Dutsen ciki ruwa page6 hausa novels

 DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡

                  *Na*

    *Haleema G Khaleel*

      

            *76-80*


""Tun suna saran haihuwarta har EDD haihuwar yazo yawuce, ba abinda kedaminta se kumburin dajikinta yake gawani haske da d'ashewa daduk jikinta yayi.

        Wata safiya suka nufi Asibiti da ita dan tun cikin dare take abu guda, dak'yar ta iya Sallah asuba. Dan itama Sallar azaune take tunda cikinta yatsufa. Abincin da Inna takawo mata taga bata bud'a komaiba. Tana kishingid'e sefitar da numfashi take da k'yar duk tahad'a gumi. Inna ta tallafota tareda jinginata ajikin garun d'akin "Inna Bayana ciwo" Naja tafad'a dak'yar. "Subhanallah! Badai abinne yazoba? Ina zuwa" Innar tafad'a tafita daka d'akin.


D'akin Mama Luba Uwargida tashiga tasanar mata "ko zatazo takai Naja'atun Asibiti tunda itace babba agidan. Bud'ar bakin Mama Luba secatai "Ita gaskiya bazata iya futaba dan bak'i zatai, yanzuma zaman jiransu take suna hanya." Inna mai sauk'in kai takuma cewa "dama dan kada abin yazama laifi shiyasa tazo tagaya mata dan abata girmanta na babba agidan... bata idasa rufe bakiba Mama Luba tace "kinga dan Allah banasan hayaniya kinzo kin gayamin tunda nace bazaniba a hak'ura mana". Sum-sum Innar tafita tana Addu'ar Allah yanuna mata ranarda mutan gidan zasu shirya.

           To yadda sukai da Mama Luba haka sukai da d'aya matar gidan wato Goggo Safiya ita cewa tai ma "Unguwa zataje taje takaita mana su innasune wasuke nema yakai musu. Ranar Inna ranta ya6aci sosai, dandai kawai batada dangi agarin za'ana yimata haka. Samiha tanemo a waya, suka rufewasu Fawad d'akin insun dawo tunda kowa zai iyaima kansa komai dama Deedat takeji inyada yaga batanan.


A Napep suka tafi Asibitin ko Alh bata sanarwaba. To duk zaman awannin dasukai Naja'atu bata haihuba aranar. K'arshema dawowa gida sukai wajen Maghriba da aka tabbatar musu da cewa "ba haihuwar ceba. Haka Naja taita fama saida taikwana biyar ahaka.

          Zuwan da Maman Usman tayine suka yanke amaidata Asibiti.kar aje asamu matsala da abincikin ko ita uwar. Da wannan shawarar sukai amfani. Motar da Maman tazo da ita suka kaira Asibitin. Basu nemi kowaba dan ita kanta Maman d'an zuwan datake gidan tafahimci irin zaman dasuke agidan. Dandai su Naja'atun da Mahaifiyarsu sun maida komai ba komaiba sam abin baya damunsu dan dole wataran zasu dena ko duniya tabasu darasi. Lallai hausawa sunyi gaskiya dasukace *"DUTSEN CIKIN RUWA..BAISAN ANA RANA BA"*. Asibitin Nagari Hospital & meternity sukaje dan tun dawowarta Kano nan take zuwa.


Tun rana da aka kaita Asibitin Naja'atu take abu guda Nak'uda sosai take likitan dake Dutyn Ranar yana kanta har dare lokacin tashinsa yai. Zuwa daren duk k'arfinta yabi yak'are Mama sai mulmula mata bayanta take. Dr nafeesa datake dutyn daren tana zuwa lavour room d'in taga yadda Naja'atun tayi cikin yabi yarairaye yai k'asa iya galabaita tayi bata haihuba. Kayan aiki aka had'a mata da taimakon wash Nurses suka shirya Naja'atun Dr Nafeesan dakanta taturata zuwa ```Theater room``` Emergency C.S zatai mata takadda tabasu sukai singning akai ciki da ita.

        Inna Addu'a take ta mata. Suna zaune jugun-jugun. Jiran tsammani har goma da rabi na dare.  Dr Nafeesa kuwa suna kan Naja'atu itada Dr Moses da sauran nurses. Baby boy akafara cirowa sannan aka ciro 'yan mata guda biyu d'ayardai andenneta sosai acikin. Yara kamar mahaifinsu duk aka gyaresu sede wadda aka ciro ta k'arshen ita sam batai kuka ba. Dr nafeesa da Dr Moses suka rik'o 'ya'yan tareda wata Nurses suka kawasu  Inna yaran. Se farinciki Mama cema tai k'arfin halin cewa Ina Maman tasu bata gama maganarba aka turota akan gado zuwa d'akin hutu aka shigaddasu duka da ragowar kayanta.


Yaran annad'esu a showel harsu uku, Maman Usman kuka tasa sosai da ganin yaran, yau ga jinin Usman alokacin da Usman yabar duniya. Batareda hayaniya ba sukaita d'aukan yaran sud'au wannan su ajiya sud'au wancan. Maman Usman kuwa ga hawaye ga dariya duk afuskarta. Waya tasa tana tai musu Hotuna jitake kamar tamaidasu ciki sekace yanzu akafara haifa mata Jikoki. Inna har tausayinta taji.

       Se wajajen shabiyu suka bar asibitin akabar Inna da Samiha. Cikin daren yaran sekuka suke mace d'aya da namijin, d'ayar ko motsawa batai ba. Zam-zam Inna tasa dabino aciki taita basu suna sha, se jijjigasu suke seda sukai bacci suma suka runtsa dukansu.


Da Asbah bayan sun idar da Sallah Dr Nafeesa tashigo dubasu dan dawuri zata wuce. Anan Inna taimata complaining kan d'ayar babyn sam batai Kukaba ko motsi bataiba. D'agata Dr tayi tak'ara jijjigata amma shiru overall d'in Jikinta tayaye duka tad'an d'ala mata, nanma shiru, tak'ara jijjigata ba alamun numfashi tace "I think so dama itace ak'arshe kuma biyun sundanneta dakuma galabaitar da mahaifiyarsu tayi yataka muhimmiyar rawa. Batazo da rai ba." Atafi da ita gida abunne. Allah yaraya sauran yabada masu albarka. "Haihuwar farine ko? Dr Nafi tafad'a tana kallan Inna tareda mik'a mata Jaririyar. Tai musu sallama tatafi  idan incharge na safe sunzo zasu duba Naja'atun may b kafunnan ta farfad'o.


Karfe 7 nasafe Maman Usman tazo hae har Yaya Yusra, lokacin sukaita bugawa dangi nakusa dana nesa waya. Suna sanar musu da haihuwar. Mik'o mata Matacciyar Jaririyar Inna tayi tace "wannan bata da rai kutafi da ita gida a bunneta". Allah sarki Mama tace "Allaj yai bame shan wuyar duniya bace." Can Sharad'an suka tafi da ita aka binneta inda aka kai mahaifinsu.


Lokacin dasuka dawo har Alh dasu Sadiq a sannan Naja'atu ta farfad'o. Likitan daya karb'i dutyn safen shiyazo dubata yace "kar abari tai jijjinan motsi sosai, espcly kafarta sannan subata ruwa ko abinci mai ruwa-ruwa, banda abu mai k'ayau. Yafaffad'a musu duk irin abubuwan daza ai mata dawanda bazataiba.

           Dataimakon wata Nurse tai brush, aka bata shayi sannan suka gyarata. 'Ya'yan data haifa aka ajiye mata kusada ita sunsha wanka sai k'amshin turaren jarirai suke. Tana daka kwance 'ya'yan duk agabanta, kallansu taitayi cike da k'auna, wata soyayyar yaran taji tanabin kafofi da jinin jikinta. "Kamarsu d'aya dashi ko Yaya Yusra? Naja tace da Muryatta dabata gama warwarewaba, k'wallace tabiyo bayan maganar tata, itama Yaya Yusran sun bata tausayi sosai taji itama kamar tasa kukan, dandai kadata k'ara bata k'arfin gwiwar yin kukan yasata danne zuciyarta. Anan suka sanarmata uku tahaifa sedai d'ayar batazo da raiba. Zaro idanu tayi tace "duk acikina, lallai Iyayenmu sunsha d'awainiya damu. Kuma dole miyi Biyayya agaresu tahanyar dabata sa6awa mahalicci ba muddin munaso mu wanye lafiya a duniya. Alllah yasaka musu da d'umbin Alkairu yabiyasu da babban rabo. Allah yak'ara bamu ikon cigaba da faranta musu dayi musu biyayya bisa turbar Islama. Itakuma Allah yamata rahma yakyautata namu k'arshen. Duk mutan d'akin suka amsa da Ameen.


Kwanansu biyar a Asibitin mai jego tawarware sosai, har tana shayarda yaran. Namijin mai hak'uri, macen kuwa rikici gareta. Danna Inna da Samiha basu gajiya da d'awainiya dasu ko kuka suke tana bacci ba kasafai suka fiya tashintaba. Inna takance "batta tai bacci tad'an samu hutu, ita kada'i tasan gumurzun datasha daga rainnan ciki har haihuwarsu." Dukda dai kowace mace da kalan nata abubuwan.



© *Didi_Sady*🍼🍉😜

[2/18, 10:50 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡ *DUTSEN CIKIN  RUWA.....*♡

               *Na*

*Haleema G Khaleel*



          *81-85*


_Afuwa Makaranta wannan labari. Bajan rai bane kunsan d'an adam ajizi ne. Abubua sunyi yawa. Kwana biyu kuma banida lpy. Ga bukukuwa da aketayi a fam. In sha Allah before Jan 2017, zan kammala. Nagode da k'aunarku gareni aduk inda kuke._



~~~Aran kwana bakwai da haihuwar aka sallamesu da rana. Duk wani kud'i da aka kashe tun farkon zuwansu Asibitin Baban Usman ne yabiya, dan cewa yai "Haryanzu da nauyinta akansu, dan haka duk abinda ake buk'ata yace "Agayamasa" Mama kuwa suka 6alle bakin aljihu akai komai cikin mutunci da girmamawa.

         Bare dasukaga anhaifar musu Tagwaye. Kayan barka sosai suka siya ranar dasuka koma aka bisu da tukwici dak'yar suka kar6a. Acewarsu "Ai yiwa kaine anriga anzama d'aya.

          Ranar suna kuwa bawani taro akai ba. Rad'in suna akai aka sawa Namijin sunan Usman itakuma macen aka samata Asma'ul Husna. Samiha tasa musu Hassan da Husna. 'Yan barka sukai tazuwa 'yan uwa da abokan arzik'i. Kayan barka iri-iri suka samu, wasuma sa shekara suna amfani dashi.


Mejego tayi k'alau da ita. Dan jego mai kyau ake mata har sukai wata biyu. Yaran sunyi 6ul-6ul dasu, kamarsu da mahaifinsu se dad'a baiyana take. Ita kanta Naja'atun kamar ba ita ta haifesu ba, dan gyara sosai Inna da taimakon k'anwarta Aunty Husna sukai mata. Irin zugudan nan dayawan masu ciki keyi bayan haihuwa, basu bari tayiba. 

         Tayi k'alau da ita. Sedai idan takalli yaran nata takanji tausayinsu natashi dazasi basuda mahaifi. Tak'udurce aranta bazata ta6a bari siyi Maraiciba.

      Duk yadda zatai takare Mutuncinsu zatai wanda bai kaucewa shari'a ba. Kuma ga kakannunsu da dangin mahaifinsu dasuke sansu da ji da k'aunarsu.



*BAYAN SHEKARA HUD'U*


Hangota nai cikin _Nagarta Shoping Complex_ d'auke da basket a hannunta. Deedat nagani yak'ara  girma rik'e da hannun wasu yara masu kyau dabazasufi shekara uku da rabi ba. Mace da Namiji, kalan kayansu iri d'aya, sedai Bambanci na Mace da Namiji. Macen anmata kalba datasha Bead se reto suke ajikinta.

          Tsayawa tai wurin kayan k'amshin gida tanata duba irin wanda takeso. Domin ita ma'abociyar k'amshi tundaka najiki zuwa na d'aki hakama kyawawan 'yan biyun 'ya'yanta Hassan sa Husna.


Naja'atu kenan matashiyar Bazawara, datun bayan rasuwar Mijinta bata sakeyin wani auren ba. Asalima catai ita tagama, seda mahaifanta suka tsaya tsayin daka  da Addu'a da rok'on Allah tasaki ranta tadawo  da walwalarta daduk wata mu'amala harta koma  Makaranta da D.E daga level2 tafara har take shekarar k'arshe a course in ```Nursing and Nursing science```.

         Jitake zata iya Aure ayanzu, kowaye yazo muddin yanada d'abi'a da mu'amala ta k'warai, kuma yakwanta mata tayi Na'am dashi da wanna  tasamu tarufe bakin Iyayen nata. Ganin ana shirye-shiryen Auren Samiha da sauran k'annanta Mata, amma ita shiru.


K'wace hannunsa Hassan yayi, daga hannun Deedat ganin Husna tayi gurin toys dandama tafishi wayo. Da gudunta nayara tayi gurin toys tagano 'yar tsana, Bangazar mutumin dataine yasata tsayawa. (Sanadi😻)


Agogon daya d'aukane samfurin ```Dior``` yafad'i daka hannunsa har saida Glass in ya tsage. "Ya salam! Ya furta da _Husky voice_ insa mai amo. Irin yawan dayasha yana neman ```Wrist watch``` in besamuba se anan gashi yanzu kuma abinda yafaru ko biyan kud'inshi baiyiba, cikin jin haushi da takaici afuskarsa yad'ago zai mata masifar wata irin matace dabata tafiya a hankali? Tajamai wannan d'anyen aikin. Batasan irin wuyar dayasha yana abu guda naneman brand na Agogonba.

        'Yar k'aramar yarinya kyakyawa idanuwansa  sukai tozali dasu.

Husna kam ganin yasha mur bashiri takama kunnuwanta tai kalar tausayi tace "Am sory Uncle" ai saurayin besan sanda ya murmusaba yaji yarinyar ta burgeshi sosai. Inama 'yar sace, tunano yadda Mahaifiyarsa babu abinda takeso irin yayi Aure, har matakaiga samun zuri'a.

          Shafa kanta yai yace mata "Be careful kinji Babyta next time kirik'a tafiya a nutse karkije kima wani irin tawa yadakeki, bama haka ba kada kiji ciwo kinji." D'aga kanta tayi alamun taji tace "Thank you Uncle" Matashin saurayin yace "Oya give me five" yabata hannunsa suka tafa sunata dariya.


Hassan ganin ba a daki Husna ba, sunata  dariya, shima yataho yana dariya dabaisan akan me ake ba.

        Da mamaki afuskarsa yake kallansu duka. Mik'amai hannu Hassan yayi da nufin su gaisa. Saurayin kuwa yakama d'an hannun Hassan suka gaisa. Tsugunawa yai dai-dai tsayinsu yace "U are identical 2wins?" Saboda tsananin kamanninsu yayi yawa. Yakuma fad'in "Am i right?" Yana cigaba da kallansu.


Husna da surutu takuwa hau zuboshi "Mamynmu tace mu Triplet ne amma d'ayar tamutu ita bamugantaba.

        Dariya yahauyi sosai daya jima baiyi irin taba. Yace "Shikenan nikam nayi new friends yau, amma bansan sunankuba."

          Husna takuma cafe maganar tace "Mu 2wins in Mamynmune yanzu amma sunannu ni tanuna kanta sunana Husna Usman Bello Galadima, shukuma Hassan sunanshi Usman Usmab Bello Galadima, sunan Babanmu aka samai shine ake cemasa Hassan. Amma har yanzu Abban bai dawoba Mamy tace "Yayi tafiya inda ba a dawowa. Shiyasa bayanan.


Kuma mu kullum baya d'aukomu a school, sukuwa su Farouk Abbansune  yake zuwa d'aukansu." Tafad'a tareda kama hannun Hassan. Shima yace "Se Mamynmu ko Uncle."

         Sunbashi tausayi sosai, yafahimci  komai wato Mahaifinsu yarasu basuda wayo ko ba a haifesuba.


Kama hannayensu yai duka yace "Tare dawa kukazo gurin nan?

     Hassan yace "Da Mamy da Ya Deedat. Batasan munzo nanba dan tace mudena surutu inba Alkairi mutum zai fad'a ba yai shiru. Har Rok'o  dayawoma tace. Ana sace mutum inyaje yawo inda baisaniba yadena ganin kowa har Mamanshi." Ko Husn Yafad'a yana kallan Husna. Surutun kuwa sukai tamasa yanata record dan sun birgeshi. hadda tambayarsu to in aka saceku yazakuyi. Zaro ido sukai suduka. Husna datafi wayo tace "semu kira Mamynmu awaya ko Uncle Isma'il da Ibrahim." 

       Yace "To tayaya zaku kira?" Digit tahau fad'omasa yanata mamaki.

  

Jiyai sunkuma shiga ransa, kamar yatafi dasu tunda duk yaji details insu har Adress in gidansu dana kakanninsu. Suka gayamai yaran masu d'ankaren surutu kamar sunci Kabarai. Ga wayo. Kuma ai shima 'ya'yansane. Tunda hausawa sunce *D'a nakowane*

        Tinanin dayai idan yatafi dasu Mahaifiyarsu yazatai dan ko ina take bazataji dad'i ba. Toma haka ake daka ganin Sarkin Fawa sai Miya tai zak'i Koshi bazaiso amai haka ba. Dankuwa sai inda k'arfinsa yak'are.


Yace musu "Shi sunansa Uncle mai zane, daga yanzu yazama Uncle insu shima. Sukuma sun zama Friend d'insa. Suka tafa dukansu. Sunata mumma, yama manta da batun Agogonsa.

          Zagaye sukai tayi, yasai musu toys da chocolate, wafer,biscuit dayawa. Aikam yasha godiya gurinsu.


Sukaje aka biya kud'in. Har waje yarakosu, kaya taganosu dasu nik'i-nik'i. Ita Husna ma jan kayan take.

            Nemansu take tayi har suka futo zasu shiga mota. Cogewa tai tana kallansu se muzurai suke.




© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜

[2/18, 10:50 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*

                *Na*

     *Haleema G Khaleel*



           *86-90*


~~~Yaran sunsan in Mamyn tasu tai shiru, tana kallansu sunyi laifi kenan.

         Tun basu fahimtaba, har suka gane me shirunta kenufi, dukansu suka saki kayan hannunsu suka kama kunnuwa atare sukace "Afuwa Mamy" ganin tayi shiru batace komaiba suka k'ara langa6ar dakai, kalar tausayi sukai sosai.


Shigewa mota tai kamar zatatafi basu, da gudunsu suka taho har Hassan yakusa kifewa, "kayanfa wakuka barwa" Mamyn tasu tace, tana kuma kallansu, tasha mur. Suma d'if sukayi suka sunkuyar dakai.

        Bud'e motar tai atsawace tace "Kushige mutafi, zakusan kunje yawo daga zuwa daku harda rok'o, punishment zaku kwana kunayi, Abincima bazakucuba tunda bakujin magana.


Ai bata k'arasa maganganunta ba suka shige motar dasauri suna kuka dukansu jin hukuncin daza amusu.

      Duk abinda yafaru yanadaka gurin k'ofar shiga _Complex_ in yana hangosu,"dukda baiga fuskartaba, hakan datai musu yanuna tanasan sukasance cikin tarbiya, ba kwad'ayi dasan abin duniya ba.


Kayan dayasimusu suka bari, yazo yad'ibesu amotarshi yasa, yabar gurin shima ko siyayyar dayazoyi baiyiba. Direct gida yawuce.

          Mahaifiyarsu dasuke kira da Umma, tana zaune littafin *Garkuwar Musulmi* ne a hannunta tana dubawa, da Sallama yashiga falon. Ganinshi tai d'auke da kaya. "Sannu da gida Umma" yace tareda zama. Ummantasa tadubeshi da kulawa tace "Harka dawo ashema ba jimawa zakaiba, afitarba?"

Ajiyar zuciya yasauke  yace "Ah Umma d'an akasi akasamu a inda naje.

      Anan yakwashe komai yagayamata, dan itace abokiyar shawararsa tun yana k'arami, shi ko yawan abokanai bashida su. Ummansa itace kominsa,  har _recording_in surutun di Hassan da Husna yakunna mata taji, na dariya tayi na tausayi ta jimanta, yad'ora dacewa "Shifa gaskiya seya bisu yakai musu kayan" yashige d'akinsa. Umman tasu  tabishi da kallo aranta tana Addu'ar Allah yabashi mata tagari dazata kuladashi. Shima yai Auren koya dad'a samun nutsuwa  arayuwarsa.



Arc Sulaiman Tajuddin Kazaure shine sunansa. Mahaifinsa Alh Tajuddin Hafiz Kaxaure da mahaifiyarsu Hajiya Maryama. Asalinsu 'yan jihar Jigawane, Aurensu tunna Saurayi da Budurwa, Allah ya albarkacesu da 'ya'ya Hudu duk Maza, Muhammad Kabir shine Babba Barister ne mai zaman kansa,  suna zaune a Abuja tareda Matarsa Farha da 'yayansu uku.

        K'aninsa Tasi'u shima da iyalansa su suna zaune a Kazauren inda yake aiki. Mebimsa Yusuf dabai dad'e da Aureba yatafi da Amaryarsa can Bony a Phorthacoat inda yasamu Aiki.


K'araminsu shine Sulaiman matashi dabai haura shekara 30 ba, Archtecturing yakaranta a Jami'ar ```Kano University of Science and Technology dake Wudil ```A Kano . Zane zane da Allah yabashi  baiwa da fasaha akan haka, Taswirar Gidaje da Ma'aikatu har mutane ma, yamaida kai sosai akan harkar tasa. Allah kuwa yasamai Nasibi acikinta. Hayarsa ake d'auka gari-gari wani sa'in har wasu K'asashe . K'ark'ashin kamfaninsu mai suna _"The Shariff Construction"_.


Suna zaune a D'an Agundi G.R.A, dake Zoo road, sakamakon Aiki dayada da Mahaifinsu Ma'aikatar Ruwa ta Hadeja-Jam'are, reshen jihar Kano.


Hajiya Maryama mace ce mai tsafta, kawaici dasanin yakamata, uwa uba rik'o da Addini. Ga zumincin 'yan uwa nakusa dana nesa, duk ta d'ora 'ya'yanta akan

turbar hakan.

    Allah baibata haihuwa dayawaba, shiyasa takeso Sulaimanu in yai Aure yazauma kusa da ita. Kota rik'a ganin 'yan kufi-kufi akusada ita. Duk sauran 'ya'yannata da iyalansu sunmata nisa.


 Wannan kenan.

  

Naja'atu dasuka koma gida ko kayan data siyo bata idasa ajewaba, takamo 'yan biyun nata Hassan da Husna "Kneel down & close your eyes" tace tana zare idanu. Bashiri sukayi atsorace bawanda yace uffan.

       Harta gama jera kayayyakin, ta adana komai inda yadace. Abinci tazubo dantaci, kasa cin abincin tai, dan tasaba yanzu tare dasu takecin Abincin. Abunka da Uwa da d'a tausayinsu yatasomata, janyosu tai duka tarungumesu  tsam ajikinta kamar za'a k'wace matasu.


Hak'uri suka bawa Mamyn tasu, taja musu warning sosai, suka fara cin Abincinsu cikeda ladabi dan duk takoyar dasu Ladubban ci dasha:-

*Kaci da hannun dama*

*kaci da Bismillah*

*kaci Abinda ke gabanka*

*kada kai Numfashi acikin kofi/k'waryar ruwan*

*kada kashafi band'aki da hannunka*

Ire irensu da neman yafiya yayinda kaima mutum badedaiba. Duk takoyardasu.

     Bayan sungama cin Abincin, aka hau labarai anan taji labarin Uncle mai zane daduk yadda sukai dashi. Taita dariya kuwa, toilet tanufa dan haramar Sallar Magriba.



Sulaiman tunaninsu duk ya addabi kwanya da zuciyarsa, ranar da wuri yashige d'aki bayan yaci Abinci. _Recording_ na surutunsu  dayayi yazame masa abokin hira alokacin, tunani yai tayi koyaje yakaimusu  kayan gida? To maizaice, gurinwa yazo? Tambayoyin dasuka dami zuciyarsa kenan.

       Cikin lokaci k'ank'ani yabi yatakura kansa, zaman hira dasuke da Umman tasu yarage, bashida aiki se saurara _Recording_ insu kusan ya haddaceshi har zanasu yai yadda yagansu. Yakumayi wani haddashi. Yaita kallan zanen hoton.


Ummantasu ganin haka tafara mai zancen yai Aure koya samu nasa Iyalin. Secemata yai "Lokaci nayi zaiyi tacigaba damasa Addu'a.




© *Aneesa_didi*🍼🍉😜

[2/18, 10:50 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*

                 *Na*

      *Haleema G Khaleel*


                   *91*


    ~~~K'arshe shawarar da Umman tabashi, yaje yakai musu kayan, koya samu ganinsu yaji sassauci da rangwame.

   Number wayar daya rik'eta akansa kamar karatu, wadda baisan tak'amaimai tawaye cikin wanda suka lissafo maiba, ya rubutata cikin tasa wayar. Yai jimm, yakira koya je harcan gidan? To inyaje, yace gurinwa yazo? Cin biyun dole yai d'aya. Kiran wayar yashiga yi.


   Naja'atu zaune akan k'aramin  cushing, Hafsa k'awarta data kamata ziyara tana mata Oiling agashinta,mai tsayi da santsi, Husna nagefanta tana bacci. Hassan kuwa wasansa yaketayi, dan intana gida duk inda tasa k'afa suna gurin. Intatafi School kuma suna gurin Inna, harta dawo.

     Wayarta tashiga ruri, ganin bak'uwar Lamba  harta katse bata d'agaba, yakuma kira har sau uku, akaro nahud'u ne Hafsa tadubeta tace "Haba my K'awa ki amsa mana, inkuma kink'i ni mik'on wayar nad'aga, wayasan ko sabon Miji muka samu".

   Naja'atu dai batace komai ba tad'aga wayar.

     "Peac be upon you, danAllah ahad'ani da friends ina, Hassan da Husna. Inason jin lafiyarsu, nakasa sukuni, since the time i was meet them, am feeling like they are my Kids". Yashiru yaji maizata ce.

    Itakuwa _Husky Voice_ insa taji amonta har tsakar kanta, kalamansa nak'arshe sun ta6a zuciyarta, basan sanda tace "Kaine Uncle mai Zane da ake tamun surutunta?"

     Murmusawa yai kamar yana gabanta yace.

   "Nine Arc Sulaiman T Kazaure, Uncle mai Zane,i hope bazaki hanani jin muryar Yaranaba?"

   "Gasu"

Tace tamik'awa Hassan wayar. "Hassan ga Uncle mai Zane".

   Da murnarsa yakar6i wayar suka hau surutu kuwa hartaji yafad'a masa "Husna tayi Bacci".

    Labari Naja'atu suka shiga itada Hafsat, dukda tunaninta yatafi gurin wayar da Hassan suke.

     Hassan yamik'o mata wayar tasa akunnanta.

  "Please Mamynmu abani Permision nazo naga yarana?"

   Dariya tai tace

    "Anbaka"

Batasan miyasaba tun kafin suhad'u taji yakwwanta mata, kodan yanasan 'ya'yantane.

   Sallama sukai duk sun murmushi, suka aje wayar.


   Yammacin ranar kuwa, segashi yazo dukda bata fito ba, yaji dad'in ganin yaran dayazo sabidasu.

    Sukai tasurutu yana biye musu harda hotuna. Kayayyakin daya siya musu suka bari yabasu, hadda k'arin zanensu dayai Manya, sukad'ai  dawanda yahad'a harshi. Seda yaga shigewarsu gidan shima yatafi.


  Kayan  suke ta duddubawa, idanuwanta sukai tozali da kyakyawan bahaushe d'an mutan Kazaure, kan Zanen dayai musu, Hoton taji yashi Zuciyarta, taita shafar fuskarsu.


  Duk abinda take da yanayin datashiga, a idan Inna, Murmushi tai irin nasu na manya, zataga iya gudun ruwansu duka.


  Yawan wayar dasukeyi da sulaiman, yafakaice dayiwa Hassan da Husan waya. Abin yashigesu sosai, har takai ga in ba ai wayar ba basa jin dad'i, banda sak'onni dasuke turawa junansu. dukda basu had'u ba. *Soyayya da Shak'uwa*(littafin my xoxo) tashiga Zuk'atansu.

  Naja'atu gani take sabida yanasan 'Ya'yanta, shima yasamu gurbi aZuciyarta.


  Sungama waya da Yaran dadaddare, yace

   "Subawa Mamynsu"

Mik'a mata wayar sukai, sukatafi kallan Cartoon da Deedat yakunna.

   Cikin wata iriyar murya dabata sabajin yayi irintaba a shagwa6ance yace.

   "Mamyta!"

Har cikin jikinta da kanta taji amon furucin, kamar shikad'ai yafi kowa iya Ambatar sunan.

   Akasalance ta amsa da "Na'am Uncle yaukuma nima nazama taka?"

 Kamar yana ganinta yai murmushi tareda fad'in "Zanso hakan Mamyta"

  Rintse idanu tai, besam yadda kalamun ambaton sunanta da yake lugwigwita Tanderun zuciyartaba, daya tausaya yak'i ambaton sunan.

Yakuma cewa 

   "Please kibani dama nanuna miki hakan, bakida matsala dani, in short kiji labarina. Yad'an gaya mata ```Biographynsa```," yakashe wayar yabatta da tunani.


Nannauyar ajiyar zuciya tayi tasan za'ai haka dama.




© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜

[2/18, 10:50 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*

                  *Na*

      *Haleema G Khaleel*


   

               *92-93*


~~~Bata 6oyewa Inna komai akan saba, yadda yagayamata, Innartamusu fatan alkairy da za6in Ubangiji.


  To 6angaren Sulaiman yagayawa Ummansa yasamu Mata, amma Bazawarace hadda 'Ya'ya biyu, Umman tai shiru kamar bazatai maganaba.

   "To amma ita yarinyar tana sanka?"

 Murmushi yai yace

   "Batada matsala Ummana ki amince tazama Surukarki, Matar d'anki, dazata bawa Autanki cikakkiyar kulawa."

  Umman tadubeshi tareda cewa "to Allah yatabbatar da Alkairi."

  Rungumeta yai yace "ina sanki Ummana, Nagode Nagode yabata peack agoshi."

 

  Dariya Umman tahauyi, tana hango yadda Matar dazata Auri Sulaimanunta zatai d'awainiya dashi, da shagwa6a dukda ya girma befasaba.

    Sukaita hirarrakinsu kafin akirashi awaya yafice daga Gidan.


 Fad'uwar da gabanta yake ya tsananta aranar, tunda Sulaiman(Uncle mai Zane) yace mata zaizo.

   Simple makeup tayi, ita kanta kwalliyarma takwan biyu bataiba. Less _Mint Blue_ tasa riga da skirt tai d'aurinta daidai da zamani, spray tasa kad'an da turarenta _Urban Woman_ ta d'ora babban gyale akan kayan. Jelolinta Hassan da Husna suna gefanta suma sunsha ado. Sun nutsu kamar basuba kar ace kartace bazata fita dasuba. Ta dubesu tai murmushi.


  Wayarta tashiga Sauti, Hassan dasaurinsa ya mik'a mata, ganin sunan "Uncle Sman" a Screen d'in wayarta, dan haka tai _saving_. Samun kanta tai  da rikicewa kaman bata ta6a tsayawa da namijiba. Seda takai zuciyarta nesa tad'aga wayar. Cikin sassanyar muryatta, ya amsa tareda langa6ar dakai "Ran Gimbiya yadad'e, fatan nasameku lafiya?"yafad'a kamar yana gabanta.

   Murmushi takumayi, suka gaisa yasanarmata dagashi ya iso, tasa aimasa iso. Seda tai jim sannan takashe wayan.


  Innarsu tasanarwa take tasa Fawad yashigo dashi falon bak'i na Babansu, Ruwa tabayar aka kaimasa da leman d'anyar citta, daya d'au sanyi dai-dai sha had'eda Meat-pie.

  Akunyace tacewa Inna bari taje, tabita da Murmushi tanaimata Addu'ar samun Alkairy.


  Zaune yake d'aya daka cikin Kujerun falon, wadda take fuskantar k'ofar shigowa, yanata danna wayarsa. Sassanya kuma Zazzak'ar Muryatta datai masa Sallama tasashi d'agowa, ya amsa idanunsa akanta, sanda ta d'ago itama idanunsu suka had'u, dukkansu saida wani bak'on al'amari ya tsirga musu, itatai saurin d'auke idanunta ta sunkuyar dakanta.


  Tana guri guda daka can gefe tazauna, su Hassan da Husna suka gaidashi kowa ya mak'ale agefan kafafun "Uncle mai Zane" injisu da fad'a.

   Naja'atuma ta d'ago kai tareda rusunawa tagaidashi "Barka da Yamma" muryatta kaman ana busa sarewa.

  Ya maidamata da "Barka kadai Mai kyau, nasameku lpy?"

  Murmushi tai daya k'ara fito da tsantsar kyanta. Tace "Lafiya lau ya mutan gida?"


  Hira yaitamata, dukda rabin hira ta Yarantace, Hassan da Husna, sedai tad'an saki jiki dashi kad'an.

   Jaka yad'auko agefansa guda biyu, yabasu kowa d'aya ahannunsa yace "Sukaiwa Inna" danduk yaji labarinsu gurin 'yan biyu, yahad'asu da Sweat suka fita sunata Farinciki. Dukkansu suka bisuda kallo suna murmushi.


  Haske tagani Walll! Tajuya tana kallansa, yasakar mata k'ayataccen Murmushinsa daba kowa yakewa shiba. Waya tagani a hannunsa alamun Hoto yamata. Sulaiman Ganindayai takafeshi da _Bold Eyes_ d'inta yasashi cewa "Am sory  Ummana zan kaiwa taga Surukarta mai kyau that why nai Snapinng naki dukda Original Pic inki yananan Album guda a Bottom of my heart" sunkuyar dakai takumayi ganin irin kallon dayake binta dashi yace "Lallai yau kinaso nakwana gidannan indai zaki cigaba damun wannam Smile innaki dake tafiya da Ruhin mai kallo, Uwa Uba Kunyar ki datake k'aramin shauk'in san kasancewa tare dake."


  Anan yarik'a bayyana mata *Babban Sirri (My Yaya Hajja Novel)* dake ransa. Ita kuwa Naja'atu mamakinsa take daga *Had'uwar Farko* mutum ya zak'e, lallai saitayi dagaske zata gano irin San dayake mata bata k'ara mamakantuwaba seda taji Sulaiman yace "Naja'atu ga k'ask'antaccen bawa yazo gareki da k'ok'on barar soyayya har tazama ta Aure *Ni dake (Phertylicious ta)* muzama k'ark'ashin inuwa d'aya, ga miji yazo gareki akaro nabiyu. Amma zanbaki lokaci ki shawara saidai da had'uwarmu da Auren  bazai wuce wata biyuba banma son hakan."

   Baijira maizata ceba yaimata sallama yatafi.

 Ita kuwa Naja'atu bin bayansa tai da idanu harya fice. Dak'yar tatattaro dukkanin nutsuwarta tashige cikin gida.



© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜

[2/18, 10:50 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*

                 *Na*

     *Haleema  G Khaleel*



               *94-95*


~~~Lokutan dasuka biyo baya, duk batada sukuni. Gani tai Tunanin bazeje mataba sai tashiga adduoi da neman za6in Allah.

  Har d'an fad'awa tayi yasa Inna takuma mata nasiha.


  Kullum cikin dare zatai Nafila Raka'a biyu ta *Salatul Istikara* tai addu'a danneman za6in Ubangiji.

     _Garemu 'yan uwa Musulmi yayinda wani abu yashige mana duhu komike shiga dabaibayi gameda neman abu ko samun abu na Rayuwa, Neman Aiki, Neman Aure, Karatu. Wani Abu dai makamancin haka. Inmukai hak'uri komi mai sauk'i ne_.


Cikin Hisnul Muslim(Garkuwar Musulmi) dasauran Litattafai na Addini da Addu'ar tazo.


  *Jabir bin Abdullah Allah yak'ara musu yarda: Manzan Allah S.A.W yakoyar damu ISTIKHARA acikin kowane al'amari kamar yadda yakoyar damu sura daga Al-Qur'ani yana cewa:- "Idan d'ayanku yana dawani Al-amari seya Sallaci Sallah raka'a biyu, badaga cikin Farilla ba, seyace:-* ```ALLAHUMMA INNI ASTAKIRUKA BI ILMIKA, WA'ASTAQ DIRUKA BIQUDRATIKA, WA'ASALUKA MIN FADHLIKAL AZEEM. FA'INNAKA TAQDIRU WALA AQDIRU, WATA'ALAM WALA A'ALAM, WA ANTA ALLAMUL GUYUB.

  ALLAHUMMA INKUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA(ka/ki fad'o Matsalan taki ko wani abu daki/ka ke nema) KAIRULLI FI DINIY WA MA'ASHI WA'AQIBATA AMRI, FAQADIRHULI WAYASSARHULI SUMMA BARIKLIY FIHI, WA INKUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA (ki/ka fad'o matsalan kowani abu daki/ka nema) SHARRILY FI DINIY WAMA ASHI, WA AQIBATU AMRI FASRIFHU ANNIY WASRIFNIY ANHU, WAQADURHULI KAIRA HAISU KANA SUMMA ARDINIY BIHI.```

  Yaitayi in sha Allahu zaisamu daidaito da za6in ubangiji.


**********


Sulaiman kuwa, Mahaifinsa yasanarwa yasamu mata danhaka Addu'ar dasuke masa akullum lokacinta yayi, sai aje anemomasa Auren.

  Ba jimawa Manya suka shiga maganar, aka tsaida za'a d'aura musu Aure tareda 'yan uwanta inyaso tatare daga baya.


  Shirye-Shiryen biki ake tayi. Amaren Gidan se kintsasu ake da gyata according to Sunna.

  Wayar da Sulaiman kemata, sema abinda yak'aru, har fad'a sukeyi yadda tak'i sakin jiki suzuba Soyayya dashi. 'Yan biyunta su Hassan da Husna sun zama 'yan Gidansu "Uncle mai zane" bawanda besan dazamansuba se yayunsa dabasanan kokuma insunzo lokacin bekasuba. Yazama wani sashe narayuwar yaran dayalashe gurbi dadama a zuk'atan yaran da 'yan uwan Naja'atunma tukafin ya Auri Mahaifiyarsu. Hakan yasa duk yasamu Shaidun k'warai dakykkyawan zato.


   Agajiye liss! Tadawo gida daka Sch karatun yad'auko k'arewa basuda wani hutu inba _Exams_ dake gabansu sukai suka gamaba. Ga abubuwa duk sun had'e mata, wayanma ba kasafai take barinta akunneba.

   Ruwa tawatsa tazauna tana hutawa, dan fashin Sallah take alokacin. Riga ce Bubu me fad'i ajikinta me launin ruwan Madara tasaka hula ruwan k'asa se k'amshin turarenta na _Urban Woman_ take. Wayarta takuna bata jimaba kiran "Uncle Sman" yashigo kamar bazata d'agaba.

  Jin sassanyar muryatta yasashi sakin wata wahalalliyar ajiyar zuciya yace "Haba Mamynmu(inyaso raha haka yake kiranta dashi) kina wahal da daddyn yarafa, ko laifi nayi bansaniba?"

  "Ah ah fa Uncle" 

"To miyafaru?"

"Allah Uncle ina busy ne dayawa kasan munkusa fara _Final Exams_ dole wasu abun semun hak'ura dashi mi _Concentrate_ akaratunmu kodan muwuce gurin kawai."

 Tafad"a dawata irin Murya a shagwa6e.

  Numfashi Sulaiman yakuma saki yace

 "Allah sarki kice inzo miyi karatun tare, bakomi ma ai nasan Mamynmu _Gifted_ ce ko _Guru_ zance?".

   Dariya tasaki tana "kaikam kacika tsokana. Nidai katayani Addu'a kawai."

Irin muryatta yakwaikwaya yabata amsa. Dariya takuma saki sukai ta hira kamar karsu rabu.


Abinda yai shirin fad'a mata ma yabarshi ganin abubuwane agabanta ba kad'an ba.

  "Ina sanki Naja'atu"

"Hmmmmmm! Alamun ajiyar zuciya yaji. "Nibazakice kina sonaba?"


"Ina sanka mana Uncle, kaine sanyin idaniyata dazaka maye gurbin abubuwa dayawa... harda zuciya...." bata k'arasa fad'in maizatace ba da _Hanging_ wayar ganin shigowar Inna dasu Ibrahim da Isma'il Yayunta, wanda alokacin sunzama matasa sosai dako Auren kowace mace sukaje nema za abasu yadda Allah yaimusu kwarjini da Baiwar kyau tsantsa. Sunkuyar dakai tayi tana juya Cup in hannunta. Ganin basuce mata komaiba, taware sukaita hira wadda yawancinta ta bikin dazasine da yadda suke shirya Al-amuran sukasance cikin lafiya da kwanciyar hankali har agama bikin.




© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜

[2/18, 10:50 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡

                  *Na*

      *Haleema G Khaleel*


              *96-97*


~~~Da ikon Allah, aka fara shagulgulan biki. Hausawa sukace Rana bata k'arya.....! 

  Asabar 12 gawatan Goma dubban jama'a suka shaida  d'aurin Auren 'ya'ya hud'u na Alh Abdul-Muiz Auwal, Namiji d'aya da Mata Uku. D'aurin Auren yaya Hafiz akafara d'aurowa Tudun maliki, da Amaryassa Maryam.

Juwairiyya da Angonta Aminu. Samiha da Mukhtar, wanda silar had'uwarsu Allah yamasa shiriya kamar dawasa suka fara Soyayya da Samiha kuma Allah yai matarshice takaisu gayin Aure ayau.

  Akaro nabiyu aka kuma d'aurawa Naja'atu Aure da Angonta Arc Sulaiman Kazaurw.


          Yana daka cikin Al-adun bahaushe nawannan lokacin yayin Aure. Bayan and'aura Aure, Angwaye da abokanansu, sukan shiga gidansu Amarya domin gaisawa da Iyaye Maza da Mata. Hakance takasance gidan Alh Abdul-Muiz A yacika fal da Jama'a masu Hotuna, da Marok'a seyi suke.

  Mazajen Samiha da Juwairyya se hotuna ake musu haka Yaya Hafiz ma anatayi dawasu 'yan uwan. Sa6anin Sulaiman dayakasa ganin tasa Amaryar se washe baki yake kaman gonon Auduga. Abokansa kam se tsiya suke masa.


  "Yanzuke hakan dakike yayi dai-dai kenan? Inma bazaki shiruba yaci kin kammala shiryawa" Inna data shigo tatsaya akan Naja'atu datake ta shar6an kuka, tunda akakusa bikin tazama sukuku da ita duk tasusuce banda ramar data kumayi. Dayawa sunmata magana tak'i shiru sega Innartasu takuma dawowa.

   Anty Husna ganin datai kamar Inna zata rufe Naja'atu da duka tai saurin matsawa kusada ita, Lalla6ata tashigayi ahankali tana mata Nasiha "Haba Daughter na kedama bayau ko gobe zaki tafi gidan mijinba. Ko Samiha kiduba daza akaita gobe batai wannan kukanba ammake anrasa Kukan mekike ko Aurenne bakyaso?" Tana kallanta ta girgirza kai "To maza kishiru kinji Aure ai Ni'ima ne da Daraja. Shine Cikar Zati Kamala da Mutuncin duk wata 'YA MACE muddin tarik'e mutuncinta tobamai kyetamataahi. Kuma kowace Uwa dakikagani Burinta ta Aurar da 'YA'YA MATAn dake gabanta shine samun nutsuwa da kwanciyar hankalinta. Kowa kuma da haka tasaba. Maza k'arasa shiryawa kar Mijinnaki yazo yaganki haka, kinji 'yar albarka". Shiru tai duk tasaurari metace k'awarta Jidda da Mino dake fama da ciki sukai tamata iya-ege, ahaka suka k'arasa gyaramata kwalliyarta data 6ata da kuka suka Shirya fes da french less coffee colour damayafi milk&coffee har kanta se k'amshi take Amarya tafito fess da ita se ajiyar zuciya datake saki.


  Gud'ar dasuka jiyoce, taji wata mata dabata gane waceba tanata Kabbara, sekirari takewa Inna da 'Ya'yanta. Sulaiman suka shigo har falon Inna gaisawa sukai tayi da 'yan uwa dake falon. Anty Husna tajata suka fito falon, kanta asunkuye. K'walla tataru a idanunta. Masu hoto da masu d'auka da waya sukai tayi hasken Flash kawai kake gami.

 

   Kukan datake 6oyewa ahankali take shashshek'a, Sulaiman datun shigowarsu seda yaganta farincikinsa yak'aru. Bayan mutane sund'an ragu  a falon, duk'addakai Sulaiman yai yad'an tallafo Naja'atun sesuka bada wani Style masu Cemara kam mezasiyi ba hotoba akaita _Snaping_ insu. Ni Aneesa_Didi Duk k'ok'arina na injiyo muku meya cemata akunnenta banjiyoba murmushi nikaina nasa ganin kowa yana darawa.

     Itakam ganin Sulaiman naneman bata kunya yasata sakin murmushi tareda janyewa daka jikinsa nikuwa nace kaga Masoya. _Gud Moment_ kenan "Tears & Smile".



Post a Comment

0 Comments