Azumin ilu hausa novels 1

 AZUMIN ILU*

😂😂😂😂😂😂


     *MAMAN MAMY ce nace Ku huta*✍



*sadaukarwa gareki aminiyata Kawar Alkhairi ga nawa goron azumi tunda ban sayi sugar da gero ba*😆






A guje ya shigo gidan har yana karo da tumakan dake tsakar gidan...shigar jikin shi kawai zaka kallah kasan cewa ILU ko a kauyen su babba ne wurin shirme da shiririta.. Wani zabgegen wando ne jikin shi mai irin felar nan na mutanan da ....ga wata bajejejiyar Riga wadda ake kira da Yar shara yasha wani kafcecen glass da ido dayane kawai ke gani ........kai fans ILU fa babba ne a kauye an su ..cikin nan nasa kato dashi kamar shi kadai ake cidawa gidan ......



Haba ILU baka gani ne zaka shigo mana haka ...ko dai biyoka akayi ne.... Wata Yar tsohuwa ta fara masa fada .....kai dai ba ranar da zakayi hankali ILU...... Kinga iya niba wani dogon zance na tambaye ki ba ....wai jita jita naji agari cewar gobe ne zaa tashi da azumi acan santar na kyallu na jiyo.....


Yar dariya iya tayi ...kai ILU amma bakada dama ...yanzu murnar zuwan azumince ta da ka shigo haka.... Eh da gaske ne in Allah ya amince gobe ne zaa tashi dashi sai kazama cikin shiri .....


Wayyo Allah wayyo na shiga ukku na lalace shi kenan lokacin mutuwa ta yazo na shiga ukku ni ILU ...ya fada tare da dukewa kasa yana matso kwalla......



Kai ILU lafiyarka kuwa ....yanzu AZUMIN ne kakema wannan ihun ...oh ni salame Allah na gode maka......



Haba iya ba dole inyi kuka ba... Kina gani da safe Kofi gudu nake sha na koko inci dumamen tuwo kwano guda ....da rana ta daga zani rumfar shehu inci awara ta nera Dari... Da rana in kwashi kwano guda na abinci ...kafina mangaruba inbi na sauran yaran gidannan in cinye in malam ya dawo yaci ya rage ya bani... Da daddare bayan naci tuwo kwano agida saina fita na ni almajirai bara inkara cika cikina.... Yanzu sai ace nida abinci sai anyi sallar magrib ai lokacin na mutu kawai.....





Malam ne ya babba ke da dariya dama tun sadda ya shigo ILU ke bayani... Itama iya dariyar takeyi .....ato shiyasa Nike maka fadan cin abinci amma bakaji... Kome na noma a gidannan Kaine ke cinye shi ...nikam nayi murna da zuwan WATAN RAMDAN wata mai falala da rahama kai yanzu ILU duk bazaka tuna da niimomin da zasu sauko ba sai ta abinci kake ......malam ya fada dariya cike da cikinsa......




Cikin kuka ILU ke fadin wllh malam nayi murna da zuwan shi ...ni yauma zan fara nawa ...amma can cikin zuciyar ILU ba haka abin yake ba tunanin yunwa kawai yakeyi .....uhm kai dai kasani azumi ba fashi sai kayi talatin cif ko zaka mutu kaji dai abinda nace maka ...suma mutanen kauyen sun huta da fitinarka na Dan wani lokaci.... Malam ya fada tare da shige wa cikin dakinsa yana dariya....




Iya CE ta dubeshi.. Ni kaga da wannan kukan da tashi kayi ka amso min nikan tuwo shagon talle daya fiye maka ...insamu inmana abincin sahur.....




Jiki ba kwari ILU ya mike yayi waje yana baje fantalon wandonsa....


Duk inda yaga gungun mutane sai ya tsaya yace... Ato WATAN RAMADAN gobe sai Ku shirya don yunwa badai Kanwar Babar mutum bace bare ta raga masa




Sai mutane suyi dariya suce ..ILU da kanka kake ...mai cikin Zane sai akwashe da dariya shikau gogan ko ajikinsa .....







Maman MAMY CE nace Ku huta don Allah😂😂😂😂😆😆

[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*







😂😂😂😂😂😂

*AZUMIN ILU*

😂😂😂😂😂😂


        *peg 2*


*MAMAN MAMY CE*✍



*karfa acika ILU da dariya saboda bashi kadai bane akwai masu tsoron yunwa*😂😂😂😂😂


*gaisuwa ga yan BRRILIANT*⚜hantsi leka gidan kowa







Ahaka yaje ya dakko nikan ya dawo sai shela yake gobe azumi kamar maigari ya sashi 😂



Yana dawowa sallar magriba ya tule kasa kusa da Kanwar shi asabe .....dubanta yayi wai iya bata gama sanwar bane .....dubanshi tayi kai ILU kayi mata hakuri yanzu zata gama aci ci ...ko kallon inda take bai kara yi ba yacigaba da kallon inna na tuka tuwo .....




Loma yake kamar ya kwana bai Ciba ....in kaga tuwon da aka jibgomasa saika rantse da Allah na mutum ukku ne ........


Iyah...Allah dai yasa kin yi tuwon nan da yawa saboda sahur ...kinsan sai naci Wanda ya linka wannan saboda kar inji yunwa sosai ....kinga salon way on nawa ko asabe ya kalleta tare da afka wafceciyar loma bakinsa yana side miyar da ta biyo ta bayan hannunsa .....



Dariya asabe tayi ba wani wayo ILU ....duk wannan tumbin da kake fama dashi saiya sabe.. Ta ida maganar tana kumshe dariya ....shidai baice komai ba yaci gaba da saka lomar tuwonsa baki... Aishi komai dai dai yakeji.....






Kade kaden da yaranmu suka saba lokacin azumi domin tada sahur.... To haka abin ya kasance a kauyen Ku suma.....malam ne ya hau tashin ILU dake kwasar bacci ......




Jamaa kuzo kuga uban dumamen tuwon da ILU ya kwashe su malam kallonsa kawai suke ....asabe kam kagara tayi gari ya waye taga yadda ILU zai kasance......





Washegari yana dawowa sallar asuba ya koma ya kwanta ...cike da tunanin yau ba batun shan koko ....



Misalin 10 na rana ya tashi ...cikinsa ya fara kiran ciroma ...gashi yana tashi yaje yayi uban tulin kashi kunga kenan ba magana😆




Ragwaf ya dawo ya zauna karka shin bishiyar bedi dake tsabar gidan yana kallon yadda tinkiya ke kwasar dusa abinta..... Iya ya kalla dake shara...


Wai iya meyasa su tumakai basu yin azumi ne yanzu jibi yadda shegiya r tunkiyar nan ke cin dusa kamar da gayya takeyi saita wani kalle ni saita cika baki don inji haushi .....ya fada yana Harar tunkiyar da batasan Allah ma ya aje shi ba ....




Dariya iya tayi sosai ....ILU kenan kai dai ka tashi kayi wanka ka fita can wajen abokanka Ku cigaba da salatin annabi ...kar yunwa tasa ka mazgar min tunkiya nasan halin ka ......





Mikewa yayi tare da sakin tsaki ......yunwa nata kwalkwalar sa ....jibarta da kunnuwa fala fala... Wai da tunkiyar yake


Ita dai iya batace komai ba saboda tasan abinda ke damunsa...




Afujajan ya fito wankan ya samu wata Yar jallabiya ya sagala da wata doguwar cafzaha yayi waje .....saura kadan ya bige asabe da sauri ta matsa tana dariya .....





Santar na kyallu ya nufa inda abokansa ke zama.... Tun daga nesa suka hau yimasa dariya suna cewa....

Yayi ILU n iya mai cikin Zane yunwa dai ba Kanwar  babarsu mutum bace bare ta raga masa.....



Wani wahalal Len yake yayi ...ya nemi wuri ya zauna ya fara Jan cazbaha yana kallonsu baice masu kanzil ba .....dariya basiru yayi aaa ikon Allah mutumenfa da gaske n gaske ibada yake Ku kalla salati yakeyi ILU ILU ILU na malam .....gaba daya suka babba ke da dariya....







Kudai zauna nan ...ILU ya fada a wahalce yana zare idanu .....



Anata fira ILU kam anyi tsit sai salati akeyi... Can su kaga ILU ya hau lumshe idanuwa... Aa ILU bacci zakayi basiru ya tambaya....






Aa basiru babacci zanyi ba bari dai agama min hisabi cikin cikina da alama hanjina basu da kwari .......


Post a Comment

0 Comments