Nurul kalbi 1-3


 NURUL kALBI )) page


*⃣1⃣*⃣  

      Na 

Ummee ( matar manya )   

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 


Bissmilahir rahamaninr rahim  dukan yabo da godiya suntabata ga Allah subhanahu wata Allah dayabani ikon kammala littafin  ((( ARASHIN SANI )))) lpy  sanan kuma nakawomaku wanan sabon littafin  mesuna (((( NURUL KALBI )))  Allah yasa zaifadakar Yakuma nishadantar daku  kudai kubiyo Yar gidan Nasir  masu karatu kusha lbr😍😍😍😍😍


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Ina godiya sosai gareku fans dina bazan manta dakuba musamman Feenat Umar abdullah, meenat Usman , Khadija almustafa Nana asmy  rukky isah

Allah yabar Kauna   🌺😍


Wanan littafin kagaggene kirkiranayi ba gsky gane Idan kuma yayi kamada rayuwar wani/wata tokuyi hkr 

 

Gargadi banyarda wani kowata yajuyamin labariba idan kuma akayi to wallahi banyafeba  Allah ya is a akiyaye 

 

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺





Cikin sauri ta,salami

 me adaidaitanda ya ajiyeta  kyakyawar budurwace tasaya tana karewa dankareren gidan  dake gabanta kallo wanan gida haka , tafada ahankali takalli number gidan taga lallai itace takarasa wurim gate din gidan ta kwankwasa megadi yazo yabude 


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


Ahankali cikin zakakkar muryarta tace 

Sannu baba yace yauwa yarnan. Tace, baba Dan Allah megidan yanaciki  yace E yanaciki tace to shinakenema kozan iya ganinshi  yace  E bisimillah yabata hanya tashiga ciki  saida tayi tafiya sosai mainisa a harabar gidan koina shikeshukene abun mekayartarwa ahankali tashiga falon gidan nantaga dukiya inda take magana tanata mamakin da akoi masu wanan kudin aduniya amma talaka ke kwana baiciba ,hankalinta tadawo lokacinda taji motsi a Sama nanta daga kanta tagawani iron bene mekayatarwa tahau benen, tasaya tanakaloj kofofin  wata kofar tanufa wanda takejin motsin ahankali tatura kyauren cikin mamaki kuma kyauren ya bude tadaga cotein din a hankali 


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

Takuramai ido yana tsaye dawata Yar yarinya ahanunsa da Alamar yarinya bata da rai domin duk jikinta jinine da kayanta  shikuwa saurayin da alamar tashin hankali a fuskarsa  saigirgiza yarinyar yake yanacewa ke, ke, ke,  waya kawokinan  ,itakuwa budurwar tananan tsaye tundatazo tasaita cermera , tana recording tanadauka kuma tanata kuka tagoge kwalla nan tadauko waya takira oganta sukayi Yar maganarda konima banjitaba 😅barena daukomana masu karatu  ba,afi minti 3-4 ba saigakuwa yansanda sunshigo dakin itama tashigo saikukatake tamakasa magana sainunasa take da yasa tana girgiza kai   Can cikin dasashiyar miryarta medadin sauraro tace ........... 


Kuyi hakuri da wanan sisters   huh😯.Typing wahala Allah hani ikon cimaku gaba 

Kudai kubiyoni domin jin yarda zata kaya a wanan labarin. Hmmm akace wasa farin girki

😍


By matar manya 

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

[10/25, 10:16 PM] ‪+234 813 163 8664‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


((NURUL KALBI)) page 

     

           2⃣

     Na 

Ummee ( matar many a)

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺



Wanan page nakine my  Hauwa (g) Hamza nagode sosai sisters dakaramin karfin guiwarda kuke

Allah bar Kauna

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺





Tace gashinan, gashinan reping dinta  yayi fa 😭 sai kuka take Dan sandan guda kuma yace, relax now  inafatan kinyi record vidio koh tadagamasa kai kawai domin kukan yaci karfinta,      shikuwa saurayin saikalonta yake ya kafamata mayatatun idanunsa yanamata kalon tuhuma ,hmmmm yafurzarda wani iska abakinsa ,saiyanxu yagane wato sharri akeson yimasa  ,,OK ,, kawai yafada ,daya dan sandanne 

Yace , u are under arrest, hankali kwance yakale Dan sandan Sama da kasa yace well  bcos of what "? Sabida munkamaka da kayiwa yarinya fyade, Dan sandan yabashi amsa ido ya kafe Dan sandan sanan yamaida kalonsa kan yarinyar  yakaleta shekeke kamar yaga kashi yace, wanan abine zanyiwa fyade wanan tafada yana nuna yarinyar da hannunsa injime intsinci me  mtss yaimasu tsaki , dayan dan sandanne yataba yarinyar cikik razana, yace oga batada raifa.. Ogan ma yarazana  yace babbar magana, 


Ahankali cikin rarrashi ogan  yace, amm pls yallabai kayi hakuri kabamu yadin kai cikin muryar fada yace mikake nufi  yaje kayi hakuri muje office pls hakadai da sauran yan sandan dukafinga rarrashinsa  dakyar ya amince " yace sujirashi a falo yanazuwa zaishirya domin dagashi sai towel domin time dinda yafito wankane abunyagaru nan yazabgawa budurwanan harara sukajuya sukafita ,yabude katuwar wardrope dinshi wace cike take dakayanshi sadaddu yaciro wata shadda galilah fara me tsadar faske yasa tasha aiki  sanan ya kafa hula akanshi yafesa tsadadun turarukanshi da ke kan mirror  yafito das dashi yaje falon yasamesu sukace to muje ko yallabai yace cikin voice dinsa medadin sauraro ,a Motana zanje  itakuwa badurwanan tace zata wuce sukace to saisun nemeta suna godiya tazo wucewa ta gabanshi yazabgamata harara yasa kafansa ta tadiyeta Allah ya agajeta data fadi awurin sannu sanni murya kasa tace banyafeba mugu kawai 😏 ta murguda baki tayi Sauri ta wuce shima yayi  gaba suka bishi a baya sai (((head Quarter)))


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺  

       FARKON LABARI    

Alhaji Umar abudullahi hamshakin me kuddine agarin sokoto yanxu hakama shine govenan daya lashe zaben kujerar gwamna jahar sokoto yanada mata daya,itace, hajiya Maryam sunyi auren soyayyene shida ita kuma auren saurayi da budurwa  mahaifinta babban malamine agarin sokoto wato malam siddi inda iyayensu suke aminai ne an an yaganta yakuji yanasanta itama haka har Allah yakaisu lokacin auren su  bayan shekara 5 da aurensu Allah baibata haihuwaba inda hajiya maryam keshan sanguma agun kannan Alhaji  Umar su,biyu hajiya Amina kebiwa alhaji Umar da mijinta Alhaji Sahabi yaranta biyu mata data tai aure days kuma karatu take  itakuwa hajiya umaima itace autarsu yaranta 3 mata duk sunyi aure   

Kanan alhaji Umar sun tsanguwami hajiya maryam bata haihuwa itakuwa sai dai tashiga daki tadinga kuka batagajiya da hakuri domin tasan komi Na Allah ne  ranar kwasam hajiya Maryam tatashi ba lpy akakira Dr yazo tadubata gwajin farko akagano  cikinda kejikinta Dan wata biyu murna kam ba cewa komi da iyayensu sune kam gaba dasu hajiya amina cikin yasata laulayi sosai shiyasa sai mahafiyar  alhaji Umar tadawo gidan takanas Dan takula da ita har cikinta ya isa haihuwa Allah tasauketa lapiya tasantalo danta namiji  bafilatanin sak fari das, das, murna ba a Mgn su hajiya amina  aka yi barka nagani da fada komai dai tubarkallah ranan suna yaro yaci sunan kakansa wato mahaifin alhaji Umar (Muhammad farid) amma sunmasa alkunya sunakiransa da ( UNAIS)     

Unais yataso cikin gata da kulawa hardai lokacinda sukaji haihuwa shiru suka kara kulawa da yatonsu da shikadai Allah yabasu dangi sunamatukar kaunarsa  shekararsa 4 shida mahaifiyarshi suka wuce American a can akasakashi primary, secondary, dakuma university dinsa indayakaranta medicine yazama babban Dr daga baya kuma  yajiyana Sha awar (spot) yaje sport international school yakaranta inda yafi maida  hankali da sport  American susuka rikeshi domin sunaso yayimasu aiki domin hazakarshi  da basirarshi jajircewa  sanan daga baya Momy tadawo    shikuwa saidai yazo Hutu ko yaziyarcesu ya koma  unais dai farine sosai tas tas,  ga hanci kamar Kara's dogo har baka  idanunusa farere tas Kamar xasu fado kasa da pink lips dinshi  gashi dogone da fadaden girjinshi  kailomaida yaji kamar( Mijina😛 kai ai mijikama yaninka unais😅😛)  idan sunacikin filin buga ball bamazakatana banbanta su dashiba kamar badan Nigeria ba amininsa daya shine imam makotane da gidansu imam kuma mahaifansu amijanjujane shiyasa suma  yaran sukashaku da juna imam su biyune agun mahaifansu shine babba sanan kanwarsa Amina tatasone da son unais tuntana yarinya tatabatar takamu da mahaukaciyar kaunarsa takaiga gayawa tafadawa yayanta yaji Dadi sosai domin yasan   zasuci arziki lokacinda yayiwa oga unais maganar  ranshi yabaci sosai saida sukayi rigima domin unais yace bayason Amina ran imam yabaci  tunranar yakeda wani kulli a zuciyarshi.......

 

To fans anan zansaya domin wlh banajij Dadi sosai  nahuta  zanci gaba inasha Allah

Nagode sosai masoyana masu karamin karfij guiwa dawayanda suka kirani dama wayanda hasukiranba Allah yabar Kauna  


 

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 

By matar manya  ummy baby😍♥♠😘😘🖐

[10/25, 10:16 PM] ‪+234 813 163 8664‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

(((NURUL KALBI ))) page 

        3⃣

Na Ummy matar manya 

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


Wannan page nakine my Aisha Lawal Sani Allah yabar Kauna  wayanda sukamin text nafatan samun saukina dama wayanda suka kirsni ngd sosai 



Didectet to my family

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

       🌺🌺🌺🌺

           🌺🌺

             🌺




Unais ganin yadena mishi maganar yasa yasaki fuska  sukacigama da al amuransu amma azuciyar imam tsanace tsansa ta unais din kuma yadau Alwashin saiya masa abunda  hazaitaba mantawashiba 🤔 kunjifa masu karatu  unais ,yayi futunshi lafiya ya koma american yacigaba da aikinshi  saidai""" da akoi abunda kedamunsa Na ciwon kara domin unais matsanan ciyar Sha awa kegarai kunsan abunda ya hada da lafiyayen namijin duniya😘  sparm ne yatararmashi sosai amara inda indan abun yataso saiya fita haiyacinshi saidai yafarka yaganshi hospital likiticin american sunata bashi shawarar yai aure ko yanemi wata amma yace shikam Sam bayanxu zai aureba kuma hazai zina ba  akwana atashi unais yakara zama namijin duniya isashshe  ga farin jiji da haiba ga kwarjini naira ta zauna gashi Dan governor, yanxu haka shekarunsa bazasuwuce 31 yrs ba momynshi taitai yayi aure amma yakiyayi   da akoi wani zuwanda yayi hutu aikuwa yan mazan suka motsa mararshi tayita ciwo harya fita haiyacisa  saiga Momy tashigo dakin aikuwa cikin azama takira Dady akadaukeshi sai hospital nan likitoci suka dukufa akanshi da kyar akasamu yafarfado akamai allurar baci Dr ne da Dady da Momy a office din Dr yace,your exelency gaskiya akoi Marsala sosai  cikin gidima Momy race kamarya Dr yace, danku yanacikin critical condition domin tabukatar mace ayi masa aure yatara sperm a mararshi kuma Idan ba ayi hattaraba zai iya daskarewa yasa bazai iya haihuwa ba aikuwa nan Momy takalalo ido yahanashi haihuwa a a wlh tafada, cikin rudu takali Dady shikuwa yadagamata kai.sukayi salama da Dr suka shiga daki da unaissss yake  yanata baci  yayi fiyau dashi duk yarame  nan Momy tayayita shafamai kai Dady kuwa cewa,yayi insha Allah gobe gobenan zandaurama aure   Momy tazabura tace kamar Yy dawa kuma yaceda Rukaiyya Yar Amina kanwata Momy tace tirkashi wlh wlh bazaiyiwuba karyane wlh kasan abunda kakefada kuwa amina wacce ko sunana tasana Dady yace nasani kuma nagama Mgn nayanke hukunci bisaga yarona ya mutu 

Bayan 3h unais yafarka yaiy wanka ya ci abunci Dady yaga son dinshi yaji dama sosai nan Dady kefadamai abunda Dr yafada dakuma hukuncin da yayanke aikuwa nan sukaga tashin hnkali domin unais kukayasaka masu yana rokin Dady yayi masa rai amma Dady yadage yagama magana momykam cikin fushi tabar asibitin dadare aka,salami unais nan dady yagama shaidawa kowa harda iyayensuma sunkuwa yi Murna dasa albarka itakuwa hajiya Amina harda rawa Rukaiyya kam ba acewa komi dimin tadade tana son unais mahaifiyarta kawaitagayawa aikuwa harda kukan murna nan akafarashirn biki 

👫

Momy kuwa ta kafe batayardaba da kyar da kyar Dady yashawo kanta ta amince amma ba ason rantaba domin momy akoi zuciya sosaifa 

Garinawayewa aka halaci daurin auren 

🌺♥🌺♥.  

Muhammad farid ( unais). Umar

Da Rukaiyya Sahabi 

Ranar akasha shagalin biki Na manya dadare aka kai Rukaiya gidan unais da dadu yabashi dangareren gidane nagani da fada  dake Sama road 

Bayan kowa ya watse amarya taijiran ango amma shiru abuda  batassniba unais yana dakinshi harma yayi bacci  dole ta hakura hakanan ta kwanta da safe Momy ta aikomasu break fast amma koganinshi bataibaa haryafita tadaije  dakinshi ta gyaramai tafito  

Rukaiyya zaman hakuri take a gidan unais domin tayi tayi kissa amma ko kwalar rigarsa kullun cukin adu a take Allah ya juyomata da mijinta 

Sannu sannu kuwa unais yafara jin tausayinta amma tsayinta Na kaunarsa sannu sannu yana sakar mata fuska  amma bayajin sonta ko das azuciyarsa  

Watarana taje gida  ananne take labartawa mahaifiyarta duk abunda kefaru a gidan aurenta  hajiya Amina tabata wani turare tace yau dadre tashafa taje dakinsa tasha mamaki ai kuwa Rukaiyya cikin zakuwa tadawo gida bayan  tagama abunci yashigo agajiye yaiyi wanka yatafi masallaci bayan yashigo yacemata yunwa yakeji takawomai food dinshi dakinshi  cikin rawar jiki taje daki tashafe ko INA da turare taje tadauko abincin takaima  bayan sungama ne tadauke warmers din tadawo tazauna kusadashi ai kuwa yanajin kamshin  yabiduk yasusuce yafita haiyacinshi itakuwa sai kissing dinshi take tana shashshafashi tanawani bankarewa dukkajinsu sai numfashi suke fitarwa da sauri da sauri sunajun bugun zuciyoyinsu   intakaice makudai  sunraya wanan Daren domin  sun murji junansu a wanan Daren cikin farik ciki   haka rayuwarsu tacigaba da tafiya cikin kula haryakaiga Rukaiyya cikine da ita Na wata biyar yana kulada ita sosai diminshi  baihada komi da cikinshi ba   itama kuwa tana kulada cikin sosai domin taga hard a darajar cikij takeji

Hajiya aminace magaifiyar Rukaiyya tazo inda Momy suna zaune hajiya Amina nabawa  Momy hakuri duk abunda taimata abaya Momy tace bakomi kimi yawuce nandai tawuni sunata fira hajiya Amina tace idan Rukaiyya ta haihu   idan macece kar akawomata ita domin zata kwacemata miji 😂  amma idan miji ne tanaso akawomata Momy tace a a nizan rike Mijina 😂😅. Suka dinga raha suna dariya sai 6 pm sukayi sallama takoma gidanta   

Cikin Rukaiyya yashiga watana tara haihuwa  yau ko gobe  unais kuwa kayan  baby Dana mamanshi komaina bukadai harwan ba doleba yasiyo😂  Rukaiyya nayawan mai complen din kulum tana yawan mafarkin ta haihu amma tarasu watace zata raini baby da unais zata kuladashi  unais  saidai kawai yayi dariya  yace ba gaskebane mafarkine  


Imam kuwa zasu hadu atafa ayi fira da dariya amma aranshi tunani yake yazai cimma burinshi yaraba unais da da jindadin rayuwa 

Ranar ranar kwasam ranar wata alhamis Rukaiya tatashi da nakuda gashi unais bayanan  yafita unguwa daktar ta  rarrafa tadauki waya rakirashi yanadagawa yaji muryarra yasanda  da akoi matsala  cikin kinti 3 ya iso  kodaya iso harjini ya kwacemata sai bleeding take yadauketa yasa mota sai hospital likitoci suka dukufa kanta domin shiyamakasa tabaka komi saikuwa taiyii wani irin nishi saiga baby boy yafado me kyau sak abbanshi saikukayake ( yarrr) (inyar) ai kuwa da gudu yazo yadauki yaron yanajijjigashi yadaga  waya yakirasu    Momy ya sanardasu yamaida hankalinshi kan Rukaiyya yayi murmushi yace Allah yamiki Albarka Rukaiyya yasakamiki  da aljannah,cikin karfin hali tace, ameen  yace kigayamin mikikeso namiki  kamar yadda kikamin haka tace adu arka kawai nakenema dimin nasan  ni lokacina yayi nantake tafara wasu irin kalamai masu kashe jiki dama najima INA mafarkin banice zanrayu da kai da yaronmu ba  INA mafarkin zakasami wata wace tafini data kula dakai da yaronmu  cikin zubarda kwallah tace   dukomon da kyautarda Allah yamana nagani jiki asanyaye ya doramata ajiki ta  ganshi   baby boy  fari tas me kama da abbanshi kamar kakitayi tace Allah ya maka Albaka yarona  ta subbaceshi yadaukeshi saiga su Momy sun iso  sunmata sannu suka karbi baby saimurna suke da sabon miji ahankali  tafara sabhatu tafita haiyacinta nasan  bazamtashiba ummana kiyafemin sumomy sai kuka suke  lailaha illallah Muhammad rasulilah sallallahu alaihi wasallam shknn shknn kawai ummanta tafada tana kuka momyce tai karfin halin shafe Rukaiyya  tarufeta Tanata nanata innalillahi ganinkawai sukayi unais yafadi sume  bude idonshi yayi yaganshi kwance a gadon asibiti alhaji Sahabi nagefenshi  yadafe kanshi dake saramai bayan anshiryata aka kaita gidan gasky   ranar bakwai akayi sadakar bakwai da zanene suna antaru sosai kamar ba wayansa akayiwa mutuwaba yaro   yaci sunan Dady wato Umar amma sunamasa alkunya da (ARFAT)  tun lokacin da 1yrs Momy kematsamasa da yayi aure amma yaki kuma ankoma Yar gidan jiya (wato ciwon mararshi yadawo ) arfat nada  2 yrs yakika American domin hutunshi ya kare   Yajima sosai  kafin yadawo kuma likacim cikar burin imam neyayi  dimin iman yadau Alkarik wanna zuwan shine Na karshe bayan driver yadsukoshi air port yawuce dashi gidansu nanfa akaha soyayyar  da da mahaifi arfat namatukar kaunar dadyshi Dady da Momy sunata masu dariya arfat yace cikim gwarancinsa Na yarimta "dad,dani zanje" waifa  yananufim shima zaibishi  su momy sunata mashi dariya Dady yace nima kuwa Dana  huta duk kabi kakakemin Mata tadainayidani dariya duk sukayi unais, yace ai dole Dady momy taga saurayi yaro sanon jini matashi dadu oooo wakakenufi anan Dady yace oya  friend zonan a gwada muga wazai buge wani  sukadinga dariya nan unais yamike yace to momy bari,naje gida nadanyi fresh up inhuta nagaji  yakali arfat yace oya son lest go ,arfat, yace, no Dady fraind  yace zamuje ice- cream koh yafada tareda kallon Dady  alamar tmby dady,yace yes  unais yace to vari naje nikam  , Momy sainadawo  Momy da Dady sukakasa Allah yakiyaye hanya  yakai bakin kofa arfat yace Dady chocolate yace olrigh  bye yawuce 


🌺🌺🌺🌺♥♥♥ 


Wacece HALEEMATU


Hohoho wasa farin girki 


To masu karatu anan zaj tsaya saimun hadu a page 4⃣ domin jin cigaban labarin


By matar manya Ummy baby bye🖐😘



Post a Comment

0 Comments