ALAKA 15-16 BEST HAUSA NOVELS

 ALAKA 

17-18


   *************

Bayan sun dawo  wani abokinsu Yaya Sultan mai suna Abakar da yazo daga Abuja, Yace   "gaskia mutumina ba k'aramin dace kayi da mace mai kyau ba ga hankali." 


   Yaya Aliyu yace   "ai ka bari kowa na yabonta wurin hankali da natsuwa."


   Lumshe idonshi yayi dake kallon Yaya Aliyu tunda ya fara magana, Dogon ajiyar zuciya ya sauke, dan yasan Yaya Aliyu zai iya kwafsa mashi a gaban friends nasu. 


  Murmushi Yaya Aliyu ya saki.!


Hidima ake iya hidima, wanda yau aka had'a gagarumin walimar da ya tara manyan malamai da suka bada lecture akan zamantakewar aure.


  Gaba d'aya wad'anda ke wurin hankalinsu yana wurin malamai, yanda yake shigarsu yasa duk jikinsu yayi sanyi. 


   Haka akayi aka gama bayan an raba duk abinda ya dace a wurin. 


   Ba wata k'arya suka zauna suka yi a hidiman bikin ba, sunyishi cikin girma ba tare da almubazzaranci ba. 


    *************

Yau take asabar mai d'inbin daraja a wurin   Lubabatu da angonta Yaya Sultan. 


   Inda wurin ba k'aramin tara manyan mutane yayi ba, Tare da governor da muk'arrabanshi, da sarki. 


   A take aka d'aura auran Sultan da Lubabatu kan sadaki dubu hamsin. 


  Su Sultan baki yak'i rufuwa. 

Sai gaisawa yake da mutane ana ta hotuna. 

  Daga nan kuma wurin reception suka wuce. 


   Lubabatu dake zaune abokan wasa suka tasata irinsu ummin Aunty Jamila sai tononta suke. 


   Tace   "ai da yake wanda nake so zan aura, kunga ba shawarar wanda zan d'auka."


  Yaya fatima tace  "duk wannan shirman de ki denashi kiyi hankali dan ba kowane namiji zai d'auki halin nan naki ba."


   Ta bita da kallo...." to naji na d'auka."


   Dare nayi aka fara shirin d'aukan amarya, inda duk ta gama jik'a fuskanta da hawaye. Ba k'aramin nasiha suka mata ba. 

Sai kuka take, lokacin da za a fita da ita, haka ta rink'a ihu tana kiran   Ammi da Mommy dan shed'ana harda  'yan gidan take kira. 


  Da k'yar aka shiga da ita mota sai kuka take, har suka isa unguwar da za a kaita   malali. 


  Da tuni dama sun mata danki. 


Ba k'aramin kyau gidan yayi ba, nan su Amina suka kwana. 

    Washegari da wuri k'awayenta na nesa suka tafi. 


  Bayan an gama gyara mata ko ina da yamma kowa ya watse aka bar amarya da sai kuka take. 


   *********

Sai dare ango da abokanshi suka shigo, 

Da har yanzu ta k'udundune kuka take. 

K'arasowa kusa da ita yayi... "haba Lubna me ya saki kuka haka?" 


  Kwantawa tayi a jikinshi taci gaba da kukan. 


   Abakar yace   "kai wannan amarya taka da shagwa'ba take. 


   Nan suka zauna suka gama basu shawarwari da nasihar da ba a rasa ba sannan suka tafi. 


   Bayan ya rakasu ya dawo d'akin ya taddata sai shashshek'ar kuka take. 

  

  Jawota yayi jikinshi..."haba my lubna kamar ba da  yaya Sultan d'inki kike tare ba,Kin san tuntuni bana son kukan nan naki fa."


  Share hawayenta ta fara yi, Yace   "yauwa tawan, tashi mu shiga ciki ki rage kayan jikinki kiyi wanka ko zaki ji dad'in jikinki."


   Ba musu ta mik'e ta bishi ciki, da kanshi ya had'a mata ruwan wankan, Yace "idan kin gama kiyo alwala daga nan."

ta d'aga mashi kai ta mik'e ta shiga. 

Shi kuma ya wuce d'akinshi yayi wanka tare da alwala yasa jallabiya ya dawo d'akin duk bata fito ba. 

   Bayan ta gama ta fito sanye da dogon hijabi, Murmushi yayi yace   "yau kuma ni ake 'boye ma jiki? 

Yaya sultan d'inki ne fa." 


   Duk'ar da kanta k'asa tayi. 

Bayan ta gama shiryawa. 


  Ya dubeta cikin Murya k'asa-k'asa... "yanzu ki tashi muyi sallah mu gode ma Allah da ya mallaka mana juna a matsayin ma' aurata." 


  Mik'ewa tayi suka yi sallah, ya dad'e yana koro masu addu'o'i. 


  Bayan Sun gama ya mik'e da kanshi ya d'auko masu plate da cups ya juye masu kazar da ya shigo dashi, ya zuba masu yogourt d'in da yazo dashi. 


  Duk tak'i taci, da k'yar ya lalla'bata ya dinga bata da kanshi. 


     Bayan sun gama ciye ciyensu ya fidda komai ya gyara wurin tsaf. 

Ya dawo wurinta da har ta d'are gado ta kwanta. 


   Ya kashe fitilan d'akin shima ya kwanta, 

Jawota yayi jikinshi daga nan zance ya canza. 

    Cikin kuka ta fara magana..."Yaya  Sultan kaifa Yayana ne."

Tana yi tana tureshi. 


  Ranar kam Mommy Daddy Abba Ammi, duk sunsha kira wurin Lubabatu. 


    **********

Washegari kuwa ko ido ta kasa had'awa dashi, sai de yana shan shagwa'ba a wurinta. 


   Shima ya dage sai nan-nan yake da ita, ita kuma ta samu abinda take so. 


   Sai yamma ya samu ya fita, shima dan bak'in da keta zuwa yasa ya fita. 


   Sai gasu Yaya fatima gaba d'ayansu sun shigo, da gudu ta taresu suka shiga ciki. 


   Affan sai da biyosu. 


   Ta kallesu tana murmushi na alamun akwai magana a bakinta... "in fad'a maku sai da akayi, ba k'aramin wahala naci ba, wallahi Aunty Fatu ta cuceni."           

      "Magungunan da tasa nayi tasha naci wuya, kuma zaku ji yanda naji."


  Yaya fatima sakin bakinta tayi tace  "ke wa ya fad'a maki ana fad'in abinda ya faru tsakanin miji da mata? To Ki rink'a kama bakinki." 


   Zum'buro baki tayi.! 

Zaynab tace   "ni bani labari." 


  Yaya Fatima tace   "tunda abin haka ne ku tashi mu tafi kawai." 


  Yaya Salma tace  "baku da hankali wallahi.!" 

  Gaba d'aya suka kwashe da daria. 

    Lubabatu ta mik'e ta dawo rik'e da plate d'in kazar jiya da basu cinye ba, Ta d'umama masu. 


  Mik'a masu tayi... "ga kazar siyan baki kuci bari na kawo maku d'an juice ko." 


  Ta fita ta dawo da juice da cups a hannunta ta dire masu. 


  Tace kunga ko ci ba muyi ba sosai saboda ina fargabar yanda zata kasance tsakanina dashi."


  Ta d'auka ta fara ci, tana maida jawabi. 


   Yaya Fatima tace   "wallahi idan shirman nan zaki ci gaba dayi, kina damunshi da surutu ya rink'a guduwa yana barinki ke d'aya." 


  Lubabatu tayi daria... "kema kin jiki.! 

Ai ba zai fita ya k'yaleni ba, kut! Aiko ya fita ya k'yaleni binshi zanyi." 


  Dariya ma ta basu. 

Yaya Salma tace   "gaskia har yanzu da sauranki." 


  Ba sune suka bar gidan ba sai bayan isha'i sannan Bala yazo ya d'aukesu. 


  Affan ya dage shi wurin Lubabatu zai zauna, 

Yaya Fatima ta tasashi suka tafi. 


   Da suka koma Daddy fad'a yayi ta masu... "daga kaita jiya zaku fara mata zarya haka ake yi?"

  Khadija tace  "wasu kayanta muka kai mata." 


   "ke Fatima da Salma kuma ku fito da naku mazajan kuna jina ko?" 


   A tare suka amsa da.... "to Daddy." 


  Ya Kalli Zaynab da khadija yace  "kuma harda ku duk mu aurar daku mu huta gaba d'aya."


     ***********

Watanni sunja! Lubabatu an dage sai zaman aure ake, duk da shirmanta ta dage biyayya iya biyayya take ma Yaya Sultan, bata ta'ba yarda tayi  wani abu da tasan zai 'bata mashi rai.


   Ba k'aramin jin dad'in haka yake ba. 


  Daga ita sai Almajirinta wanda take d'an aike idan tana buk'atar wani abu. 


  Daga k'arshe kuma da Yaya Sultan yaga ta cika biye mashi tana fira dashi, yasa ya sallameshi. 


     **********

   Kwance take jikinshi tana wasa da hannunshi, kwanto da kanshi yayi kanta.... "anya kuwa akwai namiji da ya fini sa'ar samun mace kuwa?" 


   "Lubabatu baki ta'ba 'bata min rai ba tunda mukayi aure." 


  Murmushi taci gaba da yi. 


   "A gaskia ina matuk'ar alfahari dake, Kinba  marad'a kunya ina jin dad'in haka  kici gaba kada a ta'ba jinmu a rana." 


   Murmushi tayi tare da juya idanunta... "nima ba k'aramin jin dad'i nayi ba da ka kasance miji a gareni mai hak'uri da iya tattalin mace." 


  Yace  "Allah yasa hakan to ya ci gaba da kasancewa a tsakaninmu har k'arshen rayuwarmu."


"Amin ya Allah."


    Fitowa tayi daga d'aki ta isa wurin Yaya Sultan dake kwance kan kujera yana d'an kallo,  cikin shagwa'ba tace "Yaya Sultan gashi ka koran min Almajiri kuma ina so inyi aike za a siyo min kayan miya."


   Mikewa yayi ya zauna..."meyasa kika bari har wani abu ya k'are ba tare da kin fad'a min ba.?"


    "Bana so kina barin wani abu ya yanke."


Tace "insha Allahu zan kiyaye."


   "yanzu de tunda ka kori almajiri sai ka tashi inyi maka lissafin abinda zaka siyo." 


  Mik'ewa tsaye yayi yace  "ina sauraranki.! 


Ta mik'a mashi dubu d'aya dake hannunta. 


"Gashi ka siyo min tumatir da attarugu sai ku'bewa, 

Tuwo nake son ci yau." 

  Ya amsa..."to ranki ya dad'e an gama."


  Ya fita can sai gashi ya dawo ya dire mata ledar a gabanta..."Gashi Hajiyata na dawo."


  Bud'ewa tayi ta duba... "ya naga kayan da yawa.?" 


  Yace  "eh saboda ba zan iya siyo kad'an ba." 


  "Taf! Aiko sai ka biyani kud'ina tunda ba duka nace ka kashe min ba."


   Dubanta yayi yan daria." ya za ayi ki bani sak'on da ban wuce na d'ari biyu ba gashi ina kallon sauran canji a hannuna."


  Duka ta fara kai mashi cikin shagwa'ba  take fad'in   "ni wallahi sai ka biyani kud'ina."


   Cikin daria yace "naji zan biyaki amma sai na dawo zan baki." 


  Da haka ya lalla'bata ta hak'ura. 


    ***********

Yaya Aliyu ya samu mata suma Yaya Fatima da Yaya Salma sun samu miji an sa masu rana. 


  Ga Lubabatu har sun fara zuwa school, sosai take dagewa tana maida hankali wurin karatunta. 


     Sa ranarsu ba wani lokaci aka d'auka ba, suka fara hidiman biki, lokacin Lubabatu nada ciki wata uku. 


   Yaya Sultan duk inda tasa k'afa nan yake sawa, dan be son ya barta ita kad'ai ba tare da suna tare ba. 


   Affan ne ya shigo yace  "Aunty Lubabatu kizo Yaya Sultan na kira."


     Da sauri lubabatu ta mik'e


      Ummi da suke zaune ta dubi Lubabatu tace  "kai wannan nanik'e ma juna da kuke ko magnet sai haka."


  Lubabatu tace   "kin jiki ya son ranki."


"Ummi tace  "sai ana cikin fira mai dad'i duk yabi ya hanaki sakewa."

    

     Zaynab tace ni ban ta'ba ganin haka ba ka hana mutum sak'at har a gidansu."


   Lubabatu tace  "a hakan nake son mijina."


"duk kunbi kun addabeni da maganar zamana da mijina, iya rik'eshi da nayi yasa baya so inyi nesa dashi dan haka ku dena 'bata bakinku koya ya kamata ku tsaya kuyi." 

   Ta fice ta barsu nan.

    

        *********

Ansha hidimar biki lafia kowa an kaishi gidanshi, Yaya Aliyu ma an kawo mashi matarshi.

     Cikin Lubabatu ya shiga wata tara haihuwa yau ko gobe. 


   Kwance suke an fara kiran sallan asuba, ta farka Yaya Sultan na ta barci, ta fara wayyo Allah cikina, ta fara bubbugashi tana fad'in cikina. 


  Da sauri ya mik'e yana fad'in "sannu tashi muje asibiti." 


  Ya suri key d'in mota, Ganin yanda ya rud'e yasa ta kwashe da daria. 


   Binta yayi da kallo,tace   "wasa nake maka." taci gaba da daria. 


  Hancinta yaja... "keko? kin kyauta." 


   Tace   "kaga yanda ka rud'e kuwa? To da kake cewa mu tafi asibiti a haka zaka tafi?" 

  Taci gaba da daria. 


   Yace   "sai kace ban damu dake ba da har zan tsaya gane abinda yake yake jikina, Ai a haka zan tafi." 


  Amma fa kin tsoratani da yawa ranar da labour d'in zaizo yana nan zuwa,sai de ina rok'on Allah ya kawo maki mai sauki. "


  Amsawa tayi da Amin ya rabbi." 


  Toilet ya fad'a yayi alwala ya fito yace tashi ki shiga kiyi."


  Jallabiya ya zura ya wuce masallaci. 


   ************

Basu da buri daya wuce suga Lubabatu ta haihu lafia. 


    Haihuwa lokaci gareta, Lubabatu ciwon baya da ciki ta fara ji, ta kira Yaya Sultan da baya gida, yana d'auka tace   "bafa lafia naga kamar haihuwa ne." 

 

  Ba tare da yace komai ba, Ya datse wayar ya shiga mota ya tada. 


 Be dad'e ba ya iso gida, ya taddata zaune kan kujera Taci kwalliya ga takalmi tasa. 


  Yanayin yanda ya shigo cikin tashin hankali, tsayawa kallonta yayi... "kin fara ko?" 


   Tace   "Allah Yaya da gaske nake, kai nake jira duk kayan haihuwan ma na kan gado na shiryasu."


  Duk kallon mamaki yake mata, yasan ba haka ake nak'uda ba. 


  Shiga ciki yayi ya d'auko kayan suka fita, duk da kanta ta fita ta shiga mota yaja suka tafi. 


   Suna isa, Bayan sun gaisa tace   "haihuwa nazo."


  Da mamaki suka kalleta.! 

Wata nurse tace "haihuwa kuma? Amma kika ci uban kwalliya haka kamar zaki gidan biki?" 


   Suna dubata suka tabbatar da haihuwa ce,

Sai de da d'an sauran lokaci, ko zaku koma gida anjima ku dawo? 

Lubabatu tace   "ba inda zani ina nan."

Doctor d'in yace  "shikenan." 


  Nan Yaya Sultan ya kira Mommy ya fad'a mata. 

Ba a jima ba sai gasu sun shigo asibitin. 


  Yanda suka ganta suma ya basu mamaki.! 


  Ammi dubanta tayi cikin mamaki... "anya kuwa Lubabatu haihuwa ce? Ko dan kiba mutane wahala?" 


  Lubabatu tace   "wai meyasa kowa yake mamaki, gashi ku tambayeshi an tabbatar da haihuwa ce."


  Mommy tace  "nan wahala zaki ta sha tunda Haihuwar bata zo gadan-gadan ba."


  Lubabatu tace  "gara de ina kusa da asibiti ba sai na fita hayyacina ba." 


  Mommy tace   "bama a fatan ki fita hayyacinki." 


  Sun dage suna ta zaman jiran haihuwa. 


  Ya motsa mata ya tsaya, firanta take, sai ya motsa mata ciwon kuma tayi shiru. 


  Can da ya murd'a mata, sai gata ta fasa ihu, ta fara masu kuka, Ammi tace   "wa y gaya maki yarinya." 


 Mommy tace kiyi hak'uri kina addu'a."


  Nan suka fita waje suka barta da nurses. 

  Azaba ya isheta, duk wanda ta cafki hannunshi da k'yar yake k'wacewa. 


  Can Allah ya temaketa ta sunkuto d'iyarta mace. 


  Wani dogon numfashi taja, tayi lamo sai maida numfashi take. 


   Bayan an gama gyarasu aka mik'a masu baby suka shiga sai sannu suke mata. 


   Mommy ta dubi Sultan..."idan ka tashi gida zaka wuce damu can zata koma."


  Yace   "Mommy ai bamuyi magana daku ba zata koma."


 "Mommy tace  "Gashi na fad'a maka yanzu."


  Ba yanda zaiyi suna sallamanta dole gida ya wuce dasu, gidan Mommy aka wuce da ita,dan Ammi nata idone. 


     ***********

Gida sai cika yake da 'yan barka, gashi a lokacin khadija Ummin aunty Jamila da zaynab suma an kusa bikinsu. 


   Gaba d'aya Sultan shima gidan ya dawo ya tare. 

  Ba fad'an da besha ba wurin Mommy da surutu. 



  Ranar suna na zagayowa yarinya Taci  suna Nana Aysha. 


   Sultan kullum cikin lissafi yake, ya samu Mommy da maganar yana so Lubabatu ta koma gida. 


  Mommy tace   "ba yanzu ba sai anyi bikin su Zaynab."


  Ranshi ya   'bata san kace wanda aka aiko ma da sak'on mutuwa..."haba Mommy yau fa satinta d'aya da gama wanka fa, biki kuma akwai sauran sati biyu a kai."


  Mommy tace "ba zata koma yanzu ba." 


  Yace   "Mommy dan Allah ki bani ita mu tafi ai ta zaunu duk wani warkewa da za tayi ai tayi."


 "ka isheni idan naga dama arba'in biyu za tayi, dan haka tashi ka fita ka bani wuri."


  Haka ya mik'e ya fita jiki a sanyaye. 

Ya kira Lubabatu ba a dad'e ba ta d'aga. 


 "kinga Mommy ta hanani ke ko? Ki nuna masu kema kina son komawa gidanki."


  Ta waro idanunta kamar yana kallonta...."kai   Yaya Sultan so kake suce bani da kunya,tunda sunce sai anyi bikin su Zaynab kayi hak'uri da hakan, yanda kwanaki ke gudu zaka har yazo."



   "kema haka zaki ce ko?" 

Ya katse wayan, tabi wayan da kallo, Tare da fad'in to ya kake so inyi daka?


   Tun daga ranar ya dena kiranta, idan ta kira yak'i d'auka, idan ta gaji ta mashi text. 


  Fushi sosai ya d'auka dasu, 


  Ammi da mommy zaune, Mommy tace   "kinga d'anki fushi yake damu har yanzu."


  Ammi tace "to kin rik'e mashi mata kin hanashi." 


  Mommy tace   "aiko ya gaji ya sauko, dan sai anyi biki zata koma yanzu ba gashi saura sati d'aya ba."


  Ammi tace hakane. 


   Lubabatu da ta gaji itama k'yaleshi tayi Taci gaba da hidimanta. 


  Gashi har sun fara shirye - shiryen biki. 


  Sai shagali ake. Lubabatu ta saki jiki, Ga Nana Aysha tayi k'iba abinta. 


   Haka suka sha hidiman biki lafia aka kai kowacce gidanta duk a cikin kaduna. 


   Mommy suka fara shirin maida Lubabatu gida. 


  Sai a lokacin Sultan ya sauko, ita kuma Lubabatu lokacin take nata fushin. 


  Da kanshi yazo y d'aukesu suka wuce gida da 'yan rakiya.  


  Bayan sun tafi sai faman nan nan yake da ita, ta shareshi, jawota yayi... "haba my one and Only.! Nine fa yayanki kike fushi dani."


  Tace  "kaima ba fushi kayi dani ba."

Ta fara kuka, ya fara goge mata hawaye, yana fad'in kiyi hak'uri ba zan k'ara ba, Ya rik'e kunnanshi."


  Amma idan baki hak'ura ba ki d'auki duk hukuncin da ya dace a kaina."


  Ta kwanto jikinshi...."na hak'ura yayana." 


  Rungumeta a jikinsa yayi tayi lamo. 



     *********

Rayuwa Taci gaba da tafiya, Zamansu suke cikin aminci da soyayyar juna. 


  Yaya Sultan haka yake jansu kamar ya had'iyesu. 


  Gashi har ta gama had'a diploma d'inta, da k'yar Yaya Sultan y lall'bata ta d'aura H.N.D

   Ya sai mata mota dan taji dad'in karatun. 

   Ga Nana Aysha ta girma tayi wayau abinta, tafi zama wurin su Ammi, sai ta tashi school ta wuce ta d'aukota. 


    Su Yaya fatima suma duk Allah ya albarkacesu da samun   'ya'ya. 


      **********

Bayan shekara hud'u da haihuwan Nana Aysha lokacin lokacin haifi 'yan biyu mace da namiji. 


   Abubakar sadik sai Maryam. 


   Gida ya zama gidan jin dad'i da annashuwa. 

Lubabatu an zama babbar mace. 


   Ga karatu ta gama, ta gama service d'inta. Yaranta gasu gwanin sha'awa. 


   Lubabatu na alfahari da Yayanta mijinta.


  Da Suke zama na mutunci da amana. 


   Ji suke kamar su had'iye junansu saboda k'auna. Su Lubabatu anyi hankali. 


  Ba abinda baya masu na jin dad'i. 

Gida mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali da 'ya'yansu. 


    Hankalin kowa a kwance, Zaune suke ta dubi Sultan...."ina rok'on Allah ya barni tare da kai har k'arshen rayuwata."


  Yace nima haka uwar 'ya' yana."



     THAMAT BI HAMDULLAH.! 

GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA ALA DA YA BANI IKON GAMA LITTAFIN ALAK'A LAFIYA KUSKURAN DA NAYI A CIKI ALLAH YA YAFE MIN. 


   MASOYA ALAK'A INA MAKU FATAN ALKHAIRI ALLAH YA BARMU TARE AMEEN.


Post a Comment

0 Comments