AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@( H,O,N,A)
Part 120.....125
Wani irin murmushi Ogansu yayi, yace nadade ina tunanin wata rana zamu hadu, segashi cikin sauki nasameki ahannu. Kai, ya daka masu tsawa, a ina kukasan wannan matar tajikin hoton nan, mesuna Hajjo? Cike da fargaba Asabe tace wlh ba ita bace amma de itama mamarta sunanta Hajjo, kuma tarasu da dadewa, wannan sunanta Falak.
Murmushi yayi yace tabbas yarinya kingirma, harkin kai minzalin aure, kinzo adede dama ina bukatar abokiyar hutawa. A wane gari suke? E to dama de AGOLAH ce agidan diyar mijina, kuma bayan mamanta tarasu itama tayi aure. Mene? Aure? Wlh dasake, kinsan koni wanene agurinta? Kai Asabe tashiga girgizawa tana hawaye.
Kawun Babanta ne ni, kinga ko inada hakki akanta, to wai ku inama zakuje da makudan kudi haka, kuma mezakuyi da wadan nan hotunan, kode wannan shine mijin nata? Dan Allah yallabai kayi hkr, wlh muma bamu akayi mukaisu gurin boka shine mukuma mukace bazamuje ba, shine mukayi kokarin guduwa da kudin.
To waya aikeku? Diyar mijina ce, itace kishiyar Maman Falak, wannan kuma mijinta ne, shine takeso amallake, ita kuma Falak akasheta. Hahhhhh, kawai kicemun kuma maciya amana ne. Lallai tunda hadaku za,a hada baki akashemun jinina, lallai kuma zaku amshi rabonku, danni bana yafema wanda yashiga gonata.
Dije tace kawa Allah kayi hkr, mude kudauki koda rabin kudin ne, kubamu sauran mutafi, wlh dama can bamuyi niyar zuwa gurin wani boka ba, muma muna tausayinsu ai..... Saukar marin datajine yasata yin shiru, ke harkin isa kizo gabana kina fadin indauki rabin kudi inbaki sauran. To bara kiji, ko wadanda suka kawo kudin basuda hurumin karbar rabin kudin bare kuda muka kama, wanda lokaci kadan yarage maku aduniyar gaba daya.
Wayyo Allah nashiga 3,ni Asabe, ina zamana Dije kinja mani, gashi nan nibanyi kudiba, zan rasa raina abanza, nide Allah ya isa tsakanina dake, duk kece kika sakani cikin wannan bala,i. A,a kada kidoramun laifi, dama can da bakin halinki kikazo garinmu, keda kika kashe mazajenki har 2, kuma kike fadin nina koya maki bakin hali.
Ya isa,,,,,,,., Ashe de kuma kananan yan ta,adda ne. Lallai kunyi kokari. Duk ku saurara, banida lokacin batawa, ke a ina zan iya samun Falak? Wlh nima bansan gidansu ba, amma de nasan gidan diyar mijina. Ok, fadamun dan sauri nakeyi.
Idan kaje Unguwar sarki kaduna duk wanda ka tambaya Alhaji Abba Bala, yasan gidan. Da kyau, kai mugu gama masu aiki kasan ni bana barin baya da kuurah. Tasssss kakejin karar bindiga andauke Asabe da Dije. ( se ince karshen Asabe da Dije kenan, dama duk wanda ya gina ramin mugunta, wata rana shine ze fada. Allah yatsaremu, sunyi 2 babu).
Mazaje, kowa yafara shiri, gobe da asuba zamu dauki hanyar kaduna, bansan ranar dawowarmu ba, harsena cika burina na tahowa da Falak, tunda munsamu isassun kudi bamu da damuwa, kudauki jakar kudin muware, lallai yau munyi babbar sa,a. Daukarmun hoton fuskarsu awayata, hakan zemun amfani idan naje gidan, diyar mijinta.
Sedare Sameer yazo yadauki Falak suka wuce gida, Zarah ko sallama bata bari sunyi ba, har mota Jalila da Alh, suka rakosu, Alh, wani irin farin ciki yakeji. Sameer yace Alh, gobe zanzo indaukeka a office kawuna yana son ganinka, yace lallai muje tare akwai wani temako dazeyi maka. To to babu komai, Allah yakaimu, bara insamaka no ta idan kazo seka kirani, yauwa gata, zantura maka da address din office din. Sallama sukayi masu, Falak kamar kada ta tafi takeji.
Kwance Jidda take abisa gado tana tunanin halin datake ciki, gashi cike take da bukatar namiji idan takira Viju akashe, tarasa yanda zatayi, murmushi tayi, tace wlh bazan tausaya ma duk wanda yanemeni da bukataba, yanda aka likamun cuta kowama yasamu badamuwata bace, Allah yakaimu inkara samun sauki, dole insamo me biyamun bukatata, meza,a fasa, tunda harnazo gargara, ai gara kawai incigaba da shakatawa ta. (Lallai kinyi kuskure Jidda, Allah yashirya). Tashi tayi tabude jakarta tadauko maganinta tasha sannan ta kwanta.
Zarah kuwa aranar kasa zuwa dakin Alh, tayi adakinta tayi kwanciyarta sbd batason yawan tambayar da Alh, yake mata, ga abin duniya yafara isarta, takira no wayar Asabe yafi akirga, amma bata shiga, gaba daya ta gama shiga tashin hankali, addu,a kawai take Allah yasa lfy. Amma ta kudira aranta dole gobe taje Zariya. Da wannan tunanin tasamu bacci yadauketa.
Kuyi hkr da wannan.
Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/16, 12:31] Nabilat Author: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@(H,O,N,A)
Part 125.....130
Karfe 9 na safe Zarah tagama shiryawa tasami Alh, afalo yagama cin abinci yana shirin fita. Bayan sun gaisa, tace Alh, dama zuwa nayi infada maka inaso inje gidan, dan jiya mafarki Baba nayi wai beda lafiya, shine nace gara inje indubashi na dade banje ba. Mamakin kalamanta yayi, dan a iya saninshi Zarah bata taba cewa zataje taduba Babanta ba, sede idan wani uzurinta ya tashi, yace tofa, ai mafarki ba gaskiya bane Zarah, insha Allahu zaki sameshi lfy. Shikenan sekin dawo, amma dan Allah kada kiyi dare kinsan banason tukin dare. Kudi yabata yace tayi mashi siyayya, yakaramata wasu yace idan taje tabashi kuma tace yana gaisheshi. Godiya tayi mashi yatafi itama tayi masu Jalila sallama ta tafi.
Alh, yana zuwa office bayan yagama abinda yakeyi, yaji kiran Sameer, nan yahada kayanshi yafita yasameshi awaje, bayan sun gaisa, Sameer yace ina ganin ka aje motarka semu tafi atawa, haka akayi suka nufi gidan Kawu.
Bayan sungaisa, Kawu yafara magana, agaskiya Alh, ka tsallake rijiya da baya, tun ranar da mukaje neman auran Falak na ganka, nasan akwai abinda yake damunka, gaskiya Alh, kana sakaci da addu,a kasan ita makamin mumunice, duk wanda yariketa, to koda wani abu zesameshi yakan zomashi da sauki. Hakan yasa asirin da akayi maka yayi tasiri akanka. Amma alhamdulillahi yanzu babu komai ajikinka, sede muce Allah yakara karewa, kuma kaima kadage da addu,a.
Alh, yanisa yace tabbas Malam nima naji alamun haka tunbayan da muka hadu da Falak a asibiti, kuma naji labarin da bansan ya akayi ba, adaren jiya sam banyi bacci ba, duk da nace bazan tsananta binciken halin dana shiga ba, amma ajiya nayi nazari sosai, kuma zuciyata tafara zargin wani abu, sede kasan ance zargi beda kyau koda yakasance gaskiya ne, hakan yasa nabar abun kuma nima nayi alkawarin dagewa da addu,a tabbas nasan nayi sakaci abaya, amma yanzu hakan yazamar mani darasi.
Kuma ina baran addu,a awajenka, Malam yace babu damuwa Alh, muna temakon wasu ma, bare kuma nagida, kuma nima shawarar dazan baka kamar yanda kace kana zargin wani abu, to kabarshi ahaka, kada kayawaita bincike, kasan kome mutum yakeyi Allah yana ara mashi rana ne, wata rana dole asirinshi ze tonu.
Abu nafarko dazaka farayi shine karika tashi cikin dare kana sallar dare, kasan Allah yace yana saukowa akowane karshen dare kuma yana amsar addu,ar duk wadanda suka rokeshi a wannan lokacin, ka yawaita karatun alkur,ani, da sadaka suma suna temakon mutum, yawan ambaton Allah safe da yamma, azkar dinka kullum dummin saurin da kakeyi kada kabari suna kubucemaka, koda kana tafiya amota ne, idan ka haddacesu to kasamu kafin ka isa inda zakaje kayisu. Allah shine mafi sani, wannan ruwan addu,a ne danayi maka tunjiya, kashanye yanzu, wannan kuma idan ka koma gida kazubashi aroba kawanke jikinka duka, insha Allah zakaci nasara akan duk wani menemanka da sharri.
Godiya sosai Alh, yayi mashi hada kukanshi, yakawo kudi yace gashi ayi sadaka, daga nan sukayi sallama Sameer yamaidashi office, yana zuwa ya dauki motarshi yanufi gida. Yana zuwa yashiga yayi wanka da ruwan maganin da aka bashi yadauro alwala yazauna yana karatun qur,ani.
Zarah kuwa tana zuwa gidansu taci karo da Babanta yana shirin kulle gida. Tsayawa yayi yana kallonta cike da mamaki, danshi har yamanta rabon daya ganta, tana fitowa daga mota tace Baba ina kwana, yace lfy lau Zarah ashe kina duniyar? Dukar da kanta tayi tana wasa da makullin motar tace wlh kuwa Baba kasan aiyuka ne sukamun yawa. Yace e gsky kam naga alama.
Yanaga kana shirin kulle gidan ina Innar take? To shigo daga ciki tukunna.
Bayan sunzauna, ya kalleta yace Asaben bata fada maki abinda yafaru ba? Saurin kallonshi tayi tace aini rabona da ita tun ranar litinin, kai ya jijjiga yace to ai tundaga ranar nima bankara ganinta ba, dan yanzu bama tare da ita, aranar lahadi tazo tace insaketa zata bar garin, nikuma na sawake mata tundaga nan bankara ganinta ba. Wata irin zufa ce tarika keto mata, tafara fifita tace nashiga 3 yanzu Baba bakasan inda ta tafi ba? Murmurshi yayi yace ai kunfi kusa ni ina zansan inda taje, dama ni asama naganta, bansan kaddarar data kaini aurenta ba, kuma gashi Allah yarabani da kaya, bana fatan musake haduwa da ita.
Shiru tayi tafiddo wayarta tana kara kiranta amma haryanzu shiru. Abinda bata saniba, tun atasha Asabe ta karya sim dinta tace setaje Lagos zata sayi wani. Baba kuma wayarta kullum akashe, dariya yayi yace toni Zarah yakikeso incemaki, kowa yasayi rariya ai yasan zatayi zuba, saboda haka kije gidan kawarta Dije kozata fada maki garinsu. Ai Baba Dije bata nan, kuma bansani ba kota dawo, gashima ni bansan gidanta ba. Kanshi yagirgiza yace waini Zarah me Asabe zatayi maki ne kike nemanta? Babu komai Baba, kawaide ina nemanta ne, kasan banida wata. Uwa data wucemun ita shiyasa hankalina yatashi danaji kace bata nan. Seda yaji kwalla tacika mashi ido jin kalaman Diyarshi, tabbas tausayinta yashigeshi, sede Asabe tayi mata mummunar huduba. Share kwllar datazubo mashi yayi, yace shikenan Zarah, amma de inaso kisani Asabe ba macen kirki bace, kada kicigaba da nemanta babu abinda zaki saku agurinta se halaka, kiyi hkr kamar yanda Allah yarabani da ita kema kidauka rabuwarku alkhairi ce.
Kallonshi tayi cike dajin haushi tace Baba nide kasa wani yarakani gidan Dije sauri nakeyi zankoma. Murmushi yayi yace Zarah kibi duniya ahankali wlh ina tausaya maki duk ranar da duniya zata juya maki baya. Tashi tayi tace nide zantafi, dubu 1 taciro tace ga wannan kayi cefane, yace A,a kirike kudinki zasuyi maki amfani ahanya niyanzu bana bukatar komai, Allah yayima Jalila albarka, tabbas yarinyar nan yar halak ce, tayi mani abinda wadda na haifa takasa.
Tashi muje innuna maki gidan, kudinta tamaida jaka tana gungunai tayi gaba, har kofar gidan Dije yarakata, ya hadu da wani abokinshi makwabcinta, shi yatambay ko tadawo. Yace ai malam Garba Dije da kawarta sunyi hijira bazasu dawo garin nan ba, dan harta saida gidanta da komai nata, nima kiya medakina take fadamun tashiga gida tasamesu suna ta shiri, suke fada mata sukam sunci gaba. Zarah jitayi kafafuwanta suna rawa, zufa kawai take fito mata, da kyar tace to Baba nizan koma, yace to yayi kyau, Allah ya kiyaye kigaishemun da Jikanyata Jalila, haka tanufi mota yana binta da kallon tausayi. Da kyar taja motar ta tafi, ikon Allah ne kawai ya kaita gida, tana zuwa tashige dakinta ta kulle tafara kuka.
Karfe 4 na yamma su Figo kawun Baban Falak suka shigo kaduna, cikin shiga ta mutunci, idan kagansu sekadauka irin manyan yan shiyasa ne, hotel suka nema suka kama daki 2 shi yadauki daya yabasu daya su 3.
Se karfe 6 suka fito shida babban yaronshi Jungle suka tari taxi suka fada mashi inda ze kaisu, suna zuwa unguwar suka sami wani suka tambayeshi gidan Alh, Abba Bala, nan take yanuna masu gidan, godiya sukayi mashi, Figo yaciro wayarshi yasa akunne kamar mekiran waya, can kuma yacire yace wayarshi akashe take kawai muje ma dawo gobe, banason shiga baya gida kasan matarshi bazata barni infito ba, zatace sena jirashi. Kallonshi Jungle yayi Figo yayi mashi signal da driver, murmushi yayi yadaga mashi hannu, suka koma hotel, bayan sun sallami driver Figo yace kasan bana aikina da ka, haka kawai muje guri da driver kuma mu tambayi gidan mutum ana nuna mana kawai mujuya ai kowaye ze iya zargin wani abu. Jungle yace gsky Oga aiki da kai akwai karuwa.
Zaune suke afalo Falak tayi matashi da kafar Sameer, shi kuma yana wasa da cikinta, yace dear idan kika haifa mun mace sunan Ummanki zansa, Idan kuma na kiji ne, sunan Babana zansa, shiru yaji tayi batace komai ba, dukowa yayi yana kallon fuskarta, gani yayi hankalinta baya gurin, girgizata yayi, tayi saurin kallonshi. Meye haka kikeyi Falak, bakisan yanzu bake daya bace, kike irin wannan tunanin, kuma ko ke dayace ma aikinsan banason dogon tunani ko. Murmushi tayi tace kayi hkr wlh ina tunanin Dady ne, ina tausayinshi, nasan Ummi bazata kyaleshi haka ba. Babu abinda zata iya kara yimashi, domin yanzu yafi karfinta, kawai mucigaba dayi mashi addu,a. Shikenan, Allah yakara tsaremu, yace yauwa kokefa, ameen, tashi muje kibani abinci dagata yayi suka nufi daki suna dariya.
Washe gari da misalin karfe 10 nasafe, Jungle da Figo suna daga gefe suka ga motar Alh, tafita. Figo yace yauwa, yatafi muje, suna zuwa suka kwankwasa kofar, megadi yabude, bayan sungaisa, Figo yace ni suna Lado, munzo gurin Alh, ne. Megadi sewashe baki yakeyi yaga manyan kutane, yace yanzu kuwa yatafi office, amma ku kirashi mana. Aa, barshi kawai idan hajiya tana ciki kafada mata zamu bata sako seta aje mashi, yace toshikenan kushigo ga banci nan kuzauna, dasauri yanufi cikin gidan, Karo sukaci da Jalila bayan sungaisa yace tayima Hajiya sallama wasu mutane suna son bata sako ta ajema Alh.
Adaki tasameta kwance tana tunani, tace Ummi wai kizo wasu kutane zasu baki sako ki ajema Dady, tace kash nifa banason yawan damuwa kije kawai subaki, tace a,a Ummi idan kuma sakon kudine fa, ai kinga keyakamata subama, saurin tashi tayi jin ance kudi, gyalenta ta dauka tafita.
Bayan sungaisa Figo ya matsa kusa da ita ahankali yace bagurin Alh, muka zoba gurinki mukazo kuma munzo da magana me mahimmanci amma idan kinasonji zamu iya matsayawa daga nan, harararshi tayi tace nikuma a ina nasanka, murmushi yayi yace amma idan baki sanni ba, kinsan Asabe da Dije ko?
Cike da fargaba tacee kushigo, murmushi yayi yace abokina muje ta matsa semunsha ko ruwane, megadi yace ai gaskiya ne, sekunfito. Bayan sunzauna afalon baki tace dan Allah ina kasan Asabe da Dije? Wayarshi yaciro ya nuna mata hotonsu yace kobasu bane wadannan, jiki narawa ta amshi wayar tafara dubawa, dasauri tace bade sun mutu ba, to ina jakar dasuke tare da ita? Yace tonide bansan wata jaka ba, munshiga mota atare dasu zamuje Lagos, se yan fashi suka tare mu, suka kwace mana kayanmu da kudinmu duka, to ita Dije tana kusa dani, alokacin da aka bude jakarta senaga wasu hotuna sunfado, ina dauka naduba senaga macen jikin hoton nasanta, ita da mamanta, garinmu daya dasu, kuma masu laifine, sunan mamarta Hajjo ko? E ita kuma Falak, haka suke, to bazan boye maki ba, agaskiya mutanen banza ne, mijin Hajjo abokina ne, yanada kudi, shine ita da niyarta suka hada baki suka kashe shi suka gudu.
Nayima yan sanda alkawarin nizan nemosu aduk inda suke, na dade ina nemansu bangansu ba, harna hakura, segashi Allah yakawomun su cikin sauki. Bayan natambayi Dije a ina suke tacemun Hajjo tarasu, ita kuma Falak tayi aure, shine nace tayi mani kwatancen inda zanganta, shine take cemun ai kekika san inda take, kema kinso akasheta kika basu kudi sukaisu gurin boka, shine sukuma ashe karya suka maki guduwa sukaso suyi da kudinki shine yan fashi suka kamamu. Ita ta fadamun sunan mijinki da unguwarku.
To dayake ansamu kudi agurin kowa sune suka boye nasu da kaya, koda yan fashin suka gano kudin suka tambayi masu su, shine suka kashesu, mu kuma suka maida mana kudinmu, nikuma nadaukesu hoto dan innuna maki. Yanzu nazo kitemakeni ki nunamun gidan Falak domin hukuma tayi saurin cafketa.
Bakin ciki tare da farin ciki ne, suka hadema Zarah, jin za,a kashe Falak cikin sauki.
Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ (H,O,N,A)
Part 135.....140
Cike da sauri Jidda tabama me taxi kudinshi tashiga gida, da Zarah suka fara cin karo tace ke lafiyarki naganki kamar arikice? Harzata fada mata, se kuma ta tuna da maganar da Figo yafada mata, akan tabada kudi akai dadynsu gurin boka. Murmushi tayi tace wlh Ummi ba komai ina Jalila? Baki ta tabe tace tana ciki, kinsan yau za,a kawo lefenta amma kika ki tsayawa akarba.
Uhm wlh Ummi wani uziri ne, yataso mun, shine nafita dawuri nadauka bada wuri zasu zo ba. Ai shikenan kishiga ciki sunan ki kalla, Jalilan ma tana falo, yauwa Ummi, da kallon tausayi tabita, aranta tace dole insama maki mijin aure kema, damma Asabe ta munafunceni ai da naje gurin boka asama maki miji medan maiko, ita de Jalila Allah yasota batare dana kashe kudina ba tasamu me kudi.
Jidda tana zuwa falo tasamu Jalila tana kara duba kayanta, cike dasauri takamo hannunta har seda Jalila ta dan tsorata, lfy de Yaya Jidda? Lfy lau kede kawai biyoni muje daki muhimmiyar magana ce bata bukatar bata lokaci, daki suka nufa Jidda ta kulle dakin taja Jalila saman gado.
Ita de Jalila kallonta kawai take cike da mamaki. Inajinki Yaya Jidda Allah de yasa lfy. Uhm Jalila inaso kibani aron hankalinki, ayau inaso infada maki wata magana wadda babu wanda yasan da ita, kuma inaso idan kinjita ki temaka mun domin insamu inyi aiki alkhairi guda daya nima arayuwata. Jalila tace inajinki.
Tun daga farkon shigarta harkar banza harzuwanta London da irin wahalar data sha, har zuwa haduwarta da Viju da irin yanda ya yaudareta, ta cutar datake dauke da ita, harzuwa haduwarta da Figo da abinda yafada mata, seda tafadama Jalila. Kuka sosai sukeyi ba kamar Jalila wadda tausayin yar uwarta yakamata, jin irin abubuwan data aikata. Jidda tace wlh Jalila tun lokacin da Umman Falak tarasu naso intuba, amma rudin duniya tare da irin halin da Ummi take nunamun yasani komawa ruwa. Tabbas Al,amin masoyine nagari, yaso inbar London indawo muyi aure amma nakasa fahimtar abinda yake nufi, seda narigada nakamu da cuta sannan yace baze iya aurena ba, tunda shi beda ita, yanzu haka bansan inda yake ba, ko no shi nakira bata shiga.
Nayi nadamar abinda na aikata, nacuci kaina da kaina, kuma hakan yasamo asaline dalilin Uwa dabamu samu tagari ba. Ko kinsan cewar Ummi dasu Inna Asabe sune silar mutuwar Umman Falak da Ameer, kuma itace ta mallake Dady, yarika yin duk wani abu dayake ma Falak. Gsky nide tsakanina da Ummi sede ince Allah ya....... Saurin rufe mata baki Jalila tayi tana kuka tana girgiza mata kai.
Kada kice haka Yaya Jidda, Uwa Uwace koda kuwa yar mafiyace bamuda wadda tafita, domin itace tayi sanadiyar kawomu duniya, dataso lokacin fitowarmu data kashemu, dataso tun muna jini datayi barinmu. Da jinin jikinta muke rayuwa acikinta, dole mudauki duk wani abu dazata mana, dan bekai rabin rabin wahalar datayi damuba. Ayanzu ko zama mu tsareta na awa 3 tayi bacci bazamu iya ba. Amma ita takan hana kanta bacci domin mu muyi. Saboda haka kada bacin rai yasa kifadi wata mummunar kalma akan Ummi, Allah ze iya kamaki da laifi akan hakan.
Addu,a itace abinda yakamata muyi mata wadda itace nake mata kuma gashi tafara canzawa, yanzu haka neman yafiyar Falak ta aikeni rannan nayo mata. Jidda tace Uhm Jalila ke yarinyace bakison kissa irinta Ummi ba. To wlh yaudararki tayi tayi amfani dake tanunama wadan nan mutana gidan Falak. Dan haka yanzu ba lokacin labari bane, kitashi muje mufada masu halin da ake ciki. Kuma akan labarina dana baki banason kowa yaji, kibarni ni nasan tawa tazo karshe, dan haka zankarbi duk wani hukunci da Allah zemun.
Jalila tace amma Yaya Jidda kinashan maganinki kuwa? Yamutsa fuska tayi tace wannan duk wahalar banza ce, tunda de ba,a iya ciremun ita gaba daya ba, babu amfanin shan wani magani, ada nafara sha daga baya kuma naga beda wani amfani, gara kawai incigaba da rayuwata haka har mutuwa ta tasameni. Jalila tace amma dakin cigaba da shan magani koba komai zaki samu lfiyar dazaki nemi yafiyar Ubangiji. Mikewa Jidda tayi tace kitashi mutafi banason dogon zance.
Adaki suka sami Zarah tabuga tagumi tana tunani, Jalila tace Ummi tunanin me kikeyi kuma? Murmushi tayi tace bakomai kawai ina dan tsare tsare akan bikinki ne, kinga saura sati 2. Hakane Ummi amma banason inga kina tunani. Yauwa Ummi zamuje mukai dinki nida Yaya Jidda.
Zarah tayi murmushi tace amma naji dadi dazaku tafi tare, sekun dawo, driver yana waje kusashi ya kaiku, to Ummi amma sede ya ajemu yadawo dan akwai inda zamu wuce. Tace toshikenan sekun dawo.
Suna zuwa gidan Jalila taga motar Saleem, tsayawa tayi Jidda tace muje mana, tace Motar Saleem nagani. Jidda tace to menene, bazaki shigaba kome? Nifa banason gulma. Jalila tace bahaka bane, inajin kunyar yaji labarinki sede idan bazaki fada masu yanda kikaji za,a dauko Falak daga gurin Figo ba. Murmushi Jidda tayi ta goge kwallan dasuka zubo mata, tace babu sauran jin wata kunya, kuma ni nadaukesu abokana shawarata, kada kidamu kobasu ji labarina ba sun riga da sunsan koni wacece sbd sunsan abinda nake aikatawa. Nasan Saleem yana sonki dan yaji labarina baze taba son dayake maki ba. Kuma dole nasan Sameer yafada mashi halin Ummi, tun kafin asamaku rana, kuma tunda kikaga bedena neman aurenki ba, ai yasan kinada hali me kyau. Kasancewarmu nida Ummi marasa hali me kyau baza,a ce dole kema ki kasance haka ba. Kinsan Allah yana fitar da shiryayye daga wanda ba shiryayye ba. Jalila tagoge kwallan idonta tace shikenan muje.
Kuka kawai Falak takeyi, Sameer kuwa gaba daya zufa ce tarufeshi, hankalinshi bakaramin tashi yayi ba, jin wai wani banza yanason zina da matarshi. Kallon Jidda yayi yace tabbas yanda kika kwatan tamana shi shine kawun Abban Falak, kuma daga gidan nan yake, Lallai biri yayi kama da mutum, tunda yatafi muma bamu yarda dashi ba, kuma aniyarmu gobe da safe zamu tafi gidanmu, sede yanzu dole mubar gidan nan, sbd meson abunka yafika dabara, yana iya canza shawara.
Jidda tace dan Allah Falak kiyafemun da duk irin abinda nayi maki, tabbas rayuwa takoyamun darasi, kuma kwadayi yakaini yabaroni, babu abinda nake nema daga gareku se addu,arku kobayan raina. Sameer yace meyasa kike fadar haka Jidda? Cikin kuka suma tafada masu labarinta.
Duk irin dauriya ta maza seda Sameer da saleem sukayima labarin Jidda kuka. Falon ya dade shiru kukan matan kawai akaji, sukam mazan sede hawaye a ido. Jidda tace narokeka Saleem kada labarina yasa wani abu yashiga zucuyarka na game da auranka ko soyayyara da Jalila. Wlh ko Qur,ani zan iya dafawa akan shedar halin kirki irin na jalila, Allah ya shiryata, duk irin yanda Ummi take nuna mata halin ko inkula lokacin da ina kawo mata kudi hakan besa ko samari Jalila tafara kulawa ba. Duk da bansan rayuwar datayi a makaranta ba, amma zan iya cemaka kaine mutum nafarko da Jalila tafara kulawa.
Dan haka inaso kada jin labarina da kuma halin Ummin mu yasa wata rana ka goranta mata. Saleem ya goge idonshi yayi murmushi yace Yaya Jidda kada kidamu. Allah ne yahadani da Jalila, bantaba son wata halitta ba kamar yanda nakeson Jalila, bayan Uwata da mahaifina zan iya cemaki Jalila itace mutum ta 3 datakeda muhimmanci arayuwata. Kima dena tunanin zan goranta mata, har abada, kuma wannan labarin naki insha Allahu daga nan yagama zuwa wani guri. Kuma batun maganinki dole zaki cigaba da shan shi, sbd rayuwa da mutuwa agurin Allah suke, idan yaso seyabarki da cutar harzuwa wani lokaci. Kifadamun idan baki shan magani kuma taci karfinki harta kaiki last stage wanda ko likitoci bazasu iya maki komai ba. Gashi Allah yaki yadauki ranki yazakiyi da wahalar dazaki sha? Alokacinne seme kaunarki sosai zeiya zama dake.
Dan haka kimun alkawari daga yau zaki cigaba da shan maganinki. Shikenan Saleem insha Allahu zancigaba dasha, dama na wata 1 aka bani kuma yana nan. Sameer da tundazu seyanzu yayi magana yace insha Allahu kema zakiyi tsawon rai harkisamu lokacin tuba zuwa ga Allah. Jidda tace Falak kinyi shiru bakice komai ba. Dan Allah kiyafemun.
Falak tagoge idonta wanda yayi ja sbd kuka, tace babu komai Yaya Jidda, niban rikeki da komai ba, kecema zanyima godiya, badan keba bansan yanda rayuwata zata kare ba. Saleem yace kutashi mutafi gidan Umma seku kwana acan, kai kuma Sameer daga can seku wuce gurin abokina D,P,O ne dan musan yanda zamu bullomasu, banason gobe tayi haryazo besameku ba, ze iya tunanin wani abu. Kema Yaya Jidda dake zamu tafi dan dole dake zamuyi amfani musamu mu cafkeshi. Tacebabu komai, ashirye nake dabada gudummuwata dama ina da no shi. Sameer yace Allah yadoramu akan sa,a sukace ameen.
Falak tace amma inaso kafin kutafi kusami Dady kuyi mashi bayani dan bazeji dadi yaji abun daga sama ba, dan yafi kowa sanin labarin Kawu. Saleem yace kinyi gsky, idan muka aje ku semu sameshi mutafi tare dashi ma.
Urs.
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
@ ( H,O,N,A)
Part 140.....145
Kaf suka fadama Alh abinda yafaru, sede sunboye abinda yashiga tsakaninsu da Jidda, sunfada masa saurayinta ne, yarage mata hanya shine taga hoton Falak amotarshi har yake bata labarin abinda zeyi mata. Kuma basu fada mashi abinda Zarah tayi ba.
Sosai Alh, yayi mamkin jin wannan al,amari, yace lallai dole mudauki mataki cikin gaggawa, dan akowane lokaci ze iya aikata abinda yayi niya, dan beda tausayi. Allah sarki Hajjo babu rabon kiga wannan rana, banyi tunanin wannan mutum yana nemansu haryanzu ba.
Abinda zefaru kai Sameer kuyi gaba zuwa gurin abokin shi Saleem kome kenan kuyi mani waya, amma dole ayau za,a je aka mashi, tunda Jidda tanada no shi kutafi da ita nasan zatayi maku rana, nima dana gama abinda nake zanzo.
Kwance Zarah take, hawayene kawai suke zuba a idonta, zumbur tayi saurin tashi lokacin data kara tuna maganar dasukayi da boka ta karshe lokacin dataje karbar maganin mallakar Alh........... 👹 Ina me tambatar maki da duk lokacin da mijinki yasan irin halinki marar kyau, wato asirinki yatonu agurinshi daga ranar zaki haukace. Tace babu damuwa boka bazan taba yarda yasan halin danake ciki ba, inde inada kai ai baxetaba dawowa cikin hankalinshi ba.
😭 Komawa tayi bisa gado tacigaba da kuka, saboda tarasa yanda zatayi tasamu wata hanya dazata temaketa kada Alh yasan halin datake ciki. Seyanzu take danasanin rashin yin kawaye, dayanzu tasan dole tasamu wadda zata kaita gurin wani bokan. Hannu tadaga sama tace ya Allah katemakeni ka rufamun asiri, kada Alh, yasan halin danake ciki.
Zaune suke aOffice din D,P,O bayan sungama kora mashi bayani. Kallon Jidda yayi yace awane hotel yace maki yake? Tace a Hamdala hotel. Kince kina da no shi ko? E gatanan, good, kirawoshi yanzu kinsan de irin kissar dazakiyi mashi yabaki damar zuwa anjima da dare. Shiru tayi tana wasa da wayarta. Saleem yace Yaya Jidda kidan fita daga waje kuyi wayarku nasan kunya kikeji ko? Murmushi tayi tajuya tafita.
D,P,O yace insha Allahu acikin daren nan zeshigo hannu dashi da yaranshi abunma yazo dasauki ai, tunda mayen mata ne. Wani guri Jidda tasamu sannan takirashi, yana dagawa tace Jidda ce, washe baki yayi yace Jidda kamar kinsan kenake tunani wlh, tundazu nake jiran kiranki, gashi banda no dinki naso inkiraki ince anjima kidawo bazan iya hakurin gobe ba.
Murmushin mugunta tayi tace kamar kasan abinda nakira infada maka kenan, nima tunda nadawo gida nake tunaninka, da na hakura se goben amma naji nakasa shiyasa nace bara inkiraka insheda maka anjima zanzo. Kara washe baki yayi yace kai amma naji dadi, gaskiya kinada kyauta me tsoka sbd wannan albishir din da kikamun. Tace shikenan nagode, karfe nawa zanzo? Yace ni wlh koyanzu ma kitaho dan amatse nake. Tace a,a kaide kawai kayi mana babban tanadi anjima karfe 8 zanzo ana ma zan kwana. Dariya yayi yace kai amma nagode, kinsan dama gobe ina da abokiyar kwana, yau semu kwana tare. Tace yauwa ni namanta room no, ok room 102 dakinzo kawai ki kirani. Sallama tayi mashi tana me hararar wayar.
Tana shiga tafadi masu yanda sukayi dashi, sosai sukayi farin ciki. D,P,O yace yauwa zansa yarana suzama cikin shiri anjima semu tafi. Godiya sukayi mashi. Sannan suka tafi. Ahanya Sameer yakira Alh, yafada mashi duk yanda sukayi, yaji dadi sosai yace Allah yakaimu daren.
Jungle ne yashiga dakin Figo, yana shiga Figo yayi saurin zuge jakar kudin daya daga, yamaidata, Jungle ya washe baki yace Oga ko kudin kake kara kirgawa? Ya daure fuska yace a,a wani abu nadauka abayan jakar. Zama yayi yace wlh Oga dama zuwa nayi infada maka ko cikin kudin nan zaka dan bamu wani abu munaso mudan shiga gari muyo siyayya.
Wani irin kallo Figo yayi mashi, yakara hade rai yace, kaga malam sauraramun, tunda mukazo kaga nadauki kudin nan nayi amfanin kaina dasu? Kuma duk abubuwan da kukeci ai acikin kudin ake maku, shine yanzu zasu turoka, kai me baki kazo ka amsar maku kudi ko? To babu wanda zanba ko sisi harsemun gama abinda yakawomu sannan aduba abinda yayi saura se abama kowa kasonshi. Sbd haka katashi kabani guri, kuma kafada masu gobe, akwai aikin dazan turaku kuzama cikin shiri. Tashi Jungle yayi ranshi abace yafita. Figo yace ashema wahalar danakeyi abanza indauki kudi inbaku.
Baba mairo tace kai duniya, lallai idan baka mutu ba, zakaga abubuwan mamaki dayawa, wai wannan tabewa dame tayi kama ace Kawu mahaifinka yake nemanka, ada yaso yanemi mamanka yanzu kuma yadawo gurin 'Ya. Sameer yace wlh kuwa Baba, nima kaina abun yana damuna, shiyasa ana kamasu baza,a bata lokaci ba, za,a turasu kotu. Saleem yace wlh da za,a barni da dukansu kashe su zanyi. Umman Sameer tace a,a ka kyalesu shari,a ma ta ishesu. Allah de yabaku ikon kamasu.
Kawun Sameer yace duniyace yanzu babu gaskiya, shiyasa komai ya lalace mana, tunda har aka iya samun Uban da yayi zina da yarshi babu abinda baza,a iya samu ba, mude mudage da addu,a akan yayanmu. Allah yakara tsaremu baki daya. Suka ce ameen.
Jungle yace wlh wannan karon hakurina yazo karshe, kutumar....., yama gama raina mana wayau, dazu fa inajinshi zanshiga dakin naji yana tare da mace, sena tsaya kusan dubu 100 yabata, kuma acikin kudinne. Shine muda mukasha wahala baze bamu ba, ti wlh sede kowa yarasa, amma bazan barmashi kudin ba. Suduka sukace ai dama Jungle kaine kake hanamu, da tuni mun gama mashi aiki, dammu munfison kazama Oga da wancan tsohon maci amana ne, mukam babu wanda yataba cin amanar wani nashi, wama yasani ko abinda yayi ma dan yayanshi ne alhakin yake binshi shiyasa kome muka samu baya zama, amma shekarar mu nawa muna fashi ace haryanzu ko yar mota babu wanda ya mallaka.
Kana ganin wadda muka siya akayi hadari da ita, tundaga ita bamu kara samun wata ba, sede musami kudi shikuma yabama mata. Jungle yace ka kyaleshi kawai wlh shima tashi tazo karshe, ayau zamuyi mashi abinda yayima yaron yayanshi. Ayau zesan zafin cin amana, kuma mu dauke kudin muyi tafiyarmu, babu wani gidan dazamuje, dama can rashin tausayi ne irin nashi amma ace wai diyar danka ita zaka nema saboda yana dan akuya. Kuzama cikin shiri, karfe 8 zamu dirar mashi, kuma ayau zamu bar garina nan.
Da misalin karfe 7: 30 D,P,O yagama tara yaranshi yayi masu bayanin komai, su Sameer kawai suke jira, basu dade ba, segasu sunzo hada Alh, da Jidda, bayan sun gama gaisawa yayi masu bayanin yanda suka shirya komai. Alh, yace amma kasan dole semun fara samun Manager na hotel din sbd aka ida bekamata police su shiga gurin mutum babu izininshi ba. D,P,O yace wannan Alh, ba matsala bace, nasan manager din damunje se yaran su tsaya awaje mufara samunshi, nasan baze bamu matsala ba. Tashi sukayi kowa yashiga motarshi suka nufi Hamdala Hotel.
Sede ince Allah yabada sa,a.
Urs.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525268
🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ ( H,O,N,A)
Part 145..... 150
Kwance yake daga shi se kajeran wando, wayarshi yadaga yakira Jidda, bugu 2 tadaga, Haba yan matana naga har 8 takusa amma najiki shiru kada de kicemun kinfasa. A'a ban fasa ba, ina hanya. Toshikenan sekinso.
Turo kofar dakin da akayi ne tasashi saurin kallon kofar. Jungle lafiyade zaku shigomun daki haka? Abinci ne, nasa ankawo maku, idan kuma aikin danace zansaku ne, bayau bane se gobe. Wai lafiya inata maku magana amma kun mani shiru? Hahhhh Oga Jungle yimashi bayani. Oga? Waye kuma wani Oga? Akwai Ogan daya wuceni?
Ada ba, amma yanzu Jungle muka sani da Oga. Jungle wai meye haka kamun magana mana. Kafa yasa yataka saman gadon da Figo yake kwance yayi, sannan yaciro sigari daya daga cikinsu yayi saurin kunna mashi ita. Seda yazuketa ya fesa mashi hayakin sannan yamikama na bayanshi hannu, wata sabuwar wuka mesheki yadora mashi ahannu.
Ganin wannan wuka bakaramin tsoratar da Figo yayi ba, lokaci guda yatashi zaune yace haba Jungle kasan fa bama irin wannan wasan, daga magana kuma meyako afito da wuka? Murmushi Jungle yayi yace aikai ba abokin wasa na bane bare inyi wasa da kai, kawai munzo muyi maka abinda kayima dan uwanka ne.
Zufa ce tafara keto mashi tako ina, yace dan Allah kuyi hkr haba jama'a yau shekararmu nawa muna tare amma ace rana daya kuzo mani da wannan magana. Idan ma matsayina kakeso wlh yanzu zan sauka inbaka, Jungle yace a,a kawai mungaji da tafiya da kaine, kuma ashekarunka yakamata ace kaima kana kabarinka yanzu kasamu ka kwanta kahuta.
Dariya suka sa, Jungle yace ina jakar kudinan take? Da hannu yayi mashi nuni, dan bakinsa yakasa magana, daukota yayi ya bude. Lallai kam kaci kudi dayawa, to bara kaji wlh kaci rabonka, mikama nakusa dashi yayi yace aje mana ita, yanzu zamu bar garinma.
Su Sameer suna zuwa bakin hotel din sauran yan sandan suka tsaya daga waje, su D,P,O da Alh, dasu Sameer ne suka shiga ciki, tambaya sukayi ko manager yana nan, akace yana ciki, kaitsaye suka nufi office dinshi. Bayan sungama gaisawa anan D,P,O yayi mashi bayani. Cike da tashin hankali manager yace ikon Allah, wlh bansan dasu a hotel din nan ba. D,P,O yace kada kadamu, kasan ba'a gane mugu afuska, mugodema Allah daya tona asirinsu ma. Manager yace amma gsky naji dadi, kuma nagode. Awane room kukace suke?102, Ok babu damuwa zaku iya zuwa. Godiya sukayi mashi suka fita.
Kafa Jungle yasa yatake cikin Figo, sunsa kyalle sun kulle mashi baki, hawaye kawai suke fita a idonshi. Hannu yahada alamun suyi hakuri. Wani yace Jungle muna bata lokaci fa, kawai aikata mashi shima. Yauwa abokina yama wannan AYAR danaji wani malami yana fadama wasu? Wace kenan? Kaini larabcin ne yakemun wahala, abinda kayi za,ayi maka ko? E e hakane, nima namanta Larabcin. Kuka sosai Figo yakeyi sede babu sauti.
Wuyanshi Jungle yakama babu tausayi yasa wuka yayi mashi yankan rago, jini yafara zuba, dede lokacin wayarshi tafara kara, daukarta Jungle yayi yace Hahhhhh mace ce, kashewa yayi yace kawai muware.
Suna murda kofar suma su Sameer suna tsaye, saurin komawa ciki sukayi, nan D,P,O yayi ma sauran yan sandan waya yace sushigo, Rarraba idanu su Jungle suka fara zarowa. Kwance suka sami Figo acikin jini, nan sukayima manager waya, shima yazo, bed sheet sukasa suka rufeshi.
Jidda kuwa kasa shiga dakin tayi haka tajuya takoma cikin motarsu, se kuka takeyi tana kara danasanin irin rayuwar datayi. Cikin lokaci kankani aka tasa keyarsu aka nufi station dasu, shikuma Figo aka nufi asibiti dashi, gaba daya mutanen Hotel din mamaki sukeyi kowa yana Allah wadai da halinsu.
Gaba dayansu zaune suke a babban falon dayake kusa da office din D,P,O sukuma su Jungle suna tsugunne, D,P,O ya kallesu yace banason mubata lokaci, kunsande munkamaku dumu dumu acikin laifi ko? Dan haka banaso kubama kanku wahala muma kubamu, kai, yanuna Jungle, inaso tsakaninka da Allah kayi mana bayanin abinda yakawo garin nan, da kuma bayani akan wanda kuka kashe.
Jungle yace tabbas yau nasan asirinmu yagama tonuwa, saboda haka bazan tsaya batama kaina lokaci ba, nine nan nakashe shi, kuma tare muke dashi shinema Oganmu............. Anan Jungle yafada masu komai da Figo yayi ma Baban Falak, sannan yafada masu yanda akayi suka san inda Falak take, da kudin dasuka samu, har yanda akayi sukaje gidan Alh, da abinda Zarah tayi. Kuma yasheda masu ita tabada kudi da hotonsu akaisu gurin boka.
Nan take Alh, yaji wata zufa tana fito mashi. Jungle yace muma yaci amanarmu shiyasa muka kashe shi, kuma ashirye muke damu amshi duk wani hukunci daza ayi mana. Kowa agurin seda yayi mamakin irin halin rashin tausayi na Figo. D,P,O yace to Alh, kunje de abinda yafaru, dan haka bazamu bata lokaci ba zamuturasu kotu, wannan kuma tunda yarasu, kawai zamuje ayardashi. Wadannan kudi kuma Alh, Allah ne yamaido maka da abunka, dannasan nakane, babu ta inda matarka zata samesu haka, amma zaka iya kaimata seta fada maka inda tasamesu. Sauran hukunci kuma yana gurinka, sede muce Allah ya kyauta.
Gabadaya Alh, kunya takamashi gashi agaban sirikanshi har 2 duka sunji bakin hali irin na matarshi, nan take yai tsanarta tashiga zuciyarshi, fita yayi batare dayace komai ba, yanufi motarshi yanufi gida zuciyarshi tana zafi.
Sameer da Saleem sukayima D,P,O godiya yabasu jakar kudin sukatafi, amota suka sami Jidda se kuka takeyi, Saleem yace dan Allah yaya Jidda kukan nan ya isa haka, keme yayi zafi maganinshi Allah. Sameer yace zakija ma kanki ciwo, kiyi hakuri hakanan. Tace haba Saleem, yanzu idan Dady yaji abinda na aikata nasan kasheni kawai zeyi, gashi zamu hada mashi zafi 2, dole yanzu yasan abubuwan da Ummi ta aikata, ina zesa kanshi? Wannan tashin hankali dame yayi kama? Kaiconmu, Dady beyi sa'ar mata da diya ba, gashi yarinyar dana raina na tsana yanzu itace zata zama abun alfahari agurin Dadynmu bani ba. Jalila kam taji dadinta dabata bari shedan yayi mata hudubar banza ba. Suduka seda sukaji tausayinta. Sameer yase ya isa haka......
Wayarshi ce tayi kara, yana dubawa yaga Alh, ne yake kiranshi yana dagawa yaji muryarshi tana rawa, yace hello, Alh, yace yauwa Sameer kadauko Falak da Kawunka, kuduka de kutaho gidana inason ganinku, yace to.
Sameer yace Saleem muce gidanmu tunda mota ta tana can se indauketa Alh yace mutaho dasu Umma , Falak da Kawu. Jidda tace innalillahi Wa inna ilaihir raji'un. Shikenan watan tonan asirinmu yakama😭😭😭.
Urs,
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🙆🏻😭😭🙆🏻AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ ( H,O,N,A)
Page 150.....155
Hannu bibiyu Alh yasa yadafe kanshi, gabadaya jiyake duniyar tamashi zafi, wani abu ya tsaya mashi a makoshi, wanda daze samu yawuce dayafi jin dadi. Kuka yakeso yayi amma sam hawayen sunki zuwa, tabbas kuka ma rahamane.
Zarah data shigo falo tace a,a Alh yaushe kashigo banji shigowarka ba? Shiru yayi bece komai, dan yanda yakeji idan yabude baki komai ze iya fada mata. Zama tayi kusa tashi tace magana fa nakeyi amma kayi shiru ka kyaleni. Ko baka da lfy? Wani ne ya mutu? Duk tambyr datake mashi hakan besa yadaga kai ya kalleta ba. Cike da masifa tace wai Alh, mekake nufi......
Sallamar da akayi ne, yasata hadiye sauran masifarta. Juyawa tayi tana kallon kofa jin sallamar bata mutum daya bace, baki ta saki ganin mutanen dasuke shigowa. Mamakinta be karuba seda taga Baba Mairo tashigo gata tayi kyau cikin shiga me kyau.
Samun guri sukayi gaba dayansu suka zauna, yaran kuma suka zauna akasa, haryanzu kan Alh aduke yake, guri Zarah tasamu tazauna, gaba daya jikinta yayi sanyi. Wata irin zufa tafara keto mata. Baba Mairo tace Alh ina wuni.
Dago kai yayi cike da mamakin ganinta, ahankali yace Baba Mairo. Tace na,am, dama kina garin nan? Murmushi tayi tace wlh kuwa Alh. Gaisawa sukayi dasu Kawu, Alh ya kalli Jidda wadda taketa kuka har idanuwanta sun kumbura saboda kuka. Yace Mamana lafiya kike kuka?
Kara sakin wani kukan tayi ta tashi tamatso kusa dashi tazube bisa guiwowinta, hankalinshi dana Zarah yatashi ganin irin kukan datakeyi. Jalila da Falak suma duk kuka sukeyi dan sun san abinda Jidda takeyima kuka. Dago kai tayi tace Dady dan Allah kayi hakuri kayafemun, tabbas banzamo diya tagari ba, na cuceka na cuci kaina.
Nasan Allah baze taba yafemun ba idan har baka yafemun ba. Nayi dacen Mahaifi nagari amma rashin samun Uwa tagari yasani nima nazama wadda bata gari ba. Alh, yace Mamana wai mekike fada haka ne? Zarah kuwa da cikinta yafara yamutsawa jitake kamar ta nutse dan kunya, agaban sirikinta Jidda take fada mata wannan maganar, jitayi kamar tashakota.
Alh yace ya isa haka mamana, kidena kuka kifadamun wane irin laifi kikamun haka. Zarah tayi saurin fadin a,a Alh, kabarta tashiga ciki tasamu ta kwanta tayi bacci ta huta kasan batada lafiya. Jidda tace, a,a Ummi ya isa haka, kibarni nafadi abinda aka dade ana boyewa agidan nan, garake Ummi kinada lafiyar dazaki iya tuba zuwa ga Allah, nifa? Ina cikin cuta, wadda ko ayanzu Allah ze iya amsar raina.
Tundaga auran Hajjo da fara shigarta cikin halin banza, da abunda Zarah dasu Asabe sukayima Hajjo da Ameer, harsukayi sanadiyar mutuwarsu, dazuwanta London, da irin hudubar da Zarah takeyi mata, zuwa auren datayima Falak da Sameer, da yanda tabama su Asabe kudi, zuwa yanda Zarah ta temaka ma su Figo har cutar datake dauke da ita seda Jidda tafada masu. Gaba daya falon yayi shiru, kukan Jidda, Jalila da Falak kawai akeji.
Zarah kuwa zama tayi kasa kamar meshirin hawa bori, takasa kuka kuma takasa magana, Alh, kawai ta kurama Ido, hatta da Kawun Sameer seda yafitar ma Jidda da hawaye, su Baba Mairo da Umman Sameer suma Kuka, kawai sukeyi. Sameer da Saleem da dama sun san da labarin amma jin sauran labarin seda yasasu kuka.
Alh da haryanzu yarasa gane wai mafarki yakeyi ko gaske gashi haryanzu hawaye sunkasa zuba a idonshi, zuciyarshi jiyake kamar ansamata wani katon dutse. Tabbas daza,a gwada jininshi babu abinda zesa aga be hau ba.
Zarah yakalla da idanunshi dasuka juye tamkar garwashi, kallonta kawai yake amma yakasa magana, Zunbur Zarah ta mike tace a,a wlh kadena kallona Alh, ka tsaya nida kaina zanyi maka bayanin duk abinda nayi, kai tafara sosawa, da jikinta, can kuma tafashe da dariya, tace.
Yo aike Jidda bakima san komai ba,,,,,, nan itama tashiga fada masu irin abubuwan datayi, komai seda tafada, tanayi tana dariya tace Mairo aike baki iya munafunci bama, gashinan kina ganin AGOLAH hada ciki, ai wlh rantsuwa nayi senaga bayanta. Hauka de tuburan Zarah tafarayi, kowa salati yakeyi yana kallon ikon Allah.
Kawu yace Alh,ai inaganin bekamata abarta haka ba, a kamata ayi mata addu,a Alh daseyanzu yayi magana, yace Malam babu abinda zankara yima wannan azzalumar matar, tsakanina da ita sede alahira. Ta cutar dani, taso tasani inkasa rike amanar marainiyar Allah dana dauki alkawari.
Babu abinda banyi mata ba, amma tarasa abinda zata sakamun dashi se wannan rashin mutuncin da cin amana, tabbas ko hakkin mahaifinta kawai ya isa ya tambayeta, bare kuma na baiwar Allah Hajjo, da karamin yaro wanda ko agurin Allah ba,a bude mashi littafin rubuta lada da zunubi ba. Kai!!! Agaskiya bazan boye maku ba Zarah tacutar dani, Allah shine zemun sakayya, kuma gashi tun aduniya tafara gani, idan da tasamu sa,ata dayanzu nakara zama rakumi da akala. Dan haka ni babu abinda zan mata.
Ke kuma Jidda bazanyi maki baki ba, sbd ba laifinki bane, duk da kema kina da laifi, meyasa Jalila batayi abinda Zarah tasakiba? Yanzu ai kinga karshe da kuma illar bariki ko? Ko ahaka Allah yabarki yahadaki da babban aiki, kuma wannan cuta taki idan har bakisha mata magani ba, zakizamo abin kyama agurin mutane. Abu daya ne zesa nazauna agidan nan, shine auren Jalila, amma iname tabbatar maki ina aurar da ita nima zanbar maku garin, bazan iya zama bakin cikinku yakasheni ba. Tashi yayi yana hada hanya, da kyar yashige dakinshi sbd jirin dayake gani.
Zubewa Jidda tayi agurin tana wani irin kuka me tsuma zuciyar me saurare, Jalila ta matso kusa da ita tariketa itama tana kuka, Falak kuwa jitayi cikinta yawani murda kamar alokacin zata haifi abinda ke ciki, kwantawa tayi tasaki wata irin kara tana kara rike cikinta, dasauri su Baba Mairo dasu Sameer sukayi kanta, jini ne yafara bin kafarta, nan take ta sume.
Cike da tashin hankali Sameer yadauketa Saleem da sauran suna binshi abaya, mota yanufa da ita suna shiga Saleem yaja suka nufi asibiti. Gaba daya hankalin Kawu yagama tashi, su Jalila se kuka sukeyi, Zarah tafito kanta ko dankwali babu, se cizgar gashinta takeyi haka tanufi bakin gate. Jalila tace Kawu kate maka mana......
To nimade hawaye sunma fuskata yawa, bara nadan huta😭😭.
Urs.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ ( H,O,N,A)
Part 155.....160
Suna zuwa asibiti aka ansheta aka nufi Emergency room da ita, Sameer hankalinshi bakaramin tashi yayi ba, yakasa zaune yakasa tsaye, Saleem ne yadafashi yace kayi hkrdan Allah, addu,a yakamata muyi mata.
Sameer yace wlh tsoro nakeji kada murasa abinda ke cikin Falak, Saleem yace insha Allah bazamu rasa shiba. Sunfi minti 30 agurin sannan wani likita yafito suka bi bayanshi zuwa office.
Bayan yagama yan rubutunshi yakallesu, murmushi yayi ganin yanda Sameer yayi kamar meshirin yin kuka, yace to alhamdulillahi, munsamu tsayar da jinin dayake zuba, kuma cikin jikinta befita ba. Sede dole ze kara ko sati biyu akan kwanakinshi.
Wani murmushin farin ciki Sameer yayi yace mungode Dr. Yanzu ya jikin nata? Yace dasauki, ansamata karin ruwa tana bacci, zuwa anjima insha Allah zata tashi, sede kada tarika aikin wahala,kuma arika kwantar mata da hankali, magunguna ya basu wanda zasu siyo mata, amsa sukayi suka mashi godiya suka fita.
Zarah kuwa gaba daya tafitar da kayan jikinta, se jan gashinta takeyi, duk tajima kanta ciwo, Jalila se kuka takeyi tarasa yanda zatayi da ita. Kawun Sameer ne yadauko ruwa akofi yayi addu,a ya watsa mata ajiki, nan take tafadi kasa bacci yadauketa. Kamata Jalila tayi takaita dakinta ta kwantar da ita bisa gado.
Wata doguwar riga tasaka mata da kyar, sannan tarufo maka kofar dan kada tafito, dakin Jidda tanufa, dan tunda aka tafi da Falak asibiti bata kara ganinta ba, kwance tasameta ta rufe da zanin gado, numfashinta yana fita dasauri.
Dasauri tahau saman gadon ta budeta, jikinta zafi taji sosai tace Yaya Jidda bakida lfy ne? Kai tadaga mata, sauka tayi taje tadauko mata maganinta, ruwa tadauko mata ta kamata tabata maganin, tana gama sha tayi saurin sauka tanufi bandaki tafara amai, seda tagama Jalila ta temaka mata ta gyara jikinta suka fito, bayan ta kwantar da ita takoma ta gyara bandakin.
Zama tayi tana kallon yanda take fitar da numfashinta kamar zebar jikinta. Wasu zafafan hawayene suka sauko mata, kai ta girgiza tana me tausayin kanta, akan irin rayuwar datake fuskantota, ga Ummi ta haukace, ga Jidda akwance. Ahankali tace Yaya Jidda kozaki shirya muje asibiti? Kai ta girgiza tace konaje asibiti babu abinda zasu mani, kawai kibarni haka. Jalila tace bara inje inkira Dady, hannunta Jidda tarike tace,
A,a Jalila, ayanzu babu abinda Dady yakeso kamar natsuwa, ayanzu yana cikin tashin hankali bekamata kije gurinshi ba, dan yanzu ma Allah kadai yasan cikin halin dayake, Jalila tace haka ne, Jidda tayi murmushi tace kiyi hkr Jalila, zamu barki cikin kuncin rayuwa, Allah yakareki daga sharrin dangin miji, tabbas nida Ummi munbar abin fadi aduniya, amma insha Allahu bazaki tozarta ba, nide ina rokon addu,arki akullum.
Jalila tace bakomai Yaya tunda har Allah yajarabceni da wannan rayuwa yasan zan iya dauka, kuma kema zaki samu rayuwa me kyau, fatana kawai kirika shan maaganinki. Ummi kuma insha Allahu zata samu lafiya. Jidda tace hadomun black tea.
Alh, kuwa tunda yashiga daki jiyayi kamar zuciyarshi zata fito waje, har ya kwanta sekuma yayi saurin tashi yanufi bandaki yadauro alwala yazo yadauki Qur'ani yafara karantawa, yadade yana karatu harseda yaji zuciyarshi tayi dadi sannan yatashi yayi raka,a 2 yayita rokon Allah akan yadora mashi duriya da dangana aduk halin daze shiga.
Jin falon yayi shiru ne, yatashi yafito, akofar kitchen yaci karo da Jalila, wani sabon tausayinta yakara kamashi, kasa kallon idonta yayi yace ina su Falak? Ana tafada mashi abinda yafaru, yace to ina Jidda take fa? Tace tana daki ita zankai ma tea ma, ze kara magana yaji wani sabon kuka yazo mashi kawai yajuya yatafi.
Da kallo Jalila tabishi itama tana kuka, dan taga lokacin da hawaye suka taho mashi.
Awaya yakira Sameer ya tambayeshi jikin Falak, Sameer yace dasauki yafada mashi duka abinda likita yafada. Alh, yace toshikenan idan naji dama dama zanshigo.
Zaune Falak take gefenta Baba Mairo da Umman Sameer ce zaune, sesu Sameer da Saleem zaune abisa kujera, Baba mairo tace sannu Falak, inaso ki kara hkr akan wanda kikeyi, Allah yana kallonki baze bari kishiga wani hali ba, inaso kidauki duk abinda yawuce yazama tarihi. Kada kisaka wani abu aranki yazo yadameki.
Ita kuma Zarah kome tayi dan kanta, gashi nan tun aduniya Allah yafara nuna mata ishara, sede abu daya nakeso kisani, ana barin halak kodan kunya, wlh tausayin Jalila nakeyi saboda zata shiga wata irin rayuwa. Kallon Saleem tayi tace dan Allah kada abinda yafaru yasa wani tunani yashiga ranka, nasan kasan komai akan Jalila tunkafin abaka aurenta, inaso kaji tsoron Allah, kuma kamar yanda wannan abu yafaru acikin gida inaso kabarta agida.
Saleem yayi murmushi yace wlh Baba babu abinda yaragu akan son danake ma Jalila, sema karin tausayinta danaji, kuma insha Allah babu wanda zeji wannan maganar abakina.
Sameer yace bara muje muyi sallah damun dawo zamu tafi gida dan banason ta kwana anan, Ummanshi tace a,a idan bataji sauki ba, babu inda zataje, Baba Mairo tace a,a tunda de komai lfy ai gara mutafi gida zefi, nima banason zaman asibitin.
Bayan mintuna 30 Zarah tafarka daga baccin da takeyi cike da firgici, sauka tayi daga kan gadon tanufi hanyar fita, sede taji kofar arufe,komawa tayi tacigaba da daukar duk wasu kayan bisa dressing mirror dinta tana fasawa, hatta da madubin seda tasa hannunta tafasa shi, duk tajima kanta ciwo, jawo sif dinta tayi cikin tsautsayi tafado mata akafarta ta dama, tundaga kwaurinta, wata irin kara tasaki wadda har megadi seda yaji.
Kasa tafadi, tana ihu, gashi takasa cire kafar daga karkashin sif din. Megadi da driver suka shigo suna sallama, Jalila tafito itama lokacin taji ihun Zarah, suka ce lfy? Wlh nima bansani ba, nade barta tana bacci sede naji ihunta, bayanta sukabi.
Tana bude kofar tasaki salati suduka sukabi bayanta, jini ne kwance akasa, Zahar hartayi shiru sbd azaba, dasauri Jalila takarasa gurinta tana kuka, megadi da driver sukayi saurin daga sif din, ai nan sukaga kafarta ta datsa biyu, kamar ansa gatari an fasa, jikin kaurinta shima harkashin ana gani, kafar se reto takeyi.
Jalila tafita tanufi dakin Dadynsu tana kuka, yana ganinta yace Jalila lafiya de? Cikin kuka tafada mashi abinda yafaru, sosai yaji tausayin Jalila, haryayi niyar kyaleta sekuma yatuna mahaifiyarsu ce, yace shikenan kije kicema driver sukamata sukaita mota inazuwa.
Amotarshi yashiga yace suwauce asibitin, Jalila tana rungume da ita, Zarah tayi shiru se hawaye take fitarwa, suna zuwa asibiti aka karbeta aka nufi accident room da ita, ana akayi mata allura tayi bacci.
Likitan yanufi Alh, yace suje office. Bayan sunzauna yace agaskiya Alh, sede ayanke kafar matarka, sbd kashi kafar yariga daya rabe 2, fata ce kawai tarike sauran rabin kafar, amma shi ciwon kaurin za,a iya mata dressing sbd kashin tsagewa ne kawai yayi. Kuma naga kamar tana da matsalar tabin hankali ko? Alh, yace Dr, inaso kuyi duk abinda zaku iya wanda yadace, babu ruwanka da matsalar haukanta, ita tajama kanta, yanzu haka ba matata bace kawai darajar 'Ya'Yanta zataci. So banason yawan tmby. Dr yamika mashi takarda yace yasa hannu, Alh, yace bara inkira diyarta taji da bakinta, sbd yanzu kome zanyi za,aga kamar nayi da wata manufa ne.
Fita yayi domin yakira Jalila.
Urs,
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady )
08028525263
🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ (H,O,N,A)
Part 160.....165
Shiru Jalila tayi tana hawaye jin bayanin da Dadynsu yayi mata. Tace shikenan Dady muje insaka hannu. Shiga sukayi Dr, ya mika mata takardar tasaka hannu. Anan Alh, yabiya duka kudin aikin dana magani. Dr, yace zaku iya tafiya dan aikin zedauki lokaci, Alh, yace to mungode, muje Jalila.
Zaune suke afalo Kawu yagama yi masu bayanin abinda Zarah tayi bayan tafiyarsu. Falak tace wlh tausayin Jalila nakeyi, Allah de yabata lfy. Baba Mairo tace ita tajama kanta, kuma gashi duniya tana koya mata hankali, sbd alhaki nawa Zarah tadauka akanta, harna mahaifinta fa, kwata kwata tamanta dashi arayuwarta.
Nide yanzu Malam abu daya nakeso aduba akalli mutunci irin na wannan yarinya Jalila, atemaka ma Zarah da addu,a tasamu lafiya.
Kawu yace bakomai, bawani abu bane yake dawainiya da ita ba, se aljanu, kuma sihirin datayima wasu ne, yanzu aljanun suka dawo kanta. Bakomai insha Allahu zamuyi bakin kokarinmu, babu abinda ya gagari Allah.
Saleem yacema Sameer bara inzo inwuce, Falak Allah yakara sauki, sallama yayi masu suka fita shida Sameer. Saleem yace zanje gida idan na huta zanje indubo Jalila dan tundazu nake kiran wayarta bata dauka ba, nasan tana cikin damuwa. Sameer yace shikenan kayi kokarin kwantar mata da hankali plsssss.
Jalila tana shiga daki tasamu Jidda kwance cikin amai, gashi ta bata jikinta da zawo, cike da tashin hankali ta juya tanufi gurin Dadynsu. Atare suka shigo dakin. Kai Alh, yadafe ganin halin datake ciki. Allahumma Ajirni fi musibatihi haza, Wa aklifini khairan minha.
Itace addu,ar da yarikayi azuciyar shi, yace Jalila kiyi hkr kitemaka mata ta gyara jikinta semutafi asibiti, kada kisa damuwa azuciyarki, kirika addu,a zaki samu sauki. Fita yayi yajirasu afalo. Zama yayi yadafe kanshi, yarasa inda zesa kanshi.
Waya yadauko yakira kanin babanshi yana dauka kawai yasa mashi kuka, se alokacin kukan dayake so yayi yazo mashi jin kamar muryar babanshi. Cike da tashin hankali yace Abba lfyrka meyake faruwa kake kuka? Shiru yayi yacigaba da kukanshi, Kawunshi yace shikenan ya isa haka, koma menene tunda ina gari ganinan zuwa.
Kashe wayar yayi ya kwanta bisa kujera yacigaba da kuka sosai, seda yayi me isarshi sannan yaji dadi azuciyarshi, duk wani nauyi dayakeji ada yanzu yaji sauki, tashi yayi yashiga bandaki yayi wanka, yashirya yasamu su Jalila sun fito suka tafi.
Suna zuwa yanda likita yaga jikin Jidda yace dole abata gado, nan aka kaita wani private room sbd yasan matsalarta. Ruwa aka samata da allurai, nan take bacci yadauketa. Alh, yace Jalila muje gida, tace to.
Suna zuwa yasata tayi masu girki yace tazubo yasata tazauna, atare suka ci abincin yana lallashinta, shima daurewa kawai yakeyi, ahaka suka gama cin abincin Jalila ta kwashe kayan, Alh, yace yauwa idan kinyi wanka semutafi ko, dan dare yayi, tace to.
Bayan tagama tadauki abincin Umminsu dana Jidda kasancewar asibiti daya suke, suka tafi.
Sadda sukaje har angama ma Zarah aikin ankaita dakin hutu, ana Dr, yafada mashi komai yayi dede amma dole akula da ita sosai sbd karta fama kafar. Godiya yayi mashi yanufi dakin Jidda.
Zaune yasameta Jalila tana bata tea, yace sannu Mamana, kallonshi tayi idonta cike da kwalla, tace yauwa Dady. Zama yayi, Jalila tace Dady ya Ummin take? Yace bacci takeyi kuma komai lafiya angama asa,a zata iya kai gobe bata farka ba, sbd haka kizauna agurun Jidda ku kwana tare. Tace to Dady, yace bara inzo intafi dare yayi kuma Kawu yamun waya yana jirana agida. Sallama yayi masu yakawo kudi yabama Jalila yafita.
Bayan sungama gaisawa Kawu ya kalleshi yace Abba lafiya kuwa nazo gida kuduka bakwanan, gashi kamun waya kana kuka, seyanzu dana ganka nakara tabbatar da babu lafiya dan ayanayin dana ganka nasan bacikin kwanciyar hankali kake ba. Kai Alh ya girgiza yace wlh kawu wani iftila,i ne yasameni alokaci guda, shiyasa narasa yanda zanyi da rai na............. Anan ya kwashe komai yafada mashi, babu abinda yaboye mashi har labarin Jidda.
Innalillahi Wa inna Ilaihirraji'un. Shine abinda Kawu yaketa fada. Yace lallai Abba ka hadu da wata irin jarabawa wadda bakowa bane ze iya irin wannan dauriya dakayi. Kada kadamu insha Allahu komai ze zama dede, kuma kada kasa abun aranka harya haifar maka da wata matsala, bara inzo intafi dare yayi, kome kenan goben zan sameku asibitin. Yace nagode Kawu, sallama yayi mashi yarakashi bayan yatafi yadawo cikin gida.
Urs,
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ (H,O,N,A)
Part 165.....170
Washe gari tunda asuba Zarah tacika asibitin da ihu, sbd tafarka kuma babu kowa akusa da ita, gashi allurar da akayi mata tasaketa, hatta daurin da aka yimata na kauri tafara cireshi, hauka sosai takeyi.
Duk da zafin datakeji hakan besa ta nutsu ba, abunka da hauka, dakin duk ya baci da jini. Cikin sauri aka shigo dakin, wasu nurse ne guda 2 mata, duk yanda suka so riketa abun ya gagara, nema take taji masu ciwo, daya ce tafita domin kira maza.
Atare suka shigo da wani Dr, tare da wasu maza cleaners 2, kamata sukayi da karfi suka zaunar da ita, Dr, yaduba file dinta, anan yace ma dayar nurse din takawo mashi allura, ko minti 5 ba,ayi ba takawo, amsa yayi tare da zuba ruwan yayi mata, cikin mintuna kadan bacci yadauketa.
Dr, yace wannan matar akwai hauka ajikinta, dama kuma jiya Dr, yafada mani kuma dole se ansamu wadan da zasu rika kula da ita sosai idan ba haka ba, wannan kafar zata bamu matsala, yanzu dole kusake mata wani dressing din. Nurse suka ce to. Yace bara na kira mijinta awaya na fada mashi tafarka dan me kula da ita yazo.
Jalila tace sannu Yaya Jidda kitashi in hada maki ko black tea ne kisha kinga tunjiya kike amai, kalli yanda kika koma acikin kwana 1, dan Allah kidaure kici abinci kisha magani kozaki samu sauki, wlh bazan iya daurema wannan rayuwar datake fuskanto ni ba, kinga Ummi tana can kwance kema kuma kice bazakisha magani ba, ai abun seyayi mani yawa, tunda Dady babu ruwanshi da Ummi.
Murmushin karfin hali Jidda tayi tace wlh Jalila nikaina ayanzu inaso in rayu kodan intayaki jinyar Ummi, inaso inrayu kodan nima nayi aure nasamu yarana, inaso inrayu kodan insamu damar neman gafara agurin Ubangijina. Amma nasan namakaro, domin sama tayima yaro nisa, nasan kwanaki na kadan suka ragemun, fatana Allah yakarbi tubata kafin in mutu. Kuka duka suka saka, babu me lallashin wani.
Jidda tace kinyima Baba na Zariya waya kuwa? Jalila tace na masa, yace yau dasafe zetaho. Kai cona, shima wannan bawan Allah ban daukeshi da daraja ba, na dauki hudubar Asabe, wadda itace tayi sanadiyar fadawar Ummin mu cikin wannan halin, duk da hada laifinta amma Asabe ce Babbar me laifi. Jalila tace bakomai insha Allah Ummi zata samu sauki.
Jidda tace gashi yau saura kwana 5 bikinki Jalila kuma ga halin damuke ciki, tabbas mun saka rayuwarki cikin takura. Jalila tace wlh niyanzu auren yafuta arai na, kuma koyanzu baza,a daura ba, harse kunsami lafiya. Jidda tace wlh kada ma kifara, aure kamar anyishi angama ne, bakison inga bikinki kafi Allah yadauki raina?😭, Shiru Jidda tayi tana kuka, Jalila takara matsowa kusa da ita tace Yaya Jidda dan Allah kibar maganar haka nan, kitashi muje kiyi wanka kiyi brush kisha tea, nasan Dady ze kawo mana abinci sekici.
Jikin Falak yayi sauki dayake agidansu Sameer suka kwana hakan yasa gurin karfe 9 suka shirya su duka suka nufi asibiti, dan Sameer yayi waya da Alh, yafada mashi suna asibiti, tafiya suke ahanya, Baba Mairo tace dole ni nazauna agurin Zarah dan nasan babu kowa agurinta, tunda nasan Jalila tana gurin Jidda, Falak tace toni se nazauna agurin Yaya Jidda. Sameer yace babu inda zaki zauna haka nan kawai ki kwaso mana cuta. Umman Sameer tace gsky kam Falak kiyi hkr zaki rika zuwa dubata amma batun kizauna betaso ba, kema haka nan karfin hali kikeyi amma duka yaushe kika warke.
Kawu yace hakane, kiyi hkr idan yaso ke Halima sekiyi masu kara kizauna agurin Jiddan, kema Allah zebaki lada, amma wlh nima ina tausayin Alh, dole kowaye Allah ya jarabta da irin wannan abu yashiga tashin hankali, kuma sbd shi da diyarshi zan nema mata magani, amma da munbarta duniya ta koya mata hnkli, duk da ayanzu ma tafara gane kuranta, tunda ance anyanke mata kafa. Umman Sameer tace ai bakomai yanzu suma sunzama yan uwanmu. Allah yakara basu lfy.
Malam Garba mahaifin Zarah da Alh, ne suka shigo asibitin, kasancewar ya iskeshi agida shine suka taho tare. Mal. Garba yace dan Allah Alh, kayi hkr da irin abinda wannan yarinya tayi maka. Babu irin yanda banyi da ita ba, amma bataji magana taba, tabbas babu abinda zance tsakanina da Asabe sede ince Allah ya isa, duk da kacemun ankashe su, amma bazan yafe mata ba, ita da kawarta, sun cuceni, gashi seda cutar takai harzuwa diyata, duk da itama da laifinta amma Asabe babbar annobace agidana.
Alh, yace bakomai Baba, Allah yakara basu lfy. Yace ameen, kuma hukuncin daka dauka akanta kayi dede, nima dande kawai zuciyar Imani amma da ko zuwa bazanyi ba, to Jalila tayi tamun kuka, kuma ina son Jalila, shiyasa nace zanzo sbd ita. Amma tabbas idan ta warke sede taje wani gurin tayi haukanta amma ba gidana ba. Alh, yace kayi hkr muje de muga jinkin nasu.
Suna shiga suka wuce Office, anan Dr, yayi masu bayani. Alh yayi shiru dan yana kunyar mal. Garba, ganin yayi shiru Babanta yace to ai ita tasani, kuyi mata abunda zaku iya kawai ku sallameta. Alh yace a,a Baba baza,ayi haka ba, Dr, inaganin abinda ze faru zansamu wani malami zamuyi maganar dashi dan gsky haukanta bana asibiti bane, kome kenan zanzo mukara magana. Dr, yace gsky dayafi, dan tana cikin wani hali, kome tayi kubarta da halinta amma ceton rai zakuyi kuma kamar jihadi ne, koba komai ai Uwar yaranka ce, kai kuma Baba ai diyarka ce, kasan da mahaifiyarta tana nan kome zata zama bazata iya barma duniya ita ba. Jikin Baba yayi sanyi yace haka ne, likita, kuma nagode da tunatarwar dakamun. Allah yamana jagora. Fita sukayi suka nufi dakin Jidda.
Adakin suka sami su Falak harsunzo, bayan sungama gaisawa, Alh, yace Jalila yajikin nata? Tace to Dady dasauki za,a ce, amma kome taci amai takeyi, yakalli Jidda gaba daya tausayinta yakara kamashi yace sannu Mamana, tace yauwa Dady, kidaure kirika cin abinci maganin baze maki amfani ba, idan baki cin abinci. Kuma banaso kirika saka damuwa akanki, mutane nawa suke dauke da irin cutarki gasunan muna hudda dasu wasu ma harsun fimu lfy da kyan fata, babu wanda ze kallesu yace suna da wata cuta. Meyasa suka zama haka? Sbd suna shan maganinsu, kuma suna cin abinci me kyau, dan haka kicire komai aranki, nide nayafe maki, insha Allahu zaki samu lfy.
Baba Mairo tace yanzu Alh, yajikin Zarah? Yace to banje ma naganta ba, dan Dr, yace mun sunyi mata allurar bacci, dan da asuba data tashi haukan yadawo sabo, duk tajima kanta ciwo, kuma ta fama ciwon kafarta, shiyasa yace dole asamu wanda zerika kula da ita.
Baba Mairo tace bakomai Alh, kome zamuyi, zamuyi ne, dan Allah da kai da kuma yaranta. Nizan zauna agurinta ita kuma Halima zata zauna agurin Jidda, tunda Jalila tayi yarinta ace tayi jinya. Alh, yace to mungode sosai Allah yasa da alkhairi. Baba Mairo tace, ammade bikinta dagawa za,ayi ko? Alh, yace ina tunanin haka, duk da nariga dana gama gayyatar abokanaina, amma tunda lalura ta gifto dole adaga.
Mal. Garba yace a,a baza,ayi haka ba, wannan yarinya ta dade ana shiga hakkinta, acikinsu babu wanda tacema yashiga rayuwar da yayi, dan haka saboda su baza,a daga bikinta ba, acikinmu waye yasan lokacin dazasu warke? To kuma kawai se ashiga hakkin baiwar Allah ace sesun warke za,ayi bikinta. Shima mijin ai anshiga hakkinshi, yagama fada ma kowa nashi, ai bikin magaji baya hana na magajiya, dan haka abar bikin nan da kwana 5 kmar yanda akasa, Allah yabasu lfy.
Alh, yace shikenan dama gani nayi kamar Jalilan bataso ayi acikin wannan halin shiyasa zan daga, amma shikenan ke Jalila kiyi hkr, nasan bazakiji dadi ba, ace za,ayi bikinki a irin wannan yanayin komai zezo karshe, ranar asabar za,a daura aurenki kuma aranar za,a kaiki. Kuka Jalila tasaka ta tashi tafita, seda tabama kowa tausayi adakin.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ ( H,O,N,A)
Part 170.....175
Haka suka wuni a asibiti, Falak da Jalila ne, suka koma gida suka yomasu girki, Kawun Sameer kuwa dakin Zarah yaje shida mal, Garba da Alh, anan yafara yimata addu,oi, shiyasa lokacin data farka batayi wani hauka me yawa ba, Baba Mairo tana gefenta ita tarika bata abinci da kyar taci sbd wasan datakeyi.
Lokacin da Saleem yazo shida Sameer bayan yaduba jikin Jidda yakira Jalila suka fita waje, cike da tausayi ya kalleta yace my dear wlh harkin rame. Murmushi tayi tace ba dole ba, yace haka ne, dazu munyi magana da Sameer har nake cemashi koza,a daga bikinmu ne, yace mun a,a Dady yace baza,a daga ba. Jalila tace nima naso adaga amma Baba na Zariya yace a,a.
Saleem yace babu damuwa ki kwantar da hankalinki babu abinda ze gagara insha Allah, fatanmu de Allah yabasu lfy, tace ameen. Yanzu mekike bukata, nasande bawani abu kikace zakiyi ba ko? Tace hakane, walima ce kawai zamuyi da yan islamiyarmu, yace shikenan idan nabaku dubu 100 yayi ko? Murmushi tayi tace basuyi yawa ba? Harararta yayi yace bansani ba, anfada maki bikin wasa zanyi, wasu ma a party kadai suke kashe abinda yafi haka, seni daza,ayi walima zakice wai sunyi yawa. Tace tonaji maida wukar, Allah yasaka da alkhairi, yace yauwa ko kefa.
Sameer yafadamun duk abinda yafaru jiya, kuma munyi magana da Abbana sede banfada mashi komai ba, kawaide nace ba,a san abinda yasamu Ummi ba, kuma yakira Dadyn ma sunyi magana, yace zeshigo yadubata se Dady yace a,a yabari tunda saura kwana 4 daurin aure seyayi zuwa daya. Kwallan dasuka zubo mata ta goge, tace nagode, bansan dawane baki zanyi maka godiya ba. Yace bakida bakin yimani godiya sbd kinbiyani dakika amince zaki aure ni. Amma inason inrokeki wani abu 1. Wannan yawan kukan da kikeyi yayi yawa, dan Allah kidena, nasan dole ne, amma inaso kiyawaita fadin Innalillahi wa inna ilaihirraji'un aduk lokacin da kikaji wata damuwa tadameki. Tace shikenan nagode.
Haka suka cigaba da jinyar Zarah da Jidda, jikin Zarah kam ana samun cigaba, amma jikin Jidda ba sauki, duk ta rame tayi baki, idan kaganta bazaka ce Jiddar daka sani bace, haryanzu aljanun jikin Zarah basuyi magana ba, sede haukan dasauki, tana samun sauki aduk lokacin da ake mata addu,a amma idan har bakowa agurinta haka zakaga kafarta tana fitar da wani irin ruwa marar kyau, kuma aranar se ansake wani gyaran dan ta kafarta suke cutar da ita, shiyasa har yanzu kafarta kamar sabon ciwo ne.
Hakan yasa Kawu yace ma Alh, dole zeyima wani abokinshi Babban malami ne, kuma yana da sani sosai akan harkar aljanu, Alh, yace to amma abari bayan biki seyazo.
Kasancewar bawani cikin keanciyar hankali ake ba, hakan yasa Jalila bata samu gyara sosai ba, sede duk da haka Falak tana kawo mata wasu abubuwan sha tana sha, Falak takaita gurin saloon akayi mata, takira wata me kunshi tayi mata, duk da ta rame amma tayi kyau sosai, duk wani shiri da za,ayi na Walima wata kawarta yar ajinsu ta mika ma komai Bilkisu, tare da wata Farida, duk ajinsu daya, malamansu da Sameer sune suka shirya komai, kuna anan makarantarsu za,ayi walimar.
Ana gobe daurin aure ranar juma,a kenan wanda kuma aranar da karfe 4 za,ayi walimar, zaune suke adakin Jidda, tana kishingide tana shan kankana, fuskarta har wasu kuraje sun fara fito mata, kadan kadan tana goge kwallar datake fito mata. Falak tace Yaya Jidda dan Allah kidena wannan kukan, babu ranar dazata zo bakiyi kuka ba. Jidda tace Uhm Falak kenan, nikadai nasan menakeji araina, da jikina. Kamata yayi ace hadani akae wannan hidimar bikinta Jalila, amma sbd son zuciya da biyema rudun duniya kalli yanda nadawo, ina nan kwance za,ayi bikin Jalila, wanda gashi de da raina amma banida ikon halartar bikin, wannan kadai ya isheni ishara.
Kalli Ummi, duk yanda taci buri da bikin nan, amma gashinan son zuciya da rudun duniya itama ya kamata ahannu, har garani nasan me akeyi, amma ita batasan meke faruwa ba, kuma hakan bazesa adaga bikin ba. Lallai mun ishi duk wani me hankali zama abun kwatance. Jalila tana kuka tace Yaya Jidda kiyi hkr Allah yana karbar tubar me tuba, insha Allahu zaki kasance daya daga cikinsu.
Baba Mairo da Umman Sameer ce suka shigo sun dawo daga dakin Zarah sunyi mata wanka, Baba Mairo tace Falak kuzo kutafi kishiryata kinga har 3 tayi, kada ayita jiranku kunsan taro za,ayi sosai bekamata ace ku tsaida mutane ba. Kuma idan kingama kisamu guri kizauna kinsan jikinki yayi nauyi, tace to. Kama Jalila tayi wadda take ta kuka, tace muje, Jalila tace tomuje inga Ummi sannan. Baba Mairo tace kuje taganta seku wuce. Kara kallon Jidda tayi, Allah sarki Jidda kifar da kanta saman cinyarta tayi, tana wani irin kuka me ban tausayi, seda tasaka su kuka. Haka Falak tajata suka nufi dakin Zarah.
Kwance take tana bacci, gaba daya tayi bakikkirin fuskarta kamar an shafa mata bakin tukunya, kafarta meciwo takoma siririya tundaga guiwarta har dungulmin da aka yanke, babu kyan gani, gashi duk tarame, kamar ba ita bace me kiba da jiki me kyau, shiru Jalila tayi tana kallonta, tace Allah yabaki lafiya Ummi. Falak ta kalleta, seta tuna Ummanta, lokacin tana cikin rashin lafiya, zuwa tayi ta taba jikin Zarah, taji babu zafi, kai ta girgiza tace ai dasauki ma tunda ita batajin zafin jikinta. Saurin fita tayi sbd kukan daya taho mata. Jalila tagane me Falak take nufi, duk se tausayinta yakamata, tace kingani ko Ummi, mutanen dakika cuta kika maida banzaye yau gashi sune suke maki rana,
Yaugashi Falak da kikaso akashe, itace take amatsayin daya kamata ace kece kikemun abinda takemun. Goge idonta tayi tace Allah yasa kina cikin wadanda Allah ze gafarta ma kura kurensu, sede nasan baze yafe maki laifin bayin dakika cuta ba. Saurin fita tayi tajawo kofar tasamu Falak amota suka tafi.
Jalila tayi kyau sosai tasha hijabinta harkasa, haka tazauna, agefenta Falak ce itama tasha hijabinta da katon cikinta, mutane dayawa sun halarci taron, taro yayi taro sosai aka gayyaci mutane dayawa, kasancewar Jalila tanada kokari amakarantar. Bangaren manyan mutane daban, hatta da Mahaifin Saleem seda yazo shida abokananshi sbd suntaho har daurin aure, Saleem da abokananshi suma sun halarci gurin, Sameer kuwa sune manyan malamai, suna ta hidima da mutane, Alh, da Kawunshi da Mal. Garba dasauran abokananshi daya gayyata duk suna zaune acikin rumfa.
Kanshi yadaga yaga irin mutanen dasuka halarcin gurin kawai seyaji kwalla tacika mashi ido, glass dinshi yaciro yasaka, Kawunshi wanda yana kula dashi yace haba Abba, kayi hkr mana kada kabari mutanen dasuke gurin nan su fahimci halin da kake ciki, nasan kana tunanin babu mahaifiyar Jalila agurin nan, da babu ita akwai wani abu daya ragu? Kalli gefen iyaye mata kagani, ga medakina can da sauran yan uwa waye ze iya cewa babu Zarah agurin? Sede wanda yasanta, kuma kowa ai yasan rashin lafiya ko. Alh, yace shikenan kawu nagode.
Haka aka fara bude taro da addu,a sannan aka gabatar da manyan baki, aka kira Jalila domin ta karanta wata sura daga cikin Qur'ani amatsayinta na wadda akema walima, da kyar tafito, seda Falak ta anshi nikaf din wata tabata tasa, sbd tundazu take kuka. Haka tafara karatu cikin dadin murya, sede dakaji muryarta kasan muryar kuka ce, tana cikin karatun tafara kuka, seda ta burge mutane dayawa, sbd sun dauka karatun ne da murna suka sata kuka, wadanda suka san halin datake cike ne kawai suka san dalilin kukanta. Shikanshi Alh, seda yatashi bada sanin kowa ba yanufi cikin motarshi yazauna yarika kuka kamar karamin yaro, seda yaji dadin zuciyarshi sannan yafito, dayake bakin glass yasa babu wanda yake ganin idonshi. Yana zama Kawunshi yagane meyayi, shima kanshi tausayinshi yakeji.
Ganin Jalila tana kuka yasa Sameer yaje ya amshi lasifikar yayi mata godiya duk da shima jikinshi yayi sanyi. Saleem kuwa seda yayi yan kwalla, har abokananshi suna janshi. Gaba daya tausayin Jalila da Sonta suke kara ratsashi.
Haka aka kira Alh, yazo yayi jawabi, dauriya kawai yayi yafito, yana magana shima muryarshi tana rawa, ahaka yasamu yagama, sannan aka cigaba da. Wa,azi. Se karfe 6:00 dede aka tashi, tare da mika ma Jalila kyaututtuka, haka kuma tasamu kyautar kudi daga gurin bakin dasukazo, aka rarraba kayan ciye ciye kowa ya watse.
Adaran ranar su Baba Mairo sukaje suka bada duk wani abinda za,a girka gobe, ita da Hajiya Fatima matar kawaun Alh, dayake anan gidan yace su sauka, sbd itama tasan komai daya faru, ko kayan gara nasiye suka siya sbd lokaci yakure ba,ayi ba, kuma sunje sunyi mata jerenta, dan dama ansayi kayan dakin, sauran abinda ba,a siya ba, na kitchen suka bari se gobe da safe suje su siyo.
Haka suka tsara komai, da sauran yan uwan Alh, dasukazo, abangaran Zarah kam babu wanda yazo se yan uwan Babanta, shima cewa sukayi sbd Jalila da Alh, sukazo dan ita bata yarda suba, amma ko asibitin babu wanda yaleka. Gida kam yacika ba laifi mutane sun taru.
Adaren ranar jikin Jidda yayi tsanani cikin dare tarika suma, haka Umman Sameer da Baba Mairo suke tsaye akanta da sauran nurse, ganin jikin yaki sauki yasa wata nurse tayi ma Dr, waya acikin daren.
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ (H,O,N,A)
Part 175.....180
Se da asuba suka samu jikinta ya dedeta, haka aka samata oxygen har seda numfashinta yadawo dede, duk abinda akeyi su Jalila basu sani ba, dan Baba Mairo tace kada afada masu tunda dare yayi.
Da misalin karfe 6 nasafe Alh, ya iso asibitin anan yakejin abinda yafaru, cike da damuwa yace amma Baba Mairo ai da kunsanar dani, ko dare yayi ai zan iya zuwa, tace hakane Alh, yace sannunku Allah yasaka maku da alkhairinsa, Baba Mairo tace Ameen ai ba komai, duk munzama daya.
Fita yayi yadubo jikin Zarah, tana kwance kamar gawa sbd allurar bacci ake mata idan dare yayi dan kada ta farka tajima kanta ciwo, haryanzu bata farka ba, tausayinta yakara kamashi, yace kaiconki Zarah, kalli yanda kika jama kanki bala,i ana bikin diyarki amma kina kwance cikin hauka, juyawa yayi yafita, yabiya gurin Dr, anan yake kara mashi bayani akan ciwon Jidda. Alh, yace Dr, kode afita da ita waje, ciwonta yana bani tsoro?.
Dr, yace E to hakan ma yana da kyau, amma gsky matsalar Jidda bawani abu bane kawai cutar jikinta ce taci karfin jikinta, kuma da karfi tasamu nasarar karya garkuwar jikinta bawai dan takai lokacin ba, da farko tayi sakaci batazo asibiti dawuri ba, na biyu kuma tafara shan magani tabari. Na ukku kuma yanzu kwata kwata maganin baya yimata amfani ajikinta, sbd kotasha amayar dashi takeyi.
Karin ruwan da ake samata ne, kadai yake amfani ajikinta, kuma babbar matsalar bata cin abinci sosai, kotaci ma baya zama. Wadannan sune matsalar Jidda, kuma duk inda kuka kaita, basuda abinda zasu mata. Alh, yace shikenan Dr, nagode. Dr, yace se hkr Alh, Allah ya jarabceka da lalura, amma idan kayi hkr wata rana komai zewuce. Karfe nawa ne daurin auren? Karfe 2 ne, toshikenan Allah ya kaimu. Sallam yayi mashi yafita.
Da misalin karfe 2 dede na rana dubban mutane suka sheda daurin auran Jalila da Saleem, wanda akayi abisa sadaki dubu 50. Adede lokacin su Jalila da Falak suna asibiti, dan Jalila cewa tayi bazata zauna agida ba, tasan anjima babu wanda zebarta tazo asibiti, zaune take agaban Zarah, se kuka takeyi. Zarah kuwa tana kallonta tana dariya tana dariya, Falak tana gefe ta kalli Jalila tace haba Jalila kukan ya isa haka, Jalila tace dole inyi kuka Falak, ace ayau ana daurin aure na, amma Ummina da Yayata suna kwance agadon asibiti, kuma su duka babu me ciwon daza,a fada ta dadi, dukansu su suka jama kansu, yakike so inyi? Kinaji jiya agabanmu wasu suke gulmar Yaya da Ummi, sbd kome kake boyewa dole mutane su sani.
Wlh yafi acema banda Uwa za,ayi bikina hakan zefi mani insan cewar bata raye bazan damu da rashin wanda zemun nasiha ba, amma gata araye kuma cikin halin hauka, wanda zuwa yanzu mutane dayawa sunsan cewar ta hauka ce, kuma qai qayine yakoma kan mashekiya, yakike tunani idan dangin mijina sukaji haka? Nide wlh Ummin kin..... Falak tayi saurin rufe mata baki tace haba Jalila da iliminki, da komai, kinsan fa kome Uwa tazama ba,a canza ta ko? Dan haka inaso kitoshe kunnuwanki da duk wata magana dazakiji daga gurin dangin mijinki, kuma duk wanda yatareki da maganar kiyi banza ki kyaleshi shine kawai abinda ze kwaceki daga gurinsu.
Baba Mairo ce tashigo, cak ta tsaya ganin haryanzu basu tafi ba, tace mezan gani haka Falak? Kinsan fa tundazu aka daura auren yakamata ace kuna gida yanzu tasamu takara wanka sannan taci abinci. Falak tace wlh abinda nake fada mata kenan, tonaji kema ai nace kidena yawo dayawa ko, kinsan fa kinshiga watan haihuwarki, dan likita yace zaki iya kara kwanaki ba lallai bane ace kinsan lokacin, kuma wahala ma tanasa mutum ya haihu babu shiri, nide kutashi kutafi.
Jalila tace Baba Mairo yajikin Yaya Jiddan, munje dakin akace antafi da ita za,ayi mata test. A,a jikinta dasauki nabaro Halima agurin suna can gaba yanzu zasu dawo, Falak tace muje driver yana jiranmu.
Fita sukayi suka nufi dakin da aka kai Jidda test, atare suka jero, tana bisa wheel chair ana turata, wasu mata da miji suka wuce su mijin yana dauke da yaronshi, harsun wuce Jidda tace ma Jalila dan kwalama wancan kira kice Al,amin. Jalila tace kinsanshi ne? Tace inaji kamar shine, amma kirashi mugani. Jalila tace Al,amin. Cak ya tsaya atare suka juyo da matarshi, dawowa sukayi da baya, dan danan matar ta bata fuska.
Al,amin yace sannunku yamejiki? Jalila tace dasauki, kuma itace ma tace amaka magana. Kallon Jidda yayi cike da tausayi yace sannu baiwar Allah yajikin? Kuka Jidda tasa, kowa ya tsaya yana kallonta, Matarshi tace dan Allah honey muje kasanfa akwai inda zamu biya ko.
Jidda tace Al,amin, Ameerah, cike da mamaki matar takara kallonta tace ni kuma? A ina kikasanni? Goge kwallan idonta tayi tace lallai duniya kenan, baku ganeni ba? Jidda ce. Gaba dayansu suka zaro ido suka hada baki sukace Jidda Abba Bala? Ta daga kai tace kwarai kuwa. Umman Sameer tace bayin Allah mun tsaya ahanya kumuje dakinta gashi can sekuyi maganar acan.
Al,amin da Ameerah kuka sosai sukeyi dasuka gama jin labarin da Jidda tabasu, tace na cuci kaina, Ameerah kece silar shigata wannan harakar, Al,amin kaine mutumi na farko daka fara sanina 'ya mace amma yau gashi kudayake kunada rabon tsira Allah yatema keku kunshiryu, abun mamaki kuma harkunyi aure hada rabo atsakanin ku.
Ameerah tagoge idonta tace tabbas Jidda na cuceki, sbd nice silar shigarki wannan rayuwar, sede wlh tun bayan damukayi fada dake akan nazo inaso inmaidake ruwa lokacin da kika tuba, mukayi fada tundaga lokacin mukabar unguwar da muke, kuma nasake waya shiyasa bankara nemanki ba, dan naga kinbar harkar danakeyi, haka nacigaba da rayuwar bariki.
Dalilin shiryuwata shine lokacin da Babana yarasu, tundaga ranar naji tsoron Allah, sbd agabana yarasu, nashiga firgici, dama akullum addu,ar Mamana Allah ya shiryeni, segashi Allah ya amshi addu,arta, nashiga damuwa tunbayan mutuwarshi nakara canza layi, duk wasu kawayena seda narabu dasu, sbd malamin dana samu nafada mashi irin rayuwar danayi kuma nace mashi inason intuba, yace abu nafarko dazan farayi shine inrabu da duk wasu kawayena.
Sbd yace mun idan har mutum yana aikata alfasha, kuma yatuba, matukar berabu da abokanan shiba, tamkar be tuba bane, dan wata rana zasu iya dawo dashi ruwa, alokacin hargidanku nazo sede bansamekiba, Umminku tace mun kina zariya, na amshi no ki amma nakiraki bata shiga, alokacin naso mukulla sabon kawance tunda nasan kin tuba.
Tundaga ranar nikuma bankara tunanin zuwa gidanku ba, haka nashiga islamiyya wannan malamin yatsaya mun sosai nayi karatu me yawa, wata rana nadawo daga makaranta, nahadu dawani dan unguwarmu tare da wani, na tsaya mugaisa kawai senaga ashe Al,amin ne, anan muka gaisa shima yayi mamakin ganina haka, shine ya amshi no ta yace zezo muyi magana, dan bayason muyi agaban abokinshi.
Naji matukar tausayinki lokacin dayabani labarinki, alokacin yayi kuka shima, dan yacemun shine sanadiyar komawarki ruwa, kuma ya kaiki inda kika hadu da matsala, haryake cemun yaso kuyi aure amma kika kiya, alokacin daya temakeki kuma yace yana zargin kina dauke da cuta, yaso kije kiyi gwaji idan baki da ita kuyi aure amma baki yarda ba.
Ganin nima nashiryu, shima yafadamun irin kallar tubar dayayi kuma yace idan zan amince ze aure ni, dama alokacin mijin aure nake nema ni kuma na amince mashi, yanzu haka yaronmu daya Sultan, kuma haryanzu banwuce karatu ba, dan gani nake gara nayi zamana nayima mijina biyayya yafi dan tsoron yan matan Jami'a nakeyi, keni zan iya cemaki kawata daya yanzu ma kwafciyata, itama tadan girmeni.
Al,amin kuwa kasa cewa komai yayi sbd kuka yakeyi tamkar mace, kowa yakasa lallashin shi. Jidda ma kukan takeyi, da kyar tayi shiru tace bakomai Ameerah wlh nayafe maku, duk da kune silar shigata wannan rayuwar amma babban laifin yana gurina da gurin Ummin mu, mekikace yanzu? Mamanki kullum addu,arta Allah ya shiryeki, toni banda wanda yakemun addu,a se kanwata. Kuma kinsan yanda addu,ar Uwa takeda tasiri akan 'ya'yanta, yakike gani idan da ace Ummina ce takemun addu,ar da Jalila takemun?.
Mutum yasamu Uwa tagari ma babban abin alfahari ne, Baban nawa daya kamata shima yatuna dani yamun addu,a bata bari yasan halin danake cikiba, bare yamun addu,a. Asalima tasashi yamanta dani acikin yaranshi.
Wannan Uwa tagari ce? Uhm, nikam ahaka nazo duniyar banci ribar komai ba, kuma gashi zanbarta babu wata riba. Al,amin bakayi laifi ba, dan ka auri Ameerah, laifi nane, fatana kobayan raina kada kumanta dani kurika sakani cikin addu,arku kuma duk wanda zebani sadaka, inarokon daya aje bayan raina agina mun koda rijiyace wadda mutane zasu amfana da ita, koda hakan nasan da kudina nabar abinda wasu zasu amfana dashi, kuma Allah zekai ladar akabarina, amma tabbas ban tara komai na lada ba, wanda zanyi guziri dashi natafiya,,,,,,, kuka ne yaci karfinta.
Shiru dakin yayi sbd gaba daya dakin kowa kuka yakeyi. Al,amin da kyar yace Jidda kiyafemun kiyafemun dan Allah, tashi yayi yadauki Sulta ya aje masu kudi wanda besan yawan suba yafita sbd gaba daya zuciyarshi tayi mashi zafi, Ameerah ta mike tana kuka tamika ma Jidda hannu sukayi musabaha, itama tafita tana kuka, akofar fita suka ga mutum tsaye ya juya baya, da alama shima kuka yakeyi.
Alh, ne yazo tafiya dasu Jalila dan Baba Mairo tace mashi suna nan, tunda yazo zeshiga yaji firarsu kawai ya tsaya akofar dakin. Tausayin Jidda yayi mashi yawa, haka yashiga dakin daka ganshi kasan yasha kuka, bakin glass ne a idonshi amma duk da haka afuskarshi ana ganewa.
Kwance ya iske Jidda tana ta kuka, yace Jalila kumuje kunga har la,asar tayi, Falak kuwuce muje. Jalila ta matsa tarike Jidda sosai, tana kuka, tace Yaya Jidda kiyafemun, zantafi, amma gobe zamuzo, Allah yabaki lfiya. Jidda tace bakitaba yimun komai ba Jalila, nice yakamata inrokeki gafara, na cutar dake, kiyafemun, Falak kema haka dan Allah kiyafemun. Falak tace nadade dayafe maki, Allah yabaki lfiya.
Da kyar aka cire Jalila daga jikin Jidda sunata kukan saurin fita Alh, yayi danshima kukan yakeyi.Jidda kwanciya tayi tana kukan zuci jitake dama Allah yadau ranta yanzu.
Da misalin karfe 7 aka gama shirya amarya, tayi kyau, sede fuskarta ko kwalli bata bari anshafa mata ba, bamaze zauna ba ko anshafa, sbd hawayen dasuke zarya afuskarta, afalon Alh, aka kaita suyi sallama, zaune suke da Mal. Garba, da Kawunshi, anan kowa yayi mata nasiha sannan akace Alh, yayi mata nasiha, kasa cewa komai yayi, sede yace Allah yabaki hkr Jalila, saurin tashi yayi yashige daki sbd kuka, daya taho mashi, itama kukan takeyi, haka matar Kawun Alh, ta dagata suka wuce, Falak kuwa dama tundazu Sameer yadauketa yakaita gidan amaryar dan yace baya so tasha wahala, manyan mata 2 ne suka sakata tsakiya, da yan uwan Kakanta, se dangin Dadynsu.
Sauran mutane suka biyo bayansu. Gidanta yayi kyau sosai, haka suka shiga da ita, bayan sunmikata ga dangin mijinta akayi abubuwan al,ada sannan Sameer yashiga yace sufito amaidasu, dan ance manya bazasu kwana ba, Falak ma Sameer ne yace ta kwana sbd Jalila. Da kyar Falak tasata takara yin wanka sbd gidan kowa ya tafi daga Falak se su Bilkisu da Farida, su 3 ne zasu kwana, lallashinta sukayi taci abinci. Suna zaune Jalila tace wlh Falak gabana faduwa yakeyi, Falak tace badole ba, tunda gobe kamar yanzu kina gaban angonki. Tace ke wlh kincika fassara, nikwai inaji ajikina kamar wani ya..... bata karasa fadi ba, Saleem yayi sallama yashigo shida Sameer, daka kalli idanunsu kasan akwai abinda yafaru. Zunbur Jalila tamike tace Ummi ko? Yaya Jidda ce? Kufadamun waye ya mutu acikinsu? Kamota Saleem yayi yace babu wanda ya mutu kawai jikin Yaya Jidda ne yatashi. Murmushi tayi tace wlh banyarda ba, shikenan kawai, nashiga 3 yazakimun haka Yaya Jidda kinsan banda kowa seke, meyasa zakimun haka,,,, kuka tasa masu, Falak taja Sameer tace meya faru, Yaya Jidda tarasu ko? Share hawayen idonshi yayi yadaga mata kai,
Wata irin zufa taji ta taso mata, mararta tawani murda, saurin dafe cikinta tayi ganin halin data shiga yasa Sameer yayi saurin kamata, yace Saleem muje inajin Falak haihuwa zatayi, kadauko Jalila kawai dasu Bilkisu kasa megadi yakulle gidan bari intafi da ita asibiti. Juyawar da Saleem zeyi yayi ma Jalila magana yaganta kwance akasa ta sume.
😭😭😭😭😭😭😭😭
Washhhhh!!!!! bara inbarku haka, nima najike sekunjini a page na gaba. Tnx alot
0 Comments