AFSANA HAUSA NOVELS

 AFSANA*🌹 

   [ *LABARI NA*] 

_*short true life story*_

🌹

🌹🌹

🌹🌹🌹

🌹🌹🌹🌹




🌹 _*TRUE LIFE STORY*_🌹





Page-3⃣



WRITTEN 

      BY

🌹AMEENA UMAR

 FARUQ🌹  


 OR

🌹MEENAT🌹



_*WANNAN page NAKINE MY SWEETHEART SADEEYA SADEEQ DOMIN NAJI KIN YABA DA AFSANA, DON HAKA GASHI NAN KIYI YADDA KIKESO DASHI.*_




_______________________


® _*PEN: WRITERS ASSOCIATION*_


_*only the exquisite and whizkid writers are opportunity to be pen writes*_





✍🏽



    



"Don Allah kayi hakuri karka cutar dani, bai saurareni ba asalima kokarin fisgoni yake don haka dasauri nasauka daga saman gadon, yayinda jikina sai rawa yake cikin zafin nama irin na cikakkun maza masuji da karfi ya fisgoni nadawo saman gadon, ya haye kaina "aikam nasaki wani irin mahaukacin ihu tareda dukansa da ya kushinsa amma ko gezau baiyi ba, balle nasa ran zaya kyaleni. 


Don haka saina fara rokonsa  yayiwa girman Allah karya ketamu mutuncina, saidai Ina baimasan inayi ba domin kuwa kokarin rabani dakayan jikina yake, ganin haka yasa nafurta araina to kodai kurmane mutumin nan?..kirjina ne yacigaba da matsanancin bugawa, idanko hakane yauna shiga ukku ni Asma'u kukana yakaru tunawa dacewa wato ihun banza nakeyi kenan?..


Wata dabara ce tafado mun, kawai saina gantsara masa cizo "akirji aikam dasauri ya dagani yana furta auchhhh!, nikam dasauri nasauka daga saman gadon yayinda jikina sai rawa yake, da gudu zan nanufi bakin kofa, saidai me?..jinayi ya  fisgoni da karfi sannan ya sharara  Mun wani irin azababben marin, 


Da Saida naji-jina yadauke nawucin gadi, sannan yafaremu kafa nasube kasa Cikin matsanancin tashi hankali na mike tsaye dasuri,


yayinda shi kuma yafisgoni jikinsa, aikam tuni muka fara kokawa yana kokarin maidani saman gado nikuma nayiki yadda.


Don haka yasake yarfa mun wani lafiyayyan marin, dasaida na gigice saboda tsananin azaba, sannan ya daukeyi yamayar saman gadon.


"Ahankali Haj Asma'u tayi ajiyar ZUCIYA  sannan tace Haj Aisha, aranan naga tashin hankalin da ban taba ganin irinsa ba tunda uwata ta haifeni,

Sannan taci gabada cewa"....


Still kokawa mukaci gaba dayi asaman gadon dambe sosai muke, Ina kuka mai tsanani yayinda nakejin zuciyata kamar zata fashe don bakin cikin abunda keshirin faruwa dani, domin tuni nagae mutumin nan FYADE yake shirin yimun, don haka turesa nake da iyakar karfina tareda dukansa da ya kushinsa, 


Shiko cizo nayi masa yafi akirga Saidai kuma baiyi tasiri agaresa ba, domin kuwa ko gezau baiyi ba asalima saikace Ina kara masa karfi ne.


Don haka gaba daya na galabai ta nafita daga hayyacina,  domin nayi abunda bantaba yinsa ba tunda nake "arayuwata wato kokawa, kokawar mada namijin cikakke wanda ya samsa sunansa namiji, dan'ni tuni na shaida haka tunganin farko danai masa saidai na nad'asa shugaban  azzalumai da marasa imani na duniya.


Sai faman turesa" nake da dukansa da dan sauran karfin da yarage mun, saidai hakan bai hanasa fasa aikata abunda yainin yar aikatawa agareni ba dan haka, Ina jinsan yara banida kayan jikina saidai kuma "a lokacin kadan yarage numfashi na yadauke, Wanda naga kokarinsa ma  da tun-tuni bai dauke ba, saidai ba mamaki! yana jiran lokacine,


Wanda kuma nasan lokacin yayi domin kuwa jinai yana kokarin shiga ta. Kirjina yatsanta bugawa yayinda na  rintse idona araina nake fadin Oh! wai yauni Asma'u ce wani namiji zaya kusanceni ba tareda aure ba, da karfi nafurta yah! Allah kadauki raina nahuta da ganin  wannan bakar rana me cikeda bakin Cikin.


Wani razanan nan Kara nasaki saka makon jinda nayi yashigeni da karfi, sai kuma naji numfashina yana kokarin kufce mun ma'ana yana shirin barin gangar jikina, Don haka banyi yinkurin hanashi ba tunda dama abunda nakeso kenan,


Don haka sai kawai na sake shi ya kufce wanda bana fatan yasake yadawo gareni, saidai kuma kash! saida yadawo domin kuwa bude idonayi naganni kwance agadon asibiti.


"Ahankali nake kallon dakin koma nace mutanan dake cikin dakin, wanda bansan kosu nawa bane nadai gawasu tsaye wasu kuma zaune akujera, idona ne yasauka akan siririn igiyar roban dake daure ahannuna wanda ga dukkansu alama a asibiti nake kuma karin ruwa akeyi mun, tambayar kaina nayi to meya kawoni asibiti?.. Kuma.


 ahankali na maida kallona kan aunty Khadija dake zaune kusada ni, tana rikeda hannuna me daureda ruwan saina ga tana sharan hawaye alamar kuka take.



Ahankali nace Aunty Khadija meyasa meki kike kuka?.. nikuma mesa meni nagani agadon asibiti kwance?..dasauri ta mike tareda cewa Alhamdulillahi yau Asma'u ta farfado, Dasauri nace Aunty Khadija tun yaushe ne nake kwance a asibiti?.. tace  yau kwananki biyu baki da lafiya shine sai yau kika farfado?.. bance mata komai ba saidai kawai nacigaba da kallonta ZUCIYATA cikeda mamakin abunda yasa menu,


 yayinda itakuma take fadin Alhamdulillahi Allah mun gode maka kuzo kugani yau Asma'u ta farfado, dasaurin naga sun nufoni Umma Malam, yaya Auwal yaya Usaman, harma da matar yaya Auwal da mijin Aunty Khadija, dukkansu sai sannun nuke mani, ban'amsaba saidai binsu da kallo danake tayi.



Aunty Khadija tace sannu Asma'u, Shuru nayi Ina kallon ta yayinda nake tunani abunda yasa aka kawoni asibiti har kwana biyu ban farfado basai yau, can sanaji komai yana dawo mani tiryan-tiryan tudaga lokacin andaukeni amota har lokacin da mugun mutumin nan yayimun fyade dakarfi, 


aikam da sauri na rintse ido tareda saki kara na fisge karin ruwan da akeyimun, ihu nake sosai tareda fisge-fisge inata sanbatun tamkar alokacin abun yafaru, cikin tashin hankali suka kira Likita yaimun alluran barci.


Kodana farka daga bacci banyi fisge-fisge ba, saidai kuma banin magana ba sannan kuma idan anyi mani bana amsawa, ahaka har naji sauki aka sallameni muka koma gida.


*******


Dukkan mu muna dakin Umma nida yan'uwana harda malam, kwance nake saman gado kaina  yana saman cinyar Umma tana shafamun, yayinda kafata ke saman cinyar Aunty Khadija tan mammatsa mun, cikin sanyin murya Aunty Khadija tace Asma'u kiyi magana kifada mana wanene yaimaki wannan zaluncin?..cikin bacin rai yaya Usaman, kasan cewar shi mutune mai ZUCIYA sosai don haka yace babban zalunci ma kuwa, Ga fyade ga marirruka sannan don mugunta aka jefarda ita bakin titin ruwa yanata dukanta, wlh inda zanga wanda yai mata wannan aikai-aikar tambas saina rabashi daransa bakin azzalumi kawai, dasauri malam yace kul-kul-kul nasa kejin wannan furucin yafito daga bakinka shuru yayi amma ransa abace,

Shikam yaya Auwal dama bame son hayaniya bane saidai abunda akai Mani yayi matukar bata masa rai sosai, cikin sanyi murya yace Asma'u kinsan wanda yai maki fyade?..


Wani abunaji yacaki ZUCIYATA dan haka, tunawa da bansan kowane ba, Kawai sai nasaki wani irin kuka mai taba ZUCIYAR mai saurare, kuka nake tamkar raina zaya fita saida nayi mai isata sannan nayi shuru ba tareda kowa yace mun Kala ba, 


Cikin sanyi murya malam yace"


Bayan kin baro gidan yar'uwarki meya faru dake?.. cikin shashsheka kuka nafada masu duk abunda yafaru tundaga farko har karshe, cikin bacin rai yaya Usaman yece kaji bakin  azzalumin Allah ya'isar maki, ajiyar zuciya malam yayi sannan yace idan kikaga mutumin zaki ganesa?..nace a ah yace to shikenan aikansa yayiwa, don haka kiyi hakuri kidauka cewa dama tun ran nan da'aka halicceki Allah ya kaddara sai hakan tafaru dake, don haka inasonki kidaukesa amatsayin  jarabawa kinjiko?.. nace to.


Sannan ya kalli yan'uwana yace kuyi hakuri da'abunda yasamu yar'uwanku haka Allah ya kaddar mata, dan haka Karna sakejin maganar nan Ku naji na ko?.. sukace to, yace yauwa musamman Kai Usman Karna sakejin furucin kisa yafito daga bakinka, yace to malam sannan yatashi yafita gurin almajirai.


******

Saida a kayi da gaske sannan nacigaba da zuwa makaranta, da nace nibazan sake zuwa school din ba Malam yace dole Na cigaba da zuwa domin abunda yafaru dani baishafi karatun ba, badan nasoba nacigaba da zuwa school din.


 Saida ZUCIYATA cikeda tsanar maza, idan kika dauke malam yaya Auwal yaya Usman da auta Aleeyu suka dai ne banajin tsanarsu a ZUNI, Amma duk wani namiji Na tsaneshi yayinda  samari sai sake tururuwa zuwa gurina suke dama bana kulasu, dan haka ko lokacin ma basa gabada karatu na kawai nasani, idan Umma tayi mun magana meyasa bana kula samari?.. bana cemata komai saidai kawai nafashe da kuka, da taga haka saita daina yimun maganar, domin talura har yanzu abunda yafaru dani yana nan acikin ZUCIYATA.


Ahaka har nakai  level 3 nakusa shiga level 4, ganin har alokacin bana kula samari yasa hankalin Umma da Mal yai mummunan tashi, ganin da gaske fa nake bazan kula samari ba, suda  sukeso Ina gama karatu  za'ayimun aure Umma tace da Malam kodai banida lafiya  ne?..yace lafiyar ta lau, amma bari Zan bincika yagani, abinciken da Malam yayi yaga lafiya ta lau babu wani abunda keda muna wanda za'ace yahanani kula samari kamar irin ace KO" aljani yashefeni KO" kuma ace ya aureni babu ko daya, sai tsabar kiyayyar da namiji da yagani cike a ZUCIYATA.


Dan haka ran alhamis nadawo daga school sai Malam yakirani, bayan Na zauna gefensa kaina nakasa cikin girmamawa nace Malam gani, yace ya makaranta?.. nace lafiya lau yace babu wata matsala daiko?..nace eh yace to Alhamdulillahi anagama anshiga shekarar karshe nagamawa duka ko?..,


nace eh yace  masha'allah to Allah ya taimaka nace ameen, Can kuma sai yace tunda ankusa gama karatun samarin nan dake tururuwar zuwa adaure adan rika sauraren su", ba mamaki asamu abokin rayuwa acikin su". Ga mamakin Malam kawai sai yaga na fasheda kuka, yace a ah Asma'u lafiya?..


 Cikin kuka nace Malam nidai gaskiya bazan kula suba, yace saboda me?.. Nace saboda bazan tabayin aure ba cikin matsanancin mamaki yace?....




Muje zuwa



Tareda Alkalamin



✍🏽



🌹Meenart🌹

[9/11, 4:31 PM] ‪+234 816 334 9332‬: 🌹🌹🌹🌹

      🌹🌹🌹

           🌹🌹

                🌹

🌹 *AFSANA*🌹 

   [ *LABARI NA*] 

_*short true life story*_

🌹

🌹🌹

🌹🌹🌹

🌹🌹🌹🌹



🌹 *_TRUE LIFE STORY_*🌹





page4⃣




WRITTEN 

      BY

🌹AMEENA UMAR

 FARUQ🌹  


 OR

🌹MEENAT🌹




_______________________


® _*PEN: WRITERS ASSOCIATION*_


_*only the exquisite and whizkid writers are opportunity to be pen writes*_





✍🏽



    


Saboda meyesa bazakiyi aure ba?..Cikin kuka nace saboda ZUCIYATA ta natsani   dukkan wani d'a namiji, aransa yace ai naga hakan, afili kuma sai yace subhalallahi! Asma'u kintsani maza fa kikace?..nace eh, 


Kai yadafa 🤦‍♂tareda cewa Oh! Allah sarki kenan harda ni da "yan'uwanki duk kintsane mu KO?..dasauri nace a ah bada kuba fa, yace a ah hardamu mana tunda muma maza ne kokin mayarda mu matane?..


 Nace a ah

Yace ayya harda mu din dai kenan, to shikenan bari muyi addu'a sai yadaga hannun wansa dake rike tasbi, sannan yace yah! Allah Ubangijin sammai da kassai yah! Ubangijin Annabi Adamu da Hauwa'u yah! Ubangijin Annabi Yakuba da Isah Dan Maryam da Ibrahim badadin ka da Musa kalimullah, 


ke! intakai cemaki saida Malam yakira dukkan sunan Annabawa, sannan yakarshe da cewa yah! Allah muna rokon ka dan DARAJAR fiyayyan halitta, Annabi Muhammadur-Rasulullah (S.A.W)  daka kayayewa Asma'ul-Husna kiyayyar mu maza "acikin ZUCIYARTA, kayaye mata duk wani abunda takeji nadamuwa acikin ZUCIYARTA Ameen yah! rabbli-alameen.


Cikin matsanancin kuka 😭Wanda nakeji araina kozan daina tsanar maza, tabbas bazan taba daina tsanar mutumin da yaimun fyade ba, lallai addu'ar  Malamai Karbabbiya ce, musamman salihan bayi irisu Malam,


 yace to nayi addu'a banji kince ameena ba Asma'u na, cikin sheshshe kar kuka nace ameen amma Allah Malam ni bada ku natsana ba, murmushi yayi irin na manya yace to shikenan mun gode sosai, amma kiyi shuru kibar kukan haka nan inasan zamuyi wata magana me muhimmanci, nace to tareda share hawaye.


Ahankali yace Asma'u nace na'am yace baki yadda da kaddaraba KO,?.. nace na yadda da'ita yace a ah Asma'u baki yadda da'itaba, dasauri nace Allah Malam Na yadda da'ita yace to idan kin yadda da'ita, meyasa baki yadda tacewa abunda yafaru dake kaddarace ba?..ummh,


Shuru nayi bance komai ba yace haba Asma'u kina musuluma amma bazakiyi imani da kaddara ba, har kina kirarin bazakiyi aure ba a matsayinki na wacce aure ya Haifa, shin kodai kin manta aure sunnar ma'aikine?.. 


nace a ah yace auto kedin ce bakisan kiyi koyi da sunnar Ma'aikin?.. nace inaso, yace to kinga KO" aure yazama dole kema kiyi  kodan kihaifa kema kamar yadda aka haifeki, nasani abunda akai maki kowane ya aikata hakan bai kyauta ba, wanda nima inajin abun araina, to amma yamuka iyada kaddaran Ubangiji.


Don haka inason kiyi hakuri kicire komai aranki kinjiko?.. infada maki aranan nasiya Malam yaimani sosai, harsaida  jikina yaisanyi kuma sainaji narage jin abunda nakeji araina, sannan yace naje naci abinci nace to shi kuma yafita kofar gida gurin almajirai.


********

Bayan kwana biyu saina fara kula samari, saidai kuma  abunda yaita faruwa dani shine. duk saurayin dana bashi fuska yana zuwa gurina, bayan kwana biyu kuma sai yadaina zuwa kuma baya daina zuwa sai ya tabbatar mani, dacewa ashema nidin sauran wanine to shi bazai ita aurena ba dan haka akai kasuwa.


Infada maki haka naita fuskantar matsaloli iri-irin agurin samari, wanda hakan ba karamin Kara mun tsanarsu yayi acikin ZUCIYATA ba, kuma duk abun nanda  yake faruwa banfadawa kowaba tunda kona fadi baza'ayarda ba kilama ace karyane koransu kawai nake, tunda bana sansu, Dan haka saidai nayi kukana 😭 nashare hawaye daga bayama, sai kawai nadaina kulasu gaba daya, na sharesu kwata-kwata naci gabada karatuna.


*********


Raran wata laraba da misalin 5:00pm  nafito daga dakin jarabawa, kasan cewar munfara tun ranan Monday.


Direct baki _get_ nanufa dan nasamu mashin din dazaya kaini gida, hon naji ana tayi abaya na sosai wanda kuma tabbas Dani akeyi, saida kuma ko juyawa banyi ba domin nasaba dajin hakan, asalima wani me mashi nagani yashigo cikin school din, dan haka saikawai natareshi dasauri nahau natafi abina.


Bayan nabiya me mashi kudinsa sai na nufi gida, saidai kuma banga Malam ba saidai almajiransa sunata karatu kamar kullum, araina nace toyau ina Malam yaje?.. ban tsaya tambayar kowa ba itunanina yana cikin gida dan haka saikawai nashiga gidan, 

 

Da sallam Umma dake tsakar gida zaune ta amsa tana cewa kindawo?..nace eh Umma yagida tace lafiya ya jarabawa nace Alhamdulillahi! tace to Allah ya taimaka, nace ameen sannan tace abincinki yana kicin , nace yauwa Ummata nagode wlh yau nakwaso yinwa sosai bari Na ajiye jakata daki na nufa.


Bayan nadauko abinci Nafito daga kicin ina kokari cewa Umma yau banga Malam akofar gida ba, saiga wani yaro yashigo mesuna Dauda tsaran auta Aleeyu ne kuma yana daya daga cikin almajirai Malam, yace  Aunty Asma'u waikizo inji wani mut.....


wani uban tsawa nadoka masa wanda yasa yakasa kareshe maganar, cikin masifa nace Dauda Ina wasa dakai ne?...cikin tsoro yace a ah, cikin bacin rai nace to ba nace duk Wanda yasake aikoka kirana kace nace bazan zoba eheee?.., yace eh, nace OK" iskanci ne yasa bakaji bako?..cikin tsoro yace kiyi hakuri bazan sake ba,Cikin jin haushin sa nace dalla gafar kaje kacema kowani "dan'iska ne, nace bazan zoba kajiko?...


murya Malam naji yana cewa subhalallahi! dasauri najuya, tsaye naganshi bakin kofar bayi hannunsa rikeda buta, jinayi gabana yayi fadi domin banyi zaton yana Cikin gidaba tunda kodana shiga gidan ban ganshi ba,


 Kai nadukar kasa Cikin matsanancin tsoro, yace ayya Asma'u duk abunda nafada maki ba shiga kunnan miban ko?..shuru nayi bance komai ba Saida kirjina daketa dukan uku-uku, yace Kai Dauda jekace gatanan fitowa yace to tareda fita,


 Sannan Cikin kakkausan murya wacce ban tabajin yayi irinta ba, kasan cewars mutunne shi mesanyi dan ko magana zayayi cikin sanyi murya zakiji yanayinta, amma narana yashababan yace kije kiga mekiran naki idan kindawo inada magana dake,

Cikin matsanancin tsoro nace?...





Muje zuwa




Tareda Alkalamin



Post a Comment

0 Comments