ALAKA
15-16
*************
Tun daga ranar Lubabatu ta rage shige ma yaya sultan, duk ta kasa sakin jiki dashi, kunyarshi take ji.
Tun yana mata maganar soyayya, tana kasa maida mashi, daga k'arshe, sai gashi ta saba.
Gidan ba wanda tayi gigin ta fad'a mashi, tana soyayya da yaya sultan.
Daga ita sai shi suka sani.
Soyayya ce sosai ta k'ullu a tsakaninsu.
Ji suke yi kamar su had'iye junansu saboda son da suke ma juna.
Lubabatu har mamaki take, idan taga yaya sultan ya sake, yana fad'a mata sirrin zuciyarshi.
************
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, an fara registration na jamb.
Abba ya kira Lubabatu, Yace "ke ya kike ciki?"
An fara registration na jamb, ya kamata kizo kiyi ko."
Ba kunya, tace "Abba ni bani da buri akan karatu, aure nake so nayi."
Abba tsayawa kallonta yayi, Yace "Lubabatu ni kike ce ma baki da burin karatu aure kike so."
Tace "Abba shi nafi so."
Abba ya kai mata duka, dede lokacin yaya sultan ya shigo.
Da sauri Lubabatu ta isa wurinshi.
Ammi tace "au ashe kina tsoro?"
Lubabatu ta fara kuka, tace "ni wallahi da gaske nake, aure zanyi."
Yaya sultan kanshi kallonta yayi, Ammi tace "karatu zakiyi."
Ko su Fatima basuyi ba, bare ke.
Lubabatu ta zum'buro baki, tace kowa fa da ra'ayinshi."
Yaya sultan jin duk abinda ya faru.
Yace "Abba ku k'yaleta, bari muje inyi magana da ita."
Suka fita tare.
Bayan sun shiga d'aki, ya zaunar fa ita, Yace "haba Lubabatu meyasa zaki fad'a ma su Abba haka?"
Tace "yaya sultan shine fa a raina, sai in kasa fad'a masu, aure nake so nayi."
Yace "to inde maganar aure ne, ai zakiyi."
"amma inaso ki yarda kiyi jamb din, dani fa kike so ki zauna."
Kuma inaso kiyi karatu.
Dan haka inaso ki yarda kiyi jamb din."
Tace to shikenan zanyi, amma bani so auran ya d'au lokaci."
Yace "kai Lubabatu, halinki sai ke,to naji."
Da gaka ya lallabata ta yarda.
*************
Gaban su Ammi ta yarda za tayi karatun, Amma ita aure za tayi ta gama karstunta a gidan mijinta.
Ammi tace "wai kina ta maganar aure, aure.!
Ina kika samu mijin?"
Kuma ma duka shekarunki nawa, Ina kike da hankalin da zaki je kiyi zaman aure."
Lubabatu tace "ai da nayi auran, hankali zaizo,
Ni wallahi bana son karatun nan, kawai de dan yaya sultan yace yana so ne, da ba zanyi ba."
Ammi tace "wannan ai ke ya shafa."
Karatu de in kinyi k'aruwar kanki ne, ba ta wani ba."
Lubabatu tace "yauwa Ammi tunda k'aruwa tace, dan Allah ku k'yaleni da maganar auran nan."
Ammi de da taga shirman na Lubabatu ya mata yawa.
Tace "tashi ki fita ki bani wuri."
Ta mik'e ta bita da gudu, ta fice gidan,
Tayi wurin mommy, nan taci karo da daddy,
Yace "Lubabatu ya akayi ne?"
Harda guntun hawauenta, suka shige ciki tare, Yace zauna ki fad'a min me ya faru?"
Tace "Daddy aure nake so nayi, Su kuma su Ammi wai sai de nayi karatu."
kuma naga ai aure shine gaba da karatu, tunda shi na duniya ne, Ba tare zamu lahira dashi ba."
Daddy yace "wannan gaskia ne, mommy tace "in banda abinki, duka nawa kike Lubabatu?!
Daddy yace gasu fatima da salma, duk ba karatunsu suke ba."
yanzu ga zainab nan da khadija duk sunyi registration na jamb kefa?"
Tace "banyi ba."
Yace inde aure ne za a maki, amma ki fara karatun ko."
Da haka shima ya lalla'bata.
************
An samu Yaya sultan yasa sunje tare.
Saide fa ita maganarta, aure za tayi.
Yaya sultan da suke tare, Yace Lubabatu meyasa kike maganar aure aure."
Tace "yaya Sultan ba dole nayi magana ba, kana ganin an fara cewa ku fiddo da matan aure, tunda kun fara aiki."
To ba dole in matsa in fad'a masu aure nake so ba,Tun kafin wata ta k'wace min kai."
Dariya yayi, Yace dan wannan kada ki damu, ba wanda zai k'wace maki ni. "
Tace "nafa san halin matan zamanin nan."
Yace ki kwantar da hankalinki, banda macen aure sai ke, baki ga ban ta'ba yin budurwa ba."
Tayi Dariya.
Sai de fa har yanzu a tsorace take.
K'ara tada maganar tayi, Abba daddy yaje ya samu, suka zauna, Abba yace "maganar gaskia na fara tsorata da maganar Lubabatu, tana nan kan bakanta na ita aure take so, kana ganin har dukanta nayi akan haka, amma maganarta d'aya aure take so."
"ban sani ba, ko ta samu wani ne, da yake hure mata kunne a waje."
Daddy yace "gaskia kam, ya kamata, mu zauna da ita, ayi magana da ita, tunda har ta nuna auran take so, gara a mata, da sharad'in za tayi karatu."
Abba yace kana ganin fa ko su fatima bamu bari su tsaya da samari.
Tunda suma nawa suke, yanzu fa take da shekara sha bakwai."
Daddy yace "wannan ba abin damuwa bane."
Inde yaron da take so, na gari ne, sai a aurar da ita d'in, inde yaro ya cire kunya, Yace aure yake so, to gara a mashi, inde har an yaba da halin wanda take so."
Abba yace to shikenan, Allah ya za'ba mafi alkhairi. "
Daddy yace " to Amin."
Idan Allah ya kaimu gobe, ma zauna da ita muji ko."
Abba yace to Allah ya kaimu, da haka ya mik'e ya wuce gida.
******************
Washegari kuwa, Kamar yanda Daddy yace za a kira Lubabatu suji ta bakinta,
Haka kuwa akayi.
Yasa an kirata, tazo ta duk'a, Bayan ta gaidasu.
Daddy yace "Lubabatu, naji wani zance ne, Na kina son aure, hakane?"
Ta duk'ar da kanta k'asa tana wasa da hannunta.
Yace "ke nake saurare, ki saki jikinki, kiyi min bayani."
Tace "eh hakane Daddy."
Yace "A ina kika samu mijin bamu sani ba?"
Tace "dama... Sai kuma tayi shiru.
Daddy ya k'ara gyara zamanshi, Yace "kada ki ji komai, ki fad'a min ke kawai nake saurare."
Tace "yaya sultan nake so.
Gaba d'aya suka kalli juna.
Daddy yace "dama kun dad'e kuna soyayya dashi ne, mu bamu sani ba?"
Ta d'aga mashi kanta.
Daddy yace "to ashe me hure mata kunnan a cikin gidan nan yake."
Ya d'auki waya ya kira Sultan, yana d'auka.
Yace "kazo yanzu ina buk'atan ganinka."
Ba a jima ba, sai gashi sun shigo shi da Yaya Aliyu.
Suka samu wuri suka zauna.
Daddy ya kalli Sultan yace dama kaine kake hure ma Lubabatu kunne, kana so ka hanata karatu ko?"
Yaya Sultan yace "ni kuma Daddy?"
"Ni ban hanata tayi karatu ba."
Daddy yace "ka hanata mana, tunda gashi har kasa mata kwad'ayin aure."
Yaya Sultan zaro ido waje yayi.!
Sannan ya kai dubanshi wurin Lubabatu da kanta yake a k'asa.
Daddy yace "yaushe kuka fara maganar aure ba tare da mun sani ba?"
Yaya Sultan yace "mun d'an dad'e."
Daddy yace "yayi kyau, sai de gashi muna so Lubabatu tayi karatu.
Zaka ita barinta tayi?"
Tunda ta nuna auran take so."
Yaya Sultan yace "zan barta tayi."
Daddy yace "to Alhamdulillah.!
Ya Kalli Abba yace "to kaji komai, ka yarda suyi auran ko kuwa?
Tunda gashi de suna son junansu."
Abba yace "na yarda."
Daddy yace "to yayi kyau."
Kuma de kunji ko? Yakai dubansu wurinsu Ammi.
Gaba d'aya suka ce Allah ya sanya alkhairi."
Daddy yace "to zamu duba, muga yanda za ayi.
Sai a tsaida ranar biki."
Ya dubi Aliyu, Yace "kaifa? Ya kamata ka fiddo taka, tunda lokaci d'aya nace ku fiddo da mata.
Aliyu ya d'an sosa kai, Abba yace "kode sai mun nemomaka ne?
Gaba d'aya sukayi daria.
Da haka duk suka tashi.
Bayan sun koma cikin,
Ammi ta dubi Lubabatu, tace kinde fi son auran ko?"
Za a maki, idan ma kinje can ba zakiyi karatun ba, wannan damuwarki ce."
Duka shekarunki nawa Lubabatu?
Lubabatu tace "kai Ammi dan zanyi aure, Kamar na aikata wani mugun abu.
Godiya ga Allah ya kamata kuyi fa."
Kema ya kamata ki fahimta, Kamar yanda su Abba suka fahimta."
Ammi shiru kawai tayi, tana kallonta.
*************
Zaune suke, Aliyu ya dubi Sultan.
Yace "Amma ka bani mamaki bros.!
" Ka rasa wadda zaka aura, sai wannan shirmammiyar yarinyar nan.?
Wadda duka nawa take, Ka aureta kace ka auri budurwa."
Sultan ya dubeshi ranshi a 'bace.!
Yace "yanzu baka ji komai ba, ka fad'a min irin wannan maganar?
"koda Lubabatu mahaukaciya ce, A haka nake sonta."
"Idan zanso mace zan sota dan Allah ne, Ba dan wani abu nata ba.
Ko sai ta cika budurwa, naga abinda ya birgeni a jikinta ba, a haka nake sonta.
wannan shine son gaskia."
Aliyu yace "wai nufinka haushi kaji?!
To nide gaskia na fad'a, ba zan iya auran irinta ba."
Sultan yace kai kace ai, kai daban ni daban."
Aliyu ya koma ya kwanta, gami da rufe idonshi.
**************
Bayan sati d'aya da yin maganar, Daddy duka ya tarasu, Harda wasu 'yanuwansu na zaria.
Dan asa rana.
Ranar itama Aunty jamila tazo gidan ita da ummi.
A take a kasa ranar bikinsu wata d'aya.
Ba k'aramin dad'i suka ji ba.
Aunty jamila dake zaune, tace Lubabatu duka nawa kike? Da kike son aure?
Lunabatu tace "kai Aunty Jamila harda ke?
Aunty Jamila tace "eh mana, yanzu Zamani ya canza, ilimi ake nema, sai kiga kinfi k'arfin d'a namiji ya wulak'antaki."
Lubabatu tace "Aunty Jamila ina da tabbaci akan Yaya Sultan, baze ta'ba wulak'antani ba."
Aunty Jamila tace "nima nasan da haka, Sultan yaro ne na gari."
Lubabatu ta Washe baki.
Aunty Jamila tayi daria, tace "mara kunya."
Lubabatu ta mik'e da gudu, ta shige d'aki tana daria.
Ummi da ta fito daga toilet, ta kalli Lubabatu, tace "Amarya ya akayi kike ta daria haka?
Murmushi ta k'ara yi.
Ummi tace "naso ace kin fara karatu, Sannan zaki yi aure."
Lubabatu tace "wai meyasa yanzu ake fifita ilimin boko ne akan aure?"
Nifa abin nan na bani mamaki.!
Ummi tace "a'a ba fifita boko ake ba."
Lubabatu tace "to kowa sai ya dameka akan boko boko, haba."
Sai ace wai mutum be isa aure ba.
Ummi tace to kiyi hak'uri, ni bance baki isa aure ba."
Rayuwar nake kalle maki."
Lubabatu tace "ko nace maku ba zan yi karatu bane, zanyi."
*************
Yaya Sultan ne ya kira Lubabatu, ta fita.
Binta yayi da kallo, a zuciyarshi yana fad'in, "ance baki da hankali ni kuma a haka nake son kayata."
Ta k'araso kusa dashi, ta d'an hura mashi iska a idonshi.
Ya lumshe idonshi.
Tace "wannan kallon haka fa Yaya Sultan?"
Yace "kin san idan ina ganinki, komai nawa kwancewa yake.
Shiyasa idona be iya cirewa a kan kyakykyawar fuskan nan naki."
Dariya tayi, tace "nima haka Yayana."
Ina jinka sosai a zuciyata.
Sun dad'e suna fira.
Yace "kinga bikin ba a sa da yawa ba."
Ya kamata kije ku shirya duk abinda ya dace ko.
Idan kun gama sai ki fad'a min."
Tace "to shikenan."
Da haka ta koma gida, ta tara Ummi da basu tafi ba, dasu zaynab, suna shirya yanda zasu yi.
Yaya Fatima ta kira Lubabatu, tace "tace yanzu Lubabatu aure zaki yi?
Ko mu bamu yi ba fa.
Memakon ki bari ki fara koda karatun ne."
Lubabatu tace "haba Yaya Fatima dan zanyi aure, wani abu ne?"
Wai kode bak'in ciki kuke min na samu miji baku samu ba? da duk zaku dameni da maganar zanyi aure."
Banfa hana kowa yayi ba."
Yaya Fatima tace "mahaukaciya.!
Yimin shiru, Akan me zan maki bak'in ciki? Koma wa zaki aura?"
Kije kiyi auran mana, wannan damuwarki ne."
Ta kashe wayan.
Lubabatu ta bi wayan da kallo,da taga abu zai dameta.
Ta mik'e taci gaba hidimarta.
*****************
Lubabatu Amarya, an bazama sai shirye shiryen biki take.
Ta dage sai raba kayan sa rana take ma k'awayenta.
Ta fito da shirinta tsaf, ta zauna kusa da Ammi, tace "Ammi na gama shiryawa, zanje wajen Amina."
Ammi ta fara daria, Lubabatu ta kalleta a shagwa'be, tace "Ammi dariyar me kike?"
Ammi tace "ke kike bani daria idan na tuna aure zakiyi, gashi kin dage sai rabon kayan sa rana kike."
Tace gaba da daria.
Lubabatu ta zum'buro baki, tace "kai Ammi shine kike min daria."
Ammi tace "ai abin daria ne, ko kunya baki ji."
Lubabatu ta mik'e, tace "nide na tafi sai na dawo."
Ta fice d'akin tana mamakin yanda gaba d'aya 'yan gidan suka d'auketa.
Ta isa wurin su Mommy ta shiga d'akinsu Zaynab, tace "kun shirya ko?"
Khadija tace "ke kawai muke jira Amarya."
Murmushi tayi, Sannan ta kalli kanta, tace wallahi ina mamakin su Ammi da har yanzu na rasa me suka d'aukeni."
Zainab tace mai ya faru kuma?"
Lubabatu tace "uhmm da suke d'aukata k'aramar yarinya, Kamar ban isa aure ba.
Ku kalleni da kyau, ta juya jikinta, tace ban isa aure bane?
Khadija tace "kin isa mana sude suke kallon haka."
Lubabatu tace "Mommy ce kawai har yanzu banji tace komai a kan haka ba, ko ta kushe."
"Wallahi duk wanda ya nuna k'arara be son aurena da Yaya Sultan, kallon mak'iyina nake mashi."
Zainab tace "kajiki da wata magana,
Akan me za a ce ba a son auranki da Yaya Sultan."
Lubabatu tace "ai hakane mana, sai aka 'bige da wai nayi k'ank'anta, to ayi min auran a ga idan ban zauna ba harda k'aruwan d'a."
Khadija tace "ai mun lura da haka."
Lubabatu tace "kada ma ku lura, nide nasan Mommy ce kawai bata min bak'in ciki."
Zaynab tace "kede kika sani, Mommy abinda yasa kika ji ba tayi magana ba,kunya take ji, tana surukuta dake."
Lubabatu tace "kai ina k'aryane, Mommy ba zata ta'ba surukuta dani ba.
Bari ma kuga inje wurinta ku gani, Mommy d'in da har yanzu ba abinda ta fasa min wanda take min a da."
Ta mik'e tace "ku sameni d'akin Mommy ku gani."
Tayi d'akin Mommy ta fad'a jikinta.
Mommy tace "ke rufa min asiri kada ki idasa ni."
Lubabatu tayi daria, tace "Mommy wai kinji su khadija da wata magana, wai surukuta kike dani.!"
Mommy tace "a'a ya za ayi nayi surukuta da d'iyata?"
Daidai lokacin su Zaynab suka shigo.
Lubabatu tace "to kunde ji da kunnanku."
Khadija tace "eh munji, ki tashi mu tafi, dan yau garin zafi yayi yawa muyi mu dawo."
Ta mik'e tace "Mommy sai mun dawo."
Mommy tace "a dawo lafia."
Suka fice,Bala dake zaune yana jiransu ya mik'e.
Suka shiga suka wuce F. G. C
Saida suka fara shiga gidan principal, suka gaidata gaba d'ayansu.
Ta amsa cikin sakin fuska, tace Lubabatu 'yan mata kayan rigima."
Lubabatu tace "ai yanzu rigima ta k'are, gashi har zanyi aure."
Principal tace "aure kuma? Ba zakiyi karatu ba?"
Lubabatu tace "zanyi gashi har zanyi jamb, sai de a gidanshi zanyi karatuna."
Principal tace "Masha Allah!
Allah ubangiji ya nuna mana."
Gaba d'aya suka ce amin.
Lubabatu tace "dama nazo wurin Mate d'ina ne."
Principal tace "to ai ba damuwa zaki iya zuwa wurinsu, duk suna hostel yau weekend ai."
Suka mik'e, Lubabatu tace "sai mun fito."
Suna fita, Zaynab tace "kede baki da kunya."
Lubabatu ta kalleta tare da yatsina fuska, tace "rashin kunyar me nayi?"
Zaynab tace "memakon ki bari mu mu fad'a, amma kika tashi kika fad'a."
Lubabatu tace "au shine nayi rashin kunya?
Aiko banga abinda nayi ba, abin alkhairi fa ya sameni na fad'a."
Har suka isa hostel suna magana.
Amina na ganinsu, da gudu ta rugo ta rungume Lubabatu, suka shige ciki.
Haka ta fara d'awainiya dasu.
Gaba d'aya duk suka hallara, aka zauna fira.
Lubabatu tace "garin kwakwi nake son a kwad'a min inci."
Amina tayi daria, tace "inde garin kwakwi ne ai kinzo gidanshi, yanzu kuwa za a had'a maki."
Haka ta mik'e ta had'o masu, Lubabatu naci, tace "amma fa garin nan ya min dad'i sosai, students power kenan,
ko dan an dad'e ba a sadu ba."
Zaynab tace "kede ci, kinsa munzo zamu rage masu aukin abinci."
Amina tace "kin jiki da wata magana, Bayan duka sati biyu ya rage muyi candy."
Lubabatu tace "Allah sarki, dafa anyi candy zanyi aure."
Amina tace ban son k'arya fa."
Lubabatu tace "ga Sisters d'ina ki tambayesu."
Amina tace "wai da gaske?
Khadija tace "eh mana, kayan sa ranar ne ma muka kawo maki, gaba d'aya wurin suka d'auki gud'a.
Wata maryam tace "dole ne mu dangane da bikin Lubabatu."
Suka ce sosai kuwa.
Lubabatu tace "amma de kuna koya ma yaran nan hankali ko?"
Amina tace "suwa kenan?
Lubabatu tace "yaran nan mana."
Maryam tace "Lubabatu ba dama, nasan da har yanzu kina school d'in nan sai juniors sun raina kansu."
Lubabatu tace "ai da babu sauk'i."
Amina tace Allah ya shiryeki, har yanzu de hali na nan."
Lubabatu tace "me za a fasa, mutuwa ko hisabi?"
Zaynab tace "ba ko d'aya, Allah de ya shiryeki."
Sai yamma ta basu kayan da suka kawo masu, Sannan suka yi shirin tafiya.
Ta mik'a ma Amina miyar da tayi mata.
Amina tace "kai amma de na gode.
Har wurin motanmu suka rakosu.
Ranar de iyakarsu nan suka koma gida.
*****************
Su Lubabatu manyan 'yan mata, anyi candy.
Gashi ko jamb d'inta ba yanda Yaya Sultan baiyi da ita ba tasa ABU tunda gasu Fatima, tace ita polytechnic za tayi,tunda abinda za tayi a can shi za tayi a nan. Su Lubabatu 'yan computer science.
*************
Ga kuma shirye shiryen biki ana tayi.
Ba k'aramin k'ok'ari yayi ba wurin had'a mata lefe wanda fasaltashi ba zai yuwu a nan ba.
Kullum ba zama an dage sai yawon rabon IV.
Yaya Sultan ne ya kirata ta fita ta sameshi.
Ya dubeta yana murmushi gami da cewa.... "Amarya.!
Murmushi tayi, Yace "to ga d'inkin na amso maki duba kiga yayi kyau ko?"
Tana dubawa, ta kalleshi.. "Haba Yaya Sultan ya zaimin d'inkin da bashi nace ba, gaskia bana so,sai de ka maida mashi yasan yanda zaiyi."
Binta yayi da kallo..."to ni d'inkin yamin ai ni za a sa mawa in yaba ko? To yamin."
D'an harararshi tayi tace "gaskia bana so sai de in hak'ura dashi."
"to tunda baki so ki barshi a nan."
"Au haka zaka ce min ko? To a barshi a nan d'in."
Ya fara shigewa cikin gidan.
Ta saki ledar rigar a nan ta wuce ciki itama.
Can an d'an bada mintuna, ta fito harabar gidan, sai kalle-kalle take sai kace mara gaskia.
Tana isa tasa hannu zata d'auki ledar, Yaya Sultan dake la'be yace "na ganki!"
ta saki ledar ta dank'ara cikin gidan da gudu.
Daria ya hau yi mata.... "kai Lubabatu! Allah ya shiryeki da wannan shirman naki."
Yaya Aliyu da ya k'araso wurin, Yace "ai dama kasan wadda zaka aura, kaga duk shirman da tayi sai ka zauna kaita daria tunda aiki ya sameka."
Ya shige ya barshi nan.
Zurfa'u ce tazo wucewa.
Yace "yauwa Zurfa'u d'an shigar ma Lubabatu da kayan nan ciki."
Amsa tayi ta shige ciki, ta mik'a ma Lubabatu ledar.
Lubabatu tace "wannan fa na miye?"
"Yaya Sultan yace na kawo maki."
Mtssw... "to meyasa kika amso?"
Zurfa'u tace "ikon Allah!
Ni daga bani sak'o in kawo sai nayi laifi."
Ammi ce ta fito..."Sarkin fitina me kuma ya faru?"
Lubabatu ta fiddo da kayan dake cikin leda ta d'aga ma Ammi... "Ammi dan Allah ki dubi d'inkin da Yaya Sultan yasa aka min fisabilillahi!
Ya tashi sai zuzuta min telanshi yake wai ya iya d'inkin mata sosai."
Ammi tace "ni ai banga aibun d'inkin nan ba jibi fa yanda yayi kyau"
Lubabatu tace "Allah yasa ba dan hankalina ya kwanta kika ce ba?"
"bari na kai ma Mommy ta gani, nasan zata fad'a min idan beyi ba. "
Dariya Ammi tayi, tace "kai ana de mahaukaciyar amarya."
Ranar de d'inkin nan ba wanda ba a nuna mawa ba.
***********
sun fara hidimar biki cike da annashuwa, bakin nan na Lubabatu yak'i rufuwa.
Gashi Aunty Fatu k'anwar mamanta da tazo daga maiduguri tun ana saura sati d'aya ta rik'eta a d'aki sai had'ata take da k'amshi kala kala, Ga uban had'in magunguna da take ta d'inkira mata.
Duk yanda Yaya Sultan yaso ya ganta dole ya hak'ura.
Duk wasu k'awayenta har sun iso irinsu Amina, sai 'yan ciki gari.
Gashi har sun fara shagali, anyi shirin tafiya dinner,da Daddy ya had'a masu.
D'aya k'wak'k'wara d'aya sukayi da ya k'ayatar ba sai an cika ba.
Amarya ba k'aramin kyau tayi ba, yanda kasan ba Lubabatu ba,shigar da tayi ya k'ayatar.
Yaya Sultan ne ya bita da kallo.... "anya ko Lubabatu na ce haka?"
"gaskia ayi a d'aura auran nan kada wani ya sace min ke."
Murmushi tayi... "Yaya Sultan dena fad'in haka me sace maka ni ai sai ya shirya."
Yace "gaskia kam nima na yarda da haka, wannan k'amshin da kike zubawa ai sai kisa na kasa sukuni."
Tace "ai wannan k'amshi aikin Aunty Fatu ce, Kasan 'yan maiduguri wurin had'in k'amshi dole a sara masu."
Har suka isa wurin dinner sai fira suke.
Lokacin da suka shiga aka sa masu wak'an bikinsu da yaji kalangu.
Kowa na wurin saida suka birgeshi.
Sosai dinner ya k'ayatar inda ya had'a da manyan mutane.
An gama ciye ciye da tand'e-tand'e sun gama lafia inda aka fara kwashe mutane ana maidasu gida.
0 Comments