auren sirri 7

 AUREN SIRRI

      💖💖💖

💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO



Page 25- 26


Bai ko kalli inda take ba hasali ma operating  din system dinsa yacigaba dayi.

"  tayi kusan minti goma tsugunne a gabansa batare daya dago idanunshi ya kalleta ba .


 Shr Tayi tare da" sunkuyar da kanta kasa  .

Yayinda zuciyarta ke tsananta bugawa .


 cikin daddaden muryarsa may cike da dadin   sauraro "fiyye da komai  datafi kauna  .


Yace tun yaushe kike tare da wance sakaran   Dana ganku shekaranjiya ?


 Batasan sanda ta zauna  ba ,dan tsabar frigice da  tsoron   daya shigeta na lokaci guda  .


,zuciyarta ce tasoma rawa...rawa  tare dokawa .tarasa yadda me za tace.

 cikin  ya'n sakanni nan hankalinta  yayi matukar mugun tashi. kwakwaluwarta "tashiga tariyo mata abinda ya faru  a shekaranjiya  din .


 gabadaya tagama 

 frigita  da tmbyr daya jiho mata, tunaninta  ya ta'alaka ne akan ya  manta da abinda yagani din .

dan ganin ya share  Bai  nuna koda a fuskarsa ba .

  da kyar ta iya bude bakita tare da son  nuna  masa , itama batasan inda  zancesa ya nufa ba.

 ,   muryarta cike da rudani  tace wa kenan ?


Sai Lokacin ne ya  dago rikitattun  idanunshi ya dubeta dasu .

,tare da zabgamata wata uwar  harara .

cikin  sanyayyayiyar muryarsa, ta isa ya sake yin magana  Yace wawa ..... .ni zaki waskewa ya nuna kirjinsa da yatsansa

 bakaramin laifi zaki karawa kanki   wajen nuna min bakisan abinda nake nufi  ba .


Domin bana bukatar

 rainin hankali ko  karyata min  abinda idanuna suka gane me .


Amsa  tmbyta kawai nake da bukata . 


take  muryarta tasoma  rawa alamun kuka keson kufce mata.

   ,ahankali ya daura yatsan  hannunshi akan lip's dinshi " shiiiiiiiiiii....... karki kuskura naga Tear's dinki ko rawar murya .

dan  banida  bukatar su .

I said tun yaushe kuke tare ,  that's ol .... 

  A boye ya dinga sauke ajiyar zuciya sannan ya"

 yacigaba  ko duk dadewarku bakisan tun lokacin da kuke tare ba ?


 Lokacin daya taji maganarsa na neman birkita mata Brain dinta. to up side down" wani irin rudewa  da gigicewa  ta sake  yi .  


 Ba bakinta kadai ke rawa ba ,yanzu kam har gangar jikinta rawa yake .


 Ta dawo tamkar wata zautacciya Da kyar tasamu ta iya hadeye abinda taji ya tsaya mata a makoshi .

tare da zubda hawayen  da suka  taru a idanunta, cikin rawar murya  tace shekara biyu kennan.

Tana gama fadar haka 

 ,  tayi saurin sunkuyar da kanta kasa dan gudun jin saukar mari .


yayinda hawayen tausayin kanta suka cigaba da bin kuncinta.


 a hankali ya dinga girgiza kanshi shekara biyu kennan ya sake  maimaitawa kansa.

Cikin sanyi   ya  maida jikinsa" ya kwanta rigingine  ya Kuma cigaba da operating din system dinsa batare da ya sake ce mata  komai ba .

 ,Take yaji    zuciyarsa ya dauki  beating ,wanda yarasa dalilin jin haka  .


Kusan minti shabiyar kennan idanunshi  na kan system  dinshi yana cigaba da aikinsa  .

, wanda mutun zai iya    dauka aikin ne kawai a gabansa" 

 amman a zahirin gaskiya hankalinsa ya rabu gida biyu ne . kan aikinsa da nazarinta yanayinta " maganarta ba iya kunnenshi kadai ta tsaya ba " har gangar jikinsa takaiwa farmaki . ahankali ya dinga furzar da iskar mai zafi  daga bakinsa . gashi dai  magana yake son yi amman taki fitowa sakamakon zuciyarsa dake bugawa .

    ,da kyar yasamu  iya bude bakinsa  .

  yace kina nufin shima sonki yake yi kennan  ?


 Tsoro da faduwar gaba ne suka taru suka mamaye zuciyarta.

 cikin in..inna ..tace wai wai  haka yace "amman ,  dan Allah kayi  hakuri  .

  

 da sauri DEENi dake rigingine  ya mike zaune cikin daga murya  yace mene ? Nayi hakuri ubanki "

Da sadakin nawa akanki idan da kuna kula juna ,I don't care .

Amman yanzu iskanci ne yasa  kika, cigaba sauraran wancen sakaran dan tsabar kin raina min hankali.


Bakinta na rawa  tace Ai shima yasani" shiyasa ma  yace ya hakura dani .

, ok da shi m...

  sai km yayi shr yakoma ya kwanta . hade da runtse idanunshi . Lips dinshi na kasa yakamo yana  cizawa a hankali ahankali " cikin zafin rai  da kunar zuciya   ya nuna mata kofa da yatsansa alamun ta bar masa  dakin  .


 ,kasa Mikewa tayi tsabar tsoro gabanta yacigaba da faduwa ,muryarta na rawa" ta sake yunkurin bashi hakuri  dan Allah yaya kayi hakuri wlh mun rabu dashi tun ba ya...


Wata irin  tsawa ya daka mata take maganar ta makale "tun batakai ga karasa yin ta ba   .

 wanda hakan yasa ta mike tsaye da sauri  batare da tashirya   yin hakan ba.

  jikinta yacigaba da kirma . 

   Ahankali ya bude rikitattun idanunshi "kasa kasa yake kallonta ji yake tamkar ya tashi ya shakota" tare da  yaryarfa mata maruka" ko zai dan samu ya ragewa kansa  tension din daya addabe shi tun shekaranjiya.

 amman ina baya ji zai iyayi haka.

 kodan   "

,sanin halin Umminsa.

   yasa  muddin yayi haka ranta zai baci ,hakan kadai ne yasashi kasa aiwatar da komai akanta.


 idanunshi ya watsa mata yana mai  sake  kafeta dasu wani irin kwarjini ya sake  yi mata wanda hakan shi ya kawo katsewar duk wani kuzarin dake tattare daita  . 

Muryasa a sarke yace    live dis room now  before I skater  you .Ai Bai kai ga rufe bakinshi ta kwasa  "

 da sauri   ta soma kokarin barin  dakin.

  Hade da  tabe baki a ranta  Tace matsefafe banza kawai  "anya zan iya daukar wulakancin nan  naka  kuwa ? 

ta fice tana goge gumi  duk da ba lokacin zafi bane jikinta sharkaf yake da  gumi .

Tana fita ta dinga fidda numfashi  sama sama tamkar mai cutar asma.

    sai data goge gumin  daya cigaba tsatsafo  mata  sannan ta shiga daki . 

Zaune ta samu Ummi. Tana balle magani zata sha .

Ummi tabita  da wani irin kallo tace ke km daga ina haka ?  Tace yaya DEENi ne yakirani" Ummi tace yashigo ne ta girgiza mata kai" kawai " alamun Eh " to yana ganki duk a frigice  kmr wacce tayi  gudun  tsire ,ko wani abun yayi miki.

 zeenat tayi narainarai da idanuwa  tace A'a  Ba abinda ya  min   .

  Ummi ta sake dubanta hade da  tabe baki tace ke kika sani ma idan wani abun yayi miki .


,ba kinki tsayawa waje daya ba, sai  wani rawar jiki  kike yi  akansa dan tsabar sakarci irin naki .


Zeenat  dake tsaye tana duban Ummi   taji  tamkar ta  zubda kwalla   dan jin takaicin abinda Ummi tace mata  .

  ,  Tace to ni   yanzu Ummi  wani rawar kai nayi km ? tmbyta  abu kawai  yayi fa.

 Tace to  me Yace miki ko abinci zai ci  zeenat ta sake girgizawa Ummi  kai.

 , baki da bakin ne da zaki dinga  amsa minb da ka.   cikin rawar murya zeenat tace Allah Ummi   tmbyta kawai yayi. 

tmby ce kawai zai saki kiyi hujiga hujiga haka  kmr an kwatoki a bakin kura .

 Ki sanar dani idan wani abu  yayi miki.

Tukun na ma   , how many hours  dana dawo parlour na iske baki nan . Km nasan tun lokacin Kina dakinsa dubi yadda kike fidda gumi  dan Allah .

a sanyaye zeenat din  Tace to ni Ummi me kike so nace byn  .....

 sai km  hawaye ya balle mata   shar shar.

  yasoma bin fuskarta . Tayi saurin tare da

 sanya  byn hannuta tana goge hawayen   wasu na sake silalo mata.

  Ummi ta zuba mata idanu kawai tana kallonta tare da nazarinta tabbas tasan duk yadda akayi akwai abinda deeni ,yayi mata .

Amman dan sakarci da kafiya irin tata  gashi tski fadar gaskiya.

 sai da ummi ta numfasa sannan  ,tace meyye km na kuka ke da kika ce ba abinda aka miki  .

 ,bakiyi kuka a can inda aka ritsa ki ba sai a nan ,dan kin rai nani ko..


 kasa cewa komai zeenat din  tayi illa sanya    kai datayi cikin  bathroom, tashige abunta  tana  kuka kasa kasa , abubuwan sun taru sun cakude   mata .

 goma da ashirin ga rashin samun kulawar  DEENi gareta .

ga damuwar Ummi akan ta nacewa DEENI .


 cikin dare ma  sam kasa bacci tayi   .

Sai  faman  juyi kawai take akan gado  tare da tunanin iri iri ta jima kwance batare da bacci yayi nasarar dauketa ba  .

Wani   tunanin ne yazo  gara ta tashi  takai kukanta gurin mai duka.

 dan haka ta mike cikin sanyi jiki " taje tayo alwala .



 sallah nafila ta   dingayi ba kaukautawa  tare da neman zabbi Allah akan aureta da DEENi.


 dan ita kanta  tasan zuwa yanzu  tabbas tayi kuskuren  saurin amincewa da aurensa datayi .


Domin shine musababbabin abinda   yasa  wulakancinsa ya sake nunkuwa  gareta.  wanda   ita kanta tasan  hukuncita abinda yafi dacewa daita  kennan .

 na saurin  amincewa datayi da  auren DEENi  cikin gaggawa  batare da ta neman zabin Allah ba . 


hankalinta kan tashi.

 a duk sanda ta tuna da maganganu ummi. A  Ranta tace  anya kuwa bazan hakura da auren  nan na DEENi  na hutawa rayuwata ba .

 wai ace mijin da zaka aura  ne" ya zame maka  tamkar wani ma'alaikan daukar rai ko wani dodo . 

Kuka take sosai tana  , addu'a   neman Zabin   Allah a  game da auranta dashi .



 darajar nafilar data kwana tana yi ne  .

yasa washegari ta tashi  sakayau  daita cikin nishadi  da farinciki "

 ba  kmr ko wace  safiya  ba .

duk da bata da wani kuzari da walwala.  Amman hakan bai hana  jin dadi ba.


 kitchen ta nufa kai tsaye  dan   hada masa breakfast kasancewa weekend ce .



 " byn  wasu yan mintina ta kamla da komai na break tashirya dining . Cikin haka ummi ta iso parlour ta zauna kan dinning table   tana yi mata sannu , murmushi tayi  tare da  koma kusa   ummi  ta zauna" ta sheida mata ta gama komai .

 tana jinsa yashigo  yana  gaida ummi fuskasa a daure   kmr kullum.

Sanye yake  cikin dark blue t shirt da wando jeans . ummi ta amsa  masa cike da fara'a ka tashi lfy ya dan saki fuska kadan Yace lfy lau na tashi  first lov kujera ya zauna . a tsorace itama zeenat din  ta gaishe shi ,ya amsa mata a ciki batare daya kalli inda take ba.


 ,ummi Tace ya..ya .ayi serve  din ka ne ? Ya hade rai yaki yin magana .

da kai fa nake a zubo maka abinci  ne ta sake maimaita wa ?

  Ya dan dubi ummi a shagwabe Yace bana ci.


 ummi ta Gane tmbyrta  da tayi masa ce  ta hassala shi .

dan haka sake bi takansa ba  da kanta ,ta zuba mishi komai da'aka girka ta turo plate din gabansa ,tare da  dungure masa kai " gashi nan miskilili sarkin zuciya Yace  to ni ta yaya za'a  tmbye ni ko zanci abinci  " byn ansa zanci din " 

ummi tayi murmushinsu irin na manya Tace uhmmmm DEENi kennan halinka sai kai "Allah ya canza maka wannan budadden halin naka " Ameen yace tare da kai spoon bakinsa .


 parlour ya dauki  shr  baka jin motsin komai   baya ga karar spoon din zeenat .

 juyawa spoon din kawai take  takasa  kai ko loma daya bakinta sakamakon cika wajen da DEENi yayi"  duk  da tasan hankalinsa da idanunshi ba'akanta  suke ba .

  tayi shr ta fada cikin  duniyar tunanin abinda ya shafeta km  yafi damunta.

Wanda  a halin yanzun Bai wuce aurenta da DEENi ba .

domin kuwa   tana matukar jin tsoron zama dashi ba dan komai ba sai dan tsoron azabar da zai dinga gana mata a gidansa.

 hankalinta kan tashi a duk sanda ta tuna da hakan.

 Ahankali   Ummi ta ajiye  spoon din hannuta tare da zuba mata ido kawai  tana  binta da  kallo tarasa meke damun Brain dinta  a cikin kwanakin  nan .

 kusan  minti goma ta dauka tana kallonta batare da ita zeenat din tasani ba .


Zeenat .....ummi takira sunanta a frigice ta juyo tana kallon ummi  ,ci abinci abinda ummi ta iya cewa kennan .

 DEENi dake zaune haushi kmr ya kashe shi tsaki ya dan ja ,ummi ta juyo bangaren sa Tace lfy kai km ?  

Fuskarsa a dakune Yace babu   ,   Sai da taga  Ummi ta sake     dubeta   sannan tasoma cin abincin , shima bawani sosai .





Byn sati biyu 


Shirye shiryen bikinsu zeenat  aka soma  sosai ba kama hannu yaro.


 ,anshirya komai na  al'adar  hausa kmr   sabbabin dinkuna da gyaran jiki   komai  km tare akeyi musu ita   da shemah km iri daya.

   musamman ummi ta dauko kwararriyar  mai gyaran jikin  daga india domin ta gyara mata tilor diyarta da kyau.

 duk wani gata  da uwa zata yiwa diyarta "ummi tayiwa zeenat shi .

 shima mahaifin zeenat din yayi iya bakin kokarin Sosai .


a nyi kamu amare  idan aka feshe su da turare masu dadin kamshi na  mutune India wanda duk wacce  ummi ta dauko ta gyara zeenat din ce tazo dashi. 

Anyi musu murzar  lalle da kitso .

amman ansha fama da zeenat gurinyin kitso dan cewa tayi ita sam na attachment ,zatayi .

sai da ummi ta bude mata wuta sosai tare da cewa ,zata sanarwa DEENi tukun ta natsu .


Sau ran kwana biyu daurin aure mutane India suka iso , kusan mutum ashirin maza da mata sosai aka shiga hidimar da ,baki.ummi  taji dadi Sosai dan kusan duk  shakikanta ne suka zo wanda km shine zuwansu na farko Nigeria idan .


 ,gabadaya gidan nasu  cike yake  da baki dan haka ba kasafai  zeenat din take  zama a part dinsu ba ,tana can  gidansu shemah   .

 

 Zeenat Tace dan Maryam muje kirani part dinmu ina son naga ummi yau duk banganta ba  .

 , Maryam Tace gaskiya na gaji da yawa wlh kije kawai . zeenat ta ja saki Tace dan Allah muje kiraki ni  yanzu zamudawo.

 shemah dake kwance ta mike zaune tace muje na rakaki kinsa halin  Maryam da maseefar  son jikin tsiya.

 , Mikewa sukayi har sun fito sai ga  Maryam  Tace wlh baza kubarni ni kadai ba , zeenat tace ke km kika sani " idan zaki muje .

Tare ,  suka nufo part dinsu zeenat.

 tafe suke suna hira irin tasu ta amare  daga nisa zeenat ta hango motar DEENI parke  a kofar part dinsu "daga gefe .

" can baya km motar fk ce sai wata motar daban wanda batasan ko ta waye ba . 


Jingine  yake jikin motar shi yana amsa waya sanye cikin English wear's   black jeans da rigar ashi colour "mai gajeren hannu wanda ta fidda ainihin kyaunsa   da gargasan gashin jikinsa dake kwance kan Gabar  hannushi .

 idanunta fes akanshi  tana binshi da wani irin kallo saboda yadda taga yakara yi mata kyau. fuskasa har wani shekin annuri  take fitarwa kmr ance ya dago idanunshi  suka hada idanu.

 da sauri ta dauke idanunta wani abu ta dinga ji yana tsirga mata  ajikita. sai taga ya fita daban cikinsu fk duk da bawani kallonsa tayi sosai ba .

ta sake dago idanunta  da niyar sata kallonsa suka sake hada ido  harara ya sakar mata  ,  kallo daya ya sake yi mata ya kau da fuskarsa gefe yacigaba da wayarsa   a kallo dayan da Yayi mata yane yadda jikinta ya tsanyi .


 kai tsaye zeenat taja hannun Maryam wacce tafi kusa daita ta juya da sauri  ta karya cona itama shemah ganin haka yasa tabiyo bayansu da sauri tana jin fk na kiranta . shemah Tace  yazaki biyo damu tana km.

 zeenat Tace bbu komai mu bi nan di yafi sauki .



 ta bayan part dinmsu suka shiga , da ummi tasoma cin karo ta rungume tana sakin ajiyar ,ummi tace meyye haka ?muryata kmr mai shirin yin kuka take  Haba ummi  yau fa duk banganki ba ,baki ga har wata  rama nayi ba  " tayi murmushi tace lallai kam kin rame dan ga natsuwa nan suna bikin dariya mutane dake tare da ummi suka shiga yi .

Ummi tayi gaba zeenat nabiye daita tana  zuba mata shagwaba.

 shape shape tayi abinda zatayi  suka bar gidan . 



Ranar daurin auren da safe  ta nufo gidansu dan dauka kayanta dazata saka .

wanda ta manta bata hadu dashi ba cikin kaya .

,tafe take tana sauri . yayinda su ya faruk da abonkan DEENi  ke tsaye duk cikin  shirinsu na zuwa daurin aure .

amman banda  DEENi wanda dagani  shi suke Jira . 

Wani irin kunya ce taji takamata dan haka ta dan janyo gefen mayafinta ta rufe fuskarta ,tana jin yaya faruk nacewa amaryamu ki bude idanunta kada ki fadi mana .

amman ina ko waiwayo batayi ba tacigaba da tafiyarta ta kofar baya tabi yauma.

 tashigo dogon parlour'nsu ta baya kennan tasoma jiyo kamshin turarensa kafin tayi kokarin bude fuskarta  taji sunyi karo da mutun .

da sauri takarasa bude fuskarta  "yaya DEENi ne wanda zai fito har wayar dake hannushi ta fadi .

,gabanta ne  yayi wani irin faduwa dan har wani juya juya ta dinga ji   da sauri ta tsugunna dan miko masa shima ya tsugunna da zai dauka a tare hannunsu yakai kan wayar  ,wani irin shock ne  yajata " wanda  baita kadai ba har shi   DEENi yaji abinda taji.


 Wani iri shima yaji ajikinsa  tamkar an jona masa  lantarkin .

 . Shine yasoma kokarin janye hannushi daga kan nata ,ahankali ta  Miko masa wayar batare da ta mike ba  hade da cewa kayi hakuri  dan Allah .


komai Bai iya cewa ba baya ga amsar wayar  da Yayi ya barta nan  tsugunne.


Bayansa tabi da kallo yayi matukar yi mata kyau har batasan yadda zata misalta ba sanye yake  cikin shadda fara kal sai  kamshin yake zubawa .

  gabadaya kamshin turarensa  ya gyaraye dogon parlour'n .

Ahankali zuciyarta tasoma bugawa tamkar zata basa kirjinta ..

girgiza kai kawai tayi dan  batasan wani irin aure take shirin yi ba haka ta juya cikin sanyi jiki tabar gurin tana shiga ciki.m mutane  akama kiranta da  amarya amarya kinsha kamshi ita dai bata iya cewa komai ba dan gabadaya jikinta a sanyaye yake .



  




MMN SUDAIS CE

💗💗💗💗💗

  AUREN SIRRI

      💖💖💖

💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO




Page  27-28


Part din cike yake da  abonkan arzikin  da  en'uwa ,Ummi 

 Jikinta a sanyaye ta dinga ratsa mutane dake ,zaune a parlour ' har ta iso dakin ummi , da  idanun  take bin en  dakin da kallo .

kozata  ga  ummi  ganin bata  alamunta bane , yasa  tmbye  matar uncle din Inda ummi take.

 tace yanzu tashiga bathroom  .  

Ahankali ta fidda  numfashi tare sauke ajiyar zuciya   .

  cikin haka ummi ta fito tana ganin zeenat  din.

 ta bata  fuskarta "ta zauna tana dubanta"


 gefen ummi zeenat tasamu ta zauna fuskarta dauke da murmushi wanda da Gani na karfin hali ne .


 Cikin kasa da murya ummi tace yana ganki haka  ina kayanki ? 


Cikin sanyi jiki zeenat tace  shi nazo dauka .


,ummi tace ke dai kin cika   shiririta wlh "

   komai baza kiyi shi cikin sauri da kazar kazar ba kin dinga jan jiki kennan ,kmr wata mage .


Alhalin  kin   san halin wanda zaki aura " dan oya oya ne  . 


jin haka yasa jikin  zeenat din sake  yin  sanye, tare jin wata irin  faduwar gaba  " zuciyar ta dinga dokawa da sauri tamkar baso kirjinta.

  ahankali tasa hannuta ta kamo na   ummi 

 cikin nata jikinta har rawa yake  hade da rage    murya  tamkar mai shirin zubda kwalla  tace dan Allah ummi   kiyi hakuri kinji karkiyi fushi dani  ,zan canza inshallahu Amman  " kimin addu'a .

 wlh tun sanda aka samo shirin bikin nan nake  jin faduwar gaba wanda narasa dalili . 

ummi ta tayi shr tare da  zuba mata idanu kawai tana kallonta  .

 tausayinta  ne ya sake kamata  , ,duk sai   taga takara ramewa ba kmr kwanaki ba hakan yasa taji ba dadi aranta.

, ahankali ummi ta mike tare da riko hannuta tayi cikin  , bedroom  daita. En dakin suka bisu da kallon sha'awa duk da basu ji maganarsu ba Amman sun birgesu .


 ,Har suka shigo bedroom din Ummi na rike da hannuta Ta  zauna daita tana rarrashita kan ta kwantar da hankalinta fargaban aurene kawai ke sata jin faduwar gaba Amman   bbu abinda zai faru inshallahu "

 Ummi da kanta ta shirya diyatata   cikin wata arniyarta geziner  ligth blue sai daukar ido take da kamshi  tare da  fesheta  da turaruka kala kala masu sanyi kamshin take zeenat   ta fito  amarya sak  .tayi kyau sosai 

Ummi   ,ta dauki waya tayi mata hotuna sannan  takira Maryam tace tazo ta tafi daita din .  




Kwanciyar tayi flat  a kan gadon su shemah  tana kallo da sauraran  duk abinda ke faruwa  .

a cikin dakin dake cike da en mata da kawaye 


 abinka  ga  mai yawan  kawaye "  da  mutane kala  daban daban " yasa dayawa wayan dake cikin dakin kawayen zeenat din ne    .

gyara kwanciyarta tayi idanunta na kallon celling dakin hannuwanta duk rungume da kirjinta yayainda zuciyarta ke cigaba tsalle tamkar zata fasa kirjinta ta fito waje.


 ahankali ta runtse idanunta sanyi taji yana ratsa koina a jikinta  duk da tarin fargaban dake tattare daita hakan bai hanata jin jikinta yayi mata nauyi ba .

Tana ji ajikinta  burinta da dokin  son auren DEENi .

   duk   babu shi ahalin yanzu sakamakon fargaba da tsoron kasancewa tare dashi a muhalli daya .

 Ta dauki lokacin mai tsawo kwance yayinda ta dinga jin wani iri ajikinta .

Bugun zuciyata na sake karuwa.

 ta dinga kokarin ganinta ta cire damuwar dake damunta wanda a zahirance ita ta daurawa kanta  .

  har yanzu da take kwance  jikinta a sanyaye yake takasa tabuka komai.

 idanunta ta  runtse tana cigaba da sauraron hirar dasuke sama sama .     




10:30



Karfe goma da rabi daidai  na ranar lahadi  Allah ya cika alkawarinsa   domin    dimbin, jama'a sun shaida daurin auren NASURULDEENI ALIYU BELLO da MUZEENAT HABIB BELLO" daurin auren daya tara manya  attajirai da kusoshin gwanati hade da maikata 

 bakaramin farinciki  family din muhd bello  suka yi ba  ganin sun kara karfafa  zumunci a atsakaninsu, .

 dan haka farincikisu  ya sake karuwa takoina ka juya , family din murna ne cunkushe  a fuskokinsu 




Zeenat dake kwance har lokacin tana saka da warwara still jikinta a sanyaye yake takasa kwakwaran motse  .

 zuciyarta fall  da fargaba musamman lokacin da taji  hayaniyar mutane  ta cika gidan  alamun an daura aure, en'uwa nata  shigowa ana gaisawa , ajiyar zuciya dumin  hawaye taji yana bin kuncinta shikennan ta faru takare  tana matukar son  deeni Amman  tana jin tsoron zama dashi  hayaniyar mutane  take sake jiyowa hakan yasa  jikinta ya dauki kirma,kirrrrrr... sam ko kadan bbu wanda ya lura da yanayinta.

 Sai ma tashi sukayi suka fita waje km  har sanda suka fito tsakar gidan suna ta daukar  hotuna bbu wanda ya lura da yanayin da suka barta  .

"  Maryam ce data  karaso wajensu taga suna ta hotuna  bbu ita yasa tashiga dakin dan dubota dan kusan tana lura daita tun jiya tamkar mara lfy .


 kwance ta tadda ita tana  fidda numfashi sama sama .

 Da sauri ta karasa inda take  bbu abinda jikinta keyi sai fidda hucin zafi,  a rude ta dinga takiran sunanta zeenat ... zeenat  daman bakida lfy ne? 


Kai kawai ta iya girgiza  mata  alamun eh da sauri Maryam ta mike  ta nufi part din ummi tasanar mata  .

tare suka dawo gurinta da wasu en'uwa ummi guda biyu .

 zuwa yanzu jikinta ya tsananta zafi  tare da karkarwa   .

 ban da  salati bbu abinda ummi keyi  da sauri takarasa kusa da zeenat din ta zauna tare da riko hannuta" may zan Gani  , haka ni   fadeela ? 

, zeenat kina son ki kashe min kanki ne ?

Ko yaya ,

Alhalin kinsa ke kadai gareni  duk duniyan nan  km ke kadai debimin kewar er'uwarta dana rasa , bazan iya jurar rashinki ba dan Allah ki tausayi min  mamana.

 sai km  hawaye  shar shar daga idanun ummi  sosai Ummi ke zubda kwallar tausayi diyarta  ganin yadda  ta fita haiyacinta cikin lokaci daya   .

Ummi tace zahra kamama min ita dan Allah .

  su  aunty suka mata zeenat    sukayi  part din  Ummi daita .



  kai tsaye dakin DEENi  ummi tabada umarnin  a wuce daita.batare da bata lokaci ba ummi 

 takira family doctor dinsu .

 sannan takira DEENi tace yasameta a dakinshi yanzu yanzu  .



Doctor     bai dauki wani lokacin ba" sai gashi yana zuwa yasoma duddubata tare  dabata taimakon gaggawa  .


 ummi  ta dubi doctor  hankalinta a tashe tace  doctor meke damunta ?


doctor yace bawani abu bane   damuwace kawai tayi mata yawa  "amman inshallahu  zata. dawo daidai .


A gaugauce DEENi yashigo byn amsa kiran Ummi .

yana shigowa dakin  mutane  suka dan ragu  .


ahankali yakaraso kusa da Ummi ya tsaya yana tmbyrta abinda ke faru  sai data ja numfashi sannan ta nuna masa inda zeenat din  ke kwance tace zeenat ce ba lfy sai lokacin idanunshi suka kai gareta kwance take akan bed dinshi an lullubeta da bangon rufarsa.

 shr yayi tare da zuba mata rikitattun idanunshi. 


Daddaden kamshin turarensa tasoma juyowa may matukar sanyi ahankali ta dan lumshe idanunta .


Taku daya zuwa  biyu yayi yaja ya sake  ya  tsaya" sannan ya dubi inda ummi  ke tsaye  yace me doctor din yace yana damunta?

 , doctor din still ya sake mashi bayani kmr dai yadda yayiwa ummi  . ahankali ya sake mai idanushin kanta yana cigaba da kallonta wannan shine karo na farko daya tsaya ya Kare mata ,

  ,   sosai kamshin turarensa  ke sake kaiwa hancinta farmaki tare da susuta mata duk wata gaba dake  jikinta .

.

 jikinta da zuciyata suka dauki  rawa wani zazzabi  mai zafi yayi nasarar sake rufeta sakamakon idanushi dake yawo a gangar jikinta . 


Da sauri doctor ya  nufo inda take" deeni yasa hannu ya dakatar dashi   alamun kada yakarasa gareta" dan wani abu  yaji yana taso masa  sanda doctor ke masa bayanin abinda ke damunta , tamkar ya auna doctor waje  dan takaicin abinda ke cin zuciyarsa. 

ganin haka yasa  doctor  din yace a samo ruwa da towel a goge mata jiki dashi  dan tazo daya dubata yaji yadda jikinta ya dau zafi  yace zai je   ya dauko magani ya dawo  cikin sauri ya fice dakin  . 


  A ranta tace doctor dama kayi zamanka   dan   maganinka  kadai  ba  zai taba min  maganin damuwarta ba .


 dan ita kadai tasan abinda ke cin ranta .

Wanda   tun daga cikin zuciyarta take jin yake taso mata .

tare da haddasa mata  tsoro da faduwar gaba.



 Tsaye yake har yanzu sai  suke  hanuwanshi duka da Yayi  cikin aljihun wandonsa.


 ahankali yasoma takowa  zuwa bakin gadon km idanushi akanta.

cikin sanyi ya yaye bargon da aka lullube mata  jiki dashi. idanunshi fes akan fuskarta dake lumshe tayi fayu sannan km takara rame sosai  ahankali  ya daura  hannushi saman goshinta .

 jin yadda  goshinta  ya dau zafi da yadda take  fidda numfashi sama sama  yasanyashi kai  hannushi  da sauri jikinta.

 take yaji abinda ya sake frigitashi .

zafin dake jikinta ya ratsa tafin hannushi" wanda bai san sanda tausayinta ya lullubet shi  ba  ya dinga jin wani abu na tsigar wa ajikinsa ,  ya juyo tsaitin  Maryam yana harararta yace tsayuwar me kike anan da sauri ta fice daga dakin bata fi minti uku ba Sai gata ta dawo  da  ruwan ahanunta jikinta na rawa.

 azaton zeenat ummi ce ko auntyta  zasu goge mata jiki ,amman sai taga DEENi yakarbi robar ruwan a hannu maryam  .

Gabadaya suka fita daga dakin har ummi "tare da kulle masu dakin .


Cikin sanyi jiki ya tashi ya dawo gabanta har yanzu sanye yake cikin  shadda fara  tas sai kamshin turarensa ke  tashi a dakin .


ahankali ya cire farar hular shi ya ajiye gefe sannan yasa  hannushi duka  ya tattarota jikinsa yaja zip din rigar kasa ya zare rigar jikinta ya ajiye gefe ,take jikinta ya sake daukar kirma   gabanta  yacigaba da faduwa .

tsoro da mamaki suka taru  cika zuciyarta. aranta tace wayyo nashiga uku  me  yaya ke nufi  da cire min riga ? yana nufin shi ,zai goge min jiki  .

tana ji tana Gani ya cire mata kayan jikinta tsab   har bra dinta .

ta rage daga ita sai zani iya cibiya ,sannan ya zauna tare  daurata a saman  cinyarsa"  ya juyo daita suna facing juna  taso tasa hannu ta Kare kirjinta amman kasancewar  jikinta bbu kwari yasa takasa aiwatar da komai "dan haka  ta runtse idanunta gam.

 tana jiran taji    ruwa ajikinta Amman sai taji shr ahankali ta dan  bude idanunta ,DEENi zaune  idanunshi kyam akan kirjinta .

 da sauri ta maida idanunta ta rufe dan frigice da tsoro    ya dauko towel din ya matse sannan   yasoma goge  mata saman  jikinta   zuwa kirjinta da fuskarta , ya dimauce da ganin halitatta kirjinta    ,hakan  yasa yafi goge mata gurin a tare suka dinga sauke ajiyar zuciya .


 can yaji ana nouking din dakin  yayi sauri ya mayar mata da rigarta sannan yabada izinin  shigowa.

 doctor ne yashigo da ledar  magunguna ahannushi Yace abata abinci taci  tukun sannan tasha maganin.

 byn tafiyar doctor DEENI  yakira ummi Yace akawo  tea, en'uwa    dayawa suka shigo dakin "ummi da matar uncle din zeenat  ,Maryam har ma da shemah  . suka dinga jero mata sannu.


byn  sun  fita ne   taji tamkar kar su fita dan  bata son abarta daga ita Sai shi.

 hakan na sake frigita zuciyarta   . 

kadan tasha tea din tace takoshi bai wani takurata ba  ,ya ballo  magani ya Mike mata  ba musu tasa hannu ta karba tasha ,dan tasan halinsa  ciwonta bazai hana ya jibgeta ba .

Shiya  gabadaya a tsorace take dashi.



MMN SUDAIS

💗💗💗💗💗

  AUREN SIRRI

     ðŸ’–💖💖

💗💗💗💗💗





AYSHA A BAGUDO




Page 29-30



 Byn tasha magani . komawa tayi ta  kwanta  lomo ajikinsa' tana sakin numfashi sama sama wani iri taji ajikinta lokacin data tsinci kanta kwance kan tattausan jikinsa .

ga kamshin turaren jikinsa gyaraye dana dakin sun buwayi hancinta .

ji take tamkar sukasance haka har abada.

 ,  ahankali tasoma lumshe idanunta  har ta rufe su rufff..

   bacci ne may nauyi  Yayi nasarar daukarta  acikin mintina da basu wuce  goma ba .



Kyawawan idanushi masu matukar haske da daukar hankali ya zuba mata.

 Tare da  Kare mata kallo wani zirrrrrrrr   ya dinga ji ajikinsa" lokacin daya jita lefe a saman  kirjinsa   . 

da kyar yake jawo numfashin yana fesarwa.

hannushi ya sake kaiwa wuyanta har lokacin jikinta da sauran hucin zafi.

 janyota jikinsa ya sake yi .

Tare da  ,yasanya hannuwansa duka ya rungume tsam tsam   ajikinsa "yana fidda numfashi .

tare da  fatan samun saukin zugin da zuciyarsa ke masa wanda shi kansa yarasa dalilin haka.

   " Har lokacin bacci take  rungume ajikinsa suna musayar numfashin juna  mutuwar da jikinsa yayi ne  yasashi  sake zuba mata  rikitattun idanunshi tsawon lokaci yana kallonta 

  Da kyar yasamu yayo control din kansa cikin sanyi jiki  ya  zareta daga jikinsa ya kwantar daita ya sake lullube ta da blanket ,sannan ya Mike tsaye  yana karkabe  jikinsa.


 ,rigar jikinsa yasoma  cirewa  ya saura daga shi Sai  farar single da wanda shadda.


 Wordrob dinsa ya bude ya dauke  wasu kayan da zai canza  "  tare da yashigewa  bathroom .


 

Dakin ya sake dawo byn yagama shirya kansa  , cikin farin  yadin voyal  may matukar taushi da daukar hankali.

Agabanta ya tsaya  yana makale links din gaban  rigarsa  yayinda  idanushi ke kanta yana    cigaba da kallon fuskarta.


  Ahankali ya dinga jin reaction din jikinsa na sauyawa  ,yayinda zuciyarsa ke beating tana tsalle tamkar zata bafa masa kirji . wanda shi kansa yarasa dalilin dayasa shi  jin haka.

Ahankali ya dauke idanushi a kanta sakamakon 

 , ji yayi "ana nouking din dakin "yabada umarnin ashigo batare daya tmbyi kowaye ba . 

 Maryam ce tashigo da sallmarta .

 ta gaidashi ya amsa mata a dake .

 Cikin sanyi nan nasa 

Yakarasa gaban mirrow      ya dauki agogon  ya daura a tsintsiyar hannushi  tare daukar kwalbar turaren ya feshe ilahirin jikinsa ta cikin mirrow din  yake wa Maryam magana cikin dakakiyyar  "  muryasa ki kula daita idan ta farka .idan  kika ji zazzabi bai sauka ba ki sanar da first lov ,a tsorace tace ta amsa masa da to...

yana fita  ta bi bayansa da kallo cikin ranta tace wayyo zeenat na tausaya miki auren wannan maseefaffe .

 ,Sai kinyi   hakuri da wannan budadden  halin na shi .

 gefen gadon takoma ta zauna tana sake jin tausayin zeenat din a ranta .


Sosai zeenat tayi bacci baita ta tashi ba.

 Sai gaf da magariba.

 ji da Maryam tayi jikin zeenat din  bbu zafi ko daya .

yasa  ta sanarwa da  aunty zahra    .

 Su Aunty zahra   suka sata tayi  wanka da sallah .

 tana zaune akan prayer mat "duk jikinta a mace  taji sunce tunda jinkinta da sauki tashiyar  akaita tayi sallama da Ummi.


   fuskarta cike da tsoro  ta dubi aunty zahra tace dan Allah aunty  karku kai ni wani guri wlh bani da lfy  ..

 aunty zahra tace  A'a kiyi hakuri yanzu  za'a kai ki gidanki kya ji sauki a can.

 tana kuka tana komai aka shiryata cikin wata geziner mai ruwan kasa ,Sai kamshi ke tashi ajikinta kai tsaye  gurin ummi aka kaita ta mata nasiha mai ratsa jiki ,sannan takara da ce mata takasance may tsananin  tsafta da girki domin sune  manyan makamai dake  kara karfin aure .


Sai km hakuri ,kiyi hakuri  kiyi hakuri mamana da duk abinda zaki  Gani.gidan aure bbu komai acikknsa Sai   hakuri .

Km hakuri  shine jigon zaman  aure .

duk wata mata da kika ganta zaune gidan mijinta ,hakuri take yi 

  dan  haka ki kula da  kyau kinji mamana .

Zuciyar ummi ta tsinke tayi rauni  Sai km hawaye shar shar......suka soma zuba , en'uwa ummi da suka zo daga india sukai taba hakuri  suma sunyi mata tasu nasiha Sosai .


,  ita dai zeenat bbu abinda ummi ta fada wanda bai shiga kunneta ba .

tare  da kukan tausayin kanta .

duk sanda ta tuna yau  , za'a kaita gidan deeni hankalinta  ne  ke sake tashi .kuka sosai take har da majina .

  ganin irin kukan da zeenat din  ke yi yasa ummi kiran deeni a waya . 


Byn yan wasu yan mintina Sai gashi yashigo da sallama ,mutane dake zaune a dakin .

suka fita gabadayansu dan basu waje . 

Ahankali yakaraso cikin dakin sosai, ya  durkusawa gaban ummi yayi zaman dirshan har da tankwashe kafafunsa. ganin haka yasa itama  zeenat tazamo " tayi irin zaman da yayi  a gaban ummi" Sai dai ita zuciyarta da gangar jikinta  cike suke  da rauni.

 badan namijin kokarin datakeyi ba da tune zuciyarta ta buga tsabar frigici.

Ummi tayi shr  tare da zuba musu idanunta da suka gama canza kala saboda kukan datayi.

Tsawon lokaci tana zaune ta tasa su gaba tana kallonsu kafin daga baya tasoma magana 

 cikin sanyi muryata ta Kira " sunansa NASURUDEEN......  ahankali ya dago  idanunshi yana duban umminsa dasu  batare daya amsa ba .

Sai dai yadda takira sunanshi din ya girgiza zuciyarsa domin ya manta when last da yaji takira complete name dinshi haka   .

Dan haka ya tattara dukkan hankalinsa da natsuwarsa gareta .

Cikin sanyi murya data sha kuka tace DEENi ga zeenat nan ta sake dawo gareka" a karo na biyu . Sai dai wannan karon yasha bamban da sauran  lokuta .

'wanna karon ta dawo gareka ne da matsayi guda biyu ,kawarka km matarka .

zan ji matukar farinciki da kwanciyar hankali  idan kuka hada kanku ,kuka zauna lfy.

 , zeenat yarinya karama kayi hakuri daita"  duk wani  abinda ta maka  wanda bai yi maka ba , ka sanar min .

Ni Zan fahimtar daita ta hanyar da zata gane .

Ban yarda da duka ko zagi da cin fuska ba .

Kuka zeenat din keyi har lokacin shi kansa ya  tsausaya mata matuka 

Ga mamakin DEENI  Sai ya ga ummi itama ta sauko gabansu hawaye ne ke bin fuskarta wani nabin wani ,a rude deeni yasa hannushi yana share mata hawayen .

Cikin tsananin tashin hankali Yace dan Allah first lov ki daina zubda hawayenki  haka ,   kiyi hakuri "zubda hawayenki  bakaramin maseefa bane atattare dani "  idan har yanzu bakya son aurena da zeenat ne wlh  ashirye nake dana bar miki ita har abada .

Cikin kuka  ummi ta girgiza masa  kanta ba kukan komai nake ba DEENI facce na  tsantsar farinciki .

Farinciki ne yamin yawa har  yasani zubda su.

 ,ta janye garesu byn ta dauke hawayen idanunta.

kama hannun deeni dana zeenat tayi "ta hade su waje guda tare da daura nata hannu saman nasu .


Nagodewa Allah daya nuna min wannan rana may cike tarin farinciki mara misaltuwa , zeenat ga deeni nan nabaki shi amana har abada banida kowa Sai shi.

 ki zauna lfy dashi cikin amana "deeni kaima ga amanar zeenat nan naba  matukar ka cuceta "ban bazaka ji dadina ba. Dan Allah Ku kula   da junanku .

Ku rike min amanar junanku " ku kadai gareni byn Allah banida kowa Sai ku.

abinda tata fada kennan tana sake hade" hannuwansu waje daya .


Duk yadda yaso daurewa zuciyar kasawa yayi sakamakon  ,kaunar zeenat din da yake hangowa karara a cikin idanun umminsa.

 bai so zeenat din taga kasawarsa "  dan haka ya kife kansa kan hannun umminsa ya sumbata cikin dabara ya goge kwallar idanunshi. zuciyarsa ke kwabarsa akan alkawarin da umminsa ke so ya daukar mata " shi kadai yasan abinda ke damun zuciyarsa , aranshi ya dinga  ayyana abubuwa masu tarin yawa"anya  kuwa zai iya daukar alkawarin nan ....


jikinsa yayi masa nauyi tausayin ummin ya sake mamaye zuciyarsa. muryasa a sanyaye yace ummi ki kwantar da hankalinki  inshallahu bbu abinda zai faru  zan riketa amana yayinda a cikin zuciyarsa yake sauya kudirin ,ma,anar na karba dan kada Allah ya tuhumeshi gobe kiyama. 

 Yayinda ta kasa km hannuta dake cikin nashi  yake ta murzawa ahankali  cikin wani irin salo da yake sa tsagar jikinta tashi .

saboda nata hannu na kife ne cikin nashi tafin hannun. 

gabadaya jikinta yayi tsanyi  yasoma rawa rawa "dan samun  saukin hanyar tsira da son cire hannuta cikin nashi" yasa tayi saurin cewa na karba alkwarin ummi inshallahu ni dai addu'arki kawai nafi bukata "

.cikin sanyi ya sakar mata hannu .. 

Allah sarki ummi wani irin farinciki ne gyaraye da tsantsar kaunar ya mamaye zuciyarta . murmushin jin dadi ta dinga yi .sannan  ta mikar da zeenat din  tsaye ta rungume ajikinta . Tace Mamana ina miki addu'ar km bazan gushe wajen yi muku addu'a ba Allah ya muku albarka ,ya azurtaku da ya'ya masu albarka.


Da kyar su aunty zahra suka rikota sakamakon rukunkume ummi da zeenat din tayi  .


 sun fito  tsakar gidan dake  cike da  mutane .

Wanda ,Yawancin duk en'uwa ummi ne da kawayenta.


   Kai tsaye gidan  mahaifinta aka  kaita shima nasiha may tsara jiki yayi mata sosai  da nuna mata tayi  hakuri ta kula da mijinta , tamkar yadda mahaifiyarta tayi.  yace naji dadi kwarai da  deeni yakasance miji agareki,ina muku fatan alkhari .

Ina da   yakini deeni zai rike min ke da  amana .'

da baki duk wata kulawar da ta dace.

Ahankali  take cigaba da kukanta.. aranta kuwa cewa tayi  uhmmmm.

 abba  bakasan asalin halin deeni  bane .

shiya ka fadi haka.

 ,halinshi na zahiri kawai kasani bakasan na baniba.

 yace ta daina kuka  duk abinda take  da bukata karta zamo may  rokon miji  ta tmbye shi zai mata   .


,har gidan big dady Sai da aka kaita agurguje suka dawo gidan  kafin motar daukar amarya tazo.

 may gyaran amarya ce ta sake mata sabon gyara  na musamman zeenat din ta sake fitowa  fes abinta .

Sai sheki take zubawa ga wani irin kamshi na musamman dake tashi ajikinta .


Duk da cikin estate din zata zauna hakan bai hana motocin abokan deeni dana fk  cika kofar gidan  ummi ba  .

Dan  daukar amare .


Shemah aka soma saukewa , sannan zeenat aunty zahra ,ke rike da hannuta fuskarta rufe cikin  mayafi" har cikin gidan ta umarceta da tashiga da kafar" dama tare da yin Bismillah " tayi kmr yadda aunty'n tace.

 sannu ahankali har suka iso  dakinta ta zaunar daita akan gado.

 nan da nan mutane suka cika gidan  dan ganin dakin  amarya .


ahankali zeenat ta dan bude idanunta da suke rufe " tana kallon irin dukiyar da Ummi ta narka mata  a daki wanda take jin  ko mahaifiyarta ce a  raye .

bazata iya mata kwatankwacin haka ba , dan ma tsayawa bada labarin irin kayan da Ummi  ta zuba mata a dakin    ma bata lokaci ne ..



  Zaune dake a gefen laulausar zanin gadonta  ta cure  waje daya sakamakon tsaron daya cika . Ahankali ta kai idanunta kan agogon dake manne da bangon dakin" Karfe goma shada ta buga daidai"atsorace ta saki ajiyar zuciya saboda wani sabon tsoro dataji yana kawo mata ziyara.

A ranta tace  kar dai deeni barinni  zaiyi in kwana ni kadai.

 aiko idan haka ta kasance  da nashiga uku dan a gaskiya bazan  iya kwanta ni  daya acikin gidan ba .



Yan kawota basu minti goma da tafiya ba.

 taji saukar yayyafi sama sama wanda ya hadasawa yanayin garin yin tsanyi hade da kamshin kasa.

  " ruwa bai yi yawa ba haka nan  yayyenfin  bai tsaya ba.

Kusan tun lokacin da suka tafi suka barta anan take zaune bata ko motsa ba  Sai yanzu datayi tunanin deeni na iya barinta ta kwana ita kada . Hakan yasa ta Mike cikin tsoro ta kulle kofarta ta dawo ta zauna ,zamanta ke da wuya .


 Tasoma jiyo Hayaniyar   muryoyin  maza daban daban"  a cika gidan  hakan  yasa taji  tsinkewar zuciya  .Tare da faduwar gaba da .

 hankali  ta runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke dukan uku uku kmr zatayi tsalle ta fito waje .


Deeni tsaye a parlour'n yayi  babbake  tare da dakatar da abonkansa .

 yace to to....Nagode sosai da kulawarku. 

rakiyar ta tsaya iya nan..

 ba Sai kunshiga ba.


 fahad ne yayi murmushi sannan  Yace ko baka fada ba ma anan zamu tsaya.

 ,muma bashiga zamuyi ba .

,dan an dade da daina wannan .

 Shr tayi tare da kamkame jikinta waje daya tsoro ne ke sake kawo mata ziyara .

tun tana jiyo hayaniryasu sama sama har tadaina taji dif...alamun basa cikin gidan sun fice .

 

Juyawa suka sake yi tare ya raka su , fahad na ta mishi tsiya iri iri 

Cikin sauri sauri "gudu gudu yashigo parlour sbd ruwan daya sake yin karfi duk ya jike masa farin yadin dake jikinsa . 

Ya tsaya kulle koina .


Ahankali ya murda handle din kofar dakinta yajita a kulle .

Ganin alaum murda kofa yasa ta sake mikewa tayi  taje ta bude masa .

Tana may   sunkuyar da kanta kasa . 

.cikin sanyi jiki ya shigo  dakin  tare da rungumeta tsam tsam ajikinsa da hannushi daya "sannan ya ajiye tarin ledodin dake hannushi kamshin dake dakin kawai ya isa yasa kagane rana ce ta musamman....


Post a Comment

0 Comments