Azumin ilu hausa novels 5

 AZUMIN ILU*

😂😂😂😂😂😂


       *peg 17*

*MAMAN MAMY*......✍

09031711711 for comments


```har in bazakayi magana akan novel ba to karka dauki number nan plss```ngd


💖💖💖💖💖💖💖

*RAMADAN KAREEM*

💖💖💖💖💖💖💖


*Allah kasa muna cikin intattun bayinka Allah kayafemana zunubanmu badon yawan ibadun ba ya Allah*🙏🏻🙏🏻🙏🏻





Tun kafin ya iso inda su ILU suke ya hau balbalin masifa .....kai ILU bana hana fito da tabarmun masallaci a shimfida awaje a zauna ba... Wato kun raina arzikin mutane ko????



Basiru ne ya dubi ILU shima ILU ya dubi mudi cike da mamaki yake fadin mudi ina kaga tabarma anan iccen nan nefa da aka sare muka Dan baza ganyayenshi .....dariya basiru yasa wllh maigari najin azumin nan shifa da tsiya idanuwansa tabarma suke gane masa ba rairayi ba...


Aiko gaba daya suka kwashe da dariya ...dai dai lokacin maigari ya I so yana share zufa zai dasa wani balbalin masifar ya daga kai haka ya ga ba tabarma bace sukuti yayi yana kallon su.....


Da sauri suka dai daita Kansu da dariyar saboda sunsan halin maigari ba mutunci ne dashi ba....


ILU ne ya dubeshi ya maigari ka mance ne ka taho da but a ahannu ko ka mance nan masallaci akwai butocin yin sallah?? ILU ya fada yana kumshe dariya tare da kallon butar dake hannun maigari.....


Sai lokacin maigari ya dubi butar dake hannunshi ....lokacin da yayi alwallah ne sai ya mance bai ajiyeta ba ya taho da ita ....


Dan murmushi yayi ....kai dai bari ILU wllh alwalla nayi na mance ban ajiye butar ba nama rasa tunanin da nikeyi....


Yar dariya ILU yayi... To kodai azumin ne ya maigari??


Har maigari zaiyi magana aka kabbara sallah ...da sauri suka nufi masallacin gaba daya ba tare da an ida caftar ba...


Jamaa liman fa najin AZUMIN nan saboda karatun sallar ya fara gura gura ...inya karanta aya saiya Dan jima bai tuno ta gaba ba ...gashi sallar shaf shaf akeyinta wato yar faki inji yara ba yawa sai lada...


Jamaa sai mamakin liman suke ganin yadda ya rude yake Neman kasa yin Jam'i 


Ahaka dai aka kammala sallar su ILU nata kumshe dariya ...


Bayan anfito ne dattawan garin aka tsaya ana tattaunawa ...malam ne ke tambayar liman lfy..


Uhm bari malam liman vya fada yana dafe ciki yau dorere nikeyi bansan ya akayi na makara ba ...duniya gaba daya ta zame min doguwa ...


Har malam zaiyi magana  maigari ya rigashi ...to ai nima dorere nikeyi nikam wani irin bacci nayi da ban taba yin irinsa ba tun da Nike arywa ta ...


Subhanallah liman ya furta a wahalce ...to ai nima irin baccin da kake fadi nayi.. Wato ni kamar ma matattace na koma ...ikon Allah to wannan wace irin masifar  bacci CE ta samemu ...ko kaima irin shi kayi malam??? Liman ya fada yana kallonsa



Azabure malam ke fadin ...aa nikam banyi irin wannan bacci n ba ..saboda tun lokacin da suka fara maganar ya fara zatgin da wani Abu akasa bare daya tuno kalaman ILU da safe da yake cewa.. Yau akwai kallo a kauyen nan ....



To Allah ya kyauta ...inji maigari yawwah malam dama inaso inyi maka godiya ...jiya ILU yazo yayi min barka da shan ruwa harda abin arziki gaskiya naji dadi ILU kam an fara hankali....



Liman ne ya karbe... To Ashe bani kadai yayi ma wannan abin arzikin ba ...nima jiya saiga ILU yazo min barka da shan ruwa da lemu mai sanyin gaske ...in gama ina gama shan shi da yan mintina na hau wannan mugun bacci n....


Kallon sa maigari yayi ..to ai nima ina gama shan lemun ko minti biyar baayi ba bacci mai nauyi yayi awon gaba dani ...


Malam ne sukaji yana babbaka dariya harda tafa hannuwa ...kallon shi sukai gaba daya lfy malam??


Uhm lallai sannunku ...ai kun shiga tarkon ILU Ashe Ku har yanzu Baku gama sanin waye ILU ba ...in banda abinku wake cin kudin ILU a kauyen nan bare har ya saya maku lemu mai sanyi ...


Shiru malam yayi saboda dariyar data kubce masa ...

Amma dai anyi jairin yaro wurin nan ..haba nidai nayi mamakin irin bacci n da nayi kuma na Dade INA tunanin kyautar da ILU yayi man ban sake shiga mamaki ba said a naji maigari yace shima ankai masa.. Oh! ILU ILU


Liman ya fada cike da takaicin abinda ILU yayi masa daga baya kuma sai dariya ta kubce masa tunowa da yadda sukayi da ILU da irin ladabin da yayi masa Wanda baisanshi dashi ba ....



Shi kanshi maigari dariyar yayi ..kaga jairin yaro yasa gaba daya na fita hayyacina saboda yunwa... Kila gara ni da liman .. Shifa liman takalman kafarsa daban daban ne saboda tsabar jin AZUMIN ...


Tuni liman ya turbune fuska wane irin gara kai ...maigari tun daga gida fa ka taho da buta ahannu da alama ba kasan ka taho da ita ba ....


Dariya malam yayi ...nidai yanzu don Allah kuyi hakuri ...ni kaina Dana haifi ILU bai ragamin ba in shegantakarsa ta motsa baiji bai gani ....


Aa ba komai malam ...to amma me yasa yayi mana haka ne ...liman ya fada yana shafe zufar dake keto masa ...


Uhm tun da kukayi masa dariyar dorere shine abin ya bashi haushi ni nasani yakace kuma sai kunyi ...ai arayuwar ILU ba abinda ya tsana irin kaGanshi cikin wani hali kayi dariya saboda haka saiku kiyaye....



Ikon Allah ...maigari ya fada.. Ba komai gobe ka turomin ilun da abokansa zan zartar masu da hukunci saboda in baa hukuntashi abinda zai rikayi kauyennan ba karami bane ....



Da dai ka barshi kawai ...liman ya fada saboda shi ya tsorata da lamarin ILU ...


Shidai malam baice kar a hukunta ILU ba...saboda ana iya ganin don yana dansa...


Amma yasan bazasu iya yimasa komai ba ...saboda ILU ya ishi kowa Riga da wando...



Ahaka sukayi ban kwana kowa ya nufi gidan sa ...


Malam na zuwa gida ya hau yima iya bayan I tayi dariya sosai suna cikin hakane ILU ya shigo yana fadin 


WO! Ni ilu ilun malam wayace dani bani ba dara bataci gida ba .....


Malam ne ya dubeshi yana murmushi... To albishirinka jairin malam dara taci gidaje bama gida ba...








*hhhhhhh Muje zuwa labarin ILU donjin hukunci da maigari zai yanke masa anya maigari bai tabowa kansa ba*




*ni din daice maman mamy Nike cewa kunsha ruwa lfy*

[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*






😂😂😂😂😂😂

*AZUMIN ILU*

😂😂😂😂😂😂


       *peg 18*

*MAMAN MAMY*.....✍



💖💖💖💖💖💖💖

*RAMADAN KAREEM*

💖💖💖💖💖💖💖


*Allah ka yafemana albarkacin wannan wata mai albarka*🙏🏻


```barkanku da shan ruwa masoyan ILU ```😁



Cikeda mamaki ILU ya dubi malam ...bangane ba ya malam ILU ya fada yana gyara bajejiyar rigar dake jikinshi ....


Eh ai bazaka gane ba... Yanzu kai ILU ka kyauta kenan kasa bay in Allah dorere ba gaira babu dalili....wllh ILU kazo ka natsu kullum shekaru na gaba amma ba hankali ....


Yar dariya ILU yayi ..kayi hakuri ya malam ..ILU zaiyi hankali nan bada dadewa ba ...kuma daman ai hakane ya kamata da mai dariyar mugun ta bakaga da liman namin dariya jiya ba har wani dukewa yake ...


Kai ar jairi... Malam ya katse masa tunani ..towai ma me kasa masu a lemun ...


Dan kwanbare kafada ILU yayi ba wani Abu bane ya malam Dan maganin bacci ne irin mai nauyin nan ...sai kuma ya dubi iya ...wllh iya yau liman yana jin jiki Ashe haka limamai ke rudewa sukaji yunwa ...sai kuma ya babbake da dariya ...


Takalmin dake kafar malam ya cire ya jefe shi dashi ya kauce yana fadin tuba Nike ya malam..


Ajiyar zuciya malam ya saki ..ai gashi nan kajama kanka da abokanka gobe maigari na Neman ku ya zartar maku da hukunci dai dai da laifinku kuma wllh ban bashi hakuri ba kuma kasan halin maigari Allah dai ya kyauta ...daga haka maigari bai kara cewa komai ba ya mike ya shige dakinshi yana murmushi yasan ILU da tsoro ....


Ragwaf ILU ya zauna yana yake mai kama da dariya dariya ...uhm wllh iya maigari ya kuskura ya sani kiwon awaki cikin AZUMIN nan zaisha mamaki nasan karshen hukuncinsa kenan ...


Dariya iya tayi ..a to ai in mutum baaiji bari ba yaji hoho duk kuma Wanda baiyi sharar masallaci ba yayi ta kasuwa ...ai gara ya turaka kiwon dani nace kajemin kiwon bazaka jeba ....


 Mikewa ILU yayi yana jujjuya wa dubi nifa iya babban yaro dani duk kauyen nan ba mai kyawuna ..sai ace in rika yin kiwo ...ai iya dani mai kudi ne wllh zaaga takama da iko ...


Hararsa iya tayi da wannan bajejiyar rigar taka zakayi iko da takamar ji cikin ka wane mai kudi zai zauna yayi katon ciki irin naka ....um ni kaga bari in tashi inyi sabgar gabana da wannan sokanar taka ..wai kudi ko yaushe zai yi kudin ..



Yar dariya...ILU yayi ya dubi iya data tashi ta nufi kicin tana dariya... Uhm insha Allah sai nayi kudi iya nasa an gyara maki kafafuwan nan naki da kike dungurawa ya kara babbakewa da dariya ....


 


ILU fa lamarin yayi masa kyau mussaman suke labe bayan gidan liman suna kwasar dariya saboda kofar gida ya baje yana dafe ciki kamar ba namiji ba ...



Daga karshe liman bai kara komawa massalaci ba sai gaf da zaa kira sallar magariba ya fita yayi zaune bakin massalaci yana Jan cazbaha gsanin ban tausayi .....






Bayan an sha ruwa ne liman ya tsare ILU sai nasiha yake masa kamar zaiyi kuka... ILU kam sai to yake

 cewa in ta shiga tanan ta fita tanan ba alamun nasihar na shiga kunnuwansa baima gama nasihar ba ILU ya mike yana fadin ...ngd sosai ya liman Allah ya biya ..bai jira amsar dazai bashi ba ya kara gaba yana baje rigarsa..


Girgiza kai kawai liman yayi tare da fadin Allah ya shirya mana ILU ...


         *nima dai nace ameeen*😂




Washegari ILU ankusa ma kara ...saiga iya da asabe da ILU na cin abinci kwano guda saboda basu ma tsaya wani kasa wa ba saboda karancin lokaci ...



Washegari da wuri maigari ya aiko kiran ILU da abokansa ....

Fito wa ILU yayi yana dariya to iya mu zamu fita Allah dai ya fidda ai  ga rogo..

Dariya asabe tasa ...Allah yasa kar ta fita ai n ..


Dariya iya tasan ya harda dukewa.. Harara ILU ya zabgawa asabe ..ai asabe tuni na gano baki kaunata ...yayi waje yana fadin Muje ai maigarin ba Allah bane ...

Har ya kusa fita ya dawo ya dauki ashana ...ya dubi iya ki dakamana tasshi mai dadi ...



Cikeda mamaki iya ta dubeshi me zakayi da ashana da tasshi ...


Kila maigari zai soye ko ..asabe ta fada tana dariya... Binta yayi aguje ta shige daki tare da banko kofar...



Fita yayi yana haki... Zaki sani innadawo iya na tafi ...


To ILU Allah ya tsare ....



Said a ya biya ma basiru da mudi sannan suka dau hanyar gidan maigari ..basiru na fadin alkuran ba ruwana...






*Muje dai zuwa labarin ILU*

[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*






😂😂😂😂😂😂

*AZUMIN ILU*

😂😂😂😂😂😂


       *peg 20*


*MAMAN MAMY*......✍



*ba dai zan gajiya ba da godewa masoya ako INA ma suke tabbas ILU ya Tara masoya to Allah yayima masoyan sa albarka ameeen*💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖




Wata uwar harara ILU ya rafkawa basiru ....dad in a dakai gajen hakuri Allah dai ya kaimu goben ka ba idanuwan ka abinci ...ILU ya fada yana yana kara daga wata katuwar kaza mai manyan cinyoyi ....kai Allah yayi halitta wurin nan jar uba mudi kaga kaza kamar wani Dan akuya .......



Dariya mudi yasa hadda buga kafa ...kai wllh naji dadin kiwon nan amma ILU gobe ma zamuci ko???yar dariya ILU yayi ah sosai mana mudi ai naga maka gobe akuya zamuci mu ....ai mun dosa cin dadi har nan da sati biyu duk wani gefe na cikina daya lomake saiya taso .....


Hhhhhhh basiru yayi dariya to taya zamu yi sati muna cin kaji bayan maigari kwana ukku yabamu hukuncin sa ......ILU ne ya dubeshi I do cikin I do ai a bsyaninsa yace duk Wanda bai zo ba zai kara masa kwana ukku to jibi mu dukanmu bazamu zobs kunga kenan zai kara mana kwana kan cin kaji ....kai dai wllh kanka baija basiru ....


Eh din naji baija amma ni tsoro na daya muci naman maigari cikin azumi ai haram mukaci .....injiwa ai zamu rokeshi gafara bakiji me nace dazu ba ..kai basiru cin kajin nan fa ba dole don ni nan da kake ganina sai incinyesu duka banji komai ba bare dama anrabi da haduwa yaushe rabon da inci kaji mudi ya dubi mudi cdake gashin nama yana share zufa...


Kai rabu dashi ILU nidai wllh ci zanyi yana gani mai gari ko zakkar kajin nan bai bayar wa ..kuma basiru dake fadin haka baifi kowa hadamar nama ba ko ka mance lokacin da muna yara basiru fa don tsananin kwadayi mai tsiren bakin Santa yake ma wanke wanke in yayi ya yanmasa tsoka guda ....


Dariya suka sa gaba daya hadda basirun yana fadin to naji aiba filin tone tone bane ......


Ahaka suka gashe kaji Tass! Suka sakasu cikin Leda mai nata diga sai kuwa kamshi suke duk da bawani magi akasa ba sai kamshin suyar .....



Basu dawo gida ba sai gab da azhar anma fara kiraye kirayen sallah ...mudi aka ba rikon kaji su kuma suka tsaya hado kawunan awakai kaf ...



Said a suka sakasu gidan su sannan suka nufi hanyar fita ILU ne ya dubi bangaren kaji ....sannunku namomi sai goben kuma soyayya kuda ILU har nan da sati ...ILU ya fada yana gyara katuwar rigarsa ta gado saboda yawan sata da ILU keyi har ansanshi da ita da anhangoshi zaace ga ilun malam can kosu basiru wani lokacin da sunganshi da ita zasu fara fadin yar gado ta ILU Riga daya tamkar da dubu .....



Suna fito wa aka tsaya shawarar yadda zaakaiwa maigari makulli saboda kajin dake hannun su  .....ILU ne ya karbi makullan kujirani bari inkai masa ....


Zaune ya iske maigari yana alwalla azahar yana ganin ILU ya hau was he baki .....sannu ya maigari  inji ILU makullin ya mika masa gashi mun dawo ....


Karba yayi yawwah ILU sannunku kunsha kiwo Allah dai ya bada lada ...awakan sun dai koshi ko?? Yar hararssa ILU yayi a fake eh kwarai kau sun koshi sosai saika gansu ...



To shi kenan jeka sai kuma goben Ku dawo ina sauran ne... Tafiya ILU yayi tare da fadin suna waje ..kafin mai gari ya kara wata magana yayi waje yana gyara tashi da kwakwar dake kanshi ...




Dai daya suka raba kajin maana kowa ya tashi da dakwale guda guda ...mudi sai was he baki ake shi kanshi basirun murmyshin farin ciki kawai yake to bare uban gayya ai kunsan basai nace komai ba ...






Tun daga nesa su iya suka fara jin kirarin da ILU keyi ...ilun malam wane mutum bare buzunsa munga jiya munga yau gobe ma in Allah yayi gani zamuyi .....iya CE ta dubi asabe anya ILU na azumi ji fa yadda yake daga murya ..




Dariya asabe tayi uhum tasamu kenan duk in kikaji wannan kirarin

[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *BRRLIANT WRITER'S ASSOCIATION*⚜



Post a Comment

0 Comments