DUTSEN CIKIN RUWA. HAUSA NOVELS

 DUTSEN CIKIN RUWA.....♡

GARGADI:banyarda wani ko Wata yajuya min min wannan kirkirarren labari nawa ba,banyi Dan wani ko Dan Wata ba,sunayen da garuruwa naciki da nasa dukdan su nishadantar dame karatune banyin dancin fuskaba saboda haka kada ajuyamin wani sashe ko wani bangare naciki batare da izinina ba inhar hakan tafaru NAJA ALLAH YA ISA!!!!
              ..♡..♡..♡
    STORY AND WRITTEN BY:
HALEEMA G KHALEEL

             0⃣1⃣

Cikin sauri-sauri take tafiya kada lecturer insu yarigata shiga, sabida dokarshi ce inyarigaka shiga tom sede katara next,time.
Dauke take da lab-cout da sch bag inta dressing inta wanda kusan kullum shine shiganta, gown ne eather Material, Atamfa, ko Ready made kiran Bahrain Oman, ko Kuwait.
Yanxunma Gown ce jikinta Sea,green tayane kanta da peach colour veil. Kannan yasha Top-knot. Setashin sanyin kamshi take, wanda bazaka tantance wana irin perfumes take using ba.
Akan kwanan dazata sadata da Biology Lab insu tagansu sunata K'us-K'us i. Tai saurin fadin " ````LA ILA HA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN```." 

Inda sabo tasaba dahakan dasuke mata koyaya zata hadu dasu sesunyi magananta. That Y! tabama "Innansu labari tace mata tai ta addua duk wani mai nufinta da sharri, in sha Allah baze tasiri a kantaba.
 Musamman yadda bata shiga abinda bishafeta tun a farkon zuwansu sch in, duk abinda baruwanta bata minding buissnes inta akai. Hasalima bata fiya maganaba bakowa take kulawaba. Hakan yasa dayawa dakacin mates innasu suke ganin girman kai gareta especially Shema da Zuzu. Tun farin karatunsu suke shigemata datagan ba karatunne gabansuba yasa ta ajesu a Side. Hakan yasa suke takun saqa dasu.. A bakin kofan Lab in tatsaya tasaka lab-court inta tana zura Tag inta agaban rigan taji anbangajeta. 

Tag in yai gefe tai taga2 zata fad'i tai saurin dafa jikin block in. Ko ba a gayamataba tasan bazasu wuce Shema da Zuzuba.

Daukan Tag inta tai tasa tashige Lab in batareda ta dubi kowaye yamata hakaba. Tareda qudurcewa a ranta matuk'ar yau aka had'asu Group daya a Practical in bazata shigaba sede yakoreta. 

         Yanadaka gefe yagan duk abinda yafaru yaji tak'ara birgeshi matuk'a shima yarufamasu baya yashiga Lab in anata hayaniya seda practical teacher in yaxo kowa yanutsu. Yai dividing insu Group Group. Allah yataimata  group insu daban2, su biyu mata daka ita se Jidda ja'o. Aka fara practical in Tissue Respiration. Tanata hadamasu Apparatus tazo aje ruwa kawai tazubama USMAN BELLO GALADIMA ajikinshi. Gashi dama yabi yasa mata idanu duk abinda take idansa nakanta tun shigowanta dasafe.....

To suwaye wadannan??
Kutara kusha labari

IN DEDICATION TO MY ANEE AND MISS XOXO......
                      ✍
ANISA_DIDI🍼🍉😜
[2/18, 10:37 AM] ‪+234 703 962 5239‬: 26/10, 9:30AM
♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡
              Na
Haleema G Khaleel

Godiya ga Allah. Godiya agareki ANTY AZIZA I GOMBE{```UMMYASMEEN```} Allah yabar k'auna❤

             0⃣2⃣

     A haka har suka kammala practical innasu duk da ita atakure take yadda yaketa satar kallanta.. Kiran Attendance malamin yayi kowa yai ficewarsa.   Har suka kammala darusan ranar.

Agajiye liss tada gida kayanta kawai ta ajiye tashiga band'aki, wanka tai tareda d'auro Alwala. Shiryawa tai tanufi d'akin Innarsu.
Zaune tasami Innar tana ta gyaran kayan K'annanta, gefanta kuma Ahmad(deedat) dan,autansu yanata rikici Inna tahanashi fita. sannu da gida inna tafada cikeda ladabi, Innan ta amsa fuska sake. To Rigimau miye kuma? NAJA'ATU tafad'a tareda janyoshi jikinta. Meya faru da d'an Inna? Tace masa tana shafa kansa, alamun rarrashi. Ba Innace tahanani futaba, yafad'a tareda rufe idansa waishi yayi fushi.      

Haba Deedat banda abunka ai Inna tayi dai-dai datak'i bari ka futa bakaga Magriba takusaba. Kuma ba asan Yawo, yahakuri kaji wataran zamuje unguwa muma ko? Damurna ya amsa yace ah! Har gidansu Anwar zaki kaini muhau lilo ko? Yafara tsalle yana murna yasaki ransa kaman bashiba.

Murmushi tai k'asa-k'asa takallo Innar tasu da itama Deedat in yasata dariya. Naja'atu tace Inna gara shima Deedat asashi a Makaranta tunda ankusa d'iban sababbin D'alibai. Wannan surutun da san yawan nasa duk ya ragesu.

   Ajiyar zuciya Innar tayi hmmm! Yayar,Salim kenan. Domin Innar bata fa'dar sunanta itace 'yarta tafari. Su zauna si hirama seda Najar ta dage. Dan ita Innarsu Al-kunya gareta irin na iyayen daa. Kuma inbatai da itaba dawa zatayi tinda Rayuwar tazama Naka sai naka. Dadin zama sai bare inji Hausawa.
Innar tace Allah yakaimu muga yadda za'ayi. Domin Rayuwar gidannan tana bani tsoro. Hakuri zamu kara Inna, wataran sai labari Naja'atu tace tana mai share hawayenta.

Mutara domin jin gundarin labarin!!!


Didi_Aneesa🍼🍉😜
[2/18, 10:37 AM] ‪+234 703 962 5239‬: 28/10, 5:07PM
 ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA*.....♡
          Na
*Haleema G Khaleel*

Godiya sosai *ummyasmeen*. Allah bar kauna❤

        WAIWAYE:

         0⃣3⃣

Alh,Abdul mu'iz Auwal Getso shine Mahaifinsu Asalinsa 'yan Getso ne dake Gwarzo, su uku mahaifiyarsu Iya Rakiya tahaifa Baba,Barira seshi Abdul Mu'iz da k'aninsa Muhammadu. 

Dakanan kuma Allah yakar6i abarsa, hakan yasa mahaifinsu k'arin aure. Ya auri Baba Asabe. Har itama tahaifi nata 'ya'yan su biyar hudu mata d'aya Namiji Azeema, Furera, Saudat, Kareema sekuma Umar autansu..
            Rayuwa sukai cikeda k'aunar junansu, suntaso duka kansu a had'e. Baba Asabe takula dasu dukansu. Bata yadda wani zaije gidan yaga Alamun ba ita tahaifesuba. Sunsami tarbiya da karatun addini dana zamani dai-dai misali. Har yasamu yashiga F.C.E Bichi ita kuma Barira aka mata Aure.. Haka har lokacin da kowannensu yai aure. " Ta dalilin cigaba da karatunsa yamaidahi Birni". Yafara kasuwanci. "Tinda 6angararen dayake kenan". 

Yana zaune a unguwar 'Dorayi,Babba. Ba laifi yayi Aure-Aure.
    "Hajiya Aina'u itace matarsa ta lalle. Tanada 'ya'ya biyar. Tarasu awurin haihuwarta ta k'arshe. Matarsa ta biyu kuwa. ```Auren,zuminci```, akaimasu da ita wato Mama-Lubabatu itama 'ya'yanta takwas dashi.
     Dakanan ya Auri Momy Lami da Goggo Safiya. Goggo Safiya itama 'ya'ya takwas ta haifa.

Tarasu yai su duka  "yasanar masu zai 'kara Aure". Bakowo bace kuma face, Ummu-Salma. K'anwa gawani abokin cinikayyarsa dake Gusau. "Wadda itace Innarsu Naja'atu".
        Jin hakan bak'aramin Tayarwa da Momy Lami hankali yaiba. Ta tada K'ayar baya. "Hakan kuwa yai sanadiyar barinta gidan.

Inna Salma itace matar daya auro ta 'karshe kuma yake Matuk'ar santa da tausayinta. "Domin tasha wahala agurin mutan gidan dama 'ya'yansa mata manya dasuke ganin Sa'arsu aka auro." Kuma tanama kansha. 
   Danma tana  Hak'uri da kawar dakai gameda abubuwa da dama.
**********
 Wannan kenan!!!

*Didi_Aneesa*🍼🍉😜
[2/18, 10:40 AM] ‪+234 703 962 5239‬: 29/10, 12:30PM
 ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA*....♡
             *Na*
*Haleema G Khaleel*
  
              0⃣4⃣

Banafsha itace Babbar 'ya agidan, Allah yayita mai Larurar, Kurmanta dakabaya ma ta,rasu. Daka ita sai Habiba, se yaya Lawan shine babban namiji kuma 'da na uku duk 'ya'yan hajiya Aina'u ne takuma haihuwar  Adam inda A haihuwar Kausar ta rasu. Se rik'onta yakoma gurin Mama Luba. Itama 'ya'yanta takwas. Dina, Fadil, Bahijja, Fahad, Haris, Labiba, Rumaisa da Habibu. 

Momy Hadiza kuwa 'ya'yanta hudu:  Bilkisu, Afiya, Fa'iza se Musa su kadai tahaifa tabar gidan. Inda Goggo Safiya takeda Takwas itama: Hafiz, Idrisa, Mabruka, Madina Bilal, Dauda, Nasir da Juwaira.

. Inna Salma, Mahaifiyar su Naja'atu. Tun lokacin datazo gidan, Dina da Habiba sunga Sa'arsu mahaifinsu ya auro suke taya Iyayensu Kishi. Bak'aramin wuya tasha agurinsuba. Gashi bata haihu da wuriba sedaka baya. "Bayan anmasu Aure har Dina tahaihu" da shekara biyu sannan Inna Salma tahaifi tagwaye, Isma'il da Ibrahim. Sannanne haihuwa ta bud'e mata akai-akai. 

"Ta haifi  Naja'atu dak'annanta Kamal, Samiha, Fawad , Salim da Autansu kuma Autan gidan, wato Ahmad(Deedat)".

Duka 'ya'yan gidan su 32 ne biyu sun mutu.
Naja'atu itace 'ya ta Ashirin da biyar Agidan. Duka in an ha'da da kannanta tara dana sauran d'akin dakuma wadda suke Uwa daya Uba 'daya.
        "Alh Abdul-Mu'iz yakasance mai yalwatawa iyalansa komi dayake ahakkun Uba shiyakeyi. Makaranta mekyau da tarbiya gwargwadan iyawarsa " Lokacin dayake kan samunsa. "Tinkamin karayan arziki tasameshi.

Watarana Inna suka tashi Samiha bata da lafiya, ciwan ido dakyar aka wanke, mata da ruwan 'dumi yabud'u.
 "Ga Alh, bashida kudi" 
    Sukarasa yazasiyi,
Ita ba sana'a ba.

 dakyar Hafiz d'an Goggo Safiya yasamo mata 'dari hu'du. "Dominshi yana tausayamata" kuma jininsu ya had'u. "Tamaidashi tamkar ita ta haifeshi ita dama bame zafi ba".
    Sau dayawama inyasamo 'yan ku'di wurin sana'arsa yakan raba biyi yabata, duk abinda yasameshi kuwa na dad'i ko akasin haka zai gaya mata tabashi shawarwari. Kuma yaga fa'idan hakan.

Hausawa sukace ```Abinda babba ya hango, yaro ko yahau Dala baze ganoba.```

Post a Comment

0 Comments