MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
www.maryamahmadpaki.blogspot.com
Facebook: Kainuwa Writers Association
*GAISUWAR TAKU CE*
_Noorul-jannarh (Marubuciyar Detective Noor)_
_Maman Usy_
_Faeedaabdullahi1_
_Habiba Rabo_
_Hajiyar Allah_
_Surar da take karantar da cewa duka abubuwan duniya suna da dangantaka da junan su, dangantaka bayyananna ko ‘boyayya, kuma zumuntar sun a gudana gwargwadon dangantar su da juna ita ce Suratul Rum_
69-70
Tun da muka d’auki hanya banyi magana ba, Hajiyan Wagini ce ke jan yaya Faruk da hira jefi-jefi, yanayin shi na nuna ba dad’in hirar yake ji ba, kawai dauriya yake yi, alamun shi na nuna kamar bai da lafiya.
A haka muka ci gaba da tafiya, in ban da tunani ba abin da nake yi, Hajiya ita a dole fushi dani take yi shi yasa ba ta ja ni da hira ba.
Muna shiga Kaduna yaya Faruk ya wuce da mu gidan Abbu, in ban da gaba na da yake fad’uwa, ba abin da yake yi, da ina da hali da na ce ma yaya Faruk kar ya kaini gidan mu, ya fara kaini gidan su duk da nasan ba lallai ba ne in samu tarba daga gurin su Momi da Anisa, nasan Dadi ba zai canza min a fuska ba, sai dai ya min fad’a akan abin da na aikata, nasan ko da ba a cikin hayyaci na nake ba, ban isa in nemi wannan alfarmar daga gurin yaya Faruk ba, yanayin fuskar shi kad’ai tsoro yake bani, ga wani kwarjini da min da ban tunanin zan iya mishi magana.
Ina ganin yaya Faruk yayi horn, Malam Musa ne yazo ya bud’e mai gate d’in, nan na ji jiki na ya d’auki rawa, ga wani tsoro da fad’uwar gaba da had’u ya min dabaibayi a zuciya ta, duk wanda ya kalle ni a lokacin yasan ba na cikin natsuwa ta.
Parking yayi a ma’ajiyar adana motoci kana ya bud’e ma Hajiyan Wagini mota ta fito daga ciki.
Tafiya suka fara yi ba tare da sun damu da halin da nake ciki ba.
Cikin rashin k’arfin jiki na bud’e motar na fito, a lokacin na ji wasu zafafan hawaye na zubo min, ni kaina a lokacin ba zan iya fad’ar dalilin hawayen nawa ba.
Tsayawa na yi a jikin motar na kasa tafiya, jiki na ne ya min nauyi wanda ya haddasa min rashin k’arfin motsa k’afa ta.
Yaya Faruk ne ya lura da rashin tawowa ta, hakan yasa ya juyo ya watsa min wani kallo mai isar da gargad’i.
Ganin kallon da ya min yasa na ji tsoro ya k’ara shiga ta, ban san lokacin da na fara taka k’afa ta na fara tafiya ba, duk kuwa da yadda k’afa ta tayi min nauyi.
Sallama su Hajiyan Wagini suka yi suka shiga cikin falo.
Ummu ce ta amsa musu sallamar cikin walwala.
Yaya Khalil ne ya gaishe su kana Ummu ta gaishe da Hajiyan Wagini.
Yaya Faruk sun gaisa da Ummu cikin girmama wa.
Ummu da yaya Khalil ne ta tare da tambayar shi ya k’arfin jikin shi.
Amsa mata yayi da ya ji sauk’i.
Sai a lokacin na tabbatar da zargi na akan rashin lafiyar yaya Faruk saboda yadda yanayin shi ya nuna hakan.
Yaya Khalil ne cikin tsokana ya kalli Hajiyan wagini ya ce "Matar ke ce a garin mu, gwara da Allah ya kawo ki, dan nayi kewar ki".
Cikin dariya Hajiya ta ce "Ja’iri ni matsa can, in da ka yi kewa ta ai da kaje in da nake".
Dariya yayi yace "Hajiya ba lokaci ne shi yasa".
"Ai na ga agogo ma a aiki" Hajiya ta fad’a cikin dariya.
Suna cikin hirar ne Abbu ya fito daga shashen shi ya shigo main parlour.
Murmushi ya saki lokacin da yaga Hajiya.
Cikin farin ciki suka gaisa na irin tsakanin Uwa da d’anta.
"Ina wuni Abbu" yaya Faruk ya furta cikin sanyin murya.
"Lafiya lau Faruk, ya jikin naka".
"Da sauk’i Abbu".
"Allah ya k’ara sauk’i" Abbu ya fad’a cikin kulawa.
"Amin Abbu".
Hajiya ce ta ce "Wai Ibrahim me ya samu Sojan ne na ji kuna ta tambayar shi ya jiki, rashin lafiya yayi kenan sosai ban sani ba?".
Abbu ya amsa mata da cewa "Yayi fama da rashin lafiya ne, amma yanzu da alama jikin da sauk’i".
Juyowa tayi ta kalli yaya Faruk ta ce "Hala ciwon naka ba zai rasa nasaba da abin da Fatima ta maka ba ko, dan nasan har da dalilin ta kayi wannan rashin lafiyar, ai ba ta isa ta bijire ma wannan auren ba ta sa ka a wani hali, sai ta aure ka ko ba ta so, sai dai in mutuwa za tayi k’arewar rashin son ka kenan".
"Hajiya, Allah ne ya d’aura min ciwo ba ruwan Fatima" yaya Faruk ya fad’a cikin sanyin murya.
Cikin Hasala Hajiya ta ce "Ai dama haka za ka ce, tun da kai ba son laifin ta kake yi ba, ka riga ka makance a son ta".
Sai a lokacin Hajiya ta kalli falon ta ga ba na ciki.
Ni kuwa duk wannan abin da yake faruwa ina can jikin k’ofa a ra’be ba tare da na shigo ba, in ba ka lura da gurin ba, ba lallai kasan ina tsaye a gurin ba .
Hajiya ce ta hango ni a tsaye a bakin kofa kana ta ce "Au Fatima can kika tsaya, ai dole ne ki kasa shigowa tun da ba ki da gaskiya" Hajiya ta fad’a.
Duk wanda yake d’akin maida hankalin shi bakin k’ofa yayi jin Hajiya ta ambaci suna na, sai a lokacin suka lura da ni.
Ummu tun da muka had’a ido da ita ta min wani kallo, hakan yasa na k’ara jin jiki na yayi sanyi.
Falon ne ya d’auki shiru kamar ba kowa a ciki.
Abbu ne ya kalli Hajiya, fuskar shi cike da ‘bacin rai ya ce "Hajiya ina kika samo wannan yarinyar".
"Guri na ta tawo, ashe gudun hijira ta yi ta tawo guri tana ganin za ta samu tallafi na, sai da Soja yazo yake fad’a min ai ba a san da zuwan ta ba, Soja ya sanar dani halin da ake ciki, ni kuma na ce ta sha ruwan k’arya ta ce ba za ta auri Soja ba".
Yaya Khalil ne ya mik’e ya tawo in da nake, saboda rashin kuzari a jiki na yasa na kasa motsawa.
Hannu na ya rik’o ya shigo da ni cikin falon.
Guri na samu na zauna a can gefe, ni kaina na tsargu da zama na a falon saboda laifin da nayi.
Ummu wacce takaicin abin da na aikaita wanda dashi take kwana take tashi a ranta yasa ta taso ta fara duka na.
Ba wanda ya hana Ummu duka na saboda haushin abin da na aikata, sai Hajiya ce ta wa Ummu magana akan ta daina duka na, addu’a ce magani ba duka ba.
In ban da shashshek’ar kuka ba abin da nake yi, yau ni kaina nasan na daku a gurin Ummu.
Abbu ko saboda ‘bacin ran dake damun shi kasa magana yayi, sai bi na yake yi da ido kawai.
Kuka na naci gaba da yi ba mai lallashi na, nasan dama ba wanda zai kula ni tun da suna jin haushin abin da na yi, ni kaina nasan ban kyauta ba.
Hajiya ce ta kau da shirun da cewa "Ibrahim ka kira min yayan ka ayi komai a gaban shi, dalilin zuwa na kenan, na ga alamar Fatima so take yi tayi fito na fito da kowa akan wannan maganar".
Waya yayi ma Dadi ya sanar dashi zuwan Hajiyan Wagini da sak’on neman shi da take yi.
Ba a d’au wani lokaci ba sai ga Dadi da Ummu da Anisa sun zo.
Zama suka yi aka gaggaisa kafin Hajiya ta d’aura da cewa "Isuhu".
Dadi cikin ladabi ya amsa "Na’am Hajiya".
Hajiya ta ci gaba da cewa "Abin da yasa Na ce Ibrahim ya kira min kai shine akan maganar Soja da Fatima, naji k’udirin da Fatima take son aiwatarwa akan bijire ma auran, tun da ta na so ta nuna mana ita ‘yar zamani ce ta hanyar bijire maganar da aka riga aka gama ta, lokaci kawai ake jira, rana d’aya ta bad’a wa idon ta k’asa ta nuna bare yafi d’an uwanta, saboda haka na yanke hukunci Fatima ba ta isa ta auri wani ba in ba Soja ba".
Dadi ne ya ce "Amma Hajiya….".
Hajiya tayi saurin kar’ban maganar da cewa "Isuhu bana buk’atar jin wani bayani in dai ba goyon baya za ka bayar ba akan maganar auran".
Falon ya d’auki shiru, kowa da irin tunanin da yake yi a ransa.
Yaya Faruk ne ya nisa kana ya katse shirun da cewa "Hajiya ki yi hak’uri da hukuncin da na yanke kamar yadda na fad’a miki a baya, nasan kina son auran mu da Fatima, amma Allah bai k’addara ba, tun da Fatima ta nuna tana da wanda take so, ba ni take so ba, ina ganin Hajiya gwara a barta ta auri za’bin ranta dan guje ma wata matsalar da ka iya tasowa in aka yi auran, Hajiya bazan iya auran yarinya da ta mallaka ma wani zuciyar ta ba, ina neman afuwar ku, ni na hak’ura da auran Fatima" ya k’arasa maganar a hankali.
Hajiya cikin fad’a ta ce "Wai kai Soja kana da hankali kuwa, akan ka faranta ma Fatima shine kai ka yarda ka sa kan ka a cikin damuwa, ita har ta isa ta ce ba ta son ka, to tayi k’arya dan bantan uban ta, ko kai ka hak’ura ni ban hak’ura ba, dole ne sai an yi wannan auran, sai dai in an yi auran ta d’au wuk’a ta yayyanka naman ka gunduwa-gunduwa saboda k’in ka da take yi".
Abbu duk wannan maganganun da ake yi bai yi magana ba sai a yanzu ya kalli Hajiya ya ce "Hajiya ki kwantar da hankalin ki, ko da a ce kowa ya hak’ura da wannan auran ni sai na d’aura shi, Fatima ta sa min wani bak’in ciki a cikin zuciya ta da banyi zato ba, da nayi niyyar in zuba mata ido tayi duk abin da ta yanke ma kanta saboda yadda ta fifita saurayi akan mu iyayen ta, sai nayi wani tunanin akan in na k’yale ta hakan na nuna kamar ita ta haife mu kenan, saboda haka nima na ce Fatima ba ta da miji in ba Faruk ba in dai na isa da ita".
Ba maganar da ta d’aga min hankali sama da ta Abbu, nasan yanzu ban da wata hanya da zan bi in samu in cimma muradina, hakan na nufin in rabu da Dr kenan.
Hawaye ne ya fara zuba a idanu na, ni kaina na fara tausaya ma kaina halin da zan shiga matuk’ar ban samu Dr ba a matsayin miji.
Yaya Faruk cikin sanyin jiki ya ce "Abbu na gode da kulawar ku gare ni, sai dai ina neman alfarma Abbu kayi hak’uri ku bar Fatima ta auri wanda take so, hakan zai fi wa kowa kwanciyar hankali akan a zo ayi abin da za ayi danasani daga baya".
Ummu da Momi kuwa ba wanda ya samu k’arfin yin magana, kowa da abin da yake kissamawa a ranshi.
Dadi cikin ladabi ya kalli Hajiya ya ce "Hajiya ba wai zan ja da maganar ki ba ne ko hukuncin da kika yanke, sai dai nima ina neman alfarmar ku akan ki duba wannan al’amarin, ku bari Fatima ta auri shi wannan Dr tun da har ta nuna shi take so, ni kaina zanyi farin ciki idan Fatima ta auri Faruk tunda duk d’aya ne a gurin mu, su duka ‘ya’yan mu ne, tun da auren yazo da tangard’a, hak’urin shi yafi".
Haka Daddy yaci gaba da lallashin Hajiya da kawo mata hujjoji akan illar yin auran, da alama jikin Hajiya ya fara yin sanyin da maganganun da Dadi yake fad’a mata.
D’aura zancen yayi da cewa "Hajiya ki yi hak’uri kar ki sa ma kan ki damuwa, mu yadda hakan Allah ya k’adar ta".
Hajiya ce ta ce "Yanzu Isuhu kana nufin kenan dai Soja ya hak’ura da Fatiman, shi kenan tun da kana ganin hakan yafi, Allah shi ma ya kawo mishi ta gari wacce za taso shi" ta k’arasa maganar tare da fashewa da kuka.
"Amin dai Hajiya, ki yi hak’uri Hajiya, mu rok’i Allah yasa hakan yasa shi yafi zama alkairi a gurin su" Dadi ya fad’a cikin sanyin murya.
Da k’yar aka samu aka lallashi Hajiya tayi shiru.
Momi wanda takaicin hukuncin abin da Dadi ya yanke yasa ta kalli Dadi ta ce "Yanzu Alhaji an ma yaron nan adalci kenan, kana ganin halin da ya shiga, shine yanzu za ka yanke wannan hukun…".
Katse ta yayi da cewa "Rukaiyya ba na so ki sa bakin ki a cikin wannan maganar, hukuncin da kika ga na yanke, to ina fatan hakan ya sa yafi zama alkhairi da kuma samun maslaha ba tare da an shiga hakk’in wani ba a cikin su".
Abbu ne ya kalli Dadi cikin taushin harshe ya ce "Kayi hak’uri yaya, ba wai zan yi jayayya da hukuncin da ka yanke ba ne, sai dai kamar yadda na fad’a a farko ban sauya ba, Fatima ba ta da wani miji sai Faruk".
Cikin d’aure fuska Dadi yayi ya ce "Yanzu na gano hujjar ka Ibrahim, kana so ka nuna min ban da iko akan Fatima kenan tun da har zan zartar da hukunci akanta ka nuna k’in amincewar ka".
Abbu cikin kwantar da murya ya ce "Kayi hak’uri yaya, ba haka nake nufi ba, Fatima ‘yar ka ce duniya da lahira, ka isa ka zartar da kowane hukunci akan ta, sai dai in aka yi haka ba a kyauta ma Faruk ba duk da shi ya ce ya hak’ura".
Dadi k’ara tamke fuska yayi ya ce "Indai har na isa in yanke ma Fatima hukunci, na ba ta damar kawo shi wannan Dr da take so in d’aura musu aure".
Abbu wanda bak’in ciki ya taru ya mishi dabaibayi a ranshi yasa ya kasa yi ma Dadi musu, shi kad’ai yasan halin da yake ciki a yanzu.
Dadi ne ya ce "Ka bani wannan damar Ibrahim" ya k’arasa maganar da tambayar sa.
Cikin takaici Abbu ya ce "Duk hukuncin da ka yanke daidai ne yaya".
Dadi ne ya kalle ni ya ce "Fatimah!".
"Na’am Dadi" na amsa a hankali.
"D’ago ki kalle ni kin ji Fatimah".
Kasa bin Umarnin shi nayi, wata kunyar Dadi ce ta kama ni, duk wannan abun da yake yi akai na dan ya samar min farin ciki ne, amma shine ni na bad’a ma ido na k’asa ta hanyar bijire ma auran d’anshi, ai da kunya in iya had’a ido dashi.
Bai damu da d’agowa ta ba yaci gaba da cewa "Fatima, za mu baki za’bin ki na auran shi wannan Dr ba wai dan guduwar da kika yi yasa za muyi haka ba, za mu baki za’bin ki ne saboda ke ‘ya mace ce, bazan so a tauye miki hakk’in ki ba, saboda haka ki turo min shi Dr d’in mu yi magana dashi, sannan zan yi bincike akan shi".
Wani irin dad’i ne mara fasaltuwa ya saukar min a lokacin jin cewa Dadi ya amince, nasan komai zai zo da sauk’i, sai dai a halin da nake ciki ba zai bani damar nuna farin ciki na a fili ba, sannan nasan duk wani bincike da zai yi akan Dr ba zai samu wani aibun shi ba, dan haka ban damu da binciken da zai yi akan shi ba.
Ci gaba yayi da cewa ‘Fatima kin yi kuskure, ba ki kyauta ba akan abin da kika yi, ke mace ce, bai kamata akan d’a namiji ki bar gidan ku ki tafi wani gurin ba duk da gurin Hajiyar mu kika je, saboda ita mace abu kad’an ne yake zubar mata da mutunci a idanun mutane ba, kin ga hakan da kika yi kin sa iyayen ki da duk wani makusancin ki a cikin halin damuwa na rashin sanin in da kika tafi, da ni kika zo ki ka sama ki ka min bayani zan fahimce ki, bai kamata ki d’au zugar zuciyar ki ba ki aiwatar da k’udirin ki, yin hakan babban kuskure ne, kar ki sake makamancin haka kin ji Fatima".
Kalamen da Dadi yayi amfani dasu wajen yi min nasiha ne yasa jiki na yayi sanyi, hak’ik’a Dadi mutum ne mai karamci, ba kowa ba ne zai iya nuna dattakun da yayi ba, k’aunar Dadi ce ta k’ara shiga raina na yadda ya d’auke ni kamar ‘yar shi, nima bazan gaji da d’aukar shi a matsayin mahaifi ba.
Wasu zafafan hawaye ne suka fara ambaliya a idanu na.
"Abbu na gode, insha Allah ba zan sake ba".
"Yawwa Fatima haka ake so".
Abbu da Ummu na kalla wanda yanayin su kad’ai ya nuna ba su ji dad’in hukuncin da Dadi ya yanke ba, ba yadda za suyi ne.
A hankali na furta "Ummu da Abbu kuyi hak’uri akan abin da nayi, bazan sake ba".
Cikin su ba wanda ya min magana, da alama har yau ba su sauka daga fushin da suke yi da ni ba.
Sai a yanzu muka had’a ido da yaya Khalil, wani irin kallo yake watsa min mai nuna ‘bacin ran da yake ciki da takaici na da ya cika shi.
Anisa ma kallo na kawai take yi na mamakin abin da nayi da kuma haushin abin da nayi.
Abbu ne ya ce "Yaya na amince da wannan maganar saboda ka riga kasa baki, sai dai nima akwai wani sharad’i da zan gindaya ma Fatima, ina rok’on ka yaya da kar ka hana ni".
Dadi ne kalle shi ya ce "Wani sharad’i ne wannan Ibrahim".
Abbu ya juyo da kallon shi gare ni ya ce "Fatima kin ce dai Dr ki ke so ko?" ya k’arasa maganar yana jiran jin amsa ta.
Shiru na yin a kasa bashi amsar tambayar da ya min.
Tsawa ya daka min wacce ta razana ni ya ce "Ba dake nake yi ba kika min shiru".
Cikin rawar murya na ce "Eh…Abbu".
Takaici ne ya k’ara kama Abbun jin yadda ta amsa da ta amince amma sai bai nuna ba.
Shiru yayi yana mamakin wai Fatima ce a gaban shi take son yin jayayya dashi saboda soyayya.
"Good tun da kin ce Eh, ni ma na amince sai dai a bisa sharad’in duk wata matsala da za ta taso tsakanin ki da shi Dr d’in kar ki tunkaro nan gidan ko wajen ‘yan uwa na da sunan za ki kawo mana matsalar ki, idan kin amince shi kenan, kamar yadda aka sa lokacin bikin ba za a d’aga ba".
Kowa a d’akin ni ya zuba ma ido dan jin amsar da zan bayar.
Nima kaina wannan maganar ta min tsauri a guri na, yanzu za’bi ya rage gare ni.
Abbu ne ya katse min tunani na da cewa "Ke na ke jira Fatima".
"Na amince Abbu" na furta a hankali.
Ido muka had’a da yaya Faruk, wani irin kallo ya watsa min da na fassara shi da kallon tsana yake min, idanun shi sun kad’a sun yi ja alamar ‘bacin rai, kallon ya ci gaba da jefo min dashi, hakan yasa na kasa jure kallon na sunkuyar da kaina.
Hajiya ce ta fashe da kuka tace "Fatima ke wace irin shed’aniyar yarinya ce, yanzu mahaifin ki ya fad’a miki wannan maganar, amma saboda ke kin isa da kan ki, so ya riga ya rufe miki idanu, shine kika amince da sharad’in da ya fad’a miki, yanzu akan d’a namiji kika za’bi ki ‘ba ta wa mahaifin ki rai, Fatima ki gyara kuskuren ki tun kan ki zo ki fara nadama a lokacin da ba za tayi miki amfani ba".
Abbu ne ya kalli Hajiyan Wagini ya ce "Hajiya ki k’yale ta tun da ta ga wannan hukuncin ya mata ai shi kenan".
Yaya Faruk tashi yayi ya bar falon, a yadda yake jin zuciyar shi na k’issima mishi abubuwa marasa kyau akai na, yana ganin barin shi d’akin shi yafi, ko da yake cewa ya hak’ura da ni k’arfin hali kawai yake yi, ba wai dan zuciyar shi ta lafa da ciwon da take mai akan so na, sai dai ya k’udurta a ranshi ya hak’ura dani kamar yadda ya furta, zai ci gaba da rok’on Allah akan ya bashi juriyar hak’uri da ni.
Zazza’bi ne yaji yana niyar kama shi, hakan yasa ya shiga motar shi ya tafi gida.
Dadi ne ya kalle ni ya ce "Fatima sai ki fad’a ma Dr ina jiran shi".
"To Dadi zan fad’a mai".
Abbu ne ya kalle ni cike da ‘bacin rai ya ce "Zaman me ki ke yi tun da an miki abin da kike so, ina ganin sai ki tashi ki bamu guri ko".
Jiki a sanyaye na tashi na tafi d’aki na.
Yaya Khalil ma tashi yayi ya bar falon ya tafi shashin shi.
Anisa ma bin shi tayi a baya ta nufi d’aki na.
Su Dadi ne suka ci gaba da tattaunawa akan maganar, Dadi ne yaci gaba da ba kowa hak’uri akan hukuncin da ya yanke da kuma dalilin shi da yasa shi yin hakan, ba laifi su Abbu sun samu sauk’i akan halin da suke ciki.
San da na shiga d’aki na nemi guri na zauna, na rasa abin da yake min dad’i a rayuwa ta, yau gashi an amince min in auri Dr, sai dai hanyar da aka bi gurin amince min ne yazo da akasi, hakan ya hana ni jin farin ciki a raina.
Duk yadda nake so muyi aure da Dr, zan so da amincewar iyaye na, sai gashi da alama Ummu da Abbu ba su nuna farin cikin su da hakan ba, a yadda na lura ma a family d’in ba wanda yake bani goyon baya akan aure na da Dr.
Zan so a ce na samu wanda ya fahimce ni akan son da nake ma Dr ba yana nufin ina k’in yaya Faruk ba ne, ina mishi so ne irin na ‘yan uwantaka, amma nasan hakan ba zai samu ba.
Hawayen tausayin kaina ne ya zubo min a ido na masu zafi, yanzu nasan sai nayi hak’uri da abin da zan dinga gani a family akan za’ben Dr da nayi.
Tuno da kallon da yaya Faruk yake min na ji na k’ara tausaya ma kaina, ban ga laifin shi ba dan ya nuna ‘bacin ranshi akan abin da na mai, da zai bani dama da na bashi hak’uri akan ya yafe min, dan nasan yana min kallo a matsayin wacce ta ci amanar shi, sai dai kash! Na san ba zan samu wannan damar a gurin shi ba.
Hawaye ne ya ci gaba da zubowa a ido na, saboda halin da nake ciki ban damu da in goge su ba.
Anisa ce ta yi sallama ta shigo d’akin, in b aka lura da motsin bakin ta ba baza kace magana tayi ba.
Amsa mata sallamar nayi na sunkuyar da kaina, dan na san ba lallai ba ne ta min magana saboda haushi na da take ji.
Kallo na take yi kamar wacce take son gano wani abu.
Ido muka had’a ta watsa min harara, ban damu da hararar da ta min ba dan nasan tayi hakan ne cikin ‘bacin rai.
"Fatima kenan, ina ganin zubar da hawaye ba naki ba ne a yanzu, ina ganin da tanadar hawayen kika yi ki ka ajiye dan akwai lokacin da zaki zubar da hawaye a lokacin da hakan ba zai miki amfani ba, yau kamata ya yi ya zama ranar farin ciki a gare ki tun da kin samu cikar burin ki, Fatima ba na zo in miki nasiha ba ne dan nasan ba d’auka za ki yi ba tun da kin yi nisa ba kya jin kira, Fatima sai kin yi nadamar abin da kika aikata duk daren dad’e wa, ki rubuta ki ajiye wannan maganar da na fad’a miki"
Tun da ta fad’a min wannan zaffafan maganganun ba ta sake ce min komai ba, sai ma danna wayar ta da taci gaba da yi.
Maganganun da Anisa ta fad’a min sun min zafi a cikin zuciya ta, sai dai ni kaina nayi mamaki da na kasa maida mata martanin maganganun da ta fad’a min, na alak’anta hakan da halin da nake ciki.
Shiru d’akin ya d’auka kamar ba kowa a cikin, kowa da irin kalar tunanin da yake yi.
K’arshe ma Anisa tashi tayi ta bar d’akin.
Kiran Dr ne ya shigo cikin waya ta.
Cikin sanyi jiki na d’auki wayar, mun d’au tsawon lokaci muna waya dashi kafin na sanar dashi halin da ake ciki da kiran da Dadi yake mai.
Bayan gama tattaunawar su Dadi ne suka yi sallama suka tafi.
A can ‘bangaren Dr kuwa tun san da na sanar dashi amincewar su Abbu yaji farin ciki ya kama shi, bai yi zaton amincewar su Abbu cikin sauk’i haka ba, lallai yarda da irin son da nake mai tun da har na iya jajircewa aka fasa aure na yaya Faruk.
Gida ya wuce dan ya sanar da Dadi da Momi halin da ake ciki.
San da ya shiga falon ne ya tarar da su Hanan da Farida suna kallo.
Sannu da zuwa suka mishi kana ya tambaye su Momi.
Sun sanar da shi tana d’aki.
San da ya shiga d’akin ya same ta hakimce akan kujera.
Guri ya samu ya zauna kana ya mata sannu da gida.
Kallon shi tayi kana ta ce "Yau ba patients ne a asibiti na ga ka dawo gida da wuri".
Murmushi yayi ya ce "lafiya lau Momi, dama mun yi waya da Zarah ne take sanar dani an ce in turo, kuma parent d’in ta sun ce ba za su d’aga bikin ba, shine nace bari in sanar daku".
Momi ce ta ce "Au daman ba ka hak’ura da yarinyar nan, ina ce ka ce da d’an uwan ta za a had’a ta auran".
"Eh Momi, Zaran ce ta nuna ni take so, shine shi d’an uwanta yace ya hak’ura".
Ta’be baki Momi tayi kana ta ce ‘Ni tun farko nafi maka sha’awar Meemat yarinyar Hajiya Suwaiba amma ka na ce sai wannan yarinyar".
Cikin shagwa’ba ya ce "Kai Momi, wannan Meemat d’in da ba ta da tarbiyya za ki ce in aura, ni nafi son Zarah ta".
Momi ce taci gaba da cewa "Yanzu suna nufin a before two weeks suke nufin mu gama shirye-shiryen mu na biki, bayan kai kan ka kasan yadda muke so muyi organizing d’in bikin ka idan yazo, ina ganin sai an k’ara mana time dan ina bikin ka ya zama special…".
Da sauri ya katse ta da cewa "Plss Momi don’t say that, da kyar fa aka shawo kan su suka yarda ita Zaran ta aure ni, yanzu idan aka nemi favour d’in su akan su k’ara mana time zai iya jawowa in rasa ta, tun da dai an fi k’arfin komai ina ganin a bi su a yadda suke so".
‘‘Ai shi kenan tun da ka na ce sai Zaran, in Dadin ku ya dawo zan sanar dashi halin da ake ciki".
"Thanks Momi, bari in je in d’an huta" yana gama fad’ar haka ya fita daga d’akin.
*MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞
🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
www.maryamahmadpaki.blogspot.com
Facebook: Kainuwa Writers Association
*SAK'ON GAISUWA*
_Ba zan gaji da Mik’a godiya ta da fatan alkhairi ga masoya wannan Littafin, ban da abin ce muku na yadda ku ke bibiyar wannan labarin, fatana darasin da ke ciki Allah yasa ayi amfani dashi_
_'Yar Mutan Paki na marhabin da duk wanda yake bibiyar littattafai na_
*QUESTION OF THE DAY*
_Ya sunan matar da ta d’auki takobi ta kare Manzon Allah (S.A.W) a lokacin da mazaje suka guje daga gare shi, akwai san da annabi ya ce mata "Tambaye ni abin da kike so? sai ta ce masa "Ina rok’on ka kasancewa mak’ociyar ka a Aljanna da son ka a duniya da son ka a lahira_
71-72
*WANENE DR ABUBUAKAR SADIK MUHAMMAD?*
Dr Sadik d’a ne ga Arc Alhaji Muhammad, haifaffen d’an garin Kaduna ne, mahaifin su shahararren d’an gwal ne, ya karanci ‘bangaren zane-zane, mahaifiyar su Haj Hauwa lecturer ce a Open University, su hud’u ne a gurin iyayen su.
Dr Sadik suna zaune ne a Unguwar Dosa.
Dr Sadik shi ne babba a gurin iyayen su, daga shi sai Hauwa (Hanan) wacce taci sunan mahaifiyar su, tana karanta Socio-logy, tana 300 level a Kasu, daga ita sai Farida da take 100 level a Open University, daga ita sai autan su Ahmad, yana primary 4 ne a school d’in su.
Dr Sadik yayi karatun shi a ABU Zaria in da ya karanci medicine, yanzu haka yana aiki ne a cikin asibitin Kaduna Polythecnic, sannan yana aiki a wasu asibitocin idan buk’atar hakan ta taso.
Gidan su Sadik wata irin rayuwa ake yi ta ‘yan boko da kuma ‘yanci, babu mai matsa ma wani akan abin da yake so, akwai freedom ta ‘bangaren iyayen, hakan yasa su ma yaren su ka taso da wannan d’abi’ar.
A cikin su Farida ce ba ta cika d’aukan rayuwa da zafi ba, ba ta d’aura ma kanta social life ba, shi yasa su ke samun sa’bani da Hanan akan banbancin ra’ayin su.
Duk da yadda mahiafin su ke basu ‘yancin yin duk abin da suke so, hakan bai hana wani lokacin in sun yi ba daidai ba ya musu fad’a.
Dr mutum ne da bai cika son hayaniya ba sannan shi mai ji da kanshi ne, yana tafiyar da rayuwar shi akan turawa.
Wannan shine tak’aitaccen tarihin Dr Sadik..
San da yaya Faruk ya koma gida, d’akin shi ya wuce ya kwanta, jin zuciyar shi yake yi tana mishi zafi, ga k’irjin shi da yake ji ya mishi nauyi, ya san hakan ba zai rasa nasaba da ciwon rabuwa da ni ba.
Yana k’ok’arin yaga ya cire ni a ranshi, a yadda yake jin son ta a ranshi, yasan hakan ba mai sauk’i ba ne a gurin shi cire ni a lokaci d’aya a cikin zuciyar shi, zai ci gaba da add’u’a akan Allah yasa komai yazo mishi cikin sauk’i.
Haka ya ci gaba da zama a d’akin, ciwon k’irjin na k’ara matsa mai, sai da ya d’auki lokaci kafin yaji k’irjin ya daina mishi ciwo.
Tashi yayi ya watsa ruwa ya canza kayan jikin shi kana ya fito main parlour ya zauna ya kunna Tv dan ya rage ma kan shi tunani.
A haka su Momi su ka dawo suka same shi, sun ji dad’in yadda su ka ganshi yana kallo, duk da idan kayi duba da yanayin shi kasan yana cikin damuwa, dauriya kawai yake yi.
Zama suka yi suka dinga kwantar mishi da hankalali da mishi nasiha akan yarda da k’addara a duk yadda ta zo maka.
Yaji dad’in yadda su Momi suke nuna mishi kulawa, ba sa son ganin cikin damuwa, shi yasa shima yake k’ok’arin ganin ya kwantar da hankalin shi dan kar yasa su cikin damuwa duk da kuwa yanda yake jin rad’ad’in abin da na mishi a zuciyar shi.
Murmushi yayi ya ce "Zan yi amfani da shawarar ku Dadi da Momi, na gode da kulawar ku gare ni, addu’ar ku na ke buk’ata a ko wane lokaci, nasan ita ce nasara ta a dukkan lamura na".
Tausayin yaya Faruk ne ya kama shi, sun san dauriya yake yi a matsayin shi na jarumtaccen namiji, amma abin na mishi ciwo a zuciyar shi.
"Insha Allahu za mu ci gaba da maka addu’a Faruk, kullum kana cikin addu’ar mu, Allah biya maka buk’atun ka na alkhairi, ka dinga rage tunanin da kake yi ka ji Faruk, saboda gudun kamuwa da wata cutar, komai da ka ke gani muk’addari ne daga Allah" Dadi ya fad’a.
"Amin Abbu na gode, zan kiyaye insha Allah".
Momi ta ji dad’in yadda yaya Faruk yadda ya ke k’ok’arin ‘boye damuwar shi, hakan yasa ita ma taji damuwar da take ciki ta ragu.
"Allah ya za’ba maka abin da yafi alkhairi Faruk" Momi ta fad’a.
"Amin Momi" ya fad’a a hankali.
Anisa kuwa in ban da murmushi ba abin da take yi ganin yaya Faruk bai sa damuwa akan abin da na mishi ba.
Yaya Faruk ne ya kalli Anisa ya ce "Anisa ya aka yi ne, ko akwai abin da yake damun ki?" yaya Faruk ya tambaye ta.
Murmushi ta mayar masa kana ta ce "Ba komai yaya Faruk".
Haka suka zauna suka ci gaba da hira, wannan hirar da suka zauna suka yi tasa sun samu sauk’i na damuwar da suke ciki.
Tun bayan tafiyar su Dadi na kasa fito wa falo, nasan ko na fito bazan samu tarba ba ta kowane ‘bangare, yaya Khalil ma nasan tun kan matsala ta da yaya Faruk muka rage shiri dashi, daman shi kad’ai wanda a ko wane lokaci nake tunanin samun sauk’i.
Sallah kawai nake iya tashi in shiga band’aki in d’auro alwala in zo in yi sallah, ni kaina zaman ya ishe ni, ga yunwa da take addaba ta.
Haka na wuni a d’aki ba tare da kowa ya lek’o ni ba, hakan ya k’ara sa ni cikin damuwa.
Ganin zan cutu yasa nayi k’arfin halin fito wad an samar wa kaina abin da zan ci.
Ina fito wa na tarar da Hajiyan Wagini da Momi da Khalil suna hira, fitowa ta da suka ga nayi ne yasa su ka bi ni da ido.
Kitchen na wuce na d’ebo abinici na dawo d’aki na zauna na fara cin abinci na.
Bayan na gama ci abinci ne na ci gaba da zama na a d’aki, duk kuwa da yadda na takura da zaman d’akin, ina ganin hakan shi yafi min akan fito wa ta.
Ranar haka na zauna ni kad’ai a d’aki ba tare da kowa ya lek’o ni ya ga a wani hali nake ciki ba.
Hajiyan Wagini ma nasan ba shigo wa za tayi ba tun da tana fushi dani.
Yaya Aminu ma yazo saboda Abbu ya kira shi ya fad’a mishi na dawo, jin gurin Hajiyan Wagini na je yasa ya ji ya rage matakin da yayi niyar d’auka a kaina, yanda ya tashi a harzuk’e ya nufo d’aki na Abbu yasan har yau ranshi a ‘bace yake da abin da nayi.
Abbu ne ya kira shi ya dawo ya zauna ya fad’a mishi halin da ake ciki, da kuma sharad’in da ya gindaya min na amince.
Abbu ne ya ce ya k’yale ni tun da har na amince, ba buk’atar k’ara d’aukar mataki a kaina tun da na amince da sharad’in shi.
Washegari ina jin su Ummu nayin Breakfast, amma na kasa fitowa, ba kuma wanda ya aiko akan in fito in yi breakfast.
Nasan ‘bacin ran da nasa su ne yasa suka yi watsi da al’amari na, hakan kuwa ba k’aramin sa ni a damuwa zai yi ba.
Ummu kuwa rashin fitowa ta ba k’aramin damun ta yayi ba, tana tsoron kar wani ciwo yazo ya kama ni, sai dai idan ta tuno abin da nayi sai taji takaici na ya kama ta.
Tashi nayi na fito falon dan in gaishe dasu.
Ko da na fito ba wanda ya d’ago ya kalle ni, a hankali na k’arasa inda suke.
"Ina kwana Hajiyan Wagini".
Hajiya wacce haushin abin da nayi bai sake ta ba ta fara fad’a da cewa "Ina ruwan ki da kwana na har da za ki gaishe ni, ni yanzu na yafe gaisuwar ki, na bar ma waccan fitsararren Dr da yake sa ki rashin jin magana duk ki dinga mishi".
Wasu hawaye ne suka fara zubo min a idanuna, yadda Hajiyan Wagini ke min a yanzu kamar waccce ba ta san inda na fito ba, tun san da yaya Faruk ya je can Wagini ya fad’a mata abin da nayi take min fad’a, kamar ba ita ce muke wasa da dariya ba.
Sauri na yi na goge hawayen da suke zubo min, a lokacin muka had’a ido da yaya Khalil yayi saurin kau da idon shi.
A hankali na juya ga su Abbu da Ummu na ce "Barkan ku da Safiya Abbu da Ummu".
A tak’aice suka amsa min da "Lafiya".
Tun daga wannan amsawar da suka yi ba wanda ya sake kula ni.
Jiki na ba k’wari na kalli yaya Khalil na ce "Yaya Khalil ina kwana".
Duk yadda yake jin haushin abin da nayi ba zai iya jurar gani na a cikin wani yanayi ba, gashi a wajen su Ummu da Abbu ma duk fushi suke yi dani.
Sakar fuskar shi yayi kad’an ya amsa min da cewa "Lafiya lau Fatima, ya kike?".
Ganin yadda yaya Khalil ya amsa min yasa na d’an ji dad’i a raina.
"lafiya lau yaya Khalil".
Shima tun daga amsawar da yayi bai sake ce min komai ba, gajiya da zaman da nayi ne a falo ba tare da kowa ya kula ni ba yasa na tashi na koma d’aki.
Hirar su na dinga jiyowa jefi-jefi.
Haka suka gama breakfast kowa ya kama harkar gaban shi, falon shiru alamar ba kowa a ciki.
Tashi na yi na d’akko kayan breakfast nayi kalaci a d’aki na, yayin da na ci gaba da zaman kad’aici.
Ni kaina tunanin halin da na sa su Ummu na ‘bacin rai ya hana ni samun sukuni, dan haka zuciyata ta yi ta nusar dani akan in je in k’ara basu hak’uri ko na samu sassauci.
Da wannan shawarar ta zuciya ta na samu k’arfin gwiwar tunkarar Ummu.
Zuwa na yi na same ta a zaune a d’aki, da alama ita ma tayi zurfi a cikin tunanin da take yi ganin yadda tayi shiru.
Tun da nayi sallama na nemi guri na zauna.
Kallo na tayi ta amsa min sallamar ciki-ciki.
Shiru ne ya ratsa falon kana na kalli Ummu da fuska da ta koma kalar tausayi na ce "Ummu dan Allah ki yi hak’uri ke da Abbu abin da na muku, nasan ban kyauta ba, bazan sake kamanta tafiya wani gurin ba tare da izinin ku ba".
Duk wannan maganar da nayi Ummu bi na take yi da kallo, har yau takaici na ne ke cikin zuciyar ta.
Shirun da na ji Ummu tayi ne ya k’ara sanyayar min da jiki.
Can ta kau da shirun da cewa "Fatima ai ban zaci zaki iya zuwa k’i k’ara ba mu hak’uri ba a yadda yanzu ki ka canza halayen ki, kina yanke hukunci ne akan duk abin da zuciyar ki ta yanke miki ba tare da kin yi duban da hakan zai haifar miki ba, amma kar ki manta hausawa na cewa Son zuciya ‘bacin zuciya, duk wanda zai bari zuciyar shi ta dinga jagorantar shi yana tare da danasani, Fatima ban ta’ba tunanin za ki iya aikata abin da kika aikata ba na guduwa, wai yau ke Fatima akan d’a namiji kika za’bi tafiya wani guri dan guje ma auran da za a miki da d’an uwanki da bai wuce sauran kwanaki ba, me yasa tun farko ba ki nunar mishi da yayi hak’uri bashi kike so ba, sai da kika bari har ki ka had’u da wannan Dr sannan za ki fito da wata magana wai ba kya son Faruk, Fatima yadda na ke jin Faruk a raina kamar ni na haife shi haka nake jin shi saboda yadda nima ya d’auke ni kamar Mahaifiyar shi, yake k’okarin yi min biyayya da kyautata min, ta ya ba zan ji ciwon abin da kika yi mai ba, shi yasa ban ga laifin Hajiya Rukaiyya ba akan yadda ta d’auki zafi akan wannan maganar, ko ni ce aka yi ma d’a na haka dole zan ji zafi, tun da kin riga kin amince da sharad’in da Abbun ki ya gindaya miki shi kenan namu ido, sai dai ina so in tunasar dake wani abu da ba ki gama sani ba akan d’a namiji, duk yadda kika za’be shi dan ganin kin mik’a miki yardar shi, wataran zai iya baki kunya, ba kowane namiji ba ne yake sanin ka mishi halacci, sabida haka ni ba abin da kika min, wanda kika ma shine Faruk, tun da yace kuma ya hak’ura dake ina ganin magana ta riga ta k’are".
Tana gama fad’ar haka ta tashi ta barni a zaune.
Jiki a sanyaye na tashi na koma d’aki na tun da ban da wanda zan yi hira.
Da yamma yaya Aminu ya kawo su Anty Jidda su gaishe da Hajiyan Wagini, ina ji tana tambayar ina nake aka ce mata ina d’aki.
Tashi tayi ta tawo d’akin ta same ni kad’ai, kallo na kawai take yi kafin ta nemi guri ta zauna.
Gaishe ta nayi ta amsa min cikin fara’a.
Hira ta fara ja na dashi jefi-jefi kafin ta d’akko min zancen abin da nayi na tafiya wai gari ba tare da sanin su Abbu ba.
Nasiha ta min sosai akan abin da na aikata bai kamata ba, tare da nuna min illar hakan da nayi.
Ni kaina nasan ba kyauta ba, na kuma yi danasani akan haka.
Ta d’an dad’e a d’aki na kafin ta fito falo suka ci gaba da hira da su Hajiyan Wagini.
Abbu ma naje na same shi na k’ara bashi hak’uri akan abin da nayi, ya nuna min ‘bacin ranshi akan abin da na aikata, ya kuma nunar min da cewa shi yanzu ba ya fushi dani, tun da har na amince da sharad’in da ya gindaya min shi kenan.
Jin hakan da nayi yasa na samu kwanciyar hankali tun da shi da Ummu sun ce ba sa fushi dani, ni a gani na wannan sharad’in da Abbu ya gindaya min ba wata matsala ba ce, ina ganin ba za mu samu wata matsala ba da har zai sa in zo gida in fad’a yadda muke son junan mu, ta ‘bangaren ‘yan uwan Dr ina ganin mai zai had’a ni dasu tun da ina gida na suna gidan su.
Da wannan tunanin nake samun k’arfin gwiwa.
Dr Sadik ya kira ni ya sanar da ni zai je gidan su Dadi akan neman da yake mai kasancewar ya ta’ba sauke ni a gidan, hakan ya min dad’i dan nasan komai ya kusan zuwa k’arshe.
Sadik ya je ya samu Dadi inda ya mishi tarba mai kyau ba tare da ya nuna mishi wani abu a fuskar shi ba, ya mishi tambayoyi game da rayuwar shi, Sadik ya amsa mishi duk tambayoyin da Dadi ya mishi, ba laifi Dadi ya gamsu da amsoshin da ya bashi, dama ya riga ya sa an mishi bincike akan Sadik, ba a samu wani aibu ba akan labarin da aka mishi bincike, sai dai an sanar dashi gidan su irin rayuwar boko suke yin a ‘yanci, yana ganin wannan ba wata babbar matsala ba ce.
Da haka su kayi sallama dashi akan ya turo iyayen shi a yi magana tun da bikin bai wuce sati biyu ba.
Dr Sadik ya amsa mishi da in ya koma zai fad’a ma iyayen shi halin da ake ciki.
Nan suka yi sallama ya tafi tare da jin dad’in yadda Dadi ya sakar mishi fuska.
San da ya koma gida ya tarar da su Dadi a falo ana hira, guri ya nema ya zauna.
Dadi ne ya kalle shi cikin kulawa yace "Sadik ya aka yi ne na ga kamar your mood shows that you a happy".
Tsadadden murmushi yayi yace "Daga gurin parent d’in Zarah nake, sun ce in fad’a muku kuzo a gama maganar bikin mu da ita, tun da kwanakin da suke so a d’aura auren bai wuce two weeks ba".
Dadi ne yayi murmushi ya ce "That is a good news, Momin ku ta fad’a min halin da ake ciki, insha Allah zan ma Uncle d’in ku na Abuja magana da Alhaji Hamza sai ka mana jagora gidan su ita yarinyar".
Momi ce ta kalli Dadi ta ce "Amma in aka yi haka Alhaji ba a kyauta ba, yanzu kai Alhaji sai ka iya sanar da Alhaji Hamza yazo aje neman auren Sadik dashi alhalin kana ganin yadda Meema take son shi amma shi Sadik yak’i ba ta fuskar da za su yi soyayya, Hajiya Hadiza kullum cikin k’orafi take min akan Meema na son Sadik amma shi sai wahalar da ita yake yi, In ban da abin Sadik miye aibun ita Meema d’in da ba zai so ta ba, tana da kyan da duk namiji ya ganta zai so ta, gashi ta gama Degree d’in ta akan Economics, nasan yanzu in taji maganar auren da zai yi sai ta shiga cikin damuwa".
Dr Sadik ne ya kalli Momin shi ya ce "Momi na fad’a miki am not interesting with that girl, yarinyar da ba ta da tarbiyya da sagarta ya mata yawa, she is not my type" yana gama fad’ar haka ya tamke fuska.
Hanan ce ta kalli Dr Sadik cikin shagwa’ba ta ce "Haba yaya Sadik, miye laifin Meema da ka ke cewa she is not your type, Meema na so ka amma ban san me yasa yaya Sadik ba ka kula ta, ina ganin dan ba ka ga manyan mutanen da ke son ta ba, ko Momi…?" ta k’arashe maganar tana tambayar Momin su.
Cikin tsawa Dr Sadik ya katse da cewa "Will you stop that rubbish explanation or else you will face the consequences".
Tsawar da Dr Sadik ya ma Hanan ne yasa idon ta yayi narai-narai kamar me shirin yin kuka.
Farida duk wannan maganganun da ake yi ba ta ce komai ba, ita ma a nata ra’ayin ba ta son Dr Sadik ya auri Meema saboda wayewar ta tayi yawa.
Dadi cikin lallashi ya kalli Dr ya ce "Cool down Son, tun da ba ka son ta ina ganin shi kenan, ba za ma d’a na auren dole ba, ita Meeman ta hak’ura tun da Sadik d’in ba ya son ta".
Dr Sadik ne ya tashi ya bar falon ya nufi side d’in shi.
Dadi ya ci gaba da Momi fad’an akan ta daina matsa ma Dr akan sai ya so Meema, tun da yace yana da wacce yake so a k'yale shi.
Dr Sadik ya kira ni ya fad’a min yadda suka yi da Dadin Faruk da yadda ya mishi tarba mai kyau, ni kaina na ji dad’in hakan dan nasan Dadi bai da matsala, ya sanar dani Dadin su na nan zuwa gurin Dadin Faruk akan maganar bikin.
Yau ina zaune a falo ina kallon wani Nigerian film da aka sa a Afican Movie channel mai suna "My Affairs with Mother and Daughter" rabin hankali na yana ga kallon, rabin hankali na kuma yana ga tunanin halin da na tsinci kaina a yanzu.
Tunanin yadda yaya Khalil ba ya shiga harka ta shi ya fi tsaya min a rai, Anisa daman nasan ba kula ni za tayi ba ganin yadda ta d’auki fushi, rabon da muyi waya da ita tun kan in tafi Wagini.
Shawarar da na yanke shine in je in tunkari yaya Khalil in bashi hak’uri duk kuwa da fad’an da zai min, hakan zai sa in fi samun kwanciyar hankali.
Tashi nayi na lek’a ta slice window na hango motar shi a parking space shaidar yana gida kenan.
Side d’in shin a nufa nayi sallama.
Amsa min yayi ya danna laptop d’in dake kan centre table.
Tun da ya amsa min sallamar ya ci gaba da danna laptop d’in da yake yi ba tare da ya k’ara kallo na ba.
A hankali na k’arasa inda yake na zauna.
Shiru d’akin ya d’auka kamar ba kowa a ciki.
Kau da shirun nayi da kiran sunan shi a hankali "Yaya Khalil gurin ka na zo".
Har yanzu bai daina abin da yake yi ba na danna laptop d’in da yake yi ya ce "Ina jin ki".
"yaya Khalil kayi hak’uri da abin da na aikata, nasan ban kyauta muku ba, nima kaina nayi danasanin abin da na aikata, plss yaya ka tausaya min ka yafe min" Na k’arasa maganar murya ta na rawa.
Sai a lokacin ya d’ago ya kalle ni, shi kanshi yana tausaya min yadda yanzu kowa ba ya shiga harka ta da yadda nake takura kaina a d’aki ni kad’ai, sai dai in ya tuna tafiyar da nayi da kuma amincewar sharad’in Abbu da nayi a gaban mutane sai yaji ranshi ya k’ara ‘baci.
"Fatima ni ba ki min laifi ba, in ma kin min bai wuce yadda kika tafi wani gari ba tare da Sanin su Abbu ba, ki ka sa mutane a cikin damuwa da tunani, Fatima ko ba a fad’a miki ba, ke kan ki kinsan ba ki kyauta ba, bayan da kika dawo kiyi k’ok’arin ki faranta ma su Abbu da cewa kin hak’ura za ki auri yaya Faruk, sai ba ki yi haka ba, sai ma amincewa da kika yi akan sharad’in da ya gindaya miki, Fatima akan ki an fara samun rashin fahimta a family, hakan kuma ya faru ne duk a dalilin abin da kika yi, yanzu Momi tana jin haushin abin da kika yi ma Yaya Faruk, gashi yanzu ma Anisa ba ta saurara ta duk a dalilin tana jin haushin abin da kika yi ma d’an uwan ta, kuma ni ban ga laifin ta, ki kwatanta misali akan ni aka yi ma haka, nasan kema irin matakin da za ki d’auka kenan, tun da ke ba kya jin nasiha da fad’a shi kenan Fatima zan zuba miki ido in ga iya gudun ruwan ki, tun da an amince miki da wanda kike so wanda duk akan shi ne kike aikata hakan ai ina ganin ba ki da sauran wata matsala".
"Why me?" Na tambayi kaina.
"Me yasa mutane ba za su fahimce ni ba? me yasa suke ganin laifi na dan zuciyata ta za’bi Dr a matsayin abokin rayuwar ta?".
Wannan su ne tambayoyin da nayi ma kaina.
Idanuna ne suka cika da hawaye na ce "Yaya Khalil kayi hak’uri akan laifin da Anisa ta d’aura a kan ka, nasan tayi haka ne akan jin haushin abin da nayi ma yaya Faruk, banyi haka dan in ‘bata ma kowa rai ba, sai dan ba ma zuciya ra abin da take so, in ma za ta ga laifi, ni ya dace ta ga laifi na".
Murmushin yak’e yayi ya ce "Kar ki damu Fatima, Anisa ba irin ki ba ce, nasan duk yadda ta had’a dani wajen yin hukunci akan abin da kika yi ma yaya Faruk daga baya za ta fahimci abin da tayi bai dace ba, ita ba zuciyar ta ba ce take jagorar ta wajen aikata abu, ajizanci ne irin na d’an adam".
Maganar yaya Khalil ta yi min zafi, nasan magana ce ya fad’a min a hankalce mai isar da sak’o.
D’akin ne ya sake d’aukar shiru yayin da yaya Khalil ya ci gaba aikin da yake yi a laptop.
Jiki na ba k’wari na tashi na bar d’akin, yaya Khalil ko bi na yayi da kallo na takaicin rashin gaskiya da na k’i yi da kuma tausayi na.
Iyayen Dr Sadik sun je gurin Dadi akan maganar auren mu da Dr.
Kasancewar Dadi ya amshi numbar Dadin su Sadik lokacin da ya yi kiran shi, shima Dr ya amshi numbar Dadin, hakan ne yasa Dadin su Sadik ya fad’a ma Dadi ranar da za su zo ayi maganar bikin.
Ran da za su ne Dadi ya kira Abbu ya sanar dashi halin da ake ciki, hakan yasa Abbu ya shirya yaje dan yasan rashin zuwan shi zai sa Dadi ya mishi fad’a.
Haka Dadi ya kira wani kawun su na Wagini suka mishi bayani, ba da ‘bata lokaci ba shima ya tawo Kaduna.
Iyayen Dr Sadik sun je shi da Kawun Sadik d’in da Abokin shi Alhaji Hamza mahaifin Meema.
A ‘bangare na kuwa Dadi da Abbu da Kawu Lawan ne suka tarbi iyayen su Dadi.
Sun gaisa cikin mutunci da girmama juna kana su Dadin su Sadik suka nemar ma Dr Sadik aure na.
An yi duk abin da ya dace na shari’a da Al’ada kana aka tsayar da bikin a ranar da aka sa na auren mu da yaya Faruk wanda yayi daidai da saura kwana 10 kenan.
Sun ba da kud’in gaisuwar iyaye da kud’in sa rana, kana suka ba da Sadaki dubu d’ari.
Haka suka rabu cikin mutunci.
Abbu tun da ya dawo gida ya sanar da Ummu da Hajiyan Wagini da yaya Khali halin da ake ciki, San da yaya Aminu yazo ma Ummu ta sanar dashi tsayar da biki na da aka yi Dr.
Hajiyan Wagini ko san da Abbu ya fad’a mata maganar biki na da aka tsayar da Dr sai da tayi kuka akan rashin auran yaya Faruk da na k’i,
Ko su Abbu da Ummu sun fi son aure na da yaya Faruk, ganin hakan Allah ya k’adarta shi yasa suka hak’ura, sun barshi akan watak’ila Allah yayi ni ba matar yaya Faruk ba ce shi yasa hakan ya kasance.
Abbu ya shawarci Hajiyan Wagini da Ummu da su maida ma yaya Faruk akwatunan shi, sun yi na’am da wannan shawarar tashi.
Hakan yasa Abbu ya umarci yaya Khalil da ya kaisu Ummu gidan su Dadi a maida akwatunan.
San da suka je gidan ba su tarar da Dadi ba, Momi suka sama.
Yaya Khalil ne ya shigo da akwatunan.
Bayan an gaisa ne Hajiya ta kalli Momi ta ce "Rukaiyya, ina so kuyi ma Ibrahim da Aisha fahimta mai kyau, Akwatunan Soja ne aka kawo mishi abun shi tun da auren bai nufa dashi ba, sabida ga kayan nan ku ajiye mishi abin shi, hakk’in shi ne".
Momi duk da itama har yanzu ba ta daina jin haushin abin da nayi ma yaya Faruk ba, tana ganin bai kyautu su amshi kayan ba kasancewar duk d’aya ne.
Cikin ladabi ta Hajiyan Wagini ta ce "Hajiya ina ganin da ba ku dawo da kayan nan ba, dawo da kayan bai da wata fa’ida, dan Faruk bai auri Fatima ba sai a dawo da akwatunan, ina ganin ko da Faruk bai auri Fatima ba, zai iya ma Fatima kyauta tun da k’anwar shi ce, Alhaji ma in ya dawo ya ga kayan fad’a zai yi".
Ummu ce ta ce "Hajiya Rukaiya ki yi hak’uri ki bar kayan nan a gurin ki, rashin amsar kayan zai sa in za ta ko har yanzu kuna fushi da abin da Fatima ta yi ne".
Hajiyan Wagini ta kar’bi zancen da cewa "Wannan gaskiya ne abin da Aisha ta fad’a, rashin amsar kayan kamar yana nufin ba ku huce da abin da Fatima ta yi ba, saboda haka in Isuhu ya dawo ki fad’a mishi ni na ce a bar kayan".
Hira suka ci gaba da yi kafin suka yi sallama da Momi suka tafi.
San da Dadi ya dawo Momi ta mishi bayanin dawo da kayan da su Ummu suka yi ya nuna ‘bacin ranshi akan me yasa su Ummu suka dawo da akwatunan, nan ya dinga ma Momi fad’an akan me yasa ta masa, haka ya kira Abbu ya nuna mishi rashin jin dad’in shi na dawo da akwatin da aka yi, sai da Abbu ya dinga bashi hak’uri kana Dadi ya hak’ura.
Yaya Faruk ma da Momi ta sanar dashi dawo da akwatin da su Ummu suka yi ya nuna ‘bacin ranshi, dan shi a ganin shi tun da ya hak’ura da ni zai iya hak’ura da abin da ya min.
Dr Sadik suna ta shirye-shiryen biki kasancewar shine wanda za a fara aurar wa a gidan su, kud’i kawai ake kashe wa tun da akwai wadatar 'ya'yan banki.
Gidan su Sadik sun kawo akwatuna na gani na fad’a, daga gani an kasha kud’i wajen had’a akwatunan.
Kasancewar gidan mu an riga an da an gama shirye-shirye tun kan bikin ya koma kan Dr, k’arashe kawai ya rage.
Dr Sadik ya zo ya bani kud’in da zanyi hidimar biki da katunan da zan raba ma k’awaye na.
Halima na kira na ba ma katin akan ta raba ma wanda ya dace, ita ma sai da ta min k’orafin tafiyar da nayi.
Na kira Aisha na fad’a mata zancen bikin da ranar, ta tabbatar min da tana nan zuwa.
Na so in je gidan su Anisa mu tattauna akan bikin, amma nasan ko a kaina aka saukar da rashin kunya da kunya in iya zuwa gidan su Anisa da wannan maganar, saboda haka na tura mata text akan in ta samu lokaci ta zo.
Yaya Faruk ya kira Anisa ya mata fad’a akan shariyar da take ma yaya Khalil, ya nunar mata da laifin wani ba ya shafar wani, ya nunar mata in dan shi take mai haka ta daina dan shi Khalil bai mishi komai ba, ya k’ara nusar da ita halayen yaya Khalil nigari, hakan yasa Anisa tayi nadamar abin da tayi ma yaya Khalil duk da ‘bacin rai da kuma damuwa da halin da d’an uwan ta ke ciki yasa ta yin haka, ta ma yaya Faruk alk’awarin cewa in yaya Khalil ya zo za ta kula shi, za kuma ta bashi hak’uri akan abin da ta mishi.
Yaya Faruk yaji dad’in wannan bayanin na Anisa.
Yau biki na ya rage saura sati d’aya, yaya Faruk ne a d’akin shi yana tunanin da ya fara zaman mai jiki, duk yadda yake iya k’ok’arin shin a ganin ya daina tunani hakan ya gagara a gareshi, idan ya tuna ba shi zan aura ba hakan na k’ara sa shi a damuwa, yanzu yana ji yana gani zan auri wanda nake so bayan shi yafi cancanta da in so ganin yadda ya dad’e yana d’awainiya da so na, wannan su ne tunanin da ke addabar zuciyar yaya Faruk.
Wani abu ya tsaya mishi a k’irjin shi, daga nan sai yaji k’irjin shi ya fara mishi ciwo, tun yana daurewa har ya k’arfin shi ya fara k’arewa.
Haka ya kasance cikin wannan halin ba tare da wani yasan halin da yake ciki ba.
Anisa ce ta shigo da food flask d’in abincin dake hannun ta, ganin halin da yaya Faruk ke ciki yasa ta saki food flask d’in abincin ya watse yayin da ta fita da gudu ta koma side d’in su Dadi.
Cikin Kuka Anisa ta sanar da su Dadi halin da yaya Faruk ke ciki, gaba d’aya suka koma d’akin.
Ganin halin da yaya Faruk ke ciki yasa Dadi ya kira family Doctor d’in su, bayan ya d’auka ne ya fad’a mishi halin da yaya Faruk yake ciki, umartar su yayi da su kawo shi asibiti saboda yanzu yana duba patients ne ba zai samu zuwa ba.
Haka aka d’auki yaya Faruk aka tafi dashi asibitin da suke ganin likita, suna zuwa aka yi admitting d’in shi a wani special room.
0 Comments