AZUMIN ILU*
😂😂😂😂😂😂
*peg 9*
*MAMAN MAMY*..✍
Nace Ku huta👍🏻
*wannan peg nakine zuzun Alkhairi ...Allah ya raya mana hafeez da hanan*🌹🌹
A firgice ILU ya tashi ji yayi kamar ana kiran sallah.... Da gudu ya nufi dakin Iya yana kwalamata kira... Iya Ku tashi wllh lokaci ya kusayi Ku tashi muyi sahur.. Gani yayi zuwama dakin Iya bata lokacine sai kawai ya wuce kicin da makekiyar rigarsa yana fadin....
Nidai duk Wanda bai tashi ba Matsalar shi CE ..nidai innayi sahur kowa ma ya gane sai ayita tadaku kunaji kuyi banza da mutane ...
Yana fitowa da kwanon abinci malam na fitowa dama sallah yake yanajin duk abinda ILU ke fadi.... Kardai ka kuskura ka ci abincin nan saboda lokaci yayi ...
Sakin kwanon ILU yayi woyyo Allah na shiga ukku ni ILU yanzu shine zaaki tadani wayyo Allah... Saiga ILU na ruwan hawaye ....
Iya CE ta fito da hijab jikinta ...haba ILU sai kace ba namiji ba don bakayi sahur ba sai ka ishemu da ihu sai kace Wanda ya rasa iyayensa ...
Kyaleshi yayi salame wane irin tadine ba a yi masa ba yaki tashi ...kuma dorere ba fashi akan shi tunda ba kanshi farau ba....
Aa malam ba kowane tadi aka yimin ba naki tashi.. Tsakani da Allah an watsa min ruwa anga ban tashi ba ko anturamin lomar abinci anga ban tashi ba... ILU ya fada cikin muryar kuka ...ni banma ga alamun anwani tadani naki tashi ba... Kawai dai kunaso yunwa ta kashe nine shiyasa ...
Eh yunwar ta kashe ka .....Ai wurin
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*
😂😂😂😂😂😂
*AZUMIN ILU*
😂😂😂😂😂😂
*peg 10*
*MAMAN MAMY*..✍
*fans Ku yafeni ganin peg 9 kadan wllh bisa kuskure ya tsaya haka plsss ayi hakuri*
Ai wurin ibada ka mutu... Kaga maza kaje kayi alwalla mu tafi massalaci kar mu rasa sallah ...wucewa ILU yayi yana fadin shikenan dai an cuceni wllh ancuce ni sai Allah ya sakamin ...
Salame dake gefe ..dariya tahauyi kasa kasa .....ahaka yayi alwallar suka tafi massalaci sai gunguni yake shidai malam bai kara CE mashi kanzil ba dama yasan zaa Rina ansaci zanen mahaukaciya ....
Bayan an fito salla h ne aka tsaya ana gaggaisawa liman ne ya lura da yanayin ILU ....aa mutumen lafiya na ganka haka... Daure fuska ILU yayi tare da dauke kai can sama baida alamar ba liman amsa... Malam ne yayi murmushi ..Ai liman yau mutumen ka baiyi sahur ba shine yake wannan tubukurin .. Saiga liman da maigari na dariya harda dukewa jin cewa yau ILU baiyi sahur ba sunsan cewa akwai bidiri kenan ...
ILU kau kara daure fuska yayi basu San cewa dariyar nan ta bata masa rai ba....liman ne ya dafashi haba namijin duniya ka nuna mana kai jarumi ne ba raggo ba ...duk da dai gaskiya bantaba yin dorere ba kusan shekara biyu kenan rabon da inyi dorere bansan wahalar shi ba amma nasan namijin kwarai lfy Lau zaiyi shi ba irinka ba ILU ..yana magana suna dariya da maigari malam ma murmushi kawai yakeyi ...
Wani Dan guntun murmushin mugunta ILU yayi harya hango ta inda zai rama dariyar da liman da maigari keyi masa ....
Tare suka jero da basiru ya baro malam can suna tattaunawa da mai gari ...wllh basiru inna yadda nayi dorere nan mutum hudu sai sunyi shi sunji yadda naji ...zaro idanuwa basiru yayi dawa dawa ILU...
Da salame da Iya suda suka ki tadani inyi sahur sai liman da mai gari da sukemin dariya bare liman har wani fadi yake rabon da yayi dorere anyi shekara biyu to wannan shekarar zaiyi shi ...abinda yasa bansa malam ba saboda shi dama wani lokacin ko ya tashi sahur din ba abinci yake ci ba sai dai yasha ruwa yacigaba da sallah ...
Kai ILU tayaya zaka hanasu tashi sahur.. Dariya ILU yayi tana kara gyara bajejejiyr rigarsa da tasha faci kala kala... Kai dai sa ido kayi kallo basirun inna... A haka sukayi bankwana kowa ya nufi gida shikam basiru baiyi mamaki ba yasan duk abinda ILU yace zaiyi tofa sai ya aikata shi ....
Misalin 8 na safe ya tashi yaufa ILU ba kanta ..tun lokacin ya fara jin yunwa ...fitowa yayi tsakar gida yayi tsaye gidan shiru kowa sai baccin shi yake hankali kwance ....wani takaici ne ya tokare ILU haushin baccin da yan gidan keyi ya keji shi kuma ya kasa yi ....
Ai wllh yadda banyi baccin nan ba bamai yinshi gidannan ..Ai yau an tokalo tsuliyar dodo.. ILU ya fada tare da nufar tumakan dake tsakar gidan ..ya hau kwance su ..maza kuyi xwaje ...
Saida ya korasu tsaf sannan ya leka dakin Iya ya hau buga masu kyaure ...Ku tashi sai bacci kuke ga tumakai can sun fice daji... A azabure Iya ta mike tare da fizgo wani yagaggen Zane ta rufa tayo waje harda bige ILU.. Ina sukayi ILU yau naga ta kaina ni salame ...da gudu Iya ta fita waje harda tuntube... Dariya ILU ya hauyi dama yasan haka zata faru yadda Iya keji da tumakanta shiyasa bata barin su fita koda yaushe suna cikin gida .....
Asabe CE ta fito da hijab ..haba ILU muje mana mu koro su sai kabar Iya ta fita Ita kadai ...hhhh hhhh kedai jeki asabe biya ina nan kuje Ku kuro su badai kunyi sahur ba yaci gaba da dariya ...hararshi asabe tayi haba nidai nayi mamaki ace gaba daya tumakai sun kwance kuma lokaci guda ..uhm wllh ILU kaji tsoron Allah yanzu don bakayi sahur ba sai kaita wahalar damu alhalin mun tadaka kaki tashi....
Malam ne ya nufosu da kara... Da gudu ILU yayi gefe yana dariya yi hakuri ya malam ...jeka Ku tafi akorosu dakai jairi maza Ku tafi tare kaima ka shawo wahalar da zasu sha wurin korosu ....
Da gudu ILU ya fita yana dariya ..lafiya lau malam aini dama yau rayuwata a wahala zata kare ....mutumen da baiyi sahur ba har an tambayeshi wahala ....
Asabe CE tabi bayan shi tana dariya taji dadin yadda malam yayi masa..
Girgiza kai kawai malam yayi ya koma daki ..dama yasan yau abinda ILU zaiyi ba karami bane ...
Saida suka wahala sannan suka samu suka hado kan tumakan ..zanen da Iya ta yafa saida ya dawo bisa kai saboda wahala kafafuwannan sunyi futu futu kamar basu taba ganin ruwa ba... Asabe CE ke fada mata ILU ne ya sake su..
Uhm Ai dama nasan wannan akininshi ne to Ai shima ya wahala tunda dashi aka korosu...
Dariya ILU yayi ...ba komai Iya don na wahala ni dama baccine banso kuyi gaba daya yadda yunwa ta hanani baccin safe to gara kowama ya tashi...
Asabe CE ta kalli Iya itama Iya asaben take kallo .....
*hhhhhh Maman MAMY ce duk Wanda ya karanta novel di nan baiyi dariya ba plss plss ya aiko min da sako zai iso gareni ..ni kuma zan bashi amsa ngd*🤣🤣🤣
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*
😂😂😂😂😂😂
*AZUMIN ILU*
😂😂😂😂😂😂
*peg 11*
*MAMAN MAMY*.....✍
Iya ce ta yi Dan guntun murmushi... Yanzu kai ILU tsakanin ga Allah baccin da zamuyi shine zai tsone maka idanu saboda kai ka kasa yi ...Ai ni dama nasan zaayi haka shiyasa naso malam ya barni inta tadaka koda zan kwana tsaye ya hanani ...
Dariya ILU yayi... Ato Ai kunsan cewa baa kyauta min ba to saboda haka kowa sai yaga rashin kyautuwar .....
Ita dai asabe batace komai ba tasan karamin aikin ILU ne ya bibbigeta akan hanyar yau yadda yakejin fitina ....
Tsakar gida suka iske malam tsaye da cazbaha a hannu shine ya kama masu suka daure tumakan ....duban ILU yayi saura ka kara jawo maku wani aikin tunda kai har gobe ba zakayi hankali ba....
Zumbura baki ILU yayi tare da wucewa ya kwalhi ruwa ya shige kewai yin wanka .....
Yana fitowa ya zira rigarsa ta gado yayi waje... Inda abokasan ke zama ya nufa sai busar iska yake kamar bijimin sa.....
Tun daga nesa basiru ke masa kirari ...sai kai namijin duniya ILU abin alfahari.mu duk yau ba mai dorere a kauyen nan sai kai saboda Kaine jarumin garin .....
Wani murmushin takaici ILU yayi tare da fadin Kaine mutum na biyar da zaiyi dorere Dan ubanka.. Ya fada aransa afili kuwa ba basiru hannu yayi suka tafa nagode ya abokina basiru.....
Tunda ya nemi wuri ya zauna bai kara cema kowa komai ba ...hardai ya kai gaya kishin gida sai lokacin bacci mai nauyin gaske yayi awon gaba dashi ...sai kau minshari yake abinsa...
Basiru ne ya dirka masa bugu... Ya tashi firgigi Yaya akai basiru ILU ya fada yana zare idanu....
Haba ILU kowa na salati anata karatun qur'ani amma kai sai lafta bacci kake wai shin ka kausan me ake nufi da azumi ko kuma watan Ramadan..
Uhm zakaci ubanka basiru... ILU ya fada aransa yana girgiza kai irin zai gane kuransa kenan ......
Wllh ILU ka daina baccin nan ka tashi mu nemi RAHAMA... Dakata basiru ILU ya dakatar dashi.. Kanaso in zagi inna ...aa ILU bazanso ka zagi innata ba.. To ka kyaleni koko nace ladarka sai an raba biyu anbani Rabi shima baccin Ai iba Dane ...ko an fada maka ban lazimi cikin baccin ..
Mudi ne ya hau kumshe dariya yasan daya bari ta fito zai jawo ma kanshi balai ...dubanshi ILU yayi ..uhm mudi kaji da katon bakin nan naka...
Dariya sukasa gaba daya ...wayyo Allah macji maciji ILU ya fada tare da mikewa ya zura da gudu.. Ba arzuki su basiru suka Mara masa baya suna fadin ihu maciji...
Saida ILU yayi gudu sosai har ya iso bakin masallaci sannan yaja birki tare da juyawa yaga yadda su mudi ke shega uban gudu kamar zasu bar kauyen....
Kusa da ILU sukaja birki suna maida numfashi .. ILU ne ya kallesu ya kwashe da dariya ...wai Ashe biyo ni kukayi amma gaskiya bakuda wayo ya kara tuntsirewa da dariya...
Basiru ne ya dubeshi yana maida numfashi... Me kake nufi ILU kar dai kace karya kake ba maciji n bane....
....hhhh basiru kenan Ai tunda banyi sahur ba uban kowa sai ya dandana kurensa.. ILU ya fada yana dariya....
*muje zuwa fans*
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*
😂😂😂😂😂😂
*AZUMIN ILU*
😂😂😂😂😂😂
*peg 12*
*MAMAN MAMY*......✍
*wannan peg na sadaukar dashi dungurigum gareki kawata Lubabatu Umar malumfashi tabbas ki wuce haka awurina kin kuma cancanci yabo ....ngd sosai Allah yabarmu tare*🤝💋💋💋
Amma wllh ILU bakada kirki yanzu saboda Allah abinda kayi ka kyauta... Mudi ya fada yana share uwar zufar dake keto masa .....
Yo Ai kai mudi ba Wanda ya kaini kyautawa saboda da na jawoku aguje bakin masallaci na ajiye Ku ...kunga da an kira sallah alwallah kawai zamuyi mu shige masallaci muyi sallah .....
Ai kuwa hakane ilun malam ..basiru ya fada yana dariya sai kawai suka babba ke da dariya su duka kamar sabbin kamu ...
Wata Yar bishiya suka zauna suna jiran lokacin sallah ya ida suyi kowa ya tafi gida saboda kwatsetsiyar ranar da akeyi ....
Can suka hango liman buzun buzun da babbar Riga sai zabga sauri yake ya kira sallah ...ya kama kan nan nashi ya nade da rawani da katuwar cazbaha a hannunsa ....ILU ne ya fara magana ....dubeshi kamar Wanda zaya janaiza wllh da liman zai gane daya bar Nada rawanin can ...shidai ba sarki ba ba dogari ba amma sai ya kama kai ya nanndae kam kamar kan rago .....
Gaba daya suka fashe da dariya... Kai ILU amma bakada kirki wllh yanzu liman kake ma wannan sharrin kasan kau duk balain ka bazaka sa ya cire rawanin can ba koda yaushe yana kansa kai har bacci dashi yakeyi....
Uhm yanzu kam zansa ya kwance shi ..bari Ku gani ....mikewa ILU yayi tare da nufar liman a firgice ....
Wayyo liman kunama kunama ...da sauri liman ya hau dire dire yana fadin a ina ilun malam kasan ni kunama batamin da kyau ....
Wani ihun ILU ya kara saki gata can bisa kanka ya malam ...a azabure liman ya sauke rawanin kasa ya hau shafa kai cike da furfura yana fadin subhanallah subhannala .....mutane ne zagaye dasu ILU kowa na mamakin tsoron kunama irin na liman ....saida ya gama dire dirensa sannan ya tsaya tare da duban ILU da yayi kasake yana kumshe dariya...
ILU malam ina kunamar ban ganta ba.... Yar dariya ILU yayi nima sai yanzu na lura liman wai Ashe wani Dan kwaro ne ba kunama ba kasan me yin dorere bai gani sosai ....
Aiko mai mutane zasuyi ba dariya ba abokan ILU su basiru harda dukewa kasa ...shikau liman kunyace ta lillbshi dukawa yayi ya dauki rawaninshi ya Dora bisa kai ya wuce buguzun buguzun yana fadin irinku agari annobane ILU n malam ....
Ana gama sallah ...ILU yunwa ta fara cin karfinsa ....da kyar ya Iya fitowa bakin masallacin yayi kwance ...kowa yazo wucewa sai yace sannu ILU malam Ai yunwa dai ba Kanwar Babar mutum bace bareta raga masa ba ...ILU dai ba bakin magana sai idanu....
Liman ne ya dubeshi ...dariya yayi jairi Ai yunwa ita kadai ke maganinka ILU baccin yunwa da wahalarka da zamu sha taka cikin AZUMIN nan ba karama bace ....
Ba yadda su basiru basuyi da ILU ba akan ya tashi su tafi gida amma yaki tashi saima ya fara kuka yana kiran malam! Wayyo malam ...da sukaga haka sai suka kyaleshi sukayi tafiyar su saboda malam na cikin masallacin yana jinshi.....
ILU! Malam ya fada rike da bulalar bugun almajirai ...zaka tashi mu tafi koko sai jikinka ya gayama ka yaufa jairin Yaro raggo ....
Da sauri ILU ya mike yasan karamin aikin malam ne ya zuzzura masa ita ....haba ya malam tama zaayi in kasa tashi Ai dole nane ma in tashi in ina son ganin rahamar Allah ......
Dan murmushi kawai malam yayi ..to muje... Haka malam ya tusa ILU gaba sai fadi yake Allah dai ya tsinewa yunwa yunwa batai ba arayuwa ....
Suna shiga malam ya wuce daki abin shi yabar ILU zaune in war dasu Iya keshan iska.....
Asabe CE ta kalli Iya wai Iya yau me zamuyi ne na budabaki..... Wllh asabe bansani ba amma da ILU zai daure daya auno mana filawa shagon dahiru da sai muyi fanke ....eh wllh don Allah ILU ka taimaka ka auno mana ..asabe ta fada kasa kasa cike da tsoron abinda zai biyo bayan maganar tata ....
Asabe! Naam ILU da mai kamfanin da ake filawar da wanda yayi asalin kawota kauyen nan da mai shagon da filawar take dake kanki dake rokona in auno maki Allah yasa Ku rika jin yunwar da nikeji ...ke Allah ma ya tsinema matar data kirkiri fanke a duniya ....
Dariya asabe tasanya itama Iya dariyar take hatta dai malam dake cikin daki saida yayi murmushi ....
Haba ILU daga tace ka auno filawa ayi fanke sai cibi ya zama kari ...in kuma munyi fanken nan bamu kadai zamuci ba harda kai kilama saika fimu ci .....Iya ta fada cikin sigar rarrashi .....
Uhm iya asabe ta rainani in baccin rain I ita bata Iya zuwa sai ta aikeni niba wanta bane ...kuma da ake maganar hardani zaaci to a hanani mana ga gidaje da yawa a kauye ....wllh Ku kyaleni inba haka ba yanzu nan zan saki tumakai...
Aa yi hakuri ILU anbar zance iya ta fada da sauri tasan halin ILU...
*hhhhhh muje zuwa labarin ILU*
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*
😂😂😂😂😂😂
*AZUMIN ILU*
😂😂😂😂😂😂
*peg 13*
*MAMAN MAMY*...✍
```ayi hakuri fans najina shiru kwana biyu labarin ilu na nan don yanzu akazo wurin saboda yanzu muke dai dai da ilu yanzu be duk mai hali irin na ilu zai San yayi aboki```😆😆😆
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*RAMADAN KAREEM*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*wata mai rahama da Allah ka sadamu da alkhairan dake ciki Allah rahamar dake ciki Allah ya sada mu da ita ba don ibadun mu ba ba don halayenmu ba ya Allah*🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Itama asabe bata kara cewa komai ba saboda tasan karamin aikin ILU me ya jawo masu aikin dayafi wannan ....bats kara cemasa komai ba ta mike ta ziri hijab tayi waje sayen filawar .....ILU kam kara gyara kwanciya yayi yaci gaba da hamma .....
Koda asabe ta dawo nan ta sameshi kwance sai zare idanu yake kamar tsohon dodo ....asabebiya ya fada cikin rawar murya... Naam ILU yaya ko bazaka kai labari bane ....asabe ta fada tana murmushi ...uhm asabe kenan ai indai ILU bai kai labari ba to ba Wanda zai kai a kauyen nan... Nidai yanzu ki taimaka ki kaimin ruwa inyi wanka shine kawai abinda zan rokeki ....ILU ya fada awahalce ...kamar tace baza tai ba sai kuma ta tuno halin ILU ...zumbura baki tayi ta dauki bokiti ta kwalhi ruwa ta kai mashi ...
Dawowa tayi bisa kanshi ...ILU nakai maka ...yawwah year kanwata Allah dai ya baki miji na gari dazai rika saki dafamin abinci kala ukku duk ranar da naje gidanki ziyara harma inna tashi tahowa yasa ki juyemin sauran aleda ya matsamin sai na taho dashi gida.... Ya kuma bani naira Dari yace insha ruwa ahanya ....
Ba asabe da iya dake tsakar gida ba hatta malam dake cikin daki dariya yake hard a dukewa ......said a ILU ya bari sun gama babbaka dariyar sannan ya mike tare da fadin kamani ki kaini yar kanwata ya fada yana lumshe idanuwa shi kadai yasan azabar dayake sha ....
Dan matsawa asabe tayi ...aa ILU no bazan iya kamaka ba ...bari dai iya ta karaso kila ta iya kamaka amma ba no ba.....
Murmushi ILU yayi ..uhm asabe kenan ai indai sai iya ta kamani zan tashi ai kila saina shekara ban matsa daganan ba ...ai ita waccan tsohuwar ki barta kawai da aukin kula da tumakai wannan fa in akuya daya zata yini kwancewa ta fita tofa iya zata yini itama tana kamota no na rasa gane wannan soyayyar dake tsakaninsu ba.... Dariya asabe ta hauyi hadda tafa hannuwa...
Da ka kalli iya zakasan ran tsaffi ya baci da sauri ta karaso gaban ILU ta fizgi hannunsa guda saiga ILU ya ida mikewa .....wllh ILU ka kiyayi tsufa na wato kai nan gani kake ka fini karfi ko to ba zaa taba had a tsohon kashi da sabo ba .....
Dariya ILU yayi spsai... To ai dama no wasa Nike maki yanzu da cewa nayi iya zoki taimaka ki kamani in tashi da langabewa zakiyi kice kafafuwanki ciwo suke amma yanzu cikin ruwan sanyi kin kamani na mike ....kai asabe wllh tsohuwar nan Nada karfi ...ya fada tare da kyalkyalewa da dariya... Malam me yaji dramar tayi mass dad I sai ya fito waje ya shimfida tabarma ya zauna yana kallon ikon Allah...
Asabe in banda dariya ba abinda take ...iya kam sukuti tayi tana yar dariya ...nufoshi tayi da niyyar kai mashi bugu ...cikin zafin nama ya nufi bayi da Dan gudunsa yana dariya wahala...
Uhm tunda Nike ban taba ganin jairi irin ILU ba kaini ko ada baa tabayin jairi irin wannan yaron ba ...iya ta fada tana dariya tare da kallon malam...
Shima dariyar yayi ...salame kenan ai ILU sai addua CE kawai zata iyayin tasiri akanshi ...Allah ne kuma kadai zai iya shirya shi saboda haka mu cigaba da tayashi addua acikin wannan wata mai alfarma kunsan cewa wannan watan rahama ne ana gaggauta amsar rokon bawa ...to Allah yasa dai mu dace ...ameeen suka fada gaba daya ....
Can saiga ILU ya fito daga wanka gefen wuyanshi da gefen fuskarshi duk kumfa wai nan anyo wanka.... Malam ya fara wucewa ...shikam malam baice komai ba girgiza kai kawai yayi tare da yar dariya yaci gaba da duba quranin dake gabanshi ...yazo ya wuce iya itama batace komai ba sai dariya ...asabe CE ta kalleshi tare da babbakewa da dariya.....
*muje zuwa labarin ILU*
0 Comments