ABOTA*
*DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD MU'AZZAM*
*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*
*BY AISHA M MU'AZZAM*
*Page 22~23*
Washe gari mommah ta gaya ma shatu abinda abban su yace sai da ta koma daki sannan da kira shi bayan sun gama wayar ne take fada mai ya turo iyayan shi murna ah wurin shi ba'a magana daga nan sukayi sallama.
Zaune suke gaba daya anan shatu take sanar da mahaifiyar ta zasuje yola suyi ko sati daya ne da kyar ta yarda amma pha sai dai tare da majid zasu je kuma sunyi na'am da hakan.
Abban su na dawowa suka fada mai shima yayi na'am amma kafinan sai sun je wurin yan uwa suhaima sun gaisa tukun yasa musu albarka suka tapi.
Washe gari da wuri suka tashi sukayi aiyukan su tsaf sannan suka shirya sallama suka yi ma mommah tukun kafin suka tafi shatu ce mai driving kai tsaye hayin banki suka nufa sun dan dade kafin sukayi kabala dagacan kuwa nasfat sukayi haka sukayi tabi suna gaisuwa kowa sai albarka yake sanya musu basu suka koma gida ba sai kusan magrib sbda sun hadu da wasu frnds dinsu na sec school anan suka kafa daaba shiyasa basusan time ya wuce ba tare da alqawarin zasu sauran gidan frnds nasu idan suka dawo daga yola.
Tunda suka koma suke shiri kamar wadda zasu wani kasa sai da suka hada komai sukayi isha'i sannan suka fita hira cikin gida basu suka tapi daki ba sai goma.
Sis dan allah kunna min hotspot cewar shatu toh kawai tace bayan ta kunna mata ne suka fara chat da usman mata chat din bai ishesu ba sai da suka qara da waya sai kusan 12 ta kwanta.
Yau ne su suhaima zasu tapi tun wuri suka tashi dan 9 zasu tapi shima majid da wuri ya tashi 9 din ma bata cika ba sukayi sallama suka tapi ah sauka lafiya.
*KANO*
Usman ya sanar da iyayan shi batun maganr gidan su shatu ranar friday zasuje sbda abban shi nada wasu issues shiyasa.
Alawiya zaune ah gidan su firdausi tana jira sugama su nufi gidan su aliya daga can ayi gidan su husna dan allah babe kiyi sauri lkci yana tapiya haba qawata kiyi hkri ynxu xan gama sai da ta kusan minti shabiyar kafin suka tapi gaba dayan su gidan su husna suka hadu bayan sunci sunsha aka dauko chapter hira anan ne alawiya take gaya musu yadd sukayi da umma usman.
Alawiya ni ah nawa tunanin kiyi hkri tunda baya sanki koma ya aureki ke zaki sha wahala ga mustapha da gaske yake sonki amma kin tsaya biye ma wanda baya sonki haka dai husna tai ta fahimtar da ita tuni jikin ta yayi sanyi husna nagode sosai da shawarar da kikaban insha allah xanyi amfani da ita haba alawiya miye na godiyan dama haka zaman tare ya gada ai karkiji komai.
Hirar su suka cigaba dayi sai da sukayi sallah sannan sukayi shirin tapia kar ki manta kawata maganr karshe dana na gayamiki baxan manta ba bye sai munyi waya hakanan suka hau napep sukayi gida.
Aisha😘
[9/22, 9:55 AM] Aisha m mu'azzam: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
*ABOTA*
*DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MZZ DADDY)*
*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*
*BY AISHA M MUA'ZZAM*
*Page 24~25*
Basu suka isa yola ba sai karfe hudu shatu an zage sai bacci akeyi sai da taji mota ya tsaya tukun ta farka ya min iso ne ta tambaya eh lilsis wurochekke suka nufa gidan bappan mommah.
Bayan sun shiga ne matar gidan ta tashi da murnar ta yau munada babban baqi ashe wurin zama suka zauna sbda duk sun gaji abinci ta kawo musu da abubuwan sha sai da sukaci sukayi kat sannan ta nuna musu dakonan su kayan su suka kwasa shiga dakin sukayi nan suka baje gaba daya ah kan gadon sis wlhy na gaji cewar suhaima habawa ai baki kaini gajiya ba kinga bari nadan yi wanka sai na kwanta dan wlhy na gaji haka kuwa sukayi wanka dukkan su suka kwanta shima bangaran majid kwanciya yayi.
Mai gidan ne yayi sallama alamun ya dawo sai da ya huta kafin ya tambaya har ynxu basu iso bane suna daki baccin gajia sukeyi toh alhamdillah su rabi'a basu dawo bako eh sai anjima enaga suka cigaba da hira.
Kiran sallar magrib ne ya tashe su saida sukayi sallah kafin suka fito ai nan pha aka kafa dabar hira hiran yaushe gamo gasu rabi'a sun dawo da kanwar ta hanifa shiyasa hiran nasu yayi nisa saida sukaji bacci sanan sukayi daki.
Usman ta kira yau basu dade ba sukayi sallama dan ta gaji sosai itako suhaima sai da suka sha hirar su sannan suka yi sallama koda ta koma daki tuni shatu anyi daya daya ana bacci itama tabita suka kwanta.
Washe gari basu suka tashi ba sai wurin 12 lkcin dasuka fito har angama gyara gidan tas komai yyi dai dai gaisuwa sukayi wa matar gidan kasan cewar shi ya tapi kasuwa nan ma hira suka sha sunayi suna karyawa.
Yamma tadan gabato suka nufi gidan kanwar mommah sbda kwana zasuyi nan ma tarba suka samo sosai haka dai sukaita zaga dangi shima majid ya hadu da frnda dinshi bila adadin wasu kuwa ashe suna kaduna bai sani ba sai daya karbi numbobin su tukun.
Kwanci tashi ba wuya su shatu sunyi sati guda da zuwa kuma gobe zasu tapi kayan arxiki da suka samu ba'a magana washe gari kuwa da wuri suka kama hanyar komawa gidan.
Bangaran usman iyayan shi sunje an tsaida magana sbda abban su yayi musu bayanin komai harda suhaima sun kuma yadda da hakan.
Itama ah bangarn alawiya tayi hakuri da usman kuma tanemi hkri sun sasanta abunsu shirin da suke ynxu kam ba'a mgana kuma suna zuba soyayyar su itada musty nata.
Karfe 3 wannan karan suka iso nan gidan ya hade da murna amma suhaima duk sanda taga gidan su saita tuna iyayan ta iyaka tayi musu addu'a tadanyi kwalar ta.
Watanni sunga gashi ynxu su suhaima za'a koma makaranta ranar da zasu tapi iyayan ne suka kaisu kamar ko yaushe kuma majid ya musu alqawari duk sati biyu zai dinga zuwa musu daga haka sukayi sallama sukayi gida su kam hostel suka nufa dakinsu suka gyara sukayi komai suna kwance alawiya da kawayan ta suka shigo lkcin shatu na waya da usman akan makaranta ba dadi tunda babu shi.
Tsayawa tayi da wayar kuma bata kashe ba alawiya maiya kawoki dakin mu haba shatu yau ba da fada naxo ba hkrin abubuwan da suka faru naxo na baki laa karki damu ai ba komai toh ngde sukayi sallama suka pita ita kuma taci gaba da wayan ta sunjima kafin sukayi sallama.
Tunda suka dawo ynxu suka maida hnkli sosai wurin karatun su duk sati biyu majid yana xuwa musu wannan satin ne yaxo musu da takardar samun aikinshi kuma wnan karan su uku suka zo shi da auwal sai Ahmad abokan shi ne sosai kusan magrib suka tafi shikam usman baida ranar zuwa ko yaushe ta raya mai zuwa yake ana haka lkcin exams dinsu yayi wnan karan basu dade ba suka gama koma ranar suka tapi.
Tunda suka koma gida mommah ta shiga gyara su da kannan maman suhaima suma suna iya bakin kokarin su ganin sun agaza ma mommahn nasu.
Kwanci tashi ba wuya hutun su ya qare sun koma makaranta iyayan usman sun kai komai da ake bukata na aure kayan sunyi sosai suma sun hadawa suhaima kayan ba kadan ba.
Abbansu gidan shi na nasfat yaba majid domin su zauna an gyra gidan sosai komai yayi dai dai kasancewar ynxu majid bai cika zama ba shiyasa bai samu daman duba gidan ba.
Shiko usman sabon gida aka siya musu ah court road shima ya samu aiki ah zenith bank dukka gidajan shiri suke ba kadan ba suma yan uwan suhaima ba'a barsu ah baya ba sunmt abubuwa dayawa fatan allah ya qara budi.
Aisha😘
[9/22, 9:55 AM] Aisha m mu'azzam: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
*ABOTA*
*DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD(MZZ DADDY)*
*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*
*BY AISHA M MU'AZZAM*
*Page 26~27*
Bayan wattani biyu su shatu na hango baki yakasa rufuwa sai hota ake zubawa ana murnar kammala makaranta ta wani bangaran suna murna wani bangaran sunajin ba dadi rabuwa da frnds dinsu haka abin ya gada.
Yafiyar juna gaba daya suka cigaba da nema yayinda majid yake famar jiran su domin su kadai yake jira sai da ya kira suhaima kafin suka bar rungume rungume suka tapi suna ma A B U bye bye allah ya rabasu lafiya.
Tafe suke ah hnki bawani gudu yau yake ba suhaima ce ah gaba shatu na baya tana chatting da ussy nata sai murmushi takeyi duk abinan majid yana kallon ta lil wai murmushin miye haka kikeyi hmm ya baxaka gane ba dama tayaya xan gane bayan baki ganar dani ba zancan ta watsar ta cigaba da hidiman ta.
Minti talatin ya kaisu kaduna ah kofan gidan sukayi parking sunga yanayin gidan akwai mutane masu yawa ah ciki sai da majid ya fito sukabi bayan shi cikin gidan suka kutsa wow shine kawai abinda suka furta gaba dayan su wurin yasha gyara an masa kwalliya mai kyan gaske ga yan uwa duk sun hadu anata musu congrat banda dariya babu abinda sukeyi kowa gift dinshi yake basu basu gara mamaki ba sai da suka shiga cikin gidan kawayan su suka gani birjik ah ciki nan pha aka shiga rungume rungume da murna wurin aka basu suka shiga wanka kawai suka samu sukayi shiryawa sukayi cikin dogayan riguna komai iri daya nan pha aka fara hidimar walima basu suka gama ba sai da aka kira magrib dama gashi sun gaji lkcin mutane dayawa sun tapi sbda anyi kiran sallah ciki suka shiga suka baje ah kasa tsabajen gajiya kan kace me gidan yayi shiru alamun duk an watse.
Dakinsu suka koma shatu ne tafara shiga wanka yayin da suhaima tunanin iyayan ta ya addabeta bata san sadda ta fashe da kuka ba kukan da shatu taji ne yasata fitowa ba shiri sis maiyafaru kike kuka haka.
Shatu naso ace wannan ranar iyayena sun ganta basu da burin daya wuce suga ranar kamalla makaranta na ashe allah baiyi zasu gani ba mutuwa maiyasa baki hada dani ba maiyasa kika barni ni kadai sosai take kuka wadda itama shatu tuni tafara rungume juna sukayi bamai lallashin wani ah cikin su mommahn sune taji hayaniya kadan kadan dakin ta shiga ganin su haka bakaramin tada mata hankali sukayi ba maiyafaru ta shiga tambaya kai kawai suke girgixamata alamun ba komai itadai hankalin ta gaba daya ya tashi lallashin su tashiga yi da kyar suka saki juna sukayi shiru sai ajiyar zuciya suke yi.
Tunda kunyi shiru sai ku fadamin maiya faru shatu ne ta fada mata komai haba yan albarka ba kuka yakamata kuyi musu ba addu'a yakamace su ah wnan halin duk sadda kuka tunasu addu'a zaku dinga yi musu nandai tai ta musu har ta samu sukayi saitu suka dawo dai dai ynxu kutashi muje ga abincin yana jiran ku sai da suhaima tayi wanka tukunnan suka fita xaman cin abinci.
Tunda suka dawo mommah tacigaba da kula dasu mai gyaran jiki aka dauko daga maiduguri maman batula ita ta shiga gyara su ciki da waje bawani hidima zasuyi ba sbda abban su yahana iya kaci suyi walima abinda ya yarda suyi knan.
Tuni anje an musu jere kowa saisan barka yake komai nasu iri daya aka musu satin auran su ya shigo gabadaya gidan an cika mommah uwar amare ba zama yan uwan ta tundaga yola sunxo haka yan uwan suhaima gaba daya sun hallara sai da aka bude dayan part din gidan sbda yawan mutane.
Yau juma'a ah yaune za'ayi walimar tin safe ake shirin inkaga abubuwan da aka shirya abun ba'a magana su usman shida abokan shi sukaxo tinda yaga shatu ya kasa dauke idon shi daga kanta kawai su yake su kebe subiyu amma ina hakan baiyu ba.
Karfe hudu aka nufi arewa house domin acan xa'a gabatar da Waliman wurin zaman amare da ango daban ne sai da suka zauna tukun malan abdulkadir abdulsallam yafara wa'axi sosai yayi wa'azi mai ratsa jiki ba amare kadai ba har masu aure sun garu da wnan wa'axi karfe 6 aka tashi lkcin an gama nan aka sallami malan gaba dayan su suma sukayi gidan.
Washe gari asabar rana bata karya karfe biyu aka daura auran AISHA ABDULLAHI YUSUF DA ANGON TA USMAN MUHAMMAD KASIM
ABDULMAJID ABDULLAHI YUSUF DA AMARYARSHI SUHAIMA HASSAN WADDA DUNBIN MUTANE SUKA HALLARTA.
Haka aka watse ah wurin angwaye kuwa baki yaqi rufuwa suma nan sukayi gida yan daurin auran da sukazo daga kano sun tapi sai yan kai amarya kawai suka rage.
Karfe hudu aka shirya su domin tapiya dakin abbansu aka kaisu nan sukayi musu fada sosai idan kunga yadda suke kuka sai da suka sa uwar kokawa itama yan uwan suhaima suna sunyi masa fada sosai abin sai wadda ya gani suhaima aka fara kaiwa sun rungume juna da kyar aka rabasu da anzo sata cikin mota da gudu xata fito ta rungumeta haka dai aka samu aka cusata cikin motar suka tafi itako shatu durkushe wa tayi tana kukan rabuwa da suhaimar ta.
Yan kai amarya sun kaita sun dawo lafiya sai kawayenta da aka bari sanda akaxo fita da shatu rigima ita wlhy tafasa baxata bar mommah ba da ita kanta uwar sai da tayi kwallah nan dai aka samu suka tapi fatan allah ya sauke su lafiya .
Aisha😘
[9/22, 9:55 AM] Aisha m mu'azzam: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
*ABOTA*
*DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD(MZZ DADDY)*
*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*
*BY AISHA M MU'AZZAM*
*Page 28~30*
*Last page*
Karfe shida suka esa kano kai tsaye gidan su usman aka nufa da ita sosai umman usman tayi murnar ganin surukar tata ta yaba da zabin da danta yayi dukkan su aka hada sai da suka sha nasiha kafin suka tapi nan aka kai shatu gidan ta sai da su usman da abokan shi suka zo tukun suka dan musu abinda zasuyi kafin su kwashi sauran mata su tapi dasu kamar jira dama usman yake yabi bayan su ya kulle gidan.
Kusan ta ya dawo ya zauna haba shatu na kukan ya isa haka karki karar min da hawayen ki wnan ba ranar kuka bane ranar farin ciki ne so pls ki daina min asarar hawayan haka lallashi ya shiga yi da kyar tayi shiru.
Ynxu sai ki tashi muyi sallah mu gode ma ubangiji daya nuna mana wannan rana haka kuwa ta tashi suka dauro alwala bayan sun idar dafa kanta yayi yai mata addu'a tambayoyi yai mata duk haka ta amsa daganan ya jawo kazar da ya shigo dashi sai freshmilk ah cup ya zuba musu ita dai shatu da kyar taci hakan yasa kadan taci tace ta kushi barin ta yayi toilet ta shiga tayi wanka sanda ta fito baya dakin da wuri tasaka kayan ta bayan ta balbale turare ah jikin ta karshen gado tahau taja bargo ta rufu.
Bata wani dau lkci ba bacci ya dauketa jin da tayi ana lalubarta ne ya farkar da ita marai rai cewa tayi magan ganu masu dadi yai ta mata harta dan saki jiki daganan lbr ya canja nima naja kafana nayi waje.
Bayan wasu awanni na leka daki idan kukaga usman bazaku tantance halin dayake ciki ba banda albarka babu abinda yake sa mata ruwan zafi ya hada daukarta yayi har cikin toilet din ya kaita ah ruwan ya sata zafin data jine yasata tsala ihu hkri ya shiga bata sosai ba kadan ba saida ya ga ta zauna sannan ya koma daki gadon ya gyara kamar bashi ba sannan ya koma lkcin tayi wanka tsarki tana shirin fitowa knan sai gashi da kanshi ya kaita kan gadon da towel din dake jikin ta haka tayi bacci tsabar wahala nan da nan bacci yay gaba da ita shiko usman sallah yay ya gara gode ma allah daya bashi shatu ah matsayin mata.
Sallan da ake kira ne yasa shi nufan gadon ya tashe ta alwala ya kaita tayi ya dawo da ita dogon hijabi ta saka nan yaja su sallah sun idar bayan sunyi addu'oi sannan suka koma suka kwanta.
Buga kofan dasukaji anayi shi ya tayar da su fita yayi mai aikin umma ce ta kawo musu abinci sanda ya dawo shatu harta shiga toilet domin yin wanka shima dakin shi ya nufa yayi wanka kanan kaya ta saka riga da wando parlo suka sauko bayan sunci abinci ya kunna musu kallo tana kan cinyar shi shiko sai xulayarta yakeyi.
Wayan ta ta jawo takira mommah suka gaisa kafin ta kira suhaima tana tambayar yayan ta bashi wayan tayi suka gaisa yaya sbda anyi amarya shine har an manta dani haba lil sis waya esa ya manta k sosai suka sha hira kafin suyi sallama.
Soyayya suke abinsu cikin kwanciyar hankali abin sai wanda ya gani.
Yau suhaima ta tashi sa matsanancin tashin xuciya gashi batada kuzari gwada ta majid yayi da kanshi abinda yagani ne ya sashi farin ciki dagata sama yayi kamar baby yana shillata nikam ka sauke ni irin wnan murna haka kaman an mka albishir da gidan aljanna direta yayi yafada mata itama murna take xubawa kamar me haka suka cigaba da tatallin cikin su.
Yau su usman sun shirya xuwa kaduna amma shatu kwana biyu xatayi tunda suhaima ta fada mata albishir sai da suka biya gidan su usman tukun suka kama hanya kafe 1 suka isa gidan suhaima suka fara nufa sallaman da sukaji ne yasa su ganin su waye da gudu shatu ta ruga ta rungume suhaima murna ba'a magana k sakar min mata karkiji mata ciwo kai yaya banida wani girma pha zama sukayi abinsha ta kawo musu suka sha nan sukace xasu tapi itama suhaima daro tasa saida sukabi bayan su ah tare suka shiga gidan rungume mommah da abbansu sukayi lkci daya ranar wunin farin ciki akayi da yamma usman ya tashi tapia shatu har mota ta rakashi kamar kar su rabu haka ya kama hanya ita kuma ta koma cikin gida.
Ranar itama suhaima ah gidan ta kwana washe gari tayi gidan ta.
Kwanan ta biyu usman yaxo ya dauketa tunda suka koma shatu itama tafara laulayi sudin ma hakane sun dau san duniya sun daura ma ciki ah hnkli cikinta yayi ta girma.
Watan cikin ta ya shiga wata takwas lkcin suhaima ta Haiti yarta mace ah lallabe shatu taxo sbda tayi nauyi ranar suna yarinya taci sunan umman suhaima wato Fatima ana kiranta bintu su shatu an koma satin ta biyu da komawa abu yaki ci yake cinyewa dan dole usman ya maidata gida.
Kwananta uku da zuwa ta haifi danta namiji ranar suna yaci sunan mahaifin suhaima wato hassan sosai aka sha shagalin biki suhaima sai da tayi arba'in ta koma gidan ta ranar kamar zasu cinye kansu .
Shiko usman ah kullum yana hanyan kaduna da haka hartayi arba'in itama ta koma gidan ta soyayyan su kullum qara karfi yakeyi.
Bayan shekara biyar
Wasu yara na hango da gudun su sun shigo gidan shatu na hango zaune ah kujera yarana dawa kukaxo mum da umma mukaxo nan su hajiya suhaima aka shigo nan aka kafa hira kwana biyu sukayi suka koma kaduna.
Zaune suke gaba dayan su family guda sai murna ake xubawa mai hoto na daukan su ana gamawa shatu ta umarcesu suje waje suyi wasa hassan da hanifa knan haka suka tapi su kuma lbr ya canza fatan allah ya qara soyayya.
ALHAMDULLILAHI ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFINAN MAI SUNA ABOTA.
Kunga dai sanadin ABOTA shiyasa suka zama tamkar yan uwan jini ta auri yayan kawarta duk sanadin ABOTA iyayan suhaima sun rasu bataje wurin yan uwanta ba amma sanadin ABOTA yasa tazama kamar yar gidan ne.
Allah ubangiji ya hada mu da masu sanmu tsakani da allah amin.
Sai mum hadu ah littafi nagaba insha allah.
Aisha 😘
0 Comments