auren sirri hausa novels 2

 AUREN SIRRI

      💖💖💖

💗💗💗💗💗




Aysha A bagudo




Page 3-4


 Sai da tagama kallonta tsab Sannan ta canza Chennal hade da   tashige kitchen dan daura abinci  abincin dare 

 bakin kofar kitchen din ta dawo  Tayi tsaye abunta  tana cigaba da kallonta Chennal data canza,  ajima ajima    tana zuwa tana  duba abinda ta daura.

 Karar bell taji ba kaukautawa shiyasa  da sauri   taje ta bude gudun maseefar DEENi  dan tasan muddin yana    gida baya son yawan hayaniya , yanzu ne zai gama daita,   Maryam   tagani tsaye  da wasu en school dinsu su biyu    tuni murna yakama  zeenat ,ta rungume su  daya bayan daya tana musu sannu da zuwa  hade da basu hanya "suka shigo har cikin main parlour din  hade da  Sallamar su  .

waje ta nuna musu da hunnu kuzauna mana  suka zauna  ita kuma takoma kitchen ta duba abinda ta daura taga yayi ta kashe gas din sannan ta  dawo inda tabarsu hade da kawo musu drunks mai tsanyi da snacks ta ajiye agabasun  .

 gabadaya hayaniyya ce ta barke a  atsakaninsu da murna ganin juna ,zeenat ta kalli su Sumy hade dayin  kasa kasa da muryata tace  kuyi magana ahankali fa   sannan tace  kun kyauta sai yau kuka ga damar zuwar mana , Sumy tace ba gara mu ba muna zuwa time to time.

 kufa sai aikin sa rana   kullum,  hira suka shiga .

a inda   Maryam ta dube zeenat  tace wai nan fa IV suka kawo mana na birth din rukky, zeenat ta zaro idanu waje I ....me Maryam tace  IV .

zeenat Tayi dariya hade da cewa uhmm badani ba" kema kinsa sarai baza'a taba  barinmu zuwa wani birthday party ba " Sumy Tayi murmushi sannan tace ai sai da nagaya rukky Amman tace ga zance ga magana " gashi nan, ni ai nasan bazakuyi attending birthday party dinta ba ,da day itace sarkin shishigi da neman suna , zeenat tace kmr kinsani  ,duk abinda ya wuce cikin gidan nan namu "ta girgiza kanta baza'a taba  barinmu ba ,ki bata hakuri  kawai  Amman wlh har ga Allah naso zuwa ko dan rukky   Sumy tace to why nut ku sace hanya kuje a boye batare da kowa yasani ba ... zeenat ta  kalli Sumy fuskarta a hade tace kefa kin cika matsala fa wlh.

 kmr bada hausa nake miki  magana ba.

 ta bude bakinta kennan da niyar sake balbale summy.

 sai ga DEENi ya sake fitowa   parlour  jikinsa  sanye da jallabiya marun colour may maseefar kyau sai kyalli take zuwa ga kamshin turarensa mai mugun sanyi dadi wanda tun tasowar zeenat ta sanshi da auren Hamilton  har yanzu fuskarsa  a daure take tam ..  kmr koda yaushe "  take ta hadiye maganarta batare da tasan Tayi hakan  ba  ,ta zuba masa idanu tana  kallon kwayar idanunshi, sai data ya  hararata, sannan   ta dauke idanunta ,ta maida kallonta da hankalinta kacukam a kansu Sumy dake zaune surusuru. Yayinda    gabadaya Maryam duk ta fisu tsurewa ko dan ita Yar gidan ce oho.. 

  cikin wata irin murya mai  sanyi dadi  tamkar  ba soja ba yace ke......ta juyo ta ahankali ta sake  zuba masa  idanunta dan tasan dai daita yake dan haka tabada duk  attention dinta  garesa.

     bakisan kibawa mutun abinci bane ? Dan iskanci sai an roka ,zatayi magana ya katseta a fusace , ai ba  tun yanzu nasan ke muguwar  rowa ce dake ba Tayi surusuru  da idanu ,da   sauri tace  kayi hakuri dan Allah nayi zaton ko kana azumi ne "naga kullum kana  yi "

yace "oh "dama kinsa min ido ne har kinsa cewa azumi nake kullum ?

Jikin Maryam har rawa yake ,a hankali tace wayoo Allah ashe ya dawo ,bari in gudu tun bai gama daita ya da kanmu ba , zeenat tayi shr har sanda   ya sake maimaita tambayarsa hade da cewa dan ubanki bada ke nake ba kike bina da idanu kmr zaki cinyeni" ta sake     girgiza masa  kai,. Tana bashi hakuri

  marowaciyace banza kawai mai mugun gado.  shiru  yayi na dan wani  lokaci hade da sauke numfashi .

Sannan can kuma yace ai idan bakiyi rowa ba sai Allah ya tambayeki" km baza'asan ke...Yar uncle Habib bace .

kin taba ganin barewa Tayi gudu danta yakasa rarrafe" zeenat ta sake  girgiza kai da sauri ,yace  OK ashe dai kema kinsa gaskiya dole kiyi gadon rowa.

Ganin haka yasa su sumy suka nemi sulalewa duk yana kallonsu sai daya ga Maryam na shirin gudu  itama dan  har summy ta  daura hannuta kan handle din kofar ,ya dakatar dasu da hannusa , sannan yacigaba duban zeenat yace  barikiji da kyau  yana mai  nuna da  yatsansa" nan ba gidan marowata bane gidan masu bayarwa ne aci . yace menace ? Da sauri tace  gidan masu bayarwa ne.

 yace gud daga yau  bama ni ba ,ko wani ki kaga yazo gidan nan  ki  bashi ruwa da abinci yaci dan ba naki bane.

 ya sake jiho mata wata  tambayar yace ko abincin naki ne?, da sauri ta girgiza masa kai    dan gabadaya ta sure  ta kasa kwakwaran motsi sai ajiye zuciya kawai take yi , yace" baki da baki ne kike kadawa mutane kai , tace naji kayi hakuri dan Allah. Sannan  ya juya kan  Maryam da kadan ya rage ta fashe da kuka , ya zuba musu ritattun idanunsa da suka fi kama da mage masu saurin raunana mutun kai tsaye , yace   ku kuma en iskanci banza kun wani cikawa mutane kunne   da hayaniya tamkar kuna club  ,kallo daya yayi musu kowace tabawa kafarta iska  yaja tsaki  ya juya   ya nufi dakinsa.


 ahankali zeenat take  sauke ajiyar zuciya hade da dafe kirjinta , batasan meyasa ba ,idan har Yaya DEENI  yana guri Sam  bata samun cikakkiyar natsuwa  "sai tarinka ganin duk yacika guri ga tsananin tsoransa da take ji yana mamaye zuciyarta  . Maryam har da kuka tayi byn sun fita dan daman can ita haka take ,shegen tsoro gareta   aiko, su sumy suka ce mezasu ba dariya ba dariya suka dinga yi har da rike ciki suna nuna ta aiko tace yau sai da suyi ta zama a estate din dan bazata rakasu gun securities ba sai da sukayi ta bata hakuri sannan suka jera suna hirar abunda ya faru. 


Ko lokacin da ummi tadawo tuni murna da farinciki Ganin tilon "dan " nata  yamamayeta zuciyarta nan suka zauna a parlour suna hira cikin hirar ne ummi take masa maganar aure  in da tace masa yakamata yanemi mata yayi aure   kasan shekararka nawa kuwa  yanzu ?yayi  murmushi ai dole nasan shekaruna ,muke nan  kullum cikin rubuta date of birth ,talatin da biyu ne kawai fa ummi Tayi dariya 32 din ne kawai   kusan duk sa'annin haihuwar ka duk sunyi aure acikin estate din nan  gasu yasir nan ma duk ansa musu rana  dan haka kaima  ka fidda mata kafin azumi DEENI yazaro idannu yana bin ummi da kallo a shagwabe yace haba first love dan sunan da yake kiranta dashi kennan tun tasowarsa  .... ni din guda nawa nake da zakice inyi wani aure yanzu. Dan Allah kiyi hakuri my  first lov zuwa wani lokaci  ,duk hirar da suke zeenat  na zaune tana jinsu haka kawai taji gabanta na faduwa lokacin da taji abinda ummi tace ,Amma jin amsar da yaya DEENI yabata yasa taji  wani irin  sanyi na ratsa  zuciyarta .

  kmr ance ya dago idanunsa suka sauka cikin nata harararta yayi  yace kallon fa kin wani tsare mutun da idanu, ummi tace uhmm kafa dawo kennan karka takuramin yarinya ,

 ya langwabar da kansa  yana maida idanunsa kan ummi cikin sanyi murya yace  haba first lov baki ga irin kallon da take bin mutune dashi bane, kmr bata san mutun ba , ummi tace kai da wani idanu ka kalleta har kasan tana kallonka. kuma ma  ni  banga komai ba kai dai ta kurace kawai dakai indai kana gida  baka barin yarinya nan ta huta  ta sarara ,  ya dubi ummi ya tabe baki , Sannan yace ke....kawo min  coffee ,ta mike  taje ta hado  coffee din takawo masa gabanta na wani irin faduwa ta durkusa har kasa ta ajiye masa .


Adaidai wannan  lokacin ne zeenat  ta kammala karatunta na secondary school , ta fito da sakamakon mai kyau domin tasamu almost 7 credit masu kyau .

shi kansa DEENI yaji dadi Sosai sanda ummi ta nuna masa Amman dayake miskili ne, sai cewa yayi Sam shi bai ga wani kokari da Tayi ba tunda bata cinye duka ba .

 ummi Tayi murmushin tace kai ne dai bakaga kokarin ta ba. Amman ni nagani km  nasan Tayi kokarin Sosai .

 Ina laifi duk cikin wayanda suka rubuta jarabawa tare bbu wanda  yakaita marks ,.

yace  ok inda ta cinye duka ne zan iya cewa Tayi kokarin  ai wayanda suke cinye 9 credit ba finta brain sukayi ba.

 Ita dai  wasa da kallace kallacen banza  tasa a gaba.

 ummi ta hade fuska tana harararsa yacigaba da zagin zeenat  ganin yadda ummi Ta canza fuska ne ,yasa yabar maganar  ,  ummi ta sake  duba result din tana shafawa hade da kwallawa zeenat data tashi tun sanda taji DEENi yasoma  zaginta  kira ,takaraso  tazo ta tsaya kusa da ummi  DEENi ya dauki wayarsa yana daddannawa ba ko kalli inda take ba  ummi ta mika mata  slip din tana murmushin tace kinyi kokari sosai , zeenat ta karba ta juya ta bar gurin dan bazata iya zama a duk inda yake ba .

 ummi ta dubi DEENI tace yanzu kuma sai aure zanwa zanwa yarinyata .

 DEENI  ya juyo a sukwane  yace wani irin aure kuma first lov  da rana tsaka , kudai Bari yarinya tacigaba da karatu kawai"  dan yanzu  kai yawaye , an daina irin wannan auren,  ballanantana mata marasa illimi  "ummi ta dubesa da kyau  ta numfasa Sannan tace ni tawa iya secondary zan  aurar daita dan ma taki sauraran masu sonta . itama shegen iyayi ne daita kuma dai   kasan matan wannan family din basa wuce secondary ake musu aure .

 kuma kasan baza'a fara karatun jami'a daga kanta ba, uhm  nima nafi son na  aurar da  abita. DEENI ya tabe baki Sannan yace Allah ya kyauta  ni ko zanyi aure bazan    auren Yar secondary   ba wlh  sai wacce tagama jami'a mai tarin illimi ,kuma ba auren family zanyi ba dan baya birgeni. yakarasa maganar yana dan murmushi ,ummi tace to Allah yabaka sa'a. amman ni tawa aure zan mata da wuri .

kai kasan halin  big dady bazai taba barinka kayi aure a waje ba .

Wlh nasoma a hada aurenka dana su  yasir yace uhmmmm su dai yi nasu ni sai nan gaba .


A wata yammacin DEENI zaune akan dadduma   awajen shakatawa   shi da abokansa wayanda duk kusan  , family ne zagaye dashi gefe guda kuma flasks ne cike  da ruwan zafi da kananan cups  ,  hira suke sosai atsakaninsu Amman banda DEENI dan gabadaya daukar hirar tasu yake shirme dan duk zance nasu akan maganar aurene wanda shi kuma  Sam baya kaunar ji , dan haka ya sharesu  yacigaba da lasalasar wayarsa ya yinda ya kai  hannunsa daya  ya dauki cup din coffee wanda orready fk ya tsiyaya masa ya kai bakinsa  yasha hade da rufe rikitattun idanunshi wanda yazame masa jiki  fk ya kalli yasir da faysal dake tawowa inda suke, ya kwashe da dariya har suka karaso bai bar musu dariya ba fk yace sannuku da karasowa Mayan angwane kunsha kamshin kunsha kamshin ,faysal yace kai dai anyi dan iskan yaro ,  kai baka tsaya ruwan ido ba kana biyewa wannan ya nuna DEENI da yatsa fk yayi murmushi yace yayi   an gwanen bana wannan karon gabadaya suka dara hannu suka bawa juna suka gaigaisa  har DEENI.

 yasir ya dube fk yace ai gara muyi aurenmu tunda muna son juna kai ka zauna kar kayi har mahdi ya bayyana  ,fk yace   A'a nifa bance saboda   me zakuyi aurenku ba . Amman gaskiya zaku takura kanku ne kawai yanzu  da wani aure wayannan kananan bbys din.

   DEENI ya tabe baki Sannan ya dube fk yace shiyasa rawar kan yaran ke kara yawa ba . dukkansu suka sa dariya  suna cikin dariyar ne  fk har da rike ciki sai gasu zeenat da suka taso daga islamiyya su biyar suka jero kowace sanye da hijab dinta  raudat da  shemah  da samiha da Maryam  sai zeenat dake tsakiyar su dukkansu kyawawane .

 da hannut fk   yake nuna musu inda  suke Sannan ya dakata dariyarsa    ya kalli inda DEENi ke zaune tamkar bai san abinda ake ciki ba , ko kallon inda  suke  bai yi ba, yacigaba   daddannawa da sarrafa wayarsa .

fk yace kai gaskiya bbys din nan fa su hadu  dayawa fa , nima ko zan dan shiga daga ciki ne.

 yasir yace dako ka huta , kabar wannan ya nuna DEENi fk ya  cigaba A'a ina ai  bazan barsa ba tare zamuyi namu auren , ko yakace mutumina kaga  Shikenan mun huta da surutu jama'a   DEENi ya kallesa a kaikaice   yace A'a ku dai da kuka ji zaku iya kuje kuyi Tayi .

Amman ni ya nuna kansa da yatsansa hade da tabe baki, ba yanzu ba"    har  sanda su zeenat suka zo suka wuce . Suna hirarsu suna  dariya  Maryam ce ke basu labarin abinda ya faru jiya bbu wanda bai dara ba har ita zeenat din raudat tacewa zeenat  ai ke kika daukar masa wlh kuma yarinka yi miki kennan ina ma nice daya gane kuresan  suka sake yin dariya .


Tun lokacin daya dawo zance sa da ummi bai wuce  DEENI kayi aure  fito da mata cikin yan,uwanka kayi aure hirar kennan sai dai idan basu zauna ba  .


Yau takama walimarsu  zeenat  ta saukar alqur'ani mai girma wanda aka  shirya musu  anan islamiyyarsu dake cikin estate din ,su kusan goma   anyi taro  walima lfy  yayinda zeenat ta karbi kyaututtuka da dama saboda kokarinta har kuka ummi Tayi sakamakon tunowa datayi da er'uwarta taro ya watse lfy  kowa yakama gabansa  ,byn sun gama hirarsu da ya zame musu jiki  suka fara hada kujerun da akayi walimar dasu   .     sun fito kennan suka ga Yaya DEENI da wani abokinsa zaune   akan  kujera biyu  suna hira ,take suka ja birki samiha tacewa zeenat jeki amso wadan can kujerun, cikin zolaya tayi mata maganar dan tasan yadda take jin tsoronsa zeenat tace uhmmmm ku dai kuje "suka sa mata dariya ke wlh muguwar matsoraciyace  wlh ki rage tsoransa shiyasa yabi duk  ya renaki ,Tayi    sororo tana kallonsu , Sannan tace to bari naje amso Tayi tafiya kmr zata isa gurinsa sai kuna ta juyo da sauri" aiko suka sake  kwashe mata da dariya .

muryashi ce ta katse musu dariyar tasu lokacin daya suke kallonsa a frigice" yayinda gaban zeenat   yasoma faduwa yace ke....da hannu ya nuna musu alamun suzo 's  suka nufo  inda 

Yake cike da tsoro ya zuba musu rikitattun idanunsa  yana kallonsu daya byn daya  yana nazarinsu  Sannan yace da ganinku akwai alamun rashin gaskiya atare daku ? ya nuna su da dan yatsansa zeenat Tayi saurin cewa A'a cikin inda inda   uhm bbu komai fa Tayi gudun Kar wata cikinsu tafada masa shiyasa Tayi saurin yin magana ,to menene na inda inda wama ya tambayeki  ?Tayi shiru tamkar ruwa yacinyeta. Sannan ya juya ya kalli abokin nasa da ya zubawa zeenat   idanu yana kallonta   kafarsa  yasa ya take kafar manir  dashi ,sannan ya dawo natsuwarsa ya  mai da hankalinsa kan DEENi , DEENi ya  nuna su  zeenat da samiha hade da shemah da Maryam yace gasu nan    bansa inda sauran suka nufa ba,  manir  yace ina tayaku murna walima saukar alqur'ani mai girma, Allah yasa na tsoron Allah ne  ,suka hada baki wajen cewa Ameen , kallonsu kawai DEENi yayi jikinsu har  rawa yake suka bar wajen.

  manir yabi bayansu da kallo yace  kai sisters din nan naka  fa akwai kyau DEENi ya kallesa yana watsa masa harara ok iskancin naka kuma yau agidanmu zai Kare.

 manir yayi murmushi yace Allah barin ma wace ta tsakiyarsu gaskiya duk tafiso haduwa DEENi ya kalli inda ya nuna sai yaga zeenat yake nufi take yaja tsaki  manir yace dama ita ka zaba wlh  dan nasan karshe ma  auren zumunci za'a maka DEENi ya sake jan tsaki dan Allah malam karka dameni da wannan shirme bazan ,manir bai daddara ba ya  sake cewa Allah dama tsayawa kayi akayi Yar gida tunda duk tarin  matan dake sonka baka kallonsu , a fusace  DEENi yayi magana dan me zan kallesu alhalin  banda abinyi dasu.

 manir yayi murmushi  ina ma ni ne kai wlh tsayawa zanyi na kwashi gara son raina  har sai nagaji in more kuriciyata  , DEENi yace ai kai dan iskanci ne lamba daya , wlh  ka guji abinda kakewa ya'yan mutane "ko dan gaba .

   ka dauki neman mata tamkar wani abinci, manir ya dan  daki kafadar DEENi yace  ai sun fi abinci dadi ,.

Amman Allah koni ina son na daina bin matan bazan ,wlh  abun ne da kmr wuya Amma kacigaba da yimin addu'a . DEENi ya nuna sa  kai zanwa addu'a saboda banda abinda zan roka   Allah , manir ya dage masa gira daya yes meye dan kamin addu'a kaga idan Allah ya shiryani sai kabani wacce Yar dimadimar  sister din taka na aura , bai kulasa ba sai canza zance da yayi nan dai suka cigaba da hirarsu har zuwa sanda  sukayi  sallama da juna   .


Abinda zai daure maka kai   bai wuce yadda  ummi ke sake  bawa zeenat kulawa ta musamman ba ,ta kowani part tana iya kokarin ganin  ta fito da diyarta ta  tsab,  zeenat bata rasa komai ba tun daga  dangin sutura da  mayuka shafe masu tsada zuwa kayan kwalliya  ana cikin haka tafiya takama ummi zuwa India dan haka ta tasa diyarta gaba suka tafi   zeenat taji dadin  zuwansu India tamkar karta  dawo ,watan su daya suka tattaro suka diro Nigeria saboda bikin family dinsu yakusa koda ta dawo ma su Maryam sun dinka mata duk anco din da aka fidda tunda damar suna da telarsu ce da yake zuwa har gida ya karba dinki,.

 biki akayi sosai bakama hannu yaro an kashe kudi tamkar ba'asan  ciwonsu ba  bidia iri kuma a duk anan cikin estate din akayi komai, daga karshe akayi walima washegari ranar  Sunday aka daura auren  en mata biyar haka ma samarin aka dan kowace gidan mijinta, ya saura  mutun  uku ne cal suka rage da basu aure ba, Maryam da shemah sai zeena amaza  kuma fk da DEENi sai  kamil  .




MMN SUDAIS CE


💗💗💗💗💗

  AUREN SIRRI

      💖💖💖

💗💗💗💗💗





Aysha A bagudo




Page 5-6




Zeenat na da kyau  sai dai ba can ba" fara ce Sol Amman batada dagon hanci wannan bai sa fuskarta muni ba" haka idanunta matsakaita ne ita mutun ce mai tsananin son kwalliya wanda ko alwala Tayi sai ta sake yin  wata sabuwar kwalliya, haka  nan ummi bata gajiya da siya mata kayan kwalliya iri iri  sannan bata ganin aibunta a duk lokacin da zata bata a gurin yin kwalliyar .

abinda kawai bata so kuma bata yarda dashi ba, shine a yimata dinkin da zai bayyana surar jikinta ,nan nefa tace bazata bada goyon baya gurin  bata kamasho yada zina ba , dan a cewarta shigar da yawancin ena'mata keyi a wannan zamani itace ke sake haifar da fashadi a doron kasa.

  zeenat akwaita  da saurin sabo da mutane sannan km tana da son kawaye ita da Maryam dan ko yanzu suka san mutun   ko km kuka  hadu dasu sanadin wata kawar, Shikenan sun zama kawaye  , shiyasa suka fi dukkan sauran en'uwansu   jama'a dan daga  waje ma zuwa ake gurinsu  sabanin sauran" kullum kaga ana rikinci a bakin get da sune , gurin shigo da baki   most especially ma na school dinsu. abinda ummi tafi tsana kennan daga gareta yawan tara kawaye gata da matukar son gayu ,da son kallace kallacen film muddin tana gida kuwa bata da aikin yi sai na kallo ,daga wannan Chennal zuwa wata ,sai dai duk da wannan halin nata Allah yabata illimi sosai both arabic & school.


Daidai misali   Allah yayi mata farin jinin samari masu sonta daga waje ma biyota akeyi, sai dai bata fita dan ma ummi taki yarda tafara zance da wuri sai data kai ss2 kuma duk masu zuwa gurinta da aure suke sonta "amman matsalar dai daya ce family dinsu basa yarda da macce Tayi  auren  wajen Amman sukan bar namiji.

  kana duk masu son nata bataji son su har cikin  ranta 'har wani lokacin ummi kesata gaba da fada "tace maza ki tsaya ruwan ido daga karshe kirasa kowa kizo kina nema yawan yi mata fadan da ummi keyi ne yasa ta tsaida kamil dan gwaggonta"  yayar mahaifinta  da suke uwa guda uba guda .

  shima bakowa yasan suna tare dashi ba , dan bata gama tantancewa aurensa ba" kuma shi bai fiyye  zama a garin  ba  yana aiki ne a abuja  ". haka kawai taji idan bata samu  wanda yafi ba  , zata iya aurensa dan shima ba laifi .


Jiki da jini wata safiya  ummi ta tashi da ciwon ciki , wasa wasa  tun tana daurewa har abun yafi karfinta gabadaya tafita haiyacinta'  hankalin zeenat yayi mugun tashi dan bazata manta yawan labarin da ummi ke yawan bata na mahaifiyarta  da irin wahalar da batasha  kafin mutuwarta ,ciki har da  cewa mata Tayi ta bude ido ta zabi miji wanda zai san mutuncinta kar taje gurin ruwan idonta ta kwashi gaibu ,shiyasa take massefar jin tsoron haihuwa da mutuwa dan ta kudircewa ranta, ta amince da mutuwa tunda tasan muddin kwanakinta suka Kare Shikenan "amman ita kam bazata yarda da haihuwa ba ganinta garata tasha wahala daya .

wunin ranar da ciwo ummi ta wuni can kuma tasamu sauki    dare nayi ciwo ya sake dawo zeenat taso zuwa ta sanar da DEENi Amman ummi taki .

 washegari DEENi yashigo da shirin fita aiki  dan bai san bata da lafiya ba koda yashigo dakin yayi matukar girgiza da ganinta kwance cikin bargo da kyar take iya magana a rude yakaraso inda take  ya  tambayar ba lafiya ne ? Ummi tace eh tun jiya  yace meyasa  baki sa an tashe ni ba ,ya kalli inda zeenat ke rukube kusa da ummi duk tazama wata  kalar tausayi.

 ke....Wace irin" sakariyace da baza ki iya zuwa kisanar min ba da kyar ummi ta iya bude baki ,tace ni na hanata  ya furzar da huci ta bakinsa hade da cire hular kansa yayi wurgi dashi gefe ,take ya Ciro waya cikin aljihun bayan wandonsa yakira family doctor dinsu wanda side dinsu kawai yake dubawa.

 mintina kadan sai gashi likinta dayake bai da Nisa dasu cikin sauri yashiga duba ummi sosai har drip aka sawa ummi a ranar DEENi kasa fita yayi koina byn likinta ya wuce ne, ya kirasu ya Mahmoud ya sanar masu da ummi fa ba lfy , idanunta ta zuba mashi tana kallon bakinsa yadda yake maganar ne  tamkar wata mace shi yafi daukar hankalinta, 

ba taba jin DEENi ya birgeta  ba irin na yau.

 duk wunin  ranar  kusan shi yayiwa ummi komai  hatta magani da abinci a baki yabata sai gurin la'asar su Yaya Mahmood sukazo tare da matansu    sai zuwansu ne ma yasa mutane cikin estate din suka sani   dan DEENi bai sanar da kowa ba, shi dai ta mahaifiyarsa kawai yake.

Ai kafin kace me tuni side din ummi yacika da jama'a, haka  suka dinga shigowa duba ummi har dare DEENi na tare da ummi yana bata kulawa. duk yayi wani iri cikin lokaci kadan yafita haiyacinsa zeenat na zaune a gefe guda tana jiyo hirarsu rokonsa ummi take akan yayi aure ahankali takira sunansa NASURULDEEN ....abinda  yasake tada ma DEENi hankali kennan yaushe rabon dayaji ummi  takira complete name dinsa , tacigaba ban rasa  komai  na rayuwar duniya ba inada tarin dukiya da kadaroro  wanda ni kaina basan iyakarsu ba ,burina da muradina ahalin  yanzu bai wuce inga aurenka ba,  Amman na fuskanci kafi son sai na mutu sannan zakayi aure . Jikin DEENi ya dauki rawa hankalinsa ya sake tashi matuka ta sake kiransa cikin tattausar  muryar hade da rarrashi DEENi banida kowa daga kai sai zeenat sai kuma dan uwana wanda yake wata uwa duniya ,idan bakayi aure ka taramin jikoki masu albarka ba mezakayi min naji dadi , ina ji ajikina sai na mutu zakayi aure a rude yace first lov ki daina cewa haka  zanyi inshallahu kina raye Tayi murmushin karfin hali tace kullun haka kake cewa, ni tuni na fidda raina ka tashi katafi Allah ya maka albarka ... Amman yarinyar nan zeenat na rokeka dan Allah ko ban tashi ba kada kabari ta koma hannun mahaifinta, na damka  amanarta a hannunka ,bata da kowa duk duniyar nan daga ni sai kai ,karikemin ita a hannunka har zuwa lokacin da zata samu miji . DEENi yakamo tafin hannun ummi cikin nasa ahankali yasoma magana muryasa cike da rauni da fargaba, yace haba  first lov ki daina maganar mutuwa nan kece zaki aurar daita  da hannuki kuma kina raye inshallahu ta girgiza kai ita kadai tasan abinda take ji cikin muryarta irinta marasa lfy tace Shikenan tashi kaje ka kwanta , hankalinsa a tashe ya fice daga dakin..

 zeenat ta mike daga inda take idanunta na zubda hawaye  ta taimaka mata suka kwanta tana kuka kasa kasa ummi tace lfy zeenat  ummi . .... ummi..... cikin sheshekar kuka tace banason naji kina cewa zaki mutu kibarni dan Allah ,ummi   tace nafa da kar na fada mutuwa ta zamemin dole  sai dai idan ajalina bai zo ba . zeenat ta saki kuka hade da  kamkameta ummi a jikinta , tacigaba  da  kuka mai cin rai hade  da cewa ummi bazaki mutu ba inshallahu da kanki zaki aurar dani ni ga duk wanda kike so  da kyar bacci ya dauketa yayinda ummi Tayi nisa a bacci .


Shi kuwa DEENi tunda ya koma dakinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye  sai zariya yake daga farkon dakin zuwa karshe kafin daga baya ya nemi gurin ya zauna.

  yayi tagumi da duka hannuwansa yayi zurfi cikin tunanin yadda zai yi lallai ya zama dole ya nemo mata  domin cikawa umminsa burinta. sai dai shi matsalar sa bai san ta ina zai fara ba ? Bai taba yin buduwar ba ballanantana wata aba soyayya,  shi duk a tunaninsa raini hakan zai jawo masa idan  yaje yace yana son budurwar .

ya kamo gefen lips dinsa ya dan cizawa a hankali har daga karshe ya yanke shawara zai nemi fk da zance anan ya sulale ya kwanta rigingine idanunsa na kallon celling  dakin .

yayinda ya rungume hannushi a saman kirjinsa  yana aiyana irin type din maccen dayake son  ta mallakesa,kuma  wacce ya dace ya aura cikin sanyi ya runtse idanunsa gam  take yasoma zaiyano irin type dinsa kyakkyawa dogowa mai dirin jiki , choculate colour, mai dara daran idanu sannan educated mai wushiryar haka dai ya rinka yi har dare ya sula  bai samu wani  ishashen bacci ba. koda asuba kafin ya tafi masallaci sai  da ya fara shiga Bedroom din ummi ya sameta tana sallah ya sauke ajiyar zuciya sannan ya wuce ganinta tsaye tana sallah yasan Allah yakawo mata sauki .


A masallaci DEENi suka hadu da fk byn an idar da sallah "yajashi gefe guda da idanu fk yake binsa da kallo "abinda bai taba faruwa ba saboda DEENi  daya idar da sallah yayi yan addu'oinsa yake wuce wa  gida .

  fk ya dube sa da kyau yana nazarinsa  kafin daga baya yace lfy kuwa  naganka haka ? Gabadaya fk yagama tsurewa da ganin yanayinsa sai da ya sake maimaita tambayarsa sannan DEENi yace ina fa lfy jiya  ummi kwana Tayi  ba lfy har tana barmin wasiya burinta da muradinta yanzu bai wuce nayi aure ba.

 fk yayi shr yana jin DEENi har sanda yagama bayaninsa sannan yace baita kadai ba har big dady ma burinsa kennan  dan ko jiya sai daya min maganar nida kai  Amman tunda kai ummi ta damu  ta tsananta gara kayi  kawai kurabu lfy .

DEENi yace ai bakasan inda zan nemi matar ba nifa gabadaya en,mata family din nan basu min ba  sannan kuma sun min kankanta da aure  ,fk yace A'a bawani kankanta" mace na kankanta  da aure ne ?  kaine dai kawai  kake ganin haka ,ni   yanzu na yanke  shawarar  zan tsaida shemah kawai  tunda na dade ina sonta nida zakaji shawarata ma  da  zeenat ka aura  DEENi ya mishi wani irin kallon bakada hankali sannan yaja tsaki yace haba dai  zeenat , fk yacigaba yarinyar akwai hankali wlh ,ba kmr  wancan banzar ubannata ba, dayake duk sun tsani  halinsa.

    kaga kawai sai a hada bikinka  da nawa kawai  kaga zeenat batada matsalar, km ko bakomai ummi zata ji dadin Sosai da wannan hadin.

 DEENi yace Amma ban taba jin koda alamar digon sonta ba, kuma ni gaskiya ina ganin tamin yarinta dayawa duk fa shekarunta sha tara  zuwa sha ashirin ne  fa. nafison mutual girl wace ta mallaki hankalin kanta tasan yadda zata kula dani akan bed ,amman wannan Yar bbyn maimakon ta kula dani ,ni ne zan koma renonta.

 fk ya dubesa a kaikaice yace lallai yaran zamanin da   kasani Amman banda na yanzu, sai su maka abinda manyan matan baza su iya ba,  kana rai nata ne kawai , sai kaga mararta ta daukeka tsab, DEENi yaja tsarki kai ban son iskanci shawara nake so, ba wani shirme ka  can na bazan    ba .

fk ya kada kafada yace well tunda kaga bata maka ba kana iya duba wasu acikin gari .

DEENi ya kalleshi  yana watsamasa harara "kaifa dan iskane dan kaga nazo maka da maganata shine zaka rainawa kanka hankali " sai kuma yayi kasa kasa da murya  yace kasan Allah ni fa ko a waje ba wai ina kallon mata bane, fk yace to katsaya akan zeenat din kawai, duk inda ake neman macce mai natsuwa yarinyar nan takai ,DEENi ya sake jan tsaki yace ai inda takaicin yake kennan sai kuma nakirata ince ina sonta ...ya fada yana tabe baki "hade  jin takaici da  haushin shawarar da fk yakawo masa " fk yace inda bazaka iya ba kabi ta sama , ma'ana kasamu big dady da maganar kawai, kasanar dashi kana sonta  nasan zai ji dadi Sosai .

DEENi  ya sake watsamasa wata harara yace dan Allah malam ka dameni , ina ganin fa kmr kafara samun tabin hankali , wa yace dakai   ina sonta "zan dai yi aure badan ina so ba ,ya juya yabar fk nan  tsaye   yana binsa da kallon mamaki sannan kuma yace ai kaine babban  mahaukacin   dan iskan kawai , sai iskanci fall ciki ,shi bai ga laifinsa da yace bazata ya saukarsa a bed sai nawa sai kuma ya kwashe da dariya .


Post a Comment

0 Comments