_typing_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
*🙆🏼♀️🙆🏼♀️🙆🏼♀️🙆🏼♀️🙆🏼♀️BAƘIN CIKIN KISHIYATA*
🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀
BY
*FATIMA UMAR KAS*
*_Mummyn Mihal_*
Page 1and 2
"Wani azababben, gigitaccen Marin da naji saukarshi akuncinane,yasani saurin dawowa, daga duniyar,tinanin da na tafi."
"FARUK na gani tsaye a kaina,
"Fuskar nan tashi tamkar bai taba dariya ba."
"Cikin tsananin masifa,da bacin rai,
Ya fara magana:-
"KE yanzu rainin hankalin naki,
Da fitsarar taki,
Har ya kai in shigo
Ina miki magana
Kiyi banza dani,
Bayan tin daga parlour nake kiranki
Kinki amsawa,
Saboda kin rainani,
Bakisan matsayina
Agurinki ba,na mijinki,
" ko angaya miki muma jakaine irinki,
Da zaki zuba mana,
Gishiri a shayi don mugunta,
"To gashinan mu baza mu shaba,
Ke zaki shanyeshi,
Ke kadai, shi zai zama abincinki NA yau, kuma wallahi inna dawo baki shanye ba, sai nayi matukar saba miki,
Kinji dai na fada miki.
"Sannan ya dire flast din shayin akan mirrow. na,
Ya juya zai fita, sai kuma ya dawo.
Makulli ya dauko ya kulle toilet din, sannan ya fita shima dakin ya rufe da key, sannan yasa yayan a aljihu, yai tafiyarshi.
" yana fita na jawo yarana FUAD and MIHAL na rungume,
NA shiga raira wani sabon kukan.
"JAMILA dake lekenmu ta window ta Daka tsalle tare da "yar karar murna,
Don ganin abinda yake faruwa, tsakanina da mijina.
Ai tana ganin ya nufo dakin, tai saurin komawa kan gadonta ta dasa kukan munafirci.
Ai yana shigowa yai saurin karasowa gareta ya zauna sannan ya fara,,,,,,,,,,,,,,,
✍🏼mrs Bilyamin kaita.
_typing🖌️_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
*BAKIN CIKIN KISHIYA TA*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
WRITTEN
BY
*FATIMA UMAR KAS*
*_(Mommin Mihal)_*
Page 3and4
Da sauri ya karaso gareta tare da jawota ya fara rarrashinta.
" haba jamcy na menene kuma na kuka ,aina Riga nadau mummunan mataki akanta,
Pls kiyi shiru Dan Allah kinsan kukanki yana tayarmin da hankalin.
Ganin duk ya damune yasata yin shiru,
Taba mai farin cikin yanda ya zama nata ita kadai aranta.
Sai alokacin tai magana,cikin kissa da kisisina.
"Yanzu ace duk abinda Fatima takemin acikin gidannan kaina saita maka?
Ni tacigaba damin mana ai zan jure nai hakuri da ita,kodon kwanciyar hankalin ka,
Amma kasan duk abinda zai bata maka rai ni ba son shi nakeba,
Amma ita kullum sai tayi abinda zai bata maka rai,
Don kawai taga yau zaka fita office da wuri, shine ta hada break fast din kuma ta zuba gishiri aciki.
Ta karashe maganar tare da zakin wani shegen kuka.
Nanfa ya kara rudewa.
" Nace ki kwantar da hankalinki, indai nine inna fita zan sani abinda zanci,
Kefa me kike bukata?
Inna fita na aiko miki.
Sai alokacin tai murmushi.
Sannan ta langabar dakai,
Ni duk abinda honey yaci nima shi zanci.
Murmushi yai sannan yace:- OK ba damuwa inna fita zan sa akawo miki,
Bari na tafi karnai Letty.
Rakiya tamai har gaban motarshi said a taga tafiyarshi,sannan ta koma ciki zuciyarta fari kal.
Tana shiga ta zauna
A daya daga cikin kujerun da suke girke a parlourn,
Sannan ta bushe da wata shegiyar dariya tamkar zararriya.
Sannan ta kalli saitin dakina tana mai fadin:- Badai kin nace ba kinki tafiya?
To wallahi indai kina cikin gidannan,
Yanzu kika fara kuka,bakiga komai ba,
Donnayi alkawarin sauna tagayyara rayuwarki, daga ke har yaran naki.
Shi kuma ke dashi har abada, don ya zama nawa ni kadai.
Wata dariyar ta kara shekewa da ita.
* * *
" Azatona abban fuad idan ya tashi fita zaizo ya bude mana koda toilet dinne,
Don nasan dole zamu bukaci shiga,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
✍🏼
Mr's Bilyamin kaita
_typing🖌️_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
*BAKIN CIKIN KISHIYA TA*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
*WRITTEN
BY
*FATIMA UMAR KAS*
*_(Mommin Mihal)_*
❤💚💓AGASKIYA NAJI DADIN COMMENT'S
DINKU 😁 KUNA KARA KARFAFAMIN GWIYA NA GODE ALLAH YABAR ZUMUNCI, LOVE YOU ALL MY FAN'S.👍🏼👍🏼👍🏼
😍🥰😘
Page 5and6
"Azatona abban fuad inya tashi fita zaizo ya bude mana koda bandakinne,
Don nasan dole zamu bukaci shiga,
Amma shi bai lura da wannan ba,
Shidai kawai ya yanke hukunci ba tare da bincikeba,
Kuma bai bani damar namai magana ba,balle na bashi hakuri,
Nidai nasan ko gishiri banyi anfani dashiba a wajan had a break fast din,
Amma me ya kawo gishiri mai yawa haka?
Da har ya sauya launin shayin zuwa fari?
Nidai nasan daga ni sai jamila agidan,
Kuma nasan wanna n ba aikin kowa bane sai nata,
Domin jamila ta tsaneni,bata sona, bata kaunata bata kaunar ganin farin cikina a gidan,
Burinta kullum ta muzgunamin tare da yarana,
Balle kuma miji na,
Wanda na tabbata yana matukar Kauna ta dason farin cikina,
Amma saida tai duk wani tuggu, da makirci ta rabamu,
Take kumayin duk asirin datasan zata mallakeshi,
Gashinan kuwa tai nasara,
Ta rabani dashi,
A yanzu ba wacce take gabanshi face ita.
Cikin kuka na daga hannayena sama INA rokon ubangijina,
"Ya Allah kaga halin kuncin da nake ciki na BAKIN CIKIN KISHIYATA,
Ya Allah ka kawomin agaji,
Allah ka karkatomin da hankalin mijina,
Allah ka shiga tsakanin na gari da mugu,
Allah karka bata damar da zata cutar dani da yara nah,
Ya ubangiji Kaine maji rokon bawanka,
Kuma kana gaggauta amsar addu ar Wanda aka zalinta,
" ya ubangiji nayi tawassali da sunayenka tsarkaka,
Nayi tawassali da Alqur'aninka mai gwannan
Na kama kafa da Annabinka shugabanmu (s.a.w)
Kabani ikon cinye wanna n jarrabawar,
Ka kawomin agaji ya Allah.
Sannan na shafa adduar.
Fuad ne yace amin ummi,
Sannan ya fara sharemin hawayen fuskata,
"Kasancewar shine babba kuma yana da wayo sosai,
Ba kamar mihal ba da ban Dade da yaye taba,
Ita baccintama take akan cinyata.
Can naji tana fadin UMMI ruwa?,,,,,,,,,,,,,,,
✍🏼mrs Bilyamin kait
_typing🖌️_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀
*BAƘIN CIKIN KISHIYATA*
🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀
WRITTEN
BY
*FATIMA UMAR KAS*
*_(Mummyn mihal)_*
💖💓💚This page dedicated to my blood sister HAFSAT (intee) Allah ya bar zumunci da kaunar juna.🥰😍😘
Page 7and 8
"Gaba na ne ya yanke, ya fadi,
Sanin ba mu da komai a d'akin, koda, ruwan sha,
Sai dai wannan sha yin, da ya ajiye mana,
" Dan ha ka, na yanke shawarar, bata ko da sha yinne,
Sauke ta nayi, daga kan cinyata,
Sannan na nufi bakin mirrow,
Flast din sha yin, na d'auko,
Sannan na bud'e,
Na tsiyaya, mata a cup d'in na bata,
Bayan na zauna a kan gadon,
"Ban yi zaton za ta sha ba,
Amma sai naga ta shanye,
"Nasan yun wa ce, tasa tasha,
Don rabonmu, da abinci tin jiya,
Shi ma wanda suka ci suka, rage ne muka ci,
Sai da ta shanye sannan ta ko ma barcin ta,
Fuad ne yace UMMI nima zan sha,
Yunwa nake ji?
Shima tsiyaya mai, nayi na bashi,yasha,
Ni ma na so sha, amma ina d'an d'anawa, nai saurin furzarwa,
Dan ya za ma tamkar ruwan gishiri da sugar,
Rufe shi nayi, san nan na mayar,
Inda na d'auko,
Cikina naji ya fara mur d'awa, tin ina dau rewa, har na tashi ina zagaye d'akin, ina salati,
Da k'ar na Samu, ya lafa min,
Kwanciya ni ma nayi,ba yan na gyara musu kwan ciyar,
Barci yai awon, gaba da mu.
* * *
Tana hakimce a perlourn ta d'ora,
K'afa d'aya kan d'aya,
Tana kar ka d'awa.
Knocking taji anayi,
Tsaki ta yi, san nan ta nufi kofar,
" waye"?
Ta tam baya a wulak'an CE
Nine,
"Kaine wa?
Ta kara fad'a duk da ta gane mai maganar,
Baba mai gadi ne,
Ya fad'a cike da girmamawa,
" lafiya za ka zo ka isheni da knocking?,
Ayi hak'uri hajiya, Alhaji ne yayo aike.
Sai da ta gama b'ata mai lokaci,
Sannan ta bud'e,
Tana wani, ya tsina,
Tare da taunar cingam,
Sannan ta amsa,
"To ai sai ka kama gaban ka, ko?"
Ta fada ta na hararar shi,
Sannan ta koma ciki ta rufe kofar.
Girgi za kai kawai yayi, sannan ya juya,
Yana mata fatan shiriya,
Dan wannan kad'an ne, daga halinta, bata girmama kowa,
Sab'anin Fatima yarinyar, kirki, da son mutane,
Ga girmama manya,
Allah kai mana maganin masifa.
Baba mai gadi ya fad'a.
Ita kuwa hakimar ta na komawa, tai zaman dirshan,
Akan carpet,
Sannan ta bud'e ledar,
Gasassun ka ji ta gani, manya guda 2,
Sai d'aya, ledar ice cream ne a cikin,
Nan da nan kwadayin ya motsa,
Yawun ta har ya tsinke,
Ba b'ata lokaci ta fara ai kawa cikinta,
Tanayi ta na gyad'a kai,
Sai da ta cinye ka zar nan, tas, har kashin ba ta bari ba,
Sai da ta taune kayan ta,
Sannan ta kora da ice cream d'in,
Amma ji take da za a k'ara mata wata 2 tsaf zata cinye,
Sai da ta gama sannan ta tsallake,
Ba abinda ta kwashe,
Sannan ta nufi kitchen,
Gas ta kunna sannan ta d'aura jallop d'in taliya.,,,,,,, ,,,,,,,,,,,
Mr's Bilyamin kaita.👌🏼
😍Ina yinku over my fan's love you
😘
*typing🖌️*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
*BAKIN CIKIN KISHIYA TA*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
*WRITTEN BY FATIMA UMAR KAS*
*(Mommin Mihal)*
💕❣💓💖"Wannan page din,
Sadaukarwa ne ga,
Maman Abdul jalal, saboda inajin dadin comment dinki,kina faranta min rai,
NA gode.🥰😍😘
Page 9 and 10
Abincin rana ta d'ora,jallop d'in taliya, ta dafa, tai mata had'i sosai, tana tsaye, a kitchen d'in, har ta dahu,
Ko plet bata nema ba, ta d'auko ta, a pot d'in ta dawo perlour,
Tamkar mayun waciya, haka ta dinga, cin abincin,
Sai da ta cinye, tas,
Hatta wadda ta fara, kamawa, saida ta had a, da ita ta cinye,
Frige ta bud'e, ta dauko ruwa, ta bud'e ta sha, sannan tai wurgi, da robar,
Kai tsaye bed room, ta nufa, ta baje akan gado, ta kama barci.
Ita da ta kwanta, tin rana, sai gata sai yamma ta tashi,
Tana duba agogo tai saurin, dirowa daga gadon,
Don tasan, mai gidan, ya kusa dawowa,
Gashi batai komai ba,
A haka ta d'an karka d'e abinda taga za ta IYA, tanayi tana mita,
"Kai dole ma a nemo min "yar aiki, bazan iya ba"
Girki ta je, ta d'ora, sannan ta shiga, band'aki, tai wanka,
Bayan ta fito ta shafe, jikinta, da sihirtaccen tirarenta,
Sannan tasa kaya, ko tinanin sallahr, da ake binta batai ba,
Dama sai ta ga da ma takeyinta,
Horn d'in motor d'in shi, taji,
Wani tiraren ta k'ara fesawa, sannan ta fita harabar gidan, don ta taro shi,
Yana fitowa taje tai hugging dinshi, ko kunyar, mai gadin, bata jiba, haka ta, ruk'o hannun shi, su ka shigo d'akin nata,
shi kuwa tamkar, wani, soko, haka yake binta,
Kayan jikin shi ya rage, sannan ya shiga toilet,
Kafin ya fito ta had'a mai, abinci,
Bayan ta bad'e abincin da magani,
Bayan ya fito ya shirya cikin wata jallabiyya, ruwan madara, sannan yace bari, nayo sallah na dawo.
Ka bari muyi anan mana, kasan tafi lada, ba ya iya ma ta musu don haka yace to muyi,
Ita kuwa ba ta son, ya fita ya tina su fatima, da ya kulle,
Shi yasa tayi hakan,
Bayan sun idar ta dauko mai abin cin shi,
yana ci, tana Jan shi da fira, duk don kar ya tina,
Aikwa manta war yai, don har lokacin barci, yai, sai da tai duk wani salon makircin ta, suka kwanta barci,
Akabar bayin Allah a kulle.
Basu suka farka ba, sai wajan 9:00 NA safe, agogo ya kallah, sannan yace,
Kai gaskiya yau, mun sha barci,
Gashi har na kusa maka ra, bari inyi wanka, nai shirin office.
Ita kuwa cewa tai bari inje in hada mana, break fast,
Wane break fast kuma, ba waccen shashashar ta ha d'a ba,?
Sai kwa ta ha d'e rai,
"Me ya faru,?
Ko yauma wani, abin tai,?
Sai kuma, yai shiru, kamar, mai tinani,
Da sauri ya mik'e, tana fa d'in,
"Innalillahi wa innah ilaihirra ji,un."
"Mene kuma ?
Ta tambaya?
NA manta na rufe su, a d'aki, tin jiya,
Nan da nan ya shi ga laluben, makullin,
Da k'yar ya nemo, shi a aljihunshi,
Da Sauri ya fita, ya nufi, d'akin nasu,
Yana zuwa ya fara,
Kiciniyar, bud'ewa,
Yana bud'ewa ya shiga, sai dai meeeeeeee????????
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️
BAK'IN CIKIN KISHIYATA
🙆🏽♀️🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️
Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
AM SORRY TO SAY
Wannan page din na Riga nayishi a baya Amman sun b'ata bangansuba, page 4 ne, 11 zuwa 18 Amman yanzu
Page din sun bata shiyasa zan maimaitasu Amman a page 1 zan had'esu kuma zanyisu a takaice don in samu sauki don haka kuyi hakuri da yanda kuka gani Amman zanyi yadda zaku fahinta,
Page 11_18
Yana shiga d'akin ya gansu a wani iron yanayi na rashin lfy dukkansu bass hayyacinsu, da Saudi ya nufi d'akin Jamila don yazo ta tayashi ai tana ganin ya nufo d'akin tai saurin shigewa toilet ta kunna shower alamar eanka takeyi, shima da yaga tana wanka bai jiraba ya k'ara fitada sauri dakin ya koma sannan ya d'auko wayarshi ya kira abokinshi Dr Ahmed, ba jimawa yazo taimakon gaggawa ya shiga basu Amman basu dawo daidai ba don haka yacewa faruoq daidai akaisu can asibitinsu ciwon yai girma, ba musu ya amince aka debesu zuwa asibiti, bayan sunje aka dukufa akansu don ceto rayuwarsu saida aka day lokaci sannan aka samu suka dawo hayyacinsu ruwa yasanya musu, ganin sun samu bacci ya fito daga d'akin, yana fitowa faruoq ya taso yana fad'in "Dr yaya yarana sun dawo hayyacinsu?" Dr Ahmed ya kalleshi sannan yace " kaita yaranka make ma baka ta matarka koh?" Sai kwa ya hade rai "wacce matar? Nima duk rudewar nan danayi saboda yarana nayita don bana kaunar na rasasu,"
Da mamaki yake kallonshi juyawa yayi yana fadin ka biyoni office yanzu,"
Bayan sun zauna Dr ya kalleshi sannan ya fara mai bayanin abinda yake damunsu musamman Fatima don ita nata yafi taazzara don hard a ciwon zuciya ya kusan kamata anandai yamai gargad'in ya kiyaye abinda zaina b'ata ranta, yajishine kawai donshi ta mutu ma ba abinda ya dameshi, anan yace ayimai list din kudin da a kashe musu yaimai transfer Amman Dr yace bazai amshi komaiba ai yiwa Kaine yacedai yaje gida ya samo musu abinda zasuci in sun farka godiya yamai sannan ya tashi ya fita, motarshi ya shiga sannan ya nufi gida,
A can kuwa tin bayan tahowarsu jamcy gaba d'aya ta rud'e hankalinta ya tashi ganin rawar jikin da faruq yakeyi, zancen zuci ta fara,
"Kenan har yanzu yanason matarshi? Kalli rawar jikin da yake don kawai basuda lfy? Kai! Lallaima! Indai hakane boka bai cika musu Alk'awarinsuba na cire Fatima daga zuciyar faruq ya Santa mai tsanarta a zuciyr Shiva, waya ta d'auka ta kira mahaifiyarta tace tabar duk abinda tajeyi tazo yanzu, ba jimawa sai gata agidan don ita daman zuwa gidan d'iyartata ba wuya yake mataba, tana shigowa tags jamcy sai sintiri takeyi a parlour n " kewai lafiya me ya faru?"
"Inafa lfy hajiyarmu aini ina ganin aikin malaminnan kamar
Ya b'aci," nan ta kwashe abinda ya faru ta sanar da ita cewa tai ta d'auko mayafinta su taxi wajen bokan yanzunnan ba musu kuea ta d'auko wani yalolon mayafinta tabi bayanta suka five ko Neman izinin faruoq bataiba suna FIFA suna tari keke napep sai wajen bokansu,
Shi kuwa faruoq sanda ya shigo gidan bai gantaba kiranta ya fara Amman shiru ganin ya dudduba bai gantaba yaje ya tambayi mai gadi ko ta fita, nan ya tabbatarmai ta fita itada mahaifiyarta,
Ciki ya koma ya shiga kitchen yai tsaye bana tinanin abinda zai daga musu,yana shirin kunna gas ya gano flast din shayi akan canter d'aukowa yayi ya fito kuloli ya gani akan danning table yana bud'ewa yaga kayan break fast dad'i yaji sannan ya kwashe dukkan abincin ya fice a motar shi ya zuba sannan ya five ya nufi asibitin yana zuwa ya Tarar harsun farka fuad da mihal Raman d'akinsu d'aya d'akin fatimane daban da Saudi ya k'arasa gunsu yana musu sannu abincin days fito dashi ya zuba was kowa a fleet ya mik'a musu sunaci yanad'an yi musu fira, Dr Ahmed ne ya turo d'akin ya shigo ganin faruq a d'akin yace "'au Ashe ka dawo bansaniba nad'an fitane '"
"Eh na dawo bangankaba shine na shigo nan",
Yaran ya kallah
" Ah lallai biki yai dauk'i har an warware ana fira?
Kallon faruk yayi sannan yace matarkafa ta farka kaje ka kaimata abinci kai mata sannu", sai kwa ya had'e rai. " nifa nace ka densmin mgnrta kaki koh? To wallahi bazsn jeba kai ka d'auka ka kaimata mana, yana gama maganar ya tashi a fusace yai waje, yarsn Dr ya kallah do yasan sungamajin komai, fuad ne yace " uncle me yasa Abba bayasan ummi ? Har marinta yakeyi kuma inya gaidashi bays amsawa in ya shigo mu kawai yakewa magana,"
"A,a fuad ba tsanarta yayiba laifi tayimai kuna zata basho hak'uri zai daina kaji?"
Kai ya gyada alamar ya yarda,
"Bari inkaiwa umminku abinci"
Nunaea sukai zasu bishi yace su bari su karajin sauki Amman mihal harda kika, ganin hakanna yasa ya d'auketa ya kama hannun fuad ya d'su abincin suka nufi d'akin,
Suna shiga ta saki murmushin ganin yaranta amsarsu tayi ta zaunar akusa da ita tanajin d'uminsu, sannu yai mata sannan ya bats abincin tambayarshi tayi Wanda yai girkin? nan yace mata mijintane ya kawo matarshicr tayi,nanfa race ita bazataciba don bats yards da jjamila ba yaranma don bats saniba da bazata bari su Ciba, nan ya keantar mata da hankali yace insha Allah ba abinda zai samesu yace bari ya kira matarshi minaksha ta kawo mata abincin, koranta yayi yad'anyi mata bayani a tak'aice sannan ya fita daga d'akin, godiya Fatima tamsi sosai na irin taimakon dayai musu,
Ba ad'au lokaciba sai ga minaksha tazo tura d'akin tayi ta shiga, tayi matuk'ar girgiza da ganin hands fak'awartata aminiyarta ta koma ,
Da Saudi ta k'arasa Bakin gadon ta zauna Rana fad'in,
"Zahra me ya samrki haka kika fame kikai bak'i Lamar bakeba? Tin yaushe kike jinya Amman ba a Samar daniba wanne iron ciwone wannan,"?
Kika ta fashe dashi sannan ta ruk'o hannun minaksha tana fad'in,
"Minaksha ina cikin wani Hall mijina ya juyamin bays ko k'aunar ganina bayayi tun zuwan Jamila gidan matsayin kishiyata shiga jefani cikin wannan halin, ayanzu gidan yamin b'aki banajin dad'in zama acikinshi ko kad'an na shiga halin k'unci duk a dalilin BAK'IN CIKIN KISHIYATA."
Wani kukanne ya sarketa ta kasa cigaba da magana itama minaksha Tiini haqaye ya cika mata ido don ta tausaya mata sosai d'ago ta tayi sannan ta fara share mata haqayrn sannan yace................!
Next page 19_20
Mrs Bilyamin kai ta.
No edit pls sorry for the typing error👏🏽👏🏽👏🏽
. . 🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀
*BAKIN CIKIN KISHIYATA*
🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀
*Story and written*
*By*
*FATIMA UMAR kas*
( MUMYN MIHAl)
Page
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
*Bismillahir'rahamanir'rahim*
PAGE 19_20
"Kiyi hak'uri Zahra,komai yai farko zaiyi k'arshe,kici gaba da hak'uri domin ubangiji yana tare da masu hak'uri,ki jure wannan jarrabawar da sannu zakiga sakayya daga gurin ubangijinki,ki sani Allah yana jarrabar bayinsa ta bangarori da dama, don ya gwada imaninsu, to ke ubangiji sai ya jarrabeki da muguwar kishiya,don haka kici gaba da kai kukanki gurin Allah,shi Allah maji rok'on bawansane,,,,,,,"
Hakadai taci gaba da rarrashinta da tausasan kalamai hartai nasarar shawo kanta,
Abincin ta janyo ta zuba mata ta mik'a mata,
Sosai taci abincin said a ta k'oshi, sannan ta ajiye tasha ruwa,
Fira sukasha sosai sallah kawai ke tadasu, sai dare sannan minaksha suka tafi itada mijinta Dr Ahmed bayan ya tashi daga aiki,
Sallama ta mata tare da Alk'awarin zata dinga zuwa kullum tana d'ebe mata kewa har a sallamesu,
Ita kanta Fatima aranar zuciyarta wasai ta kwanta,
Don ta samu amayar da abinda ke damunta, sai taji tamkar ta d'auke dutse daga kirjinta,
Aranar tayi baccin data da d'e batai mai dad'i irinshiba.
Wannan kenan,
***jamcy kuwa ba su suka isa ba sai bayan azahar, duk da gudun da mai adaidaitan ke zubawa,
Bayan sun sauka suka biyashi,sannan suka fara kutsa kai ckkin duwatsun dake gurin,
Sai da sukai tafiyar k'afa sosai sannan suka isa,
Bokan ya nanan dai zaune inda yake yana ta surutai shi kad'ai,
Da baya suka shiga kamar yadda suka saba,don yace ba a shiga ta gaba,
Suna shiga yai saurin cewa,,,
"Kar kuyi mana sallama anan gurin,"
Umarninshi suka bi,
Basuyi sallamarba suka zauna,
Bayan sun zauna suka juyo suna fuskantar shi,
Zama mahaifiyar tata ta gyara tana shirin magana yai saurin katseta,
"Munsan meke tafe daku,kunzo akan maganar kishiyar " yarki da kukeson tabar gidan,shi kuma ya dawo k'ark'ashinta sai yadda tai dashi
Ko ba haka bane?"
Da Sauri jamcy ta gyad'a kai,
"Eh hakane boka,ayimin abinda ko kara na sa bai isa ya k'etare ba,"
Dariya ya kece ta ita tammar zararrre (ko da yake dama zararren ne tunda la,anannen Allah ne)
Sai da yai mai isarsa sannan ya murfuke fuska,ya zuba musu jajayen idanunshi yana cewa,,,
Za a yi miki aiki yadda kika buk'ata
Amma da k'aidoji,
Da sauri mahaifiyarta tace,,,
Zamuyi ko menene indai "yata zata mallake mai gidan da dukkan dukiyarshi,
" za Ku kawo mana bak'in jaki mai k'aho,da farin bunsuru,da bak'in kare mai k'afa shida, inkun kawo wad'annan sauran zamusa Aljanu su kawo mana,"
Shiru sukai suna rarraba idanu,an rasa mai Bakin magana,
Sai can jamcy ta daure tace,,,
"Boka ai wannan abubuwan saiku zaku iya samosu,
Saidai mu bada kud'in yadda muka saba,"
da sauri itama tace,
" eh sai dai ayi hakan,"
"Toku kawo kud'in mu zamu sa Al,janu su ka wosu,"
"Kamar nawa za a bada,?"
Inji jamcy,
"Dubu d'ari da hamsin 15000 zaku ajiye don aikinku mai wahala ne,"
Jamcy CE ta zaro kud'in daga Jakarta tana fad'in,,,
"Kud'in hannunmu bai kaiba, dubu d'ari 1,0000 ne sai dai in za a biyomu cikon",,,,,,,,,,
✍🏼Mrs Bilyamin kaita,
Pls comments..
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀🤦🏼♀
🙆🏼♀️🙆🏼♀️🙆🏼♀️🙆🏼♀️🙆🏼♀️🙆🏼♀️
BAK'IN CIKIN KISHIYATA,
Story and written
By
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn mihal)
Wannan littafin k'irk'irarren labarine, ban yishi don wani ko wataba, wanda yaji yayi kala da rayuwarshi to ina Neman afuwarshi.
Page 21_22
______wata dariyar ya k'ara kecewa da ita kamar zararre,sannan ya tsuke fuska yana muzurai yace,,,
"
Idan ba Ku cika mana Alk'awariba komai ya sameku Ku kuka jawoshi",
Gyad'a kai sukayi alamar amin cewaa,
"Ku ajiye anan, kuma kuyi gaggawar barin gurinnan kafin su dawo",
Da sauri suka mik'e, da baya da baya suka dinga tafiya har suka fita daga gurin,
Bayan sun fito titi suka tari adai daita sahu, suka nufi gida,
A dai dai k'ofar gidan suka sauka,
Bayan sun biyashi suka tura get d'in suka shiga ciki,
Yana parlor a zaune yaga shigowarsu,
Ai yana ganin mahaifiyarta yai saurin sauka daga kujerar ya durk'usa yana gaisheta,
Amsawa tayi sannan ta d'ora da fad'in ,,,
Ashe Fatima wai ba lfy"?
" eh ",
ya bata amsa,
" to Allah kyauta",
Ta fad'a cike da rashin damuwa, allah ya sawwak'e d'inma baza ta iya fad'aba,
Da amin ya amsa sannan ya fita harabar gidan don ya basu guri,
Ita kuwa jamcy ko Allah kyauta d'inma bata iya cewa ba,
juyowa tai
Kallon jamcy tai da ta hakimce a kujera tace,,,
"Kuna da d'an abin tab'awane agidan don yunwa nakeji, kinsan ulcer ce dani,"
(Uhhmmmm ni kuwa nace Ashe dai jamcy gado tai wajen ci,
Lallai kam
wai uwace zatazo gidan "yarta tana tambayar abinci 🤔)
" eh na dafa kafin mu tafi, kinsan nima bana jurar yunwar bari in d'auko mana muci,"
Ta fad'a sannan ta mik'e ta nufi danning table d'in,
Sai dai me?
Wayam! ta gani ba komai a wajen,
Kitchen ta nufa da sauri ta hau Neman abincin, amma ba ta ganiba, fitowa tai ta nufi parlorn tana fad'in,,,
Hajiya rmu kinga nayi girkin na ajiye Amman nazo yanzu kuma banganshiba",
"Kamar ya baki ganshiba, a ina kika ajiye,?
" Akan danning table na ajiyesu sai ruwan tea a kitchen, Amman banga ko d'ayaba",
Shiru mahaifiyar ta ta tai tana tinanin wani Abu
sai can ta kalleta tace,,,
"Anya ba faruq ne ya kwashe ya kai musu asibitiba?",
Wata irin bugawa k'irjinta yay,
tabbas biri yai kama da mutum, hakanema zancen mahaifiyar ta ta, don da shi yaci da taga alama kuma ko kwanukan babu, wata uwar ashar ta lailayo sannan ta d'ora da fad'in ,,,
" Tabd'ijan! Lallai ma faruq ya yi mugun raina min hankali, na yi girkin saboda cikina sannan yazo ya kwashe ya kaiwa wata k'atuwa,?
To wallahi yau saina mai rashin mutunci,kuma saiya zo ya memo mana abinci duk inda yake Donni ba baiwar su bace,"
A zuciye tai hanyar fita daga parlor n,,,,,,,,
Muje zuwa
✍🏼 Mrs bilyamin kaita
Comments and share.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
BAK'IN CIKIN KISHIYATA
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
Story and written
By
Fatima umar kas
(Mumyn mihal)
Page 23_24
_____Da hanzari mahaifiyar ta ta ta finciko hannunta ta dawo da ita cikin parlourn tana fad'in,,,
"Ke shashasha ina zakije? Zauna kiji me zan fad'a miki,ke yanzu mene abin ta da hankali?kwana nawa ne zai dawo tafin hannunki karki sake ki nuna damuwarki ko kad'an kinji dai na fad'a miki,yanzu kije ki d'aura wani abincin ki zuba mishi nashi ki bad'eshi da maganin nan don tin yau za ki fara amfani dasu, ki kwantar da hankalinki wannan rawar jikin duk sai ya denata nan kusa."
Sai a lokacin zuciyarta tai sanyi nan ta saki wani murmushin mugunta sannan tace,
"Kuma fa hakane abinda kika fad'a, bari naje na d'aura wani girkin," ta fad'i hakan tana mikewa ta nufi kitchen d'in,
Mintina kad'an ta kammala girkin don batai wani mai wahalaba, da kyar ma tayi don ko gani sosai ba ta yi saboda yunwar da takeji, zuba mai na shi tai ta bad'e shi da magunguna yanda baza a ganeba sannan ta juyo musu sauran ta fito,da ma ita bata tab'a girki da mai gadiba sai dai ya siya yaci,inko har yaci abincin gidan to Fatima ce ta girka, saida suka cinye abincin tas duk yawanshi, sannan ta d'auko musu lemo da ruwa suka kora, bayan sun gamane mahaifiyarta ta fara shirin tafiya saida ta k'ara fad'a mata yadda za tai amfani da magungunan sannan suka fito harabar gidan,
direba tasa ya kaita gida bayan ta ba ta kud'i da kayan abinci da ta sa ba ba ta, bata dad'e da tafiya ba faruq ya dawo gidan Ashe ma fita yai bai zauna a gidan ba,
bayan ya shigo parlourn ne yace "Ashe ma hajiyar ta tafi inata sauri inzo muyi sallama,"
"Eh ta tafi yanzu,"
ta bashi amsa a gajerce don har yanzu haushin abinda yai mata yana nan a ranta,
Yanzu ma gani take daga asibitin yake gurinsu,
kai tsaye bedroom ya wuce ya fara rage kayan jikinshi, sannan ya shiga wanka,bayan ya gama yai alwala sannan ya fito ya shirya kanshi ya nufi masallaci don gabatar da sallah isha'i,don tin yana wanka yaji ana ta kiraye _kirayen sallahn,
Bayan ya dawo daga masallacin kai tsaye gurin cin abinci ya nufa don sosai yakejin yunwa,saida yaja kujera ya zauna sannan yakai dubanshi gareta
tana hakimce a kujera da waya a hannunta da alama chatting takeyi,
"Kizo muci abincin mana"
Girgiza kai tayi "a'a ni nakoshi naci nida hajiyarmu" OK
Ya fad'a sannan ya fara cin abincin ko bissimillah ba bu,
Bayan ya kammala shima ya dawo kan kujera ya zauna sannan ya jona musu kallo sunayin kallon yana d'an janta da fira,
ita ta fara tashi taa nufi d'aki sannan shi ma ya tashi saida ya kashe komai na kayan wuta sannan ya haura saman don kwanciya,saida suka gama shirin bacci sannan ya kashe musu kwan suka kwanta,
Can cikin dare misalin 3:00 na dare ta tashi, a hankali ta sauko daga kan gadon sad'af_sad'af ta bud'e d'akin ta fita, kai tsaye ta sauko kasa ta nufi kitchen tana haskawa da fitilar wayarta gudun karta kunna k'wan ya tashi,
Kaskon tiraren wuta ta d'auko tazuba gawayi ta kunna ,
bayan ya kamane ta koma d'akin ta zuba wani sihirtaccen tirare akai sannan taje saitin kanshi ta fara tirara mai tana fad'in,
"FARUQ! FARUQ!! FARUA!!!"
Muje zuwa
comment's
And
Share
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
BAK'IN CIKIN KISHIYATA
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
Story and written
By
Fatima umar kas
(Mumyn mihal)
Page 25_26
_____Haka ta dinga tirara mai hayak'in a kanshi har sai da taga hayak'in ya daina fita daga kaskon tukunna taje ta maida kitchen ta dawo ta kwanta,
Washe garima haka tamai irin yadda tai na farko, saida ta jera dare 3 tana bankamai sihirinta,
a dare na ukunne ta cusa wasu layoyi a k'ark'ashin filonshi dayake ta da kai dashi sannan ta kwanta zuciyarta fari kal, don tana da tabbacin batai kuskure ba a yadda bokan ya fad'a mata yanzu sai jiran sakamako,
Aranar ko baccin kirki batayiba saboda d'oki ta matsu gari ya waye taga abinda take fata ya kasance,
Washe gari ya rigata farkawa duk da ya kusan makara Amman dai ba'a shiga sallah ba, don haka a gurguje ya shiga bathroom d'in ya d'auro Alwala ya fito, tashin ta ya dingayi Amman ko motsi batai ba ganin zai iya rasa jam'i ne yasa ya juya ya fita daga d'akin ya sauka ya nufi masallaci don daman basu da nisa da masallacin,
Ita kuwa jin fitarshi ta k'ara gyara kwanciyarta don tanajin tashin da yake mata, tsaki taja tana mitar katse mata baccin dayai bayan yasan ita bata sallah a irin wannan lokacin sai gari yai haske,
Shikuwa farouq ana idar da sallah yayo gida bai tsayaba kamar yadda ya saba sai gari yai haske yake dawowa, Amman yau wani irin azababben ciwon Kaine yake damunshi don tin farkawarshi daga bacci yaji kanshi yamai wani irin nauyi kamar and'ora mai dutse, kasancewar ba ya barin sallahn asubahi ta wuceshi yasa a daddafe ya tafi masallacin, dak'yar ya iya kawo kanshi cikin parlorn, anan kan kujera ya zube yana dafe da kanshi, tini idanunshi sun rine sun koma jajawur ga kuma jijiyar kanshi da sukai burd'in_burd'in,
Sai da ta gama juyinta a gado sannan ta sauko k'asan don baccin yak'i zuwa tin farkawarta,
Turus ta tsaya tana kallon yanda ya baje a kan kujera ko takalmin kafarshi bai cireba, k'arasowa tai ta zauna a kusa da kanshi tana fad'in,
"Honey lafiya na ganka anan baka haura samaba"?
Jin muryarta akusa dashine ya sanya ya bud'e idonshi dak'yar Wanda sukai ja suka k'ank'ance saboda azaba ya kalleta,sannan ya bud'e baki a hankali yace " kaina, kaina ne yakemin ciwo sosai",
"To ko asibiti zamuje?" Ta tambayeshi,
girgiza kanshi kawai yayi alamar a'a don maganar ma wuya takemai yanzu,
Itama bata dage sai sunje d'inba don ita tasan mak'asudin ciwon bana zuwa asibiti bane, tasan asirin ne ya kamashi don daman bokan ya fad'a mata in abin ya kamashi zai tashi da matsanancin ciwon kai, kuma yana sauka shikenan aikin gama ya gama
Aikuwa hakance ta kasance don ko cikakken minti 10 bai yiba yaji kan nashi ya dena ciwon kamar an yaye mai ciwon, jin ya dawo garau yasa ya mik'e zaune daga kwancen da yake,
A hankali yakai dubanshi gurinta yana kallonta sosai ya juba mata idonshi yana kallonta
don wani irin son ta da k'aunartane yaji yana shigarshi alokacin ga kuma wani tsoronta da shakkarta da suka dirar mai alokaci d'aya, ganin kallon da yake matane yasa ta tashi ta dawo kusa dashi sannan ta rik'e mai hannu tana fad'in,
"Please zaka iya gyaramin d'aki? yau kasala nakejine"
"me zai hana my jamcy bari inje in gyara miki"
Ya fad'a yana mik'ewa jikinshi har wani rawa yakeyi ya haura saman, da kallo ta bishi tanajin wani nishad'i na shigarta,
Bayan ya gama gyara mata d'akinne ya wanke mata band'akin sannan ya sauko ya nufi kitchen ya fara wanke kayan da a kaci abinci jiya saida ya gama sannan ya d'ora musu abin Karin kumallo,
Ita kuwa tana nan zaune a parlorn tana kallon yadda yake ta mata Aikin duk ya jigata saboda rashin sabo Amman ita ko d'igon tausayinshi batajiba a ranta,
Sai da ya gama had'a musu break fast d'in
har ya jera a danning table din tace ita ba a can zataciba ya kawo mata na ta kan carpet, haka ya kuma kwasowa ya kawo mata sannan ta fara ci, Ai tana kai cheaf d'in bakinta tai saurin furzarwa, sannan ta d'ago a fusace ta............
Comments
And
Share
✍🏽mrs bilyamin kaita
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
BAK'IN CIKIN KISHIYATA
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
Story and written
By
Fatima umar kas
(Mumyn mihal)
Page 27_28
______ A fusace ta d'ago ta watsa mishi wani mugun kallo tamkar wani d'anta ba mijinta ba, sannan ta d'ora da fad'in,,,
"Wannan wanne irin wulak'ancine zaka bani wannan abin inci ?Akuya ka maidani ko me? Kawai ka zabga wa Abu uban maggi ga mai da ka shanana aciki sannan kuma don ka maidani kwad'ayayyiya ka kawomin inci? (nikwa nace ai dama bakiyi k'aryaba kwad'ayayyiyarce 😂 kukuwa fa fan's me kukace?)
Turo mai tayi gabanshi tana fad'in " gashinan d'auki kaci kaji abakinka yanda yai"
Ba musu kuwa yaja plet d'in gabanshi ya d'auka yakai bakinshi, saidai abinda yai zato bashi ya jiba donshi a yadda yaga ta zage tana tamai masifa ya zaci maggin over yayi sosai sai dai kuma da yaci sai yaji sab'anin haka, don maggin baiyi yawan da za a kasa cin chiefs d'inba donkoshi zai iyacinshi a haka,Amma gudun karya k'ara laifi yasa shi fad'in "kiyi hak'uri don Allah bansan zaiyi yawaba, yanzu me kikeson ci na k'ara yi miki?"
Wani kallo ta k'ara watsa mishi sannan tace "banaso bazan ciba salon yanzu kuma ka zuba min clean a maimakon gishiri kenan to bazan ci na gidan nanba yau kaje ka siyomin a waje, kuma farfesun kayan ciki nake buk'ata."
tana gama fad'in hakan ta tashi ta haura sama, ba musu kuwa yaje yad'au makullin motarshi ya fice daga gidan don siyo mata abinda ta buk'ata,
tanajin fitar shi ta saurin saukowa k'asan, plet d'in cheaf d'in ta d'auka ta faraci said a ta cinye tas tukunna ta had'a shayi mai kauri da bread taci, bayan ta gama ta kwashe kayan takai kitchen sannan ta koma d'aki,
Kasancewar yana zuwa restaurant ya samo farfesun bai jima da fitaba ya dawo, bayan shigowar shi kai tsaye kitchen ya nufa ya d'auko plet ya juye mata aciki sannan ya nufi d'akin ta ya kai mata, ko kallon arzik'i bai samuba balle godiya, kasan ya sauko don yaci Wanda yai dazun Amman sai bai ganiba kitchen ya shiga azatonshi ko takaimai can Amman saidai kwanon ya gani ba komai a ciki,komawa yai saman ya tambayata b'ud'ar bakinta sai tace ta juye a shara aiko almajiri bazai iya cin wannan abin ba,duk da yaji ba dad'i a ranshi Amman bazai iya magana ba, don haka jiki a sanyaye ya juya ya koma kitchen din, tea ya had'awa kanshi mai kauri sannan ya d'auko bread d'in ya fito ya zauna ya fara karyawa,
Yana cikin karyawar sai gata ta sauko zama tai sannan ta d'ora k'afa daya kan daya ba tare da ta kalleshiba tace
"Ina buk'atar kud'i don ina da buk'atarsu, kuma a yanzu nake so basai anje anciroba,"
Da Sauri yace "kamar nawa kike buk'ata?"
"Kawai ka nunamin inda suke naje na d'auka basai kajiba ninasan nawa nake buk'ata"
Ta fad'a tana girgiza k'afa,
"Kiije d'akina ki bud'e drower ki d'iba
" tashi tai ta nufi d'akinnashi sai da ta d'ibi son ranta sannan ta koma d'akinta ta d'au waya ta shiga kiran mahaifiyarta, tana fara ringing a ka d'aga , aitanajin an d'auka cike da zumud'i ta fara fad'in
" hajiyarmu yau ina cikin far in ciki abinda nake son kasancewarshi ya kasance, don haka ki shirya yanzu zanzo mukaiwa boka cikon kud'inshi kedai sauran labari sai nazo" tana gama wayar ta canja kayan baccin da suke jikinta sannan ta d'au mayafinta da pos ta fice,
Yana ganinta ta fito da shirin fita ta fice ko kallonshi bataiba,
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kallo agogo d'aya saura lumshe idonshi yayi ya rasa me yake damunshine yau? Gashi ya manta ma da maganar zuwa office har lokacin ya kure haka, tashi yai ya haura sama, d'akinshi ya shiga wanka yai sannan yai Alwala ya fice masallaci, bayan ya dawo ya kwanta donya huta nandanan bacci ya d'aukeshi,
Alarm! D'in wayarshine daya buga 4:00 daidai ya tasheshi , Alwala ya kumayi ya fice masallaci bayan ya dawo ya zauna a wajen mai gadi suna d'an tab'a fira,
Yana nan zaune har aka kira magriba sukai masallaci, bayan sun dawone ya shige ciki ya zauna a parlor
Remote ya d'auka
Ya canja tasha ya koma MBC Action bai d'ade a parlorn ba sai gata ta shigo kamar an jefota don ita daman sallama Ba damunta tayiba,
Akan kujera ta zube tana fad'in "wash! na gaji sosai wallahi"
Bari in d'ora mini ruwan wanka,"
Ya fad'a
"Yawwa daka kyauta kuwa d'oramin"
Tashi yai ya hau saman ya shiga toilet ya had'a mata ruwan wankan sannan ya fito ya Sanar da ita ya gama, " to saura kuma abinda zanci don gaskiya yunwa nakeji sosai kuma shawarma nake shaawar ci don haka kafin inyi wankan kaje ka siyomin yanzu,"
Tana gama maganar ta juya ta fara hawa step d'in benen, shikuwa faruoq..................
Pls comments
And share
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
BAK'IN CIKIN KISHIYATA
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
Story and written
By
Fatima umar kas
(Mumyn mihal)
NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE D'IN GA K'UNGIYATA ABAR ALFAHARINA K'UNGIYA D'AYA TAMKAR DA DUBU WATO 💕ZAFAFA WRITERS 💞ALLAH YA K'ARAWA MARUBUTAN CIKINTA BASIRA DA HAXAK'A AMIN SUMMA AMIN🤲🏽
Page 29_30
Shi kuwa farouq juyawa yai ya fita don siyo mata abinda ta aikeshi, motarshi ya d'auka ya fice,
Gurin saida abinci ya dinga bi Amman bai sami shawarma ba, saida yai yawo sosai yana tambaya?
dakyar ya samo a wani restaurant mai nisa da aka kwatanta mishi,
siyo mata yayi da yawa sannan shima yasai abinda zaici yayo gida,
Bayan ya dawo yai horn mai gadi yaje ya bud'e mishi get ya shigo da motor d'inshi ya ajiye sannan ya kwashi ledojin da take away yai cikin gidan,
Yana shigowa ya ganta zaune a kujera sai zuba hamma takeyi, ai ta na ganin shigowarshi ta balbaleshi da fad'a ko zama bata bari yayi ba Wai aina yaje ya zauna ya barta tanata jiranshi bayan yasan tacemai yunwa takeji?
Shidai hak'uri ya dinga bata sannan ya mik'a mata ledar shawarma, amsa tai sannan tace ya d'auko mata plet a kitchen, d'auko mata yayi sannan shima ya zauna ya bud'e na shi ya fara ci,
Sai da ta cinye na ta tas sannan ta sauko tasa hannu a nashi suka ci tare, bayan sun gamane ta tashi tai d'aki tare da cewa "kazo kayimin tausa zanyi bacci don na gaji sosai ". Ba musu ya bita d'akin tausar ya dinga yi mata har saida tai bacci sannan yaje yai wanka tare da alwala yai sallahr isha'i sannan shima ya kwanta,
Haka rayuwar gidan taci gaba da kasancewa, bangaren jamcy ta samu abinda takeso don ta Riga ta gama da farouq ya Riga ya dawo a tafin hannunta don yanzu sai abinda tace shiyakeyi baya mata musu ko kad'an.
***** A bangaren su Fatima kuwa yanzu jiki alhamdulillah don dukkansu jikinsu yai sauk'i, Ayau nema Dr Ahmed ya basu sallama kuma shine zai kaisu gida shida matarshi,don gaba d'ayan d'awainiyar asibitin sune sukai shida matarshi don kullum minaksha intazo tin safe sai dare suke tafiya tare da mijinta ita take jinyarsu,
Kuma tana kwantarwa da Fatima hankali tare da d'ebe mata kewa shiyasa yanzu hankali fatiman ya kwanta, haka Dr ma shiyake yi musu ko mai a aljihunshi, don tin ranar da faruoq ya tafi bai k'ara dawowa ba gashi sai nemanshi yake a waya Amman kullum a kashe, don haka yau yai niyyar tashi da wuri don ya kaisu gida,
Hakance kuwa ta kasance bayan ya tashi daga aikin wayar minaksha ya kira yace su fito su wuce kar magriba tayi musu a hanya,
Bayan ta sauke wayar ne ta mai da hankakinta kan Fatima da taga duk yanayinta ya canja,
Da fa ta tayi, a hankali ta d'ago da face d'inta ta kalleta , "ZAHRA don Allah kidena sa damuwa aranki wallahi banason indinga ganinki cikin damuwa, kinsanfa yanayin ciwonki bayason tinani da b'acin rai Amman yau ina lura dake tin da nazo bakya cikin walwala kamar baya, don Allah ki daure ki k'ara hakuri insha Allah inkin koma zakiga canji daga gun mijinki kedai kici gaba da hakuri kina kaiwa Allah kukanki muma zamu tayaki insha Allah zakiga amfanin hakurin da kikayi agaba."
Hawayene ya silalowa Fatima don ita a yanzu bata k'aunar komawa wannan gidan data rad'a mishi BAKIN GIDA don ita dasun kyaleta daga asibitin Kaduna zata tafi gurin iyayenta masu sonta da k'aunarta tabar wannan bak'in gidan da muguwar kishiyar da takeson kasheta da bak'in ciki,
Rarrashinta taci gaba dayi hardai ta d'an ware sannan suka tashi suka fito daga d'akin suka nufi gun Dr Ahmed da yake ta jiransu a mota,
Bud'e musu yai suka shiga, yaran ya juba a kujerar kusa dashi su kuma su Fatima suka zauna a baya, ta da mortar yayi suka tafi,
ko a motarma kwantar mata da hankali suka dingayi da nasiha har suka iso gidan,
Mai gadine yazo ya bud'e mai get ya shigar da motar cikin gidan saida ya gama daidaita parking sannan ya kashe motar suka fito, mai gadinne ya k'araso gurinsu fuskarshi cike da fara,a suke gaisawa, har k'asa Fatima ta durkusa ta gaidashi, amsawa yai tare da mata ya jiki yanajin k'aunar yarinyar tamkar y'ar cikinshi haka yake jinta,kodan itama ta maidashi tamkar ubane?
Bayan sun gama gaisawa ne Dr Ahmed yace "Baba mai gidan yana cikine?"
"Eh yana ciki don banga ya fita ba,"
OK Dr Ahmed yace sannan yace su biyoshi, kasancewar kamar d'an gida yake yasa kai tsaye suka shiga perlon,
Faruoq na zaune akan carpet yana daddanna laptop d'in da ke gabanshi yaji sallama,
D'agowa yai don ganin wane, ido hud'u sukai da Dr Ahmed, da fara arshi ya ce "Ah! Dr Kaine agidan sannu da zuwa, au ashema kaida minakshane ?" Ya fad'a yana kallon kofar data shigo yana shirin k'ara yin magana yaga Fatima ta shigo,
nandanan kuwa yamaida fuskarshi tamkar fuskar shanu don ganinta ba k'aramin b'ata mai rai yayiba shi gaba d'aya ma ya manta da ita kwata_ kwata sai yanzu da ya ganta, wani irin mugun kallo ya shiga watsa mata,
Sunkuyar da kanta tayi don ba za ta iya jurar ganin fuskarshi a hakaba,
fuad ne ya tafi da gudu gurinshi ya fad'a jikinshi yana "Abba na I miss y....." Ai tin Kafin ya k'arasa yai saurin hankad'ashi tare da fad'in " mene haka zakazo ka fad'amin jiki? dallah! Matsa daga kusa dani..."
Dr Ahmed ne yai saurin katseshi da fad'in" haba faruoq mene haka? Kana cikim hayyacinka kuwa? Fuad ne fa kamai wannan hankad'ewar jibi yadda ka fasa mai baki sai Kace ba d'ankaba?....."
Shima farouq a fusace ya mike tsaye yana nuna Dr da hannu tare da fad'in "ya isheka haka Ahmed nikake kira bana cikin hayyacina? to acikin maye nake burkutu nasha k'arewar rashin hayyaci,"
Shigowar jamcy CE ta katseshi tana fad'in "lfy naji hayaniya agidan wane ya tab'amin kai?"
Ga su nan! wannan banzarce daga dawowarta harsun fara cajamin kai, kaini na rasa wannan wacce irin masiface ina zaune kalau da mata ta anzo za a d'agamin hankali,"
"Ai daman tunda naji hayaniyarka nasan bazai wuce wannan uwar nacinba, don ita burinta a kullum ta b'ata maka rai,
su kuma wad'annanfa da sukazo suka cikawa mutane gida?"
Ta fad'a tanawa minaksha wani wulak'antaccen kallo,
"Kee! Ya isheki haka ki iya bakinki anan gurin don ke baki is don munzo gidannan kice za ki wulak'antamuba, ki kallemu sama da k'asa munfi k'arfin wulak'anci wallahi,
Kuma wallahi ki kiyayi gamuwarki da Allah akan zalincin da kikaiwa wannan baiwar tashi,don Allah bazai k'aleki akan abubuwan da kika kullaba donshi ba azzalumin sarki bane,
kawai kinshiga kin fita kin shiga tsakanin mata da mijinta kina zaluntarsu? To ki kiyayi gamuwarki da Allah aranar da zai muku hisabi tsakaninki dasu,"
"Kee! Ni za ki k'ullawa sharri kice ina asiri? To wallahi bazan yardaba sainayi k'ararki akan k'azafin da kikayimin,"
sai kuma ta rushe da kukan munafirci,
Faruk gaba d'aya ya fud'e ganin jamcy na kuka, aikuwa a zuciye ya nun musu k'ofa,
" Ku ficemin daga gida kuma daga yau karna k'ara ganin k'afar d'ayanku a gidannan don zuwanku ba alkairi bane,"
Dr ne ya kalli minaksha yace
" taho mu tafi ko me yayimin ninaja tunda ninazo gurinshi, Amman ka sani gaskiyace bazan fasa gaya maka ba, ka tashi tsaye akan gidanka tun kafin lokacin ya k'ure maka, ka dawo hankalinka don ka gyara gidanka,
gaba d'aya kabi ka susuce akan Mace? Macenma bamai sonka saboda Allah ba ? To wallahi kaji tsoron Allah kai adalci akan matanka."
Yana gama maganar yaja hannun matarshi suka fice daga perlourn,
shi kuwa faruk rarrashin jamcy ya shiga yi don tai shiru Amman takiyi, saida yaja hannunta sukai sama sannan da k'yar tai shiru,
Ita kuwa fatima daman tuni tajayaranta suka shige d'aki,ajiye mihal tai sannan ta kai fuad bathroom ta wanke mai
jinin bakinshi sannan tazo ta canja mai kayanshi ta kwantar dashi don har zazzabi ya fara rufeshi, d'akin ta kulle sannan tazo ta zauna hawaye ya shiga kwararowa a kuncinta,nan ta shiga tinanin abubuwan da suka faru acan shekarun baya da suka wuce,
SHIN! MENENE LABARIN WAD'ANNAN MA'AURATAN?????
Pls comment's
And
Share
Mr's Bilyamin kaita.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️
BAK'IN CIKIN KISHIYATA
🙆🏽♀️🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️
Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)
Page 30_35
ASALIN LABARI
***** Alhaji umar da hajiya hauwa Jidda 'ya'ya 5 suka Haifa 3 maza 2 mata, Amman ukune yanzu araye don biyu basuyi tsawon raiba ubangiji ya karb'i abinshi,
Fatima itace babba sai Abubakar yake binta sai k'aninsu Aminu Amman Al'amin suke kiranshi,
Alhaji umar yanada tarin dukiya mai yawa kuma yana taimakon mutane sosai musammam masu b'ukatar taimakon, haka kuma ya tsaya akan tarbiyyar yaranshi, yabasu ingantaccen ilmi daga na Arabic har boko,
Don karatun su fannin addini a k'asa mai tsarki sukayishi,bangaren boko kuma waje ya fitar dasu sukeyi,
Yana kashe musu kud'i sosai kasancewar yana matuk'ar k'aunar yaranshi kuma yanason yaga sunyi ilmi mai zurfi da zasu taimaki Al,Umma dashi, ammanfa wannan burinnashi a kan mazan ya dorashi,
Don ita Aunty Fatima agida tai karatunta bai fitar da ita ba kuma tana cikin karatun Allah ya fito mata da mijinta kasancewar d'an uwansune yasa akayi auren yace in mijinta ya yarda ta k'arasa a d'akinta,hakance ta kasance kuwa bayan anyi auren taci gaba da karatunta, bayan ta gama yasamar mata aiki, ayanzu haka tana da yarinyarta d'aya NUSAIBA,
A yanzu haka su Abubakar ba sa gida suna k'asar waje sun kusa kammala karatunsu su dawo gida don rabonsu da gida shekara takwas kenan don haka suke cike da zumud'in dawowa donsunyi kewar family d'insu,
Saidai duk farin cikin da suka iso k'asar dashi ya gushe zuwa b'ak'in ciki sakamakon rashin da suka tafka na rasuwar mahaifinsu, don a ranar da suka dawo kwana 3 kenan da rasuwar mahaifinnasu mutuwar da ta girgiza mutane sosai, saboda ba rashin lfy yayiba, Accident yai a hanyarshi ta dawowa daga jos yaje gurin yan uwanshi yai karo da wata babbar mota atake motar tashi ta gangara rami sai fito dashi akayi ko shurawa baiyiba yace ga garinku nan
Hak'ik'a yan unguwar da Abokan kasuwancinshi sunshiga tashin hankali a ranar don wasuma duk yayi musu sallama kafin tafiyarshi, saidai ya sami kyakykyawar shaida daga Bakin Al,umma maza da mata,
Hajiya Jidda na ganin gawar tashi duk jikinshi ya b'aci da jini tsananin rud'ewa da tashin hankaline yasa ta yanke jiki ta fad'i,
Tun daga nan bata k'ara sanin inda kanta yakeba saida tai kwana uku a asibiti sannan ta farfad'o, bayan ta farfado ne abinda ya faru ya fara dawowa cikin kwakwalwarta, shikenan yanzu ta rasa mijinta? Shikenan yaranta sun zama marayu,?wannan tinanin da tayine yasa ta fashewa da kuka,
Kukanne ya jawo hankalin yan uwanta da ke waje da sauri suka shigo d'akin, nan suka fara rarrashinta su kuwa Abubakar da Al,amin suma hawaye suke sharewa don suna cikin tashin hankali ga rasuwar mahaifinsu ga kuma rashin lafiyar mahaifiyarsu,
Abubakarne ya fita don kiran likita,
Bayan yazo yai 'yan dune duben shi,ganin ba wata matsalane yasa yace jikin nata da sauk'i za su iya tafiya, sai magunguna da za ta cigaba dasha kuma ta rage yawan tinani da damuwa, godiya sukaiwa likitan sannan suka fara shirin tafiya gida bayan ya basu sallama,
Abubakar ne kejan motar sai Al'amin da yake kusa dashi sai Aunty Fatima da ta rik'e hajiyar ta su sune a baya,
Sauran 'yan uwantane a d'aya motar da sukazo asibitin,
Bayan isarsu gidan suka tarar gidan a cike da yan zaman makoki tin daga Bakin gate har harabar gidan a cike take anata karbar gaisuwa,
Tin fitowarsu daga motar aketa zubo mata sannu tare da gaisuwar mai gidannata, kai kawai take kad'awa don bakintama yai mata nauyi maganarma wahala take mata,bayan sun shigo ciki akan 3 siter Aunty Fatima ta zaunar da ita,
Kishingid'a tai a kujerar kasancewar jikinta ba k'arfi sosai,
ko anan d'inma gaisuwar aka cigaba da zuwa ana musu,su kuma mazan daman basu shigoba awajen suka zauna ana karbar gaisuwa,
Ranar sadakar bakwai jikin hajiyar da sauk'i sosai don sosai yan uwanta suka dage da tausarta dayi mata nasiha hardai ta dangana don yanzu ba ta zubarmai da hawaye saidai ko yaushe ka ganta da carbi da katon hijab tana yi mishi addua duk da bata magana sosai sai in maganar ta zama dole, ayanzu jikinta yai sauk'i sosai tamkar batai jinyaba,
Bayan anyi adduar bakwai mutane duk sun watse sai yan tsiraru najiki.
****** kwanci tashi asarar mai rai matuk'ar ba ya aikatawa kanshi abinda zai amfaneshi duniya da lahira,
ayanzu shekarun Alhaji UMAR biyu da rasuwa, tini anyi Rabin gado anbawa kowa hak'k'inshi, ayanzu su Abubakar tini sun duk'ufa da juya dukiyar da suka gada agurin mahaifinsu, kuma ubangiji ya sa musu albarka a ciki don yanzu dukiyar tasu ta kusan ninka tada,
Bangaren hajiyama yanzu ta murje tai k'iba don mutuwarma ta Zame mata jiki,
saidai tin bayan rasuwar mijin nata manema sukai mata caaa masu son aurenta Amman tace ita Sam bazatayi aureba zamanta haka ya fiye mata,
tun suna nacin zuwa har suka hakura, don ba Wanda take saurara,
A yanzu damuwarta d'ayace na rashin Auren yaran na ta don Abubakar yanzu ya kusan cika shekara 30 shikuma Al,amin 27 ,don shekara 3 yayanshi ya bashi, Amman dukkansu ta ga basuda niyyar Auren don haka ayau ta yanke za ta k'ara tuntub'arsu da maganar insunzo gaisheta.
Comments
And
Share
Mr's Bilyamin kaita✍🏽
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️
BAK'IN CIKIN KISHIYATA
🙆🏽♀️🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️
Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)
Page*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
Page 35_40
Hakance ta kasance kuwa ranar wata lahadi ta k'ara tada musu maganar sanda sukazo gaisheta bayan gaisuwarne ta gyara zama sannan ta k"ara da cewa,
"Kai Abbakar Kaine babba Amman bakada niyyar aure yanzu balle shima k'anin naka yayi,
Nikuma gashi inason ganin 'yan jikokina suna wasa a parlourn nan, Ku duba kuga duk girman gidan nan Amman ni kad'ai ke rayuwa acikinshi dagani sai 'yan aiki, Ku kanku yanzu ba kullum nake ganinkuba gashi lokaci na k'ara tafiya shiyasa nakeson kuyi auren nan kafin k'asa ta rufemin ido". Ta k'arashe maganar cike da damuwa a fuskarta,
Su kuwa ganin damuwa a fuskarta ne yasa sukasan lallai abin na damunta, Abbakar ne ya gyara zama sannan yace,
" Dan Allah hajiya karki sawa ranki damuwa akanmu,insha Allah indai aurenmu zai saki far in ciki kwananan zakiga mun miki maganar,"
Shima Al'amin cewa yai "ni hajiya na jima da samun yarinyar da nakeso kawai dai ganin yaya bai yiba ne ya sani banyi magana ba, Amman insha allahu kwanan nan zan kawo miki ita ki ganta,"
Nan danan ta saki faraa don taji dad'in maganar ta su, don haka tace, " to Alhamdulillah Amman naji dad'i sosai kunsanfa shi aure yana k'arawa mutum girma a idon mutane, yanzu inkun daidaita da yaran saikuyimin magana sai a tura a nema muku auren don ba b'ata lokaci za a yiba, Ku tashi kuje Allah ya muku albarka," da amin suka amsa sannan suka tashi suka fita,
Shidai Abubakar daman akwai yarinyar data nacemai fiddausi Amman bai tab'a kulataba saboda shi ba tsarin aure a gabanshi yanzu saidai dolenshi yanzu yayi kodan farin cikin mahaifiyarshi,gashi bai da wacce yakeso ayanzu saidai kawai ya amince da fiddausin wata k'il inya aureta wata rana insuna tare zai iya sonta, da wannan tinanin yaji k'warin gwiwar yin auren,
Shi kuwa Al'amin sai da yaje kwanciya sannan ya d'au waya ya kira husna yarinyar da suke matukar son juna shida ita, bayan ta d'aga wayarne yace " albishirinki" goro ta fad'a daga d'aya bangaren, "kwanan nan iyayena zasuzo nemamin aurenki"
"Da gaske"?
Ta tambaya cike da zumud'i " wallahi da gaske nan ya kwashe yanda sukai da su hajiyarshi ya fad'a mata, " kai Amman naji dad'i burinmu ya kusan cika,,,,,,,,,,," hakadai suka k'are wayar cike da farin ciki suna ta tsara yanda bikin na su zai kasance,
Anje nema musu auren kuma duk an basu,kasancewar mahaifinsu sananne ne kuma anyarda da ingancinsu don haka ba a sa bikin da yawaba,
*** kwanci tashi bikin yazo akowanne bangare shirye shirye akeyi sosai da sosai,
Aunty Fatima tin ana saura sati d'aya bikin ta sauka agidan,
Biki yayi biki bangaren angwaye shagali ake sosai haka bangaren amarenma haka,
walima kawai akayi ba ayi wani bidia ba Amman hakan ya birge kowa daya halarta
ranar lahadi aka d'aura auren
Abubakar umar kas
Da amaryarshi
Fiddausi abdullahi
Sai
Aminu umar kas
Da amaryarshi
Asma'ulHusna Ahmed
Da dare aka kai amare gidansu kasancewar gida d'aya zasu zauna Amman ko wacce da part d'inta,gida kam ya had'u haka kowa ke fad'a don ba k'aramin kud'i suka zuba ba akayi musu ginin, haka 'yan kai amare suka watse akabar amaren da jiran angwayensu.............
Pls
Comments
And
Share
Mr's Bilyamin kaita
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️
BAK'IN CIKIN KISHIYATA
🙆🏽♀️🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️
Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
Page 45_50
Haka rayuwar taci gaba da juyawa saida farouq yai shekara takwas sannan husna ta k'ara samun wani cikin, ita kuma fiddausi a lokacin zatayi haihuwa ta 3 don bayan faruq ta k'ara haihuwar mace aka sanya mata suna HAUWA sunan mahaifiyarsu Abubakar kenan Amman Jidda suke kiranta,ammanfa saida yai mata jan ido sannan ta bari aka sa sunan mahaifiyar tasu don da cewarta sunan mahaifiyarta za a sa wato Halimatus_saadiyya saadiyya
yanzu kuwa da ta samu wani cikin taci Alwashin indai ta haihu ko me za ayi sai ansa sunan iyayenta,
Har lokacin da cikinsu ya shiga wata na 5 husna batasa ran za ta haifeshiba,gani take ko yaushe zai iya b'arewa yanzu haka ma Al'amin d'inne yake ta faman rarrashinta
ya k'ara da cewa "Dan Allah husna ki tashi insaukeki ayi miki awonnan daga can na wuce aikina",
Baki tad'an turo gaba sannan tace
" nidai yaya Amin ka kyaleni da mgnr awonnan, ka Riga kasan ciki ba zama yake a jikinaba sai nasa rai saiya zube, kagafa shekararmu kusan goma da aure Amman nayi b'ari yayi Sau Biyar tin inada ran haihuwar harna hak'ura watak'il banida rabon ganin k'waina a duniya."
Ta k'are maganar hawaye na ciko idonta, guri ya samu ya zauna ganin abin nata da gaske take,
Aranshi yana jinjina k'arfin halinta Wai itada keda ciki hartanajin motsinshi Amman take fad'in bazata ga k'wanta a duniyaba, dubanta yayi sannan yace
"Haba husna ina ilminki ya tafi? Kokin manta ubangiji ke badawa kuma ya karb'e?kuma shine maiyiwa bawa k'yautar dabai zataba, bakisan me ubangiji ya b'oyeba ya kamata ki kyautata zato akan kowa balle kanki Ki sani in ubangiji yai nufin zai taka k'asa tozai taka inkuma ya kaddara bashida numfashi a duniya to haka zamu hakura mu fawwala mai komai......."
Hakadai ya dinga rarrashinta harta danji dadi ta tashi suka tafi, bayan ya sauke ta inda zatai a won shikuma ya wuce aikinshi,
Ko a wajen awonma antabbatar mata ba wata Matsala duk suna cikin koshin lafiya itada babyn, sun dai fada mata abinda zatafi ci da abubuwan da zata kiyaye don kare llafiyarta data babynta hakanne ya kwantar mata da hankali jin ba wata matsala,
Hakadai taci gaba da zuwa asibitin don a duba lfyrsu,
Yayinda Al'amin yaketa jido kayan jarirai kala kala tunkan ayi haihuwar donshidai yana saran wannan karan ya kusa zama baba,
Kwanci tashi cikin su ya shiga watan haihuwa, ranar wata juma a da daddare husna ta fara nakuda tin tana daurewa harta fara jigata k'afar Al'amin ta shiga jijjigawa da karfin, can cikin baccinshi ya jiyo nishinta ai da sauri ya dire daga gadon yanufeta yana fad'in
"Husna lfy! Me ya sameki ? Ko haihuwarce, ganin ba amsane ya sashi ya mike da Sauri yai waje, mota ya fito da ita sannan sannan ya bud'e get, ciki ya kuma ya d'aukota yasa amotar sannan ya fice ya nufi asibiti gudu yakeyi sosai kasancewar ba motoci akan titin sai tsilla_tsillah don lokacin gari ya fara haske ba jimawa ya isa asibitin da sauri kuwa aka karbeta ganin ta fara galabaita sukai labour room da ita,
Cikin ikon Allah suna shiga dakin ta haihu, ta sillib'o 'yarta mace, zo kuga murna da farin ciki gunsu, shi al,amin ana fadamai ya yai sujjada ga ubangiji saboda nuna jin dadinshi ga kyautar nan dayai musu, sundubata ba wata matsala don haka aka sallamesu,
Bayan sun dawo gida ya cika tam da yan barka don tun suna asibiti yake kira yana sanarwa
Masha Allah kowa ke fada don yarinyar tubarjallah kyakyawace sosai, fiddausi kuwa tin fitarsu da dawowarsu duk taji Amman ko lek'e, farouq kuwa bata San sanda ya Zame yai part dinba, ita zatonta baima tashiba,
Tunda yaga babyn ya nace sai anbashi ita ya d'auka ai tashice aka haifamai, ganin ba a bashiba yasa kuka hard a birgima, husnance ta d'agoshi tana rarrashinshi
" ka bari su ganta su tafi sai a baka ita babu mai kwacemaka ko?" Gyad'a kai yayi Abu tasa ta gogemai hawayenshi ta zaunar dashi kusa da ita, saida 'yan taya murna suka gama tafiya sai yan uwa husnan
can sai ga fiddausin ta shigo, guri ta samu ta zauna Rana fadin
" Ashe da sauran wasu aciki ? Aina zata duk an tafi kinsan ni bason hayaniya nakeba yanzu kaina ya fara ciwo ashema da wasu."
Ta f'ada tana yatsina fuska, Aunty maryamce ta d'ago da niyyar tankawa don ganinn rainin hankalin yarinyar ya yi yawa Wai sunema wasu suna matsayin yan uwan husnan amman ko arzikin gaisuwa basu samuba sai bak'ar magana,
Husnace tai mata Alana da ido na karta tankama ta don tasan halin yayar tasu duk dakinsu tafi kowa zafi kuma tasan intai mgn abin hayaniya zai zama,
Ganin hakanne ya sa Aunty Maryam din kawar da kanta gefe tare dajan kwafahusnace ta amshi jarirriyar ta mik'awa fiddausin ganin auntyn tasu batada alamar bata jaririyat
Amsarta tayi ta zuba mata ido tana kare mata kallo, wani irin kyashi da jin haushine suka cikata lokaci guda
Don duk kallon da take mata na San gani muninta ta NASA ganowa ji tai bata k'aunar ganin jaririyar don haka ta mikata ta tashi ta five ko uhmm bata ceba,
Da kallo dukkansu suka bita cike da mamakin hali irinnata, kairat ce k'anwar husnan tace" Wai aunty daman haka wannan matar take a haka kike zaune da ita? To wannan da kiishiyarkice YAYA kenan? Kallifa ko kulamu bataiba balls tace Allah ya raya tana matsayin facalarki ba kishiyaba gaskiya batada kirki"
"To ai wannan dakishiyartace ba as an me zatayiba?Kuma ai duk laifin husnance sai ta dinga maata biyayya kamar wata ta uwarta, ni in nice da Tini an wuce gurin don bata isa tayimin ba kuma yanzunma husnance ta dakatar dani Amman da tini na taka mata birki tin shigoearta." Cewar Aunty maryam,
Husnan ce ta d'anyi murmushi sannan tace.................!
Comments and share pls.
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️
BAK'IN CIKIN KISHIYATA
🙆🏽♀️🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️
Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
Page 40_45
*****Bangaren Al'amin da amaryarshi husna lafiya kalau suka raya Daren amarcinsu cike da farin ciki sab'anin fiddausi da kusan kwa.a sukai suna cacar baki da Abubakar Akan ita donme za a had'ata da wata a gida d'aya? Wai ita duk zaatonta ita kad'ai zata zauna agidan donme bai Sanar da ita tun wuriba, itakam baza ta had'a zama da wata ba saidai a canjawa wacce n gida, shi kuma ya ce haka suka tsarawa Kansu zama guri d'aya shida d'an uwanshi don haka bata isa ta canjamai raayiba,
Hakadai suka raba dare suna kace nacc daga k'arshe dai d'akin ya bar mata yai tafiyarshi dakinshi ya kwanta ta ranshi a bace, don shi bai taba kojin labarin angon dayai aure suka fara fada tun adaren farkonsuba,
Itama bangarenta datakaici ta kwana don taso ace duk girman gidan ita kadai zata zauna don ba ta son kowa ya rab'eta,
Haka xaman nasu yaci gaba da tafiya saidai fiddausi sosai take kishi da husna don bata k'aunar zaman da suke guri d'aya itada husnan duk da kowa da part d'inshi,
Yayinda ita kuma husnan takeda hakuri sosai kuma tana girmamata don ita tamkar yayarta haka ta d'auketa,
Ana haka husna ta sami ciki nanfa fiddausi ta k'ara rura wutar tsanarta akanta tamkar ita ta bawa kanta cikin,
Saidai tsautsayi rana d'aya tai barin cikin
yayinda fiddausi kamar ta zuba ruwa a k'asa tasha don dad'i,
Bayan wani lokaci itama fiddausin ta fara rashin lfy,suna zuwa asibiti aka gano ciki dan wata uku a jikinta nanfa aka fara murna harda husna a yan taya murna, dayake cikin nata mai laulayine nanta lanjare ba abinda takeyi, husna ce ta d'auke mata komai take taimaka mata sosai, tin tana gwaleta hardai ta d'an fara rage tsanar da tai mata,
A haka cikinta ya shiga watan haihuwa
ranar wata juma'a ta tashi da nak'uda, ba jimawa aka d'unguma asibiti ba a d'au lokaci sosai da zuwanba ba sillibo d'anta namiji kyakykyawa mai kama da mahaifinshi, ba jimawa aka cika asibitin duk yan taya murna da farin cikine, hajiya Jidda ita kamarma tafi kowa murna da zuwan jikan nata, anan take Abubakar yaiwa yaron hud'uba da sunan mahaifinshi wato UMAR FARUQ,
Kasancewar lafiyarsu k'alau a ranar aka sallamosu suka dawo gida,nanfa yan taya murna suka cigaba da zuwa ganin jariri,
Haka ranar suna ta zagayo yaro yaci sunanshi UMARUL FAROUQ, anyi su na na bajinta anyi shagali sosai yaro masha Allah kowa ke cewa mai jego ta sami kyaututtuka sosai daga 'yan uwa da abokan arzik'i,
Husna ma sosai tayiwa jariri siyayya kuma ita ta shige kan gaba akai komai cikin tsari taro ya tashi lafiya,
Haka faruoq ya taso cikin gata da kulawa don yarone mai shiga rai gashi kyakykyawa kowa sonshi yake don yana girma kyawunshi yana k'ara fitowa,
Shekararshi biyu husna ta k'ara samun wani cikin saidai shima b'arinshi tai haka suka fawwalawa Allah komai duk da sunason haihuwar Amman sunsan yana sane dasu,
Don haka suka d'auki son duniya suka d'orawa faruq tamkar su suka haifeshi,
Shima yaron ya shak'u dasu sosai
Yayinda ita kuma fiddausi tak'i jinin hakan don ita ba a son ranta suke kula mata d'aba, kawai ba yadda zatayine dashi don ko ta hanashi zuwa gurinsu saiyai ta kuka yak'ijin rarrashi, ita kuma batason kukanshi shiyasa take kyaleshi Amman ba a son rantaba,
Don ita har yanzu bata tab'ajin k'aunar husnan a rantaba.
More comment
More typing
🤦🏽♀️🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️🤦🏽♀️
🤦🏽♀️
BAK'IN CIKIN KISHIYATA
🙆🏽♀️🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️🙆🏽♀️
🙆🏽♀️
Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
Page 45_50
Haka rayuwar taci gaba da juyawa saida farouq yai shekara takwas sannan husna ta k'ara samun wani cikin, ita kuma fiddausi a lokacin zatayi haihuwa ta 3 don bayan faruq ta k'ara haihuwar mace aka sanya mata suna HAUWA sunan mahaifiyarsu Abubakar kenan Amman Jidda suke kiranta,ammanfa saida yai mata jan ido sannan ta bari aka sa sunan mahaifiyar tasu don da cewarta sunan mahaifiyarta za a sa wato Halimatus_saadiyya saadiyya
yanzu kuwa da ta samu wani cikin taci Alwashin indai ta haihu ko me za ayi sai ansa sunan iyayenta,
Har lokacin da cikinsu ya shiga wata na 5 husna batasa ran za ta haifeshiba,gani take ko yaushe zai iya b'arewa yanzu haka ma Al'amin d'inne yake ta faman rarrashinta
ya k'ara da cewa "Dan Allah husna ki tashi insaukeki ayi miki awonnan daga can na wuce aikina",
Baki tad'an turo gaba sannan tace
" nidai yaya Amin ka kyaleni da mgnr awonnan, ka Riga kasan ciki ba zama yake a jikinaba sai nasa rai saiya zube, kagafa shekararmu kusan goma da aure Amman nayi b'ari yayi Sau Biyar tin inada ran haihuwar harna hak'ura watak'il banida rabon ganin k'waina a duniya."
Ta k'are maganar hawaye na ciko idonta, guri ya samu ya zauna ganin abin nata da gaske take,
Aranshi yana jinjina k'arfin halinta Wai itada keda ciki hartanajin motsinshi Amman take fad'in bazata ga k'wanta a duniyaba, dubanta yayi sannan yace
"Haba husna ina ilminki ya tafi? Kokin manta ubangiji ke badawa kuma ya karb'e?kuma shine maiyiwa bawa k'yautar dabai zataba, bakisan me ubangiji ya b'oyeba ya kamata ki kyautata zato akan kowa balle kanki Ki sani in ubangiji yai nufin zai taka k'asa tozai taka inkuma ya kaddara bashida numfashi a duniya to haka zamu hakura mu fawwala mai komai......."
Hakadai ya dinga rarrashinta harta danji dadi ta tashi suka tafi, bayan ya sauke ta inda zatai a won shikuma ya wuce aikinshi,
Ko a wajen awonma antabbatar mata ba wata Matsala duk suna cikin koshin lafiya itada babyn, sun dai fada mata abinda zatafi ci da abubuwan da zata kiyaye don kare llafiyarta data babynta hakanne ya kwantar mata da hankali jin ba wata matsala,
Hakadai taci gaba da zuwa asibitin don a duba lfyrsu,
Yayinda Al'amin yaketa jido kayan jarirai kala kala tunkan ayi haihuwar donshidai yana saran wannan karan ya kusa zama baba,
Kwanci tashi cikin su ya shiga watan haihuwa, ranar wata juma a da daddare husna ta fara nakuda tin tana daurewa harta fara jigata k'afar Al'amin ta shiga jijjigawa da karfin, can cikin baccinshi ya jiyo nishinta ai da sauri ya dire daga gadon yanufeta yana fad'in
"Husna lfy! Me ya sameki ? Ko haihuwarce, ganin ba amsane ya sashi ya mike da Sauri yai waje, mota ya fito da ita sannan sannan ya bud'e get, ciki ya kuma ya d'aukota yasa amotar sannan ya fice ya nufi asibiti gudu yakeyi sosai kasancewar ba motoci akan titin sai tsilla_tsillah don lokacin gari ya fara haske ba jimawa ya isa asibitin da sauri kuwa aka karbeta ganin ta fara galabaita sukai labour room da ita,
Cikin ikon Allah suna shiga dakin ta haihu, ta sillib'o 'yarta mace, zo kuga murna da farin ciki gunsu, shi al,amin ana fadamai ya yai sujjada ga ubangiji saboda nuna jin dadinshi ga kyautar nan dayai musu, sundubata ba wata matsala don haka aka sallamesu,
Bayan sun dawo gida ya cika tam da yan barka don tun suna asibiti yake kira yana sanarwa
Masha Allah kowa ke fada don yarinyar tubarjallah kyakyawace sosai, fiddausi kuwa tin fitarsu da dawowarsu duk taji Amman ko lek'e, farouq kuwa bata San sanda ya Zame yai part dinba, ita zatonta baima tashiba,
Tunda yaga babyn ya nace sai anbashi ita ya d'auka ai tashice aka haifamai, ganin ba a bashiba yasa kuka hard a birgima, husnance ta d'agoshi tana rarrashinshi
" ka bari su ganta su tafi sai a baka ita babu mai kwacemaka ko?" Gyad'a kai yayi Abu tasa ta gogemai hawayenshi ta zaunar dashi kusa da ita, saida 'yan taya murna suka gama tafiya sai yan uwa husnan
can sai ga fiddausin ta shigo, guri ta samu ta zauna Rana fadin
" Ashe da sauran wasu aciki ? Aina zata duk an tafi kinsan ni bason hayaniya nakeba yanzu kaina ya fara ciwo ashema da wasu."
Ta f'ada tana yatsina fuska, Aunty maryamce ta d'ago da niyyar tankawa don ganinn rainin hankalin yarinyar ya yi yawa Wai sunema wasu suna matsayin yan uwan husnan amman ko arzikin gaisuwa basu samuba sai bak'ar magana,
Husnace tai mata Alana da ido na karta tankama ta don tasan halin yayar tasu duk dakinsu tafi kowa zafi kuma tasan intai mgn abin hayaniya zai zama,
Ganin hakanne ya sa Aunty Maryam din kawar da kanta gefe tare dajan kwafahusnace ta amshi jarirriyar ta mik'awa fiddausin ganin auntyn tasu batada alamar bata jaririyat
Amsarta tayi ta zuba mata ido tana kare mata kallo, wani irin kyashi da jin haushine suka cikata lokaci guda
Don duk kallon da take mata na San gani muninta ta NASA ganowa ji tai bata k'aunar ganin jaririyar don haka ta mikata ta tashi ta five ko uhmm bata ceba,
Da kallo dukkansu suka bita cike da mamakin hali irinnata, kairat ce k'anwar husnan tace" Wai aunty daman haka wannan matar take a haka kike zaune da ita? To wannan da kiishiyarkice YAYA kenan? Kallifa ko kulamu bataiba balls tace Allah ya raya tana matsayin facalarki ba kishiyaba gaskiya batada kirki"
"To ai wannan dakishiyartace ba as an me zatayiba?Kuma ai duk laifin husnance sai ta dinga maata biyayya kamar wata ta uwarta, ni in nice da Tini an wuce gurin don bata isa tayimin ba kuma yanzunma husnance ta dakatar dani Amman da tini na taka mata birki tin shigoearta." Cewar Aunty maryam,
Husnan ce ta d'anyi murmushi sannan tace.................!
Comments and share pls.


0 Comments