BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
6⃣
Kuka take tana murza goshinta a kan cinyarta dake lulube da turkudi, hawayen nan ya jika turkudin ya yayakune sannan ya gogun mata a fuska ya kara rinar da fuskar ya kasance wani waje ya fi wani wajen duhu sosai fuskar du ta yi jirwayi da ita
Sai da ta ci kukanta har kanta ya fara ciwo kafin take yin shiru, mangwaron nan ta kuma kallo gannin du ya yi jajajir ya nuna ya saka ta mike ta gyara zaninta da kyau ta kama kokarin hawa ,
Da kyar ta hau bakibakin ta kamo wa.inda ke kusa ta tsintsinka ta diro ta zauna nan tana gogewa da hannunta sai kuma ta sha abinta, yau bama zata iya zuwa wajen tsoho ba ta san yana da ruwa goronsa kuwa ta kai masa gobe sai ta yi safiya ta je wajen shi
Wardugu, yanzu yanzu?
Kansa ya dafe ya ce" Ayya ko kin fasa tafiyar ne?
Da sauri ta mike ta nufi dakinta tana dafe kanta, yaron nan akoy kagauta , bashi da hakuri yanzu in ba rigima ba a kai tsayen nan ya zo yace su yi tafiyar da a yanda ake bata labari garin can cikin jeji ne? Aman ba komai irin yanda take mafarkin mutumin nan abin ya tsaye mata a rai, tana tune sun yi da shi idan yaro ya samu lafiya sai ta bashi salama da abinda ya sawaka sai dai ta zo tana yiwa Wardugu magani da magungunnan aka tashe su daga garin aka maido su Capital tun daga shi bata kara ganninsa ba domin ta neme shi sosai, sai kwanan nan take jin lanarin yanzu tsufa ya kama shi sosai baya yawo yana garinsa na haihuwa harma an fada mata sunnan garin , tana son sauke nauyi domin kuwa tun daga kan maganin wajensa Allah ya aminta wardugu bai kuma Huka ba sai tana gannin haki ne ta je ta sauke ba wanda ya san gawar fari
Nade ta fito da lifaya mai ruwan ja da kyalkyalin zaiba, lifayar sai baza kanshi take , Ayya ta kwana biyu a duniya aman karshe ce, akoy iya ado da sannin hakin turare, idan ka ganta sai ta birge ka gata da saka zinare tamkar ba da kudi take siya ba, danta ya bata damar murza mulkin da ta ga dama
Tafiyar manya ba.a kwasan tufafi, mai aikinta baturiya ce ta fito da wata yar valise (yar akwati) yar karama wace a ciki ta saka du wani abin bukatarta ta nufi kofa dan kaiwa cikin mota
Gaba ya yi yana amsa waya da aminiyarsa, kawarsa, wace du duniya itace babar kawarsa sai wa.inda ba za.a rasa ba, itace basa fada, ta iya tafiyar da lamarinsa ta iya zama da shi , sannan du irin yanda ya ki jinnin jajayen buzaye ita wannan baya iya kyamatarta , ba.a shaifar mutun aman shi zai bigi kirji da halayen *ALHINAYETT*
Kana nufin yanzu yanzu? Bama zan yi maku bankwana ba?
Wardugu ya ce" Alhinayettt bafa wani jimawa zamu yi ba, ke dai ki yi mana adu.a
Yana fadin haka daidai yana zama cikin motar Hilux tamkar wani daki tana fa fadin waje,
Sai fa ya gama wayar ya dubo AYYA da ta tsura masa ido
Kallonta yake da alamar mamakin kallon domin irin kallon nan ne na tsare mutun idan ya yi karya
Bakinta ta dan turo ta ce" kuma ka ce ba budurwarka bace, mutunci ne bakwa wata soyaya da ita,
Murmushi ya yi do.in daman ya saka a ransa wannan ne, ya dan sasauto ya riko hannunta ya ce" Anna, aa, Alhinayett aminiyata ce, wace bani da amini ko aminiyar da ta kai ta
Yatsina fuska ta yi ta ce" karyar banza wai aminci mace da namiji ? Ai ba shi sai idan soyaya ake
Kawar da kansa ya yi ya ce" kin ce a lokacin da ya baki magungunnan da aka dura min ma tsofo ne, kuma har yanzu kina da tabacin yana raye? Ni din ma fa na jima a duniya
Murmushi ta saki ta mika hannayenta masu saye da zobunnan zinariya ta dankwashe masa kansa dan ta san yana so ta yi zuciya ne ita kuwa ba zata yi ba, halayensa tana gannin sai dai ta fada masa domin tun bai san kansa take tafe da shi ba
Sun Dauki hanyar airport dan zuwa garin Agadez daga nan kuma ya nemi abinda zai kai su garin da suka nufa
Mali yaro ne ke wasa a wajen auren kawar Walyn ,
Tunda ta shigo wajen wasan yake kofata da kiran General wande, Walyn kin fice yaro (Matar general),
Tunda ta nemi wajen da tana iya gannin kowa kowa na iya ganninta ta hakimce ta dauki kafa daya ta dora saman daya, ta karkace kadan ya kasance dankareriyar sarkarta ta zinari ta fito sosai, ta dora hannunta guda saman cinyarta awarwarayenta ma suka fito radau da su, takan dan saki dan murmushi hakoran makarta su bayanna, ta dan juya ta kuma juyar da kanta tana karewa mata da yan matan wajen kallo tana auna su daya bayan daya,
Kari ake masa na hauka aman hankalinsa du ya karkata kanta, ya sani ne udan ta zuge bakin wannan jakar nata mai shegen kyau sai ya yi kwasa, jakar a yashe take kusa da kafarta tamkar ba komai na anfani ciki bayan kuwa a cikinta kudane da dankara dankaran wayoyinta na kece raini
A haka har aka fito daga salar isha.i bata mike ta je ta yi sallar ba suna zaune sun zagaye mawakin da yakan silalewa ya bar yaransa da basu san ciwon kansu suma ba ya je ya gabatar da sallah ya dawo ya dora daga inda ya tsaya
Wannan dawowar da ya yi bai zame ko.ina ba sai gabanta domin ya lura yau yan mulkin ne, yan na isan ne, tana son nuna bambanci tsakaninta da sautan matan wajen,
Yana zuwa ya shiga kodata, yana waketa, yana wake jarumtar mijinta
Kanta ya fashe , ya yi gingirigin
Ai kuwa ta dauki jakar nan ta yage bakinta ta shiga zuba masa masu aku wato jika goma goma tana dangalar masa tana yi irin bata san ciwonsu ba sai da ta karar da jimki biyu wajen ya cika da ihu wata kawarta guda na daukanta vidio dan ta tura mata
A wannan rana an jima ana wasa wanda Walyn bata bar wajen wasan nan ba sai da aka gama sai da ta ga karyar ko wace yar karya kafin take mikewa ta dauki jakarta kawayenta masu mata fada suka biyo bayanta har sai da ta shige dankareriyar bakar motarta bayan ta wankesu suma da kudi ta tayar ta halba bakin titi a lokacin har karfe goma sha daya ta buga na dare
Garin niamey capital ta niger du wanda ya taba shigota ya san gari ne dake baje ta ko.ina da polisai
Basa wasa kame suke tun karfin su, in dai ka kuskura ka taka doka toh fa zasu damke ka ne ba sasauci
Tukinta take cikin nutsuwa,
Danja ce ta tsayar da ita bakin inda polisai shida ke tsaye suna duba takardun mota na mashin, da kuma takardar shedan kai wanene
Hankalinta konce take jira danja ta saki domin ta san sun san number motar general ko sun kurbi giyar bera ba zasu tunkareta ba koda kuwa ta taka dokar domin ta tsira tunda ta hau motar *DOKA* gabadaya
Kwonkwonkwon karar kwonkwasa motarta,
Da mamaki ta dubi wajen
Wani saurayin police ne fuskarsa daure tamau ba alamun wasa a tatare da shi
Da yannayin rashin mutunci ta sauke gilashin motar ta sauke masa idannuwanta masu nuni da baka da wayo
Shima fuska a daure ya ce" madame vous etes en état d'arrestation, veillez sortir calmement nous nous occuperont de la voiture (Madame mun kama ki ki fito cikin nutsuwa zamu kula da motar)
Da mamaki take yi masa kallon sakarai, baki bude ta nuno shi da yatsarta ta ce" kai aman kai sabo ne ko? Waye kai? Ka san ko wacece ni?
Sadowa ya yi sosai ya saka idannuwansa cikin nata ya ce" eh mun san ko ke wacece, umarnin mijinki ne in dai kika kai karfe bakwai a gari du wanda ya hadu da ke ya kai ki cel ki kwana da safe karfe goma a sake ki daidai gari ya cika kuma a rubuta a jarida!
Dum dum dum take jin maganar tamkar saukar aradu, quoi? (What), ita? A cel? Prison! Ita Walyn? Wardugu wardugu ta fada tun karfinta tana dukan sitiyarin motar ta .........
Ohk
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
7⃣
Ita Wardugu xai yiwa wannan wulakancin? Ta kwana a cikin kaso, batai sata batai komai ba? Dan kawai ta cika dare?
Wayarta ta warta a cikin jakarta ta shiga laluben numbersa wace ta sam zata same shi
Ta yi kira ya fi a kirga daidai lokacin polisawan sun zagayeta tamkar dai ta yi wani gagarumin laifi
Hanjaki kwonce ya daga domin lokacin yana hakimce kan gadon hotel din da ya sauka ita Ayya tana can gidan sarkin Agadez matarsa uwar gidan ce kawarta ta kusa sosai, shi kuwa ya ki sauka a nan ya je hotel , bayan ya gama harkar kasuwancinsa ne kiran Walyn ya shigo wayarsa, domin Wardugu na sana.a.o.i ya san dadin nema , yakan ce ba dole ya nema ba shi mai Ayya da Walyn
Murya irin ta yan duniya ya ce" adibinira (wato matata ) (readers kar ku manta a wannan nvel yare hudu ne, buzanci, tubanci, french da kuma hausa )
Murya ta sasauta tana tura hannunta cikin kannanuwan kitson da ta sha domin dai tubawa basa wasa da kitso ta ce" Haba mijina ya haka wannan tsatsauran hukuncin?
Murmushi ya yi jin yanda ta sasauto, kennan dai sai yanzu ta nufi gida ko? Muryarsa yanda take ya ce" hukuncin ya yi tsauri ne? Ko bai kai daidai da laifinki ba?
Idannuwanta ta lunshe tana jinsa har cikin ranta ta ce" matarka guda a prison? Ko laifi na yi ina tunanin na fi karfin nan sai dai ka hukunta ni a gida a dakin mu a saman gadon barcin mu ka rungumeni ka matseni ka haukatani da lamuranka , na san ina cika dare kuma baka so aman mutun ai ajizi ne, ka yi mini uzuri Wardugu
Murmushi mai sauti ya sakar mata, ya ce" bara dai mu gwada wannan idan ya so na dawo daga tafiar da baki tsaya kin ji ina zan je me zan je yi ba zamu yi magana
Fashe masa ta yi da kukan kisa , ta ci gaba da lalaba shi dan ya yarda ya yi masu magana su sakar mata hanya ta karasa gida dare na yi
Lumfashi ya sauke ya ce" ki bani daya daga cikin su
Cike da murna ta mikawa wanda ya fi kusa da ita tana zabga masa harara
Yana kara wayar ya kame yana sara masa tamkar yana gabansa
Murya a kausashe ya ce" wasu sutura ne a jikin matata?
Murya a ladafce ya ce" aa oga, mu mun isa mu kali matarka? Bamu kala ba bamu san irin suturar jikinta ba
A ransa ya ayana han, kafin yake cewa" idan ta ki ta fito ku zauna da ita a nan har safiya ta yi , har karfe goma sha biyu na rana kowa ya kasance ya ganta, sannan ku gayaci jarida ku bada cikaken labarin abinda ya faru, kar ku taba jikinta aman bata wahala, ka rike wayarta a hannunka sai goben ka bata! Sannan kar ku nuna mata wasa idan ta so kawo maku tsayaya ku tsoratata da bindiga
Da " a vos ordres ya amsa kafin yake katse layin ya saka a aljihun rigarsa
Wa ya ga zafi biyu 🤣
Karfe uku ne fa na dare aman ji kake gam gam gam ana dukan yar kofar gidan nasa
Da sauri *Tibillal* wato mahaifiyar su Agaishat mata a wajen *ALGABIT* mahaifin su Gaishat ta zabura ta kai dubanta wajen *AGAISHAT* dake zaune tsuru tun bugawar farko ta fara tana kallon kofar shigowar su
Mayafinta ta ja da kyau ta fito ta nufi dakin mijin nata
Tana zuwa ta tarar da shi a kwonce tamkar mai baci bayan ya farka ya yi tsuru daga kwoncen yana tsoron mikewa ma
Girgiza kafafuwansa ta fara ta ce" Algabit, Algabitt, ka tashi ana ta buga gidan nan
Hannunsa ya saka ya bige nata ya ce" naki na tashin, bayan a gari an san na amshi kudin auren yaranna , in na bude wani mugu ne fa? Koma waye ya yi hakurin safe mana aman a wannan tsofon daren? Ba zan bude ba!
Gannin ya tashi sai balbaleta yake da fadan da hujojinsa na karya ta mike ta nufi kofar wanda ya saka ya hantsilo ya rarumi wukarsa ya ja tunga yana fadin" kar ki bude mana, koma waye a daren nan ba bakon alkhairi bane!
Janye sakatar ta yi ta bude kofar,
Fado mata ta yi a jiki tana kuka, jikinta du sai rawa yake, ga sanyin garin aman wata yar ficiciyar riga ce a jikinta, mutumin da ya kawota a rakumi ne ya ce" na ga gidan zan dawo da safe a bani salamata!
Da tashin hankali Anna ta janyota cikin gidan tana ta kokarin kara dagota tana duba fuskarta dake da balshe ko.ina a tsannanin tashin hankali ta ce" *FATIMATA* fatimata , fatimata
Gaba daya mutanen gidan suka fito jin muryar Anna cikin tashin hankali
Da sauri Algabitt ya karaso ya janyota ya ce" Ke Fatimata, meye haka? Daga ina kike? Ya haka a tsiyace jiki a lalace? Ina mijin naki yake????
Dago kumburanrun idannuwanta ta yi ta sauke su kansa, da haushi haushi ta budi baki tun karfinta ta ce"'""" Aba, sai na kashe shi, kuma ko zaka kashe ni sai na hana ka kara bada kannuna a irin auren da ka yi mini!
Idannuwa ya zaro ya daga wukar nan nasa ya. Nufota ya saro daidai ita sai aka yi rashin sa.a Anna ta saka hannunta ta tare wukar ta yi mata muguwar sara a gefen hannunta ta yanketa sosai nan da nan jini ya bale
Ihu yayan suka kwasa, da sauri mariama ta karbe wukar ta yi jifa da ita ta hayayako masa da mugun bacin rai da nuni da zata iya aikata komai ta ce" ka je, kar jini ya biya jini!
Juyawa ya yi da sauri yana mamakin Kaf yayansa idan ya yi magana a da jiki na bari suke aikata abinda yake so aman kwanakin nan yana haduwa da hari kala kala da wajaje daban daban a cikin yayansa bale Mariama yarinyar na da zuciya ........
Labari bak'a ce labari ne kirkirare bisa lamarin da ba kirkirare ba, labarin yana tafiya ne bisa gaskiyar lamarin abinda ke faruwa , tabas na shiga kuma sai na fada......ku mu je zuwa a labarim bak'a ce in sha Allah
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
8⃣
Yana fita Bak'a ta cire daurin dake kanta ta daure hannun mamansu da fan kwalin du suka zauna jigum jigum suna kallon Fatimata
A hankali ta dora kanta kan cinyar mamansu da take jin zuciyarta na yi mata nauyi sosai ta ce" a ranar da aka dora ni saman Amale (Rakumi) daga ni sai mata hudun da suka zo a matsayin fagin mijin da aka aura mini muka tafi
Mun shiga garin agadez daga nan muka dauki hanya muke tafia tamkar ba zamu tsaya ba
Sai da muka je Damagaran daga nan muke mike muka dauki hanyar kano
Muna zuwa kanno muka kwana guda muka dauki motar asuba suwa Abuja
Tafiyarmu tamkar ba zata kare ba, tsakanina da su ido ne su basa jin yarena nima bana jin nasu ya kasance muna tafiyar kurame ne sai dai abinda na lura da shi tamkar masu jin haushina domin ko abinci zasu bani sai dai su wulo mini su fadi wata kalma sannan su yi mini nuni da in ci
Ba mu mu isa garin nan ba sai da safe domin da mukai dare muka tsaya muka waye a wani garin kafin mu karasa
Gida ne tafkeke, ya tsaru, ya hadu iya haduwa
Muna zuwa kowace ta yi tafiyarta aka barni a wani tankamemen falo ina zaune ni guda
Ban jima sosai ba na fara gannin wasu mata masu kyau suma kowace ta sha kwaliya sai baza kamshi take sun fifito sun layu saman kujera gefe da gefena hakan ya saka na takure waje guda
Ba.a jima ba wanda aka aura min da sunan mijina ya fito ashe yana cikin dakin du zaman nan da na yi ya zo ya zauna saman kujerar dake kallon tamu ya dora kafa daya kan daya
Walahi Anna mutumin sam ba annuri a tare da shi, mumuna ne, garjejen kato ne fuskarsa ba anuri ba fara.a ba haske ko kadan a nan ya kuna taba domin ba sigari bace taba ce ya kuna ya shiga ja wace nan take wajen ya garwaye da warin kwaya
Wasu maza ne suka fara shigowa, suka zauna suma inda suke hangen mu da kyau abin mamaki matan nan sai su ringa mukewa daya bayan daya su jujuya gaban mutanen nan wasu har su dakan masu duwawu su mamatsa a gabanmu a gaban kowa shi kuwa yana hakimce idan mace ta yi maka sai su hau ciniki cikin jarshen turanci a dauki mace a tafi da ita kwana wato Bariki
Nan wani yace wannan fa? Wato ni domin sun ga sabuwa ce a wajen
Da sauri na mike domin nunoni ya yi kafin yake yin maganar, koda ban ji me yace ba idannuwana sun nuna mini abubuwan da suka faru na ga komai na gane komai
Magana ya yi masu wace ban san me yake nufi ba suka gama kasuwancinsu ya cashi kudinsa sosai kafin suke tafiya
Sai da ya gama shaye shayensa ya taso kusa da ni sosai da muryar mashayi ya ce" ke fa sai na yi maki filafila dan kuwa an caje ni kudi kafin a bani ke kuma dan iskanci aka kawo ki daga ke sai wannan bakin kayan
Tashi ki tube
Da mamaki nake kallon shi, in tube, wai ina ne nan? Me hakan ke nufi? Matan nan su waye? In tube haka kai tsaye ai ko matarka ce ni koda mun saba da sannin juna fitsara ne gatsal ka kale ni ka ce mini tube
Mikewa na yi da yarena na rufe ido na shiga zazaga fitsara ina son sannin inda ya nufa
Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya kafin take kara sakin wani kukan mai karfi ta ce" Anna matan nan da suka fita bayan ya amshi kudaden karuwanci da zasu fita su kwana da karti ashe gaba dayan su suna zaune a matsayin matansa mace har bakwai ni ta takwas cikinsu ba daya ta yarwa sannan ba daya da ta san hanyar gidansu
A wannan ranar da katsa ya dake ni kafin yake zuwarmini da wata irin sufa yayi anfani da ni ba imani yana gamawa ya wawatsa kafafuwana ya goge gaba daya najasar nan ya shafe a fuskarsa harda jini jinin nan ya side hannayen nasa ya fice
Anna a wannan ranar.kafin gari ya waye sau tara yana zuwar mini
Mariama ce ta dauko kwan fitilar sosai ta haska wajen kafafuwan Fatimata, ruwa ne ke yawo wanda ya saka Mariama cewa" Anna ruwan nan kuma na menene?
Fatimata ta ce" fitsarina ne ba ruwa ba, haka fitsari ke zubar mini bama na sannin yana binna
Anna ta fashe da wani irin kuka kafin ta ture kan Fatimata ta mike ta yi dakin yaren da sauri hannayenta duka biyu saman kanta, *YoYo, YoYon fitsari Fatimata ke yi*!
A wannan rana yanda suka ga rana haka suka ga dare inda suka cure gaba dayansu waje guda ba mai yiwa yar uwarta magana sai dai suna bin juna da ido , nan Mariama ta mike ta dauko wata leda baka baba ta shinfida ta dauko zani ta shinfida ta kallo yan uwanta ta ce" ke fatimata taso ki kwonta saman nan, ke Agaishat(Bak'a) tafi wajen Anna, kuma ku taso mu kwonta dare na tafiya kar safiya ta yi mana a nan
A hankali ta samu ta lalaba ta hau, suma du suka samu waje suka kwonkwonta ba dan zasu samu yin bacin ba, sun dai yi zuru ne domin Fatimata bata gama basu labarin irin ukubar da ta sha ba aka ga fitsari na binta hakan kuwa ya tayarwa da Annar hankali bata ma tsaya ta ji sauran zancen ba
Anna ce duke kanta kasa ta kai sujada tana ta sheka kuka ta ce" ALLAH ka san wacece ni, kai ka halice ni, ya Allah ina cikin jarabawarka tun daga yannayin aurena har zuwa yau, na rasa me ke daure da ni da wannan mutumin ainahi Allahna idan ba a cikin sallah ba bana iya tuna wacece ni, menene tarihina, ina da yan uwa ko haka nake ni daya? Bana son a yi min maganar ko wa ya kawo min zancen zan nuna bacin raina ne, Allah yayana, ka bayannar sauran, wa.inda basu da lafia ya Allah ka basu lafia, wa.inda yake niyar aurarwa dan samun abin duniya Idan da alkhairi a cikin auren ka tabatarda, idan kuwa ba alkhairi bane Allah kai ka yi shi ka hana, ka hana ya Allah Allah sannan ka yaye min duhun dake cinkushe min ganina
Ta jima tana kai kukanta wajen Allah kafin take mikewa ta yi tahiya ta salamce ta dora adu.a tana ta yawaita istigfari domin ba abinda ke saurin yaye kunci irinta
Da safe tana tashi ta dauki sansani (tabar buzaye) a cikin nata ta matsa a bakinta ta yane jikinta ta buga safiya ta fice a gidan
Zugum suke ba mai yiwa dan uwansa magana har wajen karfe tara Anna bata dawo ba, Aba daman tun cikin daren nan ya fice basu san ina ya kwana ba sannan bai dawo ba, sun zubawa sarautar Allah ido ne kawai
A hankali Bak'a ta kali gorin tsofo, ta mayar ta kule a harshen zaninta a ranta take ayanna bawan Allah ko a wani hali yake? Ko an dauko masa ruwa? Tabas yana cikin damuwar rashin ganninta yau har za.a kwana biyu, sai dai ba zata iya fita ta bar gidansu a wannan halin ba, a hankali ta rike goron ta ce" sofo ina nan lafiata klau, ka ga na saya maka goro ma kar ka damu ina nan tafe wajenka
..........inna Anna ta tafi?????
Gyara kimtsi, mai zamani dan sarki jikan sarki, Buzu jinnin sarauta, yaro mai zamani, taka lafia bijimin sarki, taka lafiya gagara gasa, kai ne na uku baban Rabatima, ka shigo a hankali yarima, taka sanu sanu sarkina
,
Kirarin da jakadiya ke yi masa kennan tunda ya tunkaro dakin mahaifiyarsa,
dan dakatawa ya yi har ta yi gyaran murya kafin yake saka kai da salama a bakinsa
Dago kanta ta yi tana murmushi ta amsa shi, a hankali ya karasa yana wata irin tafiya idan ya daga kafa daya kafin ya daga dayar sai ya jima
Dukawa ya yi har kasa kansa kasa ya ce" ta gode Anna, ta gode Amy (Wato mahaifiyar Wardugu aminiyar matar sarki....da Amy suke kiranta bisa umarnin mahaifiyarsu,)
Murmushi take sakar masa kafin ta ce" oh son tashi mana, amynka ce fa ko dan ka daina zuwa wajena ne?
Yana murmushi ya mike ya zauna saman kushin dake wajen cikin nustuwa suka shiga gaisawa da harsen freinsh domin ita ce kawai yaren da zasu yi su jima suna hira cikib gane abinda suke fadawa juna
Dan jim ya biyo baya kafin yake cewa " Amy ya labarin Oga ne? Na yi na yi ya siyar min da wata mota aman da yake yan rigimar a kansa cewa yayi aa motar ba ta yara bace, ki ji fa Amy
Dariya suka saka gaba dayansu, Ayya ta ce" Wardugu, Wardugu baya jin magana Aghali, sai hakuri da murdaden halayen Wardugu
Mahaifiyar Aghali matar sarki ta ce" Kawata, wai ina labarin aban Wardugu ne? Ni kam ina mamakin lamarinku, kawai daga wannan dan laifin?
Ayya ta dago tana kallonta, a ranta ta ayanna ban ga laifinki ba, ku baku dauki haka a matsayin laifi ba,
A fili kuwa ta ce" manta
Murmushi Mahaifiyar Aghali ta yi, Ayya akoy mulki wannan da gidan sarauta take da an ji jiki domin mace ce mai mulki da isa, ga jan aji, da yake an dauko hirar da bata so daga haka ta katse hirar ta mike tana yi masu salama dan tana son shiga ciki ta kirayi number Wardugu rabonta da shi tunfa suka karaso jiya ba shi ba labarinsa
...........rashin Comment ne kawai zai saka ni daukan matakin siyar da novel din nan ko na tsayar da shi, 😊
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
9⃣
Ayya na zuwa dakin da aka sauketa zauna ta jinginar da bayanta jikin kujera ta daga kanta sama,
Ta jima tana tunani, kafin take sauke ajiyar Zuciya a fili ta ce " *MARAHUT*, ina ka shiga? Ka san komai ka tarwatsa rayuwarmu, Marahut ina tausaya maka sai dai mutuncina darajata ba zan yarda ka zubda mini ba! Ka zabi wancen rayuwar ko? Ba komai ka je sannu duniya zata koya maka hankali,
Ranta ne ta ji yana suya, yama aka yi ta tabo mata wannan mikin, ta sani da gangan ta tuno mata da maganar domin ta fi kowa sannin abinda ya faru, ita kadai sai Wardugu suka san takamaimai abinda ya faru aman zatana tuno mata da shi , ita so take sai ta yi hakuri bata san ta rufe babinsa ba kuma ko da jaraba sai ya saketa dan bata fatan idan ta mutu ya kasance shine alwalin gawarta (Toh fa😳 tubawa akoy zuciya)
Aghali, dan me ba zaka kara aure ba? Matanka biyu yarka daya mace sai matan daki , ko a cikinsu har yanzu ba wace ta samu ciki bayan ina kula da irin zubin da ake maka ana canzawa du wace ta kwana biyu, ko dai baka zuwa inda suken da gaske? Domin na ji kishin kishin cewar wannan matar taka ta shanye min kai,
Mahaifiyar magajin sarki ce ke fada kan ya ki karo aure bayan tana son ya tara yaya
Murmushi ya yi ya ce " zan kara aure, ki kwontar da hankalinki,
Ajiyar zuciya ta sauke kafin take miko masa yar akwati tana murmushi ta ce" ka ga Amynka ta kawowa wannan mumunar ( wato yarsa jikarta)
Hannu ya saka ya bude ya gani, sarka ne da yan kunaye na zinari masu kyau sosai kirar yara, murmushi ya yi ya ce" zata je ta gaisheta sannan ta yi godiya........ wannan kennan
Sai da ta bude lulubarta suka ga mace ce bayan ta fada masu ita mahaifiyar Gaishat ce , suka je suka shaidawa sarki ya bada izinin a shigar da ita bangaren Gaishat din yana mamakin zuwanta da fadawa zuciyarsa ba lafia ba domin shekara kusan takwas da aurensu bata taba takowa ko aiko da kannen Gaishat din ba duda tana yarta ta fari, itama bata wani zuwa gidan du ta takura rayuwarta da tsoronsa ta mayar da kanta ta daki duda kuwa irin yanda yake daukaka martabarta fiye da iyayen yayansa
Tana shiga dakin ta nemi waje nan kasa ta zauna ta sada kanta , da kujeru da komai aman ta fi fanewa zama a kasan nan
Da sauri ta fito jin sakon Sarki wai mamanta ce ta zo
Tana fitowa ta karaso da gudu ta riko hannayenta a rikice ta ce" Anna lafia? Anna wa ya mutu? Anna na shiga uku me yake damunki? Anna me ke faruwa? Me aka maki Anna? Anna.....
Shiiiiit anna ta fada tana dora yatsarta saman leben Gaishat, itama tana kare mata kallo, yarinyar bata wani karu ba a jikinta na da, sai dan girma daga fuska da ta kara, duda jikinta bai nuna alamar wahala ba aman tana da rama, kanta daure ,
Kunyar Gaishat din ta ji ta kamata, dole ta rikice domin bata taba zuwa alkhairi ko tashin hankali ba, itace ma ke yin kokari idan ta san Abansu baya gari ta leko a tsaitsaye ta koma shima ba wani zantawa suke sai dai su bi junna da ita
Tunani ta afka shin fada mata zata yi ko kawai ta yi shiru ta juya
A hankali Gaishat ta dago habar mamanta, dara daran idannuwanta na gado ta saka cikin nata ta ce" Anna, me ke damunki? Ki fada mani kin ji? In sha Allah ko bani da maganin damuwarki zan taya ki da adu.a
Anna ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Gaishat, Algabitt ne....ya samarwa su Mariama mazajen aure wa.inda bama a niger din suke ba, kin san bani da labari tghmass ita a niger din ma aka bayar da ita, jiya Fatimata ta dawo, mariama fatimata ta kamu da cutar rashin rike fitsari , kin san ba maganinsa a kauye sai asibiti, baki ga fatimata ba, ta dawo wata iri,
Ga irin tsanar Agaishat (BAK'A) , ya sako yarinyar a gaba tamkar ya kasheta dan ya san gardawan da yake zuwa da su dan zaben mata ba zasu zabeta ba, shi ya sa nake kara barinta da datinta, mai yiwuwa ita ta tsira daga muguwar rayuwar da yake saka mini yaya
Shiru ta yi kanta sade tana gursheken kuka daga ita har Gaishat din,
Ajiyar zuciya Gaishat ta sauke ta ce" Anna zan zo gidan kin ji? Sai mu samo abinda ya samu mu samu shiga asibitin
Ido Anna ta zaro ta ce" ta yaya zaki fita Gaishat?
Gaishat ta yi murmushi ta ce" Anna, ki daina damuwa da damuwata, ni na dorawa kaina, tabas Aba ya yi auren dole da mutumin da bana so, mai mulkin garina aman shi mutumen jira yake in nuna bukatata a wani abin jiki na rawa yake yi min ko menene , bana tunanin fita zata zama damuwa tsakanina da shi
Anna ta sauke ajiyar zuciya, ta dago habar Gaishat ta ce" me ya sa toh ba zaki kyautata masa ki kontar da hankalinki ba? Shekarunnan ba fa kwanaki bane, ya ci ace kin zubar da komai kun fuskanci juna, ke Allah ya taimake ki kina cikin konciyar hankali kar ki bijirewa Allah mana
Gaishat ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Anna na kara nade jikinta da fuskarta wato dai tafia zata yi, ita ba zata ki su dawama a nan suna hira da mahaifiyarta ba
Tana ji tana gani Anna ta yi mata salama ta fice a gidan tana fatan kar ta hadu da wani a kusan gidan yarta ta fari , haka kawai take jin kunyar haka .......
Da dare, bayan ya gama salama da kowa ya nufo dakin mai motsa zuciyarsa, ya sani ne ta san sarai itace da shi aman taga damar ya tarar da ta rufe kofarta
Ga mamakinsa yana taba kofar ya tarar da ita a bude,
Turawa ya yi a hankali ya shiga da salama a bakinsa
Kanta ta dago duda tana jin kunya , ta yi kokari ta amsa salamarsa cikin nutsuwa tana dubansa
Da sauri ya karasa inda take zaune, da alama har wanka ta yi, na menene? Taba jikinta ya fara yi hankalinsa a dan tashe ya ce" GAISHAT baki da lafia ne? Me ke damun ki?
Dan bakinta ta turo, kafin take dauke hannun nasa ta kara turo bakin, murya a matukar kasalance ta ce" me ya sa ka zabi aurena ta hanyar baiwa Abanna damar ya ci gaba da tafka tsiya a cikin garinka?
Dakatawa ya yi, ya yi tsai yana kallonta, a hankali ya rungumeta a jikinsa ya ce" ba dai za.a yafe min ba du irin hakurin da nake bayarwa? Ki gane dan adam nake mai cike da izgili da sabo a doron kasa,
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" ina so ka bar ni na je gida
Da sauri ya zabura ya cikata yana kallonta, muryarsa na rawa rawa ya ce" zaki tafi ki barni kennan? Yau kin fitar abinda ke cikinki shine zaki yi nesa da ni? Me yasa ba zaki yi mini adalci ba? Ina sane da du ranar da zan zo gare ki sai kin sha madaciya dan kar ki haihu da ni, na so daukan mataki a kanki aman bana iyawa Gaishat, ki yi mini adalci mana
Dora dan yatsarta ta yi saman lebensa jajaji abinka da jan buzu ruwan sarauta ko na kauye dawisu ne, ta ce" zama da kai yanzu na fara, ina son zuwa gidanmu ne dan kanwata ba lafia, muna son kaita asibiti, ka bani dama da ikon da zan yi bajinta a lamarin
Ajiyar zuciya ya sauke, ya rungumeta sosai har kamar ta yi ihun zafi, ya mikar da ita yana kallonta ya shiga warware lafayar da ta yane jikinta yanai mata kallon maita, haka ya idasa shigar da ita uwar dakanta cike da zumudi, wa ya isa in ba ita ba? Ita kadai yake tardowa har dakinta, hajia Gaishat mai sarkin garin *TIMIYA*
Kamar yanda ya yi alkawari haka ya bayar da rakumi har goma, ya bata kudi masu yawa ya lamunce mata zuwa gari dan kai kanwarta asibiti inda gari ya dauka ana ta lale lale gimbiya ta karbi soyayar sarkinsu, abinka da kauye har yar salah aka yi ta murnar hakan ...................
0 Comments