AGOLA 4

 AGOLAH!!! Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI,U ZANGO 

(Nabeelert Lady)


@ ( H,O,N,A)


Part 65.....70


Tun daga wannan rana Falak takoma me aikin Zarah, Alh yamanta da Falak, ko Ameer yadena tambayarshi, tunda Zarah tace mashi ya warke, kuma tana kula dashi, gashi yanzu baya zama sosai, 


Kudi sosai Zarah take samu agurinshi, yazama matar dazama mijin, Baba mairo da Jalila kuwa sunzama yan kallo, sosai suke tausayin Falak, aboye Baba mairo take temaka mata,ga aiki ga renon Ameer, kusan kullum seyayi suma tafi 3 saboda baya iya cin komai.


Damma Falak tana yimashi addu,a shiyasa yake dan samun sauki,  Baba mairo tace mata idan zata bashi abinci tarika yin addu,a, dahaka yake samu yana cin loma 3 ko 4.


Falak duk ta rame tayi duhu, gashi bata samun bacci sosai, dan store din wasu kwari ne, suke cizonsu, kullum cikin dare Ameer kuka yakeyi, se idan ta goyashi ne kadai yake bacci, ita tahakura da bacci, wani lokacin a kitchen take samu tayi bacci, idan Zarah bata leko ba.


Jalila kanta tayi rama, saboda bakaramar damuwa tashiga ba, datayi nufin temakon Falak seta tuna kalaman Umminta, gashi tana tsoron fushin Umminta, saboda a islamiyya anfada masu muhimmancin Uwa.


Akwai ranar da Alh, yadawo cikin dare yarika jin kuka kamar na yaro, tashi yayi yace Zarah kamar kukan Ameer nakeji, tashi tayi tace wane Ameer kuma, bacin ya dade dayin bacci, kila de makwafta ne,


Alh, yace yaushe harzamu iyajin hayaniyar makwafta agidan nan, muda mukeda da nisa dasu, Zarah tace to karya nakeyi, kasan ai nasaba yinta. Alh, yace Allah yabaki hakuri bahaka nake nufi ba, tace zauna bara inje inlekosu.


Fita tayi tana surutai, store tanufa, Falak tagani se kuka takeyi Ameer kuma yana hannun Baba mairo yanata suma, Zarah tace wai meye haka, dan iskanci zaku fito ku hanamu bacci, Baba mairo tace Haba Hajiya kalla fa kiga yanda yaron nan yake suma, ki kira Alh, mukaishi asibiti, tundazufa beci koma ba.


Zarah tace wlh babu inda za,a kaishi, daukarshi kushiga dakinki kiyi mashi wanka ze farfado, kuma ki kulle dakin banason karajin kukanshi, wlh idan kuka bari Alh, yafito sekinbar gidan nan gobe, wucewa tayi tana zage zage.


Dakin Baba mairo suka wuce, ruwan sanyi Falak tadauko suka samashi da kyar yafarfado, kuka yasaka, haka sukayita lallashinshi Falak tana mashi addu,a se can suka samu yayi bacci. Kwantar dashi Baba mairo tayi,


Kuka Falak tasa tace shikenan Baba mairo shima kila tafiya zeyi yabarni, nashiga 3 ni kuma rayuwata haka zata kare, wlh gara mutuwa ta da rayuwata, rufe mata baki Baba mairo tayi itama tana kuka.


Tace Falak kiyi hakuri, duk tsanani yana tare dasauki, kuma duk wanda yayi hakuri yana tare da nasara, ninasan wata rana komai zewuce, Falak tace Baba mairo kina ganin yanzu ko Dady baya nemammu.


Ina alkwarin daya dauka akan rikemu da amana, gaskiya Dady yazama butulu. Baba mairo tace Falak, akwai abinda nasani wanda baki sani ba, banyi niyar fada maki ba, amma dole infada maki kodan ingoge bakin panting da Zarah tayima Alh, agurinki.


Anan Baba mairo takwashe komai tafada ma Falak, kuka sosai, Falak takeyi, Baba mairo tace ko tan tama banayi wannan maganin da Zarah tasama Alh, maganin mallaka ne, domin rannan inajinsu tana yimashi tsawa, shi kuma duk yarude, yana bata hakuri, bakiga yanzu kamar itace mijin shine matar ba?


Kiyimashi uzuri, wata rana asiri zetonu, Jalila ma tana cikin damuwar halin dakike ciki, babu yanda zatayine, dan Zarah tace idan har tarika shiga harkarki zata tsine maki, shiyasa tace makarantar kwana zata tafi bazata iya cigaba dazma tana ganinki cikin damuwa ba.


Falak tace yanzu Baba mairo haka zamu zauna da Ameer babu magani, tace kiyi hakuri gobe idan zakije kasuwa zanbaki kudi kitsiyo mashi magani, haka Baba mairo tayita lallashin Falak, harta hakura, kuma tayi alkwarin saka Alh, cikin addu,a. Dahaka suka kwanta, rabon datayi bacci medadi kamar na yau harta manta.


Washe gari bayan tagama aikinta, taci abinci tayi wanka, tasaka kodaddar atamfarta, ta amshi kudi agurin Baba mairo dan zataje kasuwa, dakin Zarah tashiga da sallama tace mata tashirya, kallonta tayi tace dauka ga kudin nan, kidauka, saura kije kidade,


Fita tayi taje yima Baba mairo sallama, tace Baba mairo natafi, kudi Baba mairo takara bata tace amsa, Falak tace nameye Baba? Tace idan kinje kisiyo turare naga naki yakare, kwallan idonta tagoge, tace nagode Baba mairo, tace haba Falak ai bakomai, yisauri kije kidawo ki amshi Ameer inshiga kitchen kafin Zarah tafito. Kallon Ameer tayi yana bacci, duk yarame,fita tayi tana goge idonta.


Abakin gate taci karo da Alh, yana kokarin shiga mota, binta da kallo yayi, Zarah wadda take gefenshi tace lafiya de naga kana kallonta?  Yace naga bansanta agidan nan ba ne shiyasa, murmushi tayi tace oh, sabuwar me aikina ce, mota yashiga yace yatafi.


Bayan Falak tagama siyen abinda zata siya, taje chemist tasiyoma Ameer maganinshi, sannan taje gurin siyen turarenta. Bayan tasiya, tajuya kenan taji kamar ana kiranta. Haka tawuce batare data juya ba.


Malama Falak, yau kuma babu magana inata magana, juyawa tayi domin taji muryar malam. Sameer, ido suka hada dashi, yana cikin wani yadi mekyau yakara haske, duk se kunya takamata ganin kayan dake jikinta,gashi duk tayi baki.


Bayan sungaisa yace Falak yagida, nima jiya nadawo, shine yau nafito shago, ashe dama kina shigowa kasuwa, ke kadai, yau ina Jalila ne? Shiru tayi kanta yana kasa tana wasa da ledar hannunta, idonta har yafara kawo kwalla.


Yace Falak lafiyarki kuwanaga kamar kina cikin damuwa, gashi naga duk kin rame, inafatan de lafiya? Hadiye kwallanta tayi, tace malam, rana tanayi kada ajirani agida, zanwuce. Murmushi yayi yace shikenan, tunda bazaki fadamun ba, kodan nan kasuwa ce, amma anjima zamu hadu a islamiyya ko? Shiru tayi, yace Falak bani no wayarki mana, tace aikam banda waya, yace tobani ta Jalila, tace barade Inbaka ta Baba mairo, kallonta kawai yakeyi hartagama saka mashi, tamika mashi, amsa yayi yace sena kiraki ko.


Godiya yayi mata ta tafi, kallonta yacigaba dayi, jikinshi yana bashi kamar tana cikin damuwa, ammade bari anjima zan tsareta seta fadamun koma meke damunta, ko intambayi Jalila, haka yajuya yana me farin cikin ganin abin sonshi, dan tunda suka gama makaranta yake dokin dawowa yaganta, kuma wannan karin yayi alkwarin fada mata abinda ke cikin ranshi.


Tun daga nesa tafara ganin mutane akofar gidansu, haka takarasa, gabanta yana faduwa, da kyar tasamu tashige cikin gidan, Jalila tagani tana kuka, saurin matsawa tayi tana tambayarta meyafaru, hannunta Jalila taja suka shiga cikin gida, dakin Baba mairo suka shiga.


Yarda ledar datake hannunta tayi, tasaka wani irin kuka ganin Ameer shimfide akasa bisa tabarma, duk ya mimmike, kuma anrufeshi da zani. Baba mairo shikenan shima ya mutu ko? Kamata Jalila tayi suka zauna, tana bata hakuri.


Baba maito tace kidena magana Falak kada kiyi sabo, kinsan Allah yafimu sonshi tunda har ya amshi abunshi, addu,a yakamata kiyi mashi, kuka kawai Falak keyi, dahaka wadda zatayi mashi wanka yashigo, komawa gefe Falak tayi tana kallon yanda akeyima Ameer wanka ko motsi. Bayayi.


Bayan angama Alh, yashigo shima yana kuka, hankalinshi duk yatashi da kyar yadauki Ameer yafita dashi akayi mashi sallah sannan suka kaishi makwancinshi. Zarah kuwa tana falonta, tarufe fuskarta. Da hijabi duk wanda yashigo gaisuwa seya dauka kuka takeyi,  haka yan unguwa suka rika shigowa yin ta,aziya.


Washe gari Falak ta tashi da zazzabi me zafi, bata iyama tashi ga ciwon kai, Baba mairo duk tashiga damuwa, Jalila cetasamo mata magani adakin Zarah, haka akayita karbar gaisuwa har kwana 3, su Asabe da kawarta Dije ma sunzo.


Jidda kuwa batama san abinda akeba dan suna Lagos ita da Al,amin.   Bayan sadakar 7 su Asabe suka koma suna cike da farin cikin abinda Zarah tayi masu dan tabasu kaya da kudi masu yawa saboda tana cikin murnar aikin boka yayi.


Malam. Sameer zaune a dakinshi yana tunanin kome yahana Falak da Jalila zuwa makaranta, gashi no da Falak tasa mashi yakira harya gaji tun aranar amma bata shiga, jawo wayarshi yayi, yaduba agogo yaga karfe 9 n dare.


No yakara kira, cikin sa,a kuma tashiga, zaune au Baba mairo da falak suke adakinta, dan tunda Ameer yarasu adakin Baba mairo take kwana, wayar Baba mairo ce tayi kara, dauka tayi da sallama,  bayan sun gaisa yace Baba mairo dan Allah ko Falak tana nan? Cike da mamaki tace e tana nan, wayene, yace Malaminsu ne na islamiya Sameer.


Washe baki Baba mairo tayi, dan tanajin labarinshi agurin Falak da jalila,hartake tonan Falak tana cewa kode siriki tasamo mata. Baba mairo tace e gata nan bari abata, mika mata wayar tayi, bayan sungaisa, yace haba Falak tunda kika bani no kuma bansake ganinki a makaranta ba, gashi idan nakira ma bata shiga.


Na tambayi yan ajinku sunce wai kindena zuwa Jalila ce kadai take zuwa itama ba sosai ba. Meyafaru dan Allah, kinsan tun rannan naga kamar akwai abunda kedamunki.


Shiru tayi saboda wani kuka daya taho mata,  Baba mairo kallonta kawai takeyi, tama karajin tausayinta. Hello Falak kinajina kuwa, sautin kukanta kawai yaji daga nan takashe wayar, tafada bisa katifa tana kuka


Kara kiran wayar akayi, ganin harta kusa katsewa yasa Baba mairo ta dauka. Sameer yace hello Falak kinajina, dan Allah kiyi shiru, bana son jin kukanki wlh, yana tadamun hankali, tunranar damuka hadu akasuwa naga kamar kina cikin dakuwa nima nashiga damuwa. Kiyi hakuri idan akwai abinda yake damunki. Wlh ashirye nake da intemaka maki.


Hawayen idonta Baba mairo ta goge aranta tana mejin dadin yau Falak tasamu wanda yake damuwa, da lamuranta. Hello Falak kiyimun magana. Baba mairo tace yaro kanajina, yace e,e Baba inajinki ina Falak din?


 Tace Falak bazata iya maka magana yanzu ba, dan kamata fami akan abinda kedamunta, sede bansani ba, kawai naji ka kwanta mun arai, dama kuma inajin labarinka agurin su Jalila, tun lokacin daka bama Falak addu,a tayima Ummanta sanda batada lafiya.


Agaskiya Sameer bazan iya boye maka abunda yake damun Falak ba, saboda inaji ajikina, kaine zaka temaketa, idan harkaji labarinta, idan harzaka iya sauraron labarin Falak, kabari se gobe idan kasa kudi awaya kamar irin wannan lokacin seka kira inabaka labarinta.


Sameer yace a,a Baba mairo wlh inada kudi awayata zasu isa inji labarin Falak, bazan iya hakuri xuwa gobe kamar yanzu ba. Gyara kwanciya Baba mairo tayi, tace zanbaka labarinta, amma inaso kazam merikon gaskiya da amana idan kaji labarinta.............  Anan Baba mairo tafara bashi tarihin Falak.


Urs, 

NABILA RABI,U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[7/13, 09:40] Nabilat Author: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI,U ZANGO

( Nabeelert Lady)


@ ( H,O,N,A)


Part 70.....75


Kuka kawai Sameer yakeyi, yana sauraron Baba mairo, hartagama bashi labarin Falak, be iya magana ba, yace nahode Baba, Sautin kukanshi kawai takeji,da haka yakashe wayar.


Tunda yake arayuwarshi betaba jina labari me firgitarwa kamar na Falak, jiyake kamar a film akayi abun, da ace ba Baba mairo bace tafada mashi, labarinta ba, naze yarda ba.


Wata irin soyayyar Falak ce take shigarshi, gatausayinta daya ke shigarshi jiyake kamar yaje yadaukota tadawo kusa dashi, kuka kawai yakeyi, yana jin zuciyarshi kamar zata fito, aranar kasa bacci yayi, sede yayi alwala yafara nafila, har asuba tayi, seda yayi sallar asuba sannan ya kwanta, saboda ciwon dayaji kanshi yana yimashi.


Falak ma haka ta tashi da ciwon kai me tsanani, da zazzabi, da kyar tayi sallah ta kwanta, Baba mairo tana gama sallah taji Zarah tashigo ta watso kayan wanki tace idan wannan AGOLAR tagama sallah kice mata tayi mani wanki, saura kuma tabari gari yawaye infito bata gama ba.


Fita tayi takoma dakinta ta kwanta, Kallon Falak Baba mairo tayi wadda batama san me akeyi ba, saboda bacci me nauyi yadauketa, saurin tashi Baba mairo tayi tadauki kayan tashige bandakin dake cikin dakin tafara wankesu. Dayake bawani yawa garesu ba, kuma basuda datti, cikin minti 20 tagama, cikin sando tafita taje ta shanya, tadawo.


Kitchen tawuce tayi wanke wanke sannan takoma daki ta kwanta ganin haryanzu gari be ida haske ba, kuma dama bata fara girkin safe se karfe 7. Kwanciya tayi tana tunanin hanyar dazata bi Falak tabar gidan, sede tana tunanin Falak bazata yarda tabar gidan ba, inde ba aure tayi ba, saboda tana riko da wasiyar da Ummanta tabar mata. Addu,a tashiga yi Allah yasa Sameer yace ze auri Falak, da cikin lokaci kadan zatace yafito, sede bata sani ba ko Zarah zata yarda Falak tayi aure yanzu.


Har karfe 10 Sameer be fito daga daki ba, ummanshi Halima data gama saida kosanta harta gama aikinta, tajishiru, kuma besaba yin haka ba, dakinshi tashiga da sallama. Tsaye tayi ganinshi zaune yabuga tagumi yana tunanin, ga kuma hawaye suna fita daga idonshi.


Kusa dashi tazauna jikinta duk yayi sanyi ganin danta yana kuka, dan tasan kila mahaifinshi yatuno. Sameer lafiyarka kuwa, kake kuka? Goge idonshi yayi yace Umma ina kwana, kiyi hakuri yau natashi banajin dadi shiyasa banfito dawuri ba.


Lafiya lau, Sameer amma bawannan na tambayeka ba, rashin lafiyar ce tasa kuka kome? Tashi yayi yace Umma bara inyi wanka zan fada maki damuwata, waje yanufa domin yin wanka.


Seda Falak tayi wanka sannan Baba mairo takawo mata abinci, fa kyartaci tasha magani, dan tadanji sauki datayi bacci sosai, kallon Baba mairo tayi tace Baba mairo yaushe aka wanke ma Ummi kayanta harnaga kina linkewa? Anan Baba mairo tafadima Falak abunda yafaru da tana bacci, kwalla ce tacika idonta, tace bansan da abinda zan saka maki ba, Baba mairo, Allah yabani tsawon rai nima inyi maki wani abu wanda zakiji dadi arayuwarki.


Murmushi Baba mairo tayi tace ai keda Ummanki kungama mun komai tunda har kuka daukeni amatsayin uwa, kinga ko babu abinda yafi wannan dadi, nide fatana Allah yabani tsawon rai in kaiki dakin mijinki. Murmushi Falak tayi tace Uhm Baba mairo kenan, aini bana sa rai zanyi aure, dan nasan Ummi bazata barni inyi aure ba, tunda batason cigaba na.


Baba mairo tace insha Allahu sekinyi aure Falak, kuma ni harna zaba maki miji ma, Allah yasa zakiyi na,am da zabina. Dariya Falak tayi tace lallai Baba mairo kinkosa kirabu dani, to afadamun wanda aka zaba mun, ina fatande ba tsoho bane?


Dariya Baba mairo tayi tace a,a wanda kike sone kika boyema ranki na zaba maki, fiddo ido Falak tayi tace kai Baba mairo, yaushe mukayi haka dake, ni babu wanda nakeso. Har Malam. SAMEER din?  Rufe fuska Falak tayi tana murmushi, tace yaushe nacemaki inason malam. Sameer kuma? To inma baki sonshi ni shina zaba maki. Kai Baba mairo shifa bece yana sona ba,


Yace mana, jiya ai naji abinda yace, da kika aje waya nadauka, haka yayita surutai, yadauka kece awayar. Dariya Falak tayi tace nide banyarda ba, Baba mairo tace Allah Falak a aje batun wasa agefe, dama inaso muyi magana dake akan Sameer, nide tabbas nayarda dashi, shiyasama jiya nakasa boye mashi labarinki.


Inaso Falak ki nutsu kigane mesonki, kada kiyi la,akari da Sameer malamin makaranta ne, kice bakisonshi, nide nayarda dashi , kuma nasan zerikeki da amana, inaso insamu lokaci inganshi koda awani gurine, ko kuma yazo yakaini gidansu muyi magana dashi. Allah yasani inaso inga kinbar gidan nan. Falak tace to Baba mairo Allah yazaba mana abinda yafi zama alkairi. Amma kisani duk ranar dazan bar gidan nan kafata kafarki, idan bahaka ba, sede na hakura da auren dan kowa zan aura, seya yarda zaki bini. Dariya Baba mairo tayi tace ti naji insha Allahu ma bakida mijin daya wuce Sameer. Murmushi Falak tayi tadauki kayan Zarah tafara gogewa.


Zaune suke afalo Alh, yakalli Jalila, yace Alhamdulillahi gashide na amso maki, admission dinki, kuma nabama wani abokina yayi maki registration ana A,B,U tunda de kince bazakiyi karatu anan kadunaba, wato kinfison makarantar kwana ko?  Dariya Jalila tayi tace ai Dady anfi yin karatu acan, amma nan kila inacikin yin karatun wani abun yadaukemun hankali.


Zarah tayi murmushi tace can dinma ai gidane, damma tace bazata zauna agida gurin Inna asabe be, tafison hostel, me suka bata ne? Biological science ne suka bata, to Allah ya bada sa,a seki dage.


Alh, yace Hajiya watodesu Inna su kwace mana Jidda ko? Yanzu ko lekomu batayi, naso ace tadawo insa ayi mata exam ta kudi itama tafara karatun tunda taki fidda miji, dazama haka nan, amma gaskiya banajin dadin rashin zamanta agida kusa damu. Zarah takalleshi fuska ahade tace to mekake nufi? Tunda yarinya tace batason karatu abarta mana aiba dole bane, ni karatun nayi dakake zaune dani. Kuma menene bana yi maka, wama ze kalleni yace secondary kawai nayi, itama ta gwamnati, ina laifi ma ita tayi makarantar kudi tasan yes tasan no.


Nifa banason takura wlh, kuma dakake maganar tadawo gida tazauna, kana nufin gidanmu ba gida bane kome? Inma kyamarsu kake nima acan nataso harka ganni kace kanaso, idan tadawo nan, mezatayi maka, kaima da bazama kakeba, kuma acan tana taya Inna zama tunda ita kadai ce.


Allah yabaki hakuri Hajiya wlh ba haka nake nufiba, kawaide nafada ne, amma kiyi hakuri ba za,a sakeba. Kallon mamaki Jalila take bin Umminsu dashi, ganin yanda takema Dadynsu fada, wanda ada ko gardama batayi mashi, amma wai yau shine yake bata hakuri, har muryarta tana fin tashi yin sama. Tunowa tayi da wa,azin da malam Sameer yayi masu akan hukuncin matar datake daga ma mijinta murya. Wasu zafafan hawayene suka rika fiyo mata, saurin gogesu tayi.


Alh, yace Jalila zaki iya tafiy, amma kizama cikin shiri nan da sati mezuwa zaki tafi, anjima kizo ki amshi kudi seki siyo abunda kike bukata. Tashi tayi jikinta duk amace, tafita.


Halima tace Sameer lallai akwai abinda yake damunka, kuma ba karamin abu bane, kallifa dan abincin daka ci. Sameer yace wlh Umma banajin dadin abincin ne. Rufe kwanon tayi tace inajinka fadamun damuwarka.


Gyara zama yayi, ya kwashe duk abinda Baba mairo tafada mashi yafada ma Ummanshi. Kasan cewar Halima mace me tausayi, bata san lokacin da hawaye suka wanke mata fuska ba.


Tana goge idonta tace wai Sameer wannan labarin ba ta tsunniya bace kake bani kuwa. Wlh Umma ni kaina faba Babbar mace bace tabani labarin Falak ba, dabazan yarda ba, kuma nima naga wasu alamomi agurinta lokacin damuka hadu kasuwa, bakiga kayan jikinta ba, bazakice daga gidan masu kudi tafito ba.


Umma tace tabbas nima bantaba jin abinda yabani tausayi da tsoro irin labarin Falak ba, agaskiya Sameer ina yimaka sha,awar aurenta, koda bakace kana sonta ba, nizanyi maka umarni da aurenta kodan kafidda ta daga rayuwar datake ciki, dan wannan mata batada imani zata iya kasheta wlh.


Kuma naji dadi, dakace kana sonta, tunkafin kaji labarinta, hakan zesa nayarda bawai tausayinta ne yasa zaka aureta ba, dama nafison ace akwai soyayya atsakaninku kafin kuyi aure, hakan zesa auren yafi dadewa.


Tunda baze yuwu kaje gidansu ba, meze hana kadauko Baba mairo kuzo nan muyi magana ba. Yace shikenan Umma zanyi yanda kikace. Yauwa Sameer amma dan Allah kacire damuwa aranka, insha Allahu bakada mata se Falak, zantayaka da addu,a har Allah yadoramu akan wannan muguwar mata. Sameer yayi murmushi yace ai damuwa takare, dama ina tsoron kiji labarinta kice bazan aureta ba. Dariya tayi tace haba Sameer ai yakamata kamun sheda mekyau, Allah kada yakawo ranar dazan tauyemaka hakkinka, kamar yanda kakemun biyayya dolene nima inso abunda kakeso, matukar baze cutar da kaiba.


Sameer yace amma Umma anan gidan zamu zauna ko? Kinsan banason nisa dake, tace a,a kada ma kafara, bazan zauna da surika agida daya ba, gara de muna nesa, idan kata fima akwai A.isha diyar yaya Zainabu tagama makaranta kuma dama tace mun zata bani ita, tunda tana da yan mata, seta dawo nan mucigaba da zamammu.

Sameer yace to umma ina zan zauna? Tace bade ka gama karatunka ba, haya zaka kama kafin Allah yabude se kafara gina wancan filin naka. Amma Allah bazamu zauna tare ba. Dariya yayi yace toshikenan Umma ai base kinrantse ba, yanzu de bani abincina incinye. Dariya tayi tace oh baka koshiba kenan.


Sati yana zagayowa Jalila tagama hada komai, nata, dakin Baba mairo tashiga, zaune ta iskesu suna fira, mikama Falak takaddu tayi, idonta yana kallon kasa, saboda gab take da fashewa da kuka, ita kadai tasan abinda takeji. Falak tace nameyene Jalila? Budawa tayi tafara dubawa, cike da farin ciki ta rungume Jalila, ganin result dinta ne ta amso mata kuma gaba daya tacinye both waec dan Neco.


Kuka sosai Jalila tasak tana kara kankame Falak, cikin muryar kuka tace Falak kiyi hakuri nasan Ummice tasakaki cikin halin da kike ciki, gashi yanzu zantafi makaranta batare dakeba, wlh saboda ke nazabi intafi boarding saboda bazan iya kallonki cikin damuwa ba, ki kara hakuri akan wanda kikeyi.


Kuma dan Allah ki amince da malam. Sameer yafito kuyi aurenku kema kibar gidan nan, dan wlh koni bansan lokacin dawowata ba, banason gidan nan, gara inzauna amakaranta yafi mani zaman gidan nan. Nizan tafi, inada no Baba mairo zamu rika waya, Kudi masu yawa tasaka ma Falak ahannu sannan ta bata wata leda wadda kayan shafa ne, aciki masu yawa. Tasiyo mata.


Kuka sukeyi sosai, harseda Baba mairo itama ta tayasu, seda suka gaji sannan sukayi shiru, kufi Jalila tamika ma Baba mairo,godiya sukayi mata. Har bakin kofar dakin Baba mairo suka rakata da kyar Baba mairo taja Falak suka koma ciki ita kuma Jalila tafita tana kuka tasamu su Alh, da zarah suna jiranta awaje, dan sune zasu kaita.


Urs,

NABILA RABI,U ZANGO

( Nabeelert Lady)

08028525263

[7/13, 09:41] Nabilat Author: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI,U ZANGO

( Nabeelert Lady)


@ (H,O,N,A)


Part 75.....80


Washe gari Falak ta tashi da karfin jiki, haka tagama aikinta, sannan tashirya ta nufi kasuwa.


Yauma tana gama siyayyarta tahadu da Sameer, bayan sungaisa yajata zuwa cikin shagonsu, zama tayi kanta akasa duk kunya takeji saboda kayan dake jikinta.


Falak, taji yakirata. Amsawa tayi amma bata dago takalleshi ba, hakika naji labarinki wanda yafirgitani, gaskiya inga rayuwa, koma ince kina cikin ganinta, abinda nakeso dake ki kara hakuri abisa wanda kikeyi, babu wani rai daze rayu aduniya, face se Allah jarabceshi, da duk abinda yayi niya.


Kuma bakowane yake iya cin jarabawar da Allah yayi mashi ba seme imani. Falak akwai abinda nakeso infada maki, kuma inafatan zaki fahimceni, banaso kidauki maganar dazan fada maki kamar saboda tausayinki ne yasani fadamaki ita.


Wlh Falak tun ranar dana fara ganinki arayuwata Allah yajarabeni da sonki, ina maki son daban san irinshiba, alokacin danaji labarinki sonki da tausayinki suka kara shiga raina. Dan Allah Falak kada kice bazaki amshi roko naba, kiyi hakuri nasan natsaidaki kilama ayi maki fada, bansan inda zanganki ba, idan ba nan ba. Amma bazan matsa maki dajin amsarki yanzu ba, ga wannan wayace nasiyo maki sekirika boyeta kada akwace maki.


Ina Jalila fa? Se asannan tadago kai tana kallonshi, tace ai ta tafi A,B, U Zariya, jiya, yace tasamu admission ne? Tace e tasamu biological science suka bata. Yace yayi kyau, kema kiyi hkr insha Allah wata rana zakiyi naki kinji. Murmushi tayi tace Allah yasa. Wayar yabata da kyar ta amsa, tayi mashi godiya, sannan suka fito yarakota.


Harkusa da gidan yakaita, sannan yamika mata wata leda yace gashi tace ta meye ne, yace idan kinje kiduba zaki gani, idan kuma bakiso sekiba Baba mairo, dariya tayi tace toshikenan, nagode Allah yasaka da alkhairi, yace ameen, amma fa dakinje ki kunna wayarki nasamki ita charji, haka sukayi sallama tashige gida, sa,arta daya Zarah bata nan.


Da dare Zarah tana daki tana waya da Asabe, Baba mairo tazo domin kawo mata abincin da tace akawo mata. Harzata shiga taji Zarah yana wata magana, kara labewa tayi domin sauraron abunda take fada.


Wlh Inna Asabe sonake da inkori yarinyar nan, banaso tana zaune gidan nan wata rana Alh, ze iya ganeta, dan kinsanta dashegen tsaro da addini, kuma tanada addu,a banaso ta karya mani shirina, amma idan nakoreta tabar gidan shikenan nahuta.


Tsayawa tayi alamun sauraron Asabe, Can tace toyanzu Inna wakike ganin za,a aura mata, nifa kinsan bawani sanin yan iskan unguwar nan nayi ba, da se insamu wani yazo ni ko kudi zan iya bashi ya aureta, kona shekara daya ne bayan yagama wulakanta ta, imma da rabo yayi mata ciki sannan yakoreta, dazanfi jindadi.


Banaso yarinyar nan tabar gidan nan batare da wani mugun tabo arayuwarta ba, kibari kawai zan nemi duk dan iskan danaga yayi mun nakirashi inbashi ita kawai, damma kada yan unguwa su zargj

[7/13, 09:41] Nabilat Author: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH



Cigaban. Part 75..... 80.  AFUWAN BANGAMA TYPING5 BA YAYI SAVING BY MISTAKE, GA CIGABAN

NAN.


Banaso yan unguwa su zargi wani abu wlh da acikin kwana 2 za,a daura masu aure yadauketa duk inda ze kaita ma yakaita. Shikenan Inna nagode, a,a wannan aiki ai base munkaima boka ba, nima zan iyayi kinsan Alh, atafin hannuna yake kome nafada mashi zeyarda. Toshikenan kibani nan da kwana 2 idan har ban samuba, zan maki magana idan yaso seki samomun anan, ti nagode, idan Jidda tadawo kigaishemun ita, nakira wayarta bata shiga.


Komawa da baya Baba mairo tayi saboda wani tashin hankali dataji yana shigarta, ta dade afalo kafin naga cikin sauri tanufi dakin Zarah, da sallama tashiga, Zarah tace shigo mairo, shigowa tayi tace Hajiya ga abincin nan, Baba mairo tafada tana goge kwalla.

Zarah tace Mairo lafiyarki kuwa naga kamar kina kuka? Kara rushewa tayi da kuka tasamu guri tazauna, tashi Zarah tayi tace dan Allah Mairo kifadamun ko wani naki ne, ya mutu? Fyace majina tayi tasa zaninta tagoge, sannan tace Hajiya da irin abunda akamun aigara ace mutuwa akayi mani zan iya hakura akan cin mutuncin da wannan yarinya tayi mani.


Ace yanzu duniya babu gaskiya, duk yanda karike mutum da gaskiya da amana shi kokari yake yaga bayanka. Wlh, danasan haka yarinyar nan take simi simi da ita da bandauki amanar da mamanta tabani ba. Amma koyanzu nafada mata najanye rike amanar da aka bani, kuma nace tafitarmun adaki bazan iya zama da ita ba.


Zarah tace aini mairo baki fadamun dawa kike ba kinzauna kina ta kuka. Dawafa nake idan ba wannan Banzar AGOLAR gidan nan ba, wlh, Hajiya kinyi gaskiya tsintartar mage bata mage, wani irin murmushin dadi Zarah tayi tace Mairo wani abu Falak tayi maki ko?


 Haba Hajiya, ashe yarinyar nan yar iska ce bansani ba, shiyasa damatunda kika fara aikenta kasuwa takejin dadi,kullum bata dawowa dawuri, kuma idan tadawo sekiga tadawo da kaya masu yawa, Inazuwa bari kiga wani abu dan kada kice sharri nayi mata. Fita tayi domin dauko abun.


Wani irin tsallen murna Zarah tayi tafada bisa gado tana fadin wlh, karyarki tasha karya Hajjo kice zaki hada kanki kishi dani kizauna lafiya, nayi nasarar kaudaki keda yaronki, yanzu gashi cikin sauki diyarki zata zama karuwa. Gaskiya naji dadi da Mairo tagane gaskiya, kinga yanzu nakara samun yar uwar dazamu huro maki wuta.


Shigowa Baba mairi tayi hannunta rike da Leda, zazzageta tayi sega kayan shafa masu kyau da tsada. Zarah tace ey! Wannan kayan duk natane? Baba mairo tace sosai ma. Kuma waini ina ganin kamar na isa da ita, shine dazu nayi mata magana akan ina take samo kudi haka, se cemuntayi yawon karuwanci takeyi tana samowa kamar yanda nima nakeyi.


Wlh, hajiya kinji abinda yasani kuka wai kamar ni Falak zata kalla ta fadamun wannan maganar. Gaskiya hajiya nadawo rakiyar wannan yarinyar, gata nan duk abinda zakiyi mata kimata, babu ruwana aciki, idan ma kina da bukatar temako na domin akoreta daga gidan nan ashirye nakw da inbaki gudummuwa.


Dariya Zarah tayi, tace aini nasani Mairo, komin dadewa zakidawo gurina, domin ke renona ce, tunda nazo gidannan muka hadu dake, nasan dole kidawo gareni, nasan dama tausayine yasaki temakawa Falak, bade So ba.


Agaskiya naji dadin zuwanki adede lokacin danake neman temakon yan gari irinku, kuma maganar iskanci datakeyi wannan ita tasani, aure ma zanyi mata kowa yahuta, sede ba irin auren da kika sani ba. Anan Zarah takwashe komai tafada ma Baba mairo, sannan tace yanzu Mairo kenake ao kibani shawara ina zamu samo dan iskan dazan bashi auren Falak?


Murmushi. Baba mairo tayi tace haba Hajiya wannan aikin ai semu, kafin infara aiki agidan nan nayi sana,ar saida abinci atasha, nasan yan iskan tasha sosai, bakida damuwa, akan wannan matsalar.


Zarah tace yauwa, mairo amma naji dadi sosai, da Allah yasa kikazo awannan lokacin, yanzu yaushe yakamata ace kinkawo mani shi inganshi? Baba mairo tace kada kisamu damuwa gobe da safe zanje tasha, akwai wani mugun da shaye shaye ne dan shine ogansu atasha, babu irin aiki da baya yi, sede aikinshi kudi ne. Zarah tace karkisamu damuwa, abinda yafi wannan ma nakashe kudi akanshi, kawai kigada mashi duk abinda nake bukata, ni kuma zan damka komai agurinki, dan abanaso Alh, ya fahimci wani abu, kije kugama komai, sede zuwa jibi inason ganinshi. Baba mairo tace angama Hakiya, kada atausaya mata ko kadan, bara inje inga kota kwashe kayanta. Zarah tace a,a mairo kiyi hakuri ki kyaleta. Ai takusa barin gidan


Zaune adaki Baba mairo tasamu Falak suna waya da Sameer, zama tayi tana kallonta cike da tausayi, Baba mairo tace Falak nasan Sameer ne,  idan kungama kice masa gobe yazo dasafe gurin karfe 9 yadaukeni zamuje gidansu akwai maganar dazamuyi.


Kwanciya tayi tana jiran su gama,  haka sukasha fira kafin sukayi sallama, kamar kada surabu, Falak tanajin aon Sameer aranta sosai.

   Baba mairo tayi dariya tace kaga masoya, amma idan nace kina sonshi sekice a,a Falak tace to nadeji yanzu ai kingane abinda muke ciki ko.


Baba mairo tace e nagane shiyasa ma nazo maki da albishir medadi, sede kuma akwai wata matsala, wadda sekinyi hakuri kafin mudace da abinda mukeso, Falak tace lafiya meyafaru kuma? Kiyi hakuri da abinda zan fada maki Falak dole ne nima tasani zabar wannan hanyar, dan ita kadai ce zata bulle mana, 

 Anan Baba mairo ta kwashe duk abinda taji Zarah tana fada, da kuma. Shawarar data yanke tajetasamu Zarah sukayi magana.


Kuka kawai Falak takeyi dataji irin tsanar da Zarah tayi mata, da kuma yanda Baba mairo take kokari gurin kareta aduk halin data shiga. Kwanciya tayi bisa cinyar Baba mairo tace bansan dame zan saka maki ba Baba mairo, badan keba da rayuwata tagama shiga matsala.


Bakomai Baba mairo, duk abinda kika yanke akaina yayi dede, nasan bazaki taba yimani abunda ze cutar dani ba. Baba mairo tace gobe zanje gidan au Sameer zamuyi magana da Mamanshi, da kuma shi, duk yanda mukayi zakiji. Amma dan Allah kiyi hakuri da irin yanda naci mutuncinki agurin Hajiya. Falak tace Baba mairo banaso kina bani hakuri, akan irin wannan abun, haka rayuwata take, dole se anyi irin haka inde anaso insamu abinda nakeso, babu komai, Allah yashige mana gaba kuma yabamu sa,a. Baba mairo tace ameen, haka sukayita fira, sannan suka kwanta.


Jidda ce kwance adakin Al,amin suna waya da Zarah, Jidda tace Ummi dan Allah kisan yanda zakicema Dady, banaso yakira wayata yaji bata shiga nasan yana iya zuwa zariya, nemana, kuma kinga kawata zan raka london zata hado kayan lefenta, bazamu wuce sati 2 ba.


Zarah tace waini Jidda ke haryanzu bazakiyi kokarin kawo mijin aure ba, sede kirika bin kawayenki, kina masu wahala ke kuma kin kasa fitar da gwani, gaskiya nima nafara gajiya, nima inason inga jikokina. Jidda tace haba Ummi, duka yanzu shekarata nawa dazanyi aure, kina ganin yanda mazan zamanin suke fa yanzu, dazaran sun aureka shikenan duk wata hidima dasukeyi maka awaje sundenata. Wani lokacin ma kudin siyan anko seya gagari mutum, kuma kinga ni ba karatu nayi ba, idan ban tsaya natara kudi ba, kinsan karshenta bawani me arxiki bane zezo aurena.


Nide gaskiya Ummi kibari ayanzu inasamun kudi masu yawa dazaran nagama samun kudina zanyi aure, kinga alokacin nima nazama bussiness woman ko? Zarah tayi murmushi tace yauwa Jidda ta, kokefa, aigara kema kitara kudi kozaki fara zama cikin mata masu aji,  to Allah yabada sa,a Allah yasa daga can kena kisamo Alhjin, london kinga semu kaiki can kawai. Shi kuma Alh, kibarni dashi nasan yana zanyi dashi, kije kawai sekun dawo. Amma dan Allah kada kiwuce sati 2, kinsan Alh, dason ,ya,ya.


Damma nima. Bana daga mashi kafa, ai dayanzu yana takani son ranshi. Jidda tace waini Ummi ina Falak da Ameer kuwa? Zarah tadaure fuska tace meye kuma ana maganar arxiki zaki sako mana ta wasu banzaye. To Ameer yajima da mutuwa, Ita kuma Falak tana nan tazama karuwa, shiyasa zanyi mata aure kowama ya huta. Jidda bataji dadin abinda Umminta tafada ba.


Tace Ummi wazata aura? Tace dede da ita ne, zata aura, kewai yanzu bakiga yanda Falak tazama yar duniya ba, har zagin Mairo takeyi fa. Jidda tace dan taga tana da kyau ne shiyasa, ai garama kiyi mata aure kowama ya huta.  Ana. Mn sukayi sallama .


Al,amin ne yashigo zama yayi yace baby wlh nagaji nasha wahala, sosai yau, garin samun visa , amma gashi anan nasamo mana, ina fatan kinga kashe boss na gidanku? Dariya tayi tace tunima, yanzu de karfe nawa jirgin zetashi? Yace karfe 7 na safe. Dariya tayi tajawoshi yafado kanta tana fadin nagode sosai my luv.


Urs,

NABILA RABI,U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[7/13, 09:41] Nabilat Author: 🙆🏻😭😭🙆🏻  AGOLAH!!! Nah 

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI,U ZANGO

( Naneelert Lady)


@ ( H,O,N,A)


Part 80.....85


 Washe gari bayan Baba mairo tagama aikinta gurin karfe 10 kamar yanda Falak tafadama Sameer segashi yakirata yace mata yana inda yatsaya.


Sallama Baba mairo tayi mata, tawuce dakin Zarah tace Hajiya nagama zantafi, dan tunjiya nakira wata kawata damukayi aiki atasha nace mata idan Asid yazo ta tsaidamun shi. Murmushi Zarah tayi tace gaskiya nagode Mairo, Allah yasa amince da bukatarmu.


Baba mairo tace ameen, kudi har dubu 10 Zarah tabama Baba mairo tace tafara bashi kafin sauran suzo, dubu 1 tabama Baba mairo tace tahau abin hawa. Godiya tayi mata tace ta tafi.


Akusa da wani shago Baba mairo taga Sameer duk da bata sanshi ba, amma tana zuwa gurin yace Baba mairo ko? Dariya tayi tace ka canka dede, yace ai tunda kika taho jikina yabani kece. Ina kwana, tace lfiya lau, Sameer, yace muje ko, hawan mashin din tayi suka wuce.


Zaune suke abisa tabarma Sameer kuma yana zaune abisa kujera, bayan sun gama gaisawa, Baba mairo tafara magana. To Halima, nasan de bakisanni ba, amma kuma kinsami labarinmu agutin Sameer.


Bawani abu bane yakawoni se akan maganar da nasan Sameer yafada maki. Halima tace kwarai kuwa yabani labarin Falak me cike da tausayi, kuma yayi mun magana akan yana son aurenta, kuma nima nayi na,am da maganarshi.


Sede yanzu bansan wace magana zakiyi ba. Baba mairo tace hakane, kuma naji dadin yanda kika amshi maganar, babu abinda zamu ce maki sede muce Allah yabiyaki. Kamar yanda kika sani nide ban hada komai da Falak ba, Allah yahadani dasu, tunbayan da Alh, yakawosu gidan danake aiki.


Munyi zama na mutunci da Maman Falak, wadda itace takawomun yanci agidan danake aiki, ada babu wanda yakemun daukar uwa agidan, duk da na a haifena haifi ita kanta Hajiya ba ,ya,yanta ba. Amma suduka mutum 1 ce take bani girmana, wato Jalila. Zuwan Hajiya Hajjo tasakamun Baba mairo, dan ita tace bazata iya kiran sunana kaitsaye ba, hakan yasa tundaga kan Alh, har ,ya,yanshi suka koma kirana haka, sede Hajiyace kadai take kirana da mairo.


Bayan mutuwar Hajiya nacigaba da rikon yayanta, har Allah yadauki dayan, sede Falak kawai tayi saura. Kuma itace Hajiya ta maidata kamar baiwa agidan, datana da ikon kasheta kamar yanda tayima mamanta da kaninta itama da tuni takasheta. Nadade ina tunanin hanyar dazan bi inga Falak tabar gidan, sede kafin mutuwar hajiya tabar mata wasiyar komin rintsi kada tabar gidan Alh, har se idan aure tayi.


Nima haka tabani wannan wasiyar, duk da yanzu Falak ba abakin komai take agurin Alh, ba, kuma ba aikin kowa bane sena Hajiya Zarah, kwata kwata yanzu Alh, yamanta da wata Falak agidanshi, shi kanshi yazama shanyayye agidan.


Ina cikin neman mafita segashi Allah yakawo mana Sameee, tun ranar da yafara temakon Falak naji inama ace yazo yanemi auren Falak, alokacin hajiya bata lafiya anrasa wane irun ciwo take, Sameer yabama Falak wata addu,a cikin ikon Allah ana fara yimata ita tasamu sauki, hakan yasa muka dawo gida akacigaba dayi mata addu,a.


Sede alokacin da ciwaonta yakara tsanani Sameer. Yakoma makaranta, kuma wannan ciwon shi yazama ajalinta. Ajiya naje kaima hajiya abincinta naji wata magana data firgitani,.........   Anan Baba mairo tafada masu irin wayar dataji Zarah tanayi ajiya.


Ina gama jin wayar nan narasa yanda zanyi intemaki Falak, kawai senayi amfani da abinda nafada maku nashiga gurin hajiya da maganar, cikin ikon Allah tayarda da abinda nafada mata, kasancewar mafita take nema, kuma dama hajiya duk wani makiyin Falak to ita masoyinta ne.


Shine nataho domin infada maku shawar danazo da ita. Goge kwallan idonta Halima tayi, shima Sameer tunda yaji irin abinda akeson ayima Falak dinshi yafara kuka. Halima tace lallai wannan mata batada imani, kuma zata iya kashe Falak, damane kawai bata samuba.


Yanzu wace shawara kika kawo? To kamar yanda mukayi da ita, azuwan nataho tasha ne insamu Asid wanda haka kawai nafada mata sunan, domin acan garinmu akwai wani dan kwaya haka ake cemashi, toganin sunan yayi kama dana marasa da,a yasa nima nace mata sunanshi kenan.


Sameer kaida Falak duk sekunyi hakuri idan har kunaso mucima burinmu, Halima cewa nayi meze hana Sameer yayi basaja yazo amatsayin Asid danace zankawo. Ammafa seka canza shigarka, dole kasamu kaya irin na yan iska, da kuma sarkar dazakasa awuya, domin hajiya tayarda kayi dede dawanda takeson bama Falak, kaga idan har Allah yasa mukaci nasara, shikenan Falak tazama taka, kada kadamu da maganar hajiya dan tace shekara 1 kawai takeso Falak tayi agidan aure asaketa. Mude burinmu tabar gidan, kaga idan har igiyar aurenta tazo hannunka, kaine kake da saki, kuma nasan duk inda za,aje babu mesaka kasaketa, tunda ba ita ta haife taba.


Halima tace agaskiya Baba mairo wannan shawara tayi, koko yakace Sameer? Goge idonshi yayi yace hakane Umma , ashirye nake dayin duk wani abu daze fitar da Falak daga rayuwar datake ciki. Insha Allahu gobe zanzo gidan amatsayin Asid kamar yanda kikace Baba mairo. Allah yayi mana jagora.


Suka ce ameen. Halima tace toyanzu Sameer dole mufara shirin biki, dan nasan baze dau lokaci ba, anjima zansamu kawunka, infada mashi halin da ake ciki, nasan shima zebamu goyon baya, danshima mutum ne me gaskiya kuma gashi malami. Bab mairo tace Kada ku takurama kanku kuyi abinda zaku iya, daga baya komai zeyi dede, nasan ai anan gidan zata zauna ko?


 A,a gaskiya Baba mairo nide nafison yaje yakama masu haya mesauki suzauna, idan Allah yasa yasamu aiki ko kuma kasuwancin dayakeyi ya kara kwari tunda yanada filinshi se yafara gini, wlh, banason zama gida daya da sirika, kinsan ance yau da gobe se Allah.


Sosai Baba mairo taji dadin abinda Halima tafada, tace toshikenan Allah yatemaka, kai kuma Sameer banason katakura kanka, kasamu gida mesauk, badole sekunj dadi alokacin da kukeso ba, da sannu wata rana rayuwa take canzawa, kuma duk kudin da hajiya tabayar abaka kayi amfani dasu ka kama haya kuma kayi hidimar bikin dasu.


Sameer yace to Baba mairo, bazace zanki amsar kudin ba, sede kisani bazan yi amfani dasuba, yanda kika bani haka zanba Umma ajiyarsu, banaso in auri Falak da kudin haram, kuma nasan wata rana dole Hajiya zatayi mani gorin abinda tamun duk ranar datasan gaskiya, kuma aranar zanbata kudinta.


Baba mairo tace gaskiya wannan yaron kacika da halak, Allah yayi maka albarka. Ni bara inzo intafi, tunda Allah yasa nasamu abinda nakeso, kada taga kamar na dade. Halima tace to Baba mairo mungode, kema Allah yabiyaki irin jihadin da kikayi. Sameer yayi dariya yace au BabaMairo namanta fa Falak tace idan har badake zamu tafi ba, bazata aureni ba. Dariya sukayi Baba mairo tace haka kullum take cewa. Halima tace ai wannan haka yake, banga abinda zaki zauna kiyi agidansu ba, dama zaman Falak kikeyi, tunda tayi aure ai shikenan. Sede nima ina da tawa shawarar. Baba mairo anan gidan zata dawo da zama,ba gidanku ba. Sameer yace a,a gaskiya Umma kingafa munrigaki. Baba mairo tace kyalesu dama koda tafada nibanyi niyar zama ba, niyata bayan aurenta inkoma garinmu.


Halima tace a,a Allah baza,ayi haka ba kinga babu kowa anan gidan dama diyar kanwata ce nace zata dawo nan idan Sameer yayi aure, tunda kuma gaki ai setayi zamanta, dama ina da almajiri memun aike aike, Allah babu wani abu kidawo nan dazama. Baba mairo tace toshikenan. Allah yamana jagora. Sameer yace wato de anyimana kwace da rana tsaka ko? Sukace ai haka yafi gara abarku kukadai kusan zaman aure kukeyi. Da haka Baba mairo tayi masu sallama tare da bama Halima dubu 10dan tafara ajewa.


Haka Baba mairo tajema Zarah da albishir medadi. Zarah bakaramun dadi taji ba, tace kuma acikin sati daya za,ayi bikin. Baba mairo tace a,a yace yafison nan da sati 2. Zarah tace shikenan, idan Alh, yadawo zanyi mashi magana yabada kudi asai mata kayan aure amma tsofaffi za,a siya mata suma dan kada mutanen gari suce bamu rike amanar da,a bamu ba. Kema zanba kije gurin dillalan nan mata kisiyo mata gado da katifa, se kujeru da yan kayan kitchen, zance mashi cikin kudin dazan bashi yasiya mata kaya kala 3 wanda zatasa da biki.


Haka Baba mairo dashigo daki tasamu Falak tafada mata duk yanda sukayi da Sameer da kuma Zarah yanzu. Sosai Falak taji dadi tajiba, jitake kamar anyi mata albishir da gidan aljanna, itade idan harzata bar gidan nan to ko inama ta tafi.


Jalila tana karatunta hankali kwance, sede akai akai suna waya da Falak, amma Falak bata fada mata labarin aurenta da Sameer ba, da Baba mairo tahana tafadama kowa har Jalila, saboda tace tsakanin da da Mahaifi se Allah, tabarshi idan komai yayi dede taji. Ko maganar auren daza,ayi mata ma sede agurin Zarah Jalila takej, aranar dataji bakaramin kuka tasha ba, tana tunanin wace irin zuciya Umminta gareta.


Jidda kuwa aranar dasuka isa london kwanan Al,amin 2 yayi mata sallama yadawo nigeria, har kuka seda Jidda tayi haka yayita lallashinta, yace nan da sati 4 zezo yadauketa su koma. Tun bayan tafiyarshi suke more rayuwarsu itada abokin Al,amin Joseph, bakananan kudi Joseph yake bama Jidda ba, seda takai har Sallah Jidda tadena yi, rayuwar turai kawai takeyi, idan kaganta sekace baturiya ce, dan takara zama fara sosai.


Yawo sukesha ita da joseph, suk inda takeso yana kaita, domin sosai yakejin dadin harka da Jidda, har fada yakeyi tafi sauran yanmatanshi komai, shiyasa tunda tazo ya sallami yan matanshi, ita kadai yake harka da ita. Duk kudin dayake bata betaba barin takashe koda gwandala ba, shine yake mata komai, shiyasa ma take adana su acikin akwatinta.


Sameer yazo gidan su Falak cikin irin shigar da babu wanda zeganshi yace mutumin kirkine, sosai Zarah taji dadin ganinshi haka, kuma tabashi kudi masu yawa, tace idan Alh, yadawo nan da jibi zata kirashi yazo sugaisa. Amma inaso aranar kadan saka manya kaya, idan ma baka dasu ka aro, duk da zancema Alh, me aikina ce zatayi aure kuma shine ze zama waliyinta, kaga bazeji dadi yaganka cikin irirn wannan shigarba. Anan sukayi sallama yatafi.


Halima tasamu kawun sameer tayi mashi duk bayanin abinda akeciki agame da auren da Sameer zeyi, shima ya tausayama Falak sosai, kuma yace babu damuwa zeje yayi yanda sukace.

     Bayan Alh, yadawo Zarah tayi mashi bayani akan auren dazatayima me aikinta, dakuma abinda takeso yayi, babu gardama ya amince, kudi yabata naira dubu dari 500 yace gatashi gudummuwar asaya mata kayan daki, godiya tayi mashi, sannan tace anjima Sameer da kawunshi zasuzo gaisheshi. Alh, yace sunan yaron sameer tace E, dan shima haka yafada mata, amma yace ba,a kiranshi da sunan, sede Asid, dan Sameer cewa yayi bayaso adaura auren Falak dawani sunan banashi ba. Alh, yace Allah yakawosu lafiya.


Haka su Sameer da kawunshi sukazo suka gaisa da Alh, sosai kawun Sameer ya tausaya ma Alh, gashide cikekken mutum amma yana ganinshi yagane akwai sihiri ajikinshi, dan kawu malamine sosai, haka su kawu suka bada kudin aure da kayan sa rana akasa biki sati 2.


Zarah tabama Baba mairo dubu dari da hamsin  tace tayima Falak siyayya, daga can awuce dasu gidan dazasu zauna bataso akawo matasu, Baba mairo tace hajiya bazakije ganin gidanba? Zarah tace Allah yakyauta, ai naji dadi tunda kina nan, sekiyi komai.


Sameer yasamu dan karamin gida yakama haya, har fenti seda yasa akayi, sannan su Baba mairo suka kawo kayan daki akayi jere, gado ne da kujeru, se katifa dukansu tsofaffine, sede basosai suka tsufa ba, dan hada kudin Baba mairo aka hada akayimata siyayya, kayan kitchen ma, ansai mata rishow da tukunya 2 se kula 2, jug 2 da plate da ludduwa se cokali. Gidan balaifi yayi kyau. Ana saura kwana 2 daurin aure aka kawo kayan da Falak zatasa , suma acikin bakar leda ne, kala 3 kananan atamfofi se takalmi 1. Zarah kamar zatayi rawa dan murna, su asabe da Dije duk sunzo, amma babu abinda suka kawo.


Aranar asabar aka daura auren Falak da Sameer akan sadaki dubu 20, ba laifi mutane sunzo yan unguwa, dayake Alh, yasa anyi sanarwa amasallaci za,ayi daurin aure agidanshi, yan uwan Sameee ma sunzo.


Da dare gurin karfe 7 aka kawo mota daya somin daukar amarya, Zarah tacema Dije da Mairo suje sukai amarya se sudawo. Haka aka fita da Falak, dan babu wani fada da Zarah tayi mata, Falak taso taga Alh, amma Zarah tahana, dan boka yace duk ranar dasuka hada ido da Falak da Alh, asirin ze karye. Haka Falak tafita tana kukan rashin Uwa. Mutanen unguwa se gulmar Zarah sukeyi suna cewa takasa rike amanar da,a barmata. Su Baba mairo basu dade ba, suka juyo, Falak kuka kawai takeyi. Bayan tafiyarsu Jalila ta kirata awaya, tana kuka tana bata hakuri, tace. Wlh Falak bazan iya zuwa inga irin auren da Ummi tayi maki ba, kiyi hakuri Falak, insha Allahj wata rana komai zewuce. Falak tace bakomai Jalila nagode, haryanzu de kinkasa zuwa gida ko? Jalila tace Falak banason abinda Ummi takeyi agidan nan, shiyasa nafison zama. Makaranta akan gida. Falak tace banason Haka Jalila, da kunsamu hutu kidawo gida, ko kin manta wa,azin da Malam Sameer yayi mana akan muhimmancin uwa? Kome Ummi tayi dole kibata hakkinta amatsayintana Uwa, idan har kinaso mushirya to da kunyi hutu kizo gida. Jalila tana kuka tace shikenan Falak zanzo, nagode da tunin da kijayi mani. Allah yabada zaman lafiya, yasunan mijin naki?  Falak tace nimade Ummi tace mun sunanshi Asid. Jalila tace dan Allah jiwani suna, kiyi hakuri Falak nasan Ummi tasakaki kowace rayuwa kika shiga. Sallama tayi mata takashe wayar. Murmushi Falak tayi tace Jalila Umminki tabiyani tunda hartayi sanadiyyar sama mun farin cikina.


Urs, 

NABILA RABI,U ZANGO

( Nabeelert Lady)

08028525263

[7/13, 09:41] Nabilat Author: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!!Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI,U ZANGO

( Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)


Part 85.....90


Zaune take ita kadai tana ta tunanin irin rayuwar da tayi, addu,a tayi Allah yasa aurenta yazamo karshen yankewar wahalarta. Sallama taji anyi, Sameer ne yashigo bayan ya kulle gidan sannan yanufi dakin da Falak take.


Zaune take da ganin idonta taci kuka, harta gaji, zamayi kusa da ita tare da cire mayafin data rufa, hannu tasa tarufe fuskarta, murmushi yayi yace Falak yau kuma rowar fuskar akemun? Ai yanzy munzama daya, nazama ke kin zama ni. Cire hannunta tayi tana kallonshi tana murmushi.


Falak nagaji dayawa, tashi muje muyi wanka, kafin muzauna ko? Aini nayi wanka sede kaje kayi, uhm bawani nan banyarda ba, to koma kinyi zaki sakene, ai bance kiyi ke kadai ba, tashi tayi tashiga bandaki ta hada mashi ruwan wanka sannan tafito, kokarin cire riga yake yana fadin da gaske fa nake tare zamuyi, ai tun kafin yakarasa fadi tayi waje.


Dariya yayi yace matsoraciya, wata rana zamuyi ne, shiga yayi bandakin yayi wanka, seda yagama shiryawa sannan tashigo itama tawuce bandakin, daga cikin dakin yake mata magana, kiyo alwala kafin kifito fa.


Bayan tagama tafito tadauki diguwar rigarta a durowa takoma bandaki tasaka sannan tafito, turare kadai tashafa tashimfida masu abin sallah, shiyajasu sallah har suka, gama, sannan yayi mata tambayoyi akan addini, dayake Falak akwai kokari duka ta amsa tambayar da yayi mata,


Tashi yayi yadauko ledar daya shigo da ita, kitchen ya koma ya dauko plate sannan yazuba masu, shiyarika bata shima yana ci, harsuka koshi, Falak de kunya takeji takasa sakin jikinta. Kwashe kayan yayi ita kuma takoma bandaki tayo brush, abandakin yasameta tana shirin fitiwo, hannunta yakama, seda yagama sannan suka fito tare, rigar jikinshi yacire dagashi se gajeran wando da vest, saurin rufe idonta tayi, jitayi itama yana kokarin cire mata riga, tace sanyi fa nakeji.


Dariya yayi yace ai bargo zamushiga, haka yacire mata riga daga ita se under wear da vest yabarta, bisa gado yajata, bayan aun kwanta yajawota yadorata bisa kirjinshi, yanata shafa mata kanta, tuni jikin Falak yafara rawa. Murmushi yayi yace Falak sarkin tsoro, ni babu abinda zan maki, magana zamuyi, kuma nafiso injiki ajikina shiyasa.


Ajiyar zuciya tayi dataji kalamansa. Falak, Sameer yakirata, na,am. Dole mugodema Allah daya nuna mana wannan rana, bazan iya kwatan tamaki irin farin cikin danake ciki ba, Allah yasani duk da ga yanda akayi aurenmu. Wlh banajin haushi kokadan, nasan dayawa mutane suna gulma akan aurenmu, amma ni beda meni ba.


Nasan Falak zakiji haushi da irin yanda na aureki, kiyi hakuri, komai ze canza, duk da kinfi kowa sanin yanda aurenmu yakasance amma dole inbaki hakuri, insha Allahu gobe tela zekawo maki dinkunanki, akwatinanki kuma suna gurin Umma, suma gobe zan daukosu.


Nayi hakane saboda banaso Umminku ta fahimci wani abu, shiyasa nakawo kaya marasa kyau, inaso kidaukeni abokin rayuwa na har abada, banida niyar cutar dake, kuma insha Allahu zan zamo maki abin alfahari, idan komai yayi mana dede zaki koma makaranta kema kiyi karatu kamar kowa,


Banaso idan kina da damuwa ki boyemun, yanzu bakida kowa seni, Baba mairo tayi maki nisa, yanzu nine makusancinki, idan har muka gina rayuwarmu ahaka, tabbas zamuji dadi kuma wani abu baze shigo ya tarwatsa zamammu ba.


Kamar yanda Umma tace nan da kwana 2 Baba mairo zata koma gidanta, itama bazata kara zama amatsayin me aiki ba, shikuma Dady insha Allahu zamu sa shi acikin addu,a kawu ma yace zetayamu da addu,a domin tun ranar daya ganshi yagane yana cikin yanayi na asiri.


Allah yanbani ikon rike amanar dana dauko, kuka sosai Falak takeyi, jawota yayi yakara rungumeta yana lallashinta, shiru tayi tana maida numfashi. Dagowa tayi ahankali tace Bansan dame zan gode maka ba, Allah ya..... bata karasa ba, jin yahade bakinsu guri daya, kissing dinta yake sosai, tuni jikin Falak yafara rawa, jin irin abubuwan dayake mata. Daga haka labari ya canza.


Zaune suke adaki suna ta faman dariya, Zarah tace yakukaga irin aikina, ai nafada maku bazan taba barin Falak tayi rayuwa me dadi ba, haka zata kare daga karshe tayi mutuwar wukakanci. Dije tace gaskiya hajiya kema kin iya aiki, yanzu dasunyi shekara 1 ze saketa?


 E haka nace mashi, daga farko, amma daga baya nace mashi dayaji ta isheshi ze iya koromun ita, kuma nace mashi yatabbatar yayimata raga raga, kada ya saukaka mata dede da kwana 1, kuma nace karyayi mata riko mekyau, kinsan dangiya akwai dukan matansu, haka ze maidata kamar jakarshi, ga aiki ga duka, kafin tadawo gidan nan setakoma kamar me kanjamau.


Asabe tace, amma inafatan idan tadawo ba,anan zata cigaba dazama ba ko? Zarah tace haba de, nikam mezanyi sa wannan yarinyar, ai dama burina ta wulakanta, idan da halima sonake tafito da ciki. Dije tace duk da haka idan tafito kada kibarta tashiga duniya haka, kinsan mutane akwai tausayi, wasu zasu iya daukarta su temaka mata rayuwarta zata iya yin kyau nan gaba.


Kawai itama ayi mata yanda akayima uwarta, asamata ciwo me tsanani kinga kota tafi acan zata mutu. Zarah tace kwarai kuwa wannan shawara taki tayi, zanjira fitowarta, sekuje gurin boka yayi mata aiki. Haka sukayita fira daga nan Zarah tayi masu seda safe tawuce gurin Alh,.


Jidda da Joseph suna nan suna cin duniyarsu, Jidda tayi kyau hartagaji, lokaci zuwa lokaci suna waya da al,amin shima idan yakirata seta ga dama take dauka, ayanzu yanda takejinta cikin daula, gani take tafi karfin Al,amin, shiyasa yanzu take mashi wulakanci. Tunbaya damuwa haryafara damuwa, ganin abin nata yana kara gaba, yasa yayima Joseph magana akan zezo yadauketa.


Dayake agaban Jidda sukayi wayar tun kafin Joseph yabashi amsa ta anshi wayar, cikw da masifa tace wai kai Al,amin ana so dole ne? Nifa yanzu babu wanda zetakuramun nima inada yancin dazanyi rayuwar danakeso, saboda haka dan Allah ka sauraramun kafita ahanyata, wlh yanzu nafi karfin ace wai kai saurayinane, ko ada rashin wayo neyasani biye maka, amma yanzu kasani ni Jidda nafi karfinka, bani ba kai.


Kashe wayar tayi tacema Joseph kada yakara daukar wayarshi, ita baruwanta dashi, anan zata zauna idan taso tafiya gida zata tafi ita kadai. Wani irin mugun murmushi Joseph yayi, dama yana lallaba tane saboda idan Al,amin yadauketa, idan yakara neman tazo zata iya dawowa.


Al,amin kuwa mamaki ne yakamashi, tsayawa yayi yana kallon wayar hannunshi. Wasu irin zafafan hawayene suka rika zubi mashi, har ga Allah yaso ace Jidda ta saurareshi, yanaso tadawo kodan yafada mata shiyanzu yatuba, yanaso itama ta tuba kuma shize aureta, tunda dama shine farkon lalata ta.


Tunda yaga wani abokinshi agabanshi yarasu, tundaga ranar tsoron Allah yakamashi, kuma yayi alkawarin baze kara aikata zina da duk wani laifi marar kyauba. Hakan yasa yakira joseph dan yaje yadauko Jidda amma tayi mashi rashin mutunci. Kuka sosai yakeyi yana fadin why Jidda, meyasa zakimun haka, kinsan ina sonki, tsautsayi ne, da rudin shedan yasa harna iya bama wani banzan arne ke yake kusantarki kamar matarshi, nayima Allah laifi megirma da har na iya amincewa da makiyin Allah.


Tashi yayi yashiga bandaki yayo alwala yafara sallah, bayan yagama yakira wani abokinshi yace mashi   yanason visa zuwa ummrah idan ze samu, yace mashi babu damuwa yazo gobe. Al,amin yace gara intafi inje inemi yafiyar Allah shine abinda yafimani. Ke kuma Jidda zancigaba dayi maki addu,a insha Allahu ko ban aureki ba, yanda na kaiki nine zan daukoki, nasan Allah baze yafemunba matukar ban raboki daga gurin kafirin Allah ba.


Washe gari dasafe Sameer yatemaka ma falak tayi wanka yagyra gurin bayan sunyi sallah suka koma bacci, rungume yake da ita kamar ze maidata ciki, se albarka yake samata. Segurin karfe 10 sukatashi, alokacin Ummanshi ta aiko masu da abinci, haka suka ci , ya gyara gurin, fita yayi yace zeje gida daga can yawuce kasuwa gurin me dinki.


Shatara ta arziki Zarah tayi masu Asabe, Godiya sukayi mata tasa driver yamaidasu. Komawa tayi daki tadauko wayarta domin takira jidda, dan jiya Alh, yake tambayarta ita, harcewa yayi tadawo gida hakanan, duk da yana tsoron Zarah amma bayajin tsoron yimata magana akan yaranshi, sede idan ta taso mashi da masifa ne, yake rudewa. 


Itama Zarah hankalinta yafara taahi ganin haryanzu Jidda bata dawo ba, tsaki taja ganin haryanzu wayar taki shiga, hakan ya tabbatar mata basu dawo ba. Oh ni Zarah kada fa yarinyar nan tajawo mani abun fadi agari, daga zuwa hado kayan aure shikenan. Kuma gashi ko sunan kawarta ta bansani ba, bare insan gidansu. Danaje na tambayo ko lafiya. Gaskiya nima nayi sakaci, kuma Inna Asabe ai tacemun babu inda Jidda take zuwa kullum tana gidanta. To ina tasamo wannan kawar?


Baba mairo ce tayi sallama harya zauna Zarah batasan tashigo ba, seda ta tabata sannan taji shigowarta, Hajiya lafiya kike irin wannan tunani haka? Ai nadauka bakida sauran damuwa yanzu, Murmushi Zarah tayi tace nikam damuwar mezanyi yanzu, kawai ina lissafin wasu kuda dene.


Murmushi Baba mairo tayi, dan taga alamar Zarah batasan duk abinda take fadi afili tafadeshiba. Hajiya dama zuwa nayi ince maki inaso zanje ganin gida, kinga na dade banjeba, amma wannan karon gaskiya zan jima, kila ma zanyi kamar wata 5. Waro ido Zarah tayi tace haba mairo, wata 5 fa? Yanzu yakike so inyi da aikin gidan, to hajiya gashi bansan inda zan sama maki wata ba, sede ki bincika nasan zaki samu.


Toshikenan, yaushe zaki tafi? Gobe nakeson tafiya. Allah yakaimu, bara zanfadama Alh, anjima seya sallameki, godiya tayi mata ta fita.


Falak tana zaune ita kadai afalo gashi babu kayan kallo, sede game kawai takeyi da wayarta. Sameer ne yashigo da sallama yana fadin yi hakuri baby na, nabarki gida ke kadai, wlh ina kasuwa tundazu. Murmushi tayi ta taso takarbi kayan daya shigo dasu tana fadin sannu dazuwa.


Komawa yayi yadauko sauran kayan, ruwa takawo mashi, sannan takoma tadauko abincin da aka kawo masu daga gidansu Sameer. Jawota yayi yana fadin kinzauna shiru ko? Kiyi hakuri zamu sa kayan kallo kinji. Abinci tamika mashi abaki tana fadi bakomai wata rana ai bazan zauna shiruba ko? Yace hakane, karbar cokalin yayi yacigaba da bata shima yana ci.


Bayan sungama takwashe kayan ta kai kitchen, seda ta wankesu sannan tafito, zama tayi yafara fiddo mata kayan dinkinta, sosai kayan sukayi kyau, ga kuma sauran daba,a dinka ba, acikin akwati da kayan shafa, akawatina 3 da kit yayi mata, kayan sunyi kyau sosai. Haka yasata tayi ta gwada dinkunan.


Washe gari. Da safe Baba mairo tashiga yima Zarah sallama, dubu 5 tabata tace inji Alh, yace tahau mota, se kuma kudin aikinta na watan tabata dubu 15, ita kuma takara mata dubu 2. Duk da dubu 50 Alh, yabata yace tabata hada kudin aikinta sauran kuma tayi tsaraba da kudin mota. Amma seda tarage. Godiya tayi mata tadauki kayanta tafita tana fadin nida aiki agidan nan har abada, Allah yatoni asirinki ke kuma.


Nima nace Ameen.


Post a Comment

0 Comments