AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗
AYSHA A BAGUDO
Page 19-20
Shiyasa kaga bazan iya kai" kaina gareta ba da sunan Ina sonta , bare tamin salo .
Nan km yayi ta zazzagawa Fk maseefa hade da cewa ai shi yaja masa duk wulakancin da'aka masa .
Fk yace kwantar da hankalinka kabarni daita kawai ,nasan zata yarda ma ,.
kawai dai itama so take ta nuna mana ,itama macece , nasan jan aji ne kawai na mata Amman ita din wa dazatace bata sonka ,Ina rai inshallahu zamuyi nasara.
Cikin fushi da jin haushi deeni Yace in taki yarda ka kyaleta kawai , yarinya sai kace wata gold sai wani yawo akamin da hankali akanta, yaja tsaki hade da kashe wayar batare daya sake jin abinda fk zai ce ba .
Kwana deeni yayi da tunanin hade da zullumi halin da zai tsinci kansa idan yarinyar nan taki yarda dashi, duk shi Gani yake ba sonta yake ba. zai dai yi aure ne kawai saboda umarnin umminsa, bugu da Kari ma, bazai iya kaskantar da kansa wajen mace ba ballanantana har ya kai shi ga furta kalmar so.
Har zuwa wayewar garin ya cigaban mamakinta ganinta yake , tamkar yau aka haifeta, sannan har zuwa yanzu kallon karamar yarinya yake mata, ashe tasan abinda take yi ,uhmmmm uhmmmm ahankali ya dinga sauke ajiyar zuciya, wai zatayi tunani akai ya sake tunawa da kalmar data fadawa fk to da ko da uban wa zatayi tunani ya furta hakan a kasan rashi .
kwance take akan bed din ummi Amman ba bacci takeyi ba ,hannuta rike da wani English novel mai suna ,mumy why sanye take cikin kananan kaya, pencil jeans da riga iya gwiwa a natse take karatunta dan tana jin dadi labarin yarinyar ciki litattafin ta birgeta kwaira ,ta yadda take kokarin kwatarwa kanta enci saboda mahaifiyarta ta hanata auren saurayin da take son ..
Cikin isa da kasaita yashigo dakin , tana jin motsen bude kofa Amman tashare dan batason abinda zai katse mata karatunta .
Jin kamshin turarensa yasa ta dan dago idanunta suka sauka akansa , ganinsa yasa ta dan mike daga kwanciyar datayi, tasha jinin jikinta bata san meke sata jin yawan faduwar gaba ba, a duk sanda taga yaya DEENi .
ta gaidashi batare daya kalli inda take ba , ya amsa mata a ciki ,km cikin isa da takama sannan a takaice , tamkar dai yadda yasaba dan baya son duk abinda zai sa magana tayi tsawo atsakaninsu .
sai dai ita kam tsintar kanta tayi da zuba masa idanunta, tana binsa da wani irin mayyen kallo , cikakken namiji ne sosai mai ji da kansa , ko a tafiyarsa zaka shida haka. gabadaya bbu wata alamun ragwanta atare dashi .kana ganinsa zakaji ya birgeka ,daman aikin da yakace shi kennan wato jami'in tsaro .
Har suka gaisa da ummi dake tsaye fitowarta kennan daga bathroom ya juya da niyar barin dakin, idanun Zeenat na kansa tamkar zata ya dawo ya zauna kada ya fita saboda tsoron masu farautarsa ,takasa dauke idanunta daga kallonsa take taji wani irin masefaffen kishinsa ya diram mata zuciyarta ta dinga rawa bata idanunta a kansa ba sai data daina ganinsa .
Ummi tabita da kallo tausayi tace inkin gama kallon nashi sai ki tashi ki hado masa abinsa ko kawai soyayya aka iya ba'asan tattali ba , Zeenat ta dan turo baki tace ni dai ummi kwanan bansa abinda na miki ba komai nayi sai kin min fada, ki dinga ganin laifina , nifa bashi nake kallo ba , ummi tace eh ai nasan bashi kike kallo ba kuruwarsa kike kallo jairar yarinya kawai ni tashi ban guri .
Washegari
Zeenat tarasa dawa zatayi zance yaya DEENi taji dadi kuma yaba shawara tamkar yadda zuciyarta ta aminta dashi ,ganinta duk wanda ta nufa da maganar baza tasamu goyon baya ba ,kmr dai yadda ummi tayi ,
Maryam ce ta fado mata a rai ,dan haka tashirya taje har part din su.
Tana shiga part din idanunta sukaci karo da fuskar data tsana a halin yanzun arayuwarta ,kmr ta juya ta koma haka taji , shemah ta hango zaune akan three site suna hira da Maryam take taji wani iri abu ya caki zuciyarta .
ganinta yasa taji tamkar an soka mata kibiya ne a kahon zuciya taja ta tsaya takasa karasawa inda suke dan baza juri zama a duk inda take ba , ganin haka yasa itama shemah ta mike ta fice Tama bar part din gabadaya . Da kallo Maryam tabi kowanne su
Ahankali Zeenat takaraso tasamu waje kusa da Maryam din ta zauna zuciyarta a cunkushe , tsawon lokacin takasa cewa komai , Maryam tace wai yana ganki haka ne ? Cikin nishadi Maryam ta soma janta hira har Zeenat ta sake Sosai
Daga nan ta labarta mata duk halin da'ake ciki ,.
Maryam ta zaro idanu waje tana mamaki tace kai da gaske kike ,to Ina girman kan nasa km?
Zeenat tace yana nan bai je koina ba" sai ma abinda yakaru ,
Maryam tace in fada miki gaskiya,zeenat ta daga mata kai alamun eh "ki amince kawai" karkiyi wasa da damarki domin mata dayawa suna can suna neman miji irin yaya DEENi
basu samu ba.
amman idan kin yi saken da kika tsaya yauki ,wai ke jan aji ,kya zo daga baya kina nadama dan irinsu tsada ne dasu ,.
kin dai san halinsa da maseefar zuciyar tsiya.
maryam takarasa zance da
Uhmmmm .. Ina ma ni Yace yana so ......
jin haka yasa take Zeenat ta hade fuskarta tamau , hade da zabgawa Maryam din wata uwar harara tace kefa Yar wulakanci ce bangane dama ke yace yana so ba Maryam tace ke nifa da wasa nake dan baga kmr kin fara hassala Zeenat tace ,wani irin wasa wannan, nifa banson shirme bazan.
Ko kema zaki shiga layin shemah ne?
Maryam tayi murmushi tace bada dai Ai tsakaninmu bbu haka yauwa naji ance ma kunyi fada da shemah Kwanaki ?
wai may ya hadaku fada ne , Zeenat ta tabe baki tana sauke ajiyar zuciya sannan tace shirme tamin irin naki .
nan dai ta zaiyanewa Maryam komai ,suka tafa suna kyalkyale dariya Maryam tace kai tawan kina wuta , Zeenat tace Ai ni bata wasa bace ban daukar raini tuni nagama daita duk da batasan abinda tamin ba har yanzu.
Maryam ta sake bata hannu suka taba, tace baki da kyau fa" sai dai idan ba'a tabo ki ba.
Maryam tacigaba tawan ki Amince kawai da auren nan musha biki amman fa zakisha fama da wannan miskililin ,Zeenat ta sake yin murmushi tace indai zai cigaba da sona kmr yadda yake yi yanzu Ina ruwana da wani miskilancinsa can yakarata , ai abinda yafi ma birgeni dashi kennan.
Amman nasan wuyarta dai ayi auren da sannu zai rage duk wannan jin kan nasa .
Zeena ta kagu dare yayi saboda cewar da yaya faruk yayi zai dawo .
,tun tana Jiran zuwansa har ta fida tsammani dan tara tayi gabadaya hankalinta a matukar tashe yake,t unaninta kar dai ya deeni ya hakura daita kmr yadda tace abashi hakuri.
zuciyar tashiga rawa tamkar zata tsinke ta mike tsaye cikin sanyi jiki tasoma zariya duk dai ummi biye daita da kallo can Ganin goma tayi yasa ta nufi dakin ummi tana shiga ta fada kan gadon tana zubda kwalla,.
ahankali tace Allah Allah kasa ba hakura yaya DEENi yayi ba ,.
dako na cuci kaina da kaina tashiga zubda hawaye baji ba Gani tana jin zuciyarta na neman taewatsewa tace Allah ka tausayin ka jin kai na ka mallakamin abin kaunarta deeni ina sonka deeni tunda ka furta kana sona nakasa samun sukuni dan karkace ka fasa kuka take sosai hade da sambatu ,,.
Shadaya daidai ummi tashigo ta dubi inda Zeenat take kwance taga alamun kmr bata jin dadi karasowa yayi tace ke lafiyarki kuwa da kyar Zeenat ta iya bude bakinta,t ace kaina ke min ciwo ummi tace shine zaki zauna kina kuka ,tayi mata sannu taje takawo mata magani .
Wasa wasa sai da Zeenat tayi kwana biyar cur batare da taga zuwan yaya faruk ba.h hakan yasa hankalinta sake tashi fiyye da koda yaushe .
cikin lokacin kadan ta zabge ta sake ragewa zazzabi may zafi ya rufeta, jikinta ya dauki zafi gwau , hankalin ummi yatashi , da Ganin halin da Zeenat take ciki kmr zatayi kuka.
Ummi ta kira likitan dake duba su, wato family doctor dinsu , byn yazo ne yasoma aikinsa cikin sauri ganin yadda Zeenat din takeyi taki magana sai zubda hawaye kawai take ga zuciyarta na buguwa da sauri da sauri Ganin haka yasa doctor din ya dauko abin awo ,ya auna BP dinta ,cikin mintina da basu wace ashirin ba ya gano abinda yake damunta sannan ya daura ma drip hade da sanya allurar bacci ciki take ko bacci yayi awon gaba daita .
Gabadaya hankalin Ummi ya sake tashi wani irin tsoro ne yashigeta lokacin daya ,da sauri tace doctor meke damunta ?
doctor yayi shiru yana nazarin abinda zai cewa Ummi kafin daga bisani ya numfasa ,sannan Yace akwai abinda tasa aranta wanda shine yayi dalilin haddasa mata damuwa har takai jinita ya hau sosai , Ummi ta sake maimaita abinda doctor yace , doctor yace Amman inshallahu bbu da damuwa zata samu lfy da zarar ta tashi komai zai yi dade, ummi tace to doctor na gode yayi mata sallama tare da gayamata yadda zata bata magani.duk wannan drama da akeyi deeni bai sani ba dan ko yashiga gaida Ummi baya damuwa daita ballantana yasan ko bata da lfy ne ,ita Kuma da haushi taki sanar masa Ai shi ba makaho bane
Kwata kwata Fk bai samu damar zuwa ba sai acikon kwana na bakwai tukun yazo ,yasamu Zeenat din bayadda take yayi mamakin , yadda DEENi bai sanar masa ba gashi kusan kullum sai sun hadu .
byn sun gaisa da ummi ne ,ya fita Yace Zeenat din ta same shi a parlour .
Cikin tsanyi jiki ta mike tasoma daga karta da kyar, cikin gimtsewar fuska ummi tace Ina km zaki kefa bakida lfy ?
Zeenat tabata fuska dan kada ummi ta hanata zuwa tace ummi sako zan karbo gurin Yaya faruk ,yanzu zan dawo , Ummi ta bita da idanu kawai Zeenat tace ummi sai nadawo cikin jin haushi da akaici Ummi tace kada ma ki dawo ki kwana a can .
Da sallamarta tashigo parlour "Zaune ta same yaya faruk din suka gaisa ya sake yi mata ya jiki sannan Yace sister kiyi hakuri dan girman da rashin zuwana kmr yadda nace, wasu abubuwa ne suka sha kaina wlh, dan haka yanzun naxo naji abinda kika yanke,zeenat ta danyi shr kmr mai nazari Yace kada ki damu idan har baki son shi , kisanar dani ,danshi yace idan baki amince ba, kada atakura miki shi ya hakura, a dan frigice tace Ai yaya kaima kasan bazan iya cewa banason shi ba, ko dan ummi dan haka kace masa kawai na amince .
Fk ya saki murmushi murna yayi hamdala a zuciyarsa hade da godiyar cin nasara yace Shikenan ni zan wuce sai kin jimu .
A ranar ummi ta nemi ciwon Zeenat ,tarasa duk tana zargin ciwan nata bazai wuce akan DEENi bane ,da daddare har nafila Zeenat tayi dan Mika godiyar ga Allah. ummi tayi murmushi tace yau km ibadar ce ta motsa har da sallar dare ?
Zeenat tayi mata banza kmr bataji ba tacigaba da sallarta, Ummi ta sake cewa Allah yasa a dore in km nasamun NASURULDEENI ne nasan daga yau Shikenan .
Abinda ke sake bawa Zeenat mamaki bai wuce Ganin yadda kullum yaya DEENi ke nuna ko in kula akanta ba gabadaya ma Gani take kmr baisan da zamanta ba .
ko magana ta fatar baki bata hadu su, idan ma yana guri kennan ita kanta batason zama in da yake yanzu ,Allah Allah take tabar wanje dan juriyarta takusan karewa .
Fk bai samu ganin deeni ba, sakamakon wani aiki daya taso masa ,Amman Yace masa yabari zuwa weekend ,ya same shi a gida .sai da fk yakirasa a waya ya tabbatar masa da yana gida sannan yazo .
zaune suke cikin parlour deeni byn sun gaisa fk yayi masa bayani duk yadda suka yi da Zeenat a boye DEENi ya sauke ajiyar zuciya ,sannan Yace ta taimaki kanta da kanta , kennan , fk yabishi da wani irin kallo sannan yace kai fa dan rainin wayo ne abinda yakamata kace kennan, deeni Yace nifa bawai na matsu dole sai ta amince da aurena bane .
asalima ita din ba irin kalar type dina bace zan dai aureta ne kawai ,a rashi samun choice dina fk ya saki baki yana kallon deeni ,Yace Amman friend kasan itama tana kyawunta daidaina , sai da ya dauki lokacin sannan yace ni nace maka dan kyawunta zan aureta?
Ai bata da kyawun da zai rudeni ,km wlh har ga Allah da bata amince ba na hakura , har zuwa sanda zansamu type dina.
MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗
AYSHA A BAGUDO
Page 21-22
Wani irin kallon mamaki fk yake masa , ,gabadaya ya zamo tamkar mutun mutimi a zaune a gurin ,
Yarasa meke damun brain din DEENi , mutun Sai girman kan tsiya da nuna isa " wai shi DEENi wani irin bahagon mutun ne ?
Shi sam bbu ruwan shi da fadar duk magana da tazo bakinsa .
In a low voice fk yace yanzu duk wahalar danayi akan yarinyar nan yatashi a banza kennan?
A'a bakayi a banza ba tunda gashi "zan aureta gaskiya ce dai na gaya maka,dan kasan ita din ba ra'ayina bace .
Amman narasa dalilin da yasa zuciyata ke muradin kasancewa tare daita " fk ya sake dubanshi sannan yace dan rainin wayo kawai kar mai dani kmr wanda bai san komai ba mana .
,tunda har zuciyarka ta iya amincewa daita, har kaji zaka iya aurenta definitely kana sonta" ko yaya ne" ,.
deeni yaja tsaki hade da furzar da iska ta bakinsa" matsala dakai kennan rashin saurin fahimta fk yace idan son da kake mata ne ,na fahimta ,Amman kace wai kai baka sonta km kake kokarin aurenta , wannan ne fa bazan taba fahimta ba , DEENI ya sake first da huci may zafi ranshi tasoma baci muryasa a sarke" yace da alamun kana son musamu matsala dakai fa" muddin baka daina cewa Ina son yarinyar nan ba .
Idan km kafin son haka ya daga kafadarsa alamun Shikenan , parlour ya dauki shr na wani "dan lokaci yayinda deeni ya jingina bayansa da kujera da yake zaune, hade da runtse idanunshi ya dan jin daci maganar fk 'ta yaya ma " zai nace akan yana son yarinyar byn shi yasan aure kawai yake da bukatar yi bawata ,aba soyayya ba ...
maganar fk ce ta daki dodon kunnenshi" to yanzu meyye solution tunda yarinya ta rigada ta amince ?
Ahankali ya bude rikitattun idanunshi ya sauke su ,akan fuskar fk sannan yayi magana cikin sanyi tamkar wanda aka takura masa. Yace karkadamu zan samu yaya mahamud ,Ai kagama may wuyar "ya maida idanunshi ya sake lumshe su tamkar dai yadda yayi dazu .
girgiza kai kawai fk yayi uhmm shi wannan bazai taba canzawa zai ba .
halinsa, na nan kmr dai yadda yasan shi" haka km yataso " shi komai baya so matsawar ba ra'ayin sa bane" duk yayi magana ne akasan ransa,,.
Ganin ya bawa banza ajiyarsa yasa shima ya mike yayi masa sallama .
Daga gurin DEENi kai tsaye fk part dinsu shemah yayi yaja ya tsaya byn ya tura ayi masa kiranta fk tafito sanye da doguwar rigar material puppy colour mai shegen kyau hade yane kanta da karamin mayafe baki ahankali take isowa gareshi duk step daya Sai kirjinta ya motsa tun fitowarta ya zubawa kirjinta ido kyam yana kallon yadda kirjinta ke motsawa lumshe idanunsa shi yayi na wani lokacin sannan ya sake budesu ahankali mutuwar tsaye a gurin har takaraso inda yake ta gaisheshi cikin sanyi jiki bai dauke idanunshi akanta ba yacigaba da da binta mayataccen kallo da sallamarta iso inda yake ta gaisheshi ya amsa yana sake bin koina na jikinta da kallo cikin sanyi tace yaya faruk Gani Yace Ai naganki ,daman nazo ne na fayace miki abinda na dade Ina boyewa akanki ,nan dai yasanar mata koma , tunda yasoma magana tayi shr kawai hade da sunkuyar da kanta badan tana jin dadin abinda yake kokarin fahimtar dai ba ahankali ta dago ta zuba masa idanunta Sai data tabbatar ya gama fadar abinda yakawoshi sannan tace ,dan Allah yaya kayi hakuri wlh akwai wanda zuciyata ta dade da kamuwa da soyayyarsa , Amman kayi hakuri idan maganata ta bata maka rai ,yace Ina Gaza bata min rai Ai iya gaskiyar ki kika fada Sai dai ki sani zuciyata bazata iya hakura dake ba Amman zan baki lokaci yi tunani akai tace nifa bawani tunanin dazanyi akai ka dai yi hakuri ka nemi wata ,ta juya ta wuce tabar sa nan tsaye ,da mamaki yabi bayanta da kallo ya dauki lokacin tsaye a gurin batare yasan abinda zaiyi ba , Ganin tsayuwa nasa bata da wani amfani yasa yasoma kokarin daga kafafunta ahankali tafe yake yana saka da warwara da tunanin malomasarsa a gurinsa ,a fusace shemah tashiga part dinsu tana zuba tsaki da zage zage har mmnta ta tambayeta abinda yasameta tace matabakomai.
Byn kwana biyu
Da misalin karfe takwas na dare fk ya km samu shemah da zance shi fa ba zai iya wani hakura daita ba kawai tayi hakuri ta amincewa da bukatar domin shi yana matukar son ta km aurenta yake son yi ,tace dan Allah yaya kayi hakuri wlh da bbu wanda nake so ne ,zan iya soka dan kaima baka rasa komai da zankika ba , kadai yi hakuri kawai .
al'amarin dayayi matukar dagawa fk hankali kennan ,yayi shr kawai yana kallon yanayinta tare da nazarin kalamanta masu kokarin tarwatsa masa zuciyar rasa yadda zanyi daita yayi can dabara tazo masa,ya tsareta da idanunshi Yace ke banso iskanci da rainin hankali fa ni zaki cewa kina da wanda zaki kike so byn Banga uban da kike saurara ba ,lafazinsa yayi mugun bata mata rai dan haka a ranta abace tace to dole ne Sai na aurenka kaje Kanemi wata mana ko ana soyayya dole ? ta juya a fusace zata bar guri ,ya fizgota hannuta , gabadayanta ta fado jikinsa , idanun ta zaro a tsorace, ,take taji wani irin faduwar gaba , .
Hannuwansa dukka yasa rungumeta tsam ajikinsa yana sauke ajiyar zuciya daidai kunneta ya kai bakinsa Yace maimaita abinda kikace Ina jinki cikin tsiwa tace wannan wani irin iskanci dazaka wani rungume mutun ? Ok nine ma nake miki iskanci ?
Uhmmmm fa shemah karkibari muyi haka dake zaki amince ta girma da arziki ne ko km na jawo soyayyata ta karfin tsiya ,.batare da na wahalar da kaina ba muryarta na rawa tace anki a amince da soyayyarka .
ko ana so dole ne ?
, dan Allah ni kasake ni ,ya zuba mata manyan idanunshi kawai ,yasoma yawo da hannushi a jikinta gabadaya jikinta ya dauki kirma abinda bai taba faruwa daita ba kennan tunda take arayuwar ta ,wai namiji ya rabi jikinta har takaita ga runguma ,dan takaici ma batasan sanda , kwalla ta cicciko a idanunta ba , hawaye yaga yana silalowa daga idanunta ahankali ya sauke ajiyar zuciya, ya dan sausauta rungumar da yayi mata yasa yatsansa ya dangwalo hawayen dake bin fuskarta yana kallo Yace duk wannan kukan akan nace Ina sonki ne kike zubda hawayen ki?
,tayi shr taki cewa komai dan haushi ji tayi kmr ta daura hannuta akanta ta kurma ihu , ahankali ya sake maida ita jikinsa ya rungumeta yana shinshina wuyanta daidai nan Sai ga big dady dake dawo daga masallaci , a tsorace yake binsu da kallo cike da mamaki da alajabi abinda yagani , meke shirin faruwa km yau acikin zuri'arsu ,fk yacigaba manneta da jikinsa yana rarrashi ta amincewa aurensa , dagowar nan da zai lyi karaf idanunsa suka sauka kan big dady dake tsaye duk da duhu ne hakan bai hana gareshi ba gabansa yaji yayi muguwar faduwa jikinsa ya dauki kirma duk da ya tsorata Amman yaji dadi Ganin da big dady yayi musu ,yasan hakan zai sa a aura masa shemah batare da bata lokaci ba tsabar frigice yasa yakasa rabata da jikinsa gabadaya jikinsu rawa yake shemah da batasan wainar da'ake tuyawa ba sake lafewa tayi ajikinsa saboda irin rungumar dayayi mata ba wacce zata iya kwacewa bace har big dady ya wuce su a gurin shemah batasa big dady yagansu , ahankali fk yasoma rabata da jikinsa har zuwa yanzu hawaye bai daina bin fuskarta ba hannuta yakamo yasoma tafiya ita kum tana biye dashi bbu wanda ya iya cewa dan'uwansa komai har yakawo part dinsu yaja ya tsaya ahankali Yace shemah kiyi hakuri dan Allah kibar kuka ba nufi na kuraki ba Ina matukar kaunarki bansan lokacin dana fara sonki ba Amman zan baki lokacin kiyi tunani akai ,zan dawo zuwa jibi yana gama fadar haka ya juya da kyar yake iya daga kafafunsa tsabar frigice da nauyin da suka masa zuciyarsa tamkar zata buga , dan fargaba haduwarsu da big dady shi yasan ba makuwa tunda har big dady yagansu aure kmr anyi an gama Amman kunya fa ,har ya iso part dinsu wanda kusan nan samari suke zaune wayanda basuyi aure ,
Itama tana shiga dakisu ta wuce kai tsaye tana kuka , mamanta dake zaune a parlour tace ke lafiyarki Amman ko juyo batayi ba fadawa tayi kan gado tana risgar kuka to meye yaya faruk yake nufi daya sonta alhalin ita DEENi take mutuwar so ..... Dan haka bata taba aurensa ba ,tunawa datayi ba'a musu auren dole a family dinsu sai sun amince da juna yasa taji hankalinta ya kwanta Amman gabadaya jikinta yayi bala'in sanyi haka ta wuni a daki batare data sake fita ko parlour ba ,fk bai dawo ba kmr yadda Yace mata kusan sati tsakani shiyasa tayi tunanin ko yayi wa kansa fada ne ya hakura daita dan haka ta sake abinta kwasam Sai gashi a wani daren lahadi byn tagaishi a dage ,yayi murmushi yace yazo ne akan maganar su ,a fusace tace wata magana kennan i tough mun gama da wannan zance tunda nace ban sonka , Yace haka kika ce ,tace eh ko dole soyyaya dakai ,Yace uhmm Amman dolenki ki aureni ya wuce batare da damuwa ,
DEENi yasamu yaya mahamud yayi masa bayanin shi kuma ya samu big dady da zance tsohon yaji dadi Sosai jin sun hada kansu yace Shikenan bbu damu zai tuntubi yarinyan tukun asan abinyi .
Nan dai aka saka ranar aure tare da yanka sadaki yaya mahamud ne yayi komai ko sisin Kobo bata fita daga aljihun ogo deeni ba ko mahaifin zeenat yayi murna sosai da jin DEENi ne zai aure diyarsa
Anyaka sadaki da dukiyar aure naira duba dari biyar wanda duk a aljihun yaya mahamud suka fita .
Da kyar big dady yashawo kan Ummi dan tuburewa tayi ita sam bata yarda da wannan aure ba big dady yace Ai tunda dai yara sun hada kansu km suna juna Ai Ina Gani magana takare fatanmu Allah ya zaunar dasu lfy .
Lokacin da aka sanar da DEENi ansa ranar wata biyar deeni Yace wa yaya mahamud lokacin nan bai yi yawa ba kuwa ?
Dan akwai aiki da zai kaini akwaibon Ina Ganin zaifi kyau a takaita lokacin koma ba dan haka anawa raayin nafi son ayi nan da wata uku yaya mahamud yace Shikenan kabari dai zan samu Ummi da maganar .
Zaune take a cikin extra room dinsu wanda kusan yanzu can tafi zama tunda aka sa musu rana da yaya DEENi ta zabga uban tagumi tana mamakin hali irin na yaya DEENi yau kusan wata biyu Keenan dasamusu rana Amman ko sau daya bai taba kiranta da sunan zance ba haka nan ko cikin part din Ummi yashigo bata ishe shi kallo ba takan ji tsoro da frigice sun shigeta a duk sanda taga yaya DEENi nuna rashin damuwarsa akanta ,a kasan ranta tace, anya kuwa banyi kuskure da wautaba wajen saurin amincewa aurensa ba domin fa zuwa yanzu tasoma sarewa anya kuwa yaya DEENi yana sonta ?
kullum miskilancinsa sake gaba yake har zuwa yanzu dabatason cikakken matsayin ta a gurinsa ba ,son auren yasoma fice mata arai domin ita kadai tasan fargaban da take cikin zuciyarta ga ,gorin da Ummi kebinta dashi kullun garin Allah ya waye , dan haka ta yanke hukunci samun yaya faruk dan ta inda aka hau tanan ake sauka .ta shirya taje har part dinsu tace daman tazo ne akan maganar mu da yaya DEENi idan fa abin nan bazai yiwu ba gara tun yanzu abarshi .
Fk ya gyara tsayuwa sannan yace wani abu ne ya faru ? Tace to yaya faruk a haka ne zamu fahimci juna in San abinda yake so shima yasan wanda banaso shi fa aure ba banza bane kmr yadda ya dauki komai tacigaba bai taba kirana ba km ko gida yashigo ban ishe shi kallo ba shi bashi da lokacin kowa sai na kansa fk yace kiyi hakuri bawai zangoyi bayansa ba aikine yayimasa yawa kiyi nasa uziri Amman kina ranshi zeenat ta tabe baki dan tasan karya ne yace wai tana ran yaya DEENi Ai abinda kake son baka sakaci dashi fk yacigaba komai yakusan zuwa karshe da zarar kin zama a gidansa nasan dole ya baki dukkan lokacin sa ,zeenat tayi shr ne kawai ba wai dan maganar tashigeta ba , fk yace tayi hakuri zai masa magana da sauri ,zeenat ta dago tace dan Allah yaya kar kace ni nayi maka maganar ya sake dubanta sosai yaga duk ta wani frigice yace karki damu ni nasan abinda zanyi .
Fk yakira deeni a waya Amman ba'a daga ba
Da misalin karfe goma na dare fk ya amsa kiran DEENi tare da yin sallama byn sun gaisa yace friend dazo inata kira baka daga ba DEENi ya runtse ritattun idanunshi tamkar na may jin bacci sannan yace wlh aiki ne yasha kaina lafiya dai ko ya fadi cikin kasala dan duk a gajiye yake fk yace lfy dama akan maganar yarinyar nan ne yakama mushirya muje zance gurinta , ,anhakali DEENi ya bude idanunshi jin abinda fk yace muryasa a sarke yace wacce yarinyar km?
Fk yace sai karinka yin kmr baka san da zance ba ,byn nasan tana ranka DEENi yace dan malam karkadameni go to the point dan bangane wacce yarinyar kake nufi ba fk yace Ai dole ka manta da ko wacce yarinya ce tunda kaga kasameta cikin kwanciyar hankali km Ummi ta amince ,tsaki yaja kana yace wai zeenat kake nufi ?
Yasake jan wani tsakin mtssss wani irin hira kum kmr muna kauye byn angama magana sai jiran lokacin fk yace kai mugun dan iska ne Ai duk da haka yakamata muje dan ita yarinyar tasan raayinka kai ma haka ku samu fahimtar juna DEENi ya katse shi da itace Keenan ta aiko ka fk yace ko daya ni dai naga dacewar haka DEENi yace to baza'aje ba ... Kar Allah yasa mu fahimci juna, ita tun tasowarta, bata san abinda nake so da wanda ba,fk yace idan ita tasan abinda kake so da wanda baka so kai kasan nata ?
DEENi ya sake jan tsaki hade da kamo lip's dinshi na kasa yana dan ciccizawa sannan ahankali yace to sarkin yakinta ni ba haka taarina da raayina yake ba Ina tunanin in har zanje zance gurin budurwar ,zanje ne dan tallar kaina in samu gindin zama to ni narigada na samu shigar ,bbu dalilin da zai sa na takurawa kaina me kadauki ni ,nafa san irin son da yarinyar nan take min ,kawai dai ni banda lokacin wannan shirme dakace km nasan ita ta aiko ka fitowa ne kawai bazakayi kafada ba .
Fk yaja tsaki shima yace kai ,dan Allah wani irin bahagon mutun ne?
To wlh ka canza wannan budadden halin naka, to ko waya ce ka tsiya mata ,DEENi yace shima din baza'a tsiya ba ,duk abinda zai faru ya faru ciki har da fasa aurena ,fk yace kai fa kafiyye kafiya ,da maida karamar magana tazama babba ,. yace sake cewa yanzu dai kayi hakuri dan girman Allah ka Sai mata ko karamar waya ce.
DEENi yace kasan Allah ko game bazan Sai mata ba , ballanantana waya , tunda har taiya zuwa ta sameka da maganar bana kiranta fk yace kadaina cewa tasameni ni kawai Gani nayi ya dace muje DEENi ya tabe baki tamkar fk din na ganinsa Shikenan kai ka sani ni km kar ka sake damuna da maganar wata yarinya ya kashe wayarsa batare da ya tsaya jin abinda fk zai ce ba .
Wasa wasa lokacin bikin ya dinga karatowa da kwanaki ya wattani har zuwa yanzu dayayi sauran wata cif cif ayi daurin aure to Ganin kurewar lokaci yasa DEENi yasamu Ummi da maganar shifa baya son zamansa cikin estate din taje Ummi tayi kicin kicin da ranta sannan ta dago tana dubansa tace bangane abinda kake nufi ?
Sai da ya sake maimaita mata tukun Ummi tace sam ita bata yarda ba salon yaje yana dinga cin amanar Yar marainiyar Allah ga babbin gurin bid dady yasa an Gina musu shida sauran enuwansa shine kai dan iyayi zaka ce bazaka zauna ba ,to wlh kaji na rantse anan zaku zauna Sai naga yana yin zaman naku cikin yin kasa da murya yace Shikenan first lov na hakura duk abinda kika ce shi za'a yi tace da dai yafiye ma a yi mutun Sai girman tsiya da iyayi yace to kiyi hakuri .
Zeenat dake sauransu ta lumshe idanunta jin Ummi bata amince ba dan tana matukar jin tsoro zaman daga ita Sai shi ahankali cikin sanyi jiki ya mike idanunshi suka sauka akan inda zeenat ke kwance suka hada ido da sauri ta gaidashi hade da dauke idanunta ,bai sake kallonta ba bare ya amsa gaisuwar ta .
Shirye shiryen biki ya tashi gadan gadan enmata duka a tare suke shirinsu dan yanzu zeenat ta saki da shemah sun koma kmr da ganin da tayi wanda ma take haukar akansa bai san da zamanta ba wata safiya suka shirya zuwa siyayar su irinta amare mutun biyu ne abayanta mota Maryam da shemah yayinda zeenat ke gaba kai tsaye kasuwar Lagos suka nufa sukace derive yayi parking a idimota su kum suka shiga cikin market din
Derive yaja ya tsaya suna fitowa da yaya kamil suka soma cin karo tun shigowar motar dayaga hango zeenat zaune ya zubawa motar ido har sanda ta fito ahankali suka jiro suna hira Amman banda zeenat dataji gabanta ya yanke ya fadi dan tun lokacin da aka mata rana ,rabonta dashi dai dai sun kusan geftashi yakira sunnanta zeenat..... tacigaba da tafiyarta dan batason abinda zai km hada ta dashi cikin sassarfa ya biyo bayanta yasha gabanta cak taja ta tsaya suna kallon junansu,yayinda su Maryam suka cigaba da tafiyarsu suna tsaye batare da dukkansu suyi yunkurin yin magana ba kamil ya gyara tsayuwa ya tura hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa ya kafeta da idanunshi ta sunkuyar da kanta kasa sannan tace lfy yaya ka tsayar dani muryasa a dashi yace lfyr ce takowa haka yanzu zeenat kin kyauta kennan ki zabi wani kibarni byn duk lokacin dana dauka Ina fama da soyayyarki ,a she kinsa bakya sona kibarni inata faman hauka akanki tace Allah yaya ba haka bane Amman kayi hakuri dan Allah, ya sake gyara tsayursa , yayinda idanunshi ke kanta har yanzu yace iya hakuri ne kawai zai wadatar da zuciyar da tayi sama shekara biyu tana mata da miki so.... yace Shikenan bbu komai Nagode Kwarai da abinda kika saka min tace ka dauka haka Allah yaso ni din ba matar ka bace yayi murmushin karfin hali sannan yace haka ne fa al'amarin ubgj Amman agaskiya DEENi ya cuceni ,tace kabar cewa ,tayi ta dago suna kallon juna fuskarta dauke da murmushi ta bude baki kennan Sai ga motar DEENI ta kuno kai cikin compound din km shi suke facin Ai take maganar ta ta tsaya sakamakon DEENi data Gani zaune a mota yana kallonsu duk kasancewar akwai dan duhun magariba hakan ba zai sa takasa gane bscin ransa ba , gabanta ya yanke ya fadi , ,shima kamil din shr yayi bai sake yin magana va kusan minti goma yayi yana kallonsu koda bata ga fuskasa sosai ba tasan a daure take ,har sanda DEENi ya fito yayi matarsa key idanunshi na kansu ,cikin tsoro da frigice zeenat tace ni zanshiga ciki ,kamil yace Shikenan Allah yabaki zaman lfy ta gefensu yazo yazo ya gifta hade da jan tsaki sannan ya wuce . a filli ta furta wayo Allahna nashi uku kamil ya sake yin murmushi dole sannan yace da'aka me,da kika shiga uku, nifa Banga abinda ya birgeki a DEENi ba,har da kika iya zabarsa , kalli fa yadda jikinki ke rawa saboda Allah tamkar kinga wani malaika tsaki taja hade da zabga masa harara dan Allah kabarni naji da damuwa Ai duk kai kaja min matsala Ina zaman zamana da yanzu Ina cikin gida💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗
AYSHA A BAGUDO
Page 21-22
Wani irin kallon mamaki fk yake masa , ,gabadaya ya zamo tamkar mutun mutumi ,a zaune a gurin ,
Yarasa meke damun brain din DEENi , mutun Sai girman kan tsiya da nuna isa ,fk ya dinga masa kallon bahagon mutun wanda
Shi sam bbu ruwan shi da fadar duk magana da tazo bakinsa .
In a low voice fk yace yanzu duk wahalar danayi akan yarinyar nan yatashi a banza kennan?
DEENi ya tabe bakinsa hade da cewa A'a bakayi a banza ba tunda gashi "zan aureta gaskiya ce dai na gaya maka,dan kasan ita din ba ra'ayina bace .
Amman narasa dalilin da yasa zuciyata ke muradin kasancewa tare daita "alhalin bata sonta nake yi ba .
fk ya sake dubanshi sannan yace dan rainin wayo kawai "kar ka mai dani tamkar wanda bai san komai ba mana .
,tunda har ita zuciyartaka ta iya amincewa daita, har kaji zaka iya aurenta definitely kana sonta" ko yaya ne" ,. Amman maganar kace baka sonta,wannan ma ba gaskiya bane .
deeni yaja tsaki hade da furzar da iska ta bakinsa" sannan yace matsalata dakai kennan rashin saurin fahimta .
fk yace ta yaya kake so na fahimta ?
Alhalin ga zahirin gaskiya nan" idan son da kake mata ne ,na fahimta wannan.
,Amman kace wai kai baka sonta km kake kokarin aurenta , wannan ne fa bazan taba fahimta ba.sai dai kayi hakuri ,
DEENI ya sake furzar da huci may zafi ranshi yasoma baci muryasa a sarke" yace da alamun kana son mu samu matsala dakai fa" muddin baka daina cewa Ina son yarinyar nan ba .
Idan km kafin son haka ya daga kafadarsa alamun Shikenan ,.
parlour ya dauki shr na wani "dan lokaci, yayinda deeni ya jingina bayansa da kujera da yake zaune, hade da soma jijiga kafarsa daya a tile's dakin " runtse idanunshi Yayi dan jin daci abinda fk din yace"
'ta yaya ma " zai nace akan lallai yana son yarinyar byn shi yasan auren kawai yake da bukatar yi" bawata ,aba soyayya ba ...
maganar fk ce ta daki dodon kunnenshi" to yanzu meyye solution akan maganar, tunda yarinya ta rigada ta amince ?
Ahankali ya bude rikitattun idanunshi ya sauke su ,akan fuskar fk sannan yayi magana cikin sanyi tamkar wanda aka takura masa dole. Yace karkadamu zan samu yaya mahamud ,Ai kagama may wuyar " tare da maida idanunshi ya sake lumshe su tamkar dai yadda yayi dazu .
girgiza kai kawai fk yayi. uhmm shi wannan bazai taba canzawa ba .
halinsa, na nan kmr dai yadda yasan shi" haka km yataso da murdanden raayi " shi komai baya so matsawar ba ra'ayin sa bane"fk yayi magana ne akasan ransa,,.
Ganin da yayi DEENi ya bawa banza ajiyarsa yasa shima ya mike yayi masa sallama yayi ficewarsa .
Daga gurin DEENi kai tsaye fk part dinsu shemah yayi ,ba bata lokaci yasamu yaro ya tura ayi masa kiranta dan ya kudirtawa ransa ,yau ce, ranar da zai isar da sakon zuciyarsa gareta domin yagaji da cutar da kansa .
tafito sanye cikin doguwar rigar material puppy colour mai shegen kyau hade da yane kanta da karamin mayafe baki,
ahankali take isowa gareshi duk step daya datayi Sai kirjinta ya motsa sakamakon dukiyar fulani dake gareta.
tun fitowarta ya zubawa kirjinta idanunshi kyam ko kyafta ido bai yi yana kallon yadda albarkatun kirjinta ke motsawa, lumshe idanunsa shi yayi na wani lokacin ,sannan ya sake budesu ahankali. mutuwar tsaye yayi a gurin " har takaraso inda yake tayi sallama.
bai dauke idanunshi "akanta ba .Sai ma cigaba da yayi" da binta da wani irin mayataccen kallo wanda yasa shemah tasha jinin jikinta.
Ganin irin duban da take masa ne yayi saurin ,sauke idanunshi,tare da sakin ajiyar zuciya, ta gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska, yana sake bin koina na jikinta da kallo dan tayi masa kyau matuka ,rigar jikinta irin mai flay akasa ce Sai dai taka mata a sama sosai. cikin sanyi murya tace yaya faruk Gani , Yace Ai naganki .
,yayi shr yana tunanin ta inda zai soma ,itama shr tayi Sai dai,haka kawai ta tsinci kanta da jin ,faduwar gaba. haka nan kallon da yaya faruk din kema ,yasa taji wani iri ajikinta ,dan haka ,ta sunkuyar da kanta kasa tana Jira daga gareshi.
,can numfasa,hade da jin kwarin gwiwa yazo masa ,ya danyi gyaran murya" yace daman nazo ne na fayace miki abinda na dade Ina boyewa akanki , taji gabanta yashiga faduwa ,ta dan dago kadan ,taga ita yake kallo , ahankali tace na mefa? Sannan ta km maida kanta kasa tana jin yadda gabanta ke lugude faduwa.
Yayi murmushi yana cigaba da kallonta, cikin natsuwa da jarumta.
yasanar mata koma .
tun da yasoma magana tayi shr kawai hade da sake sunkuyar da kanta kasa, sosai badan tana jin dadin sauraron abinda yake kokarin fahimtar din bane ,taji hankalinta ya yayi matukar tashi dan haka , ahankali ta dago kanta , ta zuba masa idanunta , Sai data tabbatar daya gama fadar abinda yakawoshi a dan frigice tace ,dan Allah yaya kayi hakuri wlh akwai wanda zuciyata ta dade da kamuwa da soyayyarsa , Amman kayi hakuri idan maganata ta bata maka rai ,yace Ina fa za bata min rai Ai iya gaskiyar ki kika fada Sai dai ki sani zuciyata bazata iya wannan hakura dake bani ba Sai d zan baki lokaci kiyi tunani akai , tace tunanin me km zanyi? nifa bawani tunanin dazanyi ka dai yi hakuri kawai ka nemi wata ,ta juya ta wuce tabar sa nan tsaye .
,da mamaki yabi bayanta da kallo ya dauki lokacin tsaye a gurin batare da yasan abinda zaiyi ba , Ganin tsayuwa nasa bata da wani amfani yasa yasoma kokarin daga kafafunsa da suka masa nauyi, ahankali yake daga kafafunsa yana saka da warwara" da tunanin makomasarsa a gurinta .
,a fusace shemah tashiga part dinsu tana zuba tsaki da zage zage har mmnta ta tambayeta abinda yasameta tace mata bakomai.
Byn kwana biyu
Da misalin karfe takwas na dare fk ya km samu shemah da zance ,shi fa bai ji zai iya wani hakura daita ka " kawai tayi hakuri ta amincewa da aurensa , domin shi yana matukar sonta ,tace ni dai dan Allah yaya kayi hakuri wlh da bbu wanda nake so ne ,zan iya aurenka dan kaima baka rasa komai da zankika ba . kadai yi hakuri kawai .
al'amarin dayayi matukar dagawa fk hankali kennan ,yayi shr kawai yana kallon yanayinta tare da nazarin kalamanta masu kokarin tarwatsa masa zuciyar rasa " yatasa yadda zaiyi daita, can dabara tazo masa, dan haka ya tsareta da idanunshi Yace ke banso iskanci da rainin hankali fa" ni zaki cewa kina da wanda zaki kike so byn Banga uban da kike saurara ba.
,lafazinsa yayi, matukar bata haushi da mugun bata mata rai" dan haka ranta a bace tace to dole ne Sai na aurenka kaje Kanemi wata mana ko ana soyayya dole ? ta juya a fusace zata bar guri ,ba zato ba tsammani taji ya fizgo hannuta , gabadayanta ta fado jikinsa , idanunta "zaro a tsorace, ,take taji wani irin faduwar gaba fiyye da wanda taji dazu , .
Hannuwansa dukka yasa ,ya rungumeta tsam ajikinsa yana sauke ajiyar zuciya "daidai kunneta ya kai bakinsa Yace uhmmm maimaita abinda kikace Ina jinki?
cikin tsiwa tace wannan wani irin iskanci ne dazaka wani rungume mutun ?
Ok nine ma nake miki iskanci ?
Uhmmmm fa shemah karkibari muyi haka dake ,tace muyima mana ,dan Allah ni malam kasake ni ,yayi murmushin karfin hali sannan yace zaki amince ta girma da arziki ne.
ko km na" jawo soyayyartawa " ta karfin tsiya ,.batare da na wahalar da kaina ba. muryarta na rawa ta sake cewa anki a amince da soyayyarka .
ko ana so dole ne ?
, dan Allah ni kasake ni , tun ban saka maka ihu ba ,ya zuba mata manyan idanunshi kawai yana kallonta. ahankali ,yasoma yawo da hannushi a sansar jikinta " gabadaya jikinta ya dauki kirma " abinda bai taba faruwa daita ba kennan" tunda take arayuwarta ,wai namiji ya rabi jikinta har takaita ga runguma ,dan takaici ma batasan sanda ta saki kara ba , kwalla ce cicciko a idanunta . Ya dan sausauta
Rungumar da , yayi mata ya zubawa fuskarta ido hawaye yaga yana silalowa daga idanunta ahankali ya sauke ajiyar zuciya,yasa yatsansa ya dangwalo hawayen dake bin fuskarta yana kallo Yace duk wannan kukan akan nace Ina sonki ne kike zubda hawayen ki?
,tayi shr taki cewa komai dan haushi , ji tayi kmr ta daura hannuta akanta ta sake , kurma ihu , ahankali ya sake maida ita jikinsa ya rungumeta yana shinshina wuyanta Yace please kidaina zubda hawayenki, Akan nace Ina sonki wlh duk ma wanda kike tunanin zaki aura nafi shi sonki , yasoma shafa bayanta da hannushi daya , daidai nan Sai ga big dady dake dawo daga masallaci take yaja birki , a tsorace yake binsu da kallo cike da mamaki da alajabi abinda yagani , meke shirin faruwa km yau acikin zuri'arsu ,fk yacigaba shafa bayanta tare da sake manneta da jikinsa yana rarrashita tayi hakuri ta amincewa aurensa .
dagowar nan da zai yi da niyar rabata da jikinsa karaf idanunsa suka sauka cikin na big dady dake tsaye ,gurin da Yar sandarsa yana kallonsu. "duk da duhu ne hakan bai hana ganeshi ba gabansa yaji yayi muguwar faduwa"take jikinsa ya dauki kirma duk da ya tsorata ,hakan bai sa ya saketa ba Sai dai yaji dadi Ganin da big dady din yayi musu .
yasan hakan zai sa a aura masa shemah batare da wani bata lokaci ba "tsabar frigice da yake ciki Ne yasa yakasa rabata da jikinsa gabadaya jikinsu rawa yake shemah da batasan wainar da'ake tuyawa ba .
sake lafewa tayi ajikinsa saboda irin rungumar dayayi mata ba wacce zata iya kwacewa bace" har big sanda big dady ya wuce su a gurin shemah batasa big dady yagansu ba , ahankali fk yasoma rabata daga jikinsa " har zuwa yanzu " hawaye bai daina bin fuskarta ba. Bai tsaya Ganin yanayin datake ciki ba hannuta ya damko yasoma tafiya.
ita kum tana biye dashi a baya , bbu wanda ya iya cewa dan'uwansa komai ,har yakawo part dinsu yaja ya tsaya , sannan ahankali Yace please... shemah kiyi hakuri dan girman Allah kibar kuka nan haka ba nufi na ta kuraki ba .
Ina matukar kaunarki" Ina miki son da ko ni kaina bansan lokacin dana fara ba Amman zan baki lokacin ki sake yi tunani ,zan dawo zuwa jibi yana gama fadar haka ya juya ,da kyar yake iya daga kafafunsa tsabar frigice da nauyin da suka masa zuciyarsa tamkar zata buga , dan fargaba haduwarsu da big dady "shi yasan ba makawa" tunda har big dady yagansu" aure kmr anyi an gama Amman kunya fa? Tana nan har abada .
,har ya iso part dinsu wanda kusan nan samari suke zaune wayanda basuyi aure gumi ke tsatsafo masa,
Itama shemah da kuka ta shiga part dinsu , mamanta dake zaune a parlour tace ke lafiyarki kike kuka ?
ko juyo batayi ba daki ta wuce ,ta fada kan gado ta cigaba da risgar kuka to yaya faruk yake nufi da yana sonta alhalin ita DEENi take mutuwar so ..... Dan haka tace wlh bazata taba aurensa ba ,tunawa datayi ba'a musu auren dole a family dinsu sai sun amince da juna yasa taji hankalinta ya kwanta Amman gabadaya jikinta yayi bala'in yi sanyi, haka ta kwanta da tunanin abinda fk yayi mata Ta dinga jinsa ajikinta tsagar jikinta suka mike ga kamshi turarensa daya fureera ,ko ta juya kamshinsa da hannushi ke yawo a koina na jikinta,.
Washegari ma kin fitowa tayi daga daki ,gabadaya
Yinin ranar a kwance tayi shi batare data fita ko parlour ba .
,fk bai dawo gurinta ba kmr yadda Yace mata kusan sati kennan tsakani ,shiyasa hankalinta ya kwanta Sosai tayi tunanin ko ya janye ne Tare da yiwa kansa fada ya hakura daita ,dan haka ta sake abinta.
kwatsam Sai gashi a wani daren lahadi byn ta gaisheshi, a dage ,yayi murmushi yace shifa yazo ne akan maganar su ,a fusace tace wata magana kennan?
i tough mun gama da wannan zance tunda nace ban sonka , Yace haka kika ce ,tace eh ko dole sai anyi soyyaya dakai?
,Yace ba dole kiyi soyayya dani ba ,Amman Ina son in tabbatar miki da aurena yazame miki dole ,yakamo hannuta ya sumbaci tafin hannuta sannan wuce ya yabar nan tare da damuwa ,
DEENi yasamu yaya mahamud yayi masa bayanin shi kuma ya samu big dady da zance tsohon yaji dadi Sosai jin sun hada kansu yace Shikenan bbu damuwa zai tuntubi yarinyan tukun yaji kafin yaasan abinyi .
Bayan wata daya
A wata lahadi da takasance ta karshen wata wanda sukeyi taronsu na family.
Holl din cike da yaya da jikoki tare da iyaye kowa kagani cike yake da tsantsar murna sabanin shemah da jikinta ke a tsanyaye sakamakon jin rade radin datayi na DEENi ne zai aure zeenat km Sai lokacin tasan dalilin dayasa zeenat ta mata wulakanci kwanaki
Byn wani lokacin gaishe gaishe ne yasoma biyu baya.
Takan shemah big dady yasoma, bai tsaya jin tabakinta ba yace akwai wanda taKe so ne ? Tace A'a yace shikennan yabawa faruk aurenta Take hawaye wanke mata fuska baita ba ko fk dake kokarin kiran DEENi wanda shi kadai bai iso ba , duk da hukunci big dady yayi masa dadi hakan bai hana jin gabansa faduwa ba daidai lokacin DEENI ya dau waya yaakayi ne mlm zaka dameni da kira fk yace angama dani fa sauran kai DEENI yace mezanzo yi km ? Fk yace kai fa dan rainin hankali ne zaka ce bakasan abinda akayi ba yau , uhmmmm tare da katse kiran Yama kashe wayar gabadaya dan bai son damuwa ,.
Kuka sosai shemah takeyi ta dinga datasanin cewa bata kowa gashi an kasaba mata auren fk nan Aka kira zeenat itama big dady yayi mata Mata tmbyrta ta Amince Sai sanda akazo neman su fk aka nemi DEENI akarasa kiran duniya akayiwa wayarsa taki shiga ,daga karshe big dady yace tunda yaji raayin zeenat din Ai aishikenan.
Nan dai aka saka ranar auren DEENi da fk tare da yanka sadaki, yaya mahamud ne yayi komai na DEENi ko sisin Kobo bata bai fita daga aljihun ogo deeni ba, ko mahaifin zeenat ma yayi murna sosai da jin DEENi ne zai aure diyarsa.
Anyaka sadakin zeenat tare da dukiyar aure naira duba dari biyar wanda duk a aljihun yaya mahamud suka fita .
Da kyar big dady yashawo kan Ummi dan tuburewa tayi ita fa sam bata yarda da wannan aure ba , big dady ne yace Ai tunda dai yara sun hada kansu km suna so junansu Ai Ina Gani magana takare fatanmu Allah ya zaunar dasu lfy .
Tace Ameen.
Lokacin da aka sanar da DEENi ansa ranar auren wata biyar , Yace wa yaya mahamud anya kuwa lokacin nan bai yi yawa ba kuwa ?
,Dan akwai aiki da zai kaini akwaibon Ina Ganin zaifi kyau a takaita lokacin koma ba dan haka ba ,anawa ra'ayin nafi son ayi komai nan da wata uku yaya mahamud yace Shikenan kabari dai zan samu Ummi da maganar .
Zaune take a cikin extra room dinsu wanda kusan yanzu can tafi zama tunda aka sa musu rana da yaya DEENi ta zabga uban tagumi tana mamakin hali irin na yaya DEENi yau kusan wata biyu Keenan dasamusu rana Amman ko sau daya bai taba kiranta da sunan zance ba haka nan ko cikin part din Ummi yashigo, bata ishe shi kallo ba takan ji tsoro da frigice sun shigeta a duk sanda taga yaya DEENi nuna rashin damuwarsa akanta ,a kasan ranta tace, anya kuwa banyi kuskure da wautaba wajen saurin amincewa aurensa ba domin fa zuwa yanzu tasoma sarewa anya kuwa yaya DEENi yana sonta ?
kullum miskilancinsa sake gaba yake har zuwa yanzu dabatason cikakken matsayin ta a gurinsa ba ,son auren yasoma fice mata arai domin ita kadai tasan fargaban da take cikin zuciyarta ga ,gorin da Ummi kebinta dashi kullun garin Allah ya waye , dan haka ta yanke hukunci samun yaya faruk dan ta inda aka hau tanan ake sauka .ta shirya taje har part dinsu tace daman tazo ne akan maganar mu da yaya DEENi idan fa abin nan bazai yiwu ba gara tun yanzu abarshi .
Fk ya gyara tsayuwa sannan yace wani abu ne ya faru ? Tace to yaya faruk a haka ne zamu fahimci juna in San abinda yake so shima yasan wanda banaso shi fa aure ba banza bane kmr yadda ya dauki komai tacigaba bai taba kirana ba km ko gida yashigo ban ishe shi kallo ba shi bashi da lokacin kowa sai na kansa fk yace kiyi hakuri bawai zangoyi bayansa ba aikine yayimasa yawa kiyi nasa uziri Amman kina ranshi zeenat ta tabe baki dan tasan karya ne yace wai tana ran yaya DEENi Ai abinda kake son baka sakaci dashi fk yacigaba komai yakusan zuwa karshe da zarar kin zama a gidansa nasan dole ya baki dukkan lokacin sa ,zeenat tayi shr ne kawai ba wai dan maganar tashigeta ba , fk yace tayi hakuri zai masa magana da sauri ,zeenat ta dago tace dan Allah yaya kar kace ni nayi maka maganar ya sake dubanta sosai yaga duk ta wani frigice yace karki damu ni nasan abinda zanyi .
Fk yakira deeni a waya Amman ba'a daga ba
Da misalin karfe goma na dare fk ya amsa kiran DEENi tare da yin sallama byn sun gaisa yace friend dazo inata kira baka daga ba DEENi ya runtse ritattun idanunshi tamkar na may jin bacci sannan yace wlh aiki ne yasha kaina lafiya dai ko ya fadi cikin kasala dan duk a gajiye yake fk yace lfy dama akan maganar yarinyar nan ne yakama mushirya muje zance gurinta , ,anhakali DEENi ya bude idanunshi jin abinda fk yace muryasa a sarke yace wacce yarinyar km?
Fk yace sai karinka yin kmr baka san da zance ba ,byn nasan tana ranka DEENi yace dan malam karkadameni go to the point dan bangane wacce yarinyar kake nufi ba fk yace Ai dole ka manta da ko wacce yarinya ce tunda kaga kasameta cikin kwanciyar hankali km Ummi ta amince ,tsaki yaja kana yace wai zeenat kake nufi ?
Yasake jan wani tsakin mtssss wani irin hira kum kmr muna kauye byn angama magana sai jiran lokacin fk yace kai mugun dan iska ne Ai duk da haka yakamata muje dan ita yarinyar tasan raayinka kai ma haka ku samu fahimtar juna DEENi ya katse shi da itace Keenan ta aiko ka fk yace ko daya ni dai naga dacewar haka DEENi yace to baza'aje ba ... Kar Allah yasa mu fahimci juna, ita tun tasowarta, bata san abinda nake so da wanda ba,fk yace idan ita tasan abinda kake so da wanda baka so kai kasan nata ?
DEENi ya sake jan tsaki hade da kamo lip's dinshi na kasa yana dan ciccizawa sannan ahankali yace to sarkin yakinta ni ba haka taarina da raayina yake ba Ina tunanin in har zanje zance gurin budurwar ,zanje ne dan tallar kaina in samu gindin zama to ni narigada na samu shigar ,bbu dalilin da zai sa na takurawa kaina me kadauki ni ,nafa san irin son da yarinyar nan take min ,kawai dai ni banda lokacin wannan shirme dakace km nasan ita ta aiko ka fitowa ne kawai bazakayi kafada ba .
Fk yaja tsaki shima yace kai ,dan Allah wani irin bahagon mutun ne?
To wlh ka canza wannan budadden halin naka, to ko waya ce ka tsiya mata ,DEENi yace shima din baza'a tsiya ba ,duk abinda zai faru ya faru ciki har da fasa aurena ,fk yace kai fa kafiyye kafiya ,da maida karamar magana tazama babba ,. yace sake cewa yanzu dai kayi hakuri dan girman Allah ka Sai mata ko karamar waya ce.
DEENi yace kasan Allah ko game bazan Sai mata ba , ballanantana waya , tunda har taiya zuwa ta sameka da maganar bana kiranta fk yace kadaina cewa tasameni ni kawai Gani nayi ya dace muje DEENi ya tabe baki tamkar fk din na ganinsa Shikenan kai ka sani ni km kar ka sake damuna da maganar wata yarinya ya kashe wayarsa batare da ya tsaya jin abinda fk zai ce ba .
Wasa wasa lokacin bikin ya dinga karatowa da kwanaki ya wattani har zuwa yanzu dayayi sauran wata cif cif ayi daurin aure to Ganin kurewar lokaci yasa DEENi yasamu Ummi da maganar shifa baya son zamansa cikin estate din taje Ummi tayi kicin kicin da ranta sannan ta dago tana dubansa tace bangane abinda kake nufi ?
Sai da ya sake maimaita mata tukun Ummi tace sam ita bata yarda ba salon yaje yana dinga cin amanar Yar marainiyar Allah ga babbin gurin bid dady yasa an Gina musu shida sauran enuwansa shine kai dan iyayi zaka ce bazaka zauna ba ,to wlh kaji na rantse anan zaku zauna Sai naga yana yin zaman naku cikin yin kasa da murya yace Shikenan first lov na hakura duk abinda kika ce shi za'a yi tace da dai yafiye ma a yi mutun Sai girman tsiya da iyayi yace to kiyi hakuri .
Zeenat dake sauransu ta lumshe idanunta jin Ummi bata amince ba dan tana matukar jin tsoro zaman daga ita Sai shi ahankali cikin sanyi jiki ya mike idanunshi suka sauka akan inda zeenat ke kwance suka hada ido da sauri ta gaidashi hade da dauke idanunta ,bai sake kallonta ba bare ya amsa gaisuwar ta .
Shirye shiryen biki ya tashi gadan gadan enmata duka a tare suke shirinsu dan yanzu zeenat ta saki da shemah sun koma kmr da ganin da tayi wanda ma take haukar akansa bai san da zamanta ba wata safiya suka shirya zuwa siyayar su irinta amare mutun biyu ne abayanta mota Maryam da shemah yayinda zeenat ke gaba kai tsaye kasuwar Lagos suka nufa sukace derive yayi parking a idimota su kum suka shiga cikin market din
Derive yaja ya tsaya suna fitowa da yaya kamil suka soma cin karo tun shigowar motar dayaga hango zeenat zaune ya zubawa motar ido har sanda ta fito ahankali suka jiro suna hira Amman banda zeenat dataji gabanta ya yanke ya fadi dan tun lokacin da aka mata rana ,rabonta dashi dai dai sun kusan geftashi yakira sunnanta zeenat..... tacigaba da tafiyarta dan batason abinda zai km hada ta dashi cikin sassarfa ya biyo bayanta yasha gabanta cak taja ta tsaya suna kallon junansu,yayinda su Maryam suka cigaba da tafiyarsu suna tsaye batare da dukkansu suyi yunkurin yin magana ba kamil ya gyara tsayuwa ya tura hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa ya kafeta da idanunshi ta sunkuyar da kanta kasa sannan tace lfy yaya ka tsayar dani muryasa a dashi yace lfyr ce takowa haka yanzu zeenat kin kyauta kennan ki zabi wani kibarni byn duk lokacin dana dauka Ina fama da soyayyarki ,a she kinsa bakya sona kibarni inata faman hauka akanki tace Allah yaya ba haka bane Amman kayi hakuri dan Allah, ya sake gyara tsayursa , yayinda idanunshi ke kanta har yanzu yace iya hakuri ne kawai zai wadatar da zuciyar da tayi sama shekara biyu tana mata da miki so.... yace Shikenan bbu komai Nagode Kwarai da abinda kika saka min tace ka dauka haka Allah yaso ni din ba matar ka bace yayi murmushin karfin hali sannan yace haka ne fa al'amarin ubgj Amman agaskiya DEENi ya cuceni ,tace kabar cewa ,tayi ta dago suna kallon juna fuskarta dauke da murmushi ta bude baki kennan Sai ga motar DEENI ta kuno kai cikin compound din km shi suke facin Ai take maganar ta ta tsaya sakamakon DEENi data Gani zaune a mota yana kallonsu duk kasancewar akwai dan duhun magariba hakan ba zai sa takasa gane bscin ransa ba , gabanta ya yanke ya fadi , ,shima kamil din shr yayi bai sake yin magana va kusan minti goma yayi yana kallonsu koda bata ga fuskasa sosai ba tasan a daure take ,har sanda DEENi ya fito yayi matarsa key idanunshi na kansu ,cikin tsoro da frigice zeenat tace ni zanshiga ciki ,kamil yace Shikenan Allah yabaki zaman lfy ta gefensu yazo yazo ya gifta hade da jan tsaki sannan ya wuce . a filli ta furta wayo Allahna nashi uku kamil ya sake yin murmushi dole sannan yace da'aka me,da kika shiga uku, nifa Banga abinda ya birgeki a DEENi ba,har da kika iya zabarsa , kalli fa yadda jikinki ke rawa saboda Allah tamkar kinga wani malaika tsaki taja hade da zabga masa harara dan Allah kabarni naji da damuwa Ai duk kai kaja min matsala Ina zaman zamana da yanzu Ina cikin gida
0 Comments