninta Sa'ud yazo daka Gusau" . Da farincikinta tatareshi. Dukda bata da wani abu dazata bashi. Koba komi ```Shinfidar fuska....  Tafi ta tabarma```.

Balle d'an uwanta dasuke ciki d'aya dashi.
Sannu da zuwa sukaima juna. Yakarb'i katin asibitin, segani tai yafuta.
    Tare dasu Isma'il suka shigo, yasiyo mata magungunan da madara me sanyi.
         Bayan ya huta yaci yasha.
             Yacikasu da tsaraba da Mahaifiyarta tahad'o yakamata, kwana2 yai yacikasu da shatara ta Arzik'i. Yakoma Gusau.
     
       Haka rayuwa taita tafiya, Inna nacigaba da fuskantar k'alubalen rayuwar gidan iri-iri, da dad'i ba dad'i. Tana cigaba da hak'uri. Sabida 'ya'yanta " sune k'ananu agidan, kuma sune abun a tausaya musu. Naja'atu da yarinta, tin bata fuskantar abunda akema Mahaifiyarsu harta fara ganewa.
         Dukda tataso cikin gidan yawa. 
Allah beyita mai hayaniyaba, asalima batada yawan magana. Hakan datakeyi yasa wasu daka cikin yayyunta mata kecemata "Munafuka. Sumimi kasam. Kawai saidai tai murmushi. Inta gayawa Innarsu tace mata tayi hakuri, 'yan uwantanw." Wataran zasu dena.

*bayan shekara5*
          *Cigaban-labari*
Naja'atu yarinyace mai sanyin hali. Duk wasu haleyenta nak'warai tasamosu daka Innarsu.
      Kyakyawace sosai, farin dangin babansu kawai ta d'akko, hatta yatsunta da sirantarta, na Innane asalinsu fulanin Gusau ne. Akwai dukiyar fulanin. Sedai batada tsayi sosai.
             Tashare siraren hawayenta. Tana tunanin wannan rayuwa. Wani abubuwanma sabida ganin idon Babannasu ake bari. To inaga yafad'i yamutu! Yazasiyi?
     Taja nannauyar ajiyar zuciya. Hmmm!!

*Didi_Aneesa*🍼🍉😜
        Anisadidi.pun.bz
[2/18, 10:41 AM] ‪+234 703 962 5239‬: 31/10, 5:15PM
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA*♡
                 *Na*
*Haleema G khaleel*

        0⃣6⃣-1⃣0⃣

Ranar takama lahadi. Bata da sch, bayan ta kammala gyaran dakin Innar tasu, tashare tai moping, se tashin k'amshi dakin yake bakace sunada masu fitsarin-kwanceba.
       Babban floor ne se dakuna guda biyu da band'aki. Da k'aramin kitchen agefe. Inna da Samiha da ita, a d'aki daya, "d'aya kuma kananun k'annanta mazane su3 ne aciki. 

K'a'idar Alh ce dazarar yaro namiji yakai shekara 10 -12 za a maidaka waje boys quaters, haka duk sauran d'akunan matan gidan yake. Dukda akwai babban Kitchen, wadda takeda girki ita zatai azubama kowane 6angare.

Misalin 10am Hantsi yad'aga, tayi wankanta tanata tashin k'amshi, gefanta ☕ruwan-bunune, da wainar gero taji k'uli😋. Tagama karin safenta, tahau yin tsifa. Tawanke kan, ta gyarashi. Dan dama ita ba ma'abociyan san kitso bace, duk da yawan gashin datake dashi.

Kitchen tashiga. Dan taya Innarsu had'a abincin Rana. " Tuwan dawa, da miyar d'anyar kub'ewa taji busashshen kifi. sukayi. Suka kammala. Takaima kowana d'aki nasu. Sannan takimtsa gurin.
            Dakomawarta d'aki sallah tai, ta d'an shingid'a, Nannauyan bacci yai gaba da ita. K'arar wayanta ne yata data. Hafsa Hussain ce, 'yar ajinsu a islamiyya.    
"Salamu Alaikum ukty"
         Daka d'aya 6angaren Hafsa ta amsa, suka gaisa hafsa tak'ara mata tunida  Aikin da aka basu cikin littafin ``` *Durusulluggatul arabiyya* ```domin tayi kada tazo a hukuntata cikin wanda basiba. Tad'anyi mata bayani darasun dayadda zatayi. "Sukai sallama. Sesun hadu a islamiyyan. Duk da bakullum take zuwa ba. Amma tana kiyaye kowane abu dazesa a hukuntata. 
              Sauri tai tad'akko jakanta, tafara yin aikin, tai iya wanda tagane, sauran kuma in sunje Islamiyyan kan akar6a takarasa.

     Wanka tafarama Salim shi kuma Kamal yai nasa suka shirya seda suka jira Samiha ita ma tashirya sannan 
Naja'atu tasasu agaba sukama Inna sallama 3:30 suka tafi a hanyar islamiyyan, suka hadu da Fawad yayi futu-futu da alama daka fillin ball suke. Salim yace" yaya,Fawad yau bazaka makarantaba? "Ganin kallan da Naja'atu kemasa ya hau sosa k'eya. Yanzun zan shiryo nataho. Yafiye maka de tafad'a. Danshi tin yana yaro inda abinda yafi tsana to ace yatafi makaranta. Tin ana dukansa har akagaji aka basshi. Kunsandw maza dak'in makaranta.
             Musamman Islamiyya. Sukai gaba suka barshi karya sasu latti.

         Bayan an idar da Sallah, kowa yai Ajinsu. 
         A Ajin su Naja'atu maza sun zauna matan ko suna tsaye basu sami Tabarma ba, gashi indai Malam yariga yashigo sede su zauna ak'asa.
         Yadda kua sukeji da gayu,😉(miss u gayu-gayu). Nafisa tatashi sarkin tsiwa😜 aiko tama mazan tatas hadda fad'in basa kishinsu. "Su sunsamo abun zama amma su ko oho. Wani dan ajin Sanusi yaita bata hak'uri. Yafita yasamo masu.
        Hannun Naja'atu taja dukda ita bame yawan maganabace, se ma abum yabata dariya ganin anja Hafsa,Sady da Nafisa hassan. Aji-Aji sukai tabi, Har suka gano Tabarmassu.
     Aikan ansha jaraba kafin su kar6o. Wata Fiddausi a ajin ta tashi tanata sirfa masifa, sega Malaminsu Malam,Farouk, yakirasu shima yahau nasa waisu sun had'e kai farare, se rashinji sukai. Nafisa kuwa ta Cuno baki😚(mom heena😂).
       Yace "kuma karna k'ara ganinku haka batare da kunsa bak'a acikinkuba. Amsawa sukai yace kowa yakoma Ajinsu.

     Nafisa sarkin mita kuwa tai tayi d'ayan Nafisa da Sady natayata. Sukuwa Hafsa da Najah sede si murmushi.
            Akasa tabarma kowa yazauna. Suka kara jerewa su biyar a layi. Ita Naja'atu sarkin tsoro k'ok'arin chanja waje take aikua Nafisa tajawota hartana k'okarin fad'uwa abinka da ba k'iba. Muraja'ar Al-qur'an akafara. Hakan yasa kowa ya nutsu.   
             Sukai karatunsu suka gama. Har aka kammala karatun. Malamin Arabiyya yaxo ya ansa Aikinsa dukda bata  gamaba, haka tabayar..
       "K'arar K'ararrawace ta ankarar dasu. Sunata surutu. Sukai addu'a kowa yatafi.
        Abakin get in Makaranta ta tsaya jiransu Samiha, suka rankaya sukai hanyar gida. "Kamal bazaka tafi a hankali ba! "Kullum kai kenan kaita gudu ahanya sekace yaro. Bakaganin ko Salim baya abunda kake."

Bata ankaraba sejitai Kiiiiiiiy. Mota tai gaba da Kamal...
         Waiyoo yaya kamal Salim yafad'a da k'arfi. Ita kua Naja'atu tama rasa mizatai. Se hawaye Shaar😥. Saurin Tarota Samiha tai ganin tana neman fad'uwa.
          Innalillahi kawai taaji ana furtawa😳

Kubiyo didi👉🏽
  

*Aneesa_didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:41 AM] ‪+234 703 962 5239‬: 1/11, 12:18PM
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA* ♡
                 *Na*
*Haleema G Khaleel*

         1⃣1⃣-1⃣2⃣
Jitai itama ta fara maimaita ```Innalillahi wa inna ilaihi raji'un```. Bold eyes inta takuma zarowa😳.
Sukai saurin k'arasawa inda Kamal yake a yashe, Samiha ce tai k'okarin d'agashi. Razanannen Ihun da Kamal in yasa, bashiri Samiha ta sakeshi. 
         Naja'atu tace Kamal sannu kullum gayama nake kadena gudu amma kak'iji ai kaga irinta. "Kuka yafara yana waiyo Allah  yaya k'afata waiyo Inna.
       Shikuwa wanda yakad'eshi da motan, 
*mukhtar* ne. Anan unguwar suke.
  D'ane ga Alh Mahmud Ateeku. Da matarsa Haj Uwani,  sun haifi, Mustapha, Zainab se Mukhtar Shine d'a na uku agidansu, da k'annansa Leena, Ummi da Iman autarsu.
      Mukhtar kyakyawane, kamar shiyai kansa sede bak'i ne shi domin 6angaren mahaifiyarsa dake kathoun a Sudan yayi.
    Dan wasuma Bak'in-Balarabe suke kiransa a family. Sede yakasance  gagararren Yaro ne, duk irin yadda Iyayen nasu suka jajirce akan tarbiyassu. Amma abin nasa k'aruwa yake. Sabida muggan abokai daya had'u dasu. Gangs guda garesu. Na 'ya'yan masu hannu da shuni.
         Shaye-shaye suke kamar ba gobe. Kotayaya kuwa se annemo kayan maye. Bawanda besansuba. Musamman M.M Ateek dawani Shanto. Shikuwa Maude 'yan zugane. Tinda iyayensa bamasu kud'i bane. Yawanci kullum suna hanyar Gwazaye. Ko kamasu akai yasan abokan zasi belinsa. Shiyasa yake biye masu.
      
      Ganin haka se suka yanke shawaran akaishii karatu Dubai. Duk dan arabashi da abokanansa na nan dasuke k'ara janshi cikin sharholiyar rayuwa. Aikam bata chanja zaniba. Sema Wak'a dayaje ya koyo.


Sau biyu Alh M Ateek yana kaishi gidan mari, dan yasamu Horo yabar shaye-shaye dayakeyi.

Bayan anfito dashi akaro na biyu. Se sukadena bashi kudi akai-akai.
         Yakoma indai zaiga kud'i saiya d'auka, kowani abu dazaika kudi' tokuwa zai d'auka su siyar da abokanansa. Kawai suse kayan maye.

         Yanzunma Motar gidan yad'akko ba asaniba, tunda ko mota andena barinshi yahau shi kad'ai..

Yanata Falla gudu, aikam yabige Kamal. Futowa sukai shida abokinsa Wizzy, Mukhtar kuwa yahau Masifa "kawai yara ansakeku a hanya kaman dabbobi. Bakusan me kukeba. Yanzun ni gashinan anjamin 6ata lolacina, a wofi" yanata sababi. 
        Calm down abokina, wixxy yafurta hakan. Suka k'arasa gurin, Samiha kuwa mizatai inba Harararsuba. "Kobakada ido ai se haka malam har dazakana had'a mutane da dabba, sabida bakasan darajar mutaneba" dantasan im Naja ce bazata ce komiba.

Shikuwa Mukhtar Mamakine yacikashi. Wannan 'yar yarinyar dabatafi sa'ar Ummi k'anwarshiba take gayamasa magana.
         Gani sukai yayyansu biyu sunzo ya, Hafiz da Isma'il. Domin sunkusa kaiwa gida. Salim yaruga yafad'a agida.
         D'aga Kamal in sukai subiyi, yasami gocewar kashi a k'afarsa gashi duk ya kukkuje. Ganin hakan yasa Mukhtar in cewa susashi a motar. Suka tafi kaishi, Asibiti.

Ita kuwa Naja'atu k'wak'k'waran motsi kasawa tai, se Hawaye dake tabin fuskarta😪
      Ahaka suka k'arasa gidan. Samiha kua se mita take. Dashigarsu Mutan gidan wasu na tsakar gidan sukaimasu jaje da Allah yakiyaye. Masu jaraba kuma, suna tayi. Itadai sum-sum tashige d'aki.

Tanaji samiha tanata maidama da Inna yadda akai, da mita akan sanyin yayartasu, abin yai yawa. Wataran ma ko taresu akai za amasu duka ita sedai tai. Shiru.
          Murmushi Innar tayi. Tace bakomi daka Allah ne. Ai "kema Samiha kidinga hakuri kina rage fad'a da maganannan taki."
    Ai shikenan Inna, Allah yak'ara kiyayemu, tai band'aki abinta.

Bayan magriba, sukaga shiru, basu dawoba. Itadai duk jikinta yai sanyi. Tahau bama Inna hak'uri, "Wallahi Inna Kullum anatafiya shi baze tsayaba sede yaita gudu. To yau tsautsayi se wani d'an unguwannan yabigeshi." 
      Bakomi ai Yayar-Salim Innar tafad'i. Tareda Addu'ar Allah yamasu Albarka yak'ara kiyayewa. Suma su kuma kulawa dakansu suduka...
 
Allah kakara tsaremu Ameen!!!😄


Post a Comment

0 Comments