Azumin ilu hausa novels 2

 AZUMIN ILU*

😂😂😂😂😂😂


         *peg 3*

*MAMAN MAMY CE*✍



*Allah ka sada mu da alkhairan dake cikin wannan wata mai albarka Allah ka bamu ikon yin duk wasu ayyuka masu lada acikin wannan wata na RAMADAN*🙏🙏🙏🙏







Dariya suka sa masa gaba daya ....sannan sukaci gaba da hirarsu akan abinda ya shafi watan na RAMADAN .....ahaka har aka kira sallar azahar ..ILU kam na jinsu amma ko kallonsu baiyi bare yasa baki .....



Basiru ne ya dubeshi mutumen ankira sallar azahar ka tashi muje muyi sallah sai ka wuce gida kadan huta .....duk cikin dariya yake maganar....



Kamani basiru wllh ashirin ashirin Nike ganinku ...ILU ya fada yana kyafta idanu... Dariya sukasa gaba daya ...ahaka suka kamashi suka nufi masallacin mai gari ....kamar Wanda bai lafiya ...duk Wanda yace lafiya ILU sai yace ...yunwa Ai ba Kanwar babata bace bare ta ragamin sai mutane suyi dariya ..suce da sauran ka ILU tunda bakin bai mutu ba......





Sallah akeyi amma liman sai jawo dogayen surori yake ....kafafuwan ILU rawa kawai suke ...saura kadan ya sallame sallar yayi tasa shi kadai ...hawaye kam wani nabin wani ga wata rana mai zafi da akeyi garin....



Ana kammalawa yayi kwance yana lumshe idanu... Wllh basiru liman mugu ne dayake ya lura da yanayi shine yake Jan dogayen surori ...Wanda ya kara bin sallar shi ..😂



Da kyar basiru ya gimtse dariya ya samu yayi addua ...sannan ya dubi ILU kayi addua kuwa mutumen kake gulma ...kuma ba kyau gulma ana azumi kai ko baa azumi gulma ba kyau .....



Nayi addua mana basiru nace Allah ya nuna min asha ruwa ..wllh yau abincin da zanci ba karami bane ....kuma ni ba gulma Nike ba gaskiya ce ....



Ahaka dai suka rakoshi gida sai ruwan balai yake ma liman kamar shi yasa shi yin azumin ...su kau ba Wanda ya kula shi saboda kowa yasan Matsalar shi ......



To ILU sai anjima mun biyo maka zuwa waazi n da malam zaiyi kafin faduwa r rana..... Kar Wanda ya biyo min kuje kawai ni naje idan ranar ta fadi Ai inaga duk dayane ko... Ya fada yana hararar su ....aa yi hakuri malam ILU abin bana zafi bane...


Na zafin ne ...shin malam din ba ubana bane innaga dama sai ince ya yimin waazin cikin gida ba shikenan ba... Ya shige cikin gida yanata ruwan balai... Abokan kuma suka juya suna masa dariya .....





Yana shiga sukaci karo da asabe zata fita.... Wani wawan bugu ya kai mata cikin zafin nama ta kauce tana dariya ....waike bakida hankali ne baki ganin mutane ...yi hakuri ILU ba gani ba ta fada tana gimtse dariya.....



Wata uwar harara ya gallara mata yayi gaba yana kallon iya dake sama dabbobi abinci... Ga matsayatan da suka fi kowa cin abinci ....amma sai ace ILU ya cika cin abinci ...ga sunan yini kike basu abinci ....iya CE ta dago tana murmushi....



Haba ILU ya zaka hada kanka dasu ...sufa dabbobine kai kuma mutum ne .....eh naji ni mutum ne amma Ai yunwa duk iri daya CE kuma duk abinci abinci ne... Haka kawai sai adameni da su dabbobi ne ...ya wuce dakin shi yana tijara..... Malam ne ya dubeta dake can gefe yana lazimi...



Ki daina biye masa azumi ne dai sai yayi talatin cif koda yunwar zata kashe ka ...katon banza bai aje komai ba sai katon ciki......





Ana kiran sallar laasar ne malam ya leka dakin shi ....ILU tashi kayi alwalla mu tafi masallaci ....malam ka yafeman mutuwa zanyi ILU ya fada yana yan kwalla ....eh Ai dama kullu nafsin zaikatul maut dukkan mai rai mamaci ne ....kazo kayi sallar sai ka dawo ka mutun tunda lokaci yayi ......



Mikewa ILU yayi yana fadin ...eh dama Ai ka kagara in mutu tunda kace ina cinye maka hatsin daka ke nomawa ...to ka daina murna saina ci abinci sosai a duniya zan mutu ...oh ni ILU Ashe anyi Sukuti aga na mutu ahau murna to ina nan ......



Shidai malam murmushi kawai yayi ya wuce gaba ...inka gama shawara da mutuwar ka fito mu tafi masallaci saura ka batamin lokaci .......











*muje zuwa*

             *labarin ILU*

[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*






😂😂😂😂😂😂

*AZUMIN ILU*

😂😂😂😂😂😂


       *peg 4*



*MAMAN MAMY CE*.....✍



*hhhhhh ILU na wuta ina binshi da gas*🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣





Ahaka ya gama surutansa ya  tashi jiri na dibar shi ya yi alwalla idanuwansa har wani lumshewa sukeyi saboda tsabar yunwa .......


Ahaka suka tafi masallacin sai rangaji ya keyi shi kau malam murmushi kawai yake yi ....wani bangaren kuma tausayin ILU yakeji sosai saboda yadda yayi sabo da abinci kamar jaki😂



Ana kammala sallah ILU ya baje yana ta maida numfashi ...Nan take jamaa suka baibayeshi suna sallalami ....da yawansu dariya suke masa saboda sun San abinda ke damunsa  

..malam ne ya iso da sauri 



Sannu ILU bakada lafiya ne... Daga kai kawai ILU yayi ya kasa cewa komai... Maigari ne ya dubi malam... Gaskiya malam ILU ya aje AZUMIN nan tunda bazai iya kaishi ba shiga addinin Allah saukine dashi ko ba yanzu ba sai ya rama tunda lalura CE... Shiru malam yayi yana kallon ILU dake wani kara fitar da numfashi shidai yasan halin abinsa da anbi ta tashi da an kyale ILU yakai AZUMIN nan .....mutane ne suka dinga magana akan abar ILU ya aje AZUMIN ...ba da son ran malam ba ya amince ya koma gefe ya yi zaman shi ganin yadda zaa kaya da ILU n malam ...





Maigari ne ya Ciro naira Dari ya mikawa basiru ....ungo nan jeka siyo mashi fura ta talatin nonon ashirin sai ka dawo mashi ruwan sanyi na goma ka kawo min arbain ......


Da sauri akaga ILU ya mike ...alkuran furar talatin bazata isheni ba ...ka bari kawai ya siyo min ta duka nayi maleji... Kuma ka siyo min ruwa masu sanyi gaske inba sanyi sai ka mai dashi ....kuma duk cikin ku ba Wanda yayi kwantan abinci gidansa ya hadomin dashi ...fisabilillah wa ILU jamaa...... Shiru akayi nadan lokaci sannan jamaa suka hau dariyar ILU shi kanshi basiru tsaye yayi ya kasa tafiya saboda dariya....





Shi kanshi maigari saida ya dara bare kuma mal dake can gefe dama yasan zaayi hakan.....


Am basiru bani nerata Dari ...jamaa kar Wanda yaba ILU abinci Ku kyaleshi ya kaishi tunda shi raggon banza ne baida jumurin yunwa 

......


Komawa kasa ILU yayi ya kwanta yana fadin....to Ai shikenan Ku bari in mutu kowa ya huta dama yan kauyen nan duk kun tsane ni kowa ILU kowa ilun malam....





Ahaka kowa ya watse ya barshi nan kwance kamar matacciyar sanuwa sai katon ciki da yayo sama kamar tulin kayan wanki .....




Sai misalin 5 na yamma ya lallaba ya mike ya nufi gida... Jamaa nata masa sannu suna dariya kasa kasa saboda kowa AZUMIN na gwalar sa amma ba kamar ILU ba .....



Iya ya iske zaune tana gyara waken kosai .....yanzu tsakani da Allah iya sai yanzu zaafara aikin shan ruwan ...jibi fa saura kadan rana ta fadi to wllh aka kira sallah Baku gama ba zaa kwashi yan kallo a gidan nan....


Itadai iya batace komai ba itama yunwar ta isheta ....



Asabe ya kalla dake tace kullu... Waike meyasa baki aiki da sauri ne dubi yadda kike aiki kamar wadda kwai ya fashewa aciki .....


Shin ILU zo kayi in sauki ne abun ....afusace ya nufeta.....


















*Allah ya kawo mana watan RAHAMA lfy*

[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*





😂😂😂😂😂😂

*AZUMIN ILU*

😂😂😂😂😂😂


       *peg 6*

*MAMAN MAMY*.....✍


*sadaqa cikin azumi Allah shine zai baka lada.. Taimaka wa Wanda bai dashi baka fadi ba Allah yasa mudace*







Uhm ILU kenan ...yanzu tashi kayi alwalla mu tafi masallaci ankusa kiran sallah .....


Ba musu ya mike yayo alwalla ya Debi kosai guda goma ya zuba cikin aljihu ya dubi iya da tayi Sukuti tana kallon ikon Allah.....sannan ya kalli asabe dake harararsa ...saura asa guda goman nan cikin lissafi nasan halinki asabe kina iya cewa cikin kaso na.. To dandano ne ....Ku saiku dauki guda biyu biyu tunda tsakani da Allah Baku kaini shan wuya ba ...koma ba haka ba Ai dama kasona yafi na kowa cikin gidannan ........sudai ba wadda tace masa ci kanka 




Malam ne yace muje ..kai kasani ...har sun fita ya dawo... Iya karfa amanta kason malam nawa ne ..ehhe kar ace min an mance ....ya kuma juya ya fita ba tare daya jira amsar su ba .....




Masallaci suka nufa ...daukacin mazan garin na can domin yin sallah sai sadakar dabino da ruwa masu sanyi akeyi ...don hasana saida ILU ya karbi ruwa ukku ya rukunkume jikin shi malam na kallon shi baice mashi kanzil ba .....




Saura yan mintina liman ya tashi ya fara gyaran murya yana Dan zagayawa lokaci ya karasa.... ILU ne ta dubi basiru ...uhm dubi liman wllh abin shi harda gayya lokaci yayi ya kira sallah amma ya kiya ....murmushi basiru yayi kai ILU bakada dama ...lokaci baiyi ba da da yayi daya kira ..

.



Har ILU zaiyi magana yaji liman ya fara addua cikin lasifika ...da sauri yakai ledar ruwa bakinsa da niyyar da yace allahu! Ya datsa ma ledar pure water hakora ko tunanin addua baiyi saita abinda zaisa ma cikin shi .....basiru ne ya rike hannun ...mutumen a taimaka ayi addua tukun ...




An kwala kiran sallah ...da sauri ILU ya hau addua bai gama wata wata ke zuwa ....ya Riga kowa FASA ruwa zuka biyu yayi ma ledar ya shanye... Ajiyar zuciya ya saki sannan ya dakko wata ledar zai FASA... Basiru ya katse sa...




Kai ILU saika cika cikin da ruwa ka rasa inda zakasa abinci ...ina ba dai cikin ILU ba

..Ai nan da kake gani basiru komai da isashen wurinsa a cikin nan nawa ....


Basiru bai kara cemasa komai ba ya kyaleshi ya shanye ruwan kafin sannan ya tamne kosan daya dakko guda goma Dan ball I ya na basiru ......




Ana kammala sallah ILU ne na farkon mikewa yana fadin... Nidai malam nayi gaba saika taho kunsan Allah ma yace a gaggauta buda baki ....shiru malam yayi tunda aka dauki AZUMIN baiji ILU yace Allah yace ba sai yanzu da yake maganar ci CE is... Girgiza kai kawai yayi yaci gaba da adduar sa .... Mutane kam dariya suka hauyi kasa kasa cike da kaunar ILU....







Yana fita ya sheka da gudu yana fadin ....iya gani nan azubamin koko cikin kwanon shan ruwa ....iya gani nan ....





Asukwane ya isa gidan saura kadan yayi kwllo da bokitin kokon ....azabure iya ta dubeshi ..lfy ILU waya biyoka ...


Yunwa ta biyo ni kinsan tun dazu take bina ....ya fada tare da nufar kayan da yaga an shirya masa gefe... Dama jikin iya har rawa yakeyi ta sallameshi kafin ya iso....





Zaunawa yayi tare da bude kwanon kosai ganin shi yayi himili dariya yayi yasan cewa da kason malam aka hada masa ...kai iya Allah ya biyaki da ana samun tsaffi irinki da bayin Allah irinmu sun more ...,






Itadai iya batace komai ba tasan anjima kadan zaa amshe yabon.... Bibbiyu yake tura kosan yana hadawa da koko ana haka malam ya shigo da kwano a hannu.,..















*muje zuwa*

[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*






😂😂😂😂😂😂

 *AZUMIN ILU*

😂😂😂😂😂😂

        

      *peg 5*


*MAMAN MAMY CE*.....✍

Nace Ku huta fans😍



*wannan peg nakune masoyan ILU acici mai cikin Zane*🤣🤣🤣🤣






Hakuri ta hau bashi ....na tuba ILU bazan sake ba... Ganin yadda ta tsorata yasa ya wuce abinsa yana masifa kamar shi kadai ke azumi kauyen ......



Misalin 6 na yamma ya fito sai dukewa kasa yake yana dafe cikin shi idanuwa sunyi jajir dasu ....malam ya hango ya Debi uban kosai aroba zai fita rabawa almajirai...


Da gudu ILU ya isa gaban shi ya riko robar kosan yana maida numfashi .....


Haba malam ya mu bamu koshi ba zaa kaiwa na waje kosan ya kalla ya kuma kalli sauran Wanda iya ke toyawa ....koni kadai zan iya cinye wannan kosan ban koshi ba shine kuma sai ahau rarraba dashi.....



Murmushi malam yayi ...haba ilun malam Wanda ka bada shine naka... Wanda kaci Masai zaije.... Yanzu kai anaka haukan ko barinka mukayi da kosan nan duka zaka iya cinye shi????? 



Wllh tsab zan cinye shi har in nemi kari ...kuma da kace Wanda naci Masai zaya Ai nan ma wata sadakar nayi ma tsutsotsin dake cikin Masan tunda su zasu cinye kashin da nayi ...don Allah malam kayi hakuri kabar mana kosan mu in zan bar kosai guda yayi kwantai Allah ya tsine man ......



Dariya malam yayi ka fahimceni ILU ita sadaka ba lallai sai ka wadatu ba zaka bayar ....a musulunce anfi so ka bayar da abinda kafiso to Allah zai Baka lada sosai ....ka bada kadan Allah ya baka Wanda ya fishi ..sadaka maganin talauci duk mai sadaka Allah bazai taba barin shi cikin talauci ba zakaga da ya bayar Allah zai mayar masa da Wanda ya fishi sannan ga lada.. Bare cikin wannan watan mai RAHAMA .....ILU ka bari abada sadakar nan ni zan hada maka da nawa kason saika cinye ni nasha koko...



Sakin robar ILU yayi yana turo baki.... Abasu amma Allah da kasonka zan hada inaji ina gani bazaa kware niba .....murmushi malam yayi ya Ciro nera hamsin aljihunsa karbi wannan maza tashar alu ga kankara can ankawo ka siyo mana mu jika musha....




A wahalce ILU ya karbi kudin ya fita yana rangaji ..malam yabi bayansa da robar kosan da zai rabama yara ....saida ya tsaya ya gama Harar almajiran sannan ya wuce tare da fadin munafukan banza ......





Tun daga nesa ya hango Layin da ke akwai can ya hango basiru da mudi abokan sa nata bin layi ...dariyar mugunta yayi duk da uwar yunwar dake kwalkwalarsa .....




Can ya zagaya bayan mai sayar da kankara ya fara rada masa ....sannu da aiki bawan Allah dama maigarine ya aiko ni abashi kankara ....dubanshi mai saida kankara yayi ....yaga ILU yaci magani kamar bashi ba ....ba musu ya karbi kudin ya bashi kankara ukku harda kyautar daya gudu kenan....




ILU na dariya ya daga ma su basiru hannu yayi tafiyar shi .....


Lokacin daya isah har sun gama komai suna zaune sunata laximi ...mika masu yayi yai kwance kasa yana fadin... Astagafirrillah da karfin gaske.. Malam ne ya dubeshi ILU kayi cikin zuciya mana...







Aa malam bari inyi afili kunfi sanin halin da Nike ciki na yunwa....









😂🤣🤣😂🤣😂🤣

[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*







😂😂😂😂😂😂

*AZUMIN ILU*

😂😂😂😂😂😂


       *peg 7*

*MAMAN MAMY CE*.....✍


Nace Ku huta 😆







Saida malam ya gara zama ...sannan Iya tayi mashi barka da shan ruwa asabe ma tayi mashi banda ILU ko kala baice ma malam ba sai zubawa uwar hanji yakeyi ......



ILU barka da shan ruwa ...malam ya fada cike da zolaya dai dai lokacin daya kai kofin koko bakin shi .....a haba malam duka yaushe nasha ruwan bare afarayiman barka tukunna dai...ILU ya fada yana kara dagwalo yaji ga kosai.....




Wasa wasa ILU ya kasa cinye Rabin kosan nan... Duk hadamarshi saiga ila na zare idanu gashi daya motsa sai cikin ya bada kululu alamar ruwa ya cika cikin...bare kunsan azumi Nada haka sai kaga kamar zaka Iya cinye Abu amma sai ka kasa




Malam yana kallon shi yanaso yayi dariya amma yaki yarda ta fito ....

Wai Iya kodai AZUMIN nan da nayi an rage min fadin cikina ne ...duka dubi Dan kosan da naci da koko n da nasha amma naji cikina ba sauran wuri gashi banci abinci ba ......



Dariya Iya tayi ...wa zai rage maka fadin ciki ILU... Kawai daga yin azumi sai ciki ya ragu ...uhm dama haka azumi yake sai kaita hadama amma abinda zakaci ba wani bane .....


Ikon Allah ILU ya fada yana satar kallon malam dake tamnar naman kaji Ashe sune a kwano ....



Tuni miyan ILU ya tsinke ..dubarace ta fado masa da sauri ya dauki kwanon kosan ya isa gaban malam ya dukar da kai kasa ...



Barka da xshan ruwa Babana.... Kasan soyayya ta da da uba bazan Iya cinye kosan nan da kason ka ba dama wasa Nike ma Iya ...Itakuma ta hada min da naka ..INA wane ni ...tuba Nike dattijo mai ran karfe .....



Wllh malam karka kulashi ..wayo ne dashi karya yake.. Ka tsare shi ya cinye shi tunda shi yace yaji ya gani ....asabe ta fada tana ma ILU dariya kasa kasa....



Kai kai wai asabe meyasa ke Yar bakin cikina CE duk gidannan kin tsani kiga INA warwasawa ...yinin yau INA lura dake kina min dariya to wllh ki shiga hankalinki dani .......


Ya isa haka malam ya dakatar dashi... Naji ni yanzu na koshi da kosai kaje ka ajiye anjima kaci naci guda biyu wurin salame ya isheni... Amma daka hana abada sadaqa da duk ina zaka kaishi ...malam ya fada tare da yagar naman kaza....



Kuttt! ILU ya hade miyau ...kai dai bari malam Ai gobe in zaka bada sadakar aba harda kaji ..ILU ya fada yana kallon naman kaza yana  murmushin dole ....


Malam baisan sadda dariya ta kubuce masa ba... Duk yagama dago ILU... Kara cirar naman yayi ya mika masa kwanon ...ungo anshi ka diba ka basu sauran.....




Jiki na rawa ILU ya karba ya mike tsaye tare da fadin godiya muke ya malam... Saida ya yagi kafcececiyar  tsoka sannan ya dubi asabe.....




Wllh asabe yau sai da naga kana nan malaikun mutuwa da manyan nagani da tuni na mutu.... Uhm ni ina ruwana koma waka gani ...nidai ka bamu kason mu sai kaci gaba da bamu labarin ......



Kash! Asabe kin cika kwadayi ki rage wllh ....wata tsokar ya kara yagowa ...asabe! Ya fada da karfi . .yau anyi rana yau naji ki shirya kamar ma banda makogwaro naji.... Oh! Ni salame.. Iya ta fada tana kallon ILU ...



Ai yi hakuri Iya karbi kason ki.. Kafafuwa ya miko mata ...taki karba tacigaba da hara rarsa ..ungo mana Iya abinda yasa na baki saboda na taba mafarki ...ance in tsaffi mata nacin kafar kaza to kafafuwansu za suyi kwari sosai ...kinsan ita kaza akwai kwarin kafa ...bare ke dazu da kina aiki kina dingisa su ji nayi kamar insa hama in bigesu kowa ya huta.....



Ai da kasa hammar ka dai daita minsu Iya ta fada tana dariya tare da amsar kafafun tasan karamin aikinsa ne ya hanasu duka.....



Ke kuma asabe ungo kai.. Ya mika mata kan kazar ...saboda na lura irin kanku daya da kaza ...kinga kin kara hankali ma ...wani dogon tsaki asabe taja wllh banci ...




Alhamdulillah ....shiyasa kike birgeni asabe biya ...komawa yayi zauna yaci gaba daci... Asukwane asabe ta warci irin bayan nan ta ruga daki ta turo kofa ....



Dariya ILU yayi haba yarinya bashi kikaci ...Iya kau da malam sai dariya suke tsokar dake hannun malam yaba Iya ta kara...



Kiran sallar ishai aka hau kira... Malam ne ya dubi ILU tashi kayi alwalla mu tafi masallaci.....








*Maman MAMY CE*

[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*






😂😂😂😂😂😂

*AZUMIN ILU*

😂😂😂😂😂😂

     

      *peg 8*

*MAMAN MAMY*.....✍





To malam ILU ya fada tare da yin wata mika ta mussamman... Iya ga kosai na nan a ajemin saura ki badashi sadaqa nasanki da tausayin Dan almajiri ....wa ni na isa in taba abinci ILU ...iya ta fada tana murmushi ....


Ahayye sama duniya tayi dadi!!! Haba ina amfanin yunwa da zan ganta ido da ido ...saina kashe ta ..koni ko ita wllh iya....


Har malam zaiyi magana sukaji ankwada sallama kofar gida... ILU fito mu tafi massalaci ..muryar basiru yaji daga kofar gida...


To basirun inna mai yan kunnuwa gani nan.... Lol! Wai ILU yaushe zaka daina radawa mutane suna ne ...iya ta fada..


Uhm kyaleshi yayi Ai ansha ruwa da dazu ne ko bakin shi bakiji sai idanu.... Aa malam wllh bani kadai nasha wahalar azumi ba ..tsaya kaji..sai kuma ya fara dariya ..ina ganin maigari dazu zai shiga gida saura kadan ya bige kai da alama bai ganin kofar gidan saboda yunwa 😆😆


Dif wutarsu ta dauke mussaman malam da dariya ke cinsa ..ILU ba karamin sha kiyi bane... Saida ya gama kwasar dariyar sa sannan yace ....shi kuma liman dazu ana sallar azahar sau biyu karanta bisimilla ...nan ma wata dariya r ya saki .....


Ita kuma iya ...wani Dan karamin icce malam ya fizgo ya kaimashi bugu ya kauce ..yayi waje yana fadin muje basiru tun kafin tsohon nan ya kaini kasa....


Aida ka tsaya Dana koya maka hankali ...Ai dama nasan da yagama shsrrance yan waje zai dawo kanmu ...yana gamawa dake zai dawo kaina tunda shi jairine ....Ai ni garama ayita AZUMIN mun samu saukin ka ....


Yar dariya iya tayi ..uhm Allah dai ya kimtsa ILU v..kullum shirmensa gaba yake yi ....


Alwalla malam yayi yabi bayansu zuwa masallaci.  .....


ILU fa ya mike duk ya ishi mutanan kauyen da tsokana ba Wanda yake ragamawa ba babba...koda aka gama sallah lulawa sukayi cikin kauyen daukar magana shida abokan sa ..bai dawo gidan ba sai wurin goma na dare ...



Sanda ta hauyi yadda kar malam yaji sadda ya dawo ....iya CE ta fito fi tsari saboda har sunyi bacci ..inwa tagani tsaye cikin razsna tasaki butar tare da fadin auzubillahi waye nan....


Da sauri ILU ya fito karta tona masa asiri ..nine iya ..kai kudai mata Allah yayi maku tsoro wllh kin kuma san ko barawo ne ko kallon arzuki baki Ashe shi ba....


Haka ya ratsata ya wuce yana mita saura inji zancen wurin malam wllh saina ballswa tunkiyarki kafa... Aa bazai ji ba ni na isa iya ta fada da karfi... Saboda tasan in ILU yace zaiyi Abu to sai ya aikata shi ....


Saida ya cinye sauran kosan da tuwo mai yawan gaske sannan ya kors da koko ya kwanta ....


Tun da suka tashi sahur asabe ke faman tada ILU amma yaki tashi saima gyara kwanciya yake ....


Malam ne yace ..kyaleshi asabe jekiyi sahur dinki.. Ai gobe ya sani yayi csahur din ma ya aka kare bare baiyi ba ...



Asabe kam komawa tayi taci gaba da sahur dinta ...iyace ta mike Umm bari inkara tada shi ni kadai nasan balain da zai mana gobe ....


Ki kyaleshi ya Dade baiyi ba laifin wa ..malam ya dakatar da ita.. Mikewa tayi aa malam nasan fitinar ILU kamar yunwar cikina bari dai in gwada .....



Iya ta tada ILU ta tadashi amma ILU yayi kunnen uwar shegu da iya haka ta hakura ta dawo taci gaba dacin abincin ta kafin lokaci ya kure .....

Haka dai suka gama suka kwanta ba tare da ILU ya tashi sahur ba..









*muje zuwa dai fans.. Kunsan akwai bidiri ILU zai tashi da dorere*😆


Post a Comment

0 Comments